mata ido sai kuma kawai ya mik’e ya ce “Bara in je in yi sallolina”
Daga haka ya mik’e da kyar dan har yanzu k’irjinsa bai dawo dai-dai ba. Ya wuce zuwa d’akinsa.
Ta d’an jima a zaune a wajen kafin chaan kuma ta mik’e itama ta wuce bayi dan har an fara kiran sallar isha.
Cikin tsananin tashin hankali Inna ta nufi k’arshen tsakar gidan inda mutanen da suka kinkimo Ya Muhammad suka nufa da shi.
Jikinta har karkarwa yake yi tana isa ta durk’usa a gabansa ta shiga duddubashi a lokaci guda tana tambayar “mai ya same shi?”
Wani Yaro ne ya ce “tare suke shi da Dije yana tambayarta ‘mai ya sa ta je wajen Ma’a ta bari ya rik’e mata hannu’, sai kuma kawai ya yanke jiki ya fad’i.”
Difff!! Haka kowa ya d’auke wuta hatta Kaka wadda take ta sababin ‘kar a wani d’aga hankali ai hakan ba komai bane tunda dama an riga an san da zaman ciwon nasa na hauka’.
Sheshshek’ar kukan Dije ne ya ci gaba da tashi a tsakar gidan, cikin raunin da ba d’abi’arta ba ta matso tana zuwa ta durk’usa a kusa da Inna tana cewa “Inna mu kaishi asibiti, kar yau ma ya s…”
Wani irin gigitaccen mari Inna ta sauk’e mata wanda ya sanya ta yin shiru a lokaci guda kuma ta shiga shock! Ita da gaba d’aya al’ummar gidan na tsakar gidan da masu lab’e dan waenda za su ce sun tab’a ganin Inna ta sakawa Dije hannu k’alilan ne a cikinsu, yawanci in zata hukuntata sai su kad’ai da daddare take yi.
Cike da tsana Kaka ta ce “ai ba ki ga komai ba! Wallahi ba ki ji komai ba Halima wannan y’ar taki sai ta saka ki kuka da ciwon zuciya, kuma yanzu ai kin makaro dan lokacin hukuntata ya riga ya wuce ko kin yi a banza dan shi reshe tun yana d’anye ake tankwara shi idan ya riga ya bushe aka ce za a tankwara sa to karyewa zai yi.
Tsakanin Dije da wannan Yaro kuwa za ki ce na gaya miki wallahi komai ya riga ya gama wakana sai dai kuma kar a kuma!”
Tana gama fad’in haka ta juya ta shige d’akinta zuciyarta fesss!! Idan akwai abunda take so a duniya to bai wuce ta ga Halima da y’ay’anta sun wulak’anta sun tozarta ba.
Magana Dije ta yunk’ura za ta yiwa Inna Minu ya daka mata wata razananniyar tsawa “wuce ki shige ciki!!!”
Da sauri ta mik’e tana kuka sosai ta shige ciki Hankalinta a masifar tashe ranta a b’ace.
Tana wucewa Mallan ya ce “a kai masa shi d’aki”…..
Tun daga nan Mallan ya rufu a kan Ya Muhammad shi da wani Yaron sa aka kira Likitan bayan layinsu shima ya zo amma ba’a samu Ya Muhammad ya farfad’o ba sai k’arfe sha biyu na dare shima kuma da ihu ya tashi abunda aka fi gudu kenan dan duk lokacin da ya suma ya farka da ihu to sai an yi sama da wata d’aya ana abu d’aya.
Har wannan lokacin su Dije ba su rintsa ba haka wasu jama’ar ma a cikin gidan dan d’aya bayan d’aya suka dinga shiga d’akin Inna suna yi mata jaje tun suna d’ari-d’ari har suka ware suka shiga dannarta.
Kaka ita ma ba ta rintsa ba dan jira take ya farfad’o a gama da shi Dije ta zo ta bar mata gidan d’anta dan ta ce ‘wallahi tunda ta illatata to ta gama zama k’ark’ashin inuwa d’aya da ita.’
Dalilin ma da ya sanya ta d’an d’aga k’afa shine kukan da Mallan ya saka mata..dan suna tsaka da yiwa ya Muhammad add’ua bayan Maghrib sai gata ta zo, ta tsaya ta ce ‘ko Dije ta fita daga gidan ko ita ta tafi,’ shi kuma Mallan dama already hankalinsa a tashe yake ga shi shirun da ya ga Inna ta yiwa Kakar yau ya san definitely akwai matsala a gaba ga Ya Muhammad ya k’i ko da motsi ne shiyasa kawai ya saka mata kuka wanda kukan da taga yana yi ne ya sa ta d’an d’aga masa k’afa ta na jira ya gama ya zo ya same ta a yi ta ta k’are.
Asabe kuwa ta na gefenta in banda famfo ba abunda take yi mata ita kuma tana sake hawa zuciyarta na d’ad’a yin zafi tana ji idan ba ta kori Dije daga gidan ba to ba ta haifu ba kuma ba ta haifa ba……
Musamman ma da ta lissafa ta ga wannan d’in dama ce ta same ta a b’agas da zata yi amfani da ita ta zartar da k’udirinta na shekara da shekaru, shiyasa ta zage dantse ta kuma saka a ranta tabbas ba zata yi sanya ba.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 08.
Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.
Ciki-ciki ya yi sallama ya d’aga labulen d’akin ya shiga. A zaune ya sameta ita kad’ai kamar kullum tana karatun Alk’urani.
Bata kulashi ba shima bai katseta ba bayan ya nemi waje ya zauna kawai sai ya yi shiruuu alamun ya yi zurfi a tunani.
Sai da ta kai aya tukunna ta yi doguwar addu’a sannan ta juyo ta kama kanshi ta shiga yi masa addu’o’i….
Sai da ta ida tukunna suka shafa a tare, daga nan d’akin ya yi shiruuu….bayaga d’azu da suka gama shan azabar karara ta tayasu da addu’a..tun ranar da ya shak’e Mallan idi ta yi masa fad’a bai sake zuwa ya zauna da ita haka ba, sai dai da safe ya shigo ya gaisheta da daddare ya lek’o ya ajjiye mata abunda ya kawo ya yi mata sai da safe ya fita, shiyasa gaba d’aya take a tsorace tana ta addu’ar Allah ya sa bai saka abun a ranshi sosai ba gudun motsawar ciwonsa, shiyasa d’azun da aka kawo mata shi zuciyarta ta kusan bugawa a tunaninta b’acin ranne ya tado masa da ciwon sai daga baya tukunna ta gane ashe azaba ce, sannan sai da ta fahimci abun bai yi k’arfi da tsanani sosai ba kamar last time tukunna hankalinta ya d’an kwanta…..ta san cewa she is selfish tabbas! Amma Ma’aruf shi kad’ai take da shi a duk fad’in duniyar nan shiyasa take tsoron duk wani abinda zai janyo abinda zai rabata da shi…idan akwai abinda take tsananin tsoro shine ta ga ciwonsa ya motsa dan a yadda ya sha da kyar the last time ita kanta ba wai likitoci da suka bada tabbaci ba ta san any mistake to game over ne…….
“Barka da dare Maama”
Muryarsa ta katse mata tunaninta.
Ajiyar zuciya ta sauk’e a hankali ta ce “barka, ya jikin naka?”
A hankali ya ce “na warware”
“Garin yaya karara ya shafeka ne wai?”
Ta yi masa tambayar tana kallonsa, d’an k’uraa mata idanu ya yi kafin chan ya sunkuyar da kansa kawai.
Shiru ta yi ba ta sake yi masa maganar ba suka dasa zaman shiru a cikin d’akin.
Kafin chaan ta mik’e ta je ta d’auko wani ruwa a cikin gora ta k’araso inda yake ta zauna ta bud’e tukunna ta mik’a masa ta ce “gashi, d’azu na lek’a zan baka na tarar ka samu barci.
Ungo karb’i ka sha da bismillah.”
A hankali ya saka hannu ya karb’a, ya yi bismillah ya shiga sha. Sai da ya shanye tukunna ya ce “na gode Maama.”
Shafa kansa ta yi tana murmushi sannan a hankali ta ce “Allah ya k’ara maka lafiya da nutsuwa”
D’agowa ya yi ya kalleta yanzun ma cikin muryarsa mai cike da dakiya da izza ya ce “Ameen” Tukunna a hankali ya d’an matso ya mik’a hannunsa da yake a ta b’angarenta ya rungumota ya ce “fushin ne har yanzu?”
Dan ya lura da yanayinta. Girgiza masa kai ta yi kafin ta ce “tunani kawai nake yi ko sai yaushe Allah zai shirya mini kai! Ina yin addu’a Ina sadaka amma Astaghfirullah har yanzu ban ga wani chanji a tattare da kai ba Ma’aruf”
Ta yi maganar tana mai dag’owa ta kallesa sosai shima itan yake kallo da taimakon hasken kwan fitilar solar da ya mamaye koina a cikin d’akin. Ya jima yana kallonta haka itama kafin chaan ya furzar da huci ya d’auke idanuwansa daga gareta ya ce “a shirye nake, Allah ne bai baki ikon kallona ta fuska mai kyau ba!
A ko da yaushe a baibai kike kallona Maama”
Ya k’arashe maganar yana mai mayar da dubansa gareta.
“Wanne kallo kake tunanin zan yiwa mutum irinka? Ma’aruf kalli jikinka! Kalli yanayin rayuwar da ka zab’arwa kanka kalli mutanen da kake huld’a da su…sannan duk fa yawancin fad’an da ya shafi siyasa sai an ganka a wajen kuma har da kashe-kashe abun yake k’unsa ka kuwa san makomarka Ma’aruf?“
Ta yi maganar muryarta na rawa alamun gab take da fashewa da kuka.
“Mugu d’an daba kawai!!!”
Muryar Dije ta yi flashin cikin kwanya da kunnuwansa kamar yanzun take fad’a.
Cikin rauni d’aci da jin zafin abinda za ta furta d’in ta ce
“A ko da yaushe idan na tuna abubuwan da ka yi kuma na tuna ba ka da mafita ko wayon kare kanka a gaban Ubangiji tare da nauyi da girman zunubin ina shiga cikin matsanancin tashin hankali Ma’aruf! Ka ce min ba ka da laifin komai in yarda da kai na zab’i in yarda da kai d’in sai dai kuma ba ni da hujjar da zan ce gata saboda ita na yarda da kai, Ina ganin kaina ne kawai a matsayin uwa mai tsananin son kai wadda son kanta zai kaita ga halaka saboda ba kai kad’ai ba hatta ni inada nawa kamashon…”
Maganar tata ce ta mak’ale sakamokon kukan da ya ci k’arfinta.
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana jin wani zafi yana taso masa, da kyar ya iya d’aga d’aya hannunsa ya sakata a jikinsa ya rungume, cikin sigar lallashi yake bubbuga bayanta…..
Sun d’an jima a haka kafin chaan! Ya sauk’e wani nannauyan numfashi ya ce “ga balangu nan, na wajen Ganaye, wanda kika fi so.”
Ya k’arashe maganar da d’an murmushi a kan fuskarsa.
Ta riga ta san maganar ce baya so kuma tunda ya sako wata to an bar wacchan kenan har abada.
Kallon ledar da ya mik’o mata ta yi kamar kullum ta ce “a ina ka samu kud’in”
Murmushi ya yi kafin ya ce “ta hanyar halal, doyata dana gaya miki mun noma a Niger ita aka siyar”
Cikin tarar numfashinsa ta ce “an dad’e fa ana baka kud’in doyar nan Ma’aruf…”
Numfashi ya fesar sannan ya ce “sun kusan k’arewa saura kad’an bai kai dubu ashirin ba ma”
Daga nan ya yi shiru kamar mai tauna abin da zai fad’a kafin ya ce “Sana’a zan fara da kud’in da wanda na baki ajiya, in sha Allah”
Wani irin zabura ta yi sai kuma ta fara murmushi mai had’e da dariya kafin ta gyara zamanta tukunna ta yi sujjada.
Murmushi sosai shima ya yi wanda idan ba yana tare da ita d’in ba to ba za ka tab’a gani ya yi ba.
Bayan ta d’ago ta gyara zamanta cike da farin ciki ta kamo hannunsa ta ce “Allah ya dafa maka Allah ya taimake ka Allah ya sa ka fara a sa’a”.
A hankali ya ce “Ameen…..”
Ana fitowa daga masallacin sallar asubah Mallan da Minu da wasu samari a gidan guda biyu Ya Kamal da Ya Musa suka tafi kai Ya Muhammad asibiti
dan zuwa wannan lokacin jikin nashi ya yi tsanani sosai.
Tunda suka tafi Inna take kuka gashi ta cewa Dije ko inda ta ke kar ta kalla ballanta ta yi mata magana….sosai ta bawa mutanen gidan tausayi yayinda wasu suke ta jin dad’i kar ma Kaka da Asabe su ji labari.
Sai wajajen k’arfe goma tukunna Mallan ya amsa wayar Inna ya ce mata ‘jikin da sauk’i an d’an samu kansa yanzu haka an yi masa allurar barci baccin yake yi, ga Minu za su dawo tare da su Ya Kamal, ta bashi karin kumallo ya kai akwai maganin da dole sai ya ci abinci tukunna zai sha’
Da “to” ta amsa tana ta jera hamdala ta mik’e ta nufi kitchen, tana shiga ta tarar da Dije tanata jefa d’anwake.
Yi ta yi kamar ba ta ganta ba kawai ta juya ta fice a kitchen d’in.
A hankali kwalla ta shiga zirya saman kyakkyawar fuskarta dan idan akwai abinda bata so a duniyar nan to shine Inna ta yi fushi da ita, gaba d’aya ji take yi duniyar ta tsaya mata chak….Inna bata saba yin fushi da ita ba shiyasa a duk lokacin da ta yi take jin jiki.
Sai da ta gama jefa d’anwaken tass tukunna ta d’an zuba mai a kasko ta rufe ta ajjiye roba ta je ta d’ebo ruwa shima ta ajjiye tana jira ya gama ta kwashe.
Ganin zai d’auki lokaci ya sanya ta mik’e ta fita ta wuce d’akinsu domin ta je ta d’auko albaasa yadda tana sauk’e d’an waken sai ta d’aura man, dan rushon gawayin su ya samu matsala, da abin girki d’aya suke amfani kwana biyu.
Tana fita dede Asabe tana fitowa daga band’aki, ita Asaben ta ganta amma sam Dije ba ta ganta ba da yake baya ta bata.
Kwafa Asabe ta yi dai-dai Dije ta shige d’akinsu, ta san ta tsani Halima kuma tana kishinta amma zuwa yanzu tabbas tsanar Dije tana shirin kere ta Halima a cikin zuciyarta, sosai take jin zafin Yarinyar…tana k’arasa fitowa tsakar gidan idanunta suka sauk’a a dede wajen da ta zo ta tarar da gawar akuyarta wanda Maman Fati ta tabbatar musu aikin Dijen ne, wani irin tuk’uk’i ne ta ji yana taso mata..Kaka ta ce kar ta yi mata magana zata yi maganinta ta hanyar sakawa a koreta a gidan amma shiru yau ma gashi har ta kwana ta hantse babu alamun zata bar gidan!..
Kitchen d’in ta juya ta kalla ta ga tukunyarsu a kan murhunsu wuta tana ta ci, ba ta yi wata-wata ba ta afka cikin kitchen d’in zuciya tana cinta ta shiga ta lek’a cikin tukunyar…
K’urawa d’anwaken da yake ta tafasa ido ta yi, tana cikin tunanin me zata yi masa ta lalatashi idanunta suka sauk’a a kan uban ruwa k’anwa kusan cikin babban kofin sha biyu a cikin wata babbar roba, da sauri ta d’auka ta juye duka a ciki har da k’asa k’asar ba ta rage komai ba, hankalinta bai kwanta ba ta sake d’aukar gishiri shima ta juye a ciki ta saka ludaye ta juya sasai kamar mai burge miya sannan ta mik’e ta juya za ta fita suka ci karo da Dije.
Wani Irin tururin wutar bala’i ce take taso mata amma ta danne da mugun kyar dan ko saboda Ya Muhammad ba zata yarda ta kula kowa a gidan ba yau!
Tsaki Asabe ta yi tana jira Dije ta tanka ta ita kuma ta tada bala’in da kowa sai ya ji ko dan a sake aibanta Dijen amma ga mamakinta sai ta ga Yarinyar ta wuceta ta d’auko tsumma ta d’auki tukunyar d’anwaken nata ta fice ta nufi bakin rijiya.
Da kyar ta samu kaso biyu a cikin ukun d’anwaken da ta jefe shima kuma duk ya yi laushi, dan kanwar mai k’arfi ce sosai hakan ya sanya d’anwaken zagwanyewa…
Tana cikin wankewa Minu ya yi sallama, ya k’arasa ya ce mata ta yi sauri ta had’a abincin y’an asibiti yanzu zai juya Musa yana wajen yana jiransa a napep d’insa.
Da “to” ta amsa ta koma kitchen d’in da sauri ta d’aura mai sannan ta d’auko flask ta fito ta ci gaba da had’a kan d’anwaken.
Sai da ta gama tukunna ta nufi kitchen d’in domin ta zuba mai ta kammala komai.
A kitchen d’in ta samu Sagir da Kubra yana tayata tsintar wake suna hira suna dariya, ba ta ko kalli inda suke ba dan ta tsani Sagir tun ba yau ha tunda ta fahimci d’an iska ne ya fice mata a rai gashi uwarsa ba ta son laifinsa.
Mahaifiyar Kubran ce ta kirata dan haka ta tashi da sauri tana cewa “Na’am” ta fice daga cikin kitchen d’in.
Tsaki Dije ta yi ta rasa dalilin da ya sa ba za a kafa dokar hana maza shigowa kitchen d’in gidan ba fisabilillahi da hijab mutum zai ji ko da zafin kitchen d’in da ko windo d’aya babu, musamman ma da rana idan kowa ya kunna murhunsa kitchen d’in sai ka ji kamar oven ga uban hayak’i na masifa!
So take yi ta koma d’aki ta d’auko hijab d’inta amma kuma ta ji ya Aminu ya ce ta yi sauri gashi ba ta so ta sake yi musu wani laifin dan haka kawai sai ta ware d’ankwalin kanta ta d’an yane jikinta da shi dan ta lura Sagir d’in bashi da niyyar fita kuma dukda bata juya ba tana jin yadda idanuwansa suke yawo a jikinta.
Rigar bacci ce a jikinta amma cotton kuma hannunta d’an dogo ne dan ya kusan rufe guiwar hannunta ma, sai zani da ta d’aura a kan rigar baccin nata da d’ankwalinsa, rigar baccin loose ce amma da ikon Allah ta fito da albarkatun k’irjinta sosai haka nan shima zanin normal ta d’aura shi amma k’ugunta ya fito sosai tubarkallah.
Tsabar yadda Sagir yake sake lek’ata yana kallonta har d’an zillo yake yi daga nan zaune kan kujerar inda yake idanunsa kamar zasu fad’o k’asa, ga ta dai a gabansa amma da ikon Allah lek’e yake yi ko mai zai gano
oho!.
Ya Aminu ya fito kenan daga d’akin Inna zai zubawa kajin sa abinci ya ga mutum yana zillo shi kad’ai a kan kujera, da ke Dije tana daga chan ciki shi kuma yana a bakin k’ofar shiyasa bai ganta ba ya gansa shi kad’ai.
Da mamaki ya k’arasa bakin kitchen d’in idanunsa a kan Sagir wanda bai ma san ya k’araso ba.
Dai dai Dije ta d’an tsugunna a kan k’afafuwanta tana k’ok’arin rufe flask d’in da ya k’i rufuwa wanda tsugunnawar da ta yi ya taimaka wajen sake fito da hips d’inta ta gefe da gefe.
Wani irin murmushin iskanci ya ga Sagir d’in ya yi har da wani fito da harshe ya na sid’e Baki.
Da sauri ya juya ya kalli Dije wadda ita ba ma ta san yana yi ba Allah Allah kawai take ta gama ta fita ta bar amsa kitchen d’in.
Wani irin takaici da bak’in ciki ne suka lullub’e Minu a lokaci guda, bai san lokacin da ya juya ya zaro tsinken tsintsiyar kwakwar da
aka jingine a wajen ya tsole masa ido ba!
Dai dai Mahaifiyar Sagir d’in ta fito….abun ya faru a kan idanunta dan haka ta k’arasa cikin sassarfa tana rafka salati da k’arfi wanda hakan ya yi sanadiyyar fitowar mutanen gidan daga cikin d’akunansu.
Tana k’arasawa ta rufe Minu da duka….
Matar ta tsufa sosai ya san ko yunk’urin hana ta ya yi tsaff zata kife a wajen shiyasa kawai ya rabu da ita ya saka hannunsa ya kare jikinsa ita kuma tana ta dukansa tana kuka tana cewa “Wallahi idan wani abun ya samu idon Sagir sai na yi shari’ah da kai. Mugu kawai shegen Yaro”
Inna ba ta so shiga sabgar kowa ba yau amma duk yadda ta so sai abun ya gagareta, dan haka ta tashi ta fito fuskarnan a had’e tamau kamar ba ta tab’a dariya ba.
Ba su san ta k’araso wajen ba sai da ta shiga tsakanin Minu da matar ta rik’e mata hannu tukunna.
Murya cike da b’acin rai ta ce “Ana barin halak ko dan kunya, fisabilillahi ko me ya yi miki kuma ko me ya faru ai bai kamata ki dinga d’aga murya kina sheganta mini Yaro ba! A gidan ubansa fa kike haya.
Yanzu kuma idan na saka baki sai ace na cika fad’a a ga laifi na bayan kune kuke shiga sabgata.”
Har da d’an gudu gudu Kaka ta fito ta ce “ai tun jiya na gaya miki ki nemo ubansu ba dai d’ana ba dan haka ki daina wani hak’ilo kina ik’irari…”
Cikin katseta sannan a tsawace Inna ta ce “Dakata malama ban sako da ke ba! Ko kinga na tanka ki tun jiya? Kina so ki san dalili?”
Ba ta jira ta bata amsa ba ta ce “saboda maganarki ba ta kai in tsaya in sakata a mizanin hankali ba shiyasa, in da ace maganar mutane masu hankali kika yi da sai in saurareki amma ba ni da lokacin shirmenki ne shiyasa ban biye ki ba kuma duk mutum mai hankali ba zai biye miki ba ko kinga shi Mallan d’in ya biye ki?”
Nan ma bata jira me zata ce ba ta ce “saboda ya san me yake yi. Jakai, dak’ik’ai sannan munafukai sune suke biye ki suke bawa zancenki mahimmanci.
Ni nan kin ganni tunda har ba Mallan ne da kansa ya furta wannan zance ba to idan kinga dama Hadiza ki d’auki loudspeaker kina bi layi layi kina fad’a wallahi ko a jikina.”
Ta k’arshe maganar tana dukan cinya cike da bala’i.
Kuka Kaka ta fashe da shi ta juya ta shige cikin d’aki tana cewa ‘ko uwar da ta haifeta ba ta kiran sunanta saboda sunan mahaifiyarta ne amma yau ga suruka ta ambaci sunanta bayaga kiranta da mahaukaciya da ta yi, wallahi ba zata zauna ba bar musu gidan za ta yi yau za’a yi ta ta k’are Mallan sai dai ya zab’a dan wallahi ta gama zama gida d’aya da su Dije.’
Asabe da Maman fati ne suka bi bayanta suna rarrashinta yayinda Inna ta doka wani uban tsaki ta juya kan Maman Sagir ta ce “ke kuma me Minu ya yi miki? Wadda ba ta san alkhairi ba!”
“Ya kike magana kamar wadda ta ba ni waje na zauna a kyauta? Haya fa nake yi?…”
Cikin katseta Minu ya ce “Anty ki yi hak’uri a bar maganar nan, Inna dan girman Allah kema ki yi hak’uri ki kyaleta ya wuce.”
Cikin fushi Maman Sagir d’in ta ce “eh ai dole ka ce a bar magana tunda mu ka cuta, to wallahi ba ka isa ba! Dole a biwa Yaro hakkinsa.”
Ta fad’i haka tana Isa kan Sagir wanda zuwa yanzu ya ware daga mutstsika idon da yake yi amma yana nan zaune a inda yake kawai yana kallon Minu irin a fusace yake da shi d’innan.
Duddubashi ta yi kamar wani k’aramin Yaro tana dubashi tana cewa “ya idon naka? Kana gani sosai?”
Jinjina mata kai kawai ya yi, ba ta d’ago ba ta ce “Shege mugun Yaro haka nan kawai zai janyo maka, ido ai ba abun wasa bane….”
Wata mahaukaciyar fisga Inna ta yi mata ta juyo da ita sannan ta ce “na rantse da mahalliccina ko da wasa idan kika sake shegantamin Yaro da k’azamin bakinkin nan sai na tsinka miki mari!!!”
Da sauri Sagir ya taso ya zo ya tsaya a gaban Inna fuska a had’e ya ce “cikata!!”
Sake damk’eta Inna ta yi ta kallesa cikin fushi ta ce“ba zan cikata ba dan kutumar ubanka!!!!”
Yunk’urawa ya yi zai yi kan Inna Minu ya yi wani irin jifa da shi a fusace ya ce “kar ka soma! K’aramin mahaukaci”
Ai kuwa a take gidan ya hargitse dan Sagir sake tasowa ya yi Minu kuwa ya rufesa da duka dama a fusace yake.
Da kyar bayan mazan gidan sun shigo suka samu suka kwaci Sagir daga hannun Minu amma fa ya daku dan har ya fasa masa saman ido da hanci da baki.
Sai da Iyya ta zo itama da kyar tukunna ta lallab’a Inna ta cika uwar Sagir wadda take ta fisge-fisge amma ta gagara kwatar kanta daga hannnun Innar.
Ana cikata ta yi kan Sagir tana mai fashewa da kuka kafin ta d’ago fuska dagaje dagaje ta fara jero ‘Allah ya Isa’
Ya Kamal ne ya ce “mai ya faru?”
Ya yi maganar yana kallon Minu.
Banza Minu ya yi da shi yana huci sai da ya sake cewa “Mai ya faru?” Iyya Mahaifiyarsa itama ta cewa Minun “mai ya faru” tukunna ya ce “Kama sa na yi yana k’arewa Dije kallo ta juya baya, shine na tsole masa ido…”
Daga nan kawai ya yi shiru.
Kwashewa da dariya Ramma ta yi ta ce “Allah ya kyauta” daga haka ta juya ta wuce ciki.
Yayinda Asabe wadda fitowarta kenan daga d’akin Kaka ta k’araso wajen ta ce “amma wallahi ka ji kunya Minu!
Saboda an kalli k’anwarka?”
Cikin zafi Maman Sagir ta taso ta ce”kuma ina ita k’anwar tasa ita ce ta fito babu mayafi?
Allah na tuba Yarinya ragowar d’an daba ta gama karuwancinta komai ya fito rass ai dole Yaro Namiji mai lafiya ya kalla.”
Ta fad’i maganar idanunta jazur cikin na Inna cike da b’acin rai!
Dariya Asabe ta yi kafin ta ce “maganar ki dutse.”
“Eh
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 23