Share this page
kallo. Shawara aka tsayar tsakanin Daddy da Abbu akan dole Dr ya haƙura a je Nigeria wirin Abban shi, domin bazai taɓa yiwuwa a tsayar da magana ba tare da sanin iyayen shi ba, amma firr Dr yace shi bazai koma ba, kuma Humairah ma bazata je wurin Ummin shi ba, idan itama Hassan ya gani yace yana sonta fa?. Murmushi Daddy yayi yana duban Dr Hussain yace, "amma ashe surukina ɗin ragon namiji ne ban sani ba, har kana tunanin akwai wani da zai iya ɓanɓareka a zuciyar Hummy"? Girgiza kai Dr yayi jiki a sanyaye yace, "nidai kawai ina tsoron mu koma Abba yace babu aure tsakani na da Humaira ne, ni nafi son ayi auren a nan tukun a koma chan ɗin". Abbu ne ya gyara zama yana murmushi yace, "Haba ɗana! ae idan babu aure tsakanin ka da Humairah ae tun anan ɗin ma baza mu aura maka ita ba, Aisha ae ba ciki ɗaya kuka fito da ita ba, da ace ciki ɗaya kuka fito da Aisha da babu abinda zai sa ka auri Humairah, tou amma yazo da sauƙi akwai aure tsakaninku, saboda haka ya kamata kaje kaga a wani hali da yanayi iyayenka suke bayan tafiyan da kayi na tsawon shekaru, inaga hakan shine yafi zama dai-dai", Abbu ya faɗa yana bubbuga kafaɗan Dr. Shirye-shiryen tafiyan mu nigeria ne aka shiga fafah, haka muka hallara gaba ɗayan mu sai garin jos, ranan da muka isa mun samu Yayah Kabir ya dawo daga school, oyoyo yaje yayiwa Daddy sannan ya dinga bin kowa yana gaishe su, yana ganina ya ɗaga mun hannu kawai ya wuce cikin gida. Parlourn Daddy duk aka wuce daga nan ni kuma da Ummi da Amaal muka shiga side ɗina, Gaggo nanny na muka samu zaune a parlour tana kallo, da gudu naje inda take na rungumeta, itama babu abinda ta keyi sai murnan ganina, tana cike da mamaki tace, "uwar ɗakina yau kece a ƙasar namu babu notice"? Dariya mukayi dukkan mu dasu Ummi, duk da bawai fahimtar abunda take cewa sukayi ba, sannan na gaya mata tare mukazo da Daddy na da baƙi, jin haka ta fita da sauri tafara haɗa musu abin sha, kafin ta haɗa abinci. Munayin sallah bayan mun hutu Ummi tace mun muje na kaita ɗakin Mama domin su gaisa, da mamaki na kalli Ummi nace, "Ummi bazafa ta kulaki ba, ko Kaka tazo gidan nan har ta tafi basu kulata ita da su Yayah Ahmad, kada muje ta wulaƙanta ki Ummi nah". Haka dai Ummi na ta sakani dole muka je side ɗin Mama, duk yadda nasan Mama da baƙin halin kada wani ya raɓe ta idan ba ita da ƴaƴanta ba, amma abin mamaki Ummi ta mata kwarjini haka ta zauna suka gaisa, inda Ummi take gaya mata ni ƙawar ƴarta Amaal ne, hakan Mama ta daure ta nuna jin daɗinta da zuwansu, bamu ƙara wasu lokaci ba muka koma nawa side ɗin. Waya Daddy yayiwa uncle Abdallah ya sanar mishi da komai daya shafi Dr da Humaira, kuma ya gaya mishi duk mun taho tare, Uncle Abdallah yaji daɗin labarin dawowar Dr Hussain, sannan kuma yace a nemi Abba agaya mishi. Haka Daddy ya ƙira Abba ya gaya mishi labarin komai da kuma zuwan mu, Alƙawari Daddy yayi mishi akan zuwa gobe idan Allahu ya kaimu zai kawo mu har Bauchi. A washe gari mukaje bauchi gaba ɗayan mu, inda muka samu uncle Auwal, uncle Baba, Aunty Fatima da mijinta Hassan da yaransu duk sunzo su, domin tun a jiyan Ummi ta ƙira kowan su ta gaya musu zuwanmu, hattah su Mama da Addagana da Bappan su Ummi duk sun zo, Umma da yake ta daɗe da dawowa gidan Abba saboda yawan rashin lafiyan da ta keyi kawai sai Abba ya dawo da ita gidan, gefen Aisha aka gyara mata ta zauna a wurin. Abin tausayi muna shiga parlourn Abba inda gaba ɗayan su suke zaman jiran isowar mu, da gudu Hassan ya taso yazo ya rungume Drn mu, dukkan su kuka suka saka suna rungume da junan su, da ƙyar ya sake Drn mu ya samu ya ƙarasa gaban Ummin ya tsuguna yana kuka baice mata komai ba, ganin haka itama Ummin ta fara kwanɗa mishi pillown kan kujeran tana kuka tana kwaɗa mishi, ganin baxata daina ba Drn mu ya rungumeta yana kuka, itama rungume shu tayi tana faɗin. "Haba Baba nah! Me na maka haka da zafi na chanchanci ka gujeni irin wannan tsawon shekarun? Katafi kabarni, Aisha ma ta tafi tabarni, da wanne kuke so naji? Kasan zafin rashin Aisha da nayi kuwa? Kasan Aisha ta tafi ta barni bayan bata sake jin yadda dani ba, ta hanani riƙon abinda ta haifa? Kasan zafin rashinka yadda na dinga ji a rayuwata kuwa"? Kuka mai sauti Ummi ta cigaba dayi tana rungume da Drn mu ƙyam a jikinta kaman wani zai ƙwace mata shi. Abba na murmushi yace, "yau ko naga inda ake mun fir ƙarfi? Farko ɗan'uwan shi ya rigani rungume ɗana, na tashi zanji ɗumin ɗana kuwa wannan matar ta rigani, gashi kuma ta gama chin zalin kyakkyawan fatan ɗan nawa da duka, kuma ta hana ni naje inda yake"? Ya faɗa yana matsawa kusa da Drn mu. Da sauri Drn mu ya tashi ya rungume Abba yana cigaba da kuka, da ƙyar ya buɗe baki yana, "Abba ku gafarceni tafiyan danayi na barku, Abba kuyi haƙuri bazan sake ba, nayi laifi bazan sake ba". Jin abinda yake faɗa nayi tsulum nace, "dama ina zaka sake tafiya bayan na chafko ka kadawo gida? ae yanzu zan maka ɗaurin da akeyiwa ragon layyah da karfi bazaka sake tafiya ko'ina ba, amma idan Ummi ta cigaba da kuka kuma zan ɗauke ka mugudu mu ɓuya, tun da nice na nemo ka, bazamu dawo ba har sai Ummi ta daina kukan shagwaɓa", na faɗa ina duban cikin idon Ummi, don kullum nazo gaisheta ko ita tazo ganina ta ringa mun kuka kenan tana tuna Mummy nah, har sai nace mata idan bata daina ba zan daina zuwa wurinta tukun ta daina. Murmushi Ummi tayi ta jawoni jikinta ta rungume ni ƙam, tana bubbuga baya na tana cewa, "ni Fati naga ta kaina da wannan sarkin surutun, tou yanzu yayah zamuyi ƴace ko jika? Wanne zamu kama ne"? Gaba ɗaya parlourn dariya aka fara, inda na dubi Ummi nace, "nifah jikace, don gaskiya bazan yadda da wayon nazama ƴaba, amma ita Aunty hauwa saboda masifarta zan yadda ta zama mun kaka, don idan uwace toh ta dinga masifance ni kenan bani da iko da bakin ramawa, amma ke kam naƙi wayon ni jikace, kuma Dr na ma jika zai zama miki gaskiya", na faɗa ina turo mata bakina gaba. Ranƙwashi na Drn mu yayi yace, "Ummin nawa kike tsagalgalewa"? Dariya dukkan su suka fara inda Aunty fati ta jawo ni jikinta ta rungume tana faɗin, "doughter wato uwar tawa kike cewa mai masifah? Tou bari ta iso zuwa gobe kiga iko da gadaran da zata sauƙe miko, ta hanaki auren ɗanta naga yanda zakiyi kina tsagalgale mana iyayen mu", ........ Tashi nayi da sauri daga jikinta na dubi Uncle Hassan da tunda muka iso yakasa sake wa, saidai idan anyi abu ya share hawaye ya kuma binmu da murmushi, "Uncle Hassan kaji Aunty Fati wai baza a bani babyn baby ba? Uncle kafi kowa kusanci da baby kace mata kabani shi", nafaɗa ina turo bakina gaba. Murmushi yayi ya kamo hannu na na dawo kusa dashi yace, "ki kwantar da hankalin ki uncle babyn baby naki ne ke kaɗai, kuma daga yau na baki shi kyauta, ni zan biya sadaki ma kafin Umma taje tayi kwaskwarima ta ƙwace miki shi, kuma Ummi ni da Aisha ne kaɗai ƴaƴanta, ke kuma jikace ke da baby, Aunty hauwa ce maman Baby, nida Aunty Fati kuma mune iyayenki, ni yanzu Baby ma ɗa yake mun", ya faɗa yana wani ɗaure fuska yana hararan Aunty Fati irin kada ta kawo mana wargi. Tsaki Umman misau tayi ta harari inda Drn mu yake zaune tace, "ni kuwa idan kun kwantar da hankali ku me zanyi da wannan tsohun tuzurun? Mutum saida ya ninka shekarun mijina a duniya kafin ya rasu zan so? Ni ae ko kyauta aka ban Hussaini bana so, kede da kika ga zaki iya kije chan ki ƙarata da sauran majina", .......... Parlourn kowa dariyan maganan Umma akayi, inda aka zauna aka cigaba da hiran bayan rabuwa. Bappan misau ne ya ƙara mana bayani akan hallacin da yake tattare da auren mu da Dr, inda kowa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali, kai wannan rana baxan taɓa mantawa dashi ba a tarihin rayuwata, don kuwa naga zumunci na ƴan'uwan mahaifiyata, don kuwa dukkansu da ƴaƴan su suka zo. Uncle Auwal yana da yara shida Aunty Ummi guda huɗu Affan, Aisha mai sunan mummy nah, Zahra mai sunan Ummi, sai khalifah mai sunan baban su Aunty ummi. Uncle Baba kuma yaran shi guda uku ne, Babban mai sunan Bappah ne inda suke ƙiran shi da Ammar, na biyun kuma mai sunan Baba Umar ne, inda suke ƙiran shi da Khalifah, sai ƙaramar kuma mai sunan Aunty hauwa inda suke ƙiranta da Jiddah, kuma naga alaman ba ƙaramin su Uncle Baba yakeyiwa yarinyar ba, don duk abinda yakeyi zakaji yace na Jeddah ne, duk abinda yaro zai taɓa zaice kubari na jiddah ne, ita kuma yadda kasan Aunty hauwa da faɗa haka ta ke. Washe gari zuwa dare su Aunty hauwa suka iso garin Abuja, da ƙyar suka kwana da safe suka kamo hanyar garin bauchi, da yake jirgi suka biyo da wuri suka iso, don wasu ma basu tashi a bacci ba suka iso. Gdan su Ummi yana da girman gaske, ga guest house mai kusan threebedroom har biyu, Ɗaya aka sauƙe su Ummi da su Abba a chan, ɗaya kuma mutanen misau aka ajiye a wurin, shi kuma Daddy na a ɗakin da yake parlourn Abbaha kuma side ɗin su Drn mu da Uncle hassan, inda ana uncle Baba da Uncle Auwal suka sauƙa, uncle Hassan gidan su suka tafi tare da Drn mu, side ɗin mummy na kuma Umma da su Mama da Addagana suka sauƙa, nidai ƴar lele a ɗakin Ummi na kwana tare da Amaal, amma Amaal da wuri tayi bacci, nida Ummi kuwa kwana mukayi muna hira, rabi gaba ɗaya labarin rayuwar Mummy na take ta bani, wani lokacin ta tsaya tayi kuka, wani lokacin ta girgiza kanta tayi murmushi, har sai wurin 4 na dare bacci ya sace mu. Zuwan Aunty hauwa da Uncle Abdallah wani kukan kuma ya sake tashi, domin ranan na tabbatar Aunty hauwa ba ƙaramin so ta keyiwa iyalan Ummi ba, don daga Uncle Hassan da Drn mu gaba ɗaya haɗa su tayi ta rungume su tana kuka, da ƙyar Bappah ya mata magana ta haƙura tayi shiru, gaba ɗayan su sakata sukayi a tsakiyar su, ita kuma dukka hannayenta suna ɗaure akan su kaman zata maida su cikinta ta keji. Bayan hira da gaisuwa da akayi a tsakani, Abbu yayi wa kowa bayani dangane da abinda ya faru da mu a saudi, da kuma dalilin daya kawo Drn mu yabada labarin shi, da zuwan Daddy na, gaɓa ɗaya kowa saida ya jinjinawa Dr irin son da yake mun, daga baya Bappan misau yayi mana nasiha mai ratsa jiki da kuma yadda da *ƘADDARA* mai kyau da marar kyau, inda yake cewa da babu wanda bai so auren Aisha da Hussain ba, amma ashe babu rabon auren a tsakanin su, gashi kuma da akayi haƙuri itama tayi biyayyah wa iyayenta gashi abinda ta haifa mafi soyuwa a gareta zata auri abinda itama taso sama da komai a rayuwarta, ya cigaba da duban fuskar kowa har ya kawo kan Aunty hauwa, murmushi yayi yace. "Hauwa kinga ikon ubangiji ko? Babu abinda kike so sama da kiga kin haɗa zuri'a da ƴar'uwarki, sai gashi alokacin da kika so Allah kuma bai nufa ba, dama haka iko na ubangiji yake abinda kake ganin shine dai-dai agareka sai kaga wurin Allah kuma ya chanja maka da wani indai har kabar mishi dukkan al'amuranka, gashi yau Hassan ya auri ƴarki ta cikin ki, ga shi kuma Hussain da rawar kai ya tsallaka ya tafi har kan jikarki, don tsabar basu son wani ya kwashe musu iyalen maman nasu duk suka handame a tsakanin su", Bappah ya faɗa yana duban Hassan da Hussain da dariya. Uncle Hassan ne ya buɗe baki yace, "dik wanda yayi zagin kasuwa yasan da wa yake, don tabbasa kaso Fatima ni kuma na ƙwace maka shiyasa kake gugan zana ɗan tsohu", Ranƙwashi Abba yayi mishi yana dariya yace, "mai Bappah zaiyi da zabiyar matarka", dukkansu dariya sukayi, sannan muka shiryah mukaje Narabi mukayi ziyaran ƴan'uwa. Tunda Affan ɗan uncle Auwal ya ƙyalla ido akan Amaal gaba ɗaya ya susuce gashi ba mai yawan magana bane, yadda kasan Uncle Auwal haka yake da shiru, amma duk hankalin shi da idon shi yana kanta, mutsi kaɗan idan za'aje wuri zakaji yace tazo ta shiga motan shi, duk yadda naso na jawota amma fir ya hana, haka dole na haƙura na barsu tare, shi kuma Faisal gaba ɗaya hankalin shi nakan Jedderh autar uncle Baba da yanzu take Ss3, duk wani feleƙe irin nata baya bashi haushi sai bibiyanta kawai yakeyi, ita kuma duk da kyau irin nata amma ganin ɗan balarabe sai wani falli ta keyi, nidai babu ruwana da kowa ta Baby na kawai nakeyi. Daga Narabi tilde muka wuce family house ɗin su Daddy, inda anan muka haɗu da su Yayah Ahmad shida Yayah Aliyu, ganin su yasa Daddy ya tara musu ƴan'uwan shi akayita musu faɗa domin su daina bin halin uwarsu suyi zumunci da ƴar'uwar su ƙwaya ɗaya, haka suka nemi gafaran Daddy dani gaba ɗaya. Duk yadda Daddy yaso zama dani Ummi taƙi mishi, domin shirin auren mu da Dr akeyi cikin satin nan, domin zamu koma school, kuma su Abba sun tabbatar mishi muna gama karatun mu ya tattaro ya dawo gida ya zauna, inda Umma tace idan bai dawo ba kuwa ita zata zo ta ɗauke ni mu dawo, haka yayita murmushi bai ce musu komai ba. Shiri na musamman Ummi na ta ke mun, don watarana inaji Aunty hauwa tana mitan wai Ummi me take so tayiwa ɗanta ne kam? Mallake mata ɗa ne za'ayi irin wannan shiryani da ake tayi"? Dariya Ummi tayi tace, "ɗan nakine dole sai mun kammale kanshi wuri ɗaya, din kada mu mishi laifi ya tattara kayan shi mu rasa kuma wa zai sake dawo mana da shi gida", da sauri na buɗe bakina bayan na ajiye goran tsumin Hajiya Aisha Aliyu Garkuwa mai haɗin gaske da nake sha nace, "Ummi ae duk inda Baby ya gudu zan bishi na tarkato abuna, ina zan bari wasu masu jan kunne su ƙwace mun shi? Kinsan faman danayi da shi akan wata ƴar india mai jan kunne kuwa? Sai da na zama ƴar bariki tukun na kwace abuna, na barta da sakakken baki, ga wasu masu halittan kajin mayu a hotel da in sun ganshi suke lanƙwasa kaman macizai, da kyat na fige mishi zuwa cin abinci inda suke na dage da bashi abinci, hmmm ta ina zanyi saken wannan haɗaɗɗen babyna ɗin ya kuɓuce wani wurin kuma"? Ina rufe bakina Aunty hauwa ta kaimun dundu a bayana, baki a buɗe tace. "anya humaira kinsan ku.ya kuwa? Mufa iyayen shine kika zaƙalƙalewa a gaban mu irin haka? Tou na sake ji kince babyn nan a gabana kiga yadda zan fasa miki baki, ɗan nawa da girman shi zaki na gaya mishi baby sai kace wani Affan". Muryar Baby naji shi da Aunty Fatima da Uncle Hasan suna dariya bayan sun shigo ɗakin Baby ya dawo kusa dani ya zauna yana duban Aunty hauwa yace, "haba Aunty nawa ma nake da baza ace mun baby ba? Gaskiya ni Aunty hauwa babu ruwanki, kawai kibarni a ce mun baby kafin na tsufah, yanzu Hassan ya isa a ƙira shi da baby ne bayan ya zama wani dattijo, har zai aurar da ƴa, nikan kubar mun sweet baby na ta faɗi abinda ta keso, ku toshe kunnen ku". Nidai zunɓura baki nayi ina kallon Aunty hauwa da wutsiyar ido, azuciyata ina Allah-Allah Ummi tace ta tashi ta tafi ta barmu, Amaal kuma sai dariya ta ke tayi ita da Ummi, uncle Hassan ne yace. "Aunty hauwa nima fah ana ce mun babyn nan fa idan babu idon ko" ya faɗa yana duban Aunty fati data buɗe baki tana kallon shi, dariya yayi yace, "ƙarya nayi ne baby luv"? Gaba ɗaya ɗakin dariya aka fara har da Auntyn hauwa, don Aunty Fatima tuɓurewa tayi tana ta rantsuwa tana duban Ummi tana cewa, "wallahi Ummi faɗi yakeyi, bana wani ce mishi Baby, nikan kuce ya bari Hummy fah ƴata ce yayah yake faɗa a gabanta". Dariyanta akayi tayi don gaba ɗaya Aunty Fati bata daina shagwaɓa har yanzu. Ranan friday aka ɗaura auren mu da Dr nah agarin Tilde, inda Baban mu dama ya yi ginin shi mai kyaun gaske a gefen gidan su, zuwa yamma a ka ɗaukoni zuwa garin bauchi, ranan Daddy na ba ƙaramin kuka yayi ba, wanda dayawa sai da suka taya shi kukan, ni kuma nayi kuka domin a ranan na ƙara tausayawa Daddy na rashin mummy na da yayi. A bauchi Aunty hauwa ce ta sauƙi mutane, inda Aunty Fatima da su Aunty Ummi da Aunty Indo ne suka ɗaukoni, kai ranan gaba ɗaya ahalin Baban Narabi ƙannen Kakana duk sunzo, inda duk yadda akayi da Uncle sabo da Uncle Abdallah kada su mun komai ƙi sukayi, domin Mota ko wannen su ya saya mun, domin Daddy na da Ummi da Abba sun cika mun gida na da gadaje masu tsadar gaske, ita kuma Aunty Fatima cewa tayi kada kowa ya sayi kayan kitchen, don itace uwa ita zatayi, lokacin dana leƙa kitchen ɗina kuwa ba ƙaramin kuka nayi ba, domin nikan yanzu bazan iya cewa nayi maraicin uwa ba, dama Daddy bai taɓa barina nayi kukan rashinta ba, yanzu kuma da ya sakewa zuciyar shi yabarni cikin familynta sai naji duniya bani da abinda yafi so. Abin dariya Uncle Hassan da baby suma sukace dole abar musu side ɗin Baby, wai suma zasuyi kayan uba a matsayin su na yayun Mummy, kowa ya ga irin kayan da suka zuba a ciki sai yayi santi, domin ɗaki biyu ne da parlour a side ɗin baby, kuma babu irin kayan alatun da basu zuba a ciki ba. Side ɗina ma parlour ne da 3bedroom, shima babu irin kayan da Daddy na bai zuba ba, nidai gaskiya naga gata a wurin ƴan'uwa na, inda kuma dama anyi zama domin magana su Amaal da Faisal, haka Abbu yace ya bada Amaal wa Affan, amma ya sanar musu sickler ce, haka su Uncle Auwal suka bada Jeedderh wa Faisal, an tsayar da maganan aure har sai Amaal ta gama karatu, ana gama biki washe gari su Abbu suka wuce saudi, inda mukayi kuka nida Amaal kaman ba nan da 1week zamu haɗu ba. Bayan kowa ya watse ne Uncle Hassan ya rako Baby, har parlour na suka shigo, abin dariya ya bani inda Baby yazo "wai ke ƴan mata ki fito ki gaisa da abokai na suna parlour," ɗago da kai nayi na ɗaga mishi kafaɗa alaman bazan fito ba, murmushi yayi ya ɗaga murya da ƙarfi yace, "Uncle Hassan tace bazan fito ba ka tafi saida safe" da gudu na tashi nayi hanyar parlourn ina, "uncle Hassan Allah bance ba, gani na fito", dariya dukkan su sukeyi inda Baby ya fito ta bayana yana ta dariya. Wuri ɗaya suka zauna, inda ban taɓa tsayawa naga irin kamanini su ba irin na yau, domin kayan su iri ɗaya ne, zaman da sukayi ma iri ɗaya ne, gashi dukkan su yau fuskar su ɗauke da farin glass yake, murmushi nayi nace, "uncle kuna kama fa". Dariya yayi ya fara bani labarin lokacin da suke school, yadda yake zuwa yace wa yarinya yana sonta, ranan da ta ganshi da wata sai yace bashi bane ɗan'uwan sa take nufi, kuma basu gane su, hakan sukayi ta ban labarin yarintar su ina dariya, duban uncle Hassan baby yayi yace. "Bros ka tashi ka tafi wurin mama Fatima, domin ni yau aikin furta I luv u ne akaina har asuba, inda hali ka taho mun da maganin ciwon baki, don tabbas yau leɓe ne sai sun kunbura da furta I luv u wa baby da zan tayi", dariya suka saka gaba ɗaya, Uncle Hassan yace, "gaskiya ban mantaba, kasha gaya mun duk daren da kayi aure kwana zakayi kana gayawa mai sa'ar matar ka kalman so". Na ɗauka wasa baby yakeyi, bayan tafiyar Uncle hassan wanka mukayi, ya ɗauko mun wata white rigar bacci, shima kuma white ɗin ya saka, duk muka feshe jikin mu da wasu turaruka masu ƙamshin gaske, haka na zauna a tsakiyar gado inda baby ya umurceni da na zauna, zama shima yayi ya tanƙwashe ƙafan shi irin tadda nayi,don har gwiwarmu suna haɗuwa dana juna. Tun ina ɗaukan abin wasa har na fara karaya da irin kalaman soyayyah da baby yake gaya mun, sannan duk bayan wasu lokuta zai nuna wani wuri a jikina yace, "baby idon ki yamun kyau, baby ƙwayar idonki yafi komai kyau a jikinki, baby ban taɓa ganin kyaun lips irin naki ba, baby dubi kyaun gashinki, ban taɓa ganin mace mai kyaun tsari na halittah ba irin naki," kuma duk inda zaiyi misali da shi sai hannun shi ya kai wurin. Duk yadda nake tunanin zan iya bacci amma kasawa nayi, gaba ɗaya ma sai naji wani hawayene mai masifar yawa yana bin fuskana, a hankali na furta mishi, "ina sonka Baby! Ina sonka baby nerh!!. Rungumeshi nayi da ƙarfi bayan munji an fara ƙiran sallan asuba, ranan gaba ɗaya familyn mu suka zo mun sallama, kowa ya koma inda ya fito, nidai duk inda naga baby sai naji anƴa akwai matar da tayi dace da soyayyan miji kuwa irin nawa? Gaskiya ina son Baby. Da dare haka baby ya ɗauko mana wasu kayan baccin masu ruwan sky blue, gaba kyaun su yafi na daren jiya da muka saka, a daren yau na ɗauka baby zai ci gaba da baiyana mun sirrakan zuciyar shine da baki, ashe nayi kuskure, soyayyar da ya ƙunsheta mai zafin gaske a zuciyar shi ce yau ya sauƙe mun ita a aikace, ranan nayi danasanin irin yadda nayita buɗe bakina ina kwwankaɗan tsumin Aisha Garkuwa da gumbarta da na sha, kai hattah wannan haɗin kazarta da haɗin nasha da kankanan danayi amfani dasu nayi dana sanin amsa a wurin Ummi babu musu na dinga ci. Aunty Fatima nane tazo tayita faman rarrashina ranan, don firr baby ya kasa gane kaina, daga tayi magana tace "haba doughter babyn kine fa", da karfi zan fasa mata kuka nace, "mummy babban mutumin ne zaki ce mishi baby? Na daina ce mishi baby, kawai Baban mutum sunan shi", haka zan faɗa ban lura ba Aunty Fati kuma sai ta ɓingile da dariya tana, "haba babyn baby". Muna gama school akayi auren Amaal da Affan, Faisal da Jeederh, lokacin kuma da ƙyar nake jan cikina wanda yayi nauyin gaske, haka muka zauna a gidan Ummi don firr naƙi komawa namu gidan, don gaskiya bazan iya da fitinar baby ba, don ko duba yanayina bayayi, haka na zauna a wurin Ummi na. Ranan talata na tashi da naƙuda mai matuƙar wahala, wanda dama lokacin Uncle Abdallah sun dawo nigeria da zama, suna zaune a cikin garin jos, haka Ummi ta ɗagawa kowa hankali, babu shiri Aunty hauwa ta tattaro ta taho bauchi, itama Aunty Fatima Ummi bata barta ta huta ba, domin ko arba'in batayi da haihuwar ɗanta ba, amma haka tayi ta ƙiran su, Aunty hauwa tana isowa ko rabin awa banyi ba na haifi ƴan biyu na dukkan su mata. Ummi tana ganin su ta dubi Baby tayi mishi gwalo tace, "mu aka sake zubuwa sak, kai Hauwa nida ke jininmu yana da ƙarfi, ko kuma nace jinina na da ƙarfi, hauwa kika biyo kamanni na, Aisha ta ɗauko mu, Fatima ta biyomu, Humaira ma mu sak, gashi wasu ƴan biyun yauma babu maraba damu kenan". Murmushi Aunty hauwa tayi tace, "waƴannan sun nuna mana so ne fisabilillah, da yake Adda

Chapter 27 of 28