Share this page
d’in da ta tasarma. Addu’arta d’aya Allah dai ya sa suna wajen dan ta san lokuta da dama su kan je wajen tun kafin bayan la’asar d’in. Tafiyar kusan mintuna bakwai ce ta kaita tafkeken filin ball d’in…..tun da ta tunkaro wajen ta hango Oscar shi da Scorpion suna zagaye wajen yayinda Ma’a ya ke tsaye ya yi irin tsayuwarsa ta sojoji kamar kullum da whistle a bakinsa yana kallonsu. Sai yanzu da ta iso wajen tukunna lissafinta ya bata ‘ta yaya za ta je ta hura masa kuma har ta juya ta gudu ba tare da an ganta ba?’ Dan sholl wajen yake babu kowa sai su uku kacal gashi wajen babba. K’uruciya da k’udirin d’aukar fansar d’aureta da kukan da ya saka ta ne suka tunzurata tare da bata amannar ta tunkare sa kawai komai ta fanjama fanjam! Luckily, su Oscar gaba suke kallo suna ta gudu basu kai ga kaiwa angle d’in da za su iya ganinta ba shi kuma dama ya juya baya su yake kallo. Cikin sassarfa at the same time tana mai d’auko k’ullin dake a cikin jakarta, a haka ta k’arasa inda yake dai dai ta gama zarowa ta ware da sauri ta d’an durk’usa ta hura masa a sangalalin k’afafuwansa da yake kayan ball ne a jikinsa sai kuma ta mike ta hura masa a bayansa da wuyansa daga nan ta juya da niyyar d’iba da gudu ta bar wajen ta ji gamm!! An ruk’o hannunta da mugun k’arfi!. Yadda k’irjinta ya buga ita kanta ta yi tunanin zuciyarta ta tsage ne. Da mugun sauri ta juyo dan a yadda yake bai ci a ce har ya juyo ya rik’eta hakan ba. Da mamaki take kallon sa tana kallon su Oscar waenda sam ba ta ma san lokacin da suka k’araso wajen ba. Suma su duka ukun ita suke kallo dan haka aka tsaya ana y’ar kallon kallo. Tunda Dije take ba ta tab’a jin bakinta ya mutu murus ta rasa abin fad’a ba sai yau, wani irin kallo ta ga Ma’a yana yi mata wanda yake sanyata jin wani irin matsanancin tsoro dan bai saba yi mata irinsa ba. Yunk’urawa Oscar ya yi zai yi magana da sauri ya d’aga masa yatsunsa biyu na tsakiya sai kuma ya yi masa alamar su tafi. A take babu musu suka juya suka ci gaba da abinda suka baro ba tare da sun sake ko da kallonsu ne ba. Tsoro da firgici had’e da dana sani ne suka lullub’e Dije a take ta sake sunkuyar da kanta k’asa ta ci gaba da k’ok’arin kwace hannunta wanda ita kanta ta san it’s impossible dan wani irin rik’o ya yi mata kamar zai karyata. Kusan minti d’aya tana abu d’aya gashi a tsaye kamar wani dutse ko motsi bai fara ba ballantana rawar diskon da take tunanin zai yi, balle har ta samu ta gudu. A hankali cikin raunin da ba d’abi’arta ba ta d’ago kyawawan fararen idanuwanta da suka d’an fara kad’awa zuwa jaaa ta zuba masa da kyar ta aro jarumta ta furta “mallan ka cika mini hannu” Kallonta yake yi bai kuma cikatan ba kamar yadda ta so, a hankali ta ga jajajajaa yana maye gurbin farin cikin idanuwansa, sai kuma gumi ya fara tsattsafo masa a take. Sai da ya lumshe idanuwansa tukunna ya bud’e sannan ya juya ya kalli ledar da ta mak’ale a k’afar bencin da ke a gefensa iska tana kad’ata tana shirin barin wajen, d’an k’urawa ledar ido ya yi wanda hakan ya sanya ita ma Dije ta kalli wajen, a take kuwa gabanta ya yanke ya fad’i dan ta yi tunanin da ta gama hura masa ta yar tuntuni iska ta kwasa ta yi gaba da ita. Dakewa ta yi ta sake aro jarumta ta ce masa “mallan na ce ka cika mini hannu ko???” Cike d’an zafi. Da mamaki ya d’ago yana kallon Yarinyar kafin da kyar ya magantu kamar an fisgi maganar daga bakinsa ya ce “me na yi miki ki ka zuba mini karara??” Already jikinsa ya riga ya zama weak dauriya ce kawai yake yi amma masifaffiyar azabar k’aik’ayin da yake ji ba zai fad’u ba! Gashi shi kansa by now so yake ya sakin mata hannu amma dukda hakan da kuma kokawar da take yi ta gagara kwace hannun nata. Cike da tsiwa da fushi dan zuwa yanzu ya gama k’ular da ita ta ce “hala kana da aljanu ko? B…” Maganartata ce ta mak’ale a take ta kasa k’arasa abunda ta d’ebo za ta fad’a dan haka ta kawar da kanta tana guna guni, sosai ya tsareta da idanu gangar jikinsa tana karb’ar azabar k’aik’ayin da bai tab’a tunanin tana existing a duniya ba! Mamakin audacity d’in Yarinyar kawai yake yi dukda kuwa ya san tsiwa rashin tsoro da fad’a d’abi’arta ce amma sam bai yi tunanin zata iya zuwa har nan ta d’auki fansar abinda ya yi mata ba dan ba shi da tantama abunda ta yi masa yau d’in yana da alak’a da tare mata hanyar da ya yi kwanaki shidda da suka wuce! A b’angaren Dije kuwa bayan tsoron Inna da Kunyar Ya Muhammad da shakkar Mallan ba ta tab’a jin wani abu makamancin hakan ba ga wani d’an Adam sai a yau! Dan sosai Ma’a yake bata mamaki da kuma tsoro ita kam a ranta har ma ta fara tunanin anya kuwa ba al’jani bane ba! Saboda kararar k’auyen su Sumayya daban take, duk ranar da ta je k’auye ta taho da ita wallahi ko waye idan suka zubawa sai ya kwana yana hauka amma gashi da ikon Allah ko motsi Ma’a bai yi ba sai dai fa daga ganin yanayinsa ta san yana kan karb’ar azaba….. Wani mahaukacin k’aik’ayi da ya mintsine shi ne ya sanya bai san lokacin da ya damk’e mata hannu more than ruk’on da ya yi mata da farko ba. Zabura ta yi ta sake k’aimi wajen k’ok’arin kwacewa a lokacin guda kuma ta na jin wani irin tuk’uk’in bak’in ciki yana taso mata ga zafin da take ji, ba ta san lokacin da ta doka wani uban tsaki ba ta ce “mugu d’an daba kawai!” Da sauri ya d’ago ya kalleta cikin wani irin yanayin da ta gagara fassarawa. A hankali ta ji ya sakin mata hannu ya juya mata baya ba tare da ya sake cewa uffan ba. Shiruu ta yi kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta juya da sauri ta bar wajen cikin sassarfa……… Har ta je gidan Rabi’a ta karb’a kud’i daga nan ta k’arasa makaranta zuciyarta fal sak’e-sak’e, ganin tunanin abun da ya faru yana neman damalmala mata lissafi ne ya sanya ta kawar da duk wani abun da ya shafe sa ta shiga sabgogin gabanta, alk’awari d’aya ta yiwa kanta shine ba zata sake tunkarar Ma’a ba, hannunta da ya rik’e take tunanin sake musguna masa shima ta barshi kawai Allah ya Isar mata, dan ta lura al’amarin sa ya fi k’arfinta sai yanzu ta ga gaskiyar su Inna da suke ta cewa ta guje masa shi d’in ba tsaran yinta bane ba. Ko da Sumayya ta tambayeta ‘ya ake ciki? Bata ce mata komai ba kawai sai ta sako wani zancen, fahimtar da Summayar ta yi Dijen ba ta son yin maganar ne ya sanya itama ba ta sake cewa komai ba. …….. A bakin k’ofar gidansu ta tarar da Ya Muhammad a tsaye yana jiranta! Haka kurum tana ganinsa dama ta ji gabanta ya yanke ya fad’i. Da sauri ya taso daga kan d’an dakalin sokaway d’in da ya ke kai ya k’araso inda ta ke yana zuwa ya kama hannunta ya jaa suka wuce gidan sai da suka kai bayan layinsu tukunna ya cikata. Daga yanayin yadda ta ji jikinsa yana karkarwa tun lokacin da ya ruk’o ta dama ta san a rina! Ai kuwa yana fara magana ta fahimci yanayin da yake a ciki. Cikin inda inda ya ce “Dije mai yasa bbaa kkya ji neeee?” Sai kuma ya yi shiruu ya dafe goshinsa bakinsa ya shiga karkarwa. Kuka ta fashe da shi a take dan wannan yanayi na Ya Muhammad shine abunda take matuk’ar jin tsoro da gudu. “Shhhhhh” ya ce da ita kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru sakamokon mak’alewar da ya ji maganar ta yi. A hankali da kyar kamar an fisgi maganar daga cikin bakinsa ya ce “kar ki shiga gida yanzu” Har ya juya kamar zai tafi sai kuma ya dawo da sauri ya damk’i hannuwanta duka biyu da sauri sannan da k’arfi ya ce “Dddjee mai yyyasa ba kya ji ne?” Fashewa ta yi da kuka sosai ta ce “dan Allah Ya Muhammad ka yi hak’uri…” “Shhhh” ya sake cewa da ita cikin katseta sannan ya ce “ya zaki je wajen Ma’a da kanki??” Sosai gabanta ya yanke ya fad’i tana shirin yin magana ta ga ya fara karkarwa sai kuma ya fara kai mata duka, da sauri ta matsa Allah ya taimaketa bai sameta ba ya samu bango, cikin k’ank’anin lokaci kafin ta juyo ya zube a wajen sumamme. Zuwa lokacin dama hankalin mutane ya d’an karkato zuwa garesu dan haka aka nufesu……. Tsaye Kaka take a tsakar gidan hannunta d’aure da bandeji an sak’ala mata ta wuya ga Asabe a gefenta Ya Aminu a kusa da Inna yana huci sai Mallan shima a tsaye a gefen Kaka ta d’ayan b’angaren. Ragowar mutanen gidan kuwa kowa ta turo k’ofa ammafa da za a yi rashin sa’a wani ya tura k’ofar d’akin d’aya daga cikinsu to da tsaff zai yi tafiyar ruwa da duk ahalin d’akin saboda yadda suka kafa kunne suka mammanne a jikin k’ofofin d’akunan nasu suna d’aukar rahota. Cike da d’acin zuciya Ya Aminu ya ce “har ga Allah abunda ake yi mana a gidan nan ya Isa haka! Hak’urina ya fara k’arewa za fa a yita babu kyau wallah!” Ya k’arashe maganar cikin d’aga murya. Da sauri Mallan ya daka masa tsawa ya ce “wa kake d’agawa murya? Sa’ar ka ce ita” Wani Irin murmushin takaici Minu ya yi kafin ya ce “ni iyaka d’aga murya kawai na yi amma gashi ka ji haushi! Shin ni kuma ba ka ji abunda ta gayawa tawa uwar ba?“ Cikin zafin nama Mallan ya d’aukesa da mari mai tsananin sauti… Kafin ya yi magana Kaka ta rigashi ta hanyar cewa “ai ka ga irinta nan! Shiyasa na ce waennan Yaran ba jinina bane ba ba y’ay’anka bane su tun wuri ta je ta nemo ubansu kafin su kaimu lahira.” A mugun fusace Aminu ya yi kanta kamar zai rufeta da duka! Kuma da gaske da niyyar shak’etan ya nufeta Allah ya taimaka Mallan ya shiga tsakani. Fashewa da kuka Kaka ta yi ta ce “wallahi na gama zama gida d’aya da shegun y’ay’an nan, ka duba ka gani yanzu fa inda ace baka nan da rufeni fa zai yi da duka! Ace Yara daga mahaukaci sai marar mutunci sai y’ar iska sannan a haka a ce wai jininka ne su?? Wallahi da sake.” Da sauri Mallan wanda ya gama dakawa Minu tsawa akan ya nutsu ya juyo ya ce “Kaka ba fa Halima kad’ai kike aibantawa a nan ba har da ni tunda y’ay’anane, kuma maganar jini ma ba ta taso ba dan na riga na san nawa ne su d’in dan haka ki ma daina wannan maganar dan Allah..Dije kuma babu inda za ta je, na hukuntata tun a ranar sannan yanzu ma zan sake hukuntata amma ba zan kori y’a ta mace budurwa daga gidana ba ki yi hak’uri dan Allah kar ki kaini wuta hakkine a kaina in kula in saka ido a kanta in bata ingantacciyar tarbiyya, yanzu idan na koreta Ina za ta je??” Dai dai nan aka shigo da Ya Muhammad hankali a tashe Dije a bayansu tana wani irin kuka kamar ranta zai fita. ************** D’aki ne Babba sosai wanda a k’alla fad’insa zai kai taku 40 tsayinsa shima haka. Kallo d’aya za ka yiwa d’akin ka fahimci na y’an Sarauta ne sakamokon adon da pop da bangon d’akin har ma da k’ofofin da windunan d’akin suka sha na asalin gold da azurfa abun har abun tsoro dan kamar ba a san darajar abun da aka yi adon da shi ba. Kujeru ne na asalin Royal waenda suka amsa sunansu Royal da wata tafkekiyar tv a ajjiye gefe guda. Sai wani tangamemen gado (king size) da wardrobe d’insa da madubi da drawer da side drawers suma a gefe guda. Hatta standing acn dake a d’akin itama adon ta tsarin yanayin d’akin ne….. Dogo ne fari tass wanda kallo d’aya za ka yi masa ka san cewa shi d’in kyakkyawa ne ajin farko, sumar kanshi ba lallausa bace ba yanayin ta irinta Hausawanmu ce, bai cika k’iba ba sannan ba siriri bane ba. Yana sanye da wata fara k’all d’in alkyabba da dogon wando shima fari, k’irjin akyabbar a bud’e kuma babu komai a ciki wanda hakan ya bawa faffad’an k’irjinsa damar baiyyana wanda kana ganin yanayin jikin nasa za ka san ya saba ziyartar gym. A kwance yake (kwanciyar rigingine) a kan gadon yayinda sangalalin k’afufuwansa suke a kan cinyar wani Hadiminsa yana yi masa tausa kansa kuma yana a kan wasu pillows na feathers masu asalin taushi. Waya ce a hannunsa yana daddannawa kwata kwata baza ka ce hankalinsa yana a kan waenda suke bakin gadon ba, kamar ba buk’atarsa ce ta kawo su d’akinba. Ya fi kusan mintuna ashirin Yayinda Hadiman nan mata su uku suke a tsaye kyarr! Ko numfashi da kyar suke jaa kafin da kyar ya magantu ba tare da ya kallesu ba hankalinsa yana a kan wayarsa ya ce “undress yourselves”. A take jikinsu ya d’auki karkarwa kamar an jona musu wutar lantarki, dukda mutum d’aya ce kawai ta fahimci me yake nufi amma ragowar suma sun d’an fahimci yaren nasa…. Kuka d’ayar ta saka ta durk’usa tana shirin yin magana ya yi fito, a take sannan da gudu wani hadimi ya shigo ya na zuwa ya durk’usa a gabansa kansa a k’asa “Ka kaita mari” Kawai ya ce ba tare da shima ya kallesa ba. Da a kaika mari d’in da yake a cikin masarautar gara a kashe ka ta hanyar rataya a cikin kasuwar garin gashi a k’aida idan ka shiga Mari sai ka yi shekara uku ma tukunna za a waiwayeka. Kuka sosai ta fashe da shi jikinta yana karkarwa tana rok’o tana mai neman yafiya a wajen wanda ita kanta ta san bai ma san mecece kalmar yafiyar ba! A haka aka jaa aka fitar da ita waje babu tausayi babu jin k’ai. Yana fita waje ragowar y’an matan suka shiga yin abinda suke tunanin yana nufi hankulansu a masifar tashe dan in dai har hakan yake nufi to alk’iyamarsu ta tsaya ne saboda sun san me zai biyo baya sannan a al’adar masarautar tun daga kan matan sarki har zuwa kan baiwa in dai a cikin masarautar kike aka yi aurenki aka kaiki gidan Mijinki ya tadda hanyarki a bud’e to hukuncin kisa ne a kanki! Matan sarki da wasu daga cikin masu asalin mulkin masarautar ne kawai ake yi musu d’aurin rai da rai a kurkukun sarakuna ko kuma a yi musu tozarcin da wata sai ta zab’i mutuwa ma da shi, amma ragowar kam musamman ma bayi a washegarin ranar ake tsiresu. Tsindir haka suka yi suka tsaya a gabansa jikinsu na karkarwa. Da camerar wayarsa yayi amfani ya gama k’are musu kallo ta cikin wayartasa ta hanyar zooming kafin ya ce ‘su juya,’ nan ma ya gama k’are musu kallo…… Tsaki ya yi cikin d’an b’acin rai ya ce “get out!” Da sauri kamar za su zuba ruwa a k’asa su sha don murna suka sunkuya suka rarumi kayayyakinsu suka fice a guje tib’ir tib’ir zannuwansu kawai suka samu damar yafawa suka fice suna masu k’ok’arin mayar da ragowar suna masu jero hamdala a zuk’atansu. Suna fita ya mik’e tsaye cikin d’an fushi ya kalli amintaccen hadimin nasa wanda ya yi saurin saukk’owa ya sunkuya a gabansa. Cike da izza sannan ka na iya jiyo b’acin rai a cikin muryar tasa ya ce “is that the best you can find?” Jinjina kai Hadimin nasa ya yi ya ce “daga cikin dukkannin Hadimai kamar yadda ka buk’ata, waennnan sune kawai muka samu masu irin shekarun dai da ka ambata…Dalilin kuwa shine ka san batun satar da aka yi a parlourn Gimbiya Zakiyya ya janyo an rasa dayawa. Amma na ga wasu a cikin bayin masu lamba d’aya….” “To hell with them” Ya furta hakan cikin zafi, wanda ya sanya Hadimin na sa yin shiru. Fuuuu! Ya juya ya fita ransa a b’ace, a take Hadimin ya mik’e ya bi bayansa yana fita wasu guda goma a cikin masu tsoron k’ofar d’akin suma suka take masa baya. **************** BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 07. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Dije tana barin wajen azabar kararar k’auyen su Sumayya ta sake k’aimi a jikin Ma’a. Duk dauriyarsa bai san lokacin da ya tafi kamar zai kifa ya damk’i bencin dake ajjiye a gabansa da sauri ba, a take wani irin zazzafan gumi ya shiga tsattsafo masa fiye da farko ta ko wacce b’ular gashi dake a jikinsa kamar wanda ya watsa ruwa. Kad’an ya rage bai kurma uban ihu ba, dai dai lokacin da su Oscar suke k’arasowa wajen a guje sakamokon ganin halin da yake a ciki shi kuma bugun zuciyarsa ta fara sauyawa ya shiga janyo numfashi da kyar. A machine suka goya shi suka nufi gida da shi wanda kafin su k’arasa gidan Oscar shima ya goga, kad’an kuwa ya rage bai zubar da su ba, suna isa ko gama cikakken parking bai yi ba ya diro a gigice ya afka d’akin Ma’a ya shiga toilet ya kunnawa kansa ruwa wanda hakan ya zamo masa kamar mabud’in masifar k’aik’aiyi. Allah ya so shi bai kwab’e kayan jikinsa ba dan a hakan sa ya fito yana zabga ihu kamar ba Oscar ba. Ihun nasa ne ya fargar da Mama ta fito daga kitchen da wuri dai-dai Scorpion ya kamo Ma’a yana tafiya da kyar numfashinsa yana fita da kyar sama-sama. Shi kansa Scorpion d’in zuwa yanzu ya goga dauriya ce kawai yafi Oscar sannan shi bai zubawa kansa ruwa ba. Mama tana ganinsu a haka ta nufesu hankali a masifar tashe. Da kyar Scorpion ya iya cewa “karara ne Mama kar ki matso.” Dan haka ta ja ta tsaya sai kuma ta k’arasa ta je ta shimfid’a musu tabarma Scorpion ya k’arasa da shi kai ya samu ya taimaka masa ya kwantar rigingine dan zuwa yanzu shi kam bai ma san a wacce duniyar yake ba ga numfashi yana ta d’ad’d’aukewa kamar mai shirin barin duniyar. Kuka Mama ta saki har ta mik’e tana shirin ce musu su tafi asibiti sai kuma ta koma ta zauna dan ta san azaba da bak’in ciki ne suke jefa shi a cikin irin wannan halin dan haka ta shiga yi masa tofi. Kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta mike ta ce “bara in d’auko manja a zuba muku yana rage k’aik’ayin. Da sauri Ma’a ya ruk’o gefen zaninta tana juyowa ya girgiza mata kai kawai. Ta fahimci baya so ta bar wajen ne dan haka ta koma ta zauna ta ci gaba da yi masa tofi yayinda shi kuma ya lumshe idanuwansa kawai ya na mamakin Dije…. Da mugun gudu Oscar ya afka cikin kitchen d’in ya kinkimo galan d’in manja ya shiga kwararawa kansa gaba d’aya ya gigice, zuwa wannan lokacin shi kansa Scorpion duk dauriyarsa ya fara murk’ususu kamar mai shirin fara breakdance, ganin dauriyar fa ba zata kaishi ko Ina ba gashi abin sake k’arfi yake yi ya sanya ya mik’e ya k’arasa ya shiga shafawa jikinsa manja shima, kafin minti d’aya sun yi nasha nasha abinsu da manja in ka gansu kamar ma su tallar maita. Kuma har zuwa wannan lokacin a gigice suke dan su dai ba su ji alamun sassauchi ba. Mama ita dai tanata kallonsu duk da halayyarsu amma sai da ta tausaya musu, dan haka kawai take ta binsu da sannu. Shi dai Ma’a bai ce komai ba kawai ya lumshe idanuwansa, chaaan! Kamar a mafarki Mama ta ga wani sassanyan murmushi ya sub’uce masa. Sai bayan kusan awa hud’u tukunna da kyar aka samu k’aik’ayin ya d’an lafa, ba wai ya d’auke gaba d’aya bane kawai dai ya d’an lafa. Har zuwa wannan lokacin Mama tana tare da su tanata yi masa tofi shima kuma ta bashi add’u’o’i tace ya yi ta yi, idan ta yi salla ta idar ta yi addu’a sosai ta tofa masa, ya d’an ji dama-dama haka suma su Oscar da ta basu addu’o’i ta ce su yi ta yi, amma har zuwa wannan lokacin numfashin Ma’a bai dawo dai-dai ba kuma idanuwansa a lumshe suke…. Lissafi kawai yake yi yana mamakin Dije lokaci zuwa lokaci kuma yake sakin wani lallausan murmushin da yake shirin fara firgita Mama.. tabbas yau kam ya had’u da wadda ta azabtar da shi cikin sauk’i, abunda zaratan maza suka gagara yi yau gashi Yarinya k’arama ta yi, dan tabbas shi kansa ba zai iya expressing kalar uwar azabar k’aik’ayin da ya kwasa a yau d’in ba. Sai da ta ga sun d’an fara nutsuwa tukunna ta nemi jin ba’asi, har Oscar ya bud’e Baki Ma’a ya yi saurin juyawa ya zuba masa rinannun idanuwansa da har yanzu basu kai ga fara dawowa dai-dai ba. Shiru ya yi ya had’iye maganarsa, ya sunkuyar da kansa k’asa zuciyarsa kamar zata fashe tsabar takaici! Tabbas yau idan Oga ya hanasa halaka Yarinyar nan wallahi watak’il sai jininsa ya hau idan bai kamu da ciwon zuciya bama kenan! Ko da ace bai halaka ta ba to Yarinyar ko y’ar gwal ce ya kamata a barsu su yi mata tambarin da har tsufanta ba zata tab’a mantawa da shi ba. Scorpion kam shi bai yi tunanin yi mata komai ba dama dan ya san Oga ba zai tab’a bari ba (kamar kullum), amma fa shima ya shak’a dan har yanzun bai gama dawowa dai-dai ba, wai kamar su ace wannan y’ar Yarinyar ta haukata ta gigita a cikin k’ank’anin lokaci amma gashi da ikon Allah haka nan suna ji suna gani za su bar komai ya wuce saboda ba su isa yin komai a kai ba. Shiyasa ya shiga zaginta da aibantata kawai a iyaka cikin zuciyarsa kamar wani Yaro dan ya san bai isa ya yi a fili ba. Sai da suka sake nutsuwa tukunna Oscar da Scorpion suka ce masa “Bara su je su kimtsa” Ko da suka fita sai da suka bawa jama’a tsoro Allah ma ya so su duhun dare ya iso, yayinda waensu ma da kyar suka iya gane su, haka nan suka wuce zuwa d’akunan su da suke haya a wani gida mutane suna ta satar kallonsu dan ba su Isa su yi k’iri-k’iri ba. Suna fita Mama ta mayar da kallonta ga Ma’a wanda yake nan kwance a kan tabarma har yanzun idanuwansa a lumshe. Fuskar tasa ta k’urawa ido a take ta ji duk ta muzanta! Babu wanda zai kallesa sau d’aya ba tare da ya fahimci wayene shi d’in ba. Allah ya d’aura mata matsanancin son d’anta Ma’aruf dan zata iya cewa babu wata uwa da take son d’anta sama da ita a kaff fad’in duniyar nan, shiyasa take jin tsoro a duk lokacin da irin wannan ciwon nasa ya tashi, kuma take gujewa duk wani abunda zai tada masa ciwon nasa, dan tana matuk’ar jin tsoron abunda zai rabata da shi dan haka take kare duk wani abun da zai janyo b’acin ransa, wanda hakan ya sanya take ganin kanta as selfish take kuma jin tsoron ranar da zata tsaya a gaban Ubangiji ta yi masa bayanin amanar da ya bata, ta san tana iyaka bakin k’ok’arinta kuma tana addu’a ba dare ba rana amma tabbas wani abun har da kasawarta… Addu’a ta shiga yi masa sosai tana zaune a hakan….ta jima tana addu’a tana mai neman taimakon Ubangiji kafin chaan ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya “Babu aure babu sana’a babu girma, ko yaushe Allah zai shirya min Ma’aruf d’ina??” Ta yi maganar da ita a tunaninta a zuciyarta ta yi ba ta san a fili ta yita ba. A hankali ta ga ya bud’e idanuwansa ya zuba mata su, wanda sai a lokacin ne ta fahimci ashe maganar tata ta fito fili. A hankali ya gyara ya mik’e ya zauna kafin ya d’an k’uraa

Chapter 6 of 23