komai as sirri kar su bari kowa ya ji duba da yadda ake ta kawo mata tallar Yara ita kuma bata da vacancy dan haka hatta passports d’in duk su b’obb’oye kar su nunawa kowa.’
A take suka amince suka rik’e sirri Gwaggo hatta Ya Musa bata nunawa passport d’in Mariya ba, ba abunda idan ta tuna yake yi mata dad’i kamar yadda itama zata d’ago a cikin danginsu, saboda a halin da ake ciki yanzu haka ba’ayi da ita da y’ay’anta a danginnasu saboda bata da shi ko zumunci da ita ba a yi sam amma ta san yanzu idan ta kud’ance ta fara yin anko suka ga tana shiga tana fita tsaff zata shige cikinsu ta yi blending in….
Su Rakiya da su Fati suma tunda aka jaa musu kunne suka jaa bakinsu suka yi gum, hatta Kubra wadda ita uwarta sam abun bai shiga kanta ba basa maganar da ita, haka nan suke abinsu komai a sirrance, Fati ita wata biyar zata yi kawai ta dawo saboda Babanta bai sani ba dan haka kafin ya dawo zata je ta taro abinda ta tara ta dawo.
Mariya kam tata uwar ta ce sai dai ta dinga zuwa ganin gida ko ita a je mata, sai su Rakiya waenda uwar su ta ce ‘sai
sun kama Miji a hannu tukunna za su dawo’.
Duk wannan abun da akeyi Rakiya tana nuna musu kamar babu komai ne amma hanya kawai take nema da zata bi ta dak’ile zuwan su Mariya kawai take yi, dan har ta fi Ramma k’in son su je, wadda ita dama dan kar a ce Fiddausi ta zauna ne ya sanya take againsting yayinda ita kuwa Rakiya zallar hassada da bak’in ciki ne suka sanya take againsting zuwan nasu.
Mama ta so an had’a da Dije harma da Kubra dukda kuwa idon Kubran akwai matsala amma ta san hakan ba problem bane ba dan daga gani yana gama warkewa ma zata fara gani da shi tarr abinta….dan duk sun fi ragowar kyau da shiga rai amma kwata-kwata duk da zancen ya je kunnuwansu sun ji ta buga sunayensu a jikin k’asa sam abun ya gagara kama kan iyayensu da su kansu Yaran har gara ma Kubra tana so itama
sosai dan tun rasuwar Sagir dama take son barin Gidan uwarta ce ta hana, Dije kuwa ita da Inna kamar ana rubutu akan ruwa.
Ita Mama bata san rashin lafiyar Mallan ne ma ya dakatar da Inna daga sakawa a koreta daga gidan ba talkless of ta d’auki y’a ta bata, gashi har yanzu duk zancen tafiyar da ake yi Allah bai saka ta ji ba, dan Sumayya ko zancen ma bata son yi saboda gudun tabbatuwar abun, dan yadda ta tsani tafiya aikatau d’innan da ake shirin kaita haka ta tsani mutuwarta.
Sai bayan kwana biyu tukunna Kawu Isa ya zo, ya fake da ‘neman Ma’a ne ya sha masa kai’ wai ‘abun ba sauk’i amma akwai alamun nasarar cafkesa kwanan nan.’
Ita dai Inna “Allah ya taimaka” kawai ta ce masa daga nan suka juya suka tafi shi da su Kaka waenda suma sai a ranar ne tukunna suka je ganin Mallan d’in…bayan sun tabbatar sun gama duk wani kulle-kullensu komai ya tafi musu normal tukunna suka samu lokacin zuwa, wanda ba k’aramin dad’i suka ji ba da aka ce musu ‘ba’a buk’atar mai jinya a wajen itama Dije nacinta ne ya sanya take kwana a waje wani zubin har da Sumayya wadda zuwa yanzu itama uwarta kawai ta zuba mata ido dan ta gagara rabata da Dijen, sannan da ta tuna tafiya ma zata yi kwanan nan sai kawai ta rabu da ita.
Washegari da sassafe Dije ta lek’o gida dan ta jima bata zo ba tun ranar da aka kwantar da Mallan a icu, gashi Inna ta ce mata ta zo yau ta d’an ci abinci ta huta sai su koma tare anjima, dan haka bayan ta tabbatar Likitocin basa buk’atar komai ta lek’a Mallan d’in shima sai kawai suka kamo
hanyar gida dama da kud’in motarsu a hannu tun jiya Inna ta basu.
Tana shigowa cikin gidan ta tarar da tsakar gidan a cike an yowa Rakiya rakkiya.
Ita kuma sai wani d’add’aga hanci take yi tun bata kai ga shiga jirgin ba.
Ita dai bata kula su ba ta yi wucewarta ciki dan indai suka had’u da y’an matan k’asa-k’asa take ji suna kiranta da Annoba ko Mujiya.
Sosai abun yake damunta ga kuma matsanancin tashin hankalin da take a ciki kwana biyun nan..bata da lafiya sosai tana yawan yin ciwon mara, sai kuma kotu da ta ji k’ishin-k’ishin d’in Kaka su Kubra da Maman Sagir suna shirin kai Inna (a bakin Sumayya)
Maman Sagir dai ta san a kan kisan Sagir ne wanda shima
ba ita ce ta yi ba, Kubra ta san akan idonta ne sai dai bata san me ye dalilin kai Inna kotu da Kaka take shirin yi ba.
Wasu zafafan hawaye ne suka taho mata a ranta ta ce “watak’ila saboda kasancewata Annoba kuma ta k’i tsameni a cikin jama’a shiyasa suke son kotu ta rabamu.”
Tana shiga d’akin ta yi saurin goge hawayenta ta durk’usa har k’asa ta gaida Inna ta amsa mata tana kallonta wanda kallo d’aya ta yiwa Innar ta fahimci itama kuka take yi.
Cike da son basarwa Innar ta yi saurin sako magana “ga abinci nan” sai kuma ta yi shiru ta gagara cewa komai.
A hankali Dije ta kawar da kanta bayan ta ce “tam” tausayinsu yana dad’a lullub’eta kafin ta mayar da dubanta ga Ya Muhammad wanda tun shigowarta ya k’uraaa mata ido kamar mai son tuna an ina ya santa.
Da sauri ta sunkuyar da kanta bayan ta ce masa “Ina kwana” tana mai goge hawayen da suka zubo mata, a ranta ta ce “Tabbas wannan ma duk laifina ne”
Inna ta ga yadda ta ke sharar hawaye kuma ta fahimceta sai dai ba ta ce mata komai ba dan kwata-kwata bata da abun fad’e.
A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa itama kafin chaan ta d’ago ta ce mata “ya na ganki ke kad’ai? Ina Sumayyar?”
“Ta wuce gida, ni na ce ta tafi bacci take ji jiya bamu yi barci ba.”
Jinjina kai Inna ta yi dan dama a yadda ta ga wajen jiya ta san ba lalle su iya rintsawa ba ita kanta bata runtsa ba dama kuma ga damuwar da suke ciki, Gawarwaki tara aka fitar kuma tsakanin ko wacce baya kai tazarar awa d’aya.
Dan haka kawai sai ta yi shiruuuu tana kallonta, kafin kuma ta fara nazartarta a hankali……wata k’ilan ko idanunta ne amma haka kurum sai ta ga Dijen tanata d’ashewa kwana biyun nan, kamar wata mai Yaron ciki!!!!
Da wani irin masifar sauri Inna ta mik’e ta yi gaggawar kawar da tunanin daga kanta ta fice wanda hakan ya tsorata Dije dan yanayin na Inna babu alamun lafiya a tattare da shi.
Mik’ewa itama ta yi ta fita ta hango Innar ta shige cikin band’aki dan haka ta jaa ta tsaya a bakin k’ofar d’akin nasu ta hau tunani ita ta ma manta a waje ta ke.
Har aka gama yiwa Rakiya sallama Ya Musa ya tafi
kaisu airports ita da Mama
itakam Dije ba ma ta san sun tafi ba.
Rakiya sai bayan wata d’aya zata dawo Mama kuma a gobe ta ce musu zata dawo, a nan hannun Ramma ma ta bar y’arta Saddik’a k’awar Zainab da Fiddausi dan tare suke yanzu k’ut da k’ut.
Tunda Dije ta fito Kubra take kallonta tana sake maimaitawa
Ita a halin yanzu haka ta yi mata Illa ta lalata mata ido guda d’aya ta kumbura mata fuska amma kalli ita har wani fari ta yi ta d’ashe kamar wata sabon shigar bleaching.
Gashi ta rabata da Sagir d’inta forever……..
“Su o’o fa an zama musulma magana ma
an daina daga kuka sai salati”
Muryar Mariya ta katsewa Kubra lissafin da take yi a kan Dije.
Dariya Fati ta yi kafin ta ce “Wanne Irin musulma? Abunda ya fi k’arfinta dai ta je ta tonu, gashi ta zama Annoba, Mujiya abar gudu. Allah na tuba ace hatta Mahaifin mutum bai tsira daga masifar ka ba ai ka zama abun gudu. Ni kam ai an gama danganta shi da asibitin dan haka ya kamata Kaka ta taimaka ta zo ta fitar mana da masifa daga cikin gidan…..”
Dai-dai nan Inna ta fito daga bayi dan haka Mariya ta had’iye ragowar maganganunta.
Ita kam Inna bama ta ji su ba dan hankalinta ya gama kai k’ololuwar tashi!!!
Bata son jin abun tashin hankali shiyasa wallahi har yau ta gagara yiwa Dije maganar komai game da zuwanta d’akin Ma’a, ita dai ta san ta yarda da ita d’ari bisa d’ari sannan ta kasa yarda akwai wani abun da ya shiga tsakaninta da Ma’a a wannan ranar dukda kuwa ga shaidu nan birjik!
Amma kawai sai ta zab’i ta bi abunda zuciyarta take gaya mata sai dai kuma wannan al’amari da yake shirin kutso kai tabbas yana gab da tarwatsa duk wani sauran kuzari da jarumtarta….
Tana wannan lissafin ta zo ta wuce ciki a rikice wanda sam
Ita Dije ba ma ta san ta fito ta shige ta sake fitowa ba.
“Dije”
Ta ji muryar Inna a kanta da d’an k’arfi dan wanna kira na biyar kenan da ta yi mata.
Firgigit ta yi ta waigo ta kalleta wanda hakan ya sanya Inna ta ji wani kalar zazzafan tausayin Yarinyar ya lullub’eta dan da hawaye ta juyo mata wanda ta san ita a karan kanta ba ta san da cewar kukan take yi ba. Gashi kallon da ta yi mata yanzu a cikin hasken safiyar ya sake assasa mata zargin da take yi game da ita
Da kyar Inna ta hana kanta kuka ta daure ta dake ta bata kud’i tare da wata takarda ta ce “Ungo, je ki chemist ki siyo ki kawo min yanzu.”
Dai-dai da fitowar Asabe.
Tab’e Baki ta yi ta ce “shi fa rigakafin k’anjamau tun a ranar da aka yi zinar ya kamata a yi!!!”
Sai kuma ta tsaya ta kama k’ugu tana kallonta.
A ranta ta ce “har da wani mayar da kaya cikin d’aki ko? Za ma ku fito da su ne in sha Allahu”
A hankali Dije ta karb’a ta ce “to Inna”
Daga haka ta sa kai ta fice.
Itama Innar juyawa ta yi ta koma cikin d’akinta ko uffan bata cewa Asaben ba wanda hakan ya bata mamaki ya kuma bak’anta mata rai.
A jiya cikin dare suka so su koresu, amma sai mai unguwa ya hana ya ce, su bari Malan ya d’an ji dama-dama in sha Allahu shi da kansa zai san yadda zai yi ya aurar da Dije ko
kuma ya sallameta dan ta zama Annoba kam tabbas zamanta cikin al’umma bala’i ne. Amma Idan ita ko uwartata wani ya b’ullo da rikici to su zo su sameshi zai san abun yi a yau ba sai gobe ba.
Da ido Kaka wadda ta fito itama a yi da ita ta yiwa Asabe alama akan ta rabu da ita kawai, dan sun d’ana mata tarkuna da yawa tarkunan da dole sun san sai ta kulasu.
Mik’ewa Kubra ta yi da sauri! Ta afka cikin d’akinsu yayinda Mariya ta mik’e itama ta bita a baya da niyyar sanar mata da plan d’in da suka had’a ita da Asabe kawai ta ji Kubran tana cewa “Allah Mama zan iya da ita ki bar ni kawai wallahi ba ta Isa ta illatani ita kuma ta sha ba”
“A’a fa! Ki zauna na ce miki, Yarinyar da ta nakastaki da sauran k’arfinki da idanunki biyu ita zaki bi? Na ce ki bar ni da su kotu zata yi mana alk’alanci kar ki je ta k’arasa makanta ki gaba d’aya.”
Cikin b’acin rai Kubra ta ce “Mama kafin ma a yi zaman farko a kotu balle a kai ga kwatar mini hakk’ina Allah na san Dije ta sha, Yarinyar da ake shirin kora daga unguwar idan ta tafi muka san Ina zata je???”
Wani kalar sanyi Mariya ta ji, saboda dama har ga Allah tana d’an shakkar aiwatar da plan d’in nasu ita kad’ai duk da kuwa ta ga yadda Dijen ta yi sanyi amma a wannan sanyin da ta tab’a yi ne ta jiwa Kubran rauni, dukda kuwa wanchan bai kai wannan ba amma dai tana jin tsoro ita kam. Gashi Asabe ta ce kar ta sako Fati ita da uwarta duk munafukai ne tsaf za su iya zagayewa su sanarwa Inna a hana Dijen fita……
Sallama ta yi ta kutsa kai wanda hakan ya sanya duk su biyun suka yi shiru, Kubra ta juyar da fuskarta tana sake kumbura kumburarriyar fuskarta.
K’arasowa Mariya ta yi ba tare da b’ata lokaci ba ta sanar musu komai.
Sannan ta d’aura da cewa
“tun shekaran jiya dama muke ta addu’ar Allah ya kawota unguwar. Dan haka Mama kar ki wani damu dan Kubra ba ita kad’ai bace a fad’an muna tare da ita.
In sha Allah a yau sai mun saka ta bar Unguwar da kafafuwanta dan sai mun wulak’antata bayan mun ji mata rauni itama kamar yadda ta yiwa Kubra…….
BULAMA ✍️
0806 402 1951
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 23