An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Bismillahirrahmanirrahim.
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 01.
Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.
اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ
*Jan hankali*
K’addara mai kyau ko marar kyau ta kan samu bawa a duk lokacin da Ubangiji ya so ba dan saboda wayonsa ko akasin haka ba, ya kamata mu sake yarda da cewa bawa baya tab’a haure k’addararsa domin ita k’addara yashi ce ko
an dunk’uleta ba ta dunk’uluwa.
A ko da yaushe ana so musulmi ya kasance mai fatan alkhairi ga d’an uwansa musulmi domin shi harshe yana da kaifi kuma gatse ga k’addarar wani kuskure ne babba! Sannan gori da kyamata ga d’an uwa musulmi ba abune mai kyau ba tunda mutum ba shi ya tsarawa kansa tasa k’addarar ba…….
Ya ku samari matasa manyan gobe, shaye shaye da harkar dabanci babu inda take kai mutum sai dai ta nakasta shi, shin ina riba ga wanda bai tsaya ya mayar da hankali wajen gina future d’insa a wannan k’asa tamu da kowa kansa kawai ya sani ba?
Ku daina yiwa mutanen da ko kad’an bazasu so ganin nasu y’ay’an a rayuwar da kuka jefa kanku a ciki ba hidima, abincin ku ba a hannunsu yake ba ku tashi ku nemi na kanku, ko wanne bawa yana da tashi kalar baiwar dan haka ku daina treating kuna kallon kanku as jobless..dig deep into that beautiful brain of yours there is definitely a gift in there!.
*Gargad’i*
Littafin ANA MALIK k’agaggen labari ne wanda ni Humaira Bulama na k’irk’ira na rubuta, ban yi dan kwaikwayo ko cin zarafin wani ko wata ba, idan ka/kika ci karo da abunda ya yi kamanceceniya da rayuwarka/ki to arashi ne.
Ban yarda kuma ban lamunta sannan ban amince wani ko wata ya juya min labari ta ko wacce fuska, ba tare da izinina ba. Yin hakan babban kuskure ne.
*Farawa*
Ina rok’on Allah da ya yi ruk’o da hannayena ya bani ikon rubuta dai dai da kuma abinda zai amfani al’umma baki d’aya. Yadda na fara lafiya Ya Ubangiji ka bani ikon gamawa lafiya.
بِسْمِ ٱللَّٰهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Dare mahutar bawa! In ji masu iya magana, Hausawa.
A lokacin da hankali ya kan kwanta, shiru yake maye gurbin hayaniya, nutsuwa take maye gurbin karafniya sannan hutu yake maye gurbin gajiya. Ga kusan kowa hakanne dan in dai aka ce dare ya yi to ko wanne bawa ba shi da wani burin da ya wuce ya sanya hak’ark’arinsa a nutsuwa ya huta.
Tsakar gida ne mai d’auke da d’akuna barkatai! Da alama mutanen gidan ba su kai ga yin barci ba dan ko wanne d’aki kana iya hango fitila ko kendir d’insa a kunne ga kuma maganganu da ake iya jiyowa suna tashi sama sama kamar dai ba dare ba.
Kwance take cikin d’aya daga cikin d’akunan gidan ta inda ta yi kwanciyar rigingine ta na kallon fasashshen silin d’in da ya yiwa saman d’akin nasu k’awanya, a zahirin gaskiya idan ka kalleta silin d’in take kallo amma a asalin gaskiya gaba d’aya hankalinta ba ya a kan silin d’in dan inda ace za a tambayeta meyene shi d’in to da ba lalle ta iya bada amsa tashi d’aya ba.
A karo na uku ta sake juyawa ta kallesu ta tabbatar da sun yi barci dan har gwartin su take ji yana tashi sama sama.
A hankali jikinta a sanyaye yana wani irin karkarwa zuciyarta tana dad’a yin zafi ta mik’e ta zauna idanuwanta a kansu suna masu cicciko da ruwan kwalla sai dai ita kanta ta san hawayen ba iya zubowa za su yi ba.
Mik’ewa ta yi tsaye har yanzun idanuwanta a kansu, ba ta da kowa sai su kuma tana matuk’ar jinsu a cikin ranta..kamar yadda ba ta da kowa sai su haka nan a nasu b’angaren suma ba su da kowa sai ita shiyasa ta ke da tabbacin za su yi k’ewarta dukda kuwa a cikin bala’in da ta zamo silar jefasu amma ta san tabbas za su sake shiga cikin mawuyacin hali idan ta barsu sai dai kuma ta san hakan da yin hakan a gareta da su gaba d’aya shine dai dai..Gara ta tafi su ji zafin tafiyarta na kwanaki kad’an daga nan ta san za su ci gaba da rayuwa mai dad’i sab’anin idan ta ci gaba da zama da su wanda ta ke da tabbacin komai sake tab’arb’are musu zai yi! Tabbas ita a karan kanta ta yarda kuma ta amince da sunan da kowa yake kiranta da shi a yanzu ‘Annoba’, ba ta jin akwai alfanun ci gaba da rayuwa a tsakiyar su kai ba ma iyaka su kad’ai ba al’umma kanta gaba d’aya bataga amfanin zama a cikinta tana janyo musu bala’i dami-dami ba!
Dan haka ta juya a hankali cikin tafiyar da a yanzun ta zame mata jiki kamar ba ita ce ma’abociyar kazar kazar da karafniyar nan ba ta fara tafiya kamar marar lakka a jiki yayinda jikin nata yake wani irin karkarwa…. A haka ta nufi k’ofar fita daga d’akin zuciyarta tana mai dad’a tabbatar mata ‘Tabbas abinda kika shirya yi shine dai-dai!!!’.
Babu kowa a tsakar gidan dan yanzun misalin k’arfe sha biyu na dare ake nema amma fa baya ga mutanen da ta baro a d’aki suna bacci ta sanadiyyar alluran da aka yi musu babu wanda yake da ma shirin yin barci a kaff cikin gidan wanda dalilin rashin kwanciyar tasu da wuri yana da nasaba da alhinin da suke a ciki yayinda waenda basusan Annabi ya faku ba zaman munafurci ne suka zauna yi.
D’akunan ta bi da kallo, duk da yawansu amma ta gaza dukan k’irji ta nuna guda d’aya tak! Wanda za ta ce ba ta saka y’an d’akin a cikin alhini jafa’i tare da damuwa ba.
A hankali ta juya ta kalli d’akinsu a karo na farko tunda satin nan ya kama ta ji hawaye ya silalo ta cikin idanuwanta dan a lokacin da masifa ta kai masifa kuka yaji ya yi mata ya k’aura ya bar cikin kwayar idanuwanta. A take ta fara jin kamar ba zata iya aikata abinda ta shirya ba, gudun fasawartata da ta ji wani sashe na zuciyarta yana shirin bijiro mata da shi ne ya sanya ta wuce cikin sassarfa ta nufi tafkekiyar rijiyar da ke a chan kusurwar tsakar gidan. Ta na isa ta saka hannu ta jaa katokon da yake rufe da rijiyar a hankali ta bud’eta gudun kar a jita, so take sai da safe idan sun fahimta su tsinci gawarta a ciki idan kuma ba su fahimta ba ta rub’e a ciki su k’araci nemanta su hak’ura.
Iyaka kallon rijiyar kad’ai ya Isa ya sanya ka ji tsoro tsabar girmanta sai dai gareta sam ba hakan bane ba dan ko d’igon tsoro ba ta ji ba saboda rayuwar da take ciki a yanzu ta fi k’unci! Azabtarwa!! Kad’aici..
fiye da rayuwar da ta san zata yi na wucin gadi a cikin ruwan rijiyar kafin Allah ya karb’i ranta, sannan ko ba komai babu wanda za ta ji kunyar had’a ido da shi a cikin rijiyar sab’anin yanzu da take ji kamar ta binne kanta…….
A hankali ta taka dakalin rijiyar ta hau ba ta bari ta tsaya b’ata lokaci ba ta yi tsalle ta afka ciki tsundum!.
…….
Hayaniya mai tsananin firgitarwa ce take tashi a tsakar gidan dan harda koke koke yayinda hankulan makusantanta ya kai k’ololuwa wajen tashi!
Zuwa yanzu hayaniyar ta su ta fara gushe mata
sab’anin daa da take iya jiyosu….a hankali ta lumshe idanuwanta tana sake nutso a cikin ruwan rijiyar da ta yi lamooo a cikinsa dukda kuwa azabar rashin numfashi ta kai k’ololuwa wajen azabtar da ita amma tabbas hakan ya fiye mata akan azaba da k’uncin da zuciyarta suke ciki a doron k’asa.
UNGUWA UKU (Babban layi….)
Juma’atu babbar rana..Kamar ko wacce rana ta Juma’ah haka itama wannan Jum’ar ta kasance ranar sada zumunci da yawace yawacen gidajen k’awaye ga y’an Yara Yaran layin saboda yau d’in babu makaranta sai hutu wasa da tsalle tsalle a garesu.
Misalin k’arfe biyu da mintuna arba’in kenan..masu zaman majalisu na yi masu gaishe gaishe na yi masu yawo da tsalle tsalle suma suna na su.
A bakin kiosk d’in wani mai p.o.s kusan duk samarin layin suka taru ana hira ana raha dan basu dad’e da dawowa daga masallacin na Juma’a ba wanda hakan shi ya taimakawa layin wajen sake yin albarka ya cika taff tubarkallah.
Da gudu wata Yarinya ta k’araso wajen, tana zuwa ta sauk’e idanunta a kan wani kyakkyawan saurayi dogo bak’i, tana haki cikin mayar da numfashi ta ce “Ya Aminu! Ya Aminu!!! Ga su Ma’a chan sun tarewa Dije hanya a bakin filin kashu.”
D’iff!! Haka maganar kowa ta tsaya chak! Kamar an yi ruwa ya cinye su yayinda tsoro mai had’e da firgici ya maye gurbin raha da annashuwar dake kwance a kan fuskokinsu yanzun nan.
Da kyar wani daga cikin samarin ya ce “Minu, kuma tunda har kun san ya takura mata ku daina aikenta inda kuka san shima yana yawan zuwa mana.”
Da kyar k’irjin Ya Aminu ya na dukan uku uku ya iya cewa “na hana, ban san me ya kaita chan ba.”
Sai kuma ya yi saurin yunk’urawa ya ce “bari in je”.
Y’an layin koma ace anguwar gaba d’aya suna da masifar had’in kai, duk abinda ya shafeka to ya shafi kowa haka nan suke rayuwarsu saidai a yanzun da kyar aka iya samun mutum biyu suka bi Minu ragowar kuma suka fake da tafiya police station dan su je su taho da y’an sandan da kowa ya san basu isa su iya yiwa Ma’a d’in uwar komai ba.
Duk da cewa ita d’in budurwa ce mai tashe dan a k’alla shekarunta sun haura sha shidda da kad’an amma still yanayin k’irar jikinta ta fi shekarun nata dan kallo d’aya za ka yi mata ko daga kusa ko daga nesa ka fahimci ita d’in tana cikin jerin matan da Allah ya wadata su da k’ira mai kyau…..Daga ido idan ka kalli yanayin jikinta za ka yi mata kallon babbar budurwa duba da yadda komai na girma ya gama baiyyana da tabbata a tattare da ita, sai dai kuma yanayin d’abiarta zai sanya ka fahimci har yanzun akwai ragowar k’uruciya a tattare da ita.
Shekarun nata sun haura sha shidda amma ba su kai sha bakwai ba wanda idan ka matso ka yi mata kallon k’urilla to yanayin fuskarta ma kawai zai iya k’iyasta maka adadin shekarun nata.
Tsaye take ta kama k’ugu tana masifa da tujara babu alamun tsoro ko sassauchi a tattare da ita, wasu zaratan samari su uku ne a tsaye a gabanta wanda ko da wasa bai kamata ace ta tsaya yi musu kallon banza ba ma ballantana masifar da take ta zazzage musu kamar ta samu y’ay’an cikinta! Ba wai iyaka shekarunsu ne ya kamata a ce ya sanya a ji tsoronsu ba! Yanayi da suffar su kad’ai ta Isa ta firgita Yarinya mai shekaru irin nata, ba ma ita ba ko Babba bai isa ya ce zai kalli su Ma’a ya yi musu da su ba ma ballantana fad’a…
D’aya bayan d’aya ake watsewa a wajen, hatta masu kiosk rufewa suka fara yi masu trader suma tuni suka fara tuttura abun sana’ar su suna barin wajen, dama tun tunkarowar Ma’a da shi da Yaransa guda biyu wajen aka fara tarwatsewa to kuma yanzu behavior d’in wannan y’a marar ta ido ya sanya kowa yi ta kansa tun kafin Ma’a ya yi kan mai uwa da wabi.
Dai dai lokacin da su Minu suke isowa wajen suna haki dan gudu suka tsula dai dai ita kuma ta durk’usa ta tittilo k’asa a duka hannayenta biyu zata b’ulawa Ma’a shi da su scorpion sakamokon kunnen uwar shegun da suka yi mata (sun k’i tanka mata kuma sun k’i su bata hanya ta wuce).
Da mugun sauri Minu ya kamo ta ya juyo da ita ya kakkab’e hannuwan nata cikin fushi ya ce “sai yaushe za ki fara jin magana ne? Eh??”
Ya fad’i ‘eh’ d’in da mugun k’arfi kamar mai shirin rufeta da duka!…
..Yanzu haka Inna tana chan a kwance jininta ya hau jiya da kyar ya rage ba a basu gado a asibiti ba duk a ta sanadiyyar fad’an DIJE da Kaka wanda daga k’arshe ya k’are a kan Innar dan babu kalar cin mutuncin da Kaka bata yi musu ba a jiyan, amma shine yanzu tsabar Iskanci ta zo zata zubawa Ma’a da Yaransa k’asa a jiki salon ta janyo musu masifa….
Da kyar ya iya lallab’a zuciyarsa da take ingiza shi akan ya rufe ta da duka, ya juyo a hankali bayan ya sakata a bayansa ya na kallon k’asa dan a k’a’ida ba a had’a ido da Ma’a ya ce “ka yi hak’uri dan Allah, Yarinya ce za a yi mata fad’a.”
Irin tsayuwar sojoji ya yi…..ta inda ya saka hannayensa duka biyu a bayansa ya d’an raba k’afafunsa ba sosai ba ta hanyar bubbud’a su kad’an! Yayin da ragowar samari biyun suke tsaye a ta gefe da gefensa d’an bayansa kad’an dan basu jera da shi ba!
Dogo ne sosai sannan yana da fad’in k’ashi amma bai cika k’iba ba sam, yanayin surar jikinsa dai a murje take sannan a murmure kuma a murd’e wanda hakan ya taimakawa surar jikinsa ta giant sake baiyyana. Ba bak’i bane ba kuma ba za a kirashi da fari ba, yanada dogon hanci da madaidaitan idanuwa masu tsayi da asalin kyau, da matsakaicin baki wanda yake nan bak’i k’irin wuluk! Kyakkyawa ne idan ka k’ura masa ido wanda tsage-tsage da tabubbunan da suke a fuska har ma da ilahirin jikinsa ne suka bada gudunmmawa wajen b’oye ainahin kyawun nasa…. Daga kan tsakiyar goshinsa wata mahaukaciyar sara ce ta taho a karkace ta bi ta kan idonsa na hannun hagu ta sauk’a a dai dai setin k’arshen kunnensa, Allah ya taimake sa bata tab’a masa idon ba dan tar yake kallonta kuma kana ganin idon ka ga mai lafiya sai dai ta bi har ta kan saman fatar idon nasa ana ganinta tarr! Sai kuma yanke yanke wajen kala
biyar a sashe daban daban na fuskar tasa. Kamar yadda fuskarsa take haka nan jikinsa shima yake babu kyan gani, gashi dai shi d’in musulmi ne amma jikinsa har da tattoo a wajen damtsen hannunsa na dama an rubuta ‘mamana’ da wani font mai kyau da heart a gaba y’ar k’arama.
K’arafuna kuwa su sark’ok’i da zobuna da belt da takalmin jikinsa kamar wani kare.
Yana sanye da jeans d’in khakin sojoji da bak’ar vest kanshi babu hula sai wani d’an Iskan aski. Yaransa kuma gajerun wanduna ne a jikinsu sai tshirt da p cap a kan d’ayan, yadda jikinsa yake haka nan suma nasu ya b’aci da tabubbuna d’ayan har da k’unar wuta a kafatarin ilahirin b’arin fuskarsa.
Tunda Minu ya fara magana ya kafe shi da idanu ba tare da ya ce komai ba. Sai da ya dire aya tukunna ya sa hannu ya turesa gefe ya gyara tsayuwar sa sannan ya yi taku biyu ya isa gaban Dije yana zuwa ya sa hannu ya finciko hijabinta ta tafi zata afka jikinsa Minu ya yi kalmar shahada ya yi kukan kura ya shiga tsakaninsu ya sake ture Dije daga garesa a karo na biyu.
Cika mata hijab d’in nata ya yi ta hanyar ware hannuwansa duka biyu da k’arfi kuma a lokaci guda kamar wanda aka cewa action! D’an taku d’aya ya yi ya ja baya dan sosai Minu ya shige cikin jikinsa wajen k’ok’arin raba kusancinsa da Dije, sai da ya runtse idanunsa ya yi iyaka bakin k’ok’arinsa wajen tausar kansa dan kar ya yiwa Minu illah tukunna ya bud’e idanunsa da suka rine da b’acin rai ya zubasu a kan Minu wanda ya sha jinin jikinsa ya fara karkarwa, bakinsa na karkarwa yana shirin yin magana d’aya daga cikin Yaran Ma’a d’in ‘Oscar’ ya d’aukesa da wani irin gigitaccen marin da saida ya tafi kamar ana ingizashi ya je ya bugu da wani k’aton dutse.
Dai dai nan motar y’an sanda ta doso wajen wanda hakan ba k’aramin mamaki ya bawa mutanen da suke d’an lellek’owa ba dan basu san amfanin zuwan y’an sandan ba.
Aikuwa ilai!..Suna hango shi suka ja suka tsaya suka k’i k’arasawa wajen, suna mamakin k’aryar da samarin suka yi musu suka kwaso su suka kawo su nan wanda sun san tab’a shi dai dai yake da rasa aiyyukan su, duk matsayin mutum kuwa.
Tunda aka yi wurgi da Ya Aminu ta nufesa ta durk’usa a wajen ta fashe da kuka dan sam baya motsi gashi gefen kansa inda ya bugu da dutsen sosai ya fashe.
Kukan da take yi sai da ta bawa kowa tausayi a wajen gashi babu mai damar taimakonsu.
Tunda ta je ta durk’usa a wajen yake kallonta, kafin daga bisani ya juya ya yi wani tsaki ya bar wajen.
Sai da ya yi wajen taku biyar tukunna Yaran nasa suka samu damar binsa a baya dan abun ya yi matuk’ar basu mamaki! Su da suke shirin fara cin uwar Minu a hakan a yadda yake amma kalli abinda Oga ya yi!?
Sosai abun ya d’aure musu kai amma sai suka yi tunanin maybe barinsa zai yi ya warke tukunna ya ci ubansa ta yadda zai fi galabaituwa! Amma kuma duba da yadda Yarinyar itama ta dad’e tana yi musu hauka amma ya hana ko kallon banza ne a yi mata ya sanya suka saka kokwanto a al’amarin….
A haka dai suka bishi a baya zuciyoyinsu fal tambayoyin da basu isa su yisu ba.
Su Ma’a suna wucewa kowa ya tuttulo aka yo kan Minu har da y’an sandan da aka d’auko takanas akan su yiwa tufkar hanci kafin a yi b’arna amma suka mak’ale.
Suna zuwa wajen wata tsohowa ta ce “Dalla chan malamai ku matsa daga nan, baku da amfani kwata kwata ga al’aumma wallahi, ace Yaro kwalli d’aya ya addabemu ya hana mu sukuni amma kun kasa tab’uka uwar komai! Tsoronsa kuke ji ne? Ko
ya fi k’arfin hukuma ne?”.
Ai kuwa kamar jira jama’ar wajen suke yi nan suka hau kan y’an sandan kamar za su rufe su da duka.
Basu kula su ba instead k’ok’ari suka yi suka saka Minu a mota a ka wuce da shi asibiti zuciyoyinsu fal alhini! Tabbas abunda mutanen nan suka fad’a gaskiya ne amma suma d’in komai ya fi k’arfin su ne shiyasa.
Kusan duk mutanen da suka zo da y’an sandan ne suka tafi kai Minu asibiti, d’aya daga cikin biyun da suka taho da shi wajen Ma’a d’azu ‘Ya Kamal’ kuma ya tafi kai Dije gida domin su je su sanarwa da su Mallan halin da ake ciki.
Babban gida ne gidan haya mai d’auke da d’akuna a k’alla guda goma sha uku…ta wani dogon soro suka bi kafin su k’arasa cikin gidan wanda tsakar gidan dududu ba zai iya cinye k’ananan motoci biyu ba amma sai uban tarkace da igiyoyin shanya ga wata uwar rijiya da aka yiwa d’ogwarago kana shiga ita kake fara hange. Band’akin maza a farko-farkon dogon soron yake yayinda na mata yake ata gefe jikin k’ofar shigowa cikin tsakar gidan sai kitchen a ta chaan lungun bandak’in matan fuskarsa tana kallon ka idan ka kalli direction d’in da yake. Daga kitchen d’in har band’akunan gaba d’aya babu wanda ya samu arzik’in k’ofa sai dai in ka zo shiga bayin ka nemi zani ko dai wani kyallen ka yafa ka yi uzurin ka wanda hakan shike nunawa wanda ya tunkaro wajen akwai mutum a ciki. Siminti ne a shimfid’e a tsakar gidan wanda bashi da maraba da rairayi sakamokon farfashewar da yayi ta koina.
Daga b’angaren dama d’akuna ne guda hud’u y’an fici fici a jere sai guda uku suna kallon su yayinda hud’u suke a ta chan k’uryar gidan a jere suna kallon k’ofa sai guda biyu manya manya sosai d’ayan har da band’aki a cinkinsa suna kallon ukun k’ofofinsu jere da k’ofar shigowa amma d’ayan d’akin an bud’e masa wata k’ofar ta soro.
A tsakar gidan akwai kejin kaji mai hawa biyu da alama kiwo mai shi yake yi sannan alwai rago da akuya sabbin haihuwa ga kuma uban tulin wanki k’ulli-k’ulli wani a kan wani sun kai guda goma wanda kana gani ka san akwai mai wankau a gidan.
A tsaye cirko cirko suka tarar da mutanen gidan Yara da manya da y’an mata..tsakar gidan ya cika taff da jama’a tubarkallah har da mak’wafta.
Zainab ta hanga a tsakiyarsu Yarinyar da ba zata haura shekaru sha biyu ba, hankalin kowa a kanta tana ta zuba bayani dalla dalla, duk inda ta kai aya ta dire sai a hau salati da sallallami ana tafa hannu sai kuma a yi shiru ita kuma ta d’aura daga inda ta tsaya.
Tsabar yadda hankalin ilahirin jama’ar yake a kan Zainab babu wanda ya lura da shigowar Dije da Ya Kamal, idanunsu ya rufe daga jin labarin A’bu wanda yake kamar busharar shiga gidan aljannah a zuciyoyin wasu.
Ganin yadda aka bata muhimmanci aka yi mata k’awanya kowa ya bata hankalinsa ya sanya Zainab d’in ta fara had’awa da k’arya da sharri har da cewa “da Ma’a ya janyo Dije sai da ya rungumeta ya shafa mata k’ugu tukunna da kyar ya Aminu ya finciketa daga jikinsa”
Wata y’ar budurwa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 23