Share this page
musu inda ya yi parking. Murmushi Inna ta yi ta ce “ba komai ku je zan k’araso ni.” Shima sai a lokacin lissafinsa ya bashi baza ta iya ta bisu a machine d’in ba dan haka ya wuce ya tarar mata napep ta shiga ya biya kud’in suka wuce. Dije ji tayi kamar ta bita su tafi a kan cinyarta amma Napep d’in a cike take tap da mata biyu da y’ay’ansu Innar ma da kyar ta samu waje. Sai da ya ga wucewarsu tukunna ya juyo ga Dije wadda ta diririce a take ta hau kame-kame. Murmushi kawai ya yi a ransa yana mamakin yadda duk suka sauya daga ita har Innar kamar ba su ba. Ko da yake ya san in komai ya wuce za su dawo kamar yadda suke a daa in sha Allah idan komai ya yi settling hankali ya kwanta dan mai hali ba ya fasawa. A ransa ya ce “zan sha daru!” Fuskarsa tana baiyyana murmushin da yake nuni da nishad’in da zuciyarsa take a ciki. “Mu je ko?” Muryarsa ta katse mata hanzari. A hankali ta sake sunkuyar da kanta k’asa ta juya ta wuce inda ya nuna musu machine d’in nashi. Sai da ya hau tukunna ya karkata mata itama ta hau sannan ya kunna suka wuce, yana jin yadda ta matsa sosai chan k’arshe duk dan kar jikinta ya gogi nashi. Kad’an ya rage bai fashe da dariya ba lokacin da akazo wajen speed bumps dan sosai ta saka hannayenta a tsakankanin k’irjinta da bayansa yadda k’irjinta ba zai bugi bayansa ba. Har suka k’arasa gidan babu wanda ya cewa d’an uwansa k’ala! Yana sauk’eta ta fara k’ok’arin shigewa cikin gida…har ta hau kan d’an dakalin k’ofar gidan nasu ya yi sauri ya ce “Khadija” yana mai daidaita parking d’in mashine d’in nasa. A hankali ta ja ta tsaya kafin ta juyo, a take ta ji gabanta ya yanke ya yi wani irin mahaukacin fad’uwa sakamokon idanu biyu da suka yi da Ma’ah tsaye a bayansa. Idanuwanta ne suka wani Irin ciccikowa k’irjinta ya hau dukan uku-uku jikinta ya fara karkarwa tana mai jin wata kalar tsoro da tsanarsa suna lullub’eta. Ya kafeta da idanuwa sam ko kyaftawa ba yayi kuma bai yi motsi ba sannan bai ce komai ba yana nan a yadda yake wanda hakan ya sanya ta fara tunanin ko dai Aljani ne dan ita a iya saninta ma Ma’ah d’in baya Unguwar baya ma garin. Karkarwar jikinta ne ya k’aru gashi tsigar jikinta ta fara tashi a ta sakamokon kallon k’urillar da yake yi mata da taimakon hasken kwan fitilar nepan da ke a k’ofar gida, ga wani irin tsoro da fargaba dan haka ta yi sauri ta juyaa zata shige cikin gida ita sam ta ma manta da Ya Kamal a wajen wanda ya k’araso izuwa gareta ya tsaya yana kallonta yana mamakin yadda jikinta ke karkarwa haka tashi d’aya. Caraff! Ya yi ya ruk’o hannunta da sauri ya juyo da ita wanda hakan ya sanya Ma’ah d’in ya yunk’ura kamar zai yi kansu sai kuma ya d’an dakata. A hankali yana kallonta ya ce “mai ya faru? Ba ki da lafiya ne kema?”….. Magana Ya Kamal yake yi mata amma kwata-kwata hankalinta baya a garesa dan haka bama ta jinsa gaba d’aya idanunta da hankalinta suna a kan Ma’ah wanda take hango tsantsar b’acin rai da tashin hankali a cikin kwayar idanuwansa…Ya Kamal yana da kirki fiye da zato ba zata ce tana son shi ba a yanzu dai kam amma ta san zata so shi a gaba a matsayin Mijin aurenta! Tabbas idan wani abu ya same shi ata sanadiyyarta to bata jin za ta iya d’auka! A hankali ta ce “Astaghfirullah” sai kuma a take hawaye shaa suka kwace mata. Rikicewa ya yi ya shiga tambayar ta ‘mai ya faru?’ wanda hakan ya sanya hawayen suka k’ara dad’uwa kamar an kunna famfo. Ganin yadda jikinta ke karkarwa gashi sai kuka take yi ne ya sanya kawai ya janyota ya saka ta a jikinsa yana bubbuga bayanta alamun rarrashi. Da wani Irin mugun speed Ma’ah ya juya ya bar wajen kamar walk’iya……. Da kyar Dije ta iya cewa “Ya Kamal mai ya sa ka yarda ka aureni? Kar wani abun kaima ya sam…” Shiruu ta yi ta kasa ci gaba da maganar saboda yadda kuka ya sake taho mata da k’arfin gaske mai yawa. Bai san lokacin da murmushi ya sub’uce masa ba, kenan ta damu da shi…gashi har tana kuka bata so wani abun ya same shi kenan. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce “Khadija babu abunda ya Isa ya sami bawa sai da izinin Ubangiji, Ma’ah bai Isa ya yi mini komai ba sai abunda Allah ya riga ya rubuta kuma ina so ki saka a ranki ma ba shine yake kashe waenda aka yi baikon ki dasu ba, kar ki bari nauyin guilt d’in kowa ya hanaki yin walwala, kin ji ko?” Ya yi maganar a hankali cikin sake sakata a cikin jikinsa wanda hakan da ya yin ne ya sanya ta tuna a ina take dan haka ta yi saurin jaa daga jikinsa ta matsa gefe sosai. Murmushi ya yi ya sake kamo hannunta a karo na biyu ya ce “ki kwantar da hankalinki, kin ji ko? Sannan kar ki tab’a bari guilt ya yi tasiri a kanki zai tarwatsa miki rayuwa ne, ki yi min wannan alk’awarin.” A hankali ta jinjina kanta tana mai dudddubawa ganin bata ga Ma’ah ba ya sanya ta d’an nutsu bayan ta saka a ranta maybe ko kwakwalwarta ce take yi mata gizon sa. Juyawa ya yi ya kalli inda take kallo ganin bai ga kowa ba ya sanya ya kawar da tunanin ya ce “gobe da sassafe zan tafi Minna, Iyya ta ce in je in nema mana inda za mu zauna sannan in sanarwa k’aninta halinda ake ciki (in person) tukunna, dan daa tare zamu tafi to amma ta san za su ce suna so su zo su d’aukeki hakan babbar Al’ada ce a garemu dan haka baza su so ta sub’uce musu ba… In sha Allahu ba zan wuce 1 week ba zan dawo tare da su sai mu wuce ko? Zan had’o miki har da lefen ki in taho miki da su in sha Allah.” Ya k’arashe maganar yana murmushi yana kallonta. A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa sosai sannan ta ce “Allah ya kiyaye hanya, sai ka dawo.” Jinjina kai ya yi ya ce “za mu dinga waya ta wayar Inna. Ba zan yi miki alk’awarin waya yanzu ba saboda akwai abubuwa da yawa a kanmu amma idan muka yi settling kika ci gaba da makarantar a chan zan siya miki in sha Allah.” Jinjina kai ta yi ta ce “na gode” Har zata wuce sai kuma ta ce “Allah ya tsare hanya.” A hankali ya ce “sai na dawo” Sai kuma ya kamo hannunta ya yi kissing wanda hakan ya sanya ta d’an zabura har ta so bashi dariya sannan ya zaro dubu goma dama da ya yi niyyar bata kafin ya wuce ya ce “gashi ki rik’e a hannunki, ko?” Da kyar kuwa ta karb’a tukunna ta wuce ciki jikinta sanyi k’alau!……. Bata yi tunanin tadda kowa a tsakar gidan ba dan 12 ma ta kusa, amma tana shiga ta tarar da Rakiya da Kubra da Maman Fati suna ta k’us-k’us. Tana jin Rakiya tana cewa “Wallahi har da kiss, hmm Yarinyar nan ai ta cucesu ko da ba a kashesa ba ya kwashi ragowa, ki ga fa yadda take nuna tana cikin damuwa amma ta kasa hak’ura dan bala’i a k’ofar gida fa.” Sarai kuma ta san sun lura da ita sun ga shigowarta zuwa yanzu. Kubra ta ce “yo abune an riga an saba, kinga kuwa ai ba za a iya d’aga k’afa ba.” A take duk suka kwashe da wata y’ar iskar dariya kamar ba dare ba. Har zata kula su sai kuma kawai ta rabu da su ta yi shigewarta cikin d’akinsu zuciyarta a cunkushe……….. Washegari da sassafe sama-sama Inna ta ji Kaka tana yiwa wata mata interview…tsabar matar ta raina mata hankali wai a Jigawa aka haifeta iyayenta duk sun rasu a chan, achan ta taso sai dai bata da aure yanzu Mijinta ya rasu ya barta ita da y’arta d’aya Saddik’a, amma wai ta fad’i sunayen unguwanni uku a garin Jigawan ta gagara!. Jin da Inna ta yi Kaka tana shirin bata makulli ne ya sanya ta yi wuff ta fito, suna had’a idanu da matar ta ji tsigar jikinta ta wani tashi yaaammmmm! Gabanta ya yanke ya fad’i. Da sauri ta yi ta’a’uzi ta shiga karanto sunayen Allah tukunna ta d’an nutsu dai-dai Kaka ta mik’a mata makullin ita kuma ta mik’o mata kud’i za a yi hannun kuturu da makaho. Da sauri Inna ta k’arasa ta wafce makullin ta tura mata hannunta jikinta mai rik’e da kud’in ta ce “Malama tashi ke da y’artaki ku fice daga gidan nan bama son rainin wayo.” K’urrrr! Matar ta yi mata haka itama Inna ta yi mata k’urrr da nata idanun duk da kuwa yadda take jin fargaba da tsinkewar zuciya amma bata janye idanunta a cikin na matar ba sai ita matar ce ta janye nata idanun tana mai mamakin Inna. Mari! Kaka ta kawowa Inna a fusace ta yi saurin gocewa cikin fushi ta ce “dan ubanki har yaushe kika fara shiga sabgata a cikin gidan nan?. Ko da yake baki ma da uban ai ballanta idan an zage shi ki ji haushi. Ba ni makullin nan kafin mu kwashi y’an kallo ni da ke da asubar farin nan.” Ta k’arashe maganar tana mai daka mata wata uwar tsawar. A take sai Inna ta ji duk ta muzanta…Tabbas kam bai kamata ta shiga harkarta ba, bai ma kamata ta fito ba bama ta san me ya fito da itan ba. To amma kuma ai dai matar tare da su zata zauna a cikin gidan dan haka idan ma wata annobar ce ai abun har ita ya shafa…. Har ta yunk’ura zata yi Magana sai kuma wata zuciyar ta ce mata ‘ta bari kawai ta samu Mallan da maganar, idan ya ji sauk’i, dan ta san tunda ta nuna bata son matar to ko aman wuta aka ga matar tana yi Kaka sai ta barta ta zauna a cikin gidan ko dan ta k’untata mata! Dan haka yanzu ko ta yi wani abun ma a banza. Dan haka gara ta bari Mallan ya dawo ya bincika ya gano wacece ya yiwa Kaka bayani cikin salama a sallameta dan bata da tantama tabbas matar nan ba ta kirki bace ba…… BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 22. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Saboda hatta y’ar da ta zo da ita kana gani ka san ba tata bace ba, dan babu kama ko kad’an gashi kana kallon Yarinyar tashi d’aya zaka fahimci a tsorace take. Nufota Kaka ta yi a zuciye dan haka ta mik’a mata makullin kawai da sauri ta juya ta wuce d’akinta tana jinta tana ta zage-zage tana goranta mata har da cewa “shegiya, ke da ba kya aikin fari ballatana na bak’i daga ke har y’ay’anki, idan ba a karb’i kud’in nata ba uban waye ne kike tunanin zai biya ragowar kud’in asibitin Mallan?” Ita dai Innaa bata biye ta ba ta yi wucewarta ciki abunta… Ita kanta Kaka tunda Matar ta tare ta a k’ofar gida tana shirin shigowa (dawowarta daga asibiti kenan) gaba d’aya ta ji matar bata yi mata ba. Dalilin da ya sanya ta amince ta karb’i matar kud’i take da buk’ata ne urgent na treatment d’in Baba gashi ko kwayar shinkafa basu da ita shiyasa ma ta karb’i na wata uku ta ce mata ‘akwai mai d’akin ta yi tafiyar wata hud’u ne’, da zummar ko a ranar idan ta sami kud’i zata bawa matar ta ce mata ‘ta tashi ga mai d’aki tana zuwa’, to amma yanzu kam ta chanja shawara dan wallahi tunda Inna ta nuna bata son matar to dole sai ta zauna a gidan har zuwa lokacin da zata gaji ta tafi dan kanta. Ya zama dole ta nunawa Innaa bata fa da wata fada a gidan Mallan, sune da gida!. Dije tana jin duk wani abunda yake faruwa amma ta gagara tashi ma ballantana ta fito sakamokon wani irin rikitaccen tsoro da fargaba da suka lullub’eta tun asubah yanzu kuwa suka nunku ko motsi ma ta kasa yi, sai rawar sanyin da ta soma yi daga fitar Inna zuwa yanzu zazzab’i-zazzab’i yana shirin lullub’eta. A kumbure Inna ta dawo cikin d’akin tana ta kwafa. Sai da ta zauna tukunna idanuwanta suka sauk’a a kan Dije. K’ura mata ido ta yi sai kuma ta k’arasa gareta sannan ta ce “lafiyanki kuwa?” Dama tun d’azu ta lura da yanayinta musaman ma da Ya Kamal d’in ya yi musu sallama kafin ya wuce masallaci dan daga chan kawai ya wuce Minna d’in….. Wani murmushi Inna ta d’anyi duk da kuwa Itanma a tsorace ta ke amma sai ta yi k’ok’arin aro jarumta ta shiga kwantarwa da Dijen hankali….. Sai da Inna ta tabbata Dije ta d’an nutsu tukunna ta ce mata ta je ta ta gaida Iyya. Da “to” kawai ta amsa mata ta tashi ta saka hijabinta ta fice zuwa d’akin Iyya. Dai-dai wannan matar sabuwar zuwa ta fito da wasu kwalaye a hannunta alamun kimtsa d’akin nata take yi. Cike da shishshigi ta ce “A’a y’an mata kema a nan d’in kike? Zuwa anjima dai duk zan lellek’a mu gaggaisa a san juna a sassaba.” “Eh” kawai Dije ta ce mata daga nan ta shige d’akin Iyya tana mai jin haushin matar ganin yadda ta k’ura mata idanu kamar wata mayya. Cike da kulawa Iyya ta amsa gaisuwar tata tana ta janta a jiki a nan ma ta yi breakfast sannan ta fito…dan dagewa Iyyan ta yi ta ce ‘sai ta ci in kuma ta k’i to zata d’ura mata ne, ita da ya kamata su sake sabawa amma sai kuma ta fara ja baya da ita, gara ma ta sake dan sam ba zata lamunta ba.’ Sai da ta ga ta sake da ita sun yi hira tukunna ta yarda ta barta ta fita…da kallo ta bita har ta fice fuskarta d’auke da murmushi, tana fita wayarta ta d’auki k’ara dan haka ta mik’e ta k’arasa ta amsa kiran da sallama…. Tana shiga d’akin nasu ta tarar da Inna ta aika Umar ya je ya siyo musu y’ar tsala ta naira d’ari amma halin Inna na kyauta har Umar d’in sai da ta ajjiye ta bashi yake zaune yana ci ga na Dije itama ta ajjiye mata amma ita bata ajjiyewa kanta ba, dama saboda Dijen ne ma ta siyo dan ta san tana da ulcer. Murmushi kawai Dijen ta yi ta nemi waje ta zauna. Tana zama Inna ta ce “ga abincinki nan, ki d’auka ki karya, mu ga kuma mai anjima za ta bayar.” A hankali ta ce mata “na ci abinci fa a wajen Iyya.” Kama Baki Innaa ta yi kawai ta tsaya tana kallonta, wanda yadda ta yi d’in ya sanya Dije yin dariya ta ce “Wallahi babu yadda ban yi da ita ba amma ta ce sai na ci, k’arshe ma cewa ta yi in ban ci ba sai ta d’ura min wai ya kamar ban d’auketa uwa ba. Numfashi Inna ta fesar ta ce “Allah ya saka” Daga nan ta yi shiruu ta shiga tunanin…. Ganin tunani da k’unci yana shirin maye gurbin y’ar rahar da suka samu kansu a ciki yanzun ne ya sanya Dije ta mik’e ta je ta zauna a kusa da ita ta d’auki y’ar tsalar ta gutsira ta kai bakinta, murmushi Inna ta yi ta bud’e bakin ta saka mata a ciki ta shiga taunawa a hankali sai da ta had’iye tukunna ta ce “yanzu idan kika tafi waye zai dinga bani abincin irin haka?” Kamar wadda ta ke jira tashi d’aya hawaye suka b’alle mata sai kuma ta tafi jikin Innar ta fad’a ta fashe da wani irin kuka. Hatta Umar wanda ke a d’akin sai da kwalla ta zubo masa dan shima ya san idan Dijen ta tafi zai yi missing d’inta. Suna a haka Minu ya shigo cikin d’akin bakinsa d’auke da sallama. Da farko ya yi tunanin wani abun ne ya faru dan haka ya k’arasa da sauri yana mai tambayarsu “mai ya faru?” Sai kuma ya fahimci dalilin kukan nasu dan haka shima a take duk sai jikinsa ya yi sanyi. A hankali ya nemi guri ya zauna a gefenta, ya zamana shi da Inna sun sakata a tsakiya tukunna ya shiga lallashinta shima zuciyarsa ba dad’i. Sai da ta d’an yi shiru tukunna ya kalli Umar wanda fuskarsa ta yi dagaje-dagaje da hawaye ya yafito sa. Sai da ya zo ya goge masa hawayen tukunna ya zaro d’ari uku a aljihunsa ya basa ya ce ‘ya je ya siyo musu bredi su karya’, da sauri Inna ta ce “ai mu mun ci abinci” Amma still Minu ya ce “eh ya siyo ni zan ci in ya so sai ku ajjiye na san zai yi amfani.” Shiruu d’akin ya kasance bayan fitar Umar kowa da abunda yake tunani a ransa, kafin chaan Inna ta ce “Ba a yi muku abin karin bane?” Numfashi ya fesar sannan ya ce, ta yi masa fanke da kunu, yana cikin napep d’in Ya Musa ya shiga wanka ne yana fitowa za mu wuce.” Sai kuma ya yi wani murmushin takaici kafin ya ce “ni, ta ce idan na ci Allah ya Isa bata yafe ba, wai d’anta kad’ai ta yi mawa. Shiyasa na ke so in karya a nan dan na san Baba dole zai d’ura min kuma maybe ya ce in rantse akan na karya idan na ce masa na k’oshi.” Shiruuu duk suka yi chaan Inna ta ce “Allah ya kyauta.” A hankali Minu ya zaro kud’i dubu uku had’e da dubu biyar itama an had’eta waje d’aya ya dunk’ule ya ce “gashi” shi ya ma manta bai had’e kud’in ba a yadda aka bashi a rabe a haka ya bata duka dan ya yi alk’awarin ba zai bawa Kaka ba. Hannu Inna ta saka ta karb’a a lokaci guda tana kallonsa ta ce “daga ina?” Bai kalleta ba dan ya san zata fahimci wani abun ya ce “Mallan ne ya ce a kawo muku, jiya wani Abokinsa ya zo ya duba shi shine ya bashi duba ashirin, mun kammala biyan komai ragowar kuma ya ce in kawo miki.” Warwarewa ta yi ta shiga dubawa, dama tunda ya k’i kallonta ta san akwai abunda yake b’oyewa. Dan haka tana gama dubawa ta kallesa ta ce “Ungo kaiwa Kaka nata” Juyowa ya yi da niyyar yin musu ya ga ta had’e rai tamau! Cikin b’acin rai ta sake mik’a masa ta ce “Ungo na ce!” Ba dan ransa yana so ba ya karb’a ya mik’e ya fita. Daga nan cikin d’akin, su Inna suna jin yadda Minu yake ta rafka sallama amma an k’i a kulashi sai chaaan! Su har ma sun cire ran zata fito sai gata ta fito tana cewa “Halima tana bi na bashi ne da zaka zo ka isheni da sallama? Sannan har yanzu baku gama munafurcin da ka shige d’akin kuke yi kai da uwartaka da k’anwar taka ba ka wuce ka kai abincin ba??”. K’udin hannunsa kawai ya mik’a mata dan a k’ule yake da ita matuk’a idan ya ce zai bud’e Baki ya kulata tabbas ba zata yi kyau ba. “Bebe ka zama ne? Ba zaka bud’e Baki ka yi min bayani ba dan uwarka!” “Mallan ne ya ce a baki” Haka kawai ya ce da ita kansa a gefe dan ko kallonta bai ya son yi. K’uraa masa ido ta yi ranta na gama b’aci zuciyarta ta shiga tafarfasa kafin chaan ta ce “sai da kuka gama k’us-k’us tukunna za’a wani kawo min kud’i? To ku je ku rik’e ku ne matsiyata wallahi! Sannan ka cewa uwartaka na ce dan ubanta ta yi kad’an d’ana ya bata kud’i ya ce ta bani idan zai bani abu sai dai hannu da hannu ita ba ta Isa ko da sani ne ta yi ba! Dan haka koma wanne k’ullin kuke shirin k’ullawa ya tsaya a iyaka kanku….ka koma mata da tsiyarta ta had’a ta rik’e chaan itace talaka. Kuma wallahi ta sake gwada min wannan shirmen sai na bata mamaki.” Shiruuu suka yi kowa ya kasa cewa komai, a haka Minu ya shigo a zuciye ya same su kamar zai fashe. Ba wanda ya kulashi ya k’arachi masifar sa shi kad’ai ya juya ya fita kamar zai tashi sama, bayan ya bawa Inna kud’in ta k’i karb’a itama ta ce ‘ya kaiwa Mallan d’in in yaso sai ya bawa Kakar da hannusa kamar yadda ta ce.’ Yana fita Inna ko bi ta kansu bata sake yi ba ta kamo hannun Dije ta shiga yi mata nasiha…… Sosai ta nutsu tana sauraron Innar kamar daga sama suka ji salatin Maman Fati. A hargitse duk suka firfito, a take gabansu ya yanke ya fad’i a tare rassss!!! Sakamokon ganin k’ofar d’akin Iyya da suka yi cike taf da jama’ar gidan anata lek’awa ciki ga waya kare a kunnen Maman Fati tana cewa “ga dai number nan da ta kirata last ta shiga, bari mu ji mai ya faru haka ya firgitata har ya kai ta ga suma Allah dai ya rufa asiri, ya sa ba wani abun ne ya samu Kamal d’in ba.” Dai-dai nan su Gwaggo suka fito da Iyya wadda take a sume suka shimfid’eta a tsakar gida (kan tabarma) suka shiga yi mata taimakon al’ada na gaggawa. Dishi-dishi Dije ta fara gani k’afafuwanta suka shiga karkarwa sosai dan kana ganinta zaka shaida hakan. “Ameen wa alaikassalam, bawan Allah ka kira wannan number mun zo mun samu mai wayar da wayar a hannunta a sume, lafiya dai ko?” Muryar Maman Fati wadda Dije take iya jiyota a chaaaan nesa sama-sama ta karad’e gidan. Salatin da ta saka ta fashe da kuka ne ya sanarwa kowa halinda ake ciki! Daga nan ita dai Dije duhu ne ya maye gurbin ganinta kunnuwanta suka yi wani irin dummmm! Ta tafi ta sulale ta fad’i a wajen sumammiya. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 23. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Rabon da hawaye su zubo daga cikin idanuwansa har ya manta!… Sosai kansa yake wani irin sarawa zuciyarsa tana bugawa da k’arfi da k’arfi yana jin tashin hankalin da bai tab’a tsintar kansa a ciki ba….Bak’in ciki danasani da kuma tashin hankalin da yake ciki a yanzun sune suka taru suka bayarda gudummawa har hawaye suka samu damar zubowa daga cikin idanuwansa. A hankali wani Abokin huld’ar tasu ‘Tiger’ ya ce “Dama na dad’e ina gaya maka mutanen nan duk bakinsu d’aya siyasa ce kawai ta sanya suke rainawa mutane hankali. Kai kuma da ka fahimta, ka je ka gansu ka kuma ji abubuwan da suke tattaunawa Ma’aruf kamata ya yi ka bar gurin ka zo a san abun yi ba wai ka tsaya biyesu ba! Yanzu wa gari ya waya?”. Da wani irin masifar k’arfi ya runtse idanuwansa jijiyoyin kansa suka sake baiyyana fiye da daa, bai tab’a tunanin akwai abunda zai tab’a d’aure masa kai irin wannan ba! Adadin y’an daba kai har ma da mutane waenda suke a k’ark’ashinsu da suka rasa rayukansu a ta sanadiyyar rashin jituwarsu baza su k’irgu ba! Amma wai it turns out to be ashe su d’in best friends ne saboda siyasar su ne ya sanya suke pretending suke yin hakan, sannan dan ya nuna musu b’acin ransa har suna da guts d’in da zasu hana shi Mahaifiyarsa wadda ko motsi bata iya yi bama ta san waye a kanta ba! Tabbas yau za’a mutu! Dan muddin ya gama tabbatarwa Maama bata cikin gidan nan wallahi sai ya fasa gas a ciki uban kowa ya mutu!. Cikin b’acin rai Scorpion ya ce “ai kuwa sun janyowa kansu bala’i dan yaudarar mu da suka yi da abunda suka yi na b’oye Mama da kuma kisan da suka saka aka yiwa Oscar wallahi wallahi ba zai tab’a tafiya a banza, sai na lahira ya fi su jin dad’i” A d’an fusace Tiger ya ce “Au inda ka sha da kyar nan zaka koma gaba gadi? Scorpion sojoji ne suke gadin mutanen nan masu amfani da harsashi waenda kafin ka k’arasa sun d’aukeka da bindiga kamar yadda suka yiwa Oscar, ka tsaya ka nutsu. Mu rabu da su for now mu san abun yi tukunna. Sannan batun gawar Oscar inaga gara kawai mu bar musu, suma ai musulmai ne na tabbata baza su tab’a barinsa a haka ba

Chapter 17 of 23