ai ba zanga laifinki ba tunda na san Abokin mutuwa kike nema! Gara mu zargi kuke yi ashahadu a wuyanku! Yanzu idan aka ce ku kawo sheda na san wallahi sai dai a kasheku! Saboda na yarda da Dije d’ari bisa d’ari kuma wallahi abun kunya ba dai a kanta ba ta fi k’arfin haka!!!!
Ke kuwa a gidanku ni shaida ce y’ar uwarki sai da ta haifi shege ga shi chan yana yawo.”
Da sauri Iyya ta matso ta ce “Halima ya isa haka gori babu kyau ko me suka yi miki ki barsu da halinsu. Sannan dan Allah kar in sake ji kince wani ya fi k’arfin k’addara”
Dariyar rainin wayo Asabe ta yi sannan ta ce “Allah na tuba k’addara kuma ta nawa? Jiya ma fa kina ji an ce har filin ball ta bisa dayake abun ya motsa tana so a sosa mata inda yake yi mata k’aik’aiyi!”
Cikin tsananin b’acin rai Inna ta ce “tsabar ke dak’iyaya ce ki rasa a ina zaki yi sharrin naki sai a filin ball tangamemen waje idanun kowa a kansu? Idan kin tashi sharri ki dinga yin wanda hankali zai d’auta mana!
Ko da yake ba zan ga laifinki ba dan hatta Kattime ashe da cikinta aka yi auren iyayenki sannan yanzu haka babu aure a tsakaninsu suke zaune amma har fad’an kwana take yi da kishiyoyi, amaryar gidanku ma da aka saka kwanaki saboda fad’an kwana da tayi da uwarki ne aka saketa bayan ita uwartaki a musulunci ma bata da kwanan sai dai zina!”
D’ifff haka Asabe ta d’auke wuta, tabbas baki ya san abunda zai fad’a amma bai san me za a mayar masa ba! Ta rasa ta yaya Halima ta ke samun zafafan surrrukanta da na gidansu, wanda a duk lokacin da suka yi fad’a sai an ji new update daga bakinta.
Cikin fushi Inna ta ci gaba da cewa “dan haka Zina da kike ta ambata a gindinki ta k’are ke da y’an gidanku da iyayenki ba dai Dije ba wallahi na fad’a na k’ara fad’a Dije ta fi k’arfin wannan lalatar dan na yarda da tarbiyyar da na bata. Kuma ba ta gada ba ba ta sha a nono ba kamar yadda yake yawo a jininku.”
Ke kuma da kike cewa dole Sagir ya kalleta yanzu hakan har abun alfahari ne? Ragowar mazan gidan su mai yasa basu kalleta ba? Ko mata maza ne su? Sai shi k’aramin d’an iska ko?
Kinsan a tafin hannuna kike dan haka wallahi ku kiyaye ni in ba haka ba zan yi muku abunda hankali bai zata ba muddin kuka sake shiga sabgarmu.”
Tana gama fad’in haka ta wuce ciki ta je ta janyo hannun Dije wadda tun d’azu ta k’ame a kitchen d’in take kuka. Suka fito suka wuce d’aki aka bar ragowar mutanen gidan da k’us-k’us, wanda da yawa a kan maganar gidansu Asabe da Inna ta sakar musu latest suke yi. Mahaifin Asabe irin babban mutum ne a unguwar kowa ya sanshi sai dai mai kud’in bahaushe ne dan shi kansa idan kika ganshi ba za ki ce ya tara ba ballantana y’ay’a da matansa, kusan kaso goma a cikin d’ari na gidajen Unguwar duk nasa ne amma ko atamfar anko idan ta fito ba iya siyawa mata da y’ay’ansa yake yi ba dan abun nasa ya had’e masa da matsananciyar rowa da mammak’o da son tara kud’i (ko wa yake taramawa? Oho masa!)
Kusan kowa ya san gidansu wannan dalili ya sa idan aka ji b’im! Na gidan ake d’abbaka abun a zuzuta shi!”.
Suna wucewa Minu ya shiga ya d’auki flask d’in abinci ya fice dan sai a lokacin hankalinsa ya samu damar jiyo masa vibration d’in wayarsa da take cikin aljihun jean d’in jikinsa wanda yake da tabbacin Mallan ne.
Su Dije suna shiga d’aki ta zube a k’asa ta shiga bawa Inna hak’uri, ko kallonta Innar ba ta yi ba ta wuce ta je kan gadonta ta zauna tana huci tana jijjjiga k’afa dan bata gama hucewa ba.
Sun jima a haka kafin Dije ta zame ta kwanta a wajen tana sauk’e ajiyar zuciya ajejjere, ba ta dad’e ba bacci ya yi awon gaba da ita.
GIDAN SU DIJE.
Asalin Mallan cikakken Bahaushen garin Kano
ne, k’auyen Getso.
Kaka su biyu kacal Allah ya bata Mallan (Bashir) da d’an uwansa Kawu Isa wanda shi har yanzu yake zaune a k’auyen Getso yayinda Mallan dama shi tun lokacin da ya baro garin ya taho neman ilimi yake zaune a gidan Malaminsu, wanda zuwa yanzu Allah ya yi masa rasuwa.
A nan ya had’u da Inna (Halima) wadda babu kalar abunda Kaka bata yi ba dan kar a yi auren amma da yake rabo ya rantse sai da aka yi..Da taimakon Mahaifin Mallan wanda yake tsananin son had’in ba dan komai ba sai dan fahimtar da ya yi Halima ita ce sanyin idaniyar d’an nasa ita ce farincikinsa, dan haka ya tsaya tsayin daka har sai da ya ga auren tukunna hankalinsa ya kwanta, wanda ana yin auren da wata d’aya ciff Allah ya karb’i ransa, (shekaru talatin da d’aya kenan yanzu).
Anan Mallan ya sayi gida bayan an raba musu gado, wanda nan ma iko da kud’irar Allah kad’ai ta sanya aka sayi gidan nan dan babu yadda Inna ba ta yi ba amma ya sayar da gonar sa ya zo ya sayi gida babba mai d’akuna da yawa a unguwa uku, dan Mallan ya so tara y’ay’a barkatai hakan shine burinsa, dukda kuwa ya saka a ransa in sha Allah Halima ita kad’ai ce matar aurensa amma ya tsara zata haifa masa akai-akai in sha Allahu har sai haihuwar ta tsaya dan kanta.
Bayan rasuwar Mahaifinsa Kaka k’in ci gaba da zama a Getso ta yi ta tarkato ta dawo gidan Mallan da d’amarar korar Inna daga gidan ta ko wacce hanya.
Kwata-kwata Mallan bai san cewa Kaka ba ta son Halima ba dan ta k’ark’ashin k’asa take yin komai. Sai da Inna ta samu cikin Ya Muhammad tukunna true colour d’in Kaka ya fito fili ras! Dan kasa ci gaba da danne tsanar Halima ta yi, hankalinsa ya tashi kam a wannan lokacin dan k’iri-k’iri Kaka ta nuna ba ta son cikin k’arshe ma ta ce ba na Mallan d’in bane ba, sai da ta saka Inna ta rantse a gaban mai unguwa tukunna aka samu ta sarara mata.
Tun daga nan kuwa hankalin Mallan bai kwanta ba, dan tunda Inna ta fahimci Kaka bata k’aunarta itama ta botsare dama itama fitinanniyar ce ta bugawa a jarida shiyasa kwata-kwata sai aka gagara samun sauk’i ta ko wanne b’angare, kullum cikin rigima suke babu mai d’agawa wani k’afa.
Sai da Kaka ta kwanta jinya a lokacin da aka ce mata Inna ta haifi d’anta Namiji fari sol da shi kamarsu d’aya sak! Kamar ta yi kaki ta tofar( lokacin shekara d’aya da auran Inna da Mallan).
Bayan ta warke ta je Getso ta dawo, ita dai Inna har gobe Kaka take zargi akan rashin lafiyar Ya Muhammad dan tunda ta dawo ta d’aukesa ta shige d’akinta da shi daga baya ta dawo mata da shi shikenan Yaron ya fara shisshhid’ewa a take idanunsa suka k’akk’afe….sai da aka kai ruwa rana tukunna da kyar aka samu kansa a asibiti, ai kuwa tun daga nan ko kuka ya yi mai tsaho sai sun yi sama da sati a asibiti, sai da ya yi wayo tukunna aka fahimci ashe abun hauka ne, dan Idan ya motsa har duka yake yi kuma burinsa kawai ya kawar da duk wani da ke a kusa da shi, to idan ya lafa kuma sai ya zama kamar wani zombie kafin a hankali a hankali kuma ya warware.
Da aka haifi Ya Aminu nan ma sai da Kaka ta kusan zaucewa wanda hakan ya yi matuk’ar bawa Mallan mamaki da tsoro kuma ya sake tabbatarwa tabbas ba ta son Inna.
Tun daga nan ta tayar da ballin ‘sai Mallan ya k’ara aure’
A ganinta tunda ta kasa ita kad’ai idan aka yowa Innar kishiya kishiyar zata tayata su fitar da ita cikin sauk’i.
Asabe y’ar k’awar Kaka ce dan tunda Kaka ta dawo layin suke shiri a lokacin sune manyan layi, ita Kaka d’anta yana da gida mai d’akuna dayawa ita kuma mahaifiyar Asabe Mijinta yana da kud’i.
Daga baya baya dai Ita mahaifiyar Asabe ta d’an ja jiki lokacin da duniya ta fara yiwa Mallan zafi, dan shi bai yi karatun boko ba, kuma tunda Malaminsa (uban gidan sa) ya rasu komai sai ya jaa baya.
Sai dai kuma Kaka tana zuwa da zancen aure ta yi karaf ta amince dan a lokacin Asaben ta yi laifi Mahaifinta yana shirin aurawa wani Yaronsa ita kuma Yaron nasa a Sumaila yake matansa uku ita ce ta hud’u, gashi dama ta san Asaben tana son Mallan, fad’a ne kawai ba su yi ba a ganin uwar hakan zubar da girma ne.
Sai da Inna ta yi da gaske tukunna ta iya rik’e kanta da auren ya taho gadan-gadan. Shi Kansa Mallan d’in ba so yake yi ba babu yadda ya iya ne, haka nan Kaka ta yi ruwa ta yi tsaki sai da ta ga Asabe a d’akin Mallan tukunna hankalinta ya kwanta.
Lokacin auren Mallan da Inna shekaru 15 kenan.
Babu kalar gorin da Inna ba ta ji ba, har da cewa ‘A bawa Asabe d’akuna hud’u dan ita d’in tana da dangi da nasaba an san za’a yi mata kayan d’aki
Sai gashi Asabe ta zo daga ita sai wani gado low class a lokacin, da wata yololuwar katifa, ai kuwa nan itama Inna ta samu na yi ta tisa su gaba da nata gorin dan ko ita da take ba uwa ba uba ba dangi kayan da ta siyawa kanta a lokacin aurenta ya fi na Asabe.
Ganin wannan gorin bai ci ba sai Kaka ta fara maganar haihuwa dan a lokacin shekarar Inna goma sha biyar da auren Mallan amma y’ayanta biyu tana da cikin Dije. Kullum Kaka bata da abin fad’e sai ‘a matsa ga mai cika gidan nan ta zo’.
Sai gashi sai da aka yi shekaru hud’u lokacin har Dije an Haifa ta yi wayo sosai tukunna Asabe ta samu cikin Zainab da kyar kuma tun daga kan Zainab haihuwar ta tsaya mata ita ma Inna haka wanda zuwa wannan lokacin duk sun fahimci Mallan d’in ne bashi da rabon haihuwar da yawa.
Duniya ta yi zafi, babu tayi yawa, wannan dalilin ya sanya Mallan ya fara raba d’akunan gidansa a haya saboda su samu abin rik’e kansu, su dinga rufawa kansu asiri, dan shi Mallan bai iya sana’a ba sam bata karb’esa ba, Ya Muhammad kuma bashi da Isashshiyar lafiya, Minu ne kawai da ya taso yake sana’ar carpinter, sai ko kiwon kajin da ya fara, wanda kud’in duk a registration da handouts ya yi ta tafiya, dan yanzu haka ya kammala buk inda ya karanci geography service yake shirin farawa.
D’akuna goma sha uku ne a gidan, biyun farkon na Mallan ne da Kaka, sai na farko da yake cikin d’akunan hannun dama kuma na mazan gidan ne, duk wani Namiji tun daga kan Ya Kamal har zuwa kan Umar duk a d’akin suke. Na kusa da shi kuma d’akin Maman Fati ne, Maman Fati tana da Miji Yunusa cirani yake zuwa Lagos yana da wata a chan, ya kan yi wata bakwai bai zo ba, kuma idan ya zo bai fi ya yi kwana biyu ba ya koma.
Baban Fati irin masifaffun mazan nan ne shiyasa wani lokacin ita kanta Kaka take shakkarsa. Ita kuma Maman Fati munafurci da fuska biyun da ta kware a kai ne ya sanya take iya zama da shi, dan hatta matarsa ta chan chanjawa yake yi baya tab’a iya yin shekara d’aya da mace saboda halinsa na zuciya da saurin fushi da fad’a.
Y’ay’ansu biyu, Fatima (sa’ar Dije da Umar sa’an Zainab).
Sai d’akin su Dije, Dije shekarunta sha shidda, Ya Aminu ashirin da hud’u, sai Ya Muhammad talatin, Dije tana ss3 yanzu haka Ya Aminu ya gama University amma shi Ya Muhammad da kyar aka samu ya kammala diploma daga nan shi da kansa ya ce “ya hak’ura” dan karatun duk a daddafe ya yi gashi sai yayi ta zubewa ana kwaso shi.
Aure kuwa sau biyu ya yi sa shima daga nan ya ce “ya hak’ura”
Dan bayan wadda aka sani ya aura a nan unguwa uku, Mallan ya nema masa auren wata a Garko aka d’aura ya tare sai dai ko kwana ita kam bata yi ba ma aka fitar da ita a sume! Dan dama a tsorace yake tun da yaga an d’aura auren yake gudun abunda zai je ya dawo, kuma tsoro wahala da b’acin rai su suke triggering ciwon nasa.
Sai Maman Kubra, ita kuma tana da y’ay’a da yawa amma rasuwar Mijinta ya sanya aka karb’e su aka barta da k’ananun kawai y’an biyu Kubra da Usman (Usso), unfortunately Usman yana shaye-shaye sosai an kasa rabasa da shi haka nan ake ta fama, Kubra a k’alla yanzu shekarunta sha takwas amma rashin dai dai ita a cikin gidan ya sanya ta shiga group d’in su Rakiya. Doguwa ce sosai fara sol da ita dan asalin Mahaifinsu Igbo ne, yanzu haka duk y’an uwanta suna hannun Kakarsu wadda itama ta tsani uwarsu kamar mutuwarta saboda kasancewarta Bahaushiya ita kuma ta fi so a auri ta su. Wannan rashin jituwar da ke tsakanin Kakarsu da Uwarsu shi ya yi sanadiyyar yanke hatta zumuncin da ke tsanin su Kubra da y’an uwansu.
D’akunan da suke kallon k’ofar shigowa tsakar gidan kuma (guda hud’u) D’aya na Asabe ne, d’aya Empty ba kowa a ciki, sai na kusa da shi kuma d’akin wata copper ne (Grace) ita kam ba ma ta zama sosai
Kullum sai dare take dawowa ta kwana da safe k’arfe tara take
fita. Copper nan tana ganin ikon Allah a cikin gidan dan hatta band’aki idan ta shiga ta fito sai an yi masa wankan tsarki, gashi su yi ta munafurcinta da Hausa dan ita bata ji ammafa tana fahimta, dan suna farawa ta san me suke yi, gata shiru-shiru da ita babu ruwanta amma hakan bai hanasu nuna mata wariyar launin fata ba. Bayaga aikin da ya yi mata yawa da d’an chilling d’inta har da halin y’an gidansu Dije ya sanya ba ta yarda ta dawo gidan sai duk sun yi bacci.
Sai d’akin Ramma wanda yake a k’arshen wajen kusa da rijiya.
D’akuna uku da suke a jere da kitchen kuma na kusa da d’akin Ramma d’akin wata tshohuwa ne Iyya.
Iyya wata tshohuwa ce dan duk gidan babu mai shekarunta. D’anta d’aya kwal a duniya Ya Kamal. Business da ciku-ciku ne suka kawo sa garin Kano ganin yana shirin dad’ewa a garin ya sanya ya je ya d’auko
Mahaifiyarsa suka zo
nan. Maganar Allah idan ka d’auke Mallan to kaff gidan babu mai hankalin Ya Kamal a maza a mata kuma Iyya. Wasu irin mutane ne masu kamala da d’attako. Ya kamal a maza duk ya girmesu dan hatta Ya Muhammad ya bashi watanni biyu, yadda yake tsaye a kan duk wani al’amari na gidan da y’an gidan za ka d’auka uwa d’aya uba d’aya suke, har kwana ya tab’a yi a police station saboda Usso, sannan al’amari indai ya shafi Dije da y’an d’akinsu to ya kan tsaya tsayin daka har sai ya ga komai ya dedeta, wannan dalili ya sanya Dije take matuk’ar ganin girmansa, gashi kuma Aboki ga favorite d’inta Ya Muhammad.
Sai d’akin Gwaggo, Gwaggo itace mahaifiyar Mariya da Musa, a gidan daga Ya Kamal sai Ya Muhammad sai Musa a shekaru, shi kam Musa da aurensa ma matarsa tana da tsohon ciki dan ba a dad’e da yin aure ba, amma kasancewar duk a layi d’aya ne suma suke haya ya sanya kusan kullum yana gida. Sana’arsa keke Napep ce da shi (d’an sahu ne)
Sai Mariya ita kuma shekarunta sha bakwai ita ma tana ss3 ajinsu d’aya da Dije.
Sai d’akin kusa dashi..d’akin Maman Sagir, Sagir d’in sa’an Minu ne sai dai shi yana aiki a company na shinkafa so yana samu ba laifi dan haka uwar Kubra da uwarsa suke son aura masa Kubra wadda tun zuwansa gidan ta mato a kansa, shi baya wani sonta amma su kam sun nace haka nan yayi ta wulak’antata yana yi mata rashin mutunci amma ita ko a jikinta dan Yarinyar ba dai sauk’in kai ba, in dai ka ji ana case da ita tana hauka to akan Sagir ne. Dan kwarkwar ta ke komawa when it comes to him, ta kan je ta samu mutum har gida a yi ta rigima saboda Sagir, shiyasa su Mariya suke cewa ta haukace a kansa, duk yadda aka yi asiri ya yi mata.”
BULAMA ✍️
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 09.
Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.
Mallan bai samu ya dawo daga asibiti ba har dare sakamokon yanayin jikin na Ya Muhammad sam babu sauk’i….Inna ta je ita kad’ai babu yadda Dije bata yi ba akan a barta ta je ta gansa amma ko kallonta Inna bata yi ba haka nan aka tafi aka barta kuma da ta dawo ta tambayeta ya jikin nasa nan ma ba ta ko kalleta ba.
Inna ta so ta zauna amma sam ba zata iya jinyar tasa ba dan doke-doke yake yi sosai dole maza ne za su iya kuma asibitin basa yarda da masu jinya sama da mutum biyu.
Tun lokacin da Inna ta fita Kubra da Rakiya suka dasa kujera a tsakar gida suke ta yadawa Dije magana, da yake Kubran fiancé d’in Sagir ce ita zai aura shiyasa tunda ta ji ance yana kallon Dije wani malolon bak’in ciki da kishi suka taru suka yi mata k’abe-k’abe ta rasa inda zata saka ranta.
Rashin wayo ya sanya ta kasa danne kishinta, gashi Dijen kwata-kwata ta k’i kulasu hakan ya sanya take ga kamar ko tsoronta ta fara ji yanzun tunda dama ita duk ta girme musu, ko kuma dai ko meye za su yi mata ta san ba lalle ta kula su ba tunda ga abunbuwan da suke ta faruwa kuma duk itace sila..sun san ko dan halin da Ya Muhammad yake a ciki ba lalle ta kula su ba.
Tun safe suke abud’aya ba ta kulasu ba, da yamma bayan Inna ta dawo Dijen ta fita siyo kukar miya Kubra ta bita a baya ta lab’e ta nemo Yara wajen su biyar ta raba musu naira ashirin ashirin ta ce idan Dije ta fito su yi mata ihu su ce mata y’ar Iska.
Dukda Yaran suna d’an shakkar Dije amma hakanan suka amshe kud’in tana fitowa suka hau ihu suna kiranta da y’ar iska kafin su kwasa a guje su bar wajen gudun kar ta damk’e su.
Wani Yaro ta kama a cikin yaran d’an k’arami wanda Allah bai bawa ikon fecewa ba har ta kai ga damk’ar sa.
Sai da ta sauk’e masa maruka hud’u kyawawa tukunna ta tambayesa wa ya saka su dan daga ganin abun ta san sakasu aka yi.
Tiryan-tiryan Yaron ya gaya mata, tsabar mamaki bata ma
san lokacin da ta cikashi ya gudu ba.
Aikuwa ta na shan kwana ta ci karo da Kubra a tsaye, wadda tana ganinta sai ta d’an diririce sai kuma ta nutsu ta kama kanta.
Kallonta Dije ta tsaya tana yi kamar kuma wadda aka bawa izini tashi d’aya ta cikumo hijabinta ta nad’e mata fuska da shi ta shiga kimarta kamar an aikota, ganin Kubran tana shirin kwacewa gata Babba ya sanya Dije ta rarumi dutse ta buga mata a ka.
Ta dai ga ta tsugunna daga nan bata san ya ta kaya ba ta yi gaba abunta ta barta da fuska a rufe. Sosai su Kubra suke bata mamaki su da iyayensu idan suna wani abun ko da yake ba laifinsu bane ba duk laifin Kaka ne. Ta ji daga bakin Inna…Farko-farkon fara zuwan y’an haya gidan sosai suke yiwa Kaka da Inna fadanci har da su Ya Muhammad, a lokacin d’aki aka ware Inna take amfani da shi a matsayin nata kitchen d’in su kuma suke amfani da kitchen d’in gidan. Bak’in cikin fadanci da girman da ake bawa Inna ya sanya Kaka ta tashi kitchen d’inta ta saka ta ta koma cikin y’an haya sannan ta ce musu duk d’aya ake ko laifi su Ya Aminu suka yi musu suna da ikon kimarsu! Da Mallan ya yi magana ta hau shi da fad’a wai zai koyowa iyalinsa girman Kai. Dukda haka hankalin Kaka bai kwanta ba sai da ta dinga tsinka Inna a gaban jama’ar gidan ta tabbata sun rainata har ta kai sun fara fad’a da ita tukunna hankalinta ya d’an kwanta, kuma duk fad’a k’iri-k’iri za ta bawa Inna rashin gaskiya ta zazzageta a gaban kowa.
Zuwan Asabe gidan shi ya taimaka aka sake rainasu, dan yanzu haka mutum ba su fi biyu ne a cikin gidan ba da za’a ce ba sa bin Asabe bashi kuma ta k’i biya.
Sannan rashi da babu ma ya taimaka sosai wajen janyo musu raini dan kusan y’an hayan gidan nasu ma sun fi su rufin asiri wasu lokutan.
Suna girmama Kaka da Mallan amma Asabe kam da y’ay’an Mallan an rainasu, Inna kuma munafukai masu wayo da fuska biyu sune kawai suke bata girma (su Maman Fati)……
Tana wannan tunanin zuciyarta fal bak’in ciki ta k’arasa gida.
Tunda yamma ta yi Asabe ta ga Mallan bai dawo ba ta san cewa watak’il fa sai ya iya cewa a chan zai kwana bayan ya san yau d’in kwananta ne!
Ai kuwa sai gashi ya turo
mata message Akan ‘yana neman yardarta zai kwan a chan, Minu ba zai iya rik’e Ya Muhammad shi kad’ai ba, yanzu haka fama ake yi, gashi Ya Kamal ba ya kusa yau d’in ballanta ya yi tunanin zai ce za su kwan tare. Idan har ba ta amince ba to ta sanar masa da wuri ya san abinyi.’.
D’akin Kaka ta je ta kai mata k’orafi dan haka a take suka gama yanke hukunci.
Dare yana yi ta shirya tsaf da ikon Allah ta wuce zuwa asibiti.
Minu yana zaune Mallan yana yi masa fad’a akan abunda ya ji labari ance ya yi a gida d’azu Ya Muhammad kuma yana bacci kawai suka ga Asabe a kansu.
Da farko Mallan ya d’auka dubiya ta zo sai kuma ya ga yanayin lokaci da yanayin fuskarta dan haka ya san ba alkhairi ne ya kawota ba, gabansa ne ya yanke ya fad’i a lokaci guda kuma ransa ya b’aci a lokacin da kwakwalwarsa ta bashi watak’ila shirunta ba yana nufin ta amince bane ba, dan shi har ga Allah ya yi tunanin ta amince ne tunda ya ce idan bata yarda ta yi magana da wuri sannan ya san in da ace Asabe ba ta amince ba to da tuni ta kirasa ta ce ‘a’a’ ya riga ya san halin abarsa, to amma kuma gata yanzun ta zo masa dan haka sai kawai ya tsaya
ya ga ikon Allah.
Da kyar ta iya gaishesa ciki-ciki dan Kaka ta ce mata kar ta kuskura ta raga masa, ko gaisuwar Minu ba ta amsa masa ba ta ce “bamu guri.”
A hankali ya mik’e ya fice daga wajen shima yana mai mamakin al’amarin.
Kunya ce ta lullub’e Mallan tashi d’aya had’e da b’acin rai, gani yake yi kamar duk jama’ar d’akin sun san dalilin zuwan Asaben tunda dai ta yi k’ank’anta ace ita ce Mahaifiyar Ya Muhammad. Saboda Allah meye na biyosa har asibiti abunda ya kamata a…
Muryarta ce ta katse shi “gashi” ta fad’i haka tana mai mik’o masa wayarta.
Sunan Kaka ya gani b’aro-b’aro a kan screen d’in wayar ga timer yana tafiya alamun ita ce a kan wayar.
Ajiyar zuciya ya sauk’e ya saka hannu ya karb’a cikin sanyin murya ya ce “Assalam alaiki”
“Ameen” kawai ta ce daga haka ta d’aura da “Ga Asabe nan zata taya ka jinyar! Dan na ga take taken Halima da y’ayanta waenda ciwonsu ba ya tashi sai ranar kwanan Asabe tsaff idan aka biyesu sai
sun haramta mata keb’ewa da kai! Ka tafi asibiti baka sanar da ita zaka dawo ko bazaka dawo ba Yarinya tana ta jiranka salon ka ja mata magana da gori a cikin gida, shiyasa na ce mata ta shirya ta biyoka ku yi jinyar tare idan kwanakinta suka k’are sai ta dawo kuma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 23