ji ya fara wani irin zafii ga ife-ife suna jiyowa a waje ga result d’in ya Muhammad sam bai yi kyau ba, duk k’ok’ari da dauriya irin tashi bai san lokacin da hawaye suka zoba masa ba shaaa…
Da sauri ya kawar da kansa yayinda Iyya ta yi saurin barin wajen dan ya fiye mata ta shiga d’aki ta yiwa Kamalunta addu’a akan dai ta tsaya ganin wannan kayan k’uncin.
Iyya ta na wucewa Kaka ta ce “Wallahi tallahi ka ji dai na rantse maka ko kukan jini za ka yi yau sai ka zab’a musamman ma wannan tsinanniyar Yarinyar wallahi na gama ganinta a cikin gidannan.”
Kalli abunda ta yiwa Kubra ma jiya babu kyan gani! Yarinya gaba d’aya ta addabi kowa!” Ta yi maganar tana mai finciko Kubra sannan ta cillo musu ita da idonta guda d’aya (d’ayan ya yi kacha kacha yana ruwa) da saman goshinta a fashe wadda Mamanta ce ta kai k’ara jiya Kaka kuma ta ce kar su kulata su barta da su za ta yi maganin Dijen da zarar Mallan ya dawo. Tun ranar Kuburar take jinya sai yau ne da suka ji muryar Mallan uwarta ta fincikota suka fito dan ta ci alwashin ba zata bari wannan Abu ya tafi a banza ba wallahi.
A hankali a karo na biyu Inna ta sake ce masa “matsa in wuce”
Kuka Dije ta saka ta zo ta rungumeta ta baya ta k’amk’ame, a hankali Inna ta saka hannu ta b’amb’areta daga jikinta ta ce “kar ki damu za ki dinga gani na, ni zan tafi ke kam ki yi zamanki a nan dan babu wanda ya Isa ya kore ki daga gidan ubanki!”
Wata uwar gud’a Asabe ta rangad’a kamar ba ta san halin da ake ciki a Unguwar ba, ta ce “ai kuwa yau za ki ga wanda zai koreta dan sai ta fita!”
A zuciye Inna take sannan a fusace gata cikin tashin hankali kuma dama a k’ule take da Asaben wannan dalilin ya sanya ta juyo a fusace ta d’auketa da wani kalar rikitaccen Mari!
Da sauri Kaka ta yi kanta Mallan ya yi saurin shiga tsakani wanda hakan ya bata damar nufar k’ofa da hanzari wanda ba dan Kawu Isa yana a bakin k’ofar ba da tuni ta fice…..
Wani kalar ashar Asabe take dannawa Inna ana rirrik’eta tana fiffisgewa wanda inda ace daga ita sai Innar ne a wajen ta san k’aryarta ba ta isa ta yi mata hakan ba, ganin su Mallan ta san ba za su bari abun ya yi k’arfi ba ya sanya yau d’in take huce takaicin da ta dad’e tana nad’a.
Runtse ido Inna ta yi da k’arfi ta ce “ka bud’e min in fita na ce!!!”
Cikin rarrashi kawu Isa ya ce “idan kika fita Ina za ki je??”.
Duk yadda ta so rik’e hawayenta kasawa ta yi da kyar ta iya ce masa “kar ka sake yi min magana kamar wanda yake magana da wadda ba ta da wani gata sai naku”
“Yo kinada wani gatan ne bayan namu? Shegiya butulu tsintacciyar mage mabaraciya!!!”
Cewar Kaka.
Da sauri Mallan ya k’arasa ya jaa hannun Inna suka bar soron! Ya so ya sakata a d’akinta amma ta k’i.
Cikin b’acin rai abunda bai tab’a faruwa ba ya kalli Kaka wadda ta biyosu ya ce “A matsayinki na Mahaifiyata na zab’i in yi miki biyayya…Dije y’ata ce ba zai yiu in koreta ba dan amana ce Ubangijina ya bani, ke kuma gashi kina ik’irarin tsinantaka a kaina dan haka na kira Isa na shaida masa, da ni da shi mun yanke akan za mu aurar da ita ranar Juma’ar nan in sha Allahu ga Yusufa d’an wajen Isa daga nan ba zaki sake ganinta ba za ta tafi ta bar miki gidan nan!
Sannan magana ta biyu Kaka ki daina sheganta mini y’ay’a dan girman Allah, na yi abunda kike so na yi miki biyayya dan haka kema ki daure ki daina yin abubuwan da suke tab’a ni ko dan lafiyata.”
Yana gama fad’in haka ya juya ya wuce cikin d’akinsa ya rufo k’ofar….
Sai da Inna ta yi da gaske tukunna ta iya janyo numfashinta ya dawo jikinta, yayinda Asabe ta kwashe da dariya k’asa-k’asa ta ce “shegiyar Yarinya dama k’auyen ce ta kamace ki!!! Sai in ga ta Ina za ki zama barister”
Daga haka ta juya da sauri ta koma d’akinta dan ta ga babu Mallan a wajen tsaff Inna zata yo kanta.
Da kyar Inna ta dedeta kanta daga haka ta fara k’ok’arin fita daga cikin gidan kawai!!! Wannan karon
kuma haukace musu ta yi ta ce wallahi ko ta tsiya sai ta fita!!!
Gashi k’auri da ife-ifen waje sai k’aruwa yake yi.
Kopa d’in nan ce ta yi sauri ta afka d’akin su ya Muhammad ta shiga ta hau neman madarar bacci a kayan Usssy dan ta san ba zai rasata ba saboda ita ce favorite d’insa, ai kuwa ta samota, ta fito da gudu ta zo ta bayan Inna ta toshe mata hanci da ita, a take ta tafi ta sulale ta zube a wajen tana mai jin duniyar gaba d’aya ta koma mata upsidedown! A take ta
fara ganin mutanen wajen da su da muryoyinsu kamar slomo cartoon dan overdose Racheal d’in ta yi mata.
Duk cikinsu babu wanda yake cikin haiyyacinsu shiyasa suka gagara yiwa Racheal d’in fad’an abunda ta yi wanda ita take ganin dai-dai ne.
Sosai kunnuwansu suke jiye musu masifa da tashin hankalin da yake wakana a waje
Inna kuwa bayan slomo gaba d’aya komai juya mata yake yi gashi ta yi luuuuu amma kuma ba bacci ta yi ba sai dai hatta d’akinta sai kinkimarta suka yi suka kai ta suka ajjiye Dije tana biye da su kawai tana wani irin kuka abun tausayi.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 14.
Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.
Ba a dad’e da shiga da Inna cikin d’akinta ba jiniyar y’an sanda da ta y’an kwana-kwana suka karad’e unguwar.
Da gudu su Ya Kamal suka shishshigo gida dan har da sojoji aka zo kuma suna zuwa suka fara sakin harsashi suna kakkama jama’a, babu ruwansu da wanne b’angaren kake kawai danna duk wanda suka samu da makami suke yi cikin mota.
Ya Kamal a k’afarsa ya ji ciwo kawai, yayinda aka yanki Minu a hannu, Ussy kam sai da suka janyo sa da kyar suka afko cikin gidan tare da shi dan a buge yake kuma shima an sare sa. Ya Musa shima a hannu ne amma ba wani sosai ba, ya wuce gidansa, Sagir kuwa babu shi babu alamarsa wanda hakan ya sa Mahaifiyarsa ta zube a wajen ta shiga kururuwa gashi babu damar sake fita dan duk wanda ya bari sojojin nan suka kama shi to kafin a wanke ka a karb’o ka ma aiki ne dan ba wanda ma ya san waye ya kirawo su.
D’akin Inna Minu ya shiga yana shiga ya gansu Dije ta kama mata kai tana yi mata tofi…..
Da sauri duk suka kallesa sai
kuma Dije ta mik’e da sauri ta je ta fad’a jikinsa ta saki kuka sai kuma ta cika shi cikin hanzari ta wuce ta je ta d’auko wani clean d’ankwalinta wankakke ta zo ta fara nad’e masa hannunsa da shi wanda har yanzun yake d’igar jini.
Inna kam babu damar motsi sai binsu kawai da take ta yi da idanu.
Ganin yadda ta kasa motsi ya sanya ya nufeta a gigice yana tambayar Dijen “mai ya sameta”
Biyosa ta yi ta sake kama hannun nasa ta ci gaba da nad’e masa dan ta tsorata da yankar, tukunna ta shiga gaya masa duk abunda ya faru…..
Runtse idanuwansa ya yi da masifar k’arfi zuciyarsa tana wani irin tafarfasa….
Da kyar ya d’an yi controlling kansa sai kuma kawai ya kalleta cikin dakakkiyar murya ya ce “mai ya faru aka ce an yi garkuwa da ke garin yaya kika dawo har da allurar k’arin ruwa a hannunki??”
Kuka ta fashe da shi tana mai ci gaba da d’aure masa hannnun da ta gagara kammalawa har yanzun, sai da ya sake ce mata “eh!!”
Tukunna ta fara labarta masa komai.
A yadda Inna ta ke kwance ta fahimci komai kuma a take lissafin nata ya bata tabbas akwai wani abun game da Dije k’unshe a zuciyar Ma’ah, Minu kuwa fad’a ya rufeta da shi kamar zai cinyeta d’anya, fad’an da shi kanshi bai san dalilin yi mata shi ba!
Cikin kuka sosai ta ce “Ya Aminu dan Allah kar ka bari a aura mini Yusufa, bai yi karatu ba fa kuma k’auye za a kaini!”
Tsaki ya yi, cikin d’acin zuciya ya ce “Dalla malama ki daina kuka! Allah na tuba hauka ake yi da za’a aura miki mai mata har biyu? Karatun naki kuma fa!”
Shiruu ya d’an yi daga haka kuma kawai sai ya mik’e ya juya ya fita fuuuu kamar wanda zai tashi sama, wallahi idan Kaka bata yi gaggawar gyara halinta ta fita sabgar Mahaifiyarsa da k’anwarsa ba tabbas sai ya illatata sai dai duk abunda zai faru ya faru!!
Saboda ita haka nan kurum sai a cire Yarinya kamar Dije daga makaranta a aurar da ita a k’auye? Saboda tsabar cin zali!
Inaa wallahi ba zai yiu ba! Sai dai su bar gidan har da shi da Ya Muhammad.
Direct d’akin Mallan ya nufa amma bugun duniya ya k’i bud’ewa, Kawu Isa ma a d’akinsu ya yi masauk’i wanda Minun yake ji kamar ya rufesa da duka! Dududu fa d’an nasa ko sa’an Ya Muhammad bai kai ba amma har yana shirin yin ta uku tsabar kankanba shi kuma kalli da gani farin ciki ma yake yi……..
Sai bayan kamar awa biyu tukunna aka samu unguwar ta d’an lafa! Dan sosai abun ya munana….
An kama waensu yayinda aka mik’a deceased da injured emergency dake a Akth wanda su kansu Likitocin sai da suka tsorata!! Duba da yanayin al’amarin sauk’inta d’aya ma y’an sanda ne da kansu suka kakkawo su……Sojoji suna barin Unguwar aka fara fitowa ana bin bayan y’an sandan nan da suka tafi da deceased da injured, dan kusan za’a ce a kaff layin babu gidan da basu da missing.
Suna zaune a tsakar gida gaba d’ayansu kowa ya yi tagumi su Iyya suna ta tausar Maman Sagir suka ji bugun k’ofa!
Ita ta fara mik’ewa amma sai ta gagara nufar gurin ta zube a wajen ta sake sakin wani sabon kukan.
Ya kamal ne ya iya k’arasawa soron ya Isa bakin k’ofar ya bud’e, Mallan Manniru ya gani (Mahaifin Sumayya) tsaye sai kuma ya ga mutane suna ta nufar titi, cikin alhini Mallan Manniru ya ce “to Alhamdulillah da na ganka, ba ku dai rasa kowa ba ko?”
Numfashi Ya Kamal ya fesar kafin ya ce “ba mu ga Sagir ba”
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Mallan Manniru ya ce sannan ya ce “yi maza ka fito ka bi zugar chan, duk Asibiti za su wuce inda aka kai waenda suka ji rauni sosai, da waenda suka rasa rayukansu.”
A hankali Ya Kamal
ya sunkuyar da kansa wata kwalla ta zubo masa, kafin ya saka hannu ya goge ya ce “to”
Daga haka ya juya ya koma cikin gidan.
Kusan karo suka yi da duk jama’ar gidan a soro waenda suka yo kansa.
Sun riga sun ji dan haka ko wacce ta koma ta d’auko hijabinta aka fito aka nufi Asibiti, yau kam y’an gidansu Dije an yi had’in kai, dan karankatakaf d’insu ne suka tafi Asibitin nan banda Inna da Ussso, amma har Mallan wanda tunda ya ji shigowar su d’azu ya sake k’ulewa a d’aki sai yanzun tukunnna ya fito.
Unfortunately suna isa bakin emergency wata makwafciyarsu ta taho ta rungume Maman Sagir ta fashe da wani irin kuka wanda hakan ya fassarawa kowa halinda ake ciki dan haka duk suma sai suka fashe da kuka.
Cikin kuka matar take cewa “Sagir babu! Maman Sagir Sagir ya barmu, yanzunnan aka wuce da su mutuary…”
Yaraff!! Maman Sagir ta tafi ta zube a wajen sumammiya.
A take jama’ar wajen duk suka yi kanta, dan wajen ya cika taff mak’il da mak’ofta da y’an Unguwar tasu dama ana ta kuka ana lissafa waenda aka kashe, kusan a layin babu gidan da ba’a yi rashi ba a arean ma gaba d’aya za a iya cewa an tab’a ko wanne gida, gidajen da aka k’ona kuwa sun fi ashirin da yake irin k’ananan gidajen nan ne hakan ya sanya idan d’aya ya kama nan da nan sai na kusa da shi shima ya kama…..
BAYAN KWANAKI UKU.
Sai bayan kwana biyu tukunna aka samu aka gama cike-cike aka kakkarb’o gawarwakin daga mutuary aka yi musu sutura aka mik’a su gidansu na gaskiya.
Arear su Dije ya zamana gaba d’aya koina zaman makoki ake yi, ka je ka yi kaima a zo a yi maka haka rayuwar layukan Unguwar suka kasance a tsakankanin kwanakin.
Gidansu Ma’a kuwa tun a washegarin ranar aka zo aka fara gyara sai dai babu shi babu dalilinsa sannan sai da aka yi bincike tukunna aka gano ashe Samarin layin sojojin nan suka kakkame ba su Scorpion ba, dan haka duk aka sassakosu aka shiga neman su Scorpion d’in sai dai har yau ba’a gansu ba.
Mallan Idi shima sai bayan y’an sandan sun zo an kashe wuta tukunna aka tsinto shi a gidan wata bazawara nan kusa da su wadda Mijinta bai dad’e da rasuwa ba ya barta da y’ay’a bakwai ciki har da saurayi babba, suna ciki a d’akinta kan gadonta suna barci bala’in ya faru, wuta ta hau ci, shi dai ya iya tashi, ya afka bandak’i ko ta kanta bai bi ba yayinda ita kuma nata barcin ya yi nauyi shiyasa sai da wutar ta ci k’arfinta tukunna ta farka ta gagara tashi.
Wutar har ta shiga band’akin ta kama shi Allah ya kawo y’an kwana-kwana suka kashe ta..y’an sanda da y’an kwana-kwanan suna shiga suka fara jiyo ihunsa a band’aki dan haka aka duba aka fito da shi aka had’a da tawagar injured za a kaisu Asibiti amma babban d’an matar nan ya yi kukan kuran ya fincikosa ya hau kimarsa dama ya dad’e yana zarginsa da Mahaifiyar tasa.
Ba daban sojojin da suke a wajen nan ba tabbas da sai saurayin nan ya kashe Mallan Idi dan wani irin duka yake yi masa na hauka sakamokon yadda takaicin yadda makomar Mahaifiyarsa zata kasance duk dan saboda shi, idanunsa ruff suka rufe ya ma manta Malllan idi d’in uban waye ne a layin, sai kimarsa kawai yake yi kamar an aikosa.
Bayan an kwacesa an tsaya ana karb’ar statement kafin a wuce da su ya silala ya gudu, dan ya ji lokacin da aka ce ‘’Ga dukkan alamu Mama ta samu mummunan stroke ne dan a hannu Ma’a ya d’auketa ya wuce da ita, kamar ma ta mutu ne.”
Wanda yanada tabbacin indai
babu Mama a tsakaninsa da Ma’a to tabbas Ma’a ba zai yi wata-wata ba zai aikasa lahira……
Y’an layi kowa ya zuba ido yana jira ya ga matakin da za a d’auka dan an yi musu alk’awarin d’aukar mummunan mataki akan su Scorpion muddin aka kamasu, kuma sun zuba ido suna jira sai an gama ginin gidan da aka fara gyaraawa za su sake cinna masa wuta in sha Allah Ma’ah ya barsu kenan har abada.
Wani ikon Allah game da y’an gidansu Dije shine a washegarin ranar da Sagir ya rasu ne kawai ba’a yi fad’a a gidan nasu Dije ba, amma yanzu haka ma Ramma da Asabe duk jinya suke yi dan jiya da daddare dambe ya had’osu Ramma ta yiwa Asabe shegen duka ta wullata kan kaskon garwashin wuta hannunta ya k’one ita kuma Asabe da ta tashi ta d’auki tab’arya ta rotsa mata a hannu hannun ya karye.
Kaka ita kuma ranar sadakar uku da sassafe yau kenan wanda ya kama saura kwana d’aya tak d’aurin auren amarya Dije ta kira y’ay’an nata (Mallan da Kawu Isa) ta ce “idan fa Dije ta tafi bawai hakan yana nufin ta manta da cin kashin da Inna ta yiyyyi mata bane ba, dan haka ya had’a har da Inna ya kora.”
Wannan karon kam ba su goya mata baya ba sam! Dan ta ga fushin Mallan kam, k’arshe kuma suka had’ata da wata Antynta tsohuwa tukuff a k’auyensu ta tsawatar mata ta waya tukunna aka samu sa’ida.
Tun daga nan gaba d’aya Kaka ta rikice dan tabbas sai yanzu ta fahimci ta tafka babban kuskure da ta bar Halima a gidan d’anta har ta yi dogon zango ta tara y’ay’a haka, dan gashi gaba d’aya ta kanainaye gidan ta ko ina, ita kuma Asabe daga haihuwa d’aya tak ta ja ta tsaya, wanda a da Halimatu take yiwa gori sai da aka auro Asabe tukunna ta fahimci ashe Mallan d’in ne ba mai yawan haihuwa ba.
Ba ta son ta ba ta son jin ko da sunanta ne daga ita har y’ay’anta! Duk wani abunda ya shafeta bata k’aunar gani amma gashi kullum sai ta ganta ta gansu, ta san itace bangon su shiyasa yanzu da ta gaji ta kai mak’ura kawai take so ta yi
musu kwab d’aya dan ta
san idan ta kori Halima to kamar ta kore y’ay’an ne dan binta za su yi su je chan su shiga duniya, to amma kuma
gashi k’iri-k’iri ta yi falling flat akan face d’inta dan hatta kawu Isa bataga alamun zai goya mata baya ba shi da ba wani shiri suke yi da Innar ba, kar ma matarsa ta ji labari.
Sosai kan Mallan ya d’auki zafi kwana biyun nan, dan Kaka ta kunna masa wuta ba kad’an ba.
Bai yi karatu ba ko ajin boko bai tab’a shiga ba amma zai iya cewa shine ya sakawa Dije ak’idar son karatu a cikin ranta tun tana y’ar k’ank’anuwarta amma gashi yanzu k’iri-k’iri yana ji yana gani haka nan zai d’auketa ya kaita k’auye inda ya san in dai ta je to tabbas ta yi bye-bye da karatu kenan.
Dan ma dai Yusufa yana da addini kuma yana da k’ok’arin nema sannan Allah ya rufa asiri ya san ci da sha da sutura kam ba za ta rasa su ba in sha Allah.
An samu wani Babba a garin ya yiwa mutanen da abun ya shafa alkhairi sosai wanda rabin su duk k’in karb’ar uban kud’ad’en suka yi, dan washegarin ranar aka zo aka yi musu jaje aka rarraba musu kud’ad’e wai su gyara gidajensu, sanin da waensu suka yi kud’in daga d’aya daga cikin iyayen gidan Ma’a d’in ya fito dan a rufe musu Baki kuma ya gyara siyasarsa ya sanya suka k’i karb’a suka ce basa so sai an bi musu hakk’insu yayinda ragowar suka amshe a cewarsu raba arne da makami ibada ne.
Suna ta zuba ido su ji an cafko su Ma’ah da ikon Allah sai ga kira daga ofishin y’an sanda.
Limamin layi (Mallan) da mai Unguwa sai wasu dattawa guda uku ne suka wakilci kiran.
Ko da suka je sai da suka kusan yin ihu tsabar takaici da bak’in ciki da mamaki dan k’iri-k’iri ake so a yi musu tsakani kawai da su Ma’a a barsu abinda suka yi ya tafi a banza, wai ‘ai shima an k’ona masa gida kuma an kashe masa Aboki sannan yanzu haka Mahaifiyarsa tana kwance.’
Kamar ma laifin akan samarin layin ake so a d’aura wai ‘ai sune suka fara tayar da husuma’ Sannan aka ce wai ‘su Ma’ah ba su kashe kowa ba wasu y’an daba ne da ba’a san daga ina suka zo ba (Yaran Scorpion) suka cinnawa gidajen wuta suka yi b’arna…
Daga k’arshe dai Mallan ne kawai ya iya tsayawa ya ji k’arshen zancen ta inda aka yi musu gargard’in ‘babu su babu shi’ kowa ya yi harkar sa dan ragowar mutanen duk fushi suka yi suka fita, saboda a ganinsu hakan straight up rainin wayo ne kawai! Duba da yadda ko d’an Yaro mai tafiyar tatata idan ka tambaya a layin ya san waye Ma’ah to su kuma y’an sanda sun ce su kawo shedar wanda ya tab’a kashewa za a d’auki mataki sun kasa, dan wannan Yaron ma da ya yiwa juyin 360 da wuk’a a ciki an ci sa’a da Ikon Allah har yanzu yana icu kuma an ce ba shi bane ba Oscar ne ya yi aikin, wannan dalilin ya sanya kawai mutanen suka yi fushi suka fice daga ofishin y’an sandan ransu a masifar b’ace…….
Kamar yadda aka yi musu haka shima Ma’ah aka zaunar da shi aka yi masa tsakani da y’an layin
daga nan magana ta mutu da ikon Allah kamar ba a yi komai ba.
Jikin Mama babu kyau sam! Dan ta kwanta mummunar jinya kwarai, yanzu haka shirye-shiryen fitar da ita waje ake yi dan jinyar ba zata yiu a nan ba, wanda iyayen gidan Ma’a d’in ne suka d’auki nauyi..
He looks calm idan ka kallesa a ido amma fa shi kad’ai ya san me yake going through deep down, da mugun kyar yake iya rik’e kansa wanda yake jin kamar ba zai iya ci gaba da k’ok’arin holding kansa together ba dan tabbas jarumtarsa ta kusa k’arewa gashi idan ya tuna shine musabbabin halin da take a ciki yanzun sai ya ji kamar ya binne kansa.
Tun ranar da Mallan ya dawo daga asibiti ya fahimci Inna ta d’au zafi, dan bai had’u da ita ba sai ranar da ya sanar da d’aurin auren Dije tun daga nan kuwa bai sake sakata (Inna) a idanunsa ba, dan ko jiya da ya shiga d’akinta ma b’uya ta yi a cikin bargo gaba d’aya ta k’i yarda su had’u, ya san dai ya ci galaba a kanta tunda ya had’ata da mai unguwa ya kirata a waya ya hanata tafiya amma fa fushin da take yi da shi sosai yake tab’a shi…..
Dukda cewa y’an layin sun san baya nan hakan bai sa kowa ya hau masa sahun sallarsu ba a cikin mutane uku dattawa da suka riga su zuwa masallacin, kamar had’in baki.
Ana cikin gabatar da sallar Magrib an kusa tafiya ruku’un farko kenan kawai suka shigo shi da Scorpion da Oscar da wasu guda biyu daban waenda yanayinsu har ya ci uwar na su Oscarn.
Daidaita sahu suka yi suka kabbara sallah cikin nutsuwa kamar ba su ba.
Kafin a idar kuwa masallacin ya cika mak’il, kowa idan ya shigo ya gansu sai ya shiga shock tukunna kafin ya yi sauri ya tayar da ik’ama.
Ana idarwa aka fara kallon-kallo, da k’us-k’us….waensu su ce a rufar musu wasu su ce a barsu kawai da Allah dan ko dawowa daga jimamin b’arnar da suka yi ba’ayi ba gashi y’an sanda da kansu sun yi musu tsakani.
Farar shadda ce k’all a jikinsa yau abunda mutane da yawa za su ce basu tab’a ganinsa da shi ba wato manyan kaya, kamar ba shi ba ta baya idan bai juyo ba sai dai yana juyowa zaka fahimci waye shi d’in gashi yau idanunsa sun yi wani irin dafewa alamun ransa a b’ace yake kuma yana cikin damuwa sannan ya tamke fuska kamar wanda aka aikowa da sak’on mutuwa.
Har addu’a sai da suka yi tukunna ragowar biyun da suka zo da su suka mik’e suka fita Ma’ah shi kuma shi da Scorpion da Oscar suka k’arasa wajen da Mallan yake.
Diriricewa Mallan ya yi da farko, yayinda Kawu Isa ya tsaya kallon ikon Allah dan shi mamaki ma suka bashi!
Saboda fatar jikinsu kad’ai abun kallo da al’ajabi ce sakamokon yaddda take kacha-kacha abun kyankyami!
Ko ba’a fad’a masa ba ya san waennnan sune su Ma’a d’in da suka tashi kusan rabin Unguwa Uku kwanaki uku da suka wuce.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 15.
Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.
Sai da ya yi iyaka bakin k’ok’arinsa ya nutsu sosai tukunna ya ce “Barka da dare Baba”
Wani yawu muk’ut!! Mallan ya had’iye yana jin fad’uwar gaba matuk’a dan bai san me ke tafe da su ba. Da kyar ya tattaro kalaman ya samu harshensa ya furta “Barkanmu dai Ma’aruf, ya jikin Mahaifiyarka?”.
A hankali ya lumshe idanuwansa ya bud’e, k’irjinsa yana yi masa wani irin zafi, da kyar ya iya cewa “Alhamdulillah”.
Shiruu Mallan ya yi yana jira ya ji ko shi za su yi masa gaisuwa amma sai ya ji shiru.
Yana cikin wannan tunanin ya ji Ma’a ya fara magana cike da kwarin guiwa sannan babu wani kwana-kwana…..
“Na san ka riga ka sanni ka san iyayena, na san a musulunce idan mutum ya ga Yarinya yana so to iyayenta ya kamata ya fara zuwa ya nemi izini a wajensu kafin ita, hakan ita ce kamala.
To
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 23