Share this page
ya bita ya ga ta tsayar da abun hawa ta fad’a masa inda zata je ta shiga, tukunna ya koma ciki ya na mai gwada layin Ma’a wanda tunda ta fito ya fara k’ok’arin kiransa amma tun lokacin layinsa engaged. Da niyyar zuwa gidansu ya fita domin ya taho mata da ko da Minu ne dan ya lura a mugun tsorace take da shi wanda hakan ya sanyashi dana sanin abubuwa da yawa a karon farko na rayuwarsa. Yana fita kiran Maama ya shigo cikin wayarsa, dan haka ya amsa…. “Ka zo yanzunnan” ta ce da shi cikin sheshshek’ar kuka! Sai da gabansa ya yanke ya fad’i kafin ya ce wani abun ta kashe wayar. Gudu-gudu sauri-sauri ya k’arasa bakin titi, dan already ya aiki Grenade da motar da suka taho da ita ta dpo. Napep d’in da ya tarar akwai mutane a cikinta amma haka ya fincikosu ya watsar ya shige suma kuma basu yi yunk’urin yin komai ba saboda yanayinsa da suka gani. Shi kansa mai Napep d’in a tsorace yake da shi dan haka ya dage ya dinga tsula uban gudu kamar yadda Ma’a d’in ya umarcesa. Yana shiga cikin gidansu tun daga soro wajen d’akinsa ya fara jiyo muryar wata mata tana cewa “to ni dai bari in yi sauri in tafi kafin ya zo, dan ya saka mana dokar zuwa cikin gidannan kamar yadda na gaya miki yanzun. Kuma wallahi ya kula da kanshi dan wannan karon kam ba zamu yarda ba” Kuka sosai Mama take yi yayinda matar take k’ok’arin saka slippers d’inta dan haka duk basu lura da Ma’a wanda ya shigo a zuciye zuciyarsa tana wani irin tafarfasa ba. Sai da matar ta gama saka slippers d’inta ta d’an yo gaba kawai ta ji ta k’ume da k’irjinsa gab! Kamar wani dutse ko motsi bai yi ba amma idanuwansa kad’ai idan ka kalla sun isa su gigita ka. Inda-inda ta farayi ganin yadda ya kafeta da idanuwa sai kuma ta fashe da kuka kawai tsabar tsoro..ta durk’usa a gabansa tana kuka wiwi tana cewa “ka rufa min asiri inada jikata guda d’aya ni kad’ai gareta bamu da kowa idan ka kasheni za ta tagaiyyara” Wata mahaukaciyar shak’a ya yi mata ta mik’e tsaye ganin yadda take sake ruru wutar tsanarsa a idanun Maama, yana d’agota bai yi wata-wata ba ya d’auke ta da wani Irin mahaukacin gigitaccen Mari dama tun d’azu a k’ule yake ga kuma Dije da ya fahimci ita tsoronsa ma take ji yanzu kuma ga Maama. Matar tana zubewa a wajen dai-dai Maama itama ta durk’ushe ta fashe da wani irin gigitaccen kuka! Jikinsa ne ya hau karkarwa ya yi kan Maama zai rik’eta ta mik’e ta fara jaa da baya tana cewa “Ashe har yanzu zalincin naka yana nan Ma’aruf? Ashe har yanzu baka daina kashe mutane ba? Ashe har yanzu zuciyarka babu Allah? To wallahi tallahi bari ka ji in gaya maka da kaina nan zan mik’a ka ga hukuma in yaso sai in ga uban da zai kwatoka! Ma’aruf a gaban uwa ka kashe mata d’anta! Ya kake tunanin zata ji? Ya kake tunanin zan ji idan wani ya kashe mini kai a gaban idanuna????” A hankali ya sake tunkararta hankalinsa a masifar tashe ta ce “kar ka matso kusa da ni!!” Cikin tsawa sannan ta ce “babu ni babu kai daga yau! Ka ji abunda na fad’a maka ko baka ji ba??? A da Ina tunanin har da sharrrin K’uruciya da zafin abunda ya faru da kai ne sanadi hakan ya sanya na nad’e hannu na yafe maka b’arnar da ka yi a baya nake nema maka sassaucin azabar girman zunubinka a wajen Ubangiji amma yanzu kam baka da wani excuse Ma’aruf!! Kuma bari ka ji in gaya maka ya zama dole ka amsa laifukanka kuma a hukunta ka ko da kuwa hakan yana nufin zan rasa ka ne! Idan ka kasance d’an daba wannan zan iya yi maka addu’a idan ka yi kisan kai a lokacin k’uruciya wannan shima zan iya d’aga maka k’afa amma bazan zama selfish in nad’e hannu in zauna Ina gani kana kashe rai da hannayenka ba! An yi an gama ta faru ta k’are!!!”. Wani irin mahaukacin karkarwa jikinsa ya shiga yi yana jin wani kalar birkitaccen tashin hankali yana dad’a bijiro masa. A hankali ya matso kusa da ita wannan karon kam ihu ta yi jikinta ya na karkarwa idanunta jazir! Ta ce “na ce maka bana so ka tab’a ni ko? Ba na son ganinka!!!” A hankali ya runtse idanunsa ya d’auke numfashinsa na wasu y’an sakanni sannan ya saki yana jin tashin hankalin da bai tab’a jin kwatankwacinsa ba. Juyawa ya yi da niyyar cin uwar matar nan ko ya samu ya huce ya hangota dai-dai tana fita daga gidan… “Sannan na baka mintuna ashirin ka dawo da Yarinyar da ka yi Garkuwa da ita gidan iyayenta” Cike da rashin fahimta ya juyo yana kallonta dai-dai nan kiran Scorpion wanda yake ta yi masa babu k’ak’k’autawa ya sake shigowa cikin wayarsa dan haka ya amsa yana shirin yin magana a fusace ya ji Scorpion d’in ya ce masa ‘suna waje, yana son ganinsa.’ A k’ule ya ce “ka tabbata ka tare min matar da ta fito daga cikin gidanmu yanzunnan.” Yana gama fad’in haka ya kashe wayar ya d’ago zai yiwa Maama magana ya ji ta d’aukesa da wani irin gigitaccen Mari. Cikin mad’aukakin b’acin rai take magana tana kuka “idan suka tare maka ita kasheta itama zaka yi? Ma’aruf ina yi maka magana amma still kana cin k’asa? Ya kake so in yi? Ka san me nake ji kuwa? Da wanne kake so in ji? Ka san ya nake ji idan na tuna ni da kaina zan mik’a ka ga hukuma kuwa?” Ta k’arashe maganar tana mai durk’ushewa a wajen ta sake fashewa da wani irin kuka. Sosai ya dunk’ule hannuwansa yana jin wani kalar zafiii a k’irjinsa, tabbas idan bai sumar da matar da ta kawowa Maama zancensa ba yau to bai cika d’a ba. D’urkusawa ya yi zai yi mata magana ya kai hannu zai tab’a ta ta yi sauri ta buge masa hannun cikin zafi ta ce “na ce ka je ka kawo musu Yarinyarsu kafin a zo a tafi da kai” Tunda ta fara magana shi har ga Allah sai yanzu ya fahimci Dije take nufi. Cikin matsananciyar kasalar da take taimakawa wajen danne b’acin ransa ya ce “Maama ban yi garkuwa da kowa ba! Dije ce ta suma d’azu kuma ba zan tab’a iya tsallaketa in tafi in barta a wannan halin ba, shine na kaita Asibiti” Cikin tarar numfashinsa ta ce “k’arya kake Ma’aruf” Sai kuma ta yi shiruu kamar mai tunani kafin ta d’ago ta kallesa ta ce “kar ka ce min Dije ta wannan Unguwar wannan layin itace Yarinyar da kake so za ka aura, dan ko da ace Allah ya dubeka ka tsallake ba a kasheka ba wallahi baza a tab’a yard” Da wani irin mugun sauri ya mik’e ya fita tun kafin Maama ta yi masa bakin da zai tarwatsa rayuwarsa. Da sauri sannan zuciya tana cinsa ya fito daga cikin gidan, sai da ya kai kusan rabin gaban gidan ma tukunna idanunsa suka fara ganin dai-dai, a mugun cike taff ya ga layin amma chan nesa mutanen suka tsatstsaya, sai kuma ya ci karo da su Oscar sun yiwa matar nan cut 5 filla-filla abun tashin hankali! Har da Grenade wanda shi shigowarsa k’asar ma kenan ya zo wajensu Ma’ah d’in ya aikesa da ya dawo kuma yanzu ya kwasosu suka yo nan a motar dpo wadda suke shirin cinyewa k’arfi da yaji. Da k’arfi ya runtse idanuwansa ya kawar da kai da sauri ya juya da nufin komawa cikin gida ya ci karo da Inna da Minu suma sun kawo kai za su shiga cikin gidan nasu…. Tunda Ma’ah yake a rayuwarsa bai tab’a jin an yi abu ya so a bashi dama ya kare kansa ba sai yau, su Innna basu lura da gawar matar wadda ke yashe a bakin k’ofar gidan ba filla-filla sai da addar Oscar ta sake bada sauti wajen raba cinyarta da sangalalinta tukuunna idanuwansu suka kai gurin. Wani Irin salati Inna ta saka mai sautin gaske sai kuma jikinta ya sake k’afafuwanta suka gagara d’aukarta jikinta ya hau karkarwa ta tafi zata zube a wajen idanuwanta suna jujjuyawa..Da wani irin sauri Minu ya durk’usa ya kinkimeta ganin tana shirin zubewa ya bar wajen da ita, yana shiga gida ya ajjiyeta a d’aki ya rufo k’ofar d’akin ya fito… Ai kuwa kamar had’in baki, abunda yake cikin ransa kusan shine a zuciyar gaba d’aya waenda suka ji da waenda suka gani dan ya na fitowa ya dinga cin karo da samarin layin suna nufar gidan su Ma’ah! Masu wuta a iceee daban masu petir a gallon daban, masu tayoyi rirrik’e a hannu daban…. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 13. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Dije tana sauk’a daga napep ta wuce gida da sauri, ko ta kan mai Napep d’in wanda ya biyota yana yi mata maganar kud’insa bata bi ba dan ita bata ma jishi ba kuma ta manta da ana biya tsabar yadda hankalinta yake a tashe ranta yake a b’ace, so take kawai ta ganta a gida. Allah ya taimaka Ya Kamal wanda dawowar sa kenan daga nemanta ya ga sauk’arta daga Napep d’in da yadda mutumin ya biyota dan haka ya k’arasa ya sallamesa yana shirin shiga gida ya sameta ya ji ba’asin Ina ta je ya ga ana ta nufar gidan su Ma’a. Usso wanda ya fito a buge! Ya tare ya tambaya, a bakinsa ya ji komai dan haka ya wuce cikin gidan a mugun fusace ya wuce d’akin Iyya ya d’auko wata zabgegiya wuka………. Minu yana fita Inna ta samu ta tattaro duk wani ragowar kuzarinta ta mik’e da kyar ta bi bayansa amma sai ta tarar ya kulleta ta waje. Sosai ta saki kuka ta durk’ushe a wajen dan ta san zafin zuciya irin ta Minu da kuma yadda ta ga ya fusata bata da tantama gidansu Ma’a za su ce za su koma shi da ragowar samarin Unguwar. Sama-sama ta ji ana tab’a k’ofar kafin a zare sakatar a bud’e k’ofar aka shigo, da sauri ta tashi ta shiga k’ok’arin gane wayene da yake babu haske a d’akin..dai-dai nan kuwa kamar an san abunda take nema aka kawo hasken wutar nepa. Maimakon ta rungumeta ko ta yi mata magana kawai sai ta sake fashewa da kuka! Kukan itama Dije ta saka ta rungume Innar tata tana mai tambayarta “me yake faruwa a layin? Na ga su Ya Aminu suna ta jidar tayoyi da itace.” Zabura Inna ta yi ta fita waje tana kwala kiran Minu dai-dai Iyya itama ta biyo Ya Kamal a baya tana kiransa bai kulata ba, haka itama Maman Sagir ta biyo nata d’an amma suka fice da gudu suka banko k’ofar suka datsa k’atuwar sakatar dake a ta waje sukayi gaba abinsu zuciyar kowa a wuya…. Babu shiri su Inna suka fara k’ok’arin b’alle k’ofar dai-dai nan Mallan ya bud’e k’ofar suka shigo shi da wani k’aninsa Kawu Isa wanda yake zaune a K’auyen (Getso.) Turuss!! Suka yi suka d’an jaa baya sai kuma Inna ta matso ita ta ma manta da fushin da take yi da shi ta shiga ce masa “dan Allah ka je ka taho min da Minu ya tafi yin fad’a da su Ma’ah ba iyawa zai yi ba ka dawo mini da shi kar su kashe mini shi” A take su Iyya suma suka shiga kawo nasu zancen wanda hakan ya sanya Mallan d’in ya gagara fahimtar ina zantukan nasu suka nufa. Ta bayan gidan su Ma’ah samarin suka fara zuwa suka sassaka tayoyi kafin su zagayo ta gaba dukda yadda su Oscar suke hauka da wuk’ak’e (dan suna gama sassara matar nan suka koma kan y’an kallo) suna gani ana sarar Jama’a amma hakan bai hana mazan nan tunkarar su gadan-gadan ba. Ta inda aka ci galaba a kansu shine su Oscar d’in ba su tab'a tunanin zuciyar mutanen zata iya k'ek'eshewa su tunkare su ba dan haka basu shiryama komai ba su kuwa samarin suna zuwa tun daga nesa suka fara yi musu ruwan kalanzir da tayoyi har da masu petir..Ma'a yana ganin haka ya wuce cikin gida da guda ya kunna famfo ya jono ruwa da masifar guda dan ya san me suke shirin yi ai kuwa yana fitowa ya tarar an fara wullo musu wuta ta kama jikin Grenade sai ihu yake yi. Tunda Scorpion ya hango Minu a cikin tawagar daman ya fahimci tabbas in ba da kyar ba sai kwanansu ya k’are a yau dan ya san Ma’ah zai iya yunk’urin kare Minu su kuwa yadda suke a zuciyen nan da gani da shirin kashe su suka zo dan haka duk wani mistake ko sanya idan suka yi tsaff sai an ci galaba a kansu!! Shiyasa tun wuri ya koma gefe ya yiwa Yaransa waya ta yadda ko shi an hanasa su baza su hanu ba dan ba hankali ne ma da su ba (they are always drunk) ballantana su fahimci Ma’ah d’in idan ya ce kar a yi. Yana fitowa da mesar ya fara watsa ruwan a kan Grenade dan wutar ta kama shi da kuma waensu wajaje har jikin ginin gidan duk sun kama suna ta ci da wuta sosai…sai da ya fara kashewa Grenade wutar jikinsa tukunna ya saka k’afa ya take wajajen rabin mesar da masifar k’arfi ruwan ya daina zuwa, a gaggauce ya sunkuya ya d’auki wani galan d’in da aka jefo masa yanzu a cikin ruwan jefe-jefen da ake ya yi musu dan ya ji shi da d’an nauyi ai kuwa yana d’auka ya ga da d’an dama a ciki dan haka ya zuba abinda ke a cikin galan d’in ta bakin mesar ya kai kusan rabin inda ya take d’in..dukda jifa da tayoyi da ruwan fetur d’in da yake sha hakan bai sa ya tsorata ya sare ba gashi hannunsa ya kama da wuta dan garin zuba abun a cikin mesar ya zubar masa a hannu dan haka wuta ta kama hannunnasa amma bai sare ba abunda ya sa gaba kawai yake yi da zafi-zafi….. Kad’an ya d’an d’aga k’afarsa daga kan mesar ruwan ya taho, ya dededeci inda wuta ke ci, sai da ya tabbatar wutar ta bi ruwan tukunna ya kwaso ta da mesar ya d’aga k’afarsa daga kan mesar gaba d’aya ya watsa musu, nan kuwa wuta ta tashi buuuuu!! Ta fara kama har da galoli da tayoyinsu. Sai da ya tabbatar da ruwan ya dedeta tukunna ya kashe wutar dake a a hannunsa wanda wajen ya ji rauni matuk’a. Rikicewar da suka yi ya sanya suka yi laushi wasunsu suka gudu su kuma su Scorpion suka yi kan ragowar da basu gudu ba. Sam! ko da wasa basu nufesu da niyyar sara suka ba da niyyar kisa suka nufesu dan a wuya da ka! Suke kai musu suka wusu kuma idan suka chaka musu wuk’ar daga k’asan k’irji sai sun jaaa sun kai ta har k’asan tumbinsu kayan ciki sun fito tukunna suke jefar da su! Hakan da aka gani ya sanya aka ci gaba da guduwa. Grenade ne ya yi kan Minu ya sare shi da wuk’a a hannu Allah ya so ba sosai ba dan ya goce kuma ya kare sarar ne dan Kansa Grenade d’in ya kaiwa hari Allah ya tak’aita, garin guje-guje (wani ya taho da gudu) ya bige sa aikuwa a take ya zube a wajen, dan haka Grenade d’in ya sake d’aga wuk’ar yana shirin sauk’e masa ita a kai kenan Allah ya kawo Ma’a wanda ya hangosa tunda ya nufesa ya hankad’e sa ya tada Minu…mistakenly ya tura Grenade d’in kan su Scorpion ai kuwa suka zube rikicaa makamansu suka fad’i a k’asa…wasu a cikin samarin layin kuwa waenda basu kai ga guduwa ba suka yi kukan kura cikin zafin nama suka yi kansu wani a cikinsu ya d’auke zabgegiyar wuk’ar scorpion bai yi wata-wata ba ya sauk’eta a kan Grenade dama shi kad’ai ne Allah bai bawa ikon tashi da wuri ba sakamokon k’unar da take a jikinsa ya sanya dama dauriya ce kawai yake yi. K’arasowar Ma’a d’in shi ya taimaki su Scorpion amma da tuni suma an kasheshu, da kyar ya kwacesu ta hanyar kaiwa wajen mutun biyar sara a lokaci gudu, suma kuma mutanen dama tunda suka ga ya shiga fad’an aka fara guduwa. Suna tashi suka yi kan Minu wanda jiri ya hanasa tashi a wajen nan ma Ma’a ya sake taresu ya ingiza su cikin gida, ai kuwa suna gama shigewa aka samu wani mai k’arfin Hali ya biyosu ya datse k’ofar. Yayinda su kuma suna shiga cikin gidan kawai suka ga wuta tana ci kamar hauka sun cinna musu wuta ta baya ashe, ga Maama a yashe a tsakar gidan wadda tun fitarsa ta farko da ta yanke jiki ta fad’i bata sake shurawa ba. Da gudu suka nefeta duk su ukun dan shima sai yanzu ya ganta d’azu da ya shigo kunna ruwa sam bai ganta ba. Yana zuwa ya d’ago fuskarta, da mugun sauri ya runtse idanuwansa sakamokon yadda ya ga gaba d’aya halittun fuskartata sun zaizaye sun koma gefe guda inda ta kwanta a kai…….. Wani irin wutar bala’i ce take taso masa yana k’ok’arin dannewa dan ya san idan ya fita a haka tabbas sai ya kashe duk wani rai da yake a wajen nan…. Cikin tsananin fushi Scorpion ya ce “Shi fa Yaron da kake ta karewa a yanzu inda ace zai samu dama wallahi da sai ya kasheka!!! Bai ma fa san kana yi ba, ga gawar Grenade chan yashe a waje inaga hakan ya isa ya sanya ka fahimci idan baka daina katsemu ba to muma duk sai an kashe mu! Sannan ka gaya min ta yadda zaka fita da Mama a cikin gidan nan idan ba a yi clearing wajen nan ba???” Yana gama fad’in hakan ya d’auki waya ya kira Yaronsa yana d’auka ya ce “wai dan durun uwarka kuna Ina?” A buge Saurayin ya ce “go slow ne ya tsare mu a kan gada, ka san tal’udun da ka ce mu zo dole sai an bi ta cikin gadar ruwa” Tsaki ya yi ya jefar da wayar da wani irin mugun k’arfi ta tarwatse bai samu ya ji na gefen saurayin wanda ya ke ce masa “mun kusa fa Oga ka d’aga masa k’afa a china yake shi yanzu haka” ba. Tabbas ya san in dai ba Ma’ah ne ya shiga fad’an nan ba to sai an kashe su su duka hud’un a yau! Dan tun d’azu ya fahimci ba iyaka samarin layin bane kusan kaff y’an Unguwar ne suka yi musu taron dangi, yanzu haka kuma hayaniyar da yake ji a waje ya san sun ninka na farko! Ko da ace kanshi ba ya ja ya san cewa ‘Sarkin yawa ya fi sarkin k’arfi’ Ammafa dukda haka ba zai zuba ido a gaban idanunsa Ma’a da Mahaifiyarsa su mutu a cikin wutar nan ba ba tare da ya tab’uka uwar komai ba dan haka kawai sai ya juya ya nufi d’akin Ma’ah d’in wanda yake a soro ya bud’e ya shiga! Sun bar wuk’ak’ensu a waje dan haka yana shiga wajen da ya san zai ga wuk’ak’e da adduna ya nufa. Wata zabgegiyar Adda ya d’auka ya d’auki wata wuk’a mai mugun kaifi ya sak’ale a k’ugunsa ya fito. A bakin k’ofar d’akin ya ga Ma’a a tsaye rik’e da Maama a hannunsa… zai yi magana ya ga kawai ya wucesa ya ajjiye ta a d’akin nasa dan nan ne kawai hayak’i bai bule ba a cikin gidan…yana ajjiyeta ya d’auki wuk’ak’e ya fito ransa a mugun b’ace! Ihu suka saka suna yi masa kirari yayinda shi kuma ya k’arasa bakin k’ofar gidan ya saka dukkan k’arfin da Allah ya bashi ya dake ta da k’afa…sau uku ya kai mata duka ta b’alle ta fad’i a k’asa, y’an wajen kuwa kamar jira suke suka hau yi musu ruwa fetur basu kai ga fara cilla musu itace masu ci da wuta ba suka yi kansu……… Sun fi su d’ari wanda kaso goma ne kawai za a ce suka d’auko makamai! Zuciya mai cike da Imani da rashin iya aikata kisan kai ya sanya suka rikice gashi wani irin chachchaka Ma’a yake yi musu da hannu bibbiyu! Tsoro da kuma ganin ana ta kashe wasu ana jiwa wasu rauni ya sanya wasu kaso hamsin a cikin waenda suka yi saura sake guduwa dan haka suka sake samun galaba a kansu! Ammafa suma an sassaresu, dauriya ce kawai suke yi da kuma sabo shiyasa basu galabaita k’arfinsu ya gushe ba. Gudu sosai ake yi zuwa yanzu dan tiyagas Ma’a ya koma cikin d’akinsa ya d’auko ya zo ya sakar musu dan haka baka iya ganin komai sai dai kawai ka ji sauk’ar wuk’a a ruwan cikinka, su kuwa su duka ukun akwai glases d’in da suka saka mai tare hayak’i. Sai da ya yi clearing wajen ya tabbata it’s safe tukunna ya koma cikin gidan da mugun gudu ya kinkimo Maama ya d’auki wani briefcase dan sosai gidan yake ci da wuta! Ya fito da ita, suna fitowa gas ya yi bindiga wutar ta fi ta farko. Da gudu ya saka Mama a mota ya bawa Oscar key ya shiga ya zauna tare da ita yana kallon fuskarta yana jin wani kalar wutar bala’i da k’unci suna taso masa….Yana shiga mota Yaran Scorpion suna k’arasowa wajen!… Har an tayar da motar Ma’a ya yi kiransa.. kamar zai hanasa sai kuma abunda ya faru d’azu da rijiyar da ya tsallake da baya duk a yau suka dawo masa tarr cikin kwanyarsa dan haka kawai ya ce masa “duk rintsi kar ku tab’a gidansu Khadijah! Da y’an gidan.” Jinjina kai Scorpion d’in ya yi ya sara masa tare da addu’ar Allah ya bawa Mama lafiya tukunna ya juya ya koma kan tawagar Yaransa waenda zuwa yanzu har sun cinnawa gida uku wuta. Suna wucewa….a hankali yake bin gidansu da kallo yana ganin yadda yake ci da wuta kamar ba gobe! Ya san ko tsinke ba za a iya fitarwa ba dan da kyar shima yanzun ya iya shiga ya d’auko Mama tare da takardun credentials d’insa dukda kuwa bayajin akwai wani amfani da za su yi masa. Sai a lokacin tukunna ya tuna yau fa tun d’azu bai ga Mallan idi ba! Tsaki ya yi ya kawar da kansa a ransa ya shiga addu’ar ‘Allah ya sa ya na ciki ya bugu yana ta uban bacci, bai ji komai ba har wutar ta cinye sa’……………. A chan gidan su Dije kuwa Mallan yana gama fahimtar komai ya juya zai fita shi da kawu Isa a gigice, Kaka ta fito ta ce “Duk ku biyun idan kuka fita sai na tsine muku Wallahi, ba zai yiu in rasa y’ay’ana har biyu akan wani Minu wanda ba’a da tabbacin ma d’anka ne ba.” Ta k’arfi Inna ta runtse idanuwanta tana ganin wani irin dishi-dishi, a hankali ta juya ta koma d’aki ta d’auko mayafinta ta zo ta nufi k’ofar fita. Mallan bai motsa ba kuma bai ce mata komai ba sai da ta k’araso daff da shi tukunna ya ce mata “ki koma ki zauna Allah yana tare da su” Rikitattun idanuwanta da suka rine da kuka da tashin hankali ta d’ago ta watsa masa sannan ta ce “bani hanya in wuce! Idan kai zata iya tsine maka ai ni ba zata iya ba!” “Eh ai dama a tsinen kike!! Shegiya gantalalliya! Ina amfanin tsinewa tsinanniya!?” Cewar kaka Da sauri kawu Isa ya ce “Kaka ki yi hak’uri ba za mu fita ba ki koma ciki kin ji!!!” Cikin b’acin rai ta ce “ai Isa yau kuma a yanzu za mu yita ta k’are!! Idan ka ga na koma ciki to Mallan ya zab’a ko ni ko Dije da uwarta!! Dan wallahi na gama zama da su k’ark’ashin inuwa d’aya!!!” A hankali Mallan ya runtse idanuwansa sannan ya bud’e ya ce “Kaka dan girman Allah ki yi hak’uri ki tsaya tukunna a gama wannan tashin hankalin da yake wakana a waje!!!” Cikin halin ko in kula ta ce “yo ni Ina ruwana da wani tashin hankali?? Ai bai shafe ni ba tunda babu d’aya daga cikinku a wajen! Abunda nake so yanzu shi za a yi idan kuma su zaka zab’a to fad’a min tun wuri in fitar maka daga gida in shiga gari!!” K’irjinsa ne ya

Chapter 11 of 23