Share this page
tsarar Dijen ce a wajen ta ce “Anya kuwa A’bu wannan ba k’arya kike yi ba?”. Nan kuwa ta hau rantse rantse matan gidan suna tayata da cewa “Ai A’bu ba ta k’arya, tunda ta fad’a to an yi hakan…” Babu wanda ya ga tahowar Dije sai ingije jama’ar wajen da ta ke ta faman yi wajen k’ok’arin ganin ta isa ga A’bu ne ya fargar da wasu. Kafin su ankare kuwa har ta isa ta finciko wuyan rigar A’bu! Bata yi wata wata ba ta d’auketa da Mari ji kake tasss!!! Dama a zuciye take ranta a b’ace yake. Cike da masifa uwar A’bu wadda take wajen ta fara zaginta tana kai mata duka sai dai cunkoson mutanen wajen bai sanya dukan ya shafeta ba. Cikin lokaci k’alilan waje ya hautsine dan Dije ta damk’i wuyan A’bu kamar mai shirin aikata lahira tana danna mata ashar ta uwa ta uba tana kiranta da mak’aryaciya tsinanniya…… Wata uwar tsawa aka daka “Dije!!!” Wanda hakan ya sanya kowa ya sha jinin jikinsa yayinda wasu kuma suka hau k’unk’uni musamman mahaifiyar A’bu. Da mugun k’arfi Dije ta runtse idanunta dan bata so Allah ya kawo mai raba ta da A’bu ba a yau d’’in nan! Yarinyar ta sha k’ulla mata munafurci kala kala dama tun ba yau ba. Ita babban abunda ya fi k’ular da ita ma shine shafa mata k’ugun da aka ce wai Ma’a ya yi! Mutumin da ta tsana kamar mutuwarta…. “Za ki cikata ko sai na k’araso???” Shiruu haka wajen ya d’auka baka jin k’arar komai sai na sheshshek’ar kukan A’bu wadda hatta bakinta ya fashe. Tana haki tana huci zuciyarta a wuya ta cika ta ta d’an ja baya ta sunkuyar ta kanta k’asa tana k’ok’arin hana kanta kuka dan kwata kwata dukan da ta yiwa Abu bai gamsar da ita ba. “Wuce ki tafi d’aki” Ya ce da ita idanunsa a kanta. “Allah gafarta Mallan gaskiya yau dai sai an bi mana hakkin mu” Mahaifiyar Zainab ta fad’a tana kallon gefe tana harare harare. Ba tare da ya kula ta ko ya kalli inda take ba ya juya ya bar wajen ya nufi k’ofar d’akinsa dake a soro. Ido ta had’a da Ya Muhammad tsaye a gefen Ya Kamal wanda ya rakota gidan duk sai ta ji babu dad’i. Mallan yana wucewa Ya Muhammad shima ya juya ya bi bayansa yayinda Ya Kamal ya k’araso wajen ya ce “Inna bata da lafiya haka Minu shima kuma duk a ta sanadiyyar ki ne amma kalli abunda kika sake aikatawa.” A harzuk’e Mahaifiyar Zainab ta ce “yo ai gada ta yi! Ka ga laifinta? Ai ta san tana da d’aurin gindi ta ko wanne b’angare ne shiyasa take abunda ta ga dama, to dai gashi maza sun fara latsata kuma gashi ba a son laifinta dan haka ban san yaya zata kaya ba! Mu dai Allah kiyaye mu da ganin abun kunya.” Cikin fushi Dije ta ce “uwark.” Da sauri Ya Kamal ya ce “Au Allah??? Da k’arfi cikin katseta sannan ya ce “wuce ki tafi kafin in yi ball da ke a wajen nan wallahi.” Ba dan ta so ba ta juya ta wuce cikin d’akinsu inda Inna take jinya amma wallahi ta ci alwashi sai ta mayar wa da Asabe martani tunda ita dai bata san ya kamata ba…. Haka nan ta shige d’akin tana jinsu ita da y’an koron ta suna ta yayata maganar suna sake assasa abun. Turuss!! Haka ta ja ta tsaya sakamokon ido biyu da ta yi da Inna a zaune Anty Sakina tana yi mata allurar jijiya. Da sassarfa ta Isa gareta tana duddubawa kafin ta d’ago idanunta da har sun d’an sake kad’awa ta ce “Inna jikin dai? Sannu.” Jinjina mata kai kawai Inna ta yi tana mai sauraren zage zage da d’ibar albarkar da Asabe take zubawa har yanzu, gashi sai aibanta Dije take yi ana ta mayar da magana ana cewa “Ma’a ya rungumeta ya shashshafeta yau d’in” ita kuma tana sake rurawa abun wuta tana sake d’abbaka zancen. Ya Muhammad ne ya shigo cikin d’akin hannunsa d’auke da wani kwano wanda Mallan ya gama tofi a cikinsa yanzun ya ce ya kawowa Inna ta sha. A gabanta ya durk’usa sannan ya mik’a mata ya ce “gashi in ji Mallan.” Jinjina kai ta yi ta ce “ya ake ciki da al’amarin Aminun?” Wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce “ban je ba tukunna, ki kwantar da hankalin ki zai samu lafiya in sha Allah.” Jinjina kai kawai ta yi dai dai nan Sakina ta gama juye mata ruwan allurar a cikin jijiyar ta ta zare sannan ta fara k’ok’arin tattare kayanta, sai da ta had’a komai tsaff tukunna ta sake yiwa Inna jaje tare da addu’ar neman sauk’i daga nan ta mik’e ta fita. Tunda ya Muhammad ya shigo cikin d’akin Dije take ta faman sunne kai kamar wata ta kirki. Sakina tana fita ya zuba mata manyan idanuwansa farare k’all kawai yana kallonta ba tare da ya ce mata komai ba. Kusan minti d’aya suka kwashe a haka ganin bashi da niyyar yin magana ya sanya ta magantu da kanta, ta ce “dan Allah ka yi hak’uri, Inna ku yi hak’uri ba zan sake ba” “Ba zaki sake me ba?” Ya jefo mata tambayar idanunsa a kanta. Inda inda ta fara yi kafin ta ce “duka biyun.” Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya ce “jiya jiya aka gama case d’inki da Kaka, damuwa ta haifarwa da Inna ciwo amma kalli yau ma issue har biyu Dije duk a kanki ke kad’ai? Idan an yi magana ki ce kina son mu kina tausayinmu, an ya kuwa Dije??” Hawaye ne suka shiga sintiri akan fuskarta da kyar cikin jan hanci ta ce “sune fa suke tsokanata” K’uraa mata ido ya yi na y’an mintuna kafin chaan ya ce “ko da wasa kar in sake ganinki a nesa da Ma’a ma ballantana kusa da shi!” A hankali ta ce “Yaya shine fa ya tare min…” “Shiiii” ya ce da ita yana mai d’aura hannunsa a kan lips d’insa kafin ya ce “abunda na fad’a kenan” Daga haka ya fara k’ok’arin mik’ewa yana mai cewa “Inna bari in je wajen Minu.” Duk sai a lokacin suka lura da yadda sam hankalinta baya a kansu kwata kwata. Lumshe idanuwa ya Muhammad ya yi ya bud’e kafin ya ce “Inna dan Allah ki rabu da su kar maganar su ya dame ki” “Ai dama kina ganin yadda take kumbura kwana biyun nan kin san akwai dalili! Shegiyar Yarinya ashe latseta ake yi bamu sani ba! Ta fito tana ta juya mana mazaunai ita nan ga mai diri nan kuwa ba na Allah da Annabi bane ba…..” Muryar Asabe ta ratsa kunnuwansu. Zurufff! Inna ta yi ta mik’e tsaye, da sauri ya Muhammad ya runtse idanuwansa, kafin ka ce kwabo har ta fice waje….. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 02. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Inna tana fitowa wasu suka yi shiru yayinda Asabe ta ci gaba da magana kanta tsaye tana aibanta Dije. Cikin mad’aukakin b’acin rai Inna ta ce “sannu tambad’ad’d’iya wadda ba ta san ya kamata ba! Yanzu ke abinda kike yi tarbiyyar kenan? Kin tara Yara da muna manyan cikin gida sai zancen batsa kuke yi a gaban Yara k’ananu, haka ake tarbiyyar a garin ubanki?”. Da sauri Asabe ta ce “a kul d’inki Halimatu! Wallahi a k’ul d’in ki!! Kar ki kuskura ki sake ambato mini iyaye da k’azamin bakinki, sannan ai gara mu zancen batsa da iskancin muka yi ba aikata shi muka yi da jikinmu ba.” Daff da ita Inna ta matsa sosai ta ce “waye ya aikata iskancin? Waye d’an iskan???”Ta yi mata tambayar cikin tsattsareta da manyan idanuwanta tana huci dama tun jiya take neman wanda zata sauk’ema takaicin Kaka a ka. Duk tsageranci irin na Asabe tana shakkar Inna, ta san sarai yanzun sai ta lakad’a mata dukan mutuwa ba k’aramin aiki ta bane ba yin hakan, dan haka sam sai ta gagara ambatar sunan Dije kamar yadda ta yi niyya taketa kuma fad’a tun d’azun. Sai kawai ta yi tsaki ta juya ta shige cikin d’akinta zuciyarta fal takaici, ga abunda Mallan ya yi mata a kan Dijen yanzun sannan gashi ita da kanta ta yada kanta a gaban mutanen gidan ta sake bawa Halima girma a idanunsu tunda dai gashi k’iri k’iri ta gagara tanka mata. “Ki dawo ki tanka mana! K’aramar marar kunya k’aramar munafuka. Ku kuma y’an koronta munafukai mu zuba da ni da ku a cikin gidan nan kar ku fasa fita daga harkata ni da y’ay’ana wallahi wahala za ku sha” Da sauri wata y’ar kyamurmurar mata (Maman Fati) ta ce “Wane mutum! Ai ko giwa ta fad’i ta fi k’arfin kiyasai su ja gawarta. Su Maman Sagir ne dai y’an koronta amma mu ai mun san dai dai mun kuma san gaibu.” D’aya bayan d’aya aka fara watsewa bayan kusan rabin matan da suke tsakar gidan sun taru sun taushi Inna sun nuna mata su babu ruwansu kamar ba da su aka gama gutsiri tsoma a tsakar gidan yanzun nan ba. Asabe tana ciki tana ta kwafa tana lissafa mutanen da suke ta bawa Inna hak’uri suna cewa ‘ta rabu da Asabe ba sa’ar ta bace ba, kar ta bari ranta ya b’aci saboda Asabe’ Tana aiyyana kalar yadda itama zata gurza musu tunda ba su san mutunci ba. Umar da Usama ne kawai suka rage a tsakar gidan dan kowacce ta shige cikin d’aki, masu fita yawon Juma’a kuma sun fice amma har zuwa wannan lokacin Inna tana nan zaune a tsakar gidan tana bala’i da masifa dan tana gama waya da Minu da ta ji jikinsa da sauk’i Alhamdulillah nan ta fito ta ja kujera ta dasa a inuwa ta shiga k’arewa Asabe d’iban albarka, gori kuwa kala kala kamar ita ta yankewa k’asar garinsu cibiya….Kasancewar wata k’anwar Asabe ta tab’a yin cikin shege, a cikin yayunta maza kuma akwai mai shaye shaye wanda kowa in dai a Unguwar kake to ka san Yaron da shaye shaye da sace sace!Hakan ya sanya Inna ta samu abun yi dama ta saba goronta mata akan hakan amma na yau ya fi na kullum ga kuma wasu sabbin surrakan gidansu waenda ita kanta Asaben ba ta san ta ya aka yi Innar ta ji ba, haka nan dai ta yi mata tatass! Ta tsigale ta ta yi mata tumb’ir dan har sai da ta saka Asabe kuka ita kad’ai a d’aki. Tukunna da kyar Ya Muhammad wanda ya dawo daga wajen Minu, yau d’aya ya ci nasarar mayar da ita d’aki lokacin har sallar la’asar an yi an idar. Wunin ranar Asabe a d’aki ta yi shi gashi babu wanda ya lek’ota dan Inna tana gamawa da ta mik’e ta shige d’aki sai ragowar matan gidan da basu fita ba suka taru a d’akin Ramma aka dasa faifan munafurcin gidan su Asaben! Dama yanzu haka ma akwai wata k’anwar ta bazawara da ta fito daga gidan miji kuma matar tana da d’an tara zawarawa ga shegen yawo, to ga kuma sabbin abubuwan da suka ji daga bakin Inna yanzun, dan haka topic d’insu na ranar sai ya kasance a kanta. Jikin Minu da sauk’i, an yi masa dressing na ciwonsa inda ya yanke a ta sanadiyyar dutsen da Yaron Ma’a ya cillashi a kai, yanzu haka ma ruwa ake k’ara masa zuwa bayan sallar la’asar zai dawo tare da samarin layin da suka yi cincirundon kaisa kuma har yanzu suke a tare da shi, kud’in asibitin ma sune suka yi karo karo suka biya…… Suna shiga d’akin Ya Muhammad ya kalleta ya ce “Inna ko kin san cewa daga makwabta aka kirani aka ce min har yanzu ba ki yi shiru ba in zo in raba fad’an, haka nan na baro marar lafiya na dawo.” Cikin fad’a fad’a Inna ta ce “Gidan su Suwaiba ko? Shegu munafukai, bar ni da su! Da suka kira ka ka dawo to duka na za ka yi???” Dafe Kai Ya Muhammad ya yi saboda sam shi sentence mai tsaho ma juya masa kai yake yi ballanta doguwar muhawara, cikin rashin jin dad’i ya ce “haba mana Inna, ya kike so in yi ne? Da wannen zan ji? Dan Allah ki daina…” Cikin katse shi ta ce “na ji!” Zai yi magana ta sake cewa “na ji na ce” a d’an hassale dan haka ya ja bakinsa ya yi shiruu. So yake ya fad’a mata sak’on Mallan da ya ce ‘Ita da Dije su bada kud’i a kai Zainab chemist’ amma yana jin tsoro dan ya san ba zata bayar ba kuma bala’i ne zai kunno kai, dan haka kawai sai ya yanke shawarar kai Zainab d’in da aljihunsa in ya so ya ce mata Inna ce ta bayar da kud’in dan ya san dole Mallan zai nemi ji daga wajensu, Allah dai ya sa Yarinyar ta yarda dan a yadda aka gama kashe boss da uwarta da Innar ya san tana da wayon da ya ci ta fahimci kud’in kaita chemist ba zai tab’a fitowa daga aljihun Innaa a yau ba. Haka nan ya k’arasa ya yi sallama a k’ofar d’akin nasu ya ce “Zainab ta zo zai kaita chemist a duba mata hancinta in da ya fashe.” Sosai Asabe ta so ta hana ganin sai yanzu ma aka kula su amma kuma kawai sai ta barta ta bishi a ranta ta ce “raba Arne da makami ibada ne.” Bayan Ya Muhammad ya fita, sallah Inna ta fara yi daga nan ta zari mayafinta sai gidansu Suwaiba makwabtansu. Sai da ta yi musu tatass!! Tukunna ta ji zuciyarta ta d’an yi sanyi ba laifi dukda kuwa rashin tanka mata d’in da suka yi ya b’ata mata rai amma dai ta rage takaicinta. Haka nan ta k’are musu d’iban albarka tare da kwakkwaran kashedin su daina yi mata shishshigi da munafurci daga nan ta juya ta fita ta koma gida.. Sai gab da sallar isha tukunna aka dawo da Minu. D’akin mazan gidan shine na farko a jerin d’akuna hud’u da suke a hannun hagu, dan haka suka nufi nan da shi, amma sai Mallan ya ce ‘su dawo da shi d’akinsa mai k’ofa ta soro’ Hakan kuwa aka yi suka kai shi daga nan suka yi masa sallama suka wuce bayan wasu a cikinsu sun shiga sun lek’a sun gaida Inna tare da yi mata jaje da fatan Allah ya kare gaba. Wannan Abu da aka yi ba k’aramin sake tunzura Asabe ya yi ba, dan ta gama tsarawa idan ta je turaka ne zata warware masa abunda ya ke cikinta amma gashi ya ce a kai Minu bayan yau d’in ba kwanan uwarsa bane ba kwanan ta ne. Har wajajen k’arfe goma na dare bata ji kuma ba ta ga an fito da Minu ba dan haka hankalinta ya sake tashi ranta ya sake b’aci!! ‘Ta yaya ma za a d’auki k’asurgumin gardi a d’aura a kan katifar sunnah fisabilillahi’ Ta aiyyana hakan a cikin ranta. Ta dad’e a tsaye tana ta faman lek’en d’akin, da yake akwai wata k’ofar shiga d’akin ta inda suke shiga ita da Inna da window ya sanya ta hango yadda aka rage fitilar alamun ana shirin yin barci kenan…. Ko mayafi bata tsaya d’auka ba daga ita sai y’ar hula da sleeping dress d’in da matar manager ta bata a kayan kunce dan Asabe ba dai son gayu ba, haka nan ta fito rai a b’ace ta Isa bakin k’ofar ta saka hannu ta tura amma sai ta jita a rufe. B’acin ranta ne ya sake hauhawa dan haka ta zagaya ta Isa bakin k’ofar d’akin dake a soro ta fara bubbugawa…. Ba ta wani jima ba ya zo ya bud’e mata, har yanzun rawani ne da babbar riga a jikinsa alamun bai yi shirin kwanciya ba. Kallonta ya yi kafin ya yi gyaran murya ya ce “yi hak’uri ban nemeki da wuri ba, yanzu nake shirin zuwa in nemi yardarki akan Minu ya kwana a wajena, Ina ga ba sai kin zo ba ko? Akwai tofin da nake son in kwana yi masa saboda kin san al’amari idan ya shafi kai dole a bashi muhimmanci.” Ba tare da ta kalle sa ba ta ce “ban amince ba”. Yadda ya yi da fuskarsa zai sanya ka fahimci maganar ta dake sa matuk’a amma sai ya kawar yana shirin yin magana ta katseshi ta hanyar sake cewa “Ban fa amince ba kuma ban lamunta ba! Ai kai Malami ne mai tsoron Allah dan haka na san ka san yin hakan haramun ne.” Dai dai nan Kaka wadda tun d’azu ta ga fitowarta ta k’araso wajen cikin takunta na tsoffi rai a d’an b’ace ta ce “yanzu ja’inja za ku tsaya yi ku tarawa kanku jama’a ko yaya?” Dai dai nan Minu wanda tunda ta fara maganar ya farka ya tashi daga kan kafet d’in inda ya yi shimfida shima ya k’araso wajen… Da kyar kunya ta barshi ya iya cewa “Mallan bara in je da safe sai ka k’arasa min.” Cikin d’an b’acin rai Mallan d’in ya ce “wa ya sako da kai?” Yana shirin yin magana Kaka ta ce “Aminu wuce ka tafi d’akinku” A hankali Mallan ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai. Simi simi Minu ya zo ya wuce bayan ya yi musu sai da safe gaba d’aya jikinsa babu kwari. Cikin d’an fad’a fad’a a hankali saboda kar a ji Kaka ta ce “ka san Allah idan ba ka daina gwada wannan son kan da nuna banbancin ba to ka tabbata za mu samu matsala da kai! Wanne irin sakarci ne haka za ka d’auko k’ato ka saka a d’aki ranar kwananta?? Kuma idan ta yi magana sai a ce ba ta da gaskiya ba ta kara bayan kune da laifi! Ina ce rigimar y’ar uwarsa ce ta jefa shi a matsalar dan haka Ina ruwanka?? Ai dama abunda ake fad’a ake guje muku kenan amma sam ba kwa ji yanzu ga irinta nan! Ayi mutum kamar mai karin kumallo da wuta amma sam baka son laifinta ita da uwarta ai kuwa ka gamu da aiki babba wallahi.. Sannan Ina so ka jaa wa Halima kunne duk da na san ba jinka zata yi ba dan ta raina kowa amma dai ka fad’a mata kuma ka yi mata kashedi mai zafi!!! D’azu bayan ka fita haka nan ta wuni a gidan nan tana rashin albarka dukda kuwa kashedin da na yi mata amma bata ji ba saboda ta raina ni, ban kula ta ba a lokacin amma wallahi ka ce mata na ce idan ta k’ara to ni da ita ne a cikin gidan nan, da ni za ta yi! Ai ta sanni ta san abunda zan iya aikatawa dan haka mu zuba ni da ita a cikin gidan nan tunda ita dai ta ce bata san mutunci ba.” Tana gama fad’in haka ta juya ta bar wajen zuciyarta fal tsanar Inna da y’ay’anta. Tana wucewa ya juya shima ya wuce ciki ya barwa Asabe k’ofa a bud’e ba tare da yace mata komai ba. Ya san tana fashin sallah yau d’in shiyasa ya so yiwa Minu tofi da addu’o’in kuma har ga Allah bai yi zaton zata ji haushi ko ta ce bata yarda ba dan inda ace ya san zata yi hakan to da ba zai ma fara ba, duba da yadda Minun yake jin jiki ya sanya ya yi tunanin zata yi masa kawaici amma kalli abunda matar nan ta yi, shi kwata kwata ya rasa gane dalilin da ya sanya har gobe ita da Halima ba zasu rungumi juna su so y’ay’ansu a matsayin abu d’aya ba. Yana wannan lissafin ya k’arasa cikin d’akin ba tare da ya ko waiwayeta ba. Ta so ta yi masa k’orafe k’orafe had’e da lallashi ban hak’uri tare da kissa amma yadda ya had’e rai wanda hakan abune sabo a wajenta ya sanya ta sha jinin jikinta ta nemi gefen katifa ta kwanta………. Tunda dare ya yi dama Dije ta sha jinin jikinta, kana ganinta ka san a tsorace ta ke, ai kuwa ta fara bacci kenan ta ji sauk’ar wayar radio……Gashi babu damar ta yi ihu. Sai da Inna ta zane ta da wayar radion nan kamar wata y’ar Yarinya tukunna ta rufeta da fad’a baki da kumfa, sannan ta ce “daga yau ko a hanya ne idan ta ga Ma’a to ta chanja tata hanyar” Sam Inna ta ma k’i ta tsaya ta ji bayanin Dije da take ta cewa “k’arya Zainab ta yi mata Ma’a bai rik’eta ba Ya Aminu bai bashi dama ba” Dama ita Innar ta san da hakan, ita kawai abinda ya fi damunta shine ‘Ma’a’ d’in wanda ta lura ya fara sakawa Dijen ido dayawa kamar sauran samarin layi, gashi ita kuma mahaukaciyar Yarinyar a nata shirmen tsayawa take yi ta ce zata yi fad’a ko ta biye masa…tun kafin Dije ta kai haka Inna take addu’ar Allah ya kareta daga sharrin maza, gashi Yarinyar tun lokacin da ta fara al’ada gaba d’aya ta bunkushe kullum komai nata sake fitowa yake gashi surarta mai matuk’ar d’aukar hankali ce, shiyasa kwata kwata ko da wasa bata k’aunar abunda zai had’a ta da wani d’a Namijin idan ba su Aminu ba, dan haka take a tsaye idanunta a kanta sosai wannan dalili ya sanya ita kanta Dije in dai ta san an ganta da wani ko wani ya biyo ta to a d’ari-d’ari take wuni, idan kuwa ta san an ganta da Ma’a to a tsorace ta ke kai dare dan ta san wayar radion Inna na nan tana jiranta. Ba Inna kad’ai ba hatta su Ya Aminu da Mallan ganin Yarinya suke yi mata har yanzun, sannan karatu suke so ta yi a halin yanzun ba wai tara samari tun bata gama secondary school ba. Shiyasa sam ba su bada goyon bayan ta kula samari ba, musamman ma Minu wanda indai kana so ya daina ganin mutuncin ka to ka ce ‘kana son k’anwarsa Dije’. Washegari da safe ta kasance Asabar, ranar hutun mako ta farko, ranar da al’umma sukan d’an kwanta su huta saboda babu fitar safe..ga kowa kusan hakan take amma ga al’ummar wannan gida kuwa za a iya cewa yau d’in tun Asubar fari suka fara tashin hankalin nasu wanda ya zame musu tambari a unguwa. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 03. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Tun kiran sallar farko da aka yi Ramma ta tashi bata koma ba, tana ta fama da k’ullin fanken siyarwarn ta wanda ya k’i tashi sam! Dama tun jiya da daddare bayan ta kwanta ta d’an ji sanyi-sanyi da iska a garin sai da ta tashi yanzun tukunna ta ga ashe hadari ne a kwance gashi kuma sai da ta duba sai ta ga ashe yeast d’in marar kyau ne, dan haka ta karb’i wani a wajen Maman fati ta k’ara sannan ta d’aura ruwan d’umi a murhunta dan ba ta ga alamun rana zata fito da wuri ba yau d’in. Kasancewar ta san idan ta fita k’ofar gida tuyar fanken to ba lalle ta gama ta dawo da wuri bane ya sanya ta koma d’akinta ta shiga k’imtsawa. Mijin Ramma bai dad’e da rasuwa ba ya rasu ya barta da Yara uku..Y’ay’anta biyu mata Fiddausi da Rakiya, Fiddausi na da shekara goma Rakiya kuma sha biyar sai Usama na tsakiyar su mai shekaru sha uku…. Y’an matan suna kwance suna ta sharar barci ta shiga ta kimtsa ta gyara ta share koina ta tattare ta linke kaya, gadon da suke kwance kawai ta bar musu idan sun tashi su gyara sai kuma tallar fanken da idan ya yi saura Fiddausi za ta tafi ta kaiwa wata makarantar koyon d’inki Umar kuma shi zai yi wanke wanke Rakiya kuwa ba ta uwar komai dan har girki ba ta cika yi ba Ramma ce ta ke yi, Ramma irin matan nan ne masu masifar son y’ay’ansu da sangarta su gashi bata so su wahala musamman Rakiya . Ba su dad’e da dawowa Unguwar ba Mijinta ya rasu yau shekaru biyu kenan, tun daga nan ta d’auki nauyin y’ayanta uku daman kuma daga danginta har na marigayin Mijin nata duk ba masu zumunci bane ba dukiyar marayun ma da bata fi miliyan biyar ba gaba d’ayanta wani k’aninsa ya handame yanzu haka ana kotu. Babu yadda ba’ayi da Ramma ba akan ta bar y’ay’anta suma su yi sana’a amma furr ta k’i! Ita ce wankau ita ce suyar fanke asabar da lahadi Litinin zuwa Juma’a kuma akwai wata makarantar boko da

Chapter 2 of 23