wallahi idan na ji ka yi mata ko da kallon banza ne za mu had’u da kai!
Sannan magana ta biyu yau Halima har sunana ta ambata ta gaggaya min magana kuma ta yi mini tsaki duk a kan y’ay’anta, da farko na shirya ne akan zan tafi amma sai na ga idan na yi hakan ita ce da riba…dan haka kana dawowa gobe ka san abun yi y’ar nan tata da take hauka saboda ita wallahi sai ta bar gidanka idan kuma ba haka ba to wallahi Allah sai na tsine maka, ka ji dai rantsuwar musulmi”
Da k’arfi Mallan ya runtse idanuwansa ita kuma tana gama fad’in haka ta kashe wayarta……
Daren ranar Mallan bai runtsa ba dan ya shiga tsaka mai wuya matuk’a ga y’arsa ga Mahaifiyarsa ga kuma matarsa wadda yake tsanani so da tattali dan ya san korar Dije a gidansa dai-dai yake da rabuwar sa da Halima.
Kafin asuba shima sai da aka jona masa nashi drip d’in sakamokon jininsa da ya yi mugun hawa, dole haka aka kira Minu wanda aka cewa ‘ya tafi gida’ jiya, ya dawo yana jinyar su su biyu Asabe kuma tana kallonsu kawai dan ko wanka ta k’i ta je gida ta yi so take sai rana ta take kowa ya hallara a gidan tukunna za ta shiga dan kowa ya gani ya shaida a asibiti ta kwana wajen Mallan, kuma a tsakar gidan zata shaidawa Halima Mallan d’in bashi da lafiya duk dan dai a ga darajarta tunda Mallan d’in bai gaya mata ba sai a bakinta za ta ji, dan ta ci sa’a wayar Minu ta mutu tun da ya zo da asuba babu chaji kuma asibitin babu wuta, ita kuma ta d’auke wayar Mallan d’in tana ganin kiran Haliman ta dinga rejecting ta ga kuma message d’inta “Assalam barka da asuba ya jikin Muhammad an ce kai ka kira Minu d’azu ya taho Allah ya sa
dai lafiya” shima ta na gama karantawa ta goge.
Tun sassafe ya tashi yau sab’anin yadda yake kullum dan a k’aidarsa idan ya dawo daga sallar asuba komawa yake yi ya kwanta sai 11 tukunna ya ke tashi.
Tana kitchen ta ga ya shigo cikin gidan daga d’akinsa wanda yake a soro, sai da ya sake gaida ita tukunna ya shiga kitchen d’in ya sauk’e mata tukunyar da take k’ok’arin sauk’ewa, wanda tunda ya kama tukunyar take ta cewa “a’a fa!” Amma sai da ya ajjiyeta a k’asan tiles d’in kitchen d’in. Ajiyar zuciya ta sauk’e sannan ta ce “ni dai na san kai ba sharifi bane ba amma ban san tayaya kake iya shanye zafi ba.
Wani murmushi ya yi wanda ya tsaya a iyaka k’irjinsa sai kuma hucinsa da ya fito amma ko yanayin fuskarsa ba ta nuna ba, cikin muryarsa wadda ta ke a nutse sannan cike da izza ko da yaushe ya ce “ba wai zafin ne ba na ji ba, Ina ji! Kawai dai na kasance mutum mai iya had’iye abu tun zamanin mugun ubana.”
Turuss! Ta yi ta tsaya daga k’ok’arin bud’e kantar kitchen d’in da take yi. Sun d’an jima a haka ita bata juyo ba shi ma kuma bai sake cewa komai ba kafin a hankali ta juyo ta zuba masa ido, itan yake kallo yana karantar yanayinta a hankali ya ji ta ce “ba zan gaji da baka hak’uri ba Ma’aruf! Rashin saka idon da na yi yana daga cikin abubuwan da suka bayarda gudunmawa wajen…”
Da sauri ya k’araso inda take ya d’aura yatsansa guda d’aya a kan bakinta ya ce “shiiii, Uwa ba ta laifi, sannan k’addarata a rubuce ta ke Maama, ba ki da wayon da zaki kub’utar da ni daga abunda Allah ya riga ya k’addara zai same ni, a haka k’addarata ta zo dan haka dole duk wayon mu sai na bi ta hakan”
Ajiyar zuciya ta sauk’e za ta sake yin magana ya ce “ki manta da abunda ya faru ya wuce…
Yau zan fara sana’a ki saka min albarka sannan akwai abunda nake ta so in gaya miki”
Sake mayar da gaba d’aya hankalinta ta yi garesa ta ce “Allah ya sa ka fara a sa’a, dan Allah a kula banda fad’ace-fad’ace sannan yadda na ga sauyin nan a tattare da kai dan Allah ka zauna a haka Ma’aruf ka daina wachchar rayuwar ka barta har abada hakan sai ya fi komai saka ni farinciki.”
Shiruu ya yi kafin a hankali ya runtse idanuwansa dan yau d’innnan ma yana da operation d’in da ba zai tab’a k’in yi ba, kamar dole yake a wajensa kuma ya san definitely sai an zubar da jini kacha-kacha ma kuwa sannan in ba da kyar ba a buge zai dawo mata gidan dan ya san babu ta yadda zai yi ya iya yin nasara a aikin dole sai ya sha wani abun…….
“Wacce maganace kake so ka yi da ni???”
Muryarta ta katse masa tunani.
Kansa yana a k’asa sosai ya sunkuyar, sai da ya daidaita yanayinsa tukunna da kyar ya d’ago ya d’anyi murmushi dan zancen nata ya taimaka wajen sanyaya masa ransa.
Kamar an fisgi maganar daga bakinsa ya ce “aure na ke so in yi in sha Allah”
Ya san cewa wannan ita ce kalma mafi soyuwa da Maama take burin ta ji ya ce mata amma dukda haka sai da ya yi mamakin yadda ta rushe masa da kukan farin ciki lokaci guda.
Murmushi ya yi mai sauti a hankali ya matasa sosai gareta ya rungumeta…zamewa ta yi ta saita gabas ta yi sujjada tukunna ta mik’e ta kamo hannuwansa ta rik’e ta ce “Allah ya sa matar ka ce har a gidan Aljannah” a hankali ya ce “ameen” ta sake cewa “Allah ya sa albarka da alkhairi a tarayyarku” sosai ya yi murmushi ya sake cewa “Ameen”
Cike da zumud’in son jin kwakwaf Mallan Idi wanda shigowarsa kenan ya ce “Ahh ma sha Allah suruka muka yi ne?”
A take annurin da ke a fuskar Ma’a ya d’auke lokaci guda, a hankali ya zame hannunsa da ke a cikin na Maama ya juya ya fice daga kitchen d’in gaba d’aya.
D’akinsa ya koma ya d’auki bokiti ya fito ya zo bakin tap ya d’ebi ruwa dan ruwan band’akin sa ya lalace tun shigar Oscar da ya yi a gigice ya lalata fanfon da shower,
ya daina zuwa, dai-dai Mallan idi ya tsare Maama yana ta jero mata tambayoyi akan a ina Yarinyar ta ke shi kuma Ma’a ya fito d’ibar ruwan. Kallo d’aya kawai Ma’a ya yi masa ya d’auke kai tun daga nan ya sha jinin jikinsa har Ma’a ya fito daga wanka ya zo ya ci abinci ya fita Mallan idi bai sake cewa komai ba.
Tun k’arfe bakwai su Oscar suke tsaye a k’ofar gidan dama a k’a’idarsu breakfast ma a k’ofar gidan suke yi! Kuma ko Ma’a zai kai k’arfe d’aya na rana bai fito ba to suna nan ba zasu je koina ba ruwa! Iska! Rana ba su isa su tashe su a wajen nan ba har sai sun ga fitowar Ogansu.
Yana fitowa suka mik’e suka hau ife-ife suna sara masa, tapping shoulders d’insu ya yi suka gaggaisa idanuwanshi a kan y’ar k’urk’urar da aka kawo masa rake a cikinta himini guda!
‘In sha Allahu zai tsaya ya yi sana’ar nan tsakaninsa da Allah’ Ya aiyyana hakan a cikin ransa…dan da farko su Oscar sun shirya ne akan ‘Ana kawo raken za su dinga rabawa gida-gida dole kowa ya karb’a ya bayarda kud’i ko kana sha ko baka sha’ shi Ma’a d’in ne ya hanasu ya ce a kafa trader duk mai son siya ya zo ya siya.
Kamar daga sama suka ji jiniyar y’an sanda, kafin ka ce kwabo layin ya d’inke mak’il da motocin y’an sanda har da wasu masu kayan sojoji a tare da su.
Suna zuwa ba su yi wata-wata ba masu kayan sojojin nan su biyu suka yi kanshi suka datsa masa ankwa aka tafi da shi.
Sai da suka tafi da shi tukunna aka gane ashe wannan sabon magidancin da yayiwa b’alli b’alli kwanaki ne y’ay’ansa suka kai k’ara shine aka zo aka tafi da shi.
Tun da y’an Unguwar suka ji labari haka nan Mata da samarin layi suka dinga sintiri a gidan suna basu shawarar ‘Wallahi su tashi kafin Ma’a ya dawo Unguwar tun wuri su san inda dare ya yi musu’ Amma ba su ji ba! Babban d’an mutumin ma ce musu ya yi ‘su saka a ransu inda ya kai Ma’a ba wajen da zai je ya fito ko da nan da shekaru goma bane ba!
Ya tafi kenan har abada shi zai
kawo k’arshensa, su zuba ido su gani!’.
Ganin mutanen masu taurin kai ne ya sanya aka hak’ura aka zuba musu ido kowa ya bisu da addu’a kawai sannan kowa ya ja y’ay’ansa samari Yara da y’an mata zuwa gida aka rurrufe koina dan sun san tabbas yau akwai world warr 3 a Unguwa Uku.
Dole ce ta fito da Dije daga gida dan har yanzu Baba bai dawo ba Ya Aminu shima kuma shiru gashi basu da ko sisi a gidan dan kud’in adashin Inna ma duk an had’a jiya ya tafi a asibiti, hakan ya sanya ta cewa Dije ta je gidan wata k’awarta a bayan layinsu ta karb’o mata ranchen dubu biyu ta kawo mata ta je asibitin kawai da kanta ta ga me yake faruwa.
Sun dai ji anata hayaniya k’asa-k’asa d’azu a gidan amma ba su san me yake faruwa ba da yake throughout yau d’in suna d’aki shiyasa ma Inna ta barta ta fita.
Ta karyo kwana kenan da yake gidan k’awar Inna a layin gidan mutumin yake ta hango Babban d’ansa ya tara samari yana ta cika baki da zage-zage! Har da cewa ‘Baya gari lokacin da abun ya faru ne shiyasa Ma’a ya samu har ya yiwa Mahaifinsa hakan sannan bayan ya dawo rashin lafiyar ubansa ce dama ta sa bai kula Ma’a tun a ranar ba amma yanzu kuwa tunda ya waiwayeshi Wallahi kashinsa ya bushe su saka a ransu ya tafi kenan har abada.’
A ranta ta ce “Allah ya sa! Ma’a ko masifa.”
Da gudu ta ga wata mota ta shigo cikin layin wanda hakan ya karkato da hankalin gaba d’aya jama’ar wajen…..da ikon Allah personal motar dpo d’in police station d’in da aka kaisu suka tuk’o, Oscar shi ke driving sai Scorpion da wani daban a gaban, yayinda shi kuma Ma’a yake a baya ya hakimce ya saka wani bak’in glass.
Waenda Allah ya bawa ikon ganesu kafin su k’araso ne suka kwasa a guje, wasu kuma basu ma san mai ya faru ba suna gani ana gudu suma suka hau gudun, ragowar samarin kuwa masu son ganin kwakwaf tsayawa suka yi har sai da Oscar ya k’araso da motar wajen ba tare da ya jira ya yi parking ko ya kasheta ba ya diro daga cikin motar k’ofar ma a wangale ya barta ya zaro wata zabgegiyar Adda ya shiga sauk’eta a kan duk wanda ya samu.
A take wajen ya hargitse in banda ife-ife babu abunda kake ji.
Fitowar su Scorpion ce ta sake hautsina wajen dan suma suna fitowa suka shiga sare-sare.
Tunda Dije take Allah bai sa ta tab’a ganin irin fad’an na su Ma’a ba sai yau, ta dai san d’an daba ne ya addabesu wani zubin har curfew suke saka musu a unguwa kuma babu wanda ya Isa ya fita har sai
sun janye curfew d’in sannan har hayar sa ake yi su je su yi kashe-kashe kuma a nan Unguwar tasu ma yana yi amma bata tab’a ganin su in action suna chachchakawa mutane wuk’a ba sai yau, shock da matsanancin tsoro da suka shige ta a lokaci guda na ganin yadda akeyiwa mutane kamar wasu kajin sallah ya sanya ta k’ame k’am a wajen ta gagara motsi, dama chan ita tana da tausayi shiyasa tun tana Yarinya take cewa ba zata iya yin Likita ba dan ba zata iya yanka jikin mutum ba….tun tana Yarinya lokacin ko layya ce ta zo duk tsagarancin Dije bazaka tab’a ganinta a wajen da ake yanka raguna ta je kallo ba.
Scorpion d’in ne ya dawo ya zo ya bud’ewa Ma’a mota tukunna ya zuro
k’afarsa ya fito daga cikin motar! Wanda fitowar tasa ta sake ruruta guje-guje da ife-ifen jama’a.
Direct wajen d’an mutumin ya nufa wanda har yanzu yake a tsaye a cikin riller gidansu ya saka sakata ta ciki yana waya da alama y’an sandan yake sake kira.
K’arasawarsa wajen ta yi dai-dai da k’arasowar Mahaifiyar saurayin, tana zuwa ta tsinka masa Mari ta ce “inace daga wajensu ya tsinko
ya taho amma shine ka tsaya a waje kake sake kiransu? Wuce ka shiga cikin gidan kafin su yi
maka illah!” Ita ba ta ma lura da Ma’a ba dan duk ta rikice sai da ta ji ya saka k’afarsa ya daki riller dai-dai wajen sakatar da wani irin mahaukacin k’arfi a take k’ofar mai raga-raga ta dare biyu.
Ihu ta saka ta fara rok’onsa amma ko kallonta bai yi ba ya sa hannu ya shak’o wuyan saurayin nan ya d’ago shi kamar wani kayan wanki ya fito da shi ya dire sa a gabansa.
Wani irin wutar bala’i da tsananin fushi da b’acin rai Saurayin ya gani a cikin kwayar idanun Ma’a ga wata masifar shak’a da aka yi masa da ta sanya yake ji kamar yanzu-yanzu zai bar duniya dan haka gaba d’aya sai ya fita a haiyyacinsa idanuwansa suka fara k’ak’k’afewa.
Kuka sosai matar take yi, cikin mad’aukakin tashin hankali ta fito daga cikin barandar gidan nasu ta zo ta fara k’ok’arin kwatar d’anta amma cilli d’aya Oscar ya yi da ita tunda ta tafi ta kifa ta kasa tashi sai wani irin kuka da ta dinga yi.
Wata zabgegiyar wuk’a Ma’a ya sa hannu ya zaro daga k’ugunsa tana wani irin kyalli ya d’aga sama ya kalleta!
A take uwar saurayin ta sake gigicewa fad’i take “A’a, A’a! A’a“ tana mai k’ok’arin tashi amma ta kasa dan a kan k’afarta ta fad’a.
Cikin saurayin Ma’a ya kalla kafin ya saita wuk’ar ya soka masa ita! Sai da ta lume ciki gaba d’ayanta. Tashi d’aya matarnan ta shak’i numfashin tashin hankali ta sume a wajen.
Ido cikin ido suke kallon juna shi da Saurayin nan wanda har yanzu bai cikawa wuya ba ga kuma wuk’a ya chaka masa a ciki yana k’akarin mutuwa yana kallonsa. Cikin wani irin zafin kai ya fara juyi da wuk’ar nan tana a cikin cikin saurayin a haka sai da ya yi juyin 360 da ita a cikin cikinnasa tukunna cikin wani irin zafi yana kallonsa ido cikin ido ya ce ”Ka yi kuskure! A kaff fad’in Unguwar nan Ana Malik! Kai a kaff garin nan ma Ana Malik!!Infact a Nigerian ma gaba d’ayanta i’m untouchable!!!
Ina so ka saka hakan a ranka ka dinga amfani da shi har zuwa k’arshen rayuwarka idan kuma Allah ya sa k’arshenka kenan Allah ya ji k’an ka.”
Yana gama fad’in haka ya sakeshi ya zare wuk’ar at the same time ai kuwa jini ya hau ambaliya fiye da farko yayinda saurayin ya tafi luuu ya fad’i kansa ya bugu a jikin dakalin barandar tasu.
Fad’uwar tasa ta yi dede da fad’uwar Dije wadda sai da ta gama juye fitsarin mararta a wajen tsabar tsoro tukunna ta tafi ta fad’i sumammiya a wajen.
Yana juyowa idanuwansa a kanta suka fara sauk’a ga fuskarta nan zagaye fayau cikin brown d’in hijabinta har k’asa.
A hargitse ya juya ya kalli Oscar cike da tashin hankali ya ce “me kuka yi mata?”
Ya yi masa tambayar yana mai nufarta.
Rufa masa baya ya yi yana yi masa bayani a kan ‘tun d’azu take tsaye yanzu kuma kawai ya ga ta fad’i, ai sun san ya yi musu iyaka da ita da y’an gidansu wallahi basu tab’ata ba!’
Sam Ma’a ba jinsa yake yi ba dan hankalinsa ya kai k’ololuwar tashi saboda yadda ya ganta a yashe a k’asa kamar marar rai!
Yana zuwa ya shiga duddubata sai da ya tabbatar babu wani rauni a tattare da ita tukunna ya kinkimeta ya nufi motar da suka zo
da ita gaba d’aya ya rikice sam ya gagara b’oye zalamarsa a kanta yau d’in dan kwana biyun nan dama kamar wani wanda aka yiwa xdubu na k’aunarta haka yake ji, komai da yake ji a kanta ya nunku bilaadadin.
Tunda ya kinkimeta su Scorpion d’in suka sunkuyar da kai, Sai da ya dakawa Oscar tsawa tukunna ya zo ya kunna motar suka ja suka bar wajen su duka hud’un.
Kwata-kwata tunanin Ma’a bai bashi ya je ya kaita gidansu ko ya kira wani nata ba dan a nashi ganin hakan ka iya janyo tangard’a da delay a had’uwarta da Likita..
Suna wucewa aka fara firfitowa ana dudduba mutanen da suke zuzzube a wajen cikin jini, mutane wajen ashirin ne suka ji rauni yayinda ake da tabbacin mutuwar d’aya dan a mak’ogwaro Oscar ya chaka masa wuk’a gashi idanunsa sun k’akk’afe suna kallon sama, wannan saurayin shima suna tunanin ya rasu dan ko shurawa bai yi ba.
Akwai cases da yawa irin haka har da wanda ya kai shekara biyar a hannu ana kan yi dan duk yadda aka kai ga jin tsoron su indai suka kashe rai ana iyaka bakin k’ok’ari wajen tsayawa a kan abun sai dai matsalar da ake samu itace idan anje sai a dinga danganta abun da Oscar yayinda shi kuma Oscarn yana da file ma a Dawanau! To da haka ake fakewa kuma har gobe an gagara kullesa a gidan mahaukatan where he truly belongs.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 10.
Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.
Da mugun gudu Usama ya shiga cikin gidan nasu yana haki hannunsa yana d’igar jini.
A hargitse waenda suke tsakar gidan suka taso aka yo kansa da tambayar ‘mai ya faru?’ Yayinda na cikin d’aki suka fara firfitowa…
Cikin haki ya ce “Su Ma’a ne suka kawo hari amma ni basu tab’ani ba garin gudu ne na fad’a a kan langa-langar da aka jide a k’ofar shagon Aliyu shine na ji ciwo.”
Cikin fad’a Iyya ta ce “Amma sai da aka ce kowa ya killace nasa ko? Garin yaya ya fita?”.
Cikin rashin fahimta Inna ta ce “mai ya faru? Fad’a ake yi?”.
Juyawa Iyya ta yi ta kalli Zainab ta ce “ke baki je aiken da na yi miki d’azu wajenta ba?”.
Turo Baki Yarinyar ta yi ta na guna guni.
Cikin taraddad’i Iyya ta rafka salati ta ce “yanzu a batun rai da mutuwar ne kika sako kishi da b’akin hali dan buhun ubanki?”
Ta yi maganar tana mai kai mata duka.
Cikin b’acin rai Ramma ma ta rankwashi kan Yarinyar ta ce “shegiya mai irin halin uwarta”.
Dai-dai nan kuwa Uwartata ta shigo….kamar yadda takeso ta dawo a gajiye hakan kuwa ta dawo dan Ya Muhammad bai dad’e da komawa barci ba da kyar da taimakon allurai, tun d’azu ya tashi Mallan kuma ya aiki Minu ya ce sai ta tayashi rik’esa, har gula sai da ta sha a ciki garin rik’esa. Gashi basu ci abinci ba wai duk su biyun azumi suke yi tun jiya suka cewa Inna kar ta kawo abinci shi kuma Ya Muhammad an hana sa cin abinci wai za’a yi masa wani gwaji ba zai ci abinci ba for 24 hours.
Wani irin takaici ne ya tasowa Inna na ganinta amma sai ta d’auke kai kawai.
Tana shirin yin magana Asaben ta ce “Ramma mai ya faru kike dungure mini kan y’a?”
Sai kuma ta yi tsaki kamar an tambayeta ta ce “ko da yake ba ta ke nake ba, duk a gajiye nake, Mallan da iyawa wai ai kwanana ne dan haka in je in tayashi jinya.”
Shiruuu, kowa ya yi yayinda wasu suka fara tunanin anya kuwa kan Asabe babu motsi?.
Tsaki ta sake yi ta kalli Zainab ta ce “zee d’aura mini ruwan wanka, in samu in yi wanka na yi sallah in huta”.
Iyya ba ta san lokacin da ta ce “ikon Allah” ba.
Shiruu tsakar gidan ya kasance har ta zo ta wuce su tana tafe a gajiye, sai kuma ta juyo ta kalli Inna wadda ta bita da kallo kawai, ta ce “Yauwa, shima Mallan d’in Ina ga gajiya ce ta tarar masa yanzu haka ma drip aka d’aura masa ya ce in sanar da ke”.
Duk yadda Inna ta so sai da ta ji wani irin zazzafan kishi ya taso mata, wato bashi da lafiya ba zai iya gaya mata ba sai k’anwar bayanta ce zai aiko ita zata gaya mata kuma daga ji ma rashin lafiyar tasa ba wata serious bace ba tunda gashi har y’ar tayin kwana yake nema amma ita ya gagara d’aukar wayarta…
Da sauri ta kawar da tunanin ta ce “tam” kawai daga nan ta juya kan Usama ta ce “ka ga Dije?”.
A take hankalin kowa ya koma kan Yaron.
Jinjina mata kai ya yi ya ce “eh, na ganta ana ta gudu ita kuma tana tsaye tana kallo”.
Dai-dai nan wata mak’ociyarsu mai suna Ladidi ta shigo tana rafka salati “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Yanzunnan labari ya iske ni Halimatu Ma’a ya yi garkuwa da Dije.”
Salati tsakar gidan ya d’auka ana tafe hannuwa yayinda Inna ta tafi ta zube ta zauna dab’ass! A dede k’ofar d’akinta inda suke dama ga damuwa ga bak’in ciki yanzu kuma ga mad’aukakin tashin hankali duk sun had’e mata waje guda.
************
Idan ana maganar Fada (palace) to tabbas wannan ta cika ta kai Fada har ta wuce hakan ma…Girmanta ya kusan kai girman wani tafkeken filin ball d’in, yayinda adon ta ya bambanta da sauran Fada dan ita nata ado da tsarin na musamman ne!
Kamar yadda bangon ko wanne d’aki da parlour na duk wani mai fad’a a ji a cikin masarautar ya kasance an yi masa ado da asalin gold, haka itama wannan Fada ta ke, sam! Girma da fad’inta bai hana an yi mata wannan ado na gold a bangonta gabas da yamma kudu da arewa ba.
Bayan ka shigo cikin asalin ginin na Fadar wanda Dogarai da sojojin masarautar suke tsaronta kamar rayukansu, sai ka bi ta k’ofofi uku tafka tafka waenda suma ake bawa tsaro ba na wasa ba tukunna za ka Isa Babbar tangamemiyar k’ofar da zata sadaka da main hall na Fadar!
Ana bud’e k’ofar bayi ne (masu lamba d’aya) sanye da jajayen kaya da bak’in d’ankwali mazan kuma da bak’ar hula a zaune sun d’an rissinar da kawunansu hannayensu hard’e a kan ruwan cikinsu…waennan bayi sun kai su d’ari biyu a zazzaune tun daga farko har zuwa kusan tsak’iyar Fadar a kan layi..layi wajen ashirin, layi goma a waje guda(b’angaren dama) layi goma a waje guda(b’angaren hagu) sai hanyar wucewa wadda ta kasance a saitin k’ofar shigowa a tsakiyarsu, haka nan suke zaune cikin tsananin tsari opposite kujerar Sarki wadda take a saman wasu kujeru guda biyu ta su Wambai da Waziri
kujerun da sai ka bi ta wani stairs mai wajen taku kusan goma waenda aka k’awata da lights da gold tukunna za ka k’arasa kujerun Wambai da Wazirin yayinda ta Sarkin take a saman tasu dan a k’alla itama sai ka bi ta stairs d’in da ke a tsakaninsu kusan guda goma tukunna za ka risketa a tsakiyarsu (chan sama) kuma ta fi ko wacce kujera girma a wajen dan ta ninka ta su sau biyar a tsayi da fad’i adonta kuwa tsayawa fad’a ma b’ata Baki ne……
Ta b’angaren dama chan k’asa gefe guda kafin ka fara taka stairs d’in da zai sada ka da kujerun Wambai da Waziri har a kai ga ta Sarki wata tattausar shimfid’a ce ta alfarma tafkekiya wadda a k’alla za ta ci zaman mutane saba’in, a kan shimfid’ar a kwai wasu manya-manyan pillows na sarauta na zama masu taushi sai k’anana guda-goma a zagaye da ko wanne d’aya….waenda a k’alla sun kai guda tara a kan dardumar. Opposite wannan shimfid’a gefen hagu nan ma wata shimfid’ar ce irinta sak a tsari da fasali.
Baya ga waennan Bayi wajen su d’ari biyu da suke zazzaune irin zama na k’ask’anci, da waensu Sojojin masarautar guda biyu a tsaye suna kallon kujerar Sarki sun saka k’ofar shigowa cikin Fadar a tsakiya babu kowa a cikin Fadar kuma baka jin k’arar komai sai na standing Ac wajen guda ashirin da suka yiwa fadar k’awanya.
Tafkeken Agogon fadar ne ya buga k’arfe tara dai-dai sai kuma ya hau k’irge daga d’aya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 23