Share this page
mana lectures ba, gaba ɗaya sai naji na nemi nutsuwa na na rasa shi, haka aka yi ta mana lectures amma bana ganewa. Gaba ɗaya school ɗin da ƙasar sun fitar mun a raina, kasan cewar har ranan friday babu Dr Hussain babu labarin shi, duk wanda ya ganni yaga rashin nutsuwa a tattare da ni, domin tsabar zuwa duba ko Dr ya dawo har sai da muka saba da Peter da ɗaya neighbor ɗin mu mai suna David, don kullum na je in duba shi sai mun haɗu da su, har muka fara zama muna hira da su, wataran David zai ce na fito da books ɗina ya ɗan nuna mun wani abu, don yafi zaman hiran, saboda shi David bai cika son surutu ba, don shima alama ya nuna mayen karatu ne, dukkan su suna master ne a school ɗin mu, don bayan sun gama first degree ɗin su basu tafi ba, karatun su suka ci gaba da yi. A haka kullum yamma za ka gan mu mu dukan mu ukun a zaune a ɗan wani wuri da aka saka kujerun ƙarfe, kuma wurin akwai shuke-shuke a wajen, don dama a wurin nake yawan ganin David yana karatu. Har ranan friday ban ji ɗuriyar Dr Hussain ba, kawai sai na samu kaina da kwanciya kaman mai rashin lafiya, don ranan saturday ko fita kasa yi nayi, har a kayi sallar la'asar saiga Amal ta zo a kan muje shooping, babu yadda na iya dole na ta shi na shirya domin muje. Ina shirin rufe gidan sai ga kiran Daddy ya shigo, jiki a saɓule na ɗauki wayan na kara a kunne na, ina jin kaman na saka mishi kuka. "Sweet heart! Yaya na ji muryar ki wani iri, ko ba ki da lafiya ne?". Ya faɗa muryan shi cike da damuwa. "Daddy kawai karatun yana yawa ne shi yasa nake jina kullum a gajjiye, yanzu ma har na kwanta na tuna a kwai shooping ɗin da za muje mu yi ni da Amal, shine na ta shi mu ka fito". "Sweet heart idan ba za ki iya zuwa ba ko zaki bari na gayawa Dr'n ku yazo ya kai ku? Don yanzu muka gama waya da shi yake ce mun shima yanzu haka yana hanyar dawowa gida, ina ga idan bai gaji ba ya kama ta yazo ya kai ku ko?". Ajiyar zuciya na sauƙe tare da runtse ido na, sannan a hankali na furta, "Daddy kuna waya da shi ne dama?". Dariyan Daddy naji sannan naji yana ce mun, "Kullum sai mun yi waya da shi, kuma yana gaya mun irin ƙoƙarin da kike yi, yanzu ma haka yace mun kina kula da kan ki ba ki kula ƙawayen banza ko samarin banza, kuma naji daɗin hakan, don har nace shima yana tsawatar miki idan yaga za kiyi ba dai-dai ba, duk da nasan baki da problem ta nan Humaira na". Kallon inda Amal ta ke tsaye nayi, sannan na maida hankali na kan wayan ina tambayan Daddy, "Daddy nan gidan kaji yace zai zo ko gidan wife ɗin shi?". Na faɗa ina tsoron kada Daddy yace mun can zai je. Dariya Daddy yayi sannan yace mun, "Gaskiya ni ban iya mita ba, don ban taɓa tambayan shi yaya matar shi ba, don shi ma bai taɓa gaya mun ba". Haka mu kayi sallama da Daddy, na ƙara sa wurin Amal mika wuce bakin titi domin zuwa shooping ɗin mu. MAREMAGNUM MALL na gani rubuce a gaban mall ɗin da muka je, gaba ɗaya wurin sai naji ya tafi da hankali na, domin ba ƙaramin kyau ya mun ba, cikin jin daɗi da na ji damuwa na ya ƙaurace mun na wannan lokacin, muka saka ƙafan mu cikin mall ɗin. Muna shiga Amal ta fara ɗiban abin amfanin ta, aka sari kayan maƙula she naga tana ta ɗiba, sai can kuma naga ta maida hankali wurin sayan cosmetics ɗin ta, Amal tana ɗan jan ƙafanta yau tunda muka fito, wanda alaman ciwon ta ne yake sanɗan ta, ganin kaman kayan ya fara mata nauyi, don sai ya mutsa fuskan ta ta keyi, ya saka na miƙa hannu ina mata murmushi na ɗauka mata. ita ma murmushin tayi ta miƙa mun, sannan naga tayi hanyan wurin wasu takalma flats, ganin haka ni kuma nayi wajen turaru ka. Dr Hussain? Dr Khadija economic lecturer ɗin mu ƴar india, su na gani a gaban turaruka suna zaɓan turare, gaba ɗaya Dr Khadija cikin fara'a take, ga wani azababben kyau da tayi da shigan su na sarii, wani Red colour da Golden a jiki, sai miƙo mishi su ta keyi tana nuna mishi, amma shi kuma fuskan shi a matuƙar ɗaure, kaman bai taɓa dariya ba, sai wani kakkaucewa ya keyi, gaba nane yayi mummunan faɗuwa, a zuciya ta nace. _Kaddai ita ce matar shi?_ Lokaci ɗaya na ji ido na ya ciko da hawaye, kuma ni ban ci gaba da abinda na keyi ba kuma ban tafi ba, ƙura musu ido nayi hawaye yana shirin zuba mun a ido na, ga wani zafi da bansan irin shi ba ya ziyar ci zuciya na. Kaman ance ya ɗago kan shi, caraff Sai idon mu suka haɗu dana juna, dai-dai lokacin hawayen ido na suna gangarowa, wanda ko kaɗan ban san da zuwan su ba sai dai ɗumin su kawai naji, ƙura mun ido ya yi, yadda nima ƙura mishi ido na nayi. Juyowa Dr Khadija ta yi don nuna mishi wani turaren da ta ɗauko, amma abin mamaki sai taga Dr ya ƙurawa wata ƴar ƙaramar yarinya ido, gaba ɗaya ji tayi ya ɗaure mata kai al'amuran, domin yaushe babbar mace ma ta ke ɗauke hankalin Dr ballanta na ƴar ƙaramar yarinyar nan, da ɓacin rai Dr Khadija ta juyo ta dubi Dr tace. "Me ka ke nufi ne Dr?". Ko kallon inda Dr Khadija ta ke bai yi ba, kawai ƙura mun ido yayi shima yana kallo na. Hararan shi nayi na juya na bi inda Amal ta ke, ita ma ta gama ta na nema na. Wurin biyan kuɗi muka je na a jiye mata kayan, kallo na ta ke da mamaki amma bata ce mun uffan ba ganin yadda hawaye ke bin kunci na, haka aka buga mana aka bamu total, ɗauka mata kayan nayi har inda zamu hau taxi ba tare dana ce uffan ba, ita ma ba tace mun uffan ba. Muna shiga sai gasu sun fito dukkan su ransu a ɓace, daga ganin su kasan a ɓace ran su ya ke, ƙura mishi ido nayi har muka bar wurin. Muna isa gidan Amal naga ta ɗan jumm kaman baza ta fita ba, can kuma sai ta fita tana ya mutsa fuska, a hankali na dube ta nace, "Me yake faruwa da ke ne? Naga kaman ba kya jin daɗi ko"?. Kallo na ta yi wanda idon ta gaba ɗaya sun ɗanyi kaman green kaman yellow, tana duba na fuska a ɗan ya mutse sannan tace, "sister tun da yau na ta shi ƙafa na ya ke mun ciwo, amma na sha magani, idan Allah ya yarda zai yi sauƙi". ta faɗa ta na fita cikin dauriya. Duban ta nayi nace, "sister ko dai mu tafi gida nane ki kwana? Kada na tafi ciwon ki ya tashi cikin dare, hankali na ba zai taɓa kwanciya ba idan na tafi na bar ki". Amsa mun tayi da "to", sannan muka sallami taxi ɗin, kayan na ɗauka mata har cikin gidan ta, wanda suke su biyu ne a compound ɗin, har parlor na a jiye mata kayan, sannan ta ƙira Abban ta ta faɗa mishi yadda muka yi. Karɓan wayan yayi ya mun godiya sosai, sannan muka ɗibi kayan ta da maganin ta, abin tausayi kafin mu fita a gidan sai da ts shafa wani magani mai ɗan karen zafi a ƙafan ta, wanda zafin sai dana ji shi har ido na, amma ita alaman bata ma jin zafin, haka muka fito muka tari taxi har gidan mu. *_FATIE YAWALE, WANNAN SHAFI NAKI NE KYAUTA NA BAKI SABODA KASAN CEWAR KI ƘAWAS MAI BABBAN DARAJA A WURINA, ALLAH YA BAKI ƳAN UKU SAU UKU NAKE MIKI FATA, MASOYAN ANNABI SUCE AMEEN_* *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 8📑* *__________📖* Muna fita waje ya sa ke hannu na ya na bina da harara, tsayawa na yi baki na a zunɓure ina ta ƙunƙuni ban ko kalli inda yake ba, ba mu daɗe da tsayuwa ba, ya tsayar mana da taxi mu ka wuce gidan mu. Muna fitowa a taxi ɗin ya bini da harara, ni dai bance komai ba sai murguɗa baki na da na ke ta yi, kuma ban kalle shi ba, amma nasan yana kallo na, kuma yana sane da abinda na keyi. Har na saka key ina buɗe gida na ya matso inda nake, cikin nuna iko da gadara yace, "kada na sake ganin kin shiga motan Dr nan, idan ba haka ba kuma zan mugun saɓa miki, idan kin tashi tafiya ki mun magana". yana gama faɗin hakan ya juya yayi na shi hanyar gidan. Tsayawa na yi ina bin shi da kallon mamaki, baki na a buɗe saboda mamakin shi, yana ƙarasawa gidan shi ni kuma na ɗaga murya da ƙarfi nace, "To kai ɗan'uwa na ne da za ka takura mun? Kuma sai na ƙira shi ya kaini asibiti, ai kaima na ga matar ka kake ɗauka a motan ka, ko na hanaka ne?". Tsayawa ya yi kaman ba zai juyo ba, amma ganin ya juyo yana kallo na bakin shi ɗauke da murmushi, na yi sauri na shige gida na na rufe ƙofan, don na san murmushin naugunta ne, don banga alaman na tsakani da Allah ba ne. Ganin na gudu sai ya wuce parlon shi yana ta murmushin shi. Kowan mu yana shiga yayi hanzarin ɗalewa gado, ranan da ƙyar na tashi nayi sallan asuba, sannan na sake komawa baccin, bani na tashi ba sai after 10, a razane na buɗe ido na ina kallon time, ganin da gaske haka lokacin ya yi ya sakani tashi da sauri na shiga toilet na yi brush na yi wanka, ina fitowa na ɗauki waya na na ƙira number'n Amal. Yana fara ringing bai daɗe ba aka ɗauka, naji muryan Amal a hankali ta ke mun magana, haƙuri na fara bata ina gaya mata wani irin bacci ne ya tafi dani, don sai yanzu ma na tashi daga bacci, amma tayi haƙuri me zan kawo mata tayi breakfast? Sautin dariyan ta naji sannan ta ce, "Ki kwantar da hankalinki sister, komai da ka ke buƙata asibitin suna maka, kuma already ma Dr Hussain tun 7:30am ya kawo mun break, amma yasamu ma har suna bani, so kar ki damu kan ki, kawai kizo na ganki kafin su Abbu na su iso". ta faɗa tana mun dariya a hankali. Ina ajiye wayan na wuce kitchen na haɗa tea cikin sauri-sauri, ina gama sha na fito nayi ɗaki na, shima da sauri na shirya na fito domin tafiya duba Amal, ina fitowa na harari gidan Dr Hussain sannan na murguɗa baki na, dai-dai lokacin Peter ya fito daga nashi gidan, sauƙa nayi na ƙarasa inda yake muka gaisa, yana duba na da tausayi yace, "jiya a can ki ka kwana Preety?". Dariya na ɗanyi kaɗan na ce, "gida muka dawo ni da Dr Hussain saboda hospital ɗin basu bari a kwana da patient". sai naga ya yi sauri ya duba gidan Dr Hussain sannan ya juyo in da na ke yana murmushi yace, "Dr yana kishi akan ki Preety, halan yana so ya ɗauke sister shi ba zai bari ma kowa ba". Baki na buɗe cikin mamaki ina duban shi, sannan nima na kalli gidan Dr da wuri nace, "rufa mun asiri, ni kuma mai ya kaini auren tsoho? Kasan Dr nan ya kai 40yrs kuwa, kuma baka ga matar shi mai kyau ba ce, me zai yi da ni ƴar cukala dani, kawai masifan shi ne ya sa ka ya bimu bawai so ba". Peter yana duba na da mamaki yace, "dama yana da mata ne bamu sani ba?". Zaro ido nayi na ce, "tuntuni kuna ta re da shi baku san wife ɗin shi ba sai ni dana zo daga baya? To Dr Khadija ce fa wife ɗin shi". na faɗa kaman zanyi kuka. Dariya mai ƙarfi Peter yayi sannan yace, "your not serious baby, ai Dr Khadija kowa yasan tana son Dr, amma shi bai taɓa kula ta ba ma, kuma kin bani haushi da ki ke cewa wai tafi ki kyau, ke kinsan irin kyaun ki kuwa?". Yana bina da kallo yana duba agogon shi kuma, lokacin David ya ƙaraso in da muke tsaye, idon shi cikin ido na sai bina da kallo yake yi, yana ƙarasowa yace, "Preety kinyi kyau sosai, an taɓa gaya miki babu mai irin kyawun ki kuwa"?... Da sauri Peter ya amsa da cewa, "gaya mata dai tasan irin yadda ta ke da masifar kyau, amma kyawun wata Dr Khadija yana ba ta tsoro". Ni dai yau wani daɗi nake ji a raina, saboda sun yabe ni sunce nafi kowa kyau, sannan kuma Peter yace mun Dr na ba shi bane mijin Dr Khadija, sai wani smilling kawai na ke yi, a haka David yace, "ina za kije? Ko hospital za ki koma?". Ɗaga mishi kaina nayi alaman ehh. "To bari mu kai ki, muma church zamu wuce yau sunday, sai mushiga mu duba jikin friend ɗin kin". muna shiga motan naga Dr ya buɗe gidan shi ya fito, kuma daga ganin shirin nashi na fita ne, lokaci ɗaya naji gaba na ya faɗi, a raina nace, "Allah yasa kada ya mun masifan na bi su David". har muka fita idon shi yana kan mu, nima kuma shi ɗin na ke gani. Har ɗakin da ta ke muka shiga tare da su David, suna gaishe ta suka tafi, har lokacin tana kwance ana mata ƙarin ruwa, gefen ta na matso na zauna, na saka hannu na a kan ta ina ƙara gaishe ta da jiki. Murmushi ta yi tana maida idon ta tana rufewa, alaman wani baccin ta ke shirin komawa, abin tausayi gaba ɗaya kwana ɗaya tayi wani mummunan ramewa, wani irin tausayin ta na keji a cikin raina, na daɗe ina kallon ta cikin jimami, can naji ƙira yana shigowa waya na, da sauri na ɗaga wayan don kada ta tashi. Daddy na na gani yana yawo a saman screen ɗin, da sauri na ɗauki wayan na kara a kunne na, gaishe shi nayi, shi kuma ya tambaye ni ya ya jikin Amal? Bayan mun ɗan gaisa da shi na ajiye wayan, sai naji an buɗe ƙofan ana shigowa, kafin na ɗaga kai na dube shi ƙamshin shi ya fara isowa gare ni, da faɗuwar gaba na ɗaga ido na nadubi in da ya ke, shi ma idon shi duka biyu sauƙe suke a kaina, kaman ba zai shigo ba ya tsaya ya ƙura mun ido daga in da yake tsaye, ganin haka na sauƙa a kan gadon na ƙara sa gaban shi, turo baki na nayi ina kallon shi, cikin shagwaɓa nace, "To ba kai bane kazo asibitin ba ka tashe ni ba, shi ne nima na taho ban gaya maka ba". Na faɗa ina ɗan kawar da kaina saboda irin kallon da ya ke jifa na da shi. Kukan shagwaɓa wanda babu ko ɗigon hawaye na fara yi, ina bubbuga ƙafa na a ƙasa, "to ni me na maka kake kallo na haka? Bayan nasan ban maka komai ba". na faɗa ina kallon shi. Wucewa yayi zuwa kan kujeran da suke ɗakin guda biyu ya zauna a kan ɗaya, bayan ya daina kallo na ya maida idon shi kan Amal. "Aisha baki gaya mun meye gyenotype ɗin ki ba? Tun jiya kuma na ke tambayan ki, ko kin raina ni tunda kina da su Peter ko?". Matsowa na yi in da yake na zauna a ɗayan kujeran ina kallon shi, fuska na ɗauke da murmushi, ƙasa-ƙasa da murya don kada na tashi Amal nace, "Dr mu kasan yau su Peter da David suka ce wai ina da kyau har ma nafi matar ka Dr Khadija kyau". Na faɗa ina riƙe haɓa na alaman abin ya ban mamaki duk irin kyawun ta amma a kace na fita kyau. Harara na yayi sannan yace, "saboda baki da hankali kinje kin tsaya a gaban ƙattin banza suna ce miki wai kina da kyau, ke kuma don shirme har kina biye musu kina yarda ke mai kyau ɗin ce ko? Har kina haɗa kan ki da kyawun Khadija?". Tsaki ya ja mun ya maida kan shi kan Amal da yaga tana ɗan motsawa. Ƙura mishi ido nayi ina jin zuciya ta kaman zata faɗo, don wani irin masifan zafi na ke ji, ina kallon shi kaman na tashi na shaƙe shi, murya a hankali domin rawa ya ke mun nace, "Dr'n mu don ita wife ɗin ka ce shi yasa kafi ganin kyawun ta a kaina ko? To kai me ya sa ba ka ganin ina da kyau ne? To wallahi sai na gayawa Daddy ka ce matar ka ta fini kyau". Ɗauko waya na nayi ina neman number Daddy, sai ji nayi ya ƙwace wayan a hannu na, "saboda hankali ya miki karanci shi yasa za ki ƙira Daddy a wannan shirmen banzan na ki ko? To ke me ya dame ki idan ni bance kina da kyau ba? Ba sauran wanda kike so suga kyawun ki sun gaya miki ba". "To ni kai na ke so kace ina da kyau, ai ita kana ganin kyawun ta, ni me yasa baza kace ina da kyau ba, ni kai nafi so ka faɗa". na faɗa ina zunɓuro mishi baki na. Tsaki ya ja yana duban agogon hannun shi, sannan yace, "ni ai banga kina da wani kyau ba, saboda kyawun Khadija ba ya bari na naga kyawun kowa". "Dr'n mu ba kace ina kama da Aisha ba, to ita Aishan bata da kyau ne? Ai ya kamata saboda ita kace ina da kyau, tunda ina kama da ita ai ya kamata kana ganin kyau na saboda darajan ta, kasan ko a lahira wani yakanci albarkacin wani". na faɗa ina matsuwa kusa da shi. "Yayan mu don Allah ni mai yasa baka ganin kyau na ne? Kullum sai kace Fatin Aunty Hauwa tana da kyau saboda tana kama da Aunty Hauwa, to ai nima ina kama da Ummi da Aunty Hauwa, kuma ni nafi Fatiman kyau saboda ita bata ɗauka asalin kaman Aunty Hauwa ba, ta ɗan ɗauko kaman Baban ta ai, ni ma don Allah Yayan mu kace ina da kyau mana". muryan Aisha ya ji wani lokaci Aunty Hauwa tazo da ƴar ta Fatima wanda bata fi 5yrs ba, yarinyar ta mishi kyau saboda gashin ta da Aunty Hauwa ta gyara, shi dai yana so yaga mace mai gashi sosai a rayuwar shi, shiya sa Fatiman ta mishi kyau, bai iya ya ɓoyewa ba kuma ya faɗa, shine Aisha ta ke mitan ita bai ce tayi kyau ba, wanda ɗabi'an Aisha ne ita kullum ace tana da kyau, gashi kuma yau wannan mai rikicin ita ma haka ta ke. Tunawa da hakan ya saka ya dawo da kallon shi kaina, ƙura mun ido yayi yana kallo na, can sai yace, "mai yasa ki ka damu dani sai nace kina da kyau?". Kallon shi nayi kaman zanyi kuka nace, "ni kawai kai kaɗai na ke so kace ina da kyau, kasan me yasa na ke son hakan Dr'n mu"? Girgiza mun kai ya yi alaman a'a, dariya nayi mai ɗan sauti, sannan na sunkuya ƙasa-ƙasa da murya nace, "nifa kana mun kyau sosai Dr'n mu, kuma ai ni nace kana da kyau kuma kai mai ƙamshi ne, ya kamata kaima kace Humaira kina da kyau kuma kin iya girki mai daɗi". na faɗa da yanayin kwaikwayon muryan shi, ina duban shi ina dariya a hankali don kada na tashi Amal. Ƙura mun ido yayi amma fuskan shi kaman zai yi murmushi, sai kuma ya kanne yace, "to ke in banda abin ki ta ya ya ina da khadija zan ga kyawun wata? Ni fa banga kyawun da ake cewa kina da shi ba, kawai dai suna son ki ne kuma suna son ki kwantar da hankalin ki ne kawai, shi yasa su ke yaudaran ki". "Baki na a buɗe ina kallon shi kaman na zunduma ihu nace, "Dr Khadijan da gaske matar kace? Kuma kana son ta sosai"? Tashi ya yi ya tsaya yana gyara rigan shi, alaman kuma zai tafi ne, yana duba na yace, "idan ta tashi ki gaishe ta, 2:00pm zan zo na ɗauke ki muje kiyi lunch". sannan ya juya zai fita. Da gudu na bishi har wajen, hannu na saka na juyo da shi da ƙarfi na, idona yana zubar da hawaye nace, "bana son Dr Khadijan, kuma bata mun kyau, kuma bazan bika lunch ɗin ba, babu ruwa na da kai daga yau, munyi faɗa Dr'n mu! Munyi faɗa Dr na!! Bana....". Sai kuma nayi shiru ina riƙe da hannun shi ina kuka na. "To sa ke mun hannu na tafi wurin mai sona, wanda baza ta taɓa fushi da ni ba, wanda ta ke mun kyau sosai, kema ki koma wurin su Peter suyi ta ce miki ke mai kyau ce kinji". ya faɗa yana neman zare hannun shi daga cikin nawa. "Nima ai banyi fushi da kai ba, ni bana so kaje wurin Dr Khadija ne". na faɗa lokacin Dr Abdallah yana shirin ƙarasowa in da muke. Bansan dalila ba kawai sai naji Dr Hussain ya mayar da hannun shi ya sake riƙe nawa hannun, ya saka hannu ɗaya yana share mun hawaye na, murya ƙasa-ƙasa yace, "mun shirya to, zaki bini muje lunch tare?". Ɗaga mishi kai nayi alaman na yarda, sai ya yi murmushin da ban taɓa ganin irin shi a fuskar shi ba yace "to bana son ki kula wancan balaraben Dr, kinga shi bai san ki ba, bai san Daddy'n ki ba, zai iya cutar da ke, tun da shi namiji ne ko? Saboda haka idan kina son mu shirya wataran na gaya miki abinda kike so to kada ki kula shi kin ji?". Murmushi nima nayi sannan nace, "bazan kula shi ba ko yayi mun magana zan ɗaure fuska na". na faɗa ina kwatan ta mishi yadda zan yi da fuskar, wanda abin mamaki sai gani nayi ya tuntsure da dariya, nima cikin mamakin abin da ya yi nima na yi dariyan, sannan na ce, "Kaima baza kaje wurin Dr Khadija ba yau? Kamun alƙawari ka daina ganin kyawun ta sama da nawa?". Matse hannu na ya yi da ƙarfi ya na murmushi yace, "bazan je ba yau, sai ranan da naga kin kula Dr nima zan je, kuma ba zan sake shiryawa da ke ba, su Peter ma kawai gaisawa zaku na yi, bana so kina zama da su kuna hira kinji". Ɗaga mishi kaina na yi ina murmushi, shima yimun yayi sannan ya sake hannu na ya juya ya fita, ban bar wurin ba har saida na daina ganin shi tukun na koma ɗakin. Ina shiga ya yi dai-dai da Dr Abdallah zai fito a ɗakin, Amal kuma ta na zaune an saka mata pillow ta ɗan jingina kaɗan, gefen ta kuma nurse ce a tsaye tana taimaka mata. Kallo na ya yi yana murmushi yace, "Hello Preety" Hararan shi nayi na ja baki na na yi shiru ban kula shi ba, sai naga ya yi ɗan dariya ya juya yana duban Amal, "Amal friend ɗin ki bata magana ne? Bayan yanzu na ganta a gaban tsohon saurayin ta ta na ta doka murmushi, sai ni ne zata ƙi amsa gaisuwa na?". Ya faɗa yana ƙara faɗaɗa murmushin fuskar shi. "Saurayi na kuma? Dr Hussain ɗin ne saurayi na? Baka san yana da mata mai kyau ba zaka ce mun saurayi na, ni kam".... Sai na rufe baki na tunawa da Dr yace ka da na kula shi. Amal kallo na ta tsaya tana yi, saboda a ɗan zaman da tayi dani taɗan fahimci wasu daga halaye na, don bani da ɓoye

Chapter 4 of 28