shiga parlon mu da gudu naje na rungume Amaal, dariya ita ma takeyi muka gama zagaya wurin tukun muka zauna, "bani labari babyn Dr", ta faɗa muna dariya.
Bayan nagama bata labarin duk abinda ya faru, sai ta ɗaga kanta kaman mai tunani, chan ta sauƙo da kanta tana kallo na tace, "mistake ɗaya Hummy, baki ce mishi komai ba sai kika fara bashi labarin soyayyan ku da Faisal, hujjah"?
Dariya nayi na miƙe tsaye ina kallon ta, "16yrs nake fa Amaal, Drn mu 40yrs yake, kinga akwai 24yrs a tsakanin mu, yaushe zan tura mishi tunani na kusa da na shi? ae bazai dinga mun uzuri ba a rayuwa kullum zai mun kallon mai hankali da shekaru, amma yarinta na kullum zai zamo abinda zai banbantani da sauran mata, sannan zaina haƙuri da ni a kowani lokaci, kinga shi fah yanzu zaiyi tunanin ban fahimci abinda yake nufi ba, toh zaije ya zauna yayi ta wasa ƙwaƙwalwar shi da lissafin wani hanya zai sake bina da shi, kuma wani hanya zai ya kuce mun wannan yaron a raina, kuma ko daga baya bazaice shi kaɗai na taɓa so ba, dole shima ya haɗu da rival ta wurina, ki barshi ni bazan bashi amsa ma, yanayina kaɗai zai wadatar da shi, har ya aminta babu wani a zuciyata sama da shi, amma a hankali", na faɗa bayan na koma gefen Amaal na zauna.
"hmmm shiyasa akace ko wacce mace da irin nata kissan ake haihuwarta da shi inji kakarmu, babu wacce ka isa ka zaunar da ita ka koya mata kissa, saidai ka tunatar da ita kawai, domin ko ka koyawa mace abinda zatayi, toh bazatayi exactly irin yadda aka gwada mata ba, sai nata baiwan ya shiga ta sarrafa shi ta wani wurin daban, kaman yadda yanzu kikayi, bayan Ummi ta gwada miki nata hikiman, nima na gwada miki, sai kika yi naki hikiman, gaskiya ƴar'uwata kin burgeni, Allah ya barki da Drn ki ɗan tsoho kusha soyayyah", ta faɗa tana dariya na.
Nima dariyan nayi nace, "musha soyayyah yayi ta goyani ina jin daɗi".
Wayata na ɗauka nayi dialing number Dr ina ɗan murmushin shaƙiyanci, yana ɗauka nace, "hello Dr na baka shigo munyi dinner ba, kuma wallahi yunwa na keji", na faɗa kaman zan mishi kuka.
"ku ci kawai bana yare da yunwa", ya faɗa ya kashe wayan, kallon Amaal nayi ina dariya nace, "bari naje nayi biko".
Kaman bazai buɗe mun ƙofan shi ba bayan nayi knocking, yana buɗewa na ratsa gefen shi na wuce cikin parlon na tsaya ina duban shi babu dariya a fuskana, shima ƙura mun ido yayi yana mun wani irin kallo.
"Dr meyasa bazaka zo muci abincin ba"?
"Nace miki bana tare da yunwa, kwanciya ma zanyi zo ki wuce ki tafi, na hanaki shigowa nan ae".
Wucewa nayi na nemi wuri na zauna ina kallon TV da ake news, kallona ya tsayayi bai ce komai ba, ganin haka yasa na dube shi nace, "ka rufu ƙofan mana kazo mu zauna, tunda kace baka jin cin abinci nima ae bazan iya ci ba, kuma yau anan gidan zan kwana tunda kai yayah nane, kuma uncle ɗina ne", na faɗa ina shirin miƙewa na kwanta a wurin.
Da sauri yazo ya tsuguna a gabana yana kallo na, ƙura mun ido yayi kafin yace, "saboda me zaki kwanta anan? Baki tsoron komai ne kam ke"?
Tashi nayi na zauna, na rufe idona naƙi kallon shi, domin bana jin daɗin ƙura mishi ido, "ban taɓa tunanin zaka iya cutar da ni ba, nayi imani da Allah yadda Daddy na zai kareni ya kare mun mutuncina haka kaima zakayi, ina ji ajikina zaka iya sadaukar da rayuwarka domin tsare mun mutuncina, kuma koda a jikin ka zan kwana zaka fi kowa tsare mun mutuncina, saboda haka bani da shakku akanka".
Ajiyan zuciya ya sauƙe mai ƙarfi, sunkuyar da kanshi ƙasa yayi bai iya cewa komai ba, hannu na saka na riƙo hannun shi, wanda yayi sauri ya ɗago kanshi yana duba na, gaba ɗaya ganin idon shi sai naji ya bani tausayi, a hankali na furta, " Dr nah! Nafi son na ganka kana murmushi, amma yau kaƙi kayi, narasa me ya sameka, sai naji bana jin daɗin komai a rayuwar, don Allah me kake so"?
Nunani yayi da kanshi, duk da na fahimci yana nufin ni yake so saboda tambayan dana mishi me yake so? Amma sai nayi kaman ban fahimta ba, sai na buɗe ido nace, "kana son na fita nabaka wuri"?
Runtse idon shi yayi da ƙarfi, alamar ba haka yake nufi ba, jijjiga hannun shi nayi da ƙarfi nace, "wayyo Dr na ko na ƙira Dr Abdallah ya duba mun kai ne? Dr na baka da lafiya ne"?
"Abdallah, Faisal, duk kinfi damuwa dasu sama da ni ko"? ya faɗa da wani yanayi kaman na yaro ɗan 20yrs.
Tashi nayi na tsaya, shima tashi yayi ya tsaya ya ƙura mun ido, ni kuma turo bakina nayi gaba nace, "Faisal masoyina ne, Dr Abdallah friend ɗin Amaal ne, kai kuma na damu da kai ne, ina jin ka sama da komai da kowa, saboda haka zo mutafi bana son musu muje muci abinci sai kamun karatu", na faɗa ina tafiya hanyar waje, babu musu kowa ya biyo ni.
Duk wani text da zamuyi munyi shi, Dr Hussain ɗina babu abinda ya bari ƴa shige mana duhu, duk da rabin karatun zolayan shi nakeyi, na hana shi saƙat, ita kuma Amaal banda dariyan mu babu abinda ta keyi, idan na fara shirmena ajiye komai ya keyi ya ƙura mun ido, har sai Amaal ta gama dariyan ta tayi mun masifa tace nabar mu muyi karatu, amma shi kam baya iya hanani komai sai yadda naso.
Wataran ana karatun zan tsaya nace, "Dr mu nikan muje musha ice creem, kaina ya daina ɗaukan karatun", haka zai tattara mu muje, idan munje kuma na dinga mitan mata suna kallon shi, kuma nayi kane kane a kusa dashi ina hararan su, haka zaiyita kallona bazai ce uffan ba.
Watarana kuma ana karatun ƙiran Faisal zai shigo don neman tsokana zan ɗauka nayita maganan soyayyah, har na miƙawa Dr nace dole sai sun gaisa, toh irin wannan lokacin baya iya daurewa, tashi yakeyi ya barmu, kuma naƙi nuna wani abu ya faru, haka zanyi ta binshi har sai ya sake dolen shi.
Gashi yanzu na tsiro da wani hali sai naga muna school lokacin da muke break zan kira shi na fara damun shi da fitinan ni sai naganshi, na dinga mishi kaman zanyi kuka, babu yadda ya iya dolen shi yake zuwa ƙofan class ɗinmu, ni kuma ina fita zan je nayita gaya mishi magana kaman na soyayyah amma a fakaice, " Dr mu kasan bana jin daɗin komai idan ban ganka ba, wallahi ɗazu ma har saida nayi hawaye fa",
"toh me yake saka ki son ganina"? Ya tambayeni bayan ya jingunu da jikin wani mota, ina binshi da murmushi nace, "nima fah ban sani ba, shine nake son kagaya mun, Dr nah nifah so nakeyi kayita goyona fa, zakayi"?.
Dariya yayi ya ƙura mun ido yana ta cizon lips ɗin shi, rufe ido na nayi alaman naji kunya nace, "ni idan kana kallona sai na dinga jin wani iri".
"Don Allah me kike ji baby nah"? Ya tambayeni da sauri.
Dariya nayi nace, "sai ka goyeni tukun na gaya maka".
"Baby toh kinƙi ki yarda mu rayu dake ballantana na dinga goyonki kullum, ki amince mana".
Ina kallon shi nace, "wai baby a ina zamu rayune ni dakai? Bayan yanzu ma kullum muna tare baka taɓa goyo na ba"?
"Idan mun koma gida zan gaya miki, kinga nan school ne idon kowa yana kanmu", sallama yamun ya tafi office, ni kuma na koma class.
Muna gama dinner muka fito da books ɗinmu ya ɗan koya mana abinda ya sha mana kai, muna gamawa na matso kusa dashi nace, "Baby nah me zaka gaya mun ɗazu"?
Ɗago kai yayi ya kalli Amaal, sai ya maida kallon shi kan TV, ganin haka Amaal ta tashi ta wuce ɗakin mu tana ta dariyan drammer mu.
Juyowa yayi ya kalle ni, sai naji kaman bazan iya zama.kusa da shi ba, ina ƙoƙarin matsawa naji ya riƙo hannu na da sauri, kasa kallon shi nayi kawai sai na turo bakina gaba, "Babyn baby ina son mu rayu irin na ma'aurata, ina nufin mu rayu a ƙarƙashin inuwar aure, ina so nazama abokin rayuwar ki ni kaɗai, kuma kizama tawa kema, toh a wannan lokacin kullum kike so zan dinga goyonki har sai kince kin gajji".
Kasa ɗago ido na nayi domin na kalle shi, duk sai naji yau yamun wani girma, ina so na gudu shi kuma ganin haka sai ya ƙi sake hannuna, "Baby ki yadda dani don Allah, na rasa abubuwa masu muhimmanci a rayuwata, banida kowa sai ke, banida family, bani da komai, ki taimakeni mu zauna a inuwa ɗaya nima na samu family kafin na bar duniya".
"kana da family, bakana da Ummi da Abba ba, kana da Hassan da Aisha, kuma ni ƴar yarinya yayah zanyi na aure ka? Kamun girma, kuma ae bakace Hummy ina sonki ba, shi kuna Faisal kullum sai yace yana sona, ni yaro nake so kamun tsufah, za ayita mun dariya ne, Amaal ma dariya zata mun".
Lumshe idon shi yayi kaman bazai buɗe ba, chan kuma sai ya buɗe yana murmushi, wanda har abin yaso ya bani tsoro, na ɗauka masifah zai mun sai naga sai murmushi yakeyi, Hannun na ya ɗaga ya ɗaura a dai-dai saitin heart ɗinshi, gaba naji ya faɗi saboda yadda heart ɗinshi yake bugawa da ƙarfi, ajiye hannu na yayi a ƙasa sannan ya miƙe ya zura hannun shi a aljihun wandon shi ya juya mun baya, har saida yaje zai fita tukun ya tsaya batare da ya juyo ya dube ni ba yace.
"Abinda kike so kiji na miki alƙawari zakiji shi a wurina har sai ya hau kanki, na daɗe da sanin ga abinda kike so kiji daga gareni wanda ke baki san kina cikin yanayin hakan ba, amma na miki uzuri saboda ƙananun shekarunki, *HUMMAIRAH* tun ranan da na ganki wannna bugun zuciyata ɗin yaƙi daidaituwa, kuma tunda ga rana na sakawa raina keɗin kece mahaɗin zuciyata, shiyasa ganinki yasata ta fara aikin da yake so ya fi ƙarfinta, kece ƙaddaran da ta gifta rayuwar mutane da dama, kece ƙaddarar da ta raboni da iyayena da ƴan uwana, kece ƙaddarar data raboni da soyayyar ahalina, kece ƙaddarar da zata sake haɗa ni da farin ciki na, kada kiyi duba da shekaruna, ina so kiyi duba na dacewan masu mabanbanta shekarun da sukayi, shi kaɗai zai baki nutsuwa sa samun kwanciyar hankalin ki domin ki rayu a inuwa ɗaya da mai miki".... Sai ya yi shiru, daga baya ya buɗe ƙofar parlon ya fita.
_*SALAMATU ABUBAKAR, (SALMA D.O)*_
tare da
_*ZAINAB ALƘALI (ZEE GOMBE)*_
wannan shafi na kune ƙannena, domin nuna muku irin godiyata da jin daɗina na yadda kuke nuna jin daɗin ku akan book ɗinnan, Allah ya albarkaci rayuwar ƴaƴanku, nagode Allah ya bar zumunci
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 20📑*
*__________📖* Tunda ya fara maganan na ke jin hawaye suna bin fuska ta, har ya fita ban samu ikon tashi daga wurin ba, ina zaune a inda ya bar ni Amaal ta fito, da sauri ta rungume ni tana faɗin,
"ALHAMDULILLAH, yau Dr ya bankaɗo sirrin zuciyar shi".
Juyowa na yi ina duban ta, hawaye na zuba kan fuska na, girgiza ma ta kaina na keyi alaman a'a, ɗaure fuska tayi tana tambaya na, "me yake sa ka ki kuka? Kefa murna ya kamace ki da yi".
Tashi nayi tsaye na riƙo hannun Amaal,
"Amaal ko ɗaya banji kalmar yana sona daga bakin shi ba, kawai cewa ya yi yana son muyi rayuwa tare a inuwa ɗaya, kawai aure na ya ke son yi bawai yana so na ba, ina ga akwai wacce ya tana da ma ta wannan matsayin".
na faɗa ina sha re hawayen da ke zubowa.
Ɗakin mu na wuce Amaal tana bina a baya, wanka na shiga nayi, ina fitowa ta shiga domin itama tayi wankan, mun kwanta bayan kowa ta gama shirinta, amma babu wacce tace da ƴar'uwarta uffan.
"Hummy! Kiyi haƙuri ki bi Dr da irin nashi tsarin, na miki imani da Allah Dr yana son ki, kuma ba ƙaramin so ba, insha'Allahu kuma wata ran ke da bakin ki zaki bani labari, kuma ina miki albishir duk ranan da Dr ya furta miki kalmar ina son ki, sai kinfi jin daɗin kalmar da ganin muhimman cin ta sama da yanzu".
cewar Amaal.
Juyowa nayi ina hararanta da wasa,
"to Amaal saboda Allah a hakan zan yadda yana so na? Shi bazai buɗe baki ya furta mun kalman so yadda ko wani saurayi ya ke yiwa budurwa ba?".
Na faɗa ina shirin sa ke sabon kuka.
"Don Allah bance kimun kuka ba, wai ke Hummy har sai zuwa yaushe za kiyi wayo ne? Ni fa ban ɗauki wai sai saurayi yace yana sona da ba jin shi ba za muyi soyayya, ai ɗabi'un shi da idon shi ma kaɗai ya wadatar da mace, kawai namiji yace miki yana son ki ai tun zamanin su Ummi a kayi shi".
Ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya.
Kallon ta nayi baki na buɗe, "kina nufin kina soyayya da wani ne Amaal?".
na faɗa ina duban ta tana shiga cikin duvet tana ta ƙyalƙyala dariya.
Sai da taga na dame ta da magiyan sai ta gayamun, tukun ta buɗe idon ta tana kan dariyan, ta wani kashe ido ɗaya tace, "to ke banda shirme ya yi miki yawa har yau baki fahimce meye ke tsakanina da Dr Abdallah ba ko?".
Ido na zaro ina duban ta cike da mamaki, "kina nufin Dr Abdallah yace miki yana son ki?".
na faɗa cike da mamaki.
Dariya tayi mai ɗan sauti, sannan ta tashi daga kwancen itama ta zauna bayan ta jingina bayan ta da jikin gado, tana duba na tace,
"kina tunanin ni irin kice sakaliya wacce ban san ya ya rayuwa ta ke tafiya ba? Mufa ko acikin larabawa muna da family sosai, kuma akwai kyakkyawan zumunci a tsakanin mu, ina ganin yadda ƴan mata da samarin family'n mu suke tafiyar da al'amarin su, kinga basai an mun bayanin yanayin maza ba, zan iya karantar su".
Ɗago ido nayi na dube ta, sai naji lokaci ɗaya kewan mahaifiya yazo mun, wato da gaske ne wata friend ɗi ta Ruƙayyah muna secondry school ta ce mun,
"Humairah wataran idan kin yi abu sai naga kaman goyon kakace ke, gaba ɗaya baki da wayo, sai buhun wauta, yanzu banda ke Humairah baki lura Umaimah gatse ta miki ba ko? Ke sai yaushe za kiyi wayo ne?".
Ta faɗa tana dariyan wautan da nayi a wancan lokacin, sai Umaimah ta dube mu tana dariya tace.
"Ruƙayyah ai na gaya miki Humairah rayuwar kan carpet ce, domin ni kullum ƴan aikin gidan su nake ganin suna hidima da ita, tunda na ke zuwa gidan su ban taɓa haɗuwa da Maman ta ba sai dai step mum ɗin ta, kuma sai su wuni basu haɗu ba, to ina za tayi wayo bata zauna a gaban masu saita ta a kan layi ba, shiyasa wataran idan tayi abu sai taban haushi wataran ta ban tausayi".
ta faɗa dukkan su suna mun dariya, nima dariyan nayi dana lura da shirme da wautan dana tabka musu a lokacin.
Ina dawowa gidan mu daga school kai tsaye parlon Daddy na wuce, in da na tarar da shi da Mama da Yayah Ahmed da Adda Hafsat da Adda Halima a zaune kan dinning suna lunch, gaishe da su nayi na ƙarasa gefen Daddy na rungume shi ina faɗin,
"oyoyo Daddy nadawo a school".
shima murmushi yayi yace, "oyoyo Humairan Daddy, zo muci abinci".
ya faɗa yana manna mun kiss a forehead ɗina.
Da sauri na juyo na dubi Mama jin wani tsaki da tayi, muna haɗa ido ta sauƙe mun wani harara wanda sai dana ji zuciyata ta yanke, Adda Halima da Yayah Ahmed ma hararan suka bini da shi, Adda Hafsat ce kawai ta mun murmushi ta sunkuyar da kanta ƙasa ta cigaba da cin abincin ta, ganin abinda suka mun yasa na dubi Daddy ina murmushi nace,
"Daddy ni banyi wanka ba banyi sallah bama fa, kawai nazo na tambaye ka wai da gaske duk ɗan da bai girma agaban Maman shi ba baya wayo?".
"Jeki kici abinci sai muyi labarin, amma ki kwantar da hankalin ki, kinsan duk yadda Allah yaso mutum ya yi rayuwa haka zaiyi, wani zai yi rayuwa babu uwa babu uba, to shi kuma ya yi ya ya a rayuwa? Wani kuma bai san kowa na shi bama, a gidan marayu ya tashi, to shima ya ya zai yi? Dole duk haƙuri akeyi a rayuwar, ke da duk duniya babu wata ƴar da tayi dace da soyayyan uba irin ki to mai zai dame ki Humairah na? Kawai kiyi addu'a wa Mama'n ki Allah ya kai rahama da haske kabarinta, ni kuma nine uwa kuma nine uba a gare ki, kada ki damu, nima soyayya ta ya isa ya hanaki zama marar wayo, kina da zuciya mai kyau ne, shiyasa ake ganin kaman baki da wayo, je kiyi wanka my dear".
ya faɗa yana buga kafaɗa na.
Hawayen idona na sha re da sauri na dubi Adda Hafsat da itama ta ke sha re hawayen ta, murmushi na mayar mata yadda itama ta mun, sannan na wuce sama domin tafiya nawa side ɗin, amma ina ganin Mama da su Adda Halima sai bina da harara suke yi.
Ajiyan zuciya nayi na saka hannu na sha re hawayen ido na, sannan na dubi Amaal nace, "Amaal nima ina so naga ina rayuwa da Mama na da Baba na da ƴan'uwa na, ina son naji ya ya kuke ji, amma Allah bai nufa ba, bani labarin ki da Dr Abdallah".
Na faɗa ina ƙara sha re hawayen da yaƙi tsaya mun.
"Dr Abdallah tun ranan da muka zo registration Abbu ya haɗa ni da shi a matsayin Dr na, kuma tun lokacin na fahimci ya faɗa cikin soyayya ta, amma ban ƙarasa fahimta ba, sai da nayi ciwo na tafi gida, ya kasa zama ya bini har ƙasan mu, duk da shima ɗan can ne kuma cikin gari ɗaya muke, amma nasan ya yi haka ne don ni, soyayya ce kawai zai kawo haka, sannan wannan kwanciya ta ɗin ya nuna mun babu wata mace da ya ke so da tausayi iri na, ranan farko yace mun, ya kamata na auri likita domin na dinga samun kula, sannan ya dawo yace shi zai sama mun wanda zai kula dani, washe gari yace duk duniya shi zai fi bani kula saboda haka ya zaɓa mun kanshi don ya kula dani, ai dai baki ji yace so na yake yi ba, amma kuma yanzu ni da shi mun san soyayya muke yi, ke kuma abunda kika kasa fahimta da Dr Hussain kenan, yana miki son da ko a gaban waye sai ya nuna, amma ke duk bai ishe kiba kinfi son yace yana son ki kije kiyi tunani bayan 2 days ko? Irin yadda su Ummi suka yi da ko?".
Ta faɗa tana harara na.
Bansan lokacin dana kwashe da dariya ba, duk wannan ɓacin ran lokaci ɗaya naji ya gudu, duk dariya muke yi ni da Amaal, sai naji waya ta ta fara ringing, da sauri na jawota ina dubawa, ganin sunan Dr Hussain ya saka ni zaro ido na duban Amaal.
Harara ta mun taja duvet ta shige ta bar ni, haka na ɗauki wayan yana dab da tsinkewa,
"hello babyn Baby ba kiyi bacci ne bane?".
Naji yana tambaya na da wani irin murya wanda baza ka taɓa cewa muryan shi bane.
Lumshe ido nayi a hankali na furta,
"na kasa bacci saboda bansan ko Baby ya yi bacci ba".
na faɗa ina jin yadda zuciya ta ta ke bugawa da sauri da sauri, saboda ban taɓa tunanin baki na zai iya furta haka ba.
Daga in da Dr yake ya tashi ya zauna, murya ƙasa-ƙasa yace, "da gaske?".
"iya kacin gaskiyan da yake zuciyata kenan my Dr".
na sa ke tabbatar mishi.
Ajiyan zuciya ya yi yace, "Baby ina son ganin ki wallahi yanzu a gaba na, Baby bugawan zuciyata yana ƙaruwa, Baby ki leƙo na gan ki don Allah".
Runtse ido na nayi saboda yadda na kejin muryan shi yana rawa, a hankali nace,
"Baby ni sai dai kazo ka ɗauke ni wallah tsoron fitowa nake yi ni ɗaya, kuma ni sai nagan ka kafin nayi bacci".
na faɗa ina mishi sheshsheƙan kukan ƙarya.
"Ba,,byy,yy!" Yaja sunan da ɗan sauti sannan yace, "bana gajjiya da ganin ki, bana gajjiya da jin muryan ki, ki fito na ganki kin ji".
Tashi nayi wayan na riƙe a kunne na ina ta sauƙe mishi buhun shagwaɓa har nazo jikin ƙofan parlon na tsaya, ina jin shi ya buɗe na shi ƙofan ya ƙaraso, sai na kasa buɗe ƙofan, shi kuma sai magiya yake ta mun, ganin nayi da shi ya koma ya ƙi kawai sai na saka hannu na buɗe ƙofan, kallon shi nayi sanye da wasu kayan bacci cotton masu masifan kyau, three quater da riga mai kyau, ƙafan shi sanye da wani silifas fari, ido ya ƙura mun wayan shi yana kare a kunnen shi, har lokacin bai yanke ba, nima ina kallon idon shi ban yanke wayan ba, naji yace,
"Baby'n baby!" ta cikin wayan, ina kallon shi nace, "baby nerh!". runtse ido yayi.
_*MUM SAYYEED GA KYAUTAR WANNAN SHAFIN,BAWAI DON YA ISA YA NUNA MIKI IRIN ƘAUNAR KI DA MUKE YI NIDA BESTY BA, KO ƊAYA KINFI KYAUTAN LITTAFI GUDA MA A WURIN MU, KINA NAN CIKIN RAN MU, MUNA MIKI SON SO.*_
*Plsss keep following, commenting, voting and sharing.*
*Love you all my fans❤️😘.*
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
_Wannan shafin nakine MUM SAYYEED Allah ya bar zumunci_
*SHAFI NA 21📑*
*__________📖* Murmushi nayi ganin ya buɗe idon yana mun alaman da yara sukewa iyayen su idan suna son abu a hana su, ganin ina murmushi shima ya maida mun martanin murmushin, "Baby kaman yau bazan iya bacci ba idan bamu tare, yayah za'ayi ne wai? Babyn ki fa abin tausayine fah", ya faɗa yana ƙara matsuwa kusa da inda nake.
Murmushi nayi na ɗan matsa baya kaɗan, don yazo dab da ni har ina jin numfashin shi a kusa da ni, "Baby toh kasan babu yadda zan maka, domin Allah bai halattah kwanan mu wuri ɗaya ba, saboda haka kayi haƙuri ka koma ka kwanta, da safe zamuyi magana, yanzu kam ae ka ganni", na faɗa ina ƙara sauƙe mishi murmushi.
"Babyn baby toh ae yakamata nayi wa Daddy magana domin ayi auren akan lokacin, don gaskiya ni nafara nema na rasa nutsuwa na akan ki, kuma ni irin su Faisal ɗin nan ba zasu barni na samu kwanciyar hankali ba", ya faɗa yana harara na da wasa.
Dariya nayi mai ɗan sauti, "Baby aure kuma tun ban girma ba? Gaskiya ni sai nayi masters ma tukun nayi aure, nidai gaskiya naƙi ba yanzu ba", na faɗa ina dariyan yadda ya buɗe ido da bakin shi yana kallo na cike da mamaki.
"Gaskiya bazai yiwu ba baby, ni bana son kodawo wani semester ma ba muyi aure ba, idan ba haka ba zan taro gidan nan da zama, da kike cewa baki girma ba, bazaki iya ɗaukan Babyn ki bane?" ... Faɗin haka da yayi nayi sauri na rufe ƙofan da ƙarfi, na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 28