Share this page
Dije aure ya ce “In sha Allah”. Jinjina kai ya yi ya ce “to shikenan babu damuwa amma bari in je in sanarwa Mahaifiyata da iyalina in ya so daga nan ko bayan la’asar ne sai a d’aura”. Daga haka suka yi musabaha ya juya ya wuce zuciyarsa fes, tabbas ya san ya tsinci dami a kala! Mutane suna ta tunanin wani abu daban gashi shi zai Angonce kuma ya san in sha Allahu babu abunda zai same shi, shi fa dama tun lokacin da ya ji batun rasuwar Yusufa da aka ce Ma’ah ne sam abun bai kwanta masa ba, dan ya yi kamar tatsuniya ko wasan Yara…. Yana wannan tunanin ya k’arasa gidansa, mai d’auke da d’akuna bakwai inda yake da Mata uku Y’ay’a ashirin da bakwai da Mahaifiyarsa duk a cikin gidan kuma da ikon Allah sana’arsa ‘d’an kantin’ ne ta inda yake sayar da kayan kanti, da shi yake ciyar da iyalinsa da taimakon mata da y’ay’ansa waenda suka kama sana’a ba da wasa ba dan kaff cikin su babu mai zaman banza, hatta d’an k’aramin Yaronsa mai shekaru biyar yanzu haka yayunsa maza da suke d’aki d’aya sun fara tafiya wajen da suke fenti da shi yana kallo dan a samu ya koya da wuri. Mallan ya so ya b’oyewa Inna dan yana jin tsoro kar ta hana, shi kuma har ga Allah shi kad’ai ya san me yake hangowa a future d’in Dije muddin ba su yiwa tufkar hanci da wuri ba, amma kawai sai ya zab’i ya gaya mata. Dan haka ya koma gefe bai bari ma ya shiga gidan ba ya kirata a waya ya shaida mata batun ‘auren Dije da Mallan Manniru wanda za’a d’aura a yau in sha Allah’, daga nan ya d’an bata haske akan dalilinsa na yin hakan. Tabbas bata so had’in ba dan ko babu komai Mallan Manniru Mahaifi ne ga k’awarta kuma matayensa duk mutanen kirki ne ana shiri da su matuk’a. Amma fa Hausawa sun ce so so ne amma son kai ya fi! Shiyasa Mallan d’in yana gaya mata abunda yake hange da yadda ya rasa samawa Dijen Miji a Getso ma duk sai jikinta ya yi sanyi ta yi shiruuu kawai kafin ta ce “Allah ya zab’a duk abunda ya ke alkhairi…..” Tana baro kitchen inda ta gama wayar ta nufi d’aki. Tana shiga d’akin ta tarar da Dije da Sumayya baiwar Allah tana ta rarrashinta yayinda ita kuma ta kafe k’unshin hannunta da kallo tana ta zubar da hawaye. Tausayin su ne ya rufe Inna duk su biyun dan haka kawai sai ta juya ta bar musu d’akin ta fito tsakar gida ta nemi waje ta zauna ta rafka uban tagumi.. Ba ta dad’e da zama ba Iyya ta fito ta dinga rarrashinta tana bata baki….da kyar Inna ta ke iya danne zuciyarta ta hana kanta yin kuka, abubuwan sun yi mata yawa ne Astaghfirullah ga Ya Muhammad chan a kwance bai ma san Ina kansa yake ba, Likitoci sun ce a yi addu’a kawai, ga kyarar da Kaka take yi mata dan Wallahi kawai pretending take yi amma abun yana masifar damunta, sannan ga Mallan wanda kwana biyun nan daga ya yi wannan idan ta kawar ta share sai ya sake yin wani, gaba d’aya zaman nasu ya k’i yin dad’i ko wannensu a gigice, yanzu haka ma da ya kirata highlight kawai ya yi mata kuma da ta tambayesa ya dawo ne? Ko yanzu ya taho? Nan ma bai gaya mata ba, Mallan d’in da a da ko kaya in zai saka to tare suke zab’a amma yanzu ta lura kamar har da b’oye-b’oye ma ya fara shiga cikin lamarin nasu, ta yi masa uzuri tabbas saboda halin da yake ciki amma kuma abubuwan sun kasa fita daga kanta. Tana cikin wannan tunanin ta ga an fito da Ramma tsakar gidan an shimfid’a mata tabarma an kwantar da ita, hannun nan ya yi suntum! Ita kanta ta kumbura dan jiki take ji ba kad’an ba! Asabe itama hannun ya yi muni amma ba wani sosai ba dan tana ma iya yin komai dukda anata hanata saboda gaba amma ta k’i ji idan ka ganta ras kamar ba mai jinya ba komai yi take yi dan bayan hannun ne ba ciki ba yayinda na Ramma ya munana sosai..D’an koyo ne ya d’aurata a gida ashe ba dai-dai ya d’aura ta ba, dama tun a ranar Iyya take ta ce musu su kaita asibiti d’aurin bai yi ba amma aka k’i ko da yake saboda rashi ne da babu dan in aka je asibiti kud’in kati ma ba lalle su iya biya ba. Sai d’azu ne tukunna aka gane ashe d’aurin bai yi ba to yanzu dai an kira wani kwararre zai zo ya gyara. A gefenta y’ay’an suka zauna, sun saka ta a gaba wanda su kad’ai suka san halinda suke ciki dan ba iyaka tashin hankali ba ko da yunwar cikinsu aka barsu ta ishe su, rabonsu da abinci tun jiya da safe wanda Iyya ta zuba musu. Ita Inna bata san basu da kayan abinci ba da zata basu ko da iyakacinsa kenan gareta dan kaff gidan ita da Iyya ne kawai basu da rowa. Gashi su matan basu iya sana’ar komai ba uwar kuma da take komai gata a kwance. Usama ne ya kwanta a wajen yana ta faman murk’ususu dan shi kam hak’urinsa ya k’are zuwa yanzu, Inna tana shirin yin magana Hajiya Uwani ta shigo cikin gidan a fusace Suwaiba a bayanta tana ruk’ota tana cewa “ki tsaya mana. Kar ki yi haka dan Allah, tsaya ki ji” Ita kuma tana cewa “ki rabu da ni fa! Ki bar ni in jaa musu kunne ramin kura daga ita sai y’ay’anta wallahi bakin rijiya ba wajen wasan Makaho bane ba, ba zan zauna in nad’e hannu a cuce ni ba!” Firfitowa na cikin d’akin suka fara yi, kafin ka ce kwabo tsakar gidan ya cika tap! Hatta su Sumayya wadda suke d’aki tare da Dije. Tunda Uwani ta shigo dama Inna ta sunkuyar da kanta k’asa dan ta san labari ya iske mata kenan. Idanun matar yana sauk’a a kan Inna ta ce “muguwa azzaluma!! Butulu! Makira…. Da kika san duk wanda ya ko kalli y’arki kamar ya yanki tikitin mutuwa ne ai sai ku hak’ura da aurar da ita ko kuma ku bashi shi d’in ya aura kawai, amma shine tsabar muguwar zuciya irin taku za ku mak’alawa Mijinmu? Mai ya sa ba kwa jin tsoron Allah ne??” Rass!! Gaban Sumayya ya yanke ya fad’i k’irjinta ya fara bugawa, a hankali ta zamiye hannunta daga cikin na Dije ta k’arasa inda Mahaifiyar tata take tsaye ta ce “me ya faru? Wanne Baban ne zai auri Dije?” Cikin b’acin rai wanda yake had’e da firgici da tsoro ta ce “Baba ubanki mana! Ina da wani Mijin sama da shi ne? Shi ne dan tsabar nemawa Kai aka bashi wannan masifar” ta yi maganar tana nuna Dije, sannan ta d’aura da cewa “shi kuma ya amsa, wai anjima bayan sallar la’asar za’a aura masa ita.” Da k’arfi Inna ta runtse idanuwanta tana dad’a danne zuciyar da take tasowa take yunk’uro mata, dan sosai ta kawo iya wuya (mai hali a duk halin da yake ciki halinsa halinsa ne). Juyawa Sumayya ta yi suka had’a idanu da Dije, a hankali Dijen tana hawaye ta shiga girgiza mata kai alamun ita babu ruwanta, kafin da kyar ta matsa kusa da ita ta samu ta iya furta “Wallahi ban san ma me yake faruwa ba, muna d’akin nan tare da ke mun fi kwana uku kina tare da ni. Kuma Ina so ki saka a ranki maganar nan ba tabbatacciya bace ba dan ba zan tab’a yarda in auri Baba ba.” “Zancen banza ma kenan!! Abunda an riga an bashi ya karb’a kuma me ya rage? Sunanki da nashi ya riga ya had’u dan haka kin gama gamawa da mu! Allah ya Isa tsakani na da ke in har wani abun ya samu Mijina wallahi Allah sai na baku mamaki da ke da mugayen iyayenki” Ta fad’i hakan tana mai rushewa da kuka. Hak’uri jama’ar gidan suka lullub’eta suna bata yayinda idanun Dije suke cikin na Sumayya tana hango b’acin rai yana maye gurbin tausayinta d’in da take gani a cikin idanun nata, hannunta da yake a cikin na Dijen ta sake damk’ewa ta ce “Sumayya ki yarda da n…” Tass!! Ta d’auketa da mari sai kuma kawai ta fashe da kuka a take ta juya ta fice dan sai da ta yi Marin sai kuma ta ga rashin dacewar hakan tunda ba laifinta bane ba sannan kuma ga bak’in cikin abunda yake shirin faruwa d’in tabbas ya ci ta rufe Dijen da duka ma! Dan haka duk sai ta sake rikicewa ta sake gigicewa ga kukan Mahaifiyarta da take jinsa har tsakar zuciyarta. Ko bayan fitar Sumayya haka nan Uwani ta ci gaba da tsinewa Dije tana kuka tana aibantata ana ta bata hak’uri amma ta k’i hak’ura. Sai tsine mata take yi tana kiranta da masifa!!. A fusace Inna ta mik’e ta ce “Malama ya ishe ki! Y’a ta ba masifa bace ba”. Kusan a tare ita da Maman Sagir suka ce “Wallahi Masifa ce!” Sai kuma uwani ta d’aura da cewa “ki rubuta ki ajjiye ke kam kin gama yawo dan kin haifi ajalin ki ne.” A fusace Inna ta yi kanta kamar za ta dake ta tana cewa “ni kuma na ce ki rubuta ki ajjiye sai kin ji kunyar abunnan da kika fad’a in sha Allah y’a ta alkhairi ce kuma sai na shiga aljannah a ta sanadiyyar ta!” Gud’a ta rangad’a ta ce “ai Yarinyar da aka aurar ta kai mutuncinta gidan Mijinta ita ce ake saka rai da hakan sab’anin ita da kowa ya san karuwar d’an daba ce wanne mutunci za ta kai? Ki yi addu’ar neman gafara dan sam baku kula da amanar da Allah ya baku ba wallahi.” Hakan kuwa da ta fad’a ya taimaka wajen sake fusata Inna dan haka ta hau ta fara ita ma Uwani da Maman Sagir d’in suna yi a take tsakar gidan ya kacame kamar ana bikin bala’i…… Sai da Mai Unguwa ya zo tare da dattawan Unguwa tukunna da kyar aka fitar da uwani daga gidan nan dan rarrashin duniya ta k’i fita ta ce wallahi ba a isa a aurawa Mijinta masifa ba dole a wargaza d’aurin auren nan! Musamman ma da ta fahimci Mallan na cikin gidan dan haka ta Isa bakin k’ofar d’kinsa ta dinga bala’i shi kuwa ya yi kunnen uwar shegu da ita wanda hakan ya zamewa Inna kamar duka biyu dan duk da halinda take a ciki sai da ta k’ule na ganin Mallan a cikin gidan kawai tsulum ba tare da ta san ma ya dawo d’in ba! Mutumin da duk halinda yake ciki a da ko ruwa zai sha sai ta sani ko masallaci zai je sai ta sani ya riga da ya saba mata da hakan….. Duk bakin Dije da fad’an da kowa ya santa da shi wannan karon ta yi masifar yin sanyi an ci k’arfinta…ana fitar da Uwani su Rakiya suka rufar mata har da Kubra wadda zuwa yanzu ta tsani Dije kamar mutuwarta, habaici da bak’ak’en maganganu da gori babu kalar wanda bata ji ba musamman ma Rakiya da ta kasance duk ta fi su baki haka nan ta yi ta yi kamar ba uwarsu ce a kwance babu lafiya ba Kubra itama ta na yin nata haka suka wuni a cikin gidan suna sake damalmala mata lissafi dan dama tun usul duk haushinta suke ji saboda ta fi su komai gashi kuma ta fisu Baki dan da wuya ka ji ana fad’a an kayar da ita shiyasa yau da suka samu lagonta suka yi mata taron dangi. Duk masifar Inna ba ta cika yin fad’a da y’an matan gidan ba amma da suka k’ular da ita gashi Dijen sai wani irin kuka take yi ya sanya ta fita ta yi musu tatass!! Tukunna aka samu sauk’in su. Dije kuwa tana nan kamar za ta mutu rarrashin duniya Iyya da Inna sun yi amma ta gagara yin shiru gashi ta k’i cin abinci tun jiya dama tunda ma aka saka ranar aurenta da Yusufa ta fara yiwa abinci k’aura shiyasa yanzu da ulcer ta tashi ta sakota a gaba ta rik’e mata k’irji da baya, gashi ta k’i yin shiru musamman ma dataga la’asar ta gabato gaba d’aya sai ta sake gigicewa tana kuka tana rok’on Inna akan ‘ta rufa mata asiri kar ta bari a aura mata Baban su Sumayya’ Inna kuma ta ce “ai idan ma suka yi hakan to kamar sun ce mutane su sake tabbatar da cewa Ma’ah yana bi yana kashe mata mazan aure ne kuma indai hakan ta tabbata to sun shiga uku, dan haka ta yi hak’uri a yi auren in sha Allah babu abunda zai faru mutane za su ji kunya kuma za a daina maganganu a kanta.” Suna cikin hakan Ya Aminu ya shigo! Sosai hankalinsa ya tashi da ya ji zancen, shi da ya yi againsting aurenta da Yusufa ma ballanta wannan tsohon da yake jiran lokacin sa inaa ba zai yiu ba dan haka tashi d’aya ya birkice sai da Inna ta bud’e masa ido ta yi masa da gaske tukunna ya karb’i abincin su ya juya ya koma asibitin yana ji kamar zai mutu……………… A chan masallaci kuwa, tun kafin la’asar d’in ta yi dama labari ya gama zagaye layin har ma da waensu a cikin layukan da suke makwabtaka da su. Wasu da yawa k’in zuwa ma sallar la’asar d’in suka yi a cewarsu kar su je Ma’ah ya zo ana cikin d’aurin auren abu ya shafesu, yayinda waenda suke da tabbacin Ma’ah d’in ba ya garin suka je saboda su ga abunda zai turewa buzu nad’i. Masallacin kam ya cika har waje sai dai babu wanda ya tsaya a sahun su Ma’ah haka aka gabatar da sallar la’asar, dama tun kafin a tayar da ik’ama da aka ga babu Mallan Manniru babu alamarsa aka fara k’us-k’us yayinda hankalin Mallan ya tashi chaa! Dan kana kallonsa za ka gani shimfid’e a kan fuskarsa, a hakan ma wai Ya Kamal ya d’an kwantar masa da hankali ta inda ya ce ‘watak’ilan shirye-shirye ne ya tsayar da shi amma ya san in sha Allah kafin a idar zai shigo’.. Amma sai gashi har aka idar da sallah babu Mallan Manniru babu alamarsa wanda hakan ya sake firgita Mallan…dan ya san in ba da kyar ba cewa zai yi ya fasa. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 19. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Zuruuu! Haka aka kasance a cikin masallacin kowa ya kasa furta komai sai d’aid’aiku da suke ta k’us-k’us a chan baya…haka nan ake ta zaman jiran tsammani gashi an riga an gama sanarwa ballantana a waske, ko da ace ma ba a sanar d’in ba labarin d’aurin auren Dije da Mallan Manniru wanda ake saka ran d’aurawa a yanzu ya riga da ya gama karad’e Unguwar tun d’azu… Idan ka kalli fuskar Mallan dole ya baka tausayi dan idanunsa sun kad’a sun yi jazir kamar ma kukan zuci yake yi gashi ya yi shiruuuu dan ko magana idan aka yi masa sai an tab’a shi tukunna yake iya jin mutum.. D’auko wayarsa ya yi a karo na babu adadi daga idar da sallar su kawo yanzu ya sake gwada layin Mallan Manniru amma har ta katse ba’a d’aga ba. Sake gwadawa ya yi still yanzun ma ba’a d’aga ba dan haka hankalinsa ya sake tashi duk dauriyarsa bai san lokacin da wasu zafafan hawaye suka zubo masa ba. Da sauri Ya Kamal ya matsa ya zauna a ta gabansa da son ganin ya karesa tukunnan ya ce “Kar ka yi hakan Mallan dan Allah, zai zo in sha Allah”. “Ki tsaya mana! Haba mana ba ki ga nan d’in masallaci bane ba?” Muryar wani mutum tare da hayaniyar Uwani ta katsewa kowa da ke a cikin masallacin hanzari. Da sauri duk suka mik’e kowa aka fita wajen dan hayaniyar tasu sake kusanto su take yi alamun dai masallacin suke shirin shigowa. Suna fitowa dai-dai Uwani ta k’araso bakin masallacin itama jikinta jagafff! A jik’e wanda hakan ya sanya da yawa suka kaawar da kai dan sosai surarta ta baiyyana komai da komai saboda rigar yadin yala-yala ne a jikin nata gashi ta jik’a rigar tsaff da kalanzir, kanta ko d’ankwali babu. Idanunta suna sauk’a a kan Mallan ta yi kukan kura kamar wata actor ta dira a kanshi ta ruk’umk’umesa ta koina ta shak’osa! Fad’i yake “Subahanallah!! Astaghfirullah!!!” Amma Uwani sake ruk’unk’umesa take yi tana mai cewa “Rabi’a kunna mana!! Na ce ki kunna ko in tsine miki albarka, tun da sun hanani shiga in tashi da Dijen ai ga ubanta nan mad’aurin auren nata! Ki kunna tun kafin su k’arar da mazan layin nan da tasu sigar muguntar. Ki kunna na ce miki ko in tsine miki wallahi yau sai dai a binne gawarsa tare da ta Mahaifinku.” Salati wajen ya d’auka a take ya hautsine aka shiga tambayar Rabi’a da k’anin Mallan Manniru wanda ya biyota yake ta k’ok’arin tsayar da ita “mai ya faru?”. Rabi’a kam in banda kuka babu abunda take yi! Dan zuwa yanzu bak’in ciki ma ya hana ta tab’uka uwar komai, a d’azu gaba d’aya tsanar Dije ta rufe mata ido shiyasa da uwartata ta kawo wannan plan d’in ta yarda ta biyota da ashana da zummar idan ta ruk’umk’ume Dije ita kuma ta kyasta ta jefa musu su kama da wuta tare, ita wallahi kwata-kwata a d’azun sam lissafinta bai bata cewa idan fa ta kunna ashanar ta wulla har da uwartata za a mutu ba, tsabar yadda hankalinta yake a tashe take cikin bak’in ciki…. Da kyar k’anin Mallan Manniru ya iya basu amsar tambayar da suka yi masa chaaa suke ta zuba masa A hankali ya na sharar hawaye ya ce “Allah ya yiwa yayana Manniru rasuwa, ta sanadiyyar poision d’in da aka d’ura masa ya sha ta k’arfi da yaji dan har yanzu akwai alamun shatar hannu da aka gani a kan baki da hancinsa rad’au! Sai kuma cinyoyin hannayensa sun yi jaaa suma alamun dai matse shi aka yi. Yanzu haka hatta harshensa ma ya zagwanye tsabar k’arfin poision d’in.” Salati aka saka yayinda waensu suka fashe da kuka cikinsu har da Mallan, wanda kukan da ya saka ne ya dawo da Uwani daga duniyar nata kukan da ta lula tun daga lokacin da K’anin Mijin nata ya fara magana k’ank’ame A jikinsa, sai da ta cika shi tukunna ta d’aukesa da mari ta ce “ka daina wannan kukan munafurcin munafuki mugu azzalumi kawai!!! Ka san kuwa mutane nawa ka mayar marayu a yau d’innan saboda son ran ka!?” Sai kuma ta jiyo ta kalli Rabi ta ce “dan ubanki! Allah ya ji k’anshi ki bani ashanar idan ba za ki kyasta ba, Wallahi yau in bamu mutu tare da bawan Allahn nan ba to zuciyata na tabbata sai ta fashe cikin dare! Wai babu wanda ya ga kalar zalincin da aka yi mini ne? Mai ya sa duk kuka yi shiru kuna kallanmu ba za ku tayani yiwa wannan bawan Allahn abinda ya kamace shi ba???” Dai-dai nan matan layin da aka je aka kikkira dan su zo su tafi da ita suka k’araso wajen dan haka aka marmatsa musu Aikuwa tana ganin su ta sake k’ank’ame Mallan tamau! Hannayenta biyu zagaye a wuyansa amma dukda haka k’ok’ari take yi ta d’aga k’afafuwanta ta sak’ala a saman k’ugunsa, kuma ita har ga Allah ba ta kawo komai ko wani feelings ba tunda bama ta cikin ishashshen hankalinta, ita kawai babban burinta a yanzu shine ta ga sun kama da wuta ita da Mallan. Sai da maza y’ay’an Marigayi Mallan Manniru nata da na kishiyoyinta suka k’araso tukunna da kyar! Aka samu aka iya b’amb’are uwani daga jikin Mallan tana wani kuka kamar ranta zai fita abun tausayi. Da kyar aka iya janyeta aka shiga gidan da yake kusa-kusa da ita tana ta jero Allah ya Isa tare da fatan bala’i kala-kala ga Dije da Mallan har ma da Inna….. Ana wucewa da ita Mallan ya yanke jiki ya fad’i dan gaba d’aya k’afafuwansa sun gagara d’aukarsa, Ya Kamal sai wasu samari ne biyu kawai suka yi kansa yayinda ragowar suka tsaya ko kallonsa basu yi ba dan takaicin sa suke ji, tabbas ya tabbata Ma’ah shi ne yake kashewa Dije mazan da a ke shirin k’ulla mata alak’ar aure da su kuma Mallan d’in ya sani amma ya sake k’ullawa da Mallan Manniru tabbas hakan kam ya zama zalinci dan haka ya zama dole su d’auki mataki. Cikin masallacin suka shiga da shi ganin yadda idanuwansa suke wani k’ak’k’afewa yana nishi da kyar. Suna shiga da shi suka k’ara gudun fanka suka ware ac suna ta jera masa sannu. An kai ruwa rana dan ya d’an dad’e kafin ya samu ya dawo dai-dai da kyar, a take kuma sai ya fashe musu da kuka. Shiruuu kawai suka yi wasu suna kallon k’asa wasu kuma suna kallon gefe. A hankali Ya Kamal ya matsa kusa da shi ya ce “Baba kuka ba shi ne mafita ba, addu’a ita ce mafita a halin da ake ciki yanzu sannan kar ka damu in sha Allah ba zata tab’a rasa M…” Shigowar wasu dattawa cikin masallacin ne ya katse masa hanzari duk suka d’ago suna kallonsu. K’arasowa suka yi cikin masallacin suka nemi waje cikin dattako suka zazzauna. Gyaran murya d’ayan mutumin ya yi ya yi musu sallama suka amsa tukunna ya ce “ya muka ji da hak’urin Mallan Manniru? Dan na san kowa anan ta shafesa kasancewarsa d’aya daga cikinmu.” “Hak’uri da godiya Allah ya gafarta masa” Mallan ya ce yayinda gaba d’ayansu suka amsa da “Ameeen” daga nan wajen ya d’auki shiru kafin mutumin nan dai ya sake yin gyaran murya ya ce “Mallan Bashir, meye ne asalin gaskiyar abunda yake faruwa tsakanin y’ar wajen ka da Ma’aruf? Saboda munata jin jita-jita ya cika layi amma har yanzu ba mu san asalin gaskiyar lamarin ba! Shin soyayya suke yi ko YA ABIN YAKE? Sannan ka san shine ya kashe Yusufa amma duk da haka ka sake k’ulla aurenta da Mallan Manniru ko yaya?”. A hankali Mallan ya sunkuyar da kansa k’asa kafin ya d’ago ya kallesa ya ce “ya zo ya nemi ni akan batun yana son aurenta, na bashi hak’uri dan a lokacin an saka ranar aurenta da d’an uwanta Yusufa Allah ya ji k’ansa, to ni har ga Allah a lokacin da Yusufa ya rasu sam ban kawo Ma’aruf bane ba, da farko dai na zarge shi dan har ita Dijen na yi tunanin ko ta fad’a masa wani abun ne amma kuma da na zauna na yi tunani sai na ga hakan ba mai yiwuwa bace ba dan ni kaina sheda ne kusan tun lokacin da aka saka ranar aurenta ta ma daina fita kuma ba ma kula shi take yi ba sannan a ranar da ya ji zancen fa aka kashe Yusufa, kuma Dije ko waya ba ta da shi ballanta ace ta waya ta yi masa kwatancen gidan Yusufa wanda ko su Kamal ba na jin sun sani ballanta Ma’aruf.” A hankali ya share kwallar da ta zubo masa sannan ya ci gaba da magana “rashin yarda da shine ya aikata laifin kisan Yusufa ya sanya na k’ulla aurenta da Mallan Manniru Allah ya ji k’ansa…” Kukan da ya taho masa ne ya sanya ya kasa cewa komai ya shiga zubar da hawaye wasu na korar wasu. A hankali mutumin ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce “Mallan Bashir in dai har haka ne to a gaskiya dole ne ka yi mana alfarmar barin Unguwar nan saboda a zauna lafiya. Dan kamar yadda y’an makarantar su da suka koreta suka ce tabbas zama da ita hatsari ne! Kana gani dai yadda yake kashe duk wanda ya yi k’ok’arin k’ulla alak’ar arzik’i da ita saboda yadda yake k’aunarta wanda na tabbata hakan zai yi ga duk wani wanda ya yi fad’a da ita dan tabbas shima ba zai tsira ba ko da ace bai kashe mutum ba, na san tabbas ba ma ita kad’ai ba ko su Aminu idan wani ya yi gangancin shiga sabgarsu to sai ya karb’i rabonsa gashi su kuma kaff y’an gidan naka babu wanda za’a nunawa yatsa ya bari bai karya ba! Manyan su da k’ananu

Chapter 15 of 23