ni, sannan ya maida kanshi kan tuƙin da ya ke yi yace,
_*KU KASANCE AKO YAUSHE DA ALƘALAMIN AUNTY NICE DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA, TSAKANIN DR HUSSAIN DA HUMAIRA, SANNAN KUMA KU SAMU SANIN WACECE AISHA?*_
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
_*SADAUKARWAR PAGE ƊIN NA KUNE, HAFSAT ISAH PZ & HAUWA MUSTAPHA JAJERE A (Gaskiya Fans H) KUYI YANDA KU KE SO DA SHI, INA JIN DAƊIN YANDA KU KE SON WANNAN NOVEL ƊIN, SABODA HAKA MA BESTY NAH (Miss Xerks) TA CE NA GAISHE KU BOHOT-BOT... Kuji daɗin karatu lafiya.*_
*SHAFI NA 12📑*
*__________📖* Daga Abbu har Ummi sun ji daɗin karrama su da na yi musu, bayan munga ma dinner ta re da su, Abbu ya maida hankalin shi kan kallon News da ake yi na ƙasan, ni da Ummi kuma kaman wanda mu ka shekara muna tare, sai hira muke yi na rayuwar Amal da irin wahalar da ta ke sha.
"Ummi to me zai hana Amal ta dawo wuri na mu zauna tare? Saboda yanayin ciwon ta ina ga bai dace ta zauna ita ɗaya ba, saboda wataran ina ga baza ta iya samun sararin yiwa Dr waya ba, ko me ki ke gani Ummi?".
Na faɗa ina matsawa jikin ta, tsabar samun wuri irin nawa, dama asali ni mai son naga ana nuna mun kulawa ne, domin duk ranan da kaka ta tazo gidan mu ko naje wurin ta, sai Daddy yayi ta mana shari'a, zata yi ta mitan ina tumurmusan ta, amma ina primary 6 Allah ya yi mata rasuwa, Allah ya jiƙan ta da rahma.
Abbu ne ya juyo ya ƙurawa Ummi ido don jin mai za ta ce, amma sai Ummi naga ta sunkuyar da kanta ƙasa kaman mai tunani, har tsawon wani lokaci sai ta ɗago tace,
"Humaira ba wai naƙi shawaran ki bane, iyayen ki ina ga ba lallai ne su yadda ba, and secondly kuma ciwon Amal ba ita kaɗai ba, duk wanda ya raɓe ta ma sai ya sha wahalar jinya, keda aka kawo ki karatu, ai bai kamata mubar ki da jinyan Amal ba".
Ummi ta faɗa tana share guntun hawayen da ya biyo idon ta.
"Ummi Daddy na ba shi da matsala bazai hana ba, shima kullum sai yace tausayi na ya keyi na zama na ni kaɗai, kawai babu yadda ya iya ne, ciwon Amal kuma kawai nawa idan ya tashi ne na ƙira Dr ya tafi da ita asibiti, tun da asibitin su ba zama akeyi a wurin ba, ba kai musu abinci akeyi ba, komai acan ake musu, kinga ai babu wani matsala, bana son ta zauna ita ɗaya ne".
Abbu ya yi gyaran murya yace, "Humaira bani number shi mahaifin kin, nima nayi tunani irin naki tun da muka shigo gidan nan, idan Allah yasa ya amince ni zan fi samun kwanciyar hankali ma".
ya faɗa yana miƙo mun wayar shi.
Da sauri na amshi wayar tsabar murna jiki na har rawa ya ke tayi, number Daddy na juye mishi, na miƙo mishi ina ta murmushi.
Bai daɗe wayan yana ringing ba naji muryan Daddy yana sallama, alamar ya ɗauki wayan, Abbu ne ya fara gaishe shi, sannan ya mishi bayanin shi ne mahaifin Amal ƙawar Humairah, Allah sarki Daddy daga muryan shi za kaji yaji daɗin ƙiran da Abbu ya mishi, tambayar jikin Amal ɗin yayi, Abbu cikin farin ciki da jin daɗin an nuna kula akan ƴar ta shi ya amsa da sauƙi, sannan Abbu ya gayawa Daddy manufar ƙiran shi da ya yi.
Daddy ma ya nuna jin daɗin shi in da ya ke cewa Abbu ai daman kulum zama na ni kaɗai tausayi na ya ke ji, don ma ya bada amana na wurin Dr Hussain ne ya samu ɗan sauƙin tunanin abun, amma ai bakamar yadda zasu zauna su biyu ba, don kuwa zata daina jin kaɗaici, kuma za suyi karatu tare.
Daddy yace mishi kuma zai yi bayani wa Dr Hussain ya saka musu ido sosai a rayuwar su da kuma karatun su, duk da kullum alkhairin mu yake gaya mishi, shima Abbun yace insha Allahu kafin ya tafi zai sake samun Dr Hussain ɗin, haka suka yi sallama kaman wanda su ka daɗe da sanin juna.
Kallon mu Abbu yayi yana murmushi, ya jawo flask yana zuba shayi mai cike da kayan ƙamshi, irin su citta da su kanamfari,
"wato Humaira ina ga a wurin mahaifin ki ki ka gaji karamci, mutumin nan bai san wacece Amal ba da kuma iyayen Amal amma ya amince ku zauna tare, domin shi ɗin ɗan halak ne".
sannan ya mana bayanin duk yadda su kayi da Daddyn, kowan mu sai farin ciki ya ke yi.
Ina kallon Ummi nace, "Ummi gobe zanje na kwaso kayan Amal ɗita, ina dawowa a school".
Ummi tana mun dariya ta ce, "ki bari mana a sallame ta sai kuje tare, Ke kam ai gobe school ya kamata kije ki nutsu ki maida hankali a abinda za'a muku, ɗebo kayan kuma sai kubar shi sai weekend ko".
Ɗaga kai nayi ina murmushi, sannan na ɗauki wayana da ake kirana, ganin sunan Dr Hussain sai ya sakani tashi na wuce bedroom ɗina.
Kan bed ɗin na hau na kwanta sannan na ɗauki wayan da ya sa ke shigowa a karo na biyu, manna shi kawai nayi a kunne na ba tare da nace uffan ba, sautin murmushin shi naji, sannan naji yace,
"Babyn baby muna faɗa ne?".
Turo baki na yi kaman yana kallo na, yadda kasan jikar kulu idan sun haura da amininta Hussain 80k, na yi magana ƙasa-ƙasa nace, "to ba kai bane ba".
"To kuma ba ke bace ba".
ya faɗa yana kwaikwayon murya na.
Dariya nayi a ɓoye ina rufe baki na, ya sa ke cewa,
"kawai sai kice mata na kaman kwandon wanke-wanke, bayan irin kyawun ta da na ke gani bana tuna ita ɗin gajeruwa ce, amma yau kinsa na fara tunawa ashe fa da kaɗan tafi kwandon wanke-wanke".
Ina dariya na ce, "Dr'n mu zaka daina son ta kenan?".
"Idan na daina son ta wacece zan so? Ko zaki sama mun wata?".
Rufe ido na yi ina jin daɗin da ban san meye dalilin shi ba,
"To kace mun bata da kyau, kuma ka dai na son ta".
"Tun da ki ka ce mun kaman kwando ta ke, sai na daina son ta, kuma na daina ganin kyawun ta".
ya faɗa shima yana jin daɗi da wani nutsuwa a ranshi daga in da ya ke.
Dariya na dingayi na daɗi wanda har sai da naji Dr ma ya fara dariyan, don yadda na kasa dainawa, ina wani jin daɗi a raina.
"Hummy'n mu kina jin daɗi ne?".
Ya tambaye ni murya a hankali cikin nutsuwa.
"Allah Dr'n mu yau daɗi na ke ji sosai, to yanzu zaka daina zuwa gidan ta ko? Kuma idan nayi kwalliya za ka ce ina da kyau?".
Rufe idon shi ya yi daga in da ya ke yana ta murmushi, shi kanshi ya rasa yau wace irin rana ce a wurin shi mai girman gaske, shi fa ko lokacin da yake tsokanan ƙanwar shi Aisha baya samun jin daɗi da nutsuwa irin yadda ya keji yanzu idan ya zolayi Hummy, ɗari bisa ɗari Hummy ta canja mishi tsarin rayuwar shi, da ko kaɗan baya jin sakewa a zuciyar shi, idan bai yi ƙarya ba ya kan yi good 1yr wani abu bai saka shi dariya ba, amma yanzu kullum ne, kuma ko wani lokaci sai ya yi dariya ko da shi kaɗai ne idan ya tuno ta a ranshi, yanzun ma wani dariyan yayi sannan yace.
"To ai ke yarinya ce Hummy, bazan iya ganin kyawun ki ba yanzu, ki bari sai kin girma sai na duba naga kina da kyawun, abu ɗaya kawai nasani yanzu, Hummy ta mai hankali ce, Hummy ta mai baiwar ilimi ce, Hummy ta mai sakalci da shagwaɓa ce, Hummy ta mai rikici na, wanda kullum sai ta birkita ƙwaƙwalwar Dr ta da rikici".
"Uhmm ni kan ban yadda ba, wallahi na girma Dr ni kam kace ina da kyau, kace na fi ko wacce mace kyau, Allah Dr'n mu har na kusa iso ka tsayi fa, idan na ƙara 2yrs fa tsayin mu zai zama ɗaya".
Yana murmushi mai sauti yace, "to mu bar shi ya kai 2yrs ɗin sai na gaya miki a lokacin".
"To bazan sa ke kula ka ba sai lokacin, kuma kaima ba za ka sake kula kowa ba, sai ka jirani har lokacin".
ta faɗa kaman zata mishi kuka ta wayan.
"Wayyo Baby idan kin daina kula ni a mutuwa zan yi, kullum kuka zan ta miki fa Baby".
ya faɗa shima yana kwaikwayo na.
Dariya ya sa ka ni sannan nace, "Ba zaka mutu ba insha'Allah sai na girma kace Humaira ta fi sauran mata kyau, Humairah tafi ko wacce macce iya kwalliya da girki, Hummy kin fi Aisha kyau".
na faɗa ina rufe baki na.
Shima dariyan ya fara yana cewa, "Hummy har Aisha'n mu baki so nace ta fiki kyau? Lallai ina da aiki a gaba na, anya zaki bar ni na kalli wasu matan kuwa? Hala daga ranan da nace kin fi kowa kyau to ƙwalele na da ganin kowacce mace ko?".
Ina dariya na ce, "Dr'n mu na fiso kai ta ganin ni kaɗai ce mai kyau a duniya, duk ranan da kaga kyawun wata to mutuwa zanyi".
na faɗa mishi jiki na a sanyaye.
Ajiyan zuciya ya yi bayan ya daɗe dayin shiru,
"Hummy na miki alƙawari duk ranan da nace kinfi sauran mata kyau to bazan sa ke ganin wata nace tana da kyau ba, bazan so ki mutu na zauna a duniya ba bu ke ba, na fi so na riga ki mutuwa, don ke nasan za ki iya riƙe mun yara na ko bayan bana duniya ko Hummy nah".
"To ai baka kawo mun su nagan su ba".
na faɗa ina mishi shagwaɓa.
Dariya ya yi yace, "Hummy kema ai bai wuce na yi rainon ki ba, shiyasa bazan kawo miki nawa yaran yanzu ba, don zasu haukata mun ƴar Baby na da na su irin rikicin, ni kuma yanzu karatu na ke so Baby'n baby ta yi".
"Ni dai naƙi wayon, ka kawo munsu a weekend, wallahi ina son yaran ka Dr".
"Nasani ai Baby, duk duniya ai babu wacce zata fiki son ƴaƴana sai dai Ummi na ta biyo bayan ki, amma bana son yanzu su wahalar mun da ke ne, don nafi damuwa da kiyi karatu sama da kula mun da yaran".
"Kana nufin ko Maman su ma na fita son su"?
"Kema ai Maman su ce, ko baki so suce miki Mama?".
Ina dariya na ce,
"kasan me nake so suce mun"?
"sai kin faɗa".
Ina dariya nace, "Mamie, saboda idan na girma na yi aure na haihu haka na ke so yarana su ce mun Mamie".
na ci gaba da dariyan alaman naji kunya.
Shiru ya yi na wani lokaci, sannan yace, "ni kuma Abbie ko? Hummy kin taɓa son wani ne a zuciyar ki?".
Shiru nayi, daga baya nace, "Dr ni ban san ya ya ake jin soyayyan ba, ai sai na girma tukun nasan yadda ake soyayya, kasan Daddy baya bari na naje ko ina, don baya son a cutar dani yace mun, kaga ni ko friends da maza ya hanani, ni kai kaɗai na taɓa sabawa da kai bayan Daddy na, sai na girma idan nayi saurayi zan gane, ko zaka gaya mun yadda akeyi tunda kai ka taɓa yi?".
"Irin wanda ki ke yi yanzu".
Dariya nayi nace, "Dr ance maka ina soyayya ne? Nifa bana kula kowa, kuma zaka na gani, Dr Abdallah ma da kace kada na kula shi, ai ɗaure fuska na na keyi kaman na zama Boss".
Dariya ya yi tayi wanda har nima sai da na fara taya shi, a ƙarshe nace, "Dr'n mu yaushe za kaje wurin su Aisha?"
Lokaci ɗaya naji ya yi ɗiff bai ƙara cewa komai ba, magana nayi ta mishi amma bai kula ni ba, har sai da na fara mishi kuka tukun yace mun,
"kada ki ƙara gaya mun haka, ke baki son na zauna da ke ne"?
Ina share hawayen ido na nace, "ina so Dr, ai na tambaye ka saboda bana son ka tafi ka bar ni ne".
"Insha'Allahu bazan bar ki ba har iya ƙarshen rayuwa ta, sai dai ke idan kin guje ni".
Murya ta tana rawa a hankali nace, "Dr nah! Bazan taɓa barin kaba, ko aure nayi da kai zan tafi, bazan bari mu rabuba har abada muna tare".
"Bazan biki gidan mijin ki ba, saboda idan ya ɓata miki rai zan ƙarasa shi, kawai mu zauna tare, ko na miki tsufa?".
"Ni bana ganin ka tsufa, ni kyau ka ke mun sosai, kuma kana burge ni, kai kaɗai na ke son na dinga gani kullum, na fasa auren ma, da kai zan zauna, amma kai ma ba zaka auri kowacce mace ba, mu kaɗai zamu zauna tare".
Tashi Dr ya yi daga kwancen da yake ya riƙe kanshi, idon shi a lumshe yace, "me ki ke ji a kaina Hummy"?
Nima tashi nayi na zauna kaman zanyi kuka, don na rasa ni mai na keji ne yau akan shi, ina jin kaman zuciya ta zata fito, kuma na kasa gane yanayin da na ke ciki, a hankali nace,
"Dr nah! Ni kan kazo wuri na yanzu".
na faɗa kuka yana kuɓuce mun mai ƙarfin gaske.
Dafe kanshi ya cigaba da yi da ƙarfi ya furta, "ya Rabbi".
a zuciyar shi yace, "wayyo Baby nah kin yi nisa ya ya zan miki ne ni Aliyu Hussain".
Shima hawayen ya samu kanshi yana fito mishi.
"Dr kazo".
"Baby kwanta kiyi bacci gobe akwai school, zamu ƙarasa maganan gobe".
"ni kam naƙi Dr'n mu, to zuciya ta tana mun ciwo, zan gayawa Daddy yazo ya kaini asibiti".
na faɗa ina kuka.
"Kada ki gaya mishi, ki bari gobe zan kawo miki wani magani zaki daina ji, rufe idon ki na gaya miki wani abu".
Da sauri na rufe, amma sai naji yana mun waƙan wani tsohun film ɗin india, wanda yawanci na kanji Daddy yana jin shi amma ni bai taɓa mun daɗi ba, amma yau sai naji daɗin shi kaman zai saka ni kuka, wani tsohun waƙa ne da Amit ya yi na film ɗin *KHABI KHABI*.
*©AUNTY NICE CE*✍🏼
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
_*MAMAN ABDALLAH*, *MAMAN BASH*, *SA'EEDA SADIYA* *NA GASKIYA FANS D, WANNAN SHAFIN NAKU NE, DOMIN TUKWAICIN IRIN ZAFAFAN COMMENT DA NAKE GANIN KUNA MUN AKAN WANNAN NOVEL, NAGODE ALLAH YA BAR MU TARE, IDAN BA KU BABU BOOK.*_
*SHAFI NA 11📑*
*__________📖* Tun da na idar da sallan ban tashi a wurin ba, har lokacin ishaa yayi na tashi na fara yin sallan, ina cikin yin shafa'i da wutiri naji ana shigowa cikin ɗakin, ina cikin sujuda naji muryan su Abbu da Ummi, suna gaisawa da Amal, daga baya kuma naji Dr Abdallah ya musu sallama ya bar ɗakin.
Ina idar wa na juyo fuska na ɗauke da murmushi ina gaishe su, kaman wanda muka shekara da sanin juna mu kayi ta hira da su, in da Ummi ke bani labarin ciwon Amal da yadda yake ba ta wahala,
"yaran mu uku a duniya, daga babba Yayan Amal wanda shi tun yana ƙarami Allah ya mishi rasuwa, kuma shi sai ya kasan ce, AA, sai mai bi mishi shi kuma AS ne, yana karatu yanzu haka a Oxford university, mai suna Faisal yana shekaran shi na ƙarshe kenan, in da ya ke karantar medicine, Amal ita ce mace a cikin su, kuma ita Allah ya ɗaura mata wannan laruran, amma kuma mungode Allah da ya bamu juriya da haƙuri na kula da ita, saboda shi ciwo ne wanda mai ciwon da mai jinyan kullum a wahale suke, mun so tayi karatu a kusa da mu cewar Ummi, amma sai nayi tunanin wata rana fa Amal in tana da nisan kwana, za tayi aure kuma bamu san in da auren zai kaita ba, shiyasa muka yanke shawaran kawota nan tayi karatu, amma kullum a cinkin fargaban ciwon ta muke".
Ummi ta faɗa tana ta daddanawa Amal ƙafa, wanda tun shigowan ta abinda ta ke tayi mata kenan.
Haka mu kayi ta hira har Dr Hussain ya shigo, gaisuwa ya musu na girmamawa, wanda daga gani Abbu yaji daɗin hakan, haka ina lura da Abbu sai jan Dr da hira ya ke tayi, shi kuma cikin kunya da rashin sabo da yawan magana ya ke amsa mishi.
Muna ta hira ni da Ummi akan karatun mu, ita kuma Amal ta rufe idon ta kaman mai bacci, amma idon ta biyu don wani lokacin ta kan buɗe idon ta tana amsa mana wani maganan, wani kuma tayi shiru tana kallon mu, ko kuma ta rufe idon ta, ita kaɗai tasan irin azaban da ta ke ji a cikin ƙasusuwan ta, sai kuma ƴan uwan ta masu irin wannan lalura.
Dr Abdallah ne ya shigo fuskan shi ɗauke da murmushi yana duban Abbu cikin yaren su na larabci yace,
"Abbu lokacin cin abincin Amal yayi, mai kula da ita zata shigo, sannan a ƙa'ida ba asan visitors a ɗakin, ko zan kai ku masauƙi ne Abbu".
Ya faɗa yana bin Abbun da kallo fuskan shi yana ta fitar da murmushin da baya barin fuskar shi.
"Ba sai ka nema musu wurin kwana ba, ina ga kaman babu takura idan sun kwana a gidan Humaira ko gidan Amal".
Dr Hussain ya faɗa ba tare da ya dubi idon kowa ba.
Murmushi Dr Abdallah yayi sannan ya dubi Abbu wannan karon cikin kalmar turanci, don yayi matuƙar mamaki da yaji Dr Hussain yana jin larabci yace,
"Abbu zaku iya zama a gidan Humairan ko na Amal ɗin?".
"Nikan ina ga idan babu ta kura kuzo gida na kawai Ummi, saboda akwai extra room wanda Daddy ma anan ya zauna, ina ga zaku iya zama da Abbu idan bazan takura ku ba".
na faɗa ina matsawa kusa da Amal ina riƙe hannun ta.
"Babu komai Humairah wurin ki dana Amal ai duk ɗaya ne, so babu komai zamuje gidan ki, tunda 2days ma kawai zamuyi mu juya, saboda munga jikin Amal ɗin Alhamdulillah, bai yi mata tsanani ba sosai".
Abbu ya faɗa yana shafa kan Amal ɗin, wanda tun da taji maganan tafiyan mu ta buɗe ido tana bin mu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
A hankali ta buɗe baki tace, "Ummi kuje gidan Humairah zata baku kula sama da yadda zan baku, kuma Hummy bata da problem, za kuji daɗin zama da ita sosai".
ta faɗa hannun ta riƙe dana Ummin.
Haka muka yi sallama muka fita, muna zaune nida Dr Hussain a mota muna jiran fitowan su Abbu, don a ciki muka bar su saboda suyi sallama da ƴar su, bayan shima Dr Abdallah shima ya bar ɗakin.
"Me kika shirya musu for break fast"? Dr ya tambayeni ba tare da ya kalle ni ba.
Kallon shi nayi na kawar da kaina gefe ina kallon hanyar fitowa daga asibitin nace,
"ina ga aiɓchips is okay, sai na sayi bread su sha da tea, saboda larabawa basu wasa da cin bread".
na faɗa ina juyowa ina kallon shi.
"Kina da enough potatoe ɗin?".
Ɗaga mishi kai nayi alaman ehh, saboda ganin tahowan su Abbu.
"Idan babu na kira wife ɗina ta musu acan, idan yaso da safe sai na karɓo da sauri".
ya faɗa yana wani munafukin murmushi, kallon shi kawai nayi bance mishi komai ba, saboda ganin su Abbu suna shirin buɗe ƙofan motan.
Haka muka yi ta tafiya kowannen mu bakin shi shiru, sai Ummi da Abbu da ke zaune a baya ne kawai suke magana, in da daga baya Abbu yake tambayan Dr ya ya za'ayi da maganan school ɗin Amal? Tun da gashi gobe monday ita kuma tana asibita, ya ya za'ayi kenan"?
Yana shiga gate ɗin gidan mu ya amsawa Abbu da cewa,
"gobe insha'Allahu zan yi report a school, duk abinda akayi tunda bata nan sai ƙawarta ta nuna mata daga baya, tunda ba laifi suna maida hankali akan karatun, so abin bazai musu wuya ba, sai dai addu'an Allah yasa kada abin ya ɗau lokaci".
"Ameen ya rabbi".
Abbu da Ummi suka amsa mishi.
Gidana na buɗe musu suka shiga, muna shiga suka zauna a parlor, ni kuma na shiga ɗaki domin na shimfiɗa musu bedsheet, domin tun da Daddy ya tafi na cire, sai dai bayan 2dys ina sha re wurin na goge komai, don ni ban yadda da zama cikin ƙazan ta ba, ina ta tunanin mai zan fito na ɗaura musu mai sauƙi for dinner.
Ina fitowa na dube su ina murmushi nace, "Ummi ko za kuyi wanka kafin na girka mana abinda zamu ci?".
Na faɗa ina ƙarasuwa parlon.
"My luv kada ki wahalar da kan ki, kawai tea za musha da bread, saboda Abbun ko baya iya zama babu tea".
Ummi ta faɗa tana miƙewa tsaye tana dariya.
Shima dariyan ya yi yana miƙewa yace, "Faɗi gaskiya dai, kice bamu iya zama babu tea daga ni har ke".
Ni dai dariyan su kawai na keyi domin kaman basu suka haifi su Amal ba, babu wani girman kai ko raini suna wasa da junan su kaman ƙawaye, suna shigewa na ɗauki waya na da yake neman a ɗauke shi, domin ringing ɗin da yake yi.
"Ki fito waje ina jiran ki".
cewar Dr Hussain, ajiye wayan nayi bayan naji ya ajiye ta shi.
Ina fita nagan shi tsaye a jikin mitan shi, ina ƙarasa wurin ya miƙo mun wani babban laida, mai ɗauke da tambarin *MCDOULS* take away yai mana, sannan ya miƙo mun ɗayan leda wanda yake cike da bread da wasu snacks ɗin kala-kala, ɗagowa na yi ina duban shi.
"Kinsan larabawa da son kayan flour, saboda haka ki shiga musu da shi, ni kuma bari na shigo da Potatoe ɗin da kuma plantain da egg, na ƙaro miki ne saboda kada ku takura".
Hararan shi na yi cikin wasa nace, "hala matar ka bata iya soyawa ba ko? Shiyasa ta koro ka da shi kadawo min, dama dai nima nayi tunanin matar da ta ƙware da barin mijin ta da yunwa yana bin gidajen cin abinci? To yaushe tasan tayiwa baƙi idan ba neman magana irin na mazaje ba".
na faɗa ina ƙarasawa balcony ɗi na, wanda shima yana biye da ni abaya yana ta murmushi bai ce mun uffan ba.
Har kitchen ya raka mun da kayan hannun shi, nima ajiyewa nayi na miƙe ina kallon shi ganin yadda ya ƙura mun ido bayan ya ajiye kayan hannun shi.
Murguɗa mishi baki nayi na juya ina ɗaga eggs ɗin ina saka su a wurin dana ke ajiyewa, sannan na zuba potatoe ɗin a cikin wani standing storage na zuba dankali da onioun,
"to ai sai ka tafi tun da ka gama aikin ka".
na faɗa ina kallon shi nima.
Murmushi ya yi yace, "kin fara raina ni ko? Ni ba Malamin ki bane?".
"Kuma Baby na ba, sannan kuma friend ɗina, kuma.... ".
sai nayi shiru ina kallon yadda ya ƙura mun ido.
"Kuma ɗan aiken ki ko?".
Ya tambaya yaɓa ɗaga mun giran shi sama, alaman tambaya da son jin ƙarin bayani.
Dariya na yi nace, "ni idan ba sharri ba yaushe na taɓa aiken ka?".
"Gashi yanzu kin fitar dani naje miki aika, saboda kina ganin kin taddo ni tsayi ko".
Matsowa nayi kusa da shi ina dariya nace,
"kaiiii wlh duk tsayi na ban fi zuwa ƙirjin ka ba, kaifa dogon gaske ne Dr'n mu, don ina mamakin mai ya haɗa ka da mata wanda bata wuce kwandon wanke-wanke ba a tsayi".
Na faɗa ina dariya ƙasa-ƙasa.
"Yayan mu ina mamakin mai yasa ka ke son wannan corper? Wallahi kai dogo ne sosai gara kasamu mata doguwa, amma wannan corper kam ai bata wuce tsayin ragon
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 28