Share this page
musamman ma ita Dijen da Mahaifiyarta. Sannan Abu na biyu labari ya riskeni akan cewa kallonta kawai Sagir ya yi shima aka kashesa har lahira, ka ga kuwa idan ta fito ba zai yiu a ce ba za a kalleta ba kwata-kwata dan na san ko da mistakenly ne idanun wasu za su sauk’a a kanta. Ka ga kuwa zaman ku a tsakiyarmu babban had’ari ne tunda har gobe Allah bai bamu ikon samun wani babba kwara d’aya a kaff fad’in Nigeria wanda zai tsaya mana a kan b’arnar da Ma’aruf yake tafka mana ba, dan haka kasancewar ku surukai a garesa ya sa dole ku yi mana alfarmar barin Unguwar ba tare da shi kansa ya san dalilin tashin naku ba walaAllah idan kuka tafi shima ya biku kowa ma ya Hutu da bala’in sa…… Sannan a shawarce kar ka ce ba zaka bashi ita ba, ka aura masa ita tunda yana sonta har haka saboda gudun zubar wani jinin dan dai na san ba za a ce Dije ba zata yi aure ba har abada! Ta rungumi k’addarar ta ku bar Unguwar nan ta auresa wata k’ila ta iya chanza shi idan Allah ya so yanada rabon shiryuwa.” Tunda ya fara magana Ya Kamal ya kafesa da idanuwa…ya san cewa mutumin dama is selfish amma bai tab’a kawowa rashin ko In kula d’in nashi ya kai har haka ba. A b’angaren Mallan kuwa in da ace yana da hali wallahi da b’acewa kawai zai yi ya huta amma kuma da ya tuna a halin da zai bar su Dije sai kawai ya sare ya rasa ma Ina zai kama. Idan akwai abu guda d’aya wanda yake da tabbacin sa shine Kaka ba zata tab’a bari a tashi a Unguwar nan ba saboda su Dije, ya san cewa zata yi sai dai ita da uwarta su tafi su barsu wanda shi kansa ya san akwai abunda Kakar ta yi wanda in dai har Halima ta sa k’afa ta bar gidan da sunan yaji ko wani Abu makamancin haka to tabas to tafi kenan har abada ba za a sake ganinta ba! Da kunnensa ya ji suna maganar ita da Asabe. Ya san Kaka ya san wacece ita tun yana k’arami, shiyasa ya ke jin tsoro wanda ya san hakan bai dace ba amma asiri gaskiyar mai shi kuma gaskiya ne, shiyaasa ya kasa nema musu ko da haya ne ta koma ita da Y’ay’anta dan abunda ya ji suna tattaunawa sun yi a Haliman ba k’arami bane ba, wala ta yi kurciya wala ta mutu amma duk bala’i dai ba ta isa ta dawo gidan ko a ganta ba!. Dije amana ce a wajen sa idan ya bari bayan halin nan da take ciki a yanzu ta sake fad’awa wani Hali na daban ya san bai yiwa kansa adalci ba sannan rabuwa da Halima is the worst thing that will happen to him, ga Muhammad a kwance rai a hannun Allah ga rashi da babu dan yanzu haka ma akwai aikin da ake so a yi masa a kwakwalwa amma ya san ko sayar da kansa zai yi bai Isa ya samu kud’in ba…… “Kai muke jira, na ji ka yi shiru Mallan Bashir, yanzunnan kafin mu shigo wajen ka muka rabu da mai unguwa kuma shima maganarsa irin tamu ce ‘indai har ta tabbata akwai alak’a tsakanin Ma’aruf da Khadija to a ce muku ku bar Unguwar ko kuma ka aura masa ita a zauna lafiya amma mu a ganinmu gara kawai ko da ace za ka aura masa ita d’in ku tafi d’in kawai saboda tana budurwa ma an kalleta ya yi kisa ballanta ta zama tasa? Gashin kuma kanku zama da ku had’ari ne.” Ko da ace Ya kamal bai san komai game da halinda ake ciki da Kaka na case d’in barinsu gidan ba ya san wasu abubuwan. Dan haka ya yi shiruuu tausayin Mallan wanda ya gagara furta komai jikinsa har ya fara karkarwa yana dad’a lullub’esa. Chaan ya d’ago a hankali ya kalli mutumin ya ce “Har yanzu ba mu da tabbacin cewa Ma’ah ne ya ke kashesu fa, Hatta Sagir d’in da kuke magana akai waenda abun ya faru a kan idanunsu ta inda suka bayarda da shedar Scorpion ne ya kashesa, Shi kuma Mallan Manniru Allah ya ji k’ansa kun dai sanshi da cin bashi satin baya tabbas ya karb’i bashi a wajen wasu y’an Fagge dan ko shekaran jiya da kyar muka rabashi da su d’ayan yana ta ik’irarin sai ya kashesa. Ku dinga yiwa kanku adalci mana, yanzu idan y’ar wajenka ce za ka bayarda shawarar a d’auketa a bawa Ma’aruf ne??” Cikin d’an b’acin rai mutumin ya ce “ba na son sakarci! Mu zauna a yi ta kashe mu kenan kake so ko yaya? Duk wannan abun da muke yi kusan fa ku matasan layin za a ce ana karewa..” Tabbas tsoro da gudun zubar da jini suna daga cikin dalilan da yake so Mallan da iyalinsa su bar Unguwar amma kuma still yana son muk’amin Mallan d’in ne shiyasa yake dad’a zak’alk’alewa. Kamar had’in Baki a take ragowar mutane biyun suma suka hayayyak’o har da cewa ko dai Mallan ya bar Unguwar ko kuma su koresa k’arfi da yaji tunda sun lura son kan nasa ya yi yawa kuma idan ba a yi masa da gaske ba haka nan zai zauna daram akan jinin su Yusufa ba a d’auki wani mataki ba. Shiruu kawai Mallan ya yi ya k’i tanka musu dan a gaskiya idan za a bi ta zab’insa a barsa to bai ga dalilin da zai sanya ya bar Unguwar ba sai dai a yi ta kiransa da mai son Kai amma bai damu ba dan ba zai tarwatsa rayuwar Dije da Halima saboda zargin da ba a da shaida ballantana tabbaci a kai ba! Dan shi har ga Allah dukda cewa shima ya yarda d’in amma zuciyarsa tana dad’a jaddada masa cewa ba Ma’ah bane ba…. A hankali kamar daga sama ya ji Ya Kamal ya ce “zan aureta zan d’auketa da Iyya mu koma garinmu, Ina fatan hakan zai rufe komai daga gareku?” BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 20. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Da sauri Mallan ya hau girgiza masa kai idanunsa jazir ya ce “A’a Kamal ba za’a yi haka ba” Cikin tarar numfashinsa Ya Kamal ya ce “Mallan kar ka ce mini kai ma ka yarda da abunda kowa yake fad’a! Zargi ne suke yi wanda idan aka bari aka tafi a haka shikenan sun tarwatsawa Dije rayuwa kenan har abada! Dan a wajensu ne kad’ai barinku Unguwar nan zai zama win! Amma a wajenku kamar kun sake bawa abun mazauni ne, dan haka hakan sam ba ita ce mafita ba, sannan ka yarda da ni idan na ce maka muddin ka bari suka yi nasarar korarka a nan to babu Unguwar da zasu yarda da ku an dinga kwallo da ku kenan dan a kusan kaff garin Kano waye zaka ce bai san labarin Ma’ah ba? Ko da ace ma Unguwar da zaku je su d’in basu sani ba na tabbata ba zaku yi sati ba labarin komai zai iskesu dan yanzu kiwon mutum ake yi ba na dabba ba. Dan haka ka yi zaman ka a nan inda ka taso har ka yi aure ka tara iyali, ka bani auren Dije ni zan aureta mu bar garin nan da ita in sha Allahu babu abunda zai sameni su kuma bak’in fentin da suke shirin goga mata sai dai su shanye abunsu.” Ya k’arashe maganar yana mai kallon dattawan da suke zaune sunata muzurai. Kafin ya juyo ya kalli Mallan d’in ya d’aura da cewa “Sannan dan Allah kar ka yi min kallon wanda yake son aurenta saboda tausayin halin da take ciki dan ni saboda Allah da son da nake yi mata tuntuni nake so in aureta.” A hankali Mallan ya jinjina kai kafin ya ce “na gode Kamal, bari za mu gani.” “Girgiza kai Ya Kamal ya yi sannan ya ce “ka daina yi mini godiya Mallan I’m not doing you a favour kai ne zaka yi min ta hanyar bani Dije in aura. Sannan Ina so a d’aura a yanzu in dai har babu damuwa tun kafin ma mu fita daga nan wani ya b’ullo da wata matsalar.” Tab’e Baki wannan mutumin da ya fi kowa d’aukar abin da zafi ya yi kafin ya ce “to ai shikenan, tunda burin mutuwa ka ke da shi mu masu yi muku shedu ne!” Ya fad’i haka yana mai gyara zama……… An kai ruwa rana dan rabewa biyu mutanen suka yi wasu suka ce a d’aura wasu kuma suka ce kar a d’aura, dagewar da Ya Kamal ya yi ya sanya ba dan Mallan ya so ba ya amince a lokacin aka d’aura auren Kamal Yunusu da amaryarsa Khadija Bashir Isa akan sadaki naira dubu talatin ajalan, dan babu cash a hannunsa dan haka ya ce suna shiga gida zai wuce d’akin Iyya yana da ajiya dama ya d’auko ya kawo. D’aurin auren kwata-kwata halartar mutane goma ya samu amma kafin su kai gida da ikon Allah labari har ya iske mutanen gidan. Tun daga bakin k’ofa da Umar ya hangosu…dama already Yaran sun taru ana rige-rigen waye zai fara ganinsu, ai kuwa yana hangosu ya fella cikin gida da gudu yana ihun “ga su nan! Ga su nan!!!”. A tsaye a tsakar gidan suka tarar da kowa an yi cirko-cirko Babba da Yaro tsoho da matashi ana ta tattauna maganar. Suna shigowa Iyya ta k’arasa ta kamo hannun Ya Kamal suka wuce cikin d’akinta ta turo k’ofa ta rufe ruff. Mallan kuwa d’akin Inna ya nufa dan su kad’ai ne bai gani a tsakar gidan ba gashi maganarsa da ita emergency ce..yana so ya ji ra’ayinta. A zaune ya same su jugumm! Ita da Dije kowa ta yi tagumi tana kallon gefe, Dije ta rame ta fige har wani duhu ta yi a iya kwanakin nan, a take tausayinta ya lullub’esa ya ji kamar ya koma don baya jin zai iya jurar ganinta a wannan halin amma kawai sai ya dake ya sake maimaita sallamarsa a karo na biyu tukunna Dijen ta yi firgigit ta juyo tana kallonsa. Wani abu mai masifar tauri da d’aci ta had’iye tukunna ta ce “Ina wuni, sannu da shigowa.” Daga haka ta saka hannu ta tab’o Inna wadda ta lura sam bata ma san da shigowar Mallan d’in ba. Kamar yadda Dijen ta yi itama haka ta yi sai dai ita tana d’agowa da suka had’a ido da shi tashi d’aya fuskarta ta chanja dan haka ta cewa Dije “bamu waje” ba tare da ta kalleta ba. Simi-simi haka ta mik’e ta fice ta wuce kitchen ta je ta nemi waje ta zauna dan bata son had’a ido da kowa ji take yi kamar ta binne kanta da kanta. Dije tana fita Inna ta mik’e tsaye ta ce “ka yi hak’uri da abunda zan fad’a Mallan amma wannan karon abunda ka aikata ba dai-dai bane ba!. Da muka ga maza har biyu sun rasu duk a ta sanadiyyar Dije ya kamata ace mun dakata ba wai mu sake tafka wani kuskuren ba! Yaron nan ko dan tsohuwar Mahaifiyarsa wadda shi kad’ai gareta ya kamata ace ka yi la’akari da hakan kafin ka d’aura auren! Yanzu idan wani abun ya samesa da wanne ido za mu kalli mutane musamman ma ita Dijen? Ko baka ganin halin da take ciki ne? Yarinyar da a daa wani zubin sai na make mata Baki tukunnna nake samun hutu daga surutu da wak’e-wak’enta wai yau ita ce sai ta kwana ta wuni bata ce komai ba?! A gaskiya baka yi abunda ya dace ba wannan karon Mallan…” Cikin katseta ya ce “yanzu Halima kema kenan kin yarda da cewa duk wanda ya rab’eta kamar ya yanki tikitin mutuwa ne? Ki taimaka Halima dan Allah kar ki bari su buga mata tambarin da suke k’ok’arin yi..” “Saboda son zuciyarmu da son y’armu kuma sai mu bari jini ya yi ta zuba?” Inna ta katse shi itama. Runtse idanuwansa ya yi da mugun k’arfi sai da ya d’an jima a haka kafin ya bud’e su ya kalleta ya ce “yanzu to ya kike so a yi?”. Cikin tsananin jin zafin abunda zata ce d’in ta d’an girgiza kanta sannan ta ce “ba zan tab’a aurawa Ma’ah y’ata ba! Ba zan bayarda goyon baya ba ba zan yarda ba! Amma kuma ina mai bayarda shawarar kar ka sake yunk’urin aurar da ita a wani idan Kamal ya..” Kasa k’arasawa ta yi ta sa hannu ta toshe bakinta hawayen da take ta k’ok’arin dannewa suna masu silalo mata. A hankali ya ce “idan Kamal ya rasu? Haba Halima kar ki yi tunani irin haka mana! Sannan kina tunanin idan Dije bata a gidan wani Ma’ah zai barmu mu sha ruwa ba tare da mun aura masa ita ba? Idan ma ya bari so kike ta k’arashe rayuwarta babu aure kenan ko yaya!?”. “Saboda ba ka so y’arka ta k’arashe rayuwarta babu aure sai ka yi ta yin silar rasa rayukan wasu?” Ta yi masa tambayar a d’an zafafe. A hankali ya matso ya kamo hannayenta biyu ya ce “Halima duk abunda kika ga Ina yi shine dai-dai, a da nima na so in sare amma kamar yadda Kamal ya fad’a hakan ba ita ce mafita ba, sannan idan fa bamu yiwa tufkar nan hanci ba to tabbas akwai babbar matsalar data fi wannan da muke ciki yanzu a gaba, abunda nake so da ke shine ki yarda da ni, in sha Allahu babu abinda zai sami Kamal, za su wuce garinsu Minna shi da ita a yau ko gobe dan haka kawai ki bisu da addu’a.” Daga haka ya juya ya fita kansa yana wani irin sarawa jiri yana d’ibar sa ai kuwa yana shiga d’akinsa ya zube. ****************** Kamar kullum yau ma da safe fada ta cika mak’il an zo kwasar gaisuwa, kowa ya sha ado na gani na fad’i, gold a jikin matan nan kuwa kamar ruwa ko ina hannu k’afa yatsu wasu har da goshi da gefen hanci. Sosai abunda Gimbiya Mariya ta yi yauma ya sake fusata wasu dan tabbas abun nata dole ya tab’a kowa tunda ya shafi Giwar Mata, wai dan an turo ta a wheelchair shine ta ce sai dai a koma da ita duk lokacin da ta warke sai ta tako ta zo da k’afarta. Matar ba ta wani kula ta ba dan ita zuwa yanzu takanta take yi rashin lafiyar yau daban ta gobe daban jikin tsufa, Hakanan aka juya da ita ai kuwa ta k’arawa kanta bak’in jini a wajen dayawa yayinda wasu kuma mugun k’ullin su a kanta ita da d’anta ya nunku. Sarki yana shigowa kowa ya shiga bashi girma kamar yadda aka saba, sai da ya k’arasa wajen zamansa tukunna aka d’an nutsu da kirari dai-dai lokacin da wannan farin kyallen yake sauk’owa, ya rufe sa ruff shi da kujerar tasa ta yadda duk kwakwar mutum bai Isa ya ga komai ba. A k’a’ida yana zama idan ya gama kimtsawa to shine da kansa zai danna wani abu a jikin kujerar tasa kyallen ya yaye wanda a kullum da sauk’owar kyallen da zamansa da yayewar kyallen baya kai mintuna biyu cikakku amma gashi yau har an haura mintuna goma shiruu…. A hankali k’us-k’us d’in mutane ya fara tashi a cikin fadar yayinda hankulan wasu ya yi chaaa! Wasu kuwa kamar su kurma ihun murna dan suna da tabbacin hak’arsu ce ta cimma ruwa. Wasa-wasa sai gashi har ana shirin shiga mintuna talatin dan haka Gimbiya Mariya ta mik’e k’irjinta yana dukan uku-uku ta k’arasa wajen. A hankali ta sa hannu ta tura labulen ta shiga wajen wanda shigarta ya yi dai-dai ta kifewarta a wajen, sumammiya. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 21. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. A take Fadar ta hautsine yayinda Wambai Waziri da Galadima suka mik’e daga wajajen zamansu suka k’arasa suka shiga wajen a gigice. Shi kansa Wambai sai da Galadima ya ruk’osa tukunna da kyar aka samu ya dedeta bai sume musu ba. Amintattun Hadimanta aka kirawo suka zo su biyar suka sauk’o da ita yayinda kan kowa a wajen yake a k’asa masu kuka suna yi. Sai da suka zo tsakiyar Fadar da ita tukunna Likitocin dake a cikin Fadar waenda aka yiwa kiran gaggawa suka matso aka d’aurata a gado suka wuce babban asibitin masu mulki da ke a cikin masarautar da ita. Hatta bayin da ke a zazzaune cikin Fadar 24/7 sai da aka sallamesu aka tabbatar da kowa ya watse tukunna aka kawo wani gado mai rumfa tsakiyar Fadar su Wambai da Gimbiya Zakiyya suka d’auko Sarkin wanda ya wani lankwashe ya yamushe tashi d’aya k’afafuwa da hannayensa suka shanye ya koma d’an mitsitsi sannan a sume, suka d’aurasa a kan gadon aka wuce Gidansa direct da shi dan a chan za a jona komai a kula da shi secretly har Allah ya bashi lafiya saboda gudun fitar zance…….. Tafe take cikin shigar b’adda kama tana ta sauri kamar zata kifa. Daga ita sai amintacciyar hadimarta ne suka yi wannan fitar dan ko a cikin amintattun Hadiman nata waenda ta yarda da su su uku da wannan guda d’ayar tak wadda suke tafe tare yanzun ta yarjewa tasan akwai alak’a tsakaninta da Nuraddeen. Kusan da Daji za a kira wajen dukda kuwa a tsakiyar gine-ginen main cikin masarautar yake amma wani irin fili ne mai d’auke da wasu irin shekararrun bishiyu manya-manya waenda a k’alla sun kai guda d’ari!. Kutsawa take yi ta cikin bishiyun nan kamar zata kifa, da k’arfi ta ji an finciko hannunta bayan wata makekiyar bishiya, da farko Hadimartata bata gane shi d’in bane ba sai da ta lek’a tukunna ta fahimci shi d’in ne dan haka ta jaa baya ta koma ta tsaya. Bai jira ko gaisawa sun yi ba ya ce “amma ba ki kyauta mini ba this time around gaskiya! Tun da har kika ji na ce miki ki jira ai kinga kenan akwai dalili..akwai abunda nake so in samu kafin a k’arasa shi ko? Ko kin fi ni son ganin ya kauce ne?” Ya k’arashe maganar tashi a d’an tsawace alamun ranshi ya kai k’ololuwa wajen b’aci dan da gaske a fusacen yake saboda Allah kad’ai ya san kalar matsala da delay d’in da kwanciyar Sarkin nan ta yanzu zata janyo masa, gashi ga dukkan alamu ba lalle ma ya tashi ba. Sai da ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna ta fincike hannunta wanda ya ruk’o ta ce “da fari dai ka san tsawa daga gareka a gare ni bata da mazauni ko?” Shiruuu ya yi yana kallonta itanma shi ta tsare da dara-daran idanuwanta tana jiran apology…. Da gaske yake yana sonta kuma kamar yadda yake son abu mai matuk’ar mahimmanci daga wajen Gimbiya Mariya to haka itama wannan, besides she’s not completely useless, dan haka ba dan yana so ba ya ce mata “sorry” Yana mai kawar da kansa gefe dan sosai ta kafesa da ido kamar mai shirin rufesa da duka. Numfashi ta fesar kafin ta ce “ban yi komai ba! Saboda ka sanni ba na magana biyu dan haka ka yarda ko kar ka yarda tun daga lokacin da ka yi mini bayani na dakatar da komai yanzu ma haka zuwa na yi in yi maka maganar cewa akwai matsala amma tunda ba kai bane ba shikenan. Tabbas ko ma waye ya jik’a mana aiki. Saboda hawanka kan karagar mulkin nan ba tare da taimakon abun hannun Mariya ba it’s impossible..” Shiruu duk suka yi kafin chaan ta ce “bari in je, za’a zo nema na zuwa anjima Ina da bak’i.” Da sauri ya ruk’o hannunta ya ce “ban gaji da gan..” Dan ya lura har yanzu a fusace take, kuma da gaske bai gaji da ganin nata ba. Cikin katseshi ta ce “Plss Nuraddeen, mu ji da abunda ya ke a gabanmu yanzu dan akwai matsala tafe kuma muddin ka bari Sarki ya mutu ba tare da Mariya ta baka abunda ta yi alk’awari ba to ka san cewa da kai da babu duk d’aya. A wajena da wajen kowa ma dan haka ka yi lissafi mai kyau ka nemawa kanka mafita.” Tana gama fad’in haka ta juya ta wuce fuuu kamar zata tashi sama……bayaga Nuraddeen mutane hud’u ne manya a masarautar ta san sunada k’udiri irin nata kuma duk ta bincike su ta k’ark’ashin k’asa ta gano ba su bane ba, to wai waye haka wanda ya aikata musu wannan d’anyen aiki haka cikin bazata! Tabbas an had’a mata jagwal….. Tana wannan lissafin ta wuce ta barsa a wajen.. Ya dad’e a wajen kafin chaan ya furzar da iska a fili ya ce “za ki shigo hannu ne! Duk wannan izza da rashin kunyar taki za ta kau ne za ki yi bayani….” Sai kuma ya shiga tunani tare da lissafin waye ne mai wannan d’anyen aikin haka?… Tsaki ya yi ganin yana shirin bawa kansa headache ya ce “ko ma waye za a nemo sa ne” Dan ya san dole da had’in bakin Baiwa/Bawa ko Bafade ko Dogari aka yi aikin nan, kuma yin aiki da su ka barsu a doron k’asa hatsari ne babba! Kai ko da ace ma ka kashesu dole a gano gaskiya ta hanyar wani ko wata d’an uwa ko Abokinsu dan basu iya rik’e sirri ba gasu da shegen munafurci! Gashi idan aka fara bincike a cikin masarautar har hanji ko Ina sai an dubo an gano gaskiya. Idan kuma aka gagara aka mak’ale a taso mai gaiyya mai aiki ya bincika wanda in dai a k’asar KHAK’IL aka haifi mutun aka binne cibiyarsa kuma ya aikata laifin to fa dole sai an gano a cikin kwarya. Shiyasa su suka tura tsohuwar Jakadiya ta nemo musu waenda bama y’an k’asar ba ta yadda suna gama yi musu aiki za su aika su lahira kuma duk kwakwar mai gaiyya bai Isa ya iya gano su ba tunba ba a k’asar aka binne cibiyarsu ba, sannan za su tsoratar da su ta yadda ba su Isa su yi sirri da kowa ba idan ba su d’in ba….. *************** Sai da Minu ya dawo da daddare tukunna aka san halin da Malllan ya ke ciki. Sosai hankalin kowa ya tashi dan sam ko motsi ba ya yi dan haka aka wuce da shi emergency direct ba tare da sun san me za su bayar ba idan sun je d’in dan sun yi k’ak’aff!! Hatta Ya Muhammad ma shirye-shiryen dawo da shi gida ake yi a hakan ba tare da ya warke ba saboda basu da kud’in gado bare na magani. Duk fushin da Kaka take yi da shi tana jin labari ta baro garin Getso a rikice dan Mallan daban yake a wajenta Halima ce take janyowa suke yin fad’a ita da shi amma ba dan haka ba da an ga yadda ake ji da Yaro. Zuwan nata ne ya sanya suka samu d’an abunda aka bayar a asibitin aka ci gaba da treatment d’insa wanda daa Likitocin suke shirin ajjiyewa dan ko syringe babu a asibitin sai ka siyo tukunna za’a yi maka amfani da shi su kuwa basu da ko sisi. Tijara ta so yiwa su Inna a bainar nasi dan haka Inna ta tattaro Dije suka baro wajen, tunda har an samu wanda zai d’auki d’awainiyar tasa to Alhamdulillah, daga haka suka fito ba su da ko kud’in mota suka shiga dab’awa da k’afafuwansu ga dare. Kamar daga sama suna cikin tafiya ta ji an ce “Khadija” Tana juyawa ta ga Ya Kamal ya biyosu yana d’an haki alamun da kyar ya cimmusu. A take kunya duk sai ta lullub’e Inna dan tabbas ta san bai kamata Dije ta fito ba da saninshi ba. Sai da ya rissina tukunna ya gaida Inna itama ta amsa cikin jin kunyar da bata tab’a kawowa zata yi ta a Kamal d’in ba. Cikin rashin jin dad’i ta ce “ka yi hak’uri ta fito ba da sanin ka ba ko? Jikin Mallan ne ya motsa shine duk muka fito a d’imauce ni na ma matan w” Da sauri ya ce “haba dai Inna, ba komai wallahi Allah ya bashi lafiya, nima Iyya ce ta kira take sanar min shine na biyo sahu shigata ba wuya kuma Minu ya ce min yanzu kuka fita, shine na ce bara in duba. Bismillah mu je in k’arasa da ku ga mashine d’in chan.” Ya yi maganar yana mai waigawa ya nuna

Chapter 16 of 23