Share this page
shige cikin Ummi, sai wani shagwaɓa ta ke ta mata, akan ko ina a jikin ta ciwo yake yi ma ta, ita kuma Ummi sai rarrashin ta ta ke yi, a haka har muka iso gidan, ni dai sai bin su da kallo kawai na ke yi, don gaba ɗaya sun ban sha'awa, sai smilling na ke tayi ina kallon su. Kai gidan su Amaal ya haɗu, domin bansan yadda zan kwatan ta muku irin kyaun shi ba, duk da gidan mu yana da kyau amma tsarin ginin larabawa ba wasa bane, duk da muma daga waje Daddy ya kawo zanen da za'a mishi, amma gidan su Amaal ya ɗauki hankali na over, muna shiga parlon gidan gaba ɗaya ma sai naji ya tafi da hankali na, gaba ɗaya wani tsari ne da bazan iya rubuta shi ba a ɗan ƙaramin book ɗi na ba, sai dai kawai ku kwatantashi. ga wani ƙamshi na musamman da ya ke yi, ɗakin Amaal Ummi ta raka mu in da shima aka mishi gyara na musammam, duk yadda ɗaki na ya kai da girma na Amaal ma ya yi biyun shi, domin wani gyara da akaman sai ya baka mamaki, bed biyu aka saka amma duk da haka da sauran space a ɗakin, bamu daɗe ba Ummi tace muyi wanka mu fito parlor mu ci abinci, haka muka shiga muka yi wanka, wani riga da wando ɗan pakistan Ummi ta kawo mana muka saka, sai ƙamshi muke yi kaman daga paris muka fito. Muna kan dinning babu abinda ka keji sai ƙaran spoons, sai kuma daga parlor kana jin sautin news da a keyi a TV, gaskiya larabawa sun iya girki, idan ba wai santi ba sai nace sun fi ko wani ƴan country iya abinci, domin naji daɗin abincin da Ummi ta mana, domin duk dukiya na gidan su Amaal amma Ummi tana shiga kitchen, duk da yawan masu aiki da ke gidan amma tana saka hannu a aikin kitchen kaman wata ƴar nigeria, hakan yasa naga Amaal ta iya girki kala-kala, ga snacks da drinks iri da kala da ta iya, don bansaka girman kai ba duk sai da na koya a wurin ta, nima na gwada ma ta na ƙasan mu. Parlor muka dawo muka zauna muna ta hiran school, anan Ummi ta ke gaya mana next week Faisal ma zai zo hutun 3weeks, haka muka yita hira kaman zasu ƙashe mu. Kullum garin Allah ya waye sai mun yi waya da Daddy, yana gaya mun irin dauriyan da yake na rashin gani na, hakan zan ta bashi haƙuri, har da yace mun dabadan wani business daya sako shi a gaba ba zai tafi china, da yazo ya mun ko 1week ne, haka kullum za muyi ta hira, kuma yana gaya mun sunyi waya da Dr Hussain. Allah sarki Baby nah, kullum dare idan muna waya ya dinga ƙorafin wai rana baya gudu dare ma baya gudu, haka zan ta mishi dariya, watara na muna hira nace, "Dr mu to kaje wurin su Ummin ka mana ka yi hutu, kada kaɗaici ya dame ka kaji Dr nah". Na faɗa kaman zan mishi kuka. Kashe wayan ba tare da yace mun uffan ba, da sauri na saka hannu na rufe baki na ina tuna ranan fa yace mun kada na sa ke mishi magana su Hassan da su Abban shi, a zuciya na nace, "me yasa bana jin magana ne". Da sauri na ƙira wayan shi amma firr yaƙi ɗauka, haka na yi haƙuri na kwanta ina ta saƙe-saƙe a zuciya ta. _DON ALLAH KUYI HAƘURI BANA JIN DAƊIN JIKI NA NE._ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/20, 12:37] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 24📑* *__________📖* 2dys da zuwan mu DAMMAM Faisal ya iso, kai masha Allah wato Faisal ya ninka Amaal kyau sau babu adadi, ga wani class a tattare da shi, lokacin da na fito parlor inda suke ta murnan ganin shi tsayawa nayi ina kallon inda yake bakina ɗauke da murmushi, Amaal ce ta nuna mishi ni tana dariya tace, "Humairah" da sauri ya juyo inda nake ya ƙura mun ido yana murmushi shima. Ganin haka ya saka ni takowa zuwa inda suke cikin tafiyata kaman na tarwaɗa tsaban yauƙi daya mun yawa, wani ɗan sautin dariya ne marar ƙarfi ya ɗan suɓuce mishi a bakin shi, a hankali ya furta, "woow beautifull" sannan ya juya ya kalli Ummi yana murmushi yace, "Kai Ummi yarinyar tana da kyau da yanga, Ummi ina son yanga a wurin mace" hararan shi Ummi tayi tace, "Hummy sister ka ce fa, don haka bana son fitina". Ina ƙarasowa na mishi sallama har lokacin bakina ɗauke da murmushi, da sauri ya kamo hannu na ya jawo ni jikin shi ya rungume ni irin yadda suke gaisuwan su, sannan ya sumbaci kuncina, ba karamin faɗuwar gaba naji ba don gaskiya ni ba'a taɓa mun haka ba, gara ma Abbu da safe haka yake mana amma bana jin komai saboda shi ae uba ne, amma wannan gantsamemen saurayin fah? Ga wani ƙamshi da yake tashi a jikinshi kaman wani amaryah, cikin ƙarfin hali nake gaisheshi saboda har lokacin bai sake ni ba saidai ya ɗago ni daga jikinshi yana riƙe da kafaɗa na duka biyun, ga wani murmushi mai masifan kyau a fuskan shi. Ya kamata naji haushin abinda yamun amma sai naji na kasa saboda wani irin kyau da kwarjini da ya mun, ga shi mai tsafta ɗan gayu, ina murmushi na saka hannu na ina cire nashi da yake kafaɗa na, a hanakali yace, "kina da masifan kyau Hummy, kyaun ki mai kyau ne" gabana naji ya faɗi, gaskiya Faisal ya haɗu duk da bai kai Dr nah kyau ba, amma yau ɗaya yamun abinda Dr na ya kasa yimun kusan 4month, yau kalman da nake so naji a na yawan furta mun ni mai kyauce Faisal ya furta mun har yana wani kashe mun ido. Wucewa nayi inda Ummi ta ke zaune na zauna a gefenta , har zuwa lokacin fuskana ɗauke da murmushi, domin haka kawau Faisal ya sauƙe mun wani nishaɗi a zuciyata, gaskiya ni Humairah me kyauce, amma haka kawai nake jin son kyawawan mutane, don bana mantawa idan kakata wadda ta haifi Mamana idan tazo duk inda tayi na dinga kallonta kenan, domin ba ƙaramin kyau takeyi mun ba, gata da gashi mai tsawon gaske, bana gajjiya da kallonta, haka ita kanta Amaal bana gajjiya da ganinta domin kyau ta keyi mun, yau ɗaya naga Faisal yafi mun Amaal kyau, gashi shima yana yaba nawa kyaun. Da sauri na ɗaga kaina domin jin abinda Faisal yake gayawa Amaal, "sister dama haka Hummy ta ke da kyau shi ne baki taɓa nuna mun ita ba? bayan na biki ko a photo ne ki nuna mun ita amma kinƙi, ashe mai kyau aka ɓoye mun? gaskiya gara da nazo na ganta da kaina", ya juya wurin Ummi yana murmushi ya dafa cinyan ta yana magana cikin shagwaɓa, "gaskiya ni Ummi ina son Hummy na gaskiya bana wasa ba, gaskiya Ummi nikan dani ta dace, ko ajiye mun ita na kusa gama karatuna", ya faɗa yana kwantar da kanshi kan cinyan Ummi, idon shi kuma duk ya sauƙe mun su, sai wani kashe mun ido kawai ya keyi da zaran mun haɗa ido, nidai kunyan shi kawai nakeji, sai wani smilling mai ɗauke hankali na ke tayi. "Baka isa ba wallahi bros Faisal, ta yayah ma zanyi wa Dr Hussain haka? gaskiya toh wasan ma ya isa haka, bayan Hummy da Dr sun amincewa junan su, gaskiya kabar maganan nan bazai taɓa faruwa ba", ta faɗa tana miƙewa tsaye, idon ta akan Ummi tace "Ummi ki gaya mishi gaskiya ya dai na irin haka, ni bazai saka naji kunyan Dr ba", sannan ta kamo hannu na tace, "mu tafi ɗaki hummy". Miƙewa yayi shi ma yana hararanta yace, "wallahi sis baki isa ba, kinsan haka ta ke shi ne zaki wani sako ni acikin shirmenki, toh ni ma ae namiji ne saidai kowa ya gwada jarumtar shi, wanda yayi nasara Humairah ta zama rabon shi, kuma kibar yarinya ta zauna a inda ya mata bawai ki kai ta bedroom ki kulleta ba", ya ƙarasa faɗin maganan yana kamo hannu na, da sauri na juyo na dubi Ummi da ta zuba mana dukkan idonta akan mu bakinta a buɗe, maida kallo na nayi kan shi amma da sauri na kawar da kaina ina ƙoƙarin ƙwace hannu na, domin ni ban san me nake gani a cikin idon shi ba, gashi bana son ya riƙe ni amma kuma bani da ƙarfin gwiwan hana shi, narai-narai nayi da ido alaman zan mishi kuka domin nakasa ƙwace hannu na. Sun kuyawa yayi dai-dai kunne na yace, "kada ki tafi da bugun zuciyata ya ke ma'abociyar kyau na duniya, nafi son na dinga ganin kyakkyawan idon ki da ɗan ƙaramin bakin ki mai matuƙar tafiya da hankalina a kusa dani ya mai kyau", wayyo Allah jina nayi numfashi na yana shirin tafiya lokaci ɗaya, abin na kwace hannuna daga nashi sai na samu kaina da ƙara damƙe hannun shi cikin nawa, wanda bansan dalilina nayin hakan ba. Ganin haka ya daka Ummi miƙewa da sauri tace, "sakar mata hannu fav, baka san abunda kake yi mata ya saɓawa shari'an musulunci ba, ko ce maka akayi hannun Amaal kake rike da shi? bana son sakarci, sake mata hannunta ta bi ƴar'uwarta". Da sauri ya sa ke mun hannu yana sauƙe numfashi kaman wanda yayi gudu, ya juya yana kallon Ummi cike da shagwaɓa yace, "haba mana Ummi!! nifa wallahi bazan cutar da ita ba, kawai ki gane Ummi sonta fah na keyi over", bayan ya saka hannu yana wani dafa ƙirjin shi kaman wanda yake jin wani ciwo a wurin. Hararan shi cikin so da ƙauna Ummi tayi, sannan ta buɗe mishi hannu alaman ya taho gareta, da sauri yaje ta rungume shi ta wani bubbuga mishi bayan shi kaman wani yaro ƙarami, murya ƙasa-ƙasa ta ke rarrashin shi, "haba fav kasan fa Humairah amana ce a wurin mu, yayah karon farko zaka fara riƙe mata hannu kana jawota jikin ka? Kuma kasan akwai wanda sukayi alƙawarin aure kuma ya maida mu kaman iyayen shi, ae bai kamata mu baka daman ka so ta ba, saboda bazai ji daɗi ba kuma bazai yadda damu ba a gaba, kayi haƙuri farin cikina Allah zai baka wacce tafi Humairah insha Allahu". bamu jira munji mai zai ce ba Amaal ta jawo hannuna da sauri muka wuce ɗakinta, muna shiga ta fara masifa kaman zata mare ni, "haba Hummy ki zama very careful da ɗan'uwa na domin kada ki bari yaje ya ɗauke hankalinki akan Dr, don wallahi Dr bazai taɓa yafe miki ba, kuma nima zaki sakani jin kunyan shi, don wallahi tsab Faisal zai gama da zuciyar ki acikin kwanaki kaɗan", ta faɗa tana hararana. Murmushi nayi ina duban ta, a hankali na zauna a kusa da ita na saka hannu na riƙo nata hannun nace, "nikan Amaal kibar tunanin akwai abinda zai ɗauke hankali na akan Dr, ni ina yiwa Dr son da ban taɓa tunanin wata mace tana yiwa wani ɗa namiji ba, kai ko tunanin wani zai ɗauke hankali na akan Dr bana yi, saboda haka ki kwantar da hankali ki besty nah", na faɗa ina bin ta da murmushi. "Hmmm bazaki fahimta bane, wallahi bros Faisal tsab zai ɗauke hankalin ki domin yasan yadda zai nuna miki kulawan da baxaki iya tunawa da wani ba bayan shi, nifa ɗan'uwa nane kuma nasan halinshi akan abinda yaga yana so, don ko abu yake so a mishi yasan yadda zai ɗauke hankalin su Ummi da Abbu su mishi babu shiri, kedai ki maida hankali kawai, bana son kina bashi haɗin kai ko yazo inda kike kinji", ta faɗa tana duban cikin ido na. "Ashe baki sona da alkhairi ko ƴar'uwata? wato kin fi son farin ciki wani bari akaina ko Amaal? toh bana so ki zugata kibarta tayi amfani danata baiwan ta zaɓi wanda yayi mata bawai sai kin mata shishshigi ba", Faisal ya faɗa ya na tahowa inda muke shima ya zauna a kusa dani, sannan ya dawo da hankalin shi kaina. Yana murmushi ya saka hannun shi ya riƙo nawa, ido na nayi saurin buɗe su a kanshi, amma sai na kasa ce mishi uffan domin yadda naga ya runtse idon shi bayan ya riƙe dukkan hannuna yana ta matsa mun yatsuna a hankali a hanakali, da sauri na dubi Amaal da ta buɗe baki tana kallon ɗan'uwanta. "Mine kice mun wani abu mana da daddaɗan muryanki hankalina ya kwanta", yana wani langwaɓe mun kaman mai yaron da yake shirin shan nono, murmushi nayi na ɗaga idona ina kallon shi, a hankali na buɗe bakina nace. _Toh ina team Dr, ku fito kada Faisal ya ƙwace muku Hummy, don jikina ya fara sanyi da al'amarin Faisal, amma bari mujira muji yyh zata kaya a tsakanin su_ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/24, 04:59] Miss Xerks🌺: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* _jin kanta ta ke ta musamman saboda farincikin dake ratsata gata ga Sadauki idanuwan ta raɗau tana kallon kowa. Sadauki ya kasa tantance yanayin da ya ke ciki don bai taɓa shiga irinsa ba. farin-ciki ne ko kuma tausayi? ko dai zuciyar sa ke yaudarar sa akanta?_ _yanzun ma farfesun kifin ta ke ta tsaƙura tana ci tana tunanin ko a wanne hali yanzu ya ke ciki ? kar dai yana cen tare da ƴan iskan mata ? ko kuma yana cen yana shan giya ba, ajjiye hannunta ta yi ta fasa cin kifin hankalin ta amatuƙar tashe. tana son shi, ko ayaya zata iya rayuwa da shi ko da abinda yake aikata wa ya fi haka muni._ _"Jasra kin amince da hakan? kina so na ?" ɗaga kai ta yi tana zabga murmushi. "a a, magana za ki yi." Sadauki ya ce yana jin wani irin ƙwarin gwiwa. "na amince." kasa tsayuwa Madaki ya yi maganarta ta dakar masa zuciya. hakan ya sa ya jinginar da jikinsa da ya ke jinsa tamkar ƙwarangwal saboda tsananin shafal da ya ke jin kansa._ _"kin ga mutumin ki ya zo ko ? yana cen kullum yana tare da mata a gidajen giya kin san garin nan komai na zunubi suna aikata shi, ban san inda ya sauka ba saboda yana tsoron kar na je naga matan da yake mu'amala da su......"._ *ZAIBA! ZAIBA!! ZAIBA!!!* na ƙara ce maku *ZAIBA* ku neme shi ku karanta kar da ku bari a baku labari, rashin karanta shi kuma zai sanya ka yi takaicin hakan. *SHAFI NA 25📑* *__________📖* "me kake so kaji? Bayan kasan kai ɗin yaya nane, akwai abinda ya fi shi girma ne a wurina"? na faɗa bayan na xare hannu na daga na shi ina binshi da kyakkyawan murmushi a fuskana. Juyar da kanshi yayi alaman yayi fushi, "gaskiya ni bazan taɓa amincewa da wannan hukuncin ba, kawai da ne kike ƙanwata da ban ganki ba, amma yanzu nima zuciyata ta amince da miƙa miki ragamar rayuwata, saidai kawai idan baki sona ki fito fili yau ki gaya mun, don bana barin ɗakin nan sai naji abinda ke zuciyar ki game da ni", ya faɗa yana ƙara ɗaura hannun shi saman kafaɗa na, ya kuma ƙura mun idon shi masu masifan haske da kyau akaina. A hankali na sauƙe a jiyar zuciya, sannan na ɗago ido na na dubi Amaal alamar neman a gajinta,... Tsaki taja ta harare ni, "common my friend ki gaya mishi gaskiyan yadda ya ke a mine ɗinki, kawai kina da wanda kukayi alƙawarin aure da shi, wanda sanadin soyayyan da kike mishi ne muka sako shi a rayuwar ki don ya kawo mana a gaji bawai shima ya dawo yace yana sonki ba", ta faɗa tana wani abu kaman zata zo ta yanka mun mari. "Don Allah kibar shirmen da kike yi a wurin, idan ba zaki iya zama a wurin ba ki fita ki bamu wuri, so kam zata soni, me zatayi da mutumin da ya kusa haifanta, kuma bai damu da miƙa mata soyayyan shi gaba ɗaya zuwa gareta ba", yana gama hantarar Amaal ya juyo kaina cikin sassauta murya, "plzz mine kiji dani mana". Ɗaga mishi kaina nayi ba tare da na furta komai ba, sai dai murmushin da bai bar kan fuskana ba nakeyi, "nikan mine ki buɗe baki kimun magana kada zuciyata ta fashe, wallahi ina miki son da zai iya halakani a yau ɗaya, plz kice wani abu mana dear", ya faɗa yana damƙe kafaɗa na da ɗan ƙarfi sosai. "Na amince muyi soyayyah amma bance maka zan aure ka ba, domin nayi alƙawarin auren Dr", na faɗa ina juyar da idona kan Amaal. Mtssss taja tsaki ta kalleni cikin ƙanƙance ido, "wallahi sis babu ruwa na nikan baza ki sakani jin kunyan Dr ba, kuma ke kaɗanki kiyi shirin amsan tuhuma a wurin shi, kada ma ki yadda ki sako ni a ciki, amma kin ban mamaki Hummy, ashe akwai wani sauran ɗa namiji da zai ɗau hankalin bayan idon Dr"? Ta faɗa tana bin mu da kallon banza daga ni har Faisal ɗin. "Get out my friend, ki fita a ɗakin nan ki bamu wuri, ke wacce iriyar ƴar'uwa ce wanda bata kishin nata ɗan'uwan sai wani daban da a sama kika sanshi, kuma kije ɗin itama bazata nemi taimakonki ba, shi ma ya sani wannan flower mai kyaun ae bazai zama ta shi bace shi kaɗai, dole muma mu so ta, Allah ya bawa mai rabo sa'a kawai, fita kibani wuri kafin na tashi nazo inda kike yau kiyi kwana hospital". Kuka Amaal ta fara yi, wanda daga gani na ɓacin raine, tana duban shi tace, "bros don tsabar son kai irin naka na rashin gaskiya shi ne kake fatan ka tashi ka dake ni har nayi kwanan hospital? Wallahi sai na faɗawa Abbu abinda kake shirin yi na rashin amana", sannan ta ƙarasa bakin ƙofan ta riƙe tana kallona tace, "ke kuma idan baki rabu da shi ba sai na gayawa Dr kuma yanzu ma zanje na haɗaki da Ummi, kuma babu ruwa na da ke, bana son ƙawa da ke tunda baki riƙe amana" ta juya ta fita cikin ɓacin rai. "Bros toh kayi haƙuri mu bar wannan maganan, kaga ran Ameel ɗita ya ɓaci, ina tsoron taje ta gayawa Dr Hussain zaiji haushi na, don Allah kayi haƙuri". Yana wani murmushin da ba kai ciki ba yace, "bafa zan taɓa haƙuri ba, domin sonki shi ne rayuwata, kina son ganin bana a raye ne"? Juya kaina nayi alaman a'a, "toh ki bar ni a yadda nake so, mai rabo ya samu cikin mu" ya faɗa yana tashi tsaye. Hannun shi cikin aljihun wandon shi ya ƙura mun ido bakin shi ɗauke da murmushi, nima ƙura mishi idon nayi domim wani irin kyau Faisal yake mun, ga shi da wani ƙwalisa kaman shi kaɗaine namiji a saudi, murmushi na sakeyi da naga yadda yake wani bina da kallo kaman zai lashe ni, ina kallon yadda yakeyi yasa naji kunya na sunkuyar da kaina ƙasa ina wasa da yatsuna. "Ki shiryah da yammah na kaiki yawo kiga wurare, yanzu zanje naci abinci na kwanta na huta ko ƴanmata na", ya faɗa yana fita a ɗakin. Buga ƙofan da ƙarfi ya saka ni ɗago idona da sauri, Amaal ce kaman a wani jehota ta faɗo ɗakin, sai harara ta ke sauƙe mun, tayi kaman zata yi magana kuma sai ta fasa ta juya ta fita ta bar mun ɗakin, ajiyan zuciya na sauƙe ina taɓe baki na ɗaga kafaɗa ta alaman ko a jikina, kallon wayata nakeyi cike da tsoro, ganin number Dr nah da yake yawo a saman screen ɗin, har ya yanke ban iya na ɗaga ba, a karo na biyu wani ƙiran ya sake shigowa, bansan lokacin da naji zufa a jikina ba, chan cikin zuciyata ina raya kodai Amaal ta gaya mishi wani abu ne? har zai yanke shima da ƙyar na ɗaga. "Hello" na iya faɗi ba tare da wani kuzari a jikina ba, daga ɗaya ɓangaren naji shi yana cewa, "yes hello baby, yayah naji voice ɗinki kaman kina bacci na tashe ki"? Da sauri na gyara zama na da muryah na nace, "bansan na fara baccin ba yanzu fah na ɗan kwanta", na faɗa ina jin bugun ƙirjina yana ƙaruwa. "toh ina Amaal ta tafi ta bar mun ke? Nifa idan bazata baki kulawa ba zan taho na ɗauke abuna kawai muje Daddy ya mana aure, don nafi so ni da kaina na dinga baki kula baby, ki gaya mun bata baki kulawa ko"? lokaci ɗaya naji tausayin Dr nah cikin zuciyata, runtse idona nayi sannan nace "lahh Dr na muna tare da uta fa, sai da taga na rufe ido ne inaga ta bar ɗakin, amma Amaal tana bani dukkkan kulan daya kamata har ma ina jin nauyi da kunyan yadda suke mun, ka kwantar da hankalinka babyn baby", na faɗa ina ɗan fitar da muryana don hankalin shi ya kwanta. Ajiyan zuciya ya sauƙe da ɗan ƙarfi, sannan yayi ƙasa da muryah yace, "baby komai na duniyan nan yayi mun zafi, ashe bansani ba mun shaƙu haka? Gaskiya baby na gajji da kaɗaici, next week insha Allahu zan zo na dubaki, idan yaso ko 1week sai nayi mu juya tare, don na gajji wallahi baby, ko ina baya mun daɗi", ya faɗa kaman zaimun kuka. Dariya nayi a hankali nima cikin kewan shi nace, "baby toh ae da sauran hutun mu, kuma inajin daɗin wurin wallahi, kawai kaima kazo mu zauna har sai mun gama hutun tukun mu tafi gaba ɗaya", na faɗa ina dariya. Shima dariyan yayi, "haba baby bakijin kunya dukkanmu muje mu taru musu a gida? ae suma zasu kuremu, nidai zanzo nayi 1week, kuma a hotel zan sauƙa ba a gidan ba". "Baby meyasa bazamu zauna wuri ɗaya ba? Nikan da kai nake son zama baby", na faɗa ina masa kukan sakalci. "idan kina son mu zauna wuri ɗaya ae babu matsalah baby, kawai zanje na gayawa Daddy mun amince aure muke so, sai kawai a ɗaura mana mu zauna a gida ɗaya tunda kema yanzu kina son hakan", ya faɗa yana dariya. Da sauri nace "nifa bance aure zamuyi yanzu ba baby, kawai nafi so mu zauna wuri ɗaya ne dakai", na faɗa ina zaro idona don ganin Faisal daya buɗe ƙofan ɗakin ya shigo. Kai tsaye inda nake zaune ya taho fuskan shi a ɗaure, ni dai zuba mishi ido kawai nayi ina ganin ikon Allah, daga cikin wayan kuma inajin dariyan da Dr nah yake ɓaɓɓakawa, abin tsoro da mamaki kawai jin Faisal nayi ya hau kan gadon ya ɗaura kanshi akan lap ɗina, sannan ya ɗauki ɗayan hannu na ya ɗaura akan shi yana shafa kan nashi da hannuna, kuma ya wani runtse ido kaman maijin bacci, ga wani ɗan ubansun ƙamshin da yake tashi a jikin shi, wanda lokaci ɗaya naji yana sanyaya zuciyata daga bugawan da tafara daga farko. "Baby tunda kina son mu zauna wuri ɗaya ae kawai aure ne ya kamace mu, domin gudun kada Baby yayiwa babyn shi ɓarna, azo ana cewa ba haka aka soba, kinga zance ya lalace *_ƘADDARA TA RIGA FATA_* kenan, wanda ba hakan za a so ba, so kawai muyi haƙuri na zauna a hotel ɗin ko baby nah". kasa bashi amsa nayi saboda yadda Faisal ya saka hannun shi yana ta matsa mun cinyoyina kuma yana mun wani tafiyan tsutsa, runtse ido na nayi bansan

Chapter 13 of 28