mai laifin za ta yi zaman sulhu da shi su basu wata babbar Sarauta shi kuma ya karya asirin da ya yi dan tabbas irin wannan asirin tare ake had’osa da makarin sa guda d’aya tak! Dan haka ta san za a dace, amma yanzu kam tabbas ita kanta ta fara sarewa daga tashin k’anin nata sarki Zainul Abiddeen.
A hankali ya saki labulen d’akin bayan ya gama k’are musu kallo ya juya ya kalleta. Zaune take ta d’aura k’afa d’aya kan d’aya tana kallonsa, kallon da ya kasa tantance ma’anarsa.
Yana shirin yin magana ta rigashi ta hanyar cewa “Ka je ka rarrasheta mana! Na san kukan nata har cikin ranka kake jinsa.”
Wani kalar murmushin gefen Baki ya yi wanda ya k’ara masa asalin kyau da kwarjini kafin ya dawo ya zo ya tsaya ta bayanta ya kama kafad’unta ya ce “kishin nawa da ake yi har ya kai haka?”
“Bakinta ta tab’e ta mik’e ta tsaya sannan ta ce “ya batun Jakadiya? Kun yi waya?
Dan ni ba zan d’auki risk irin wanda waennan suka d’auka ba gaskiya, yanzu inda ace wani ya gansu a filin kafin su bar wajen ai da al’amari ya b’aci. Sannan na tabbata ba duk wanda ya samu leakage suka samu ba, zaka ce na gaya maka dole wani sabo zai fito a gaba.”
Kamota ya yi ya zagayo da ita ta dawo gabansa ta tsaya, a hankali ya saka hannu ya shafa soft kumatunta da kulawa ya ce “wa kuma za ki kashe bayan wanchan ba shi da maraba da gawa”
Murmushi ta d’an yi ta kalli k’asa sannan ta d’ago kyawawan idanuwanta ta zubasu a kan fuskarsa kafin ta ce “na ga kamar ba ka d’auki na wajen Mai Babban D’aki a matsayin katanga tsakaninka da kujerar nan ba ko?”
Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya ce “Baby, ki rabu da ita wannan, dan ni nata k’aramin alhaki ne a wajena, bugu d’aya kawai zan yi masa a wuce wajen, kar ki damu Ana Malik!! A k’asar Khak’il babu na biyuna sai Magajina ‘d’an mu ni da ke!’.”
Ya yi maganar cikin kashe mata ido d’aya sai kuma ya saka hannu ya kamo k’ugunta ya janyota suka had’e waje guda tukunna ya ce “Besides Ina da ke ai babu abunda zai zame mini katanga…”
Da sauri ta ture hannunsa cikin d’an b’acin rai ta ce “na ga fa kwata-kwata baka d’auki
abun nan serious ba, mutum har biyu a gabanka amma ba ka damu ba, gara fa idan ka chanja tsari kawai ka gaya min.”
Ta yi Maganar tana mai shirin barin wajen.
Numfashi ya sauk’e kafin ya ce “mutum d’aya ne yanzu a gabanmu.”
Chak! Haka ta jaa ta tsaya ba ta juyo ba kuma bata wuce ba.
“You heard me right”
Ya fad’a cikin tabbatar mata da abunda kunnuwanta suka jiye mata yanzun.
Ba ta san lokacin da wani sassanyan murmushi ya sub’uce mata ba, a hankali
ya tunkarota yana zuwa ya sake rik’e mata hannu sannan ya ce
“Za’a bani goron albishir dai ko?”
Sai a yanzu ta juyo
ta kallesa fuskarta d’auke da murmushin da yake
baiyyana asalin tsantsar kyawun da Allah ya bata ta ce “yaushe hakan ta faru? Ya ta yi da ta gani? Yana Ina yanzu haka?”
Ta yi masa tambayar cike da zumud’i.
Kallonta kawai yake yi cike da so da shauk’i kafin ya ce “d’azu Allah ya yi
masa rasuwa amma I think ita kanta ba ta sani ba har yanzu.”
Kallon da ya ga tana yi
masa ne ya sanya ya fahimci tana son k’arin bayani.
Sai da ya jaa numfashi ya fesar sannan ya ce “su kansu Likitocin tsoron gaya mata suke yi, d’azu ta na barin wajen ya jaa last breath d’insa. Gaba d’aya hankalinsu ya tashi ni kuma kawai sai na nuna musu ban ma san me ya faru ba nima na bar wajen saboda gudun matsala.”
Murmushi ta yi ta rungumesa a hankali ta ce “Alhamdulillah”…
For the first time a rayuwarsa ya ji wani feeling na rashin jin dad’i ya shigesa, sannan alhinin rasuwar Sarkin ‘ZainulAbiddeen’ ya lullub’esa, yana so ya zama Sarki tabbas yana son sarautar Kakan Kakansa ta dawo hannunsa amma tashi d’aya duk sai ya ji abun ya sire masa wanda hakan ya yi matuk’ar bashi mamaki, saboda in dai lissafinsa ya bashi dai-dai to tabbas abunda yake ji tausayi da jin k’an Sarkin ne wanda yake kamar d’an uwa a garesa, a take ya ji kokwanto ya bijiro masa akan kud’irin su na d’an wajen Mai Babban D’aki, dan a yanzu haka ma ba shi ya yi ba yana jin babu dad’i Ina kuma ga idan shine ya yi? Ko Gimbiya Sakina da aka kashe bayan abun ya lafa sai da ya yi kokawa da guilt da kyar ya yakice abun a kansa…….
A hankali ya ji ta sake rungumosa cikin wani salo da yanayinta na musamman mai tada hankalin duk wani d’a Namiji mai cikakkiyar lafiya, abu gud’a game da shi shine ko masarsara yake yi wuyarta ya ji hannun mace a jikinsa yanzunnan zai ware! Dan haka ba tare da b’ata lokaci ba ya amshe ragamar komai a take suka lalace a wajen.
***************
Kamar an fisgi maganar daga bakinta Rakiya ta ji uwartata ta ce “Rakiya za ki yarda ki yi aikatau?”
Tsayawa ta yi chak da cin garin kwakin da take yi kafin ta juyo ta kalleta dan sai ta ji maganar kamar ba daga bakin jajirtacciyar Mahaifiyartata ta fito ba.
A take tausayinta ya rufeta lokacin da idanunta suka sauk’a a kan karyayyen hannunta sannan yanayin fuskar Mahaifiyar tata ya sanya ta fahimci dole ce ta saka ba a son ranta bane ba.
A hankali Yarinyar ta sauk’e ajiyar zuciya ta ce “eh.”
A ranta har ga Allah ba ta so dan ta san ba zai wuce ace ta je Gidan Manager ta yi shara da wanke-wanke ba gashi y’ay’an mutumin (mata) ba su da mutunci sun iya wulak’anci da gori.”
Tunaninta ne ya katse a take ta d’ago ta kalli Mahaifiyar tata da sauri jin tana cewa “Wai Ingila ko Saudiyya za’a nema muku aikin ku je ku yi a chan.”
Ba ta san lokacin da wani murmushi ya sub’uce mata ba ta ce “Ramma da gaske kike dan Allah?”
Farin cikin da Ramma ta gani kwance a kan fuskar Yarinyar ne ya k’ara mata kwarin guiwa, dan haka ta gyara zama ta ce “na san ba haka kuke so ba ni kaina ba hakan na tsara muku ba amma k’addara ta riga fata.
Gara mu tashi mu had’a k’arfi da k’arfe mu taimaki kanmu rashin gata da rashin galihu bashi da mafita.
Amma kinga yanzu idan kika je kika taro kud’i kika dawo sarauniya za ki zama a cikin gidan nan.”
Sai kuma ta matso ta kamo hannunta ta rik’e sannan ta ce “amma ki yi min alk’awarin fad’amin gaskiya a game da komai sannan ko da wasa idan wani ya zo miki da tallar lalata kar ki amince ki kama mutuncin kanki dan Allah Rakiya sannan ki sanar mini zan san yadda za a yi ki dawo ko a chanja miki wani wajen.”
Cikin katseta cike da zumud’i Rakiya ta ce “ karki damu, za mu je na yarda ma ni kam d’ari bisa d’ari. Sannan zan kare mutuncin kaina a duk inda nake, in sha Allahu sai na kaiki Macca.”
Cikin tsananin farin ciki Ramma ta ce “Ameen Ya Hayyu Ya Qayyom d’iyar albarka”
Dan sosai ta ji dad’in amincewartata lokaci guda saboda a tunaninta za a kai ruwa rana kafin Yarinyar ta yarda sai gashi kamar ma ta fita zumud’i.
Da gasken kuwa Rakiya ta fita zumud’in dan a asalin gaskiya Rakiya irin Yaran nan ne masu high taste sannan tana da masifar girman kai gata ba ta son wahala da talauci, kawai so take yi ta kud’ance ta ji dad’i ba tare da ta sha wahala ba. Shiyasa wannan tayin ta ji sa kamar busharar shiga gidan aljannah, ta san ko Abuja aka kai mutum aiki dad’i yake sha ballanta kuma uwa uba k’asar waje inda zata je ta yi rayuwa irin ta turawa sannan babu k’anzo babu mai da yaji babu miyar kuka!!!
Tana wannan lissafin har ba ta san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba.
Sallama Maman Mariya (Gwaggwo) ta yi ta shigo wanda hakan ya sanya Ramma ta yi saurin gimtse maganar da ta shirya yi. Sai dai kuma ta makaro dan Maman Mariya d’in ta riga ta jiyo su jiya ma kuma dama ta ji suna maganar ita da Mama a d’akin Iyya.
Waje ta nema ta zauna, kai kana ganin yadda take rarraba idanuwa za ka san maganar sirri ce take so a yi, sai da ta yi k’asa-k’asa da murya tukunna ta ce “tun jiya nake ta so mu yi
magana Allah bai nufa ba”
“Allah sarki” kawai Ramma ta ce tana mai d’ad’d’auke kai dan ma kar ta samu fuskar yi mata zancen da ta san ta ji.
Sam Gwaggo ba ta damu da yadda Ramma take ta cika tana batsewa ba ta sake matsowa kamar za ta shige cikin jikinta ta ce “jiya na ji kuna wata magana ta abun alkahairi ke da Mama, da farko na d’auka kunnuwana ne ba su jiye mini dai-dai ba! To yanzu kuma Ina cikin jan ruwa a rijiya na jiyoki kina maganar ke da Rakiya, ya abun yake ne? In da Hali a had’a da Mariya itama.”
Da sauri Ramma ta ce “Aikuwa ba na jin Mariya za ta samu dan ba wai waje ne wanda ake kai kowa da kowa ba, nima ita ta ga Rakiya da Fiddausi ta ce za ta kaisu, kuma aikin ma na iyaka mutum biyu ne ta ce, gashi ta riga ta ce ‘Rakiya da Fiddausi kawai.”
Sai a lokacin Rakiya wadda ta yunk’uro itama zata yi magana ta ji hankalinta ya d’an kwanta. Yo idan aka had’a ita da su Mariyan aka kai wa kenan za ta yiwa yanga idan ta dawo?
Dukda kasancewar su Mariya sun girme mata sosai dan Kubra ta kai 18 ma Mariya sha bakwai Fati kuma sa’ar Dije ce amma iyayi da shegen wayo da manyance irin na Rakiyar ya sanya ta shiga cikinsu ta yi kane-kane, kasancewar ita ta yi karatu tun daga nursery ya sanya ajinsu ya zamana d’aya gabad’ayansu dan su duk basu shiga da wuri ba Dije kuma daga primary ta fara Mariya kuwa sai a ss2 ta shiga yanzu haka ko sunanta ba ta gama
iya rubutawa ba wannan ma ya taimaka wajen kasancewarta a cikinsu, sai dai kuma sun fita samari da y’an matanci dan duk d’insu suna da wayoyi da kayan gayu dai-dai gwargwadon k’arfin iyayensu musamman ma Fati, hakan ya sanya wasu lokutan idan kishin ya murd’a take kishi da su, yanzu kuwa ga dama ta samu damar da ta san idan ta je ta dawo duk sai ta fi su dan haka ba zata bari su yi gogayya da kowa ba….
Shiruuu, Gwaggo ta yi kafin chaan ta ce “to shikenan, ba komai.”
Daga haka ta mik’e ta fita a ranta ta gama aiyyanawa za ta samu Mama da maganar dan tabbas ta jiyo kyashi a cikin zancen Ramma.
Ita kanta Ramma sai da ta fita tukunna ta ji kamar ta bita ta ce mata kar fa ta samu Mama da maganar dan ta san halin Gwaggo da shegen nacii in dai ta sakawa ranta abu to ba ta da zuciya ita kuma Ramma tsoro take yi kar aje idan Mama ta ga Mariya ta d’auketa ta ce Fiddausi ta hak’ura sai ta k’ara wayo, dan a asalin gaskiya Ramma k’arawa Fiddausin shekaru ma take yi saboda Yarinyar tana da garin jiki, amma asalin shekarunta goma ne.
Kafin dare ya yi Rakiya duk ta susuce sai da ta tisa Ramma a gaba suka tafi d’akin Mama ta kira waya a gabansu aka tattauna aka tsayar da Magana akan Saudiyya za’a kaita ita da k’anwarta, ita za ta yi reno da girki, k’anwarta kuma shara da wanke-wanke.
Tukunna hankalinta ya kwanta.
Murna a wajen Rakiya ba‘a cewa komai kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha.
Ita kanta Ramma murnar take yi dan albashin Rakiya ya fi dubu d’ari biyu na Fiddausi kuma dubu d’ari da hamsin.
Inna ta na zaune ta na karatun Al’qurani Ramma ta sake lek’osu, Dije da Ya Muhammad har yanzun suna nan jiya i yau salla ce kawai take tayar da su
Shi ya yi a zaune ita kuma tana iya yi a tsaye (Sallar da sai daga baya da ta tuna tukunna ta je ta yo wanka ta zo ta shiga jerosu tun daga ta azahar d’in ranar da Ya Kamal ya rasu) amma ko abinci sun k’i ci, Inna kuma ta koma gefe ta zauna tana ta karatu, dan gaba d’aya ta ma rasa ta Ina zata fara.
Haka nan ta shiga ta nemi guri ta zauna, d’akin shiruu kamar na zaman makoki.
Ba ta yi minti biyu da zama ba Sumayya ta yi sallama ta shigo.
Duk cikinsu babu wanda bai shiga shock na ganinta ba, musamman Dije wadda tun shigowarta ta kafeta da idanuwa.
Inda take ta nufa tana zuwa kawai ta fad’a kanta ta fashe da kuka.
Ajiyar zuciya Ramma da Inna suka sauk’e a tare yayinda Dije ta tsaya kawai kamar wata mutum mutumi.
Sosai Sumayya take kuka sai da ta yi mai Isarta tukunna ta d’ago ta kalli Dije wadda zuwa yanzu take kallon k’asa ta ce “ki yi hak’uri Dije ki yafe min abunda na yi miki, alhini da bak’in ciki suka sanya idanuwana suka rufe na gagara yi miki hukunci mai kyau, na manta cewa ba ke kika rubutawa kanki k’addararki ba kuma Allah ya riga ya gama tsarawa Mahaifina ajalinsa da yadda zai rasu tun kafin ya zo duniya, ki yi hak’uri ki yafewa k’awar da ta guje miki a lokacin da kika fi buk’atarta.”
Ta fad’i hakan tana mai sake rungumeta. Ta yi kusan minti uku a jikinta tana hawaye kafin ta d’ago ta kalleta ta ce “Dije ko dai baki yafe min bane ba?”
Sai kuma ta sake rushewa da kuka, dan sosai tausayin Dije ya rufeta a lokacin da labarin rasuwar Ya Kamal ya iske ta yanzu kuma da ta ji labarin yadda aka tsinto ta a kan gadon Ma’a duk sai ta ji kamar ta kurma ihu, Mahaifiyarta kanta sai da tausayin Dijen ya baiyyana a kan fuskarta lokacin da ake labarta labarin, amma da yake idanuwanta sun rufe da jin haushi da bak’in ciki da tsana sam sai ta gagara fahimtar tausayin nata take ji k’arshe ta b’ige da yi musu Allah shi k’ara, yanzu haka ma ba ta san nan Sumayyan ta yo
ba….
Sumayya na shirin sake jijjiga Dije Ramma ta k’araso wajen ta rik’e mata hannu ta ce “haka nan take tun safe, ki d’aga mata k’afa ki barta yanzun ta d’an nutsu tukunna.”
Tsananin tausayi ne ya sanya ta sake rushewa da wani kukan kawai ta kifa fuskarta akan cinyar Dije ta ci gaba da rera shi kamar an aikota.
A wannan gab’ar kam sai da suka saka Ramma kuka dan Inna ma hawaye ta fara haka shima Ya Muhammad wanda basu gama fahimtar mai ya saka shi kukan ba tunda shi dai ba magana yake yi ba.
Sosai d’akin ya komo kamar na zaman makoki dan in banda sheshshek’a da sautin kukan Sumayya babu abunda yake tashi a cikinsa.
“Innalillahi wa Innailaihirrajiun”
Sautin muryar Kaka ta karad’e ko’ina sai kuma kukanta ya cika kunnuwansu mai
matuk’ar sauti da firgitarwa.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 28.
Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.
Dije ce ta fara mik’ewa tsaye zumbir! Amma hatta makwafta sai da suka rigata isa tsakar gidan ita da Sumayya wadda ta rik’e mata hannu tana janta da k’ok’arin ganin sun k’arasa fita tare.
Suna Isa bakin k’ofa Dije ta fara jiyo sautin kukan Inna itama ya fara tashi, ga na Asabe ga na Yaran gidan har da su Kubra dan haka ta jaa ta tsaya ta rik’e hannun Sumayya g’am! Kamar wata zararriya sai kuma ta fara magana a gigice “bari in gaya miki abinda ya faru, dama d’azu na ji Mallan ya ce hanya babu lafiya to yanzun na san accident ya yi ko kuma Ma’a ne ya kashe sa, idan muka fita kika ga ba haka bane ba Sumayya ki wanka min mari! Saboda ba ni da tantama hakan ne, gawa zan gani! Sumayya wata gawar makusancin nawa zan sake gani a yau shikenan…..”
Da sauri Sumayya ta rungume ta ta saka hannu ta toshe mata Baki ta saki wani irin kuka mai cin rai.
Yadda aka d’aga labulen d’akin aka finciko Dije zuwa waje sai da ya yi matuk’ar tsorata Sumayya.
Da kyar ta iya rik’e kanta bata zube a wajen ba, tana d’agowa aka d’auketa da wani irin mari sannan aka shak’eta.
Sam Dije ba ta yi kokawar kwatar kanta daga hannun Asabe ba dan tabbas ko da ace Asabe ba ta kashe ta ba to ita zata kashe kanta, ta gama tsara hakan tun lokacin da aka fincikota idanuwanta suka sauk’a akan wani k’onannen mutumi bak’ik’irin (hatta kamanninsa sun b’ace) kwance a kan taburma yana janyo numfashi da kyar. Wanda take da tabbacin shine dan ga rawaninsa nan yashe a gefe wanda ta sanshi da shi duk ya k’ok’k’one da kyar ma ake iya ganesa.
Lumshe idanuwanta ta yi kawai ta saki jikinta Asabe rik’e da wuyanta tana wujijjigata tana gwara kanta da bango tana tsine mata.
Da kyar Ramma da Mama suka fincike Dije daga hannun Asabe, rashin kuzari a tattare da ita ya sanya ta tafi Yaraff!! Ta zube a wajen.
Cikin mad’aukakin b’acin rai Ramma ta ce “dak’ik’iyar Ina ce ke? Ce miki aka yi kin fita jin zafin abinda ya samu Mahaifin nata ne ko yaya? Za fa ki iya chanja shi ita kuwa ba za ta tab’a samun kamar sa ba. Haba mana dan Allah ku dinga yiwa kanku adalci mana! Daga abu d’aya ya faru kuma shikenan ko wanne bala’i idan ya kunno kai sai a ce ita ce saboda tsabar dabbbanci irin naku! Ina ce d’azun nan na ji ana cewa Kaka hanya babu lafiya amma ta ce ya taho a haka kuma shine saboda tsabar rashin adalci sai ku ce Dije ce sanadi, ki gaya min had’in Dije da wannan al’amarin ai idan akwai wadda za ki tuhuma to Kaka ce tunda ita ta ce duk tsiya duk bala’i ya taho a yau ba sai gobe ba.”
Ta yi maganar ta na mai kallon Kaka fuskarta na baiyyana tsantsar b’acin ran da take a ciki. Saboda haukar ta su ta fara isarta.
Kawu Isa wanda duk ba su ma lura da shi bane ya yi gyaran murya sannan ya ce “ki bari ki ji kan labari kafin ki yanke hukunci Ramma….”
Duk waigowa aka yi aka zuba masa ido fuskarsa shima ka na gani ka san ya ci kuka.
“Kamar ya in ji….”
Ramma ta yunk’uro masa rai a b’ace amma sai wayar da ya kunna recording ta yi saurin katseta jin muryar Mallan tarr suna waya da Kawu Isa”
“Ka taho ne? Kana Ina? Tun d’azu wayarka ba ta shiga”
K’asa-k’asa murya na rawa cike da tsoro Mallan yake magana ta inda yake cewa “da na taho matsalar network ne, a tasha kuma bayan na sauk’a har na fito bakin titi zan tari abun hawa ya kawoni gida sai na ga Ma’a shi da waensu irinsa a tsaye sun fi su biyar.
Ya ce min ‘ni yake ta jira tun safe akwai muhimmiyar maganar da yake so mu yi ni da shi’. Ban so na bishi ba amma sai na ga kamar Yaran nasa suna shirin yi mini illa shiyasa na yanke shawarar binsa.
Wani gida suka kaina, to kuma har ya zauna zamu yi maganar sai aka shigo aka gaya masa wata magana a take ya mik’e suka fita a gigice. Dawowarsa ke da wuya kawai sai ya dawo min a buge kuma shi kad’ai, har yana ik’irarin sai ya kasheni!
Daga haka ya fad’i a wajen.
Allah ya so daga ni sai shi ne a d’akin ragowar suna harabar gidan, dan haka na yi saurin guduwa ta wata k’ofa a bayan gidan. Yanzu haka gani nan a chan gaba da kwankwasiyya estate
ka yi sauri ku zo ku taimakeni dan Allah dan na ji kamar sun farga sun biyoni.”
Dai-dai nan ya katse kiran da sauri, recording d’in ya k’are.
Cikin kuka sosai Kawu Isa ya ce “ko da muka je bamu tarar da komai a wajen ba sai k’onannen Mallan. Su Ma’a d’in sun gudu.
Ban kaishi asibiti ba dan na yi tunanin ya cika, sai yanzunnan kuma na ga ya fara numfashi da ikon Allah.
In banda sheshshek’ar kuka da salati babu abunda yake tashi a cikin gidan.
Sai da aka d’an d’auki lokaci tukunna Kawu Isa ya d’aura da cewa “tunda na ji shiru dama na san da walakin shiyasa yana kirana na yi saurin saka recording, saboda an had’ani da waensu y’an sandan dama masu aiki gaskiya da gaskiya an ce Wuyarta in kai sheda garesu in sha Allah idan suka gark’ame Ma’aruf to babu wanda ya Isa ya fito da shi. Tun ranar da Yusufa ya bar duniya ban zauna ba, da Mallan ya bani labarin yadda Ma’a d’in yake ta bibiyarsa sai na sakawa abun ido, to d’azun ma da ya kirani na d’auka ko biyosa ya yi ko kiransa ya sake yi duba da yadda ni da kaka muka yi ta nemansa baya amsa waya, ashe ransa yake nema.”
Ya k’arashe maganar yana mai fashewa da kuka.
Gaba d’aya wani sabon kukan aka sake a tare banda Dije wadda kukan nata ya jaa ya tsaya chak.
Inna ce ta mik’e da kyar jiri yana d’ibarta tana ganin dishi-dishi ta shiga ta d’auko purse d’inta da take da y’an kud’ad’e a ciki ta ce”mu kaisa asibiti, zama a nan ba zai yiu ba.”
****************
Wari! Hamami! K’arni had’e da wani irin azababben d’oyi ne yake tashi a cikin d’akin.
Durk’ushe take a bakin gadon ta kama hannunsa tana wani irin kuka mai tsananin cin rai.
Yayinda ita kuma gawar tasa take nan kwance a kan gado har yanzu sanye da fara k’al d’in alkyabba mai tsananin kyau da tsada.
Kasancewar sa fari tas ya sanya ake iya ganin yadda ya fara komawa kore-kore gashi ya kumbura sumtum! Gaba d’aya halittarsa ta sauya.
A hankali cannular da aka saka masa a jijiyar hannun nasa ta zilmiyo ta zamo ta fad’i a kan gadon.
Da sauri Likitocin da suke a tsatstsaye a bakin gadon suka sunkuyar da kawunansu kowa ransa babu dad’i.
Da sauri Gimbiya Zakiyya ta tashi daga kan sofar da take a kai ta fice da ga cikin d’akin gaba d’aya tana hawaye, bakinta toshe da hannunta.
A karo na babu adadi Nuraddeen wanda shima ya ga fad’owar cannular daga hannun gawar ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ya matso ya sake tsayawa a dai-dai kanta ya ce “ranki ya dad’e, abubuwa sun fara fita daga jikinsa alamun ya fara sacewa, ki bari a yi masa wanka a kaisa makwancinsa kar ki wulak’anta gawar mutum mai martaba kamarsa.”
D’agowa ta yi ta mik’e tsaye a fusace ta ce “Nura na ce kar ka sake ce mini ya rasu ko???”
Sai kuma ta yi gaba alkyabbarta tana jan k’asa tana hard’eta cikin sassarfa mai kama da gudu-gudu ta k’arasa wajen babban Likitan tana zuwa ta damk’i kwalar rigarsa gefe da gefe da hannayenta duk biyun ta ce “why are you just standing here? Tell them he’s still alive!! Tell them that my son is not dead!! They are going to bury him alive, don’t let them do that. You promised to save him, tell them he’ll soon open his eyes and see the lights again.”
Ganin ba shi da niyyar kula ta ya sanya ta koma kan d’ayan ta ce “people said you once brought back the dead, if Abidden is really dead! Please bring him back to me”
Nan ma shiruu jan baturen ya yi bai ce mata komai ba, tsananin tausayinta yana shigarsa.
Cikin matsanancin tashin hankali ta k’arasa kan d’ayan ta ce “if all of them have failed I know you won’t, you can help me right? You can bring back my child to me…”
Shima nan shiru dan haka ta k’arasa kan d’ayan ta ce “you are the best I know you can. I’ll give you all my wealth just bring back my child….”.
Ganin duk basa kulata ya sa ta koma kan Nuraddeen ta ce “they are
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 23