all useless Nura ba su da amfani, ka kira min Malaman nan wai duk sun tafi had’o magani amma har yanzu basu dawo ba, kira mini su su dawo na san za su saka Abiddeen ya bud’e idanuwansa.”
Hannayenta duka biyu da take dukansa da su bama ta kallonsa idanunta a kan gawar Abiddeen, ya rik’e gam!
Sai da ta juyo ta kallesa tukunna ya ce “Mariya Abiddeen ya rasu! Dalilin da ya sanya kika ga Malaman nan ba su dawo ba shine ‘basu san me za su ce miki ba!’
Abiddeen ya rasu tun shekaran jiya ki daina wahalar da shi da gawarsa tun kafin ya fara tsutsa ki bari a kaishi makwancinsa “
Ya fad’i hakan cikin tsattsareta da kyawawan idanuwansa da suke nuni da gaskiyar abinda ya fad’a babu alamun wasa a tare da shi.
Sai da ta yunk’uro had’e da wani nishin da yake baiyyana tashin hankali da b’acin rai ta sauk’e masa wani kalar gigitaccen mari!
Sai kuma ta durk’ushe a wajen ta fashe da wani irin kuka kafin ta saka hannuwanta bibbiyu ta kamo k’afafuwansa ta na kuka take cewa “kar ka sake cewa haka Nura”
Kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta mik’e a zabure ta ce “ku kira min oga kwata-kwata, zan bashi duk kalar adadin jinin da yake so ya tafi lahira ya je ya dawo mini da Abiddeen.” (Wa’iyazubillah)
Runtse idanuwansa Nuraddeen ya yi kafin chan ya bud’e ya girgiza mata kai kawai.
Kuka ta saki ta durk’usa ta kama k’afafuwansa ta na cewa “ka kira min shi, ka bani assurance d’in Abiddeen zai tashi hakan zai sanya in ji sauk’i, ka kira min Oga na ce maka na san zai iya dawo min da Abiddeen.”
Sai kuma ta ware murya ta kwala kiran “Ogaa!!!”
Tana wani irin kuka kamar ranta zai fita.
Da sauri ya d’agota ya saka hannu ya toshe mata Baki, dan a yadda take kiran sunan Oga kwata-kwata tabbas ya san an ji ta.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 29.
Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.
Ba’a rufe mintuna biyar ba Giwar Mata ta shigo tare da Mai Babban D’aki da Gimbiya Salaha.
Da k’arfi Nuraddeen ya runtse idanuwansa dan ya san kwanan zancen.
Salati Giwar Mata ta saki yayinda ta danna kujerar da take a kai zuuuu! Ta jaa ta kaita har gaban gawar Mai Martaba.
Runtse idanuwanta ta yi yayinda su Gimbiya Salaha suka sake toshe hancinansu dan suna shigowa suka saka hannu suka rurrufe hancinnan nasu sakamakon warin da yake tashi a cikin d’akin ba na wasa ba.
A fusace ta k’arasa ta zame hannun Gimbiya Salaha kamar zata cinyeta d’anya ta ce “Ashe baki da hankali??? Sarkin kike toshewa hanci! Idan na k’ara ganin hakan daga gareki wallahi sai kin karb’i hukunci mai tsanani.”
Amai ne ya yunk’urowa Gimbiya Salahar dan haka ta yi saurin sake mayar da hannunta wajajen hanci da bakinta.
A fusace Gimbiya Mariya ta kama hannun suka shiga kiciniya tana cewa “sai ta hukuntata a bisa toshe hancin da ta yi a Mai Martaba”
Gaba d’aya ta haukace ta haukata wajen.
Juyo da ita Gimbiya Mai Babban D’aki ta yi, ba ta yi wata-wata ba ta d’auketa da wani irin zazzafan mari wanda ya yi sanadiyyar d’aukewar wutar kowa musamman ma Gimbiya Mariya wadda ta shiga mad’aukakin mamaki.
Nunata ta yi da d’an yatsa sannan ta ce “Point of correction ‘gawar Sarki’ ba ‘Sarki’ ba!
Sannan ki nutsu kafin ki k’arawa kanki wani laifin dan a yanzu ba sai gobe ba za ki fara amsar hukuncin ki na kisan Gilla da kika yi a Gimbiya Sakina.”
Cikin mad’aukakin b’acin rai Gimbiya Mariya ta ce “kina hauka ne? Akan na hukunta wadda ta aikata laifin yunk’urin kashe Mai Martaba Sarki….”
Marin da Gimbiya Mai Babban D’aki ta sake sauk’e mata ne ya katse mata hanzari.
Wannan karon kamar mai shirin tsole mata ido haka ta nuna ta da yatsa sanann ta ce “Again!! Marigayi Sarkin k’asar KHAK’IL na goma sha bakwai!!”
Ta yi maganar cikin tsatstsareta da dara-daran idanuwanta.
Sai a lokacin Gimbiya Mariya ta d’an fara snapping out tana dawowa cikin hankalinta wanda sakamakon hakan wani kalar rikitaccen tsoro ya lullub’eta.
“Sarkin k’ofa”
Muryar Gimbiya Mai Babban D’aki ta yi sauk’ar aradu har a cikin k’irjinta.
Sai da ya nemi izini aka bashi damar shigowa tukunna ya shigo kayinsa a k’as.
Jikinta ne ya hau karkarwa yayinda ta juya tana kallon Nuraddeen wanda shima itan yake kallo sai dai tabbas kallon da ta ga yana yi mata ya yi matuk’ar firgitata.
A rikice ta k’arasa ta shak’o wuyansa ta ce ‘kana nufin ba za ka yi komai ba? Kana nufin ba zaka tsaya min ba? Anya kuwa Nuraddeen babu hannunka ma a kisan Mai Martaba? Tunda yanzu it’s obvious babu wani shamaki tsakanin ka da sarautar k’asar Khak’il, na yarda da kai na aminta da kai ashe cin dunduniyata kake yi?”
Sai kuma ta fara kai masa duka da dukkan k’arfinta dan shirun da ya yi mata ya sake rikitata.
Sarkin k’ofa wanda tunda ya shigo ya fahimci abunda ya faru a d’akin ya durk’usa ya rushe da kuka ta (Mai Babban D’aki) kallla ta ce “ya je ya taho mata da Sarkin Yari tare da sojojin (mata) da suke tsaran yarin sarakuna.”
Mik’ewa ta yi ta je ta kai mata shak’a!!! Cikin fushi take cewa “yanzu na gane! Tabbas ke ce kika kashe mini shi saboda kwad’ayin d’aukar fansa. Wallahi ba ki isa ba, uwa ce ni ga Sarki sannan matar Sarki dan haka na fi k’arfin zaman Yari.”
Dai-dai nan Gimbiya Giwar Mata wadda ta gama waya da su Wambai ta ce ‘su zo’ ta k’araso wajen a kujerarta ta ce mata “muma matayene ga Sarki ai amma bayan ya gushe me kika yi mana?”
Shiruu ta yi tana kallonta fuskarta na baiyyana gigita da b’acin rai.
Cikin rashin jin dad’i ta ci gaba da cewa “Hatta layukan da aka jajja a masarautar nan sai da kika shallake kika take Mariya, wanda hukuncin yin hakan laifi ne babba.
Sannan maganar kisan Gimbiya Sakina kamar yadda kika bi diddigi muma zamu yi namu binciken a kai amma kafin gaskiya ta fito zaki jira a gidan Yari. Tare da jiran hukuncinki na yadda kika take shimfid’add’un dokokin magabata.”
Zuwa yanzu Gimbiya Mariya ta gama fahimtar tabbas so kawai suke yi su mik’ata inda za ta k’arashe rayuwarta a chan. Saboda wata shari’ar idan aka fara yinta sai a yi shekara goma ana yi, gashi ita an ce laifukanta ba d’aya ba ba biyu ba…sannan ita kanta ta san laifukanta banda na kisan Gimbiya Sakina sun fi goma……
Tana wannan lissafin Sarkin Yari tare da Galadiman Dogarai da Sojoji mata su bakwai suka shigo.
Zubewa suka yi a k’asa a take suka fashe da kuka na ganin gawar Sarkin yayinda koke-koke ya fara tashi sama-sama a cikin masarautar.
Sai bayan kusan minti d’aya tukunna Gimbiya Giwar mata wadda itama ta gama share nata hawayen ta kalli Sarkin Yari ta ce “fad’owa Mariya laifukanta……”
Mik’ewa ya yi har yanzu hawaye a idanuwansa wani na korar wani ya d’ago wani zabgegen alllon k’arfe da ya shigo da shi ya fara karanto rubutun da aka yi a kai da alk’alamin k’arfe mai ci da wuta aka watsawa bak’ar tawada!.
A tunanin Gimbiya Mariya laifukanta ba da yawa bane ba sai da aka fara karantowa tukunna ta dinga jinsu tare da hukuncinsu wanda rashin gatan da take da shi ne ya sanya za su samu damar yi mata hakan dan ko da ace d’anta ya bar duniya a matsayinta dai bai kamata a hukuntata a kan abunda ya riga ya faru ya wuce ba.
A yadda ake karanto mata laifukanta da tsawon lokacin da ya kamata ta d’auka a hasashe ba tare da an je ma gaban alk’aliba (sabon Sarkin da zai hau a gaba) tabbas sai ta haura sama da shekaru talatin a gidan Yari banda na kisan Gimbiya Sakina…
Ba ta da wata mafita dan haka a take ta durk’ushe a gaban Giwar Mata ta kamo k’afafuwanta ta fashe da kuka ta shiga magiya tana ce da ita ‘ta rufa mata asiri ita uwa ce mai jin k’an mata ta ji k’anta dan Allah’
Ko kallonta Giwar mata ba ta yi ba ta wuce a kan kujerarta bayan ta bayar da tabbacin ‘a wuce da ita ko burial d’in d’an nata kar a bata ikon gani’.
Ganin ba ta ci riba a nan ba ya sanya ta nufi Mai Babban D’aki itama tana ta yi mata magiya har da cewa ta ji k’an maraicinta amma itama ko kallonta bata yi ba sai snapping fingers d’inta kawai da ta yi a take Sojojin nan suka yo kanta, mutanen da ganinsu ma kad’ai abun firgitarwa ne.
Kuka take yi sosai tana kallon Nuraddeen ganin bashi da niyyar taimakonta ya sanya ta fara zaginsu tana cewa sune suka kashe mata d’anta duk su ukun su jira ranar d’aukar fansa wallahi ko ta mutu sai ruhinta ya dawo d’aukar fansar jinin d’anta……………
Suna fita da ita Mai Babban D’aki ta saka hannu ta d’auke kwallar da ta biyo ta cikin idanuwanta, zuciyarta tana wani irin tafarfasa…A ko da yaushe idan ta rufe idanuwanta babu abunda take gani sai gawar Gimbiya Sakina kai a rabe da gangar jiki.
Bazata gushe ba sai ta gana mata azabar da har ta mutu ba zata tab’a mancewa da ita ba kuma ina sha Allahu sai ta rok’eta Allah da Annabi akan ‘ta kasheta’ dan sai ta zabi mutuwa sau dubu sama da rayuwar da ta shirya mata indai ta cika Mai Babban D’aki! Garkuwa kuma y’ar Sarki jikar Sarki matar Sarki……..
***************
Asibitin Mallan Aminu Kano aka wuce da Mallan wanda duk kwakwar mutum baka isa ka iya ganesa ba tsabar yadda ya k’one a koina ya yi bak’ik’irin yana k’auri jikin yana fitar da wani irin wari.
Direct I.C.U aka wuce da shi aka jojjona masa na’urorin taimako Likitocin suka yi k’arshen bakin k’ok’arin su suka fito suka ce musu su yi addua kawai, dan tabbas Allah ne mai yi amma Mallan kam babu alamun zai tashi, a hakan ma da yake ciki gara masa mutuwar kawai saboda azabar da yake kwasa it’s unbearable.
Idan ka ga Dije dole sai ka tausaya mata kamar wata zararriya gashi ta k’i yin magana a kowa sam! Har gara Inna tana amsa addu’a ita kam sai kuka da zaman shiru.
Musamman ma da Kaka ta zo ta sake zuzuta abun ta d’aura laifin komai a kanta gaba d’aya sai ta amshi hakan ta aminta da hakan wani sabon feeling na masifaffen tashin hankali k’unci bala’i damuwa da rashin nutsuwa ya yi mata rubdugu.
Ita kanta Inna kusan hakan ne a nata b’angaren shiyasa duk suka taru suka fita a haiyyacinsu. A kaff fad’in Unguwa Uku Sumayya ce kad’ai ta zauna tare da su tana dannarsu. An d’an zazzo dubiya (dukda ba samun ganinsa ake yi ba) yayinda waensu jahilan suka ce ‘Allah shi k’ara’ wai ai alhakin Mallan Manniru Ya Kamal da Yusufa ne ya hau kansa.
Amma ita kam Sumayya tana nan tare da su, ta inda Allah ya taimaketa shine Kakarta ta zo Mahaifiyar Mahaifiyarta shiyasa ko da Mahaifiyar tata ta so yi mata bore Kakar ta tsawatar mata ta ce “wannan rashin imani har Ina? Ta bar musu Sumayyar su d’an ji sanyi, sannan idan ta sake ji ta ce Dije ce silar mutuwar Manniru wallahi sai ta had’u da fushinta tunda dai ita ta ce bata san k’addara ba.”
Kamar kuwa zata mutu da bank’in ciki haka nan ta hau ta kumbura ta yi suntum!.
…BAYAN KWANAKI BIYU…
Da babu gara ba dad’i, hakan za a iya cewa game da al’amarin Mallan, dan zuwa yanzu kam ya ma daina responding to treatment. Hankulan kowa a tashe yake musamman Dije wadda ita ke ganin halin da yake a ciki dan itace zaune tare da shi dan haka tana samu su barta ta shiga ta lek’a shi ta taga duk dare, dukda har yanzun itama bata da wani aikin sama da koke-koke amma ita ce a wajen nasa. Inna da Ya Muhammad suma kullum sai chaaan dare tukunna suke tafiya..dukda kuwa yanayin jikin na Ya Muhammad da yake nan kamar Yaro d’an shekara uku hakan bai hanasu zuwa da sassafe su tafi chaan dare.
Sumayya k’awar arzik’i dukda Dijen ba kulata take yi ba dan zuwa yanzu ta zama kamar wata kurma amma Sumayya tana tare da ita kusan ko yaushe dan wanka da zuwa makaranta ne kawai
yake rabota da asibitin.
Duk da halin da take a ciki sai da al’amarin Kaka da Asabe ya d’aure mata kai waenda ta ga kamar basu damu da halinda Mallan d’in yake a ciki ba, dan ita Dije ma a tunaninta Kaka zata koreta daga jinyar ita ta karb’a ko ta ce Asabe ta yi amma sai gashi da ikon Allah gaba d’aya sun zame hannuwansu game da komai da ya shafi jinyar tasa da shi a karan kansa, dan tun ranar da aka kawosa tare da su da suka tafi har yau babu kyallinsu.
Kawu Isa shima tunda ya kammala biyan kud’in komai ya gudu yau kwana har biyu bai sake lek’ensu ba, kuma babu waya.
Zainab ce kawai a washegarin ranar ta zo tare da su Ramma itama tun daga nan ba ta sake zuwa ba jiya ba ta zo ba yau ma gashi har dare ya yi bata zo ba.
Ita kam Dije duk kalar sanyin damunar da ake zubawa tana nan safe rana dare Hatta wanka a cikin asibiti ta ke yi, har sai da waensu a cikin Likitocin suka bata shawarar ta tafi gida kawai ta kwana dan in banda sauraye babu abunda take kwasa gashi zamani na sauro da malaria. Amma furr Yarinyar ta k’i yarda ta nad’e a cikin hijabinta ta sake kwana a wajen……….Zama a nan d’in ya fiye mata kwanciyar hankali da salama dan ko sunan unguwa uku bata son ji, besides ko bayaga hakan ma ba zata tab’a iya tafiya ta bar Mahaifinta shi kad’ai ba, a ko wanne yanayi da hali ta tsinceshi Mahaifinta Mahaifinta ne kuma zata so shi ta yi masa yadda ya chanchanta.
Inna ma saboda yanayin jikin Ya Muhammad ne ta san take tafiya amma da tare za su na kwana……
Zaune Asabe take ta rafka uban tagumi hankalinta idan ya yi dubu to ya tashi!
Babu abunda yake sake d’aga mata hankali kamar idan ta tuna yadda Inna take da zaratan maza har y’ay’a biyu yayinda ita kuma take da y’a mace guda d’aya tol
a duniya…..
Numfashi Kaka ta jaa ta fesar cikin mad’aukakin b’acin rai ta ce “Asabe ai dama na dad’e Ina gaya miki, yanzu ga irinta nan.
A yanayin jikin Mallan ba na jin zai kai jibi kin ga kuwa Halima ita ce da gida ta gaje kowa da komai sai abinda Hali
ya yi, ba abunda idan na tuna yake sake d’aga mini hankali sai ‘tsintacciya da y’ay’an tsintacciya wai sune za su gaje dukiyar d’a na, dan kasonsu sai ya fi nawa, kinga kuwa ba ta ga ta tafiya ba. Sannan Halima babu Mallan a tsakanina da ita na san bazata yi mana kyau ba, k’arshenta sai dai in koma rayuwa a k’ark’ashin ikon su ko
kuma in hak’ura in koma k’auye!’
Kai inaaa ba zai yiu ba!!!!”
Ta fad’i hakan tana rushewa da wani irin kuka.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 30.
Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.
Da sauri Asabe ta taso ta zo ta rufe mata baki, ta na yi tana kallon k’ofa dan ta ga kamar Ramma tana yi
musu lab’e.
Idan akwai halittar da Asabe ta tsana a duniyar Allahn nan to bata wuce Ramma ba, kamar k’unarta ta san tunanin wa take yi a take ta hau zugi, hannun nata ta kalla ta ga yadda yake sake tab’arb’arewa dan ko wajen wanzamin da suka je last ce mata ya yi ‘idan ba ta yi da gaske ba to abun sai ya zamo mata jeji’
Yanzu haka ko kwakkwaran motsi ba ta iya yi da hannun dan tana yi a take zai hau zugi, wai fa yanzun ma rik’e kafad’un Kaka da ta yi da hannun ta toshe mata Baki da d’ayan hannun ne ya janyo zugin ya taso.
Cike da tsana ta kalleta tana wucewa alamun dai lab’en ta yi musu da gaske dan sai yanzu ta ga ta nufi d’akinta itama da nata hannun nad’e da bandeji amma wai duk da haka shanyar kayan wankin Rakiya ta fito yi da hannunta mai lafiya….
A ranta ta ce “shegiya tsinanniya a haka za ki k’are! Shi yasa ai k’anin uban y’ay’an naki ya handame muku dukiya kuma in sha Allah ta tafi kenan har abad…..”
A take tunanin ta ya katse ta yi shiruuuuu kamar wata mai lissafi..
“Um, umummmmumm”
D’in da Kaka take cewa tare da mutsu-mutsu d’inta ne ya katse mata lissafi.
Cikata ta yi da d’an sauri ta d’an kalla fuskarta kafin ta d’an saki wani lallausan murmushi.
Sakin Baki Kaka ta yi sannan ta ce “eh lalle Asabe kan ki babu lafiya. Bayan kin yi yunk’urin toshe min numfashi yanzu kuma a cikin wannan bala’in da muke ciki har kika samu sararin farincikin yi mini murmushi???”
Wani murmushin Asabe ta sake saki wanda hakan ya dad’a daskarar da Kaka a wajen.
Waje ta nema ta zauna a nan kan gadon gefen Kaka ta ce “Kaka, bani dukkannin hankalinki ki ji abunda na tsaro mana………….”
Dai-dai Ramma ta zo shiga d’akinta ta hangi Gwaggo da Mama a zaune a cikin d’akin Gwaggwon ta window!
Sosai ta ji gabanta ya yanke ya fad’i dan wannan keb’ewar tasu in ba da kyar ba Gwaggo tsara Mama take yi akan batun tafiya Ingila..
Ai kuwa ilai! Dan tana zuwa ta ji Maman tana ce mata “Ai ki kwantar da hankalinki, itama Rammar zan yi mata bayani ai ko Yaran sun kai su ashirin tsaff za a sama musu waje!
Yo Allah na tuba ai yin hakan a gareni nima kamar YI WA KAI ne, akwai fa wata Yarinya da na yi mata sanadi ta je chan d’in wallahi in gaya miki har zobe ta siya ta aiko
min na gold! Ke dai kawai ki kwantar da hankalinki sannan ku rik’e amana kar Yarinya ta je ta kud’ance ta dawo ku ce ba ku san wata Mama ba”
Washe baki Gwaggo ta yi ta ce “Ayya, ai ni na iya rik’e alk’awari da amana ba na tab’a manta halaccci.
Ita Ramma tana da muguwar zuciya shiyasa ma kika ga tana neman hanawa a kai Mariya.
Ta fi so kawai ita kad’ai ta zama a sama, shiyasa Kaka ta ke yawan cewa ‘inda Ramma wata ce to da babu wanda zai ci arzik’inta’.
Kanta kawai ta sani.”
Ta yi maganar cikin salon hannunka mai sanda a Maman.
Banko labulen d’akin Ramma ta yi ta shigo ta ce “sannu annamimiya! Muguwa! Shed’aniya.”
Mik’ewa tsaya Gwaggo ta yi dan ko ba komai ta san yau d’in idan suka kara sai ta kada Ramma duba da larurar da take tare da ita.
Cikin b’acin rai Gwaggo ta ce “Ramma ki iya bakinki! Ki san kalar maganar da zaki gaya min in ba haka
ba wallahi zan baki mamaki.”
Da mamaki Ramma take kallon matar dan bata saba tanka mata ba…..
Tana wannan tunanin muryar Gwaggwo ta katseta.
“Ai idan akwai annamimiya to ke ce! Allah na tuba a tashi tare amma tsabar bak’in Hali alkhairi ya zo sai ki nemi dak’ile shi ki tura iyaka naki
ke kad’ai? Wallahi in da ace ni ce da tun kafin ki ji zancen zan kawo miki tayinsa. Amma da yake ke d’in mugawa ce lamba d’aya….”
Kanta Ramma ta yo
a haukace wanda duk courage d’in matar sai da ta tsorata ta sha jinin jikinta.
Sam! Ita Ramma ta ma manta da wani ciwonta dan in da ace ta sameta Mama bata kai ga shiga tsakiyarsu ba wallah da babu abunda zai hana ta yi mata rubdugu, dan ba kad’an ba rainin wayon nata ya k’ular da ita matuk’a.
Sosai abun nasu yake shirin fin k’arfin Mama dan sai k’ok’arin tadda juna suke yi suna zage-zage anata bubbugeta a tsakiya.
Dai-dai nan Kaka da Ya Musa suka shigo.
Da sauri Ya Musa ya k’arasa ga Mahaifiyarsa ya rik’e ta Kaka kuma ta tsaya tana tafa hannuwa da salati kafin ta ce “Ramma meye haka yake faruwa ana tsaka da alhini? Ashe ku har yanzu ba ku san Annabi ya faku ba?”
Kamar Ramma zata yi magana sai kuma kawai fuuuu ta juya ta fita tsanar Gwaggo tana sake ratsa ta.
“Allah ya kyauta” kawai Kaka ta ce daga haka ta juya ta fita Maama ma haka, sai a lokacin tukunna Ya Musa ya ji ba’asin fad’an.. Da mamaki yake kallon Mahaifiyar tasa tana dire aya da “kuma wallahi ko zata suma sai Mariya ta je! Shegiya y’ar bak’in ciki.”
Cikin rashin jin dad’i ya ce “yanzu Gwaggo matar da kuka santa jiya-jiya ita ce za ku d’auki
amanar Yara y’an mata ku bata? Baya ga haka
ma Gwaggo me Mariya ta nema ta rasa a rayuwarta ta rufin asiri da Allah ya tsara mana?”
Cikin fushi ta kallesa kafin ta ce “Kama hanya ka
wuce!”
Zai yi magana ta sake cewa “fice min daga d’aki na ce maka!! Duk ranar da asirin k’in son ganin ci gabanmu ni da Mariya ya fita daga kanka sai ka dawo mu yi magana…..”
Zuciya a cunkushe ya juya ya fita, yayinda ta bi bayansa da harara har ya fice, ta shiga cewa “Na san wannan aikin Zainab ne, shegiya wadda ba ta son ganin ci gaban kowa dan kar a fi k’arfinta ta gagara juyamu. Kana fama da adaidaita sahu ita tana aikin nurse amma a haka kai
kana ganin dacewa ne.
Dole muma mu tashi mu nemi na kanmu mu fi k’arfin kunce da wulak’anci da k’ask’anci, bari ka ga ta je ta dawo na san hatta kai sai ta bawa jari….”
Haka nan Gwaggwo ta k’araci mitar ta ita kad’ai ta nemi waje ta zauna ta shiga lissafin yadda rayuwa zata sauya musu idan Mariya ta tafi Ingila ko Saudiyya……
Kafin awa guda labarin Ingila da Saudiyya ya karad’e gaba d’aya layin ma ba iyaka gidan ba.
Jita-jita ya sanya aka fara munafurce-munafurce wanda hakan ya sanya Mama ta sha jinin jikinta.
Dan haka bayan wasu y’an awanni ta nemi ganawa da su, ta ce musu “tunda gashi har an fara yi mata zargin wani abun, su kawo guda d’aya a kaita ta je ta yi wata d’aya ta dawo in yaso idan aka tabbatar da aikatau ta je shikenan, saboda ba zata yarda ta had’a kan y’ay’a lokaci guda ta tafi da su ba hankalin iyayensu bai gama kwanciya ba.”
Dan a maganar da ake yi yanzu haka a y’an tafiyar har da Fati wadda Babanta ko sati bai yi da komawa ba, shiyasa uwar take da tabbacin zata iya zuwa ta je ta dawo bai sani ba tunda yana d’aukar lokaci kafin ya zo. Sai kuma Sumayya wadda itama Mahaifiyarta tana jin labarin ta ce ‘ga tata y’ar!
In dai su Ramma sun gasgata gaskiyar matar to a had’a har da ita su tafi Ubangiji ya yi jagora.’ Su kuwa su Ramma dama chan sun gama yarda da ita, sannan a gabansu take yawan yin waya da (lambar saudi) da wata mata wadda take ik’irarin itace y’aruwartata da ta ce har yanzu tana chan dan haka suka sake yarda da ita, ga kuma
suggestion d’in da ta kawo a kan ‘a kai wata ta yi wata d’aya ta dawo a tabbatar’ ba kad’an ba shima ya sake saka musu yardarta.
A b’angaren Mama kuwa komai ya zo mata da sauk’i ne, dan tana fara jin jita-jita ta kira waenda suka aikota a take suka shirya komai kuma aka yi sa’a sara ta zo musu a dai-dai kan gab’a, aka samu inda zata kaita ta je da dawo wajenda ta san basu Isa su yi doubting ko questioning d’insu ba….
Tsabar ta raina musu wayo a rana d’aya tak ta karb’i hotunan Yaran duka su biyar d’in ta dawo musu da wani Abu wai ‘shedar tafiya ta gama komai hatta visa duk waenda suka d’auke su aikin sun yi musu komai sun biya kud’in jirgi da komai sun gama amma sai nan da wata d’add’aya tukunna za su tafi, for now Rakiya ce zata fara zuwa Saudiyya ta je ta gano ta dawo idan suka ganta suka ga babu matsala hankalinsu ya sake kwanciya da abun sai a tafi.
Amma dan Allah su rik’e
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 23