Share this page
fara yi mata bayani ba yayinda Mama ta k’ok’arta itama da kyar ta ce “muma ba mu san ya fita ba, lokacin ana ta kan alhini ba mu yi tunanin zai biye musu ya tafi ba. Sai d’azu ne wannan Yaron d’an biyun Kubra yake ce mana ya tafi fa kuma sun bishi har tashar mariri dan nan mai lemon bakin titi ya ji ya cewa napep d’in da ya shiga. To kuma wai sun bincika an ce an ganshi sai dai unfortunately an gagara gano motar Ina ya shiga, ma’aikatan tashar sun ce musu wai tunda ba’a gani ba to bai bar garin ba kenan. Amma ki kwantar da hankalinki sun bayar da har hotonsa, yana zuwa za’a yi kiransu in sha Allahu. Ya ce mana shi da Musa suna kan bin duk tashoshin garin nan za su bi sahunsa (ko ya tafin ko bai tafin ba) a hankali su lallab’a shi ya dawo…..” Wani irin dummmm! Inna ta ke ji ita ta ma kasa yin lissafi da kyar kwakwalwarta ta iya k’iyasta mata “Minu ya bar gidan!!” To garin yaya hakan ta faru? Ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san waye zai bata amsa ba. Still har yanzu Kaka tana waje tana ta tujara tana cewa “Inna ta fito tun kafin ta shigo cikin d’akin ta fito da ita.’ A hankali Mama ta yi gyaran murya ganin dama ta samu, ta ce “kinga tunda matar nan ta fara haka to fa idan ba d’ai-d’aita miki kan y’ay’anki ta yi ba hankalinta ba zai kwanta ba! Ga Minu yanzu dai ya tafi baki ma san inda ya je ba dan haka tun kafin ta tura miki y’arki budurwa inda baza ki sake ganinta ba, kawai ki kawota in kai miki ita aikatau Madina ko England, yanzu haka akwai k’anwata a chan nima na tab’a yin aiki a chan babu wata matsala kuma ana samun alkhairi kwarai, sannan hatta kud’in visa su waenda zata je yiwa aikin ne za su d’auki nauyin komai…. Tunda na fahimci ita Kakar tasu hankalinta ya fi tashi a kan Dije to tabbas zata hak’ura idan Dijen ta tafi na san zata sarara muku su kansu mutane za su sarara mata(Dijen)… Dan haka gara kawai ta yi tafiyarta ta huta kafin komai ya lafa, shi kansa wannan d’an daban da na ji ana ta k’ishin-k’ishin d’in shine ya kashe Kamal wallahi bai Isa ya yi mata komai ba idan ta tafi chaan d’in..idan Allah ya bata Miji a chan ta yi aure tunda na ga y’ar taki tubarkallah da ita, idan ma bata yi auren a chan ba to na rantse miki duk sanda zata tashi dawowa ta fi k’arfin raini. Ni kaina wata uku kacal na yi a chan amma dana dawo sai da na sayi d’an k’aramin fili. Kuma wallahi wallahi kin ji dai na rantse miki babu harkar karuwanci a ciki dan inda nake saka ran zan kaita ma aikin reno ne gidan babu maza ma kuma mai gidan ba mai zama bane ba, kawai albashin su ne mai kyau kuma idan kina so ma zata iya had’a aiki biyu a lokaci d’aya. Kamar ita kam na san zata iya yiwa matar girki da raino, Yarinyar gidan da na yiwa aiki ce aka yi mata aure itama ta haihu balarabiya Mijin shima balarabe, sam bata da matsala wallahi. Takanas ta yi min message ta ce tana son Yarinya budurwa da zata taya ta raino, idan na samu biyu in had’o da mai yi mata girki y’ar Babba. Za ki dinga waya da y’arki da zarar kin ji ta gaya miki wata matsala ki ce a dawo miki da ita ballantana ma ni na san ba za a samu matsalar komai ba in sha Allah.” Tunda matar ta fara magana har ta dire aya Inna bata ko fahimci kalmar ‘A’ a cikin zantukanta nata ba sam! Muryar Kaka da tunanin Inda Minu yake da kuma tashin hankalin da take a ciki sun Isa su hanata fahimtar wani sabon zance. A hankali ta mik’e ta rik’e ledar ruwanta a hannu ta yi waje. Mik’ewa matar ta yi zata ruk’ota Ramma ta yi saurin rik’eta da hannunta mai lafiya. Dan haka har Innar ta fita babu wanda ya samu damar ce mata komai… Mayar da ita ta yi ta zauna, ta share hawayenta ta fuskanceta tukunna ta ce. “Ingila kika ce ko Saudiyya?” Shiruuu matar ta yi tana lissafi kafin chaan ta ce “Duk wanda kika zab’a, idan ma kina so za ku iya tafiya tare da y’ar taki ki je ki ga inda take na san hankalinki zai fi kwanciya.” Rabonsu Ramma da su ga kwayar shinkafa ita da y’ay’anta tun washegarin ranar da ta karye, kullum sai dai a san musu idan an ga dama shima kuma bai fi sau d’aya ba, gashi Iyya ta tafi Minna wadda ita ce k’arfin ciyar da su d’in, tabbas ta tab’a jin labarin aikatau a Saudiyya amma bata san na Ingila ba, wata makwafciyarsu a inda ta baro bazawara ta tab’a zuwa da ta dawo ta kud’ance kuma an ce tabbas ba karuwanci ta yi ba albashin ne mai kyau. Ita yanzu haka ma so take ta nemi ko gidan makwafta ne ta fara tura Usama yana yi musu y’an share-share, Rakiya kuma wanke-wanke tunda babu yadda za su yi dan hannunta ya samu matsala sosai wanda ya zo ya sake gyara mata hannu (ya d’aurata) da kyar ya ce ‘ta tabbata sai ta warke garau bayan nan da kamar watanni uku tukunna ta fara aikace-aikace da shi…..’ “Kina so za ki kai Yarinyarki ne?” Mama ta yi mata tambaya tana tsattsareta da idanuwa. “Eh, amma sai na sake bincike da tunani, Yara biyu ne ma ba d’aya ba, y’an mata.” Murmushi Mama ta yi kafin ta ce “ai na d’auka y’ar taki d’aya ce Rakiya sai Usama ko?” “A’a su biyu ne y’an mata akwai Fiddausi wadda ta Baki ruwa jiya har kika aikesu ita da Abu (y’ar Asabe) da Saddik’arki (y’ar Maman) ai itanma tawa ce, sai dai ita d’in na ga kamar ta yi k’ank’anta shekarunta sha biyu, za su karb’eta a haka?” “Da gudu ma kuwa, zata yi shara da wanke-wanke da wankin band’aki ai, zasu karb’a sai dai bai fi su bata dubu d’ari ba a wata gaskiya.” Ramma bata san lokacin da ta damk’i hannun Mama ba da mugun k’arfi ta ce “Rakiya fa? Babbar ita nawa za su bata” “Eh to.. Idan aikin gida ne Ina ga dubu d’ari uku haka, idan kuma har da raino to zai iya kaiwa dubu d’ari biyar. Dan ko ni da nayi na had’a biyu d’ari hud’u ake biyana ita kuma kinga da yarintarta da k’arfinta.” Zaro Idanuwa waje Ramma ta yi tace “baiwar Allah kar ki saka mini rai fa.” Murmushi ta yi ta ce “ai baki ga komai ba, sai Allah ya sa ta samu masu kyauta idan ta tashi ta dawo miki da uban alkhairi inaga sai kin kusan suma.” Shiruuu ta yi tana lissafi sai kuma ta ce “za mu yi magana.” Daga haka ta fara k’ok’arin mik’ewa dan ta ji shigowar su Mai unguwa cikin gidan tun lokacin da Inna ta fita. Mama ce ta taimaka mata ta tashi tana cewa “to shikenan” A ranta kuwa murna fall kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha dukda kuwa Dije ta hara dan ta san idan ta kaiwa Nuraddeen ita watak’il sai ya bata kyautar gida a k’asar Khak’il, dan sai ya more K’uruciyarta kafin ya sakata aikin da suka shiryo idan ta gama su kasheta, to amma waennnan d’in ma ba laifi ai da babu gara babu dad’i sannan Dijen ma ba hak’ura zata yi ba zata ci gaba da gwada sa’ar ta. Da wannan tunanin suka fita a tare Ramma ta tsaya a wajen ana tattaunawa Mama kuwa gaisawa kawai suka yi ta afka d’akinta ta turo k’ofar ta rufe ta d’auko wata k’asa a cikin wani abu mai fad’i flat a k’asan k’atifarta ta bud’e marfin ta rubuta sunayensu ta chachchake da allura jikinta har wani irin karkarwa yake yi. Sai da ta gama tukunna ta nutsu ta k’urawa abun ido a ranta tace “naki wasa ne!! Sai in ga ta yadda za ki yi tunani da shawarar, ai in ba gani kika yi sun tafi aikatau ba hankalinki ba zai tab’a kwantawa ba! Kin yi mai wuyar ai tunda har kika bari maganar ta shiga kanki”. An kai ruwa rana da Kaka kafin ta bi maganar mai unguwa da ya ce “ta bari Mallan ya dawo daga Minna tukunna sai a san abun yi. Sannan at least ta bari alhinin rasuwar Kamal ya saki mutane.”…..dan har sai da ya fara jiyo k’amshin anya kuwa bata da wata b’oyayyiyar agenda apart from kasancewar zaman Dije hatsari ga y’an unguwa tukunna suka farga ita da Asabe, Asaben ta yi saurin janta d’aki suka tattauna, kafin ta (Asabe) fito ta ce “shikenan ba komai Kaka ta yarda, Allah ya dawo da Mallan d’in lafiya.” Da “Ameen” kawai ya amsa tukunna ya juya ya fita daga gidan bayan ya sake yiwa Inna gaisuwa, tausayinta fal ransa. Tafiya take tana had’a hanya tana adduar “Allah ya sa ta tarar da Ma’ah a gidan” A haka ta k’arasa k’ofar gidan wanda marabarsa da kango kad’an ne, sai dai an saka sabuwar k’ofa mai kyau kuma da alamu gyara ake yi har ta ciki, dan ga kayan aiki nan su yashi suminti da su bulo jibge a k’ofar gidan wanda ko da wasa duk son Yaran layin da wasan yashi basu ko je kusa da shi ba. K’irjinta yana dukan uku-uku ta taka dakalin gidan ta hau ta k’arasa bakin k’ofar gidan tana jin yadda bugun zuciyarta ya k’aru. A hankali ta d’aura hannunta a kan k’ofar gidan ta ga ta yi motsi dan haka ta ji wani sassauchi sakamokon k’amshin kusantowar cikar burinta da ta fara jiyowa. Cikin sand’a ta tura ta shiga. Sai kuma ta d’an jaa ta yi turuss!! A ranta ta shiga aiyyana yadda zata yi da zaratan maza har uku, dan warin kayan mayen da ta ji yana fitowa daga cikin d’akin soron wanda take da tabbacin nan ne d’akinsa kad’ai ya Isa ya sanar mata yana nan kuma ba shi kad’ai bane ba dan akasari wannan shaye-shayen su Scorpion ne suke yinsa shi bai cika yi ba. A take lissafinta ya Bata dole fa sai ta had’a da wayo! Dan haka ta d’an nutsu tukunna ta juya ta mayar da k’ofar gidan ta rufe dai-dai a kan idanun Mallan Idi wanda yake wasar y’ar b’uya da Ma’ah d’in. A hankali ta k’arasa bakin k’ofar d’akin, wani sanyi ta ji a cikin ranta sakamokon k’arar waya da ta ji wanda hakan yake sake bata tabbacin yana nan fa kuma burinta ya kusan cika dan idonta idon Ma’ah yau ko ita ko shi!. Har ta d’aga hannunta zata yi musu knocking sai kuma ta chanja shawara ta tsaya a dai-dai bakin k’ofar tana mai toshe hancinta dan warin ya fara damunta sosai har kanta yana sarawa…ta shiga jero sallama. Mafarkinta yake yi wai an zo an tara mutane za a d’aura musu aure amma k’iri-k’iri ta ce ‘ita fa bata son shi’ Kawai kamar a sama muryarta ta farkar da shi. Tsaki ya yi ya yarfe hannuwansa dai-dai saitin fuskarsa kamar mai kad’e k’uda ko sauro sannan ya juya zai ci gaba da baccinsa ya sake jin sauk’ar zazzak’ar muryarta cikin kunne zuciya ruhi da gangar jikinsa. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya juyo kwanciyar rigingine fuskarsa ta na kallon sama kafin ya shiga k’ok’arin bud’e idanunsa a hankali a hankali. Dai-dai bai ma kai ga fara ganin dai-dai ba ta sake sakin wata sallamar a karo na uku zuciyarta tana mai aiyyana mata ta lek’a kawai maybe ma sun bugu ne bacci suke yi ta yadda zata k’addamar da shirinta cikin sauk’i. A hankali ya mik’e zaune a kan gadon yana mai runtse idanuwansa sakamokon yadda kansa ya shiga sara masa sannan ga baccin da yake shirin sake wanchakalar da shi a nan kan gadon. “Assalam alaikom” Ya sake jin muryarta daf da daf wanda hakan ya sanya tsigar jikinsa zubawa dan a buge yake gashi ita d’in daban take a cikin ransa. Dishi-dishi yake ganin komai kafin a hankali ya fara gani sosai amma still kansa ya yi wani Irin nauyi. Zuwa yanzu ya gama gasgata ita d’in ce dan haka ya mik’e daga kan gadon wanda sai da ya dafe kansa da k’arfi sanda ya mik’e d’in saboda yadda ya sara, tukunna ya d’an nutsu ya nufi k’ofar gadan-gadan daga shi sai gajeran wandon da bai ida rufe masa guiwowi ba. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 25. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Dai-dai ta kawo kai za ta tura k’ofar ta shiga cikin d’akin shi kuma ya bud’e k’ofar ya yo waje kenan, dan haka goshinta ya bugu da k’irjinsa wanda hakan ya sanya ta jaa da baya sosai ta ce “Ya Allah” tana sosa wajen sai kuma ta d’ago a hankali suka yi ido biyu aikuwa a take ta kurma wani irin uban ihu sakamokon ganinsa a hakansa daga shi sai gajeran wando, dan sosai ta tsorata da ganinsa a hakan gashi ita in ba Ya Aminu ba lokacin da yake wani masifaffen zazzab’i Inna ta kawosa d’akinsu ta cire masa riga aka dinga goga masa towel mai ruwa.. tabbas zata iya cewa bata tab’a ganin wani d’a Namiji a hakan ba sai yau! Dan dokar Kaka ce a cikin gidansu ‘dole mace ta shiga wanka da hijabi haka shima Namiji dole ya shiga wanka da jallabiya saboda gudun b’acin rana’ dan haka ita in ba da vest ba to bata tab’a ganinsu ba shima kuma sai in by mistake. Gashi suffar Ma’ah d’in a mugun murd’e yake over ma kuwa! Gashi giant! Shiyasa abun sai ya taru ya yiwa ganinta tsauri. Tunda goshinta ya tab’a k’irjinsa ya ji kamar an sauk’ar masa da wani sabon masifaffen feeling kuma nata, gashi ta kama ta zo masa ko mayafi babu kuma sai baya-baya take yi tana sosa goshinta dan haka sosai gaba d’aya ilahirin jikinta yake shaking. Da k’arfi ya runtse idanunsa dan sosai kwayar da ya tuttula ma kansa take tunzura masa aikata abunda ya san idan ya yi ba za ta tab’a yafe masa ba. Da mamaki ya k’urawa shafaffen cikinta kallo, yana yaba surar da Allah ya yi mata dan bai tab’a ganinta a hakan ba, sannan in dai ba gizo idanuwansa suke yi masa ba to tabbas wuk’a yake hangowa a soke a k’ugunta…. Yana da kwakwalwa one thing about him kenan sannan yana da saurin harbo jirgin mutum duk kuwa nisan sa dan haka cikin seconds k’alilan zuwanta gidansu da wuk’ar da ya gani a tattare da ita uwa uba halinda take ciki da shi suka had’u suka fassara masa amsar ‘Tabbas kashesa ta zo yi.’ Yana tangad’i ya d’an matsa daff da ita ya kai hannu zai zare wuk’ar dan a yadda ta yi mata dole ta chaketa idan ta yi wani wrong move d’in… Ba zato ba tsammani kawai ta ji hannunsa a kan cikinta, ita rud’ewar da ta yi ma ya sanya Wallahi ta manta akwai wuk’a a wajen dan haka ta janye da sauri ba ta yi wata-wata ba ta d’aga hannu ta zabga masa Mari. D’agowa kawai ya yi ya zuba mata rikitattun jajayen idanuwansa yayinda kwayar da ya d’irkawa kansa take dad’a bada mahimmiyar gudummawa wajen sake ingizashi… Gefen cikin nata ya sake kalla, kawai a take sai ta ga ya nufota gadan-gadan zai kamota zuwa garesa wanda hakan ya sanya ta jaa baya sosai sai kuma ta durk’ushe a wajen da sauri da niyyar k’ank’ame jikinta waje guda sai dai bata samu damar yin hakan ba ta mik’e tsaye zumbur! Sakamokon chakar gefen mararta da tsinin kan wuk’ar ya yi…a take kuwa jini ya fito ya zirara k’asa har cikin pant d’inta. Sai a lokacin ta tuna abunda ya kawo ta dan haka ta yi ta maza ta kawar da tsoro ta zaro wuk’ar ta yi kansa. Da mamaki yake kallonta dan ko rik’e wuk’ar ma ba ta iya yi ba. Bai ankara ba ya ji ta kawo masa sara tana tangad’i sarar da ya tabbata ko b’era idan ka yiwa ita to dole ya yi maka gwalo ya gudu dan ba ka isa ka same shi ba yayinda ita kuma a nata b’angaren k’arshen bajintar kwarewarta kenan. Dan a zuciye take matuk’a. Hannunta kawai ya rik’e ya matse ya tsaya yana binta da wani irin kallo kamar zai cinyeta d’anya. Azaba da fin k’arfi suka sanya wuk’ar ta fad’i daga hannunta amma still bai cikata ba sai ma janyota da ya yi izuwa jikinsa ya rungume wai ko zai samu sassauchin abunda yake ji. Sai dai kuma hakan da yayi sai ya zame masa kamar ya barbad’a gishiri ne a kan gyambo. Ihun da ta tsala sai da ya Isar masa har dodon kunnesa rau! Ya dira a tsakiyar kansa amma sam ba shi da niyyar cikata dan zuwa yanzu ya fara rasa hankalinsa ma sakamokon laushin jikinta wanda yake nan kamar na mage da ya taimaka matuk’a wajen hautsina masa dukkan lissafinsa. Tab’a k’ofar gidan ya ji an yi ba tare da ya san me yake yi ba kawai ta ga ya mik’a hannu zai bud’esu a hakan ba tare da ya cikata ba sai ma sake ruk’ota da ya yi k’ak’am! Da hannu d’aya. Dukkanin k’arfinta ta saka wanda kwayar da ke yawo a jikinsa da mutuwar da jikinsa ya yi suka taimaka mata ta samu damar ingijesa kawai ta afka cikin d’akin dai-dai Tiger ya turo k’ofar. Tabbas ihu ya ji yanzu kuma ya ga Mallan Idi yana lek’e a jikin k’ofar sai dai yanzun shi kad’ai ya gani. Kallon da ya ga yana yi masa ne ya sanya kawai ya juya ya fita ya koma chaan lungu inda ya baro ya ci gaba da zaman gadinsa har zuwa lokacin da zai fito. Shiruuu ya yi dan ya fi mintuna uku dafe da kansa kafin chaan ya yi tsaki kawai ya juya ya nufi cikin d’akin nasa. Yana tura k’ofar ya ja ya tsaya sakamokon hangota da ya yi wanwar a tsakiyar d’akin dan tunda ta shigo ciki kanta ya juye ta nemi hanyar fita ta rasa kwayar ta fara yi mata rawar disco a ka gashi an kawo wuta fanka ta sake rura wutar d’akin ya sake yin turnuk’u. Shi kansa yana shigowa cikin d’akin abun ya ci k’arfinsa, duk yadda ya so tab’uka wani abun kasawa ya yi a take ya tafi ya zube ya fad’a a gefenta sangalalin k’afarsa ya bugu da nata sosai. Maman Sagir tana zaune a d’akinta ita kad’ai tun d’azu duk cases d’in da ake yi ta k’i fitowa. Ta ci kuka har ta gaji ta godewa Allah...A ko da yaushe idan ta runtse ido Iyya kawai take gani d’azu da safe da take ce mata “Allah ya d’aurawa Kamal irin k’addarar Sagir! Hankalinki ya kwanta yanzu?” Ji take kamar ta binne kanta dan ta san har abada Iyya ba zata tab’a mantawa da ita ba. Tana zaune ta ji hayaniya ta fara tashi sama-sama sai kuma gidan ya hautsine gaba d’aya. Sai da ta fito tukunna ta fahimci wai ashe Dije ake nema, itama zuwa yanzu duk ta yi laushi dan haka ta shiga aka dinga neman da ita….. Sune har k’arfe goma sha biyun dare suna zagaye unguwa uku amma babu Dije babu dalilinta! Idan ka ga Inna sai ka yi mata kuka duk rashin tausayinka dan kamar wata tab’ab’b’iya haka ta koma, wannan dalili ya sanya bayan an sanar da y’an sanda sun fara binciken neman Dije da Aminu su Maman fati suka bita asibiti wajen Ya Muhammad suka kwana da ita dan ita kanta patient ce ballantana ace zata ji da wani. Da ikon Allah a daren Ya Muhammad ya bud’e idonsa sai dai bai kai ga fara gane mutane ba gashi Likitansa ya fad’a ya sake fad’a tabbas kar a d’aga masa hankali ko a b’ata masa rai. Ba dan asibiti ta so ba sai dan babu taimakon da za su iya yi musu dan ba su da ko sisi, kuma kud’in komai ya k’are hakan ya sanya aka sallamo su washegari da sassafe suka dawo gida da shi, wanda da Kaka ta ji sallamarsu sai da ta kusan had’iyar zuciya ta mutu dan ita Addu’arta kar Inna ta dawo duk da dama ce mata akayi idan ta fita da fushi ko da niyyar Yaji ko barin garin ne to ta tafi har abada’ amma sai da ta saka ran Allah ya sa wannan fitar da ta yi ta jiya ta zamana ba za ta dawo d’in ba. Sai gashi da ikon Allah sun dawo da sassafe kuma har da Ya Muhammad. Ba su dad’e da zama ba aka aiko ana sallama da Mallan. D’agowa Inna ta yi ta kalli d’an aiken kafin ta ce masa “ka je ka ce baya nan, ya yi tafiya.” Fitar Yaron da kamar minti uku sai ga Babansu Fati ya shigo tare da Mallan Idi. Zuba masa ido duk suka yi suna ji kamar su rufesa da duka, amma ganinsa tare da Baban Fati ya sanya suka d’aga k’afa kawai suna jira su ji me ke tafe da shi amma fa bayan sun gama ji tabbas sai sun yi masa walmukalifatu yau idan ba su sumar da shi ba kenan! Da gudu Umar ya fito daga cikin d’akinsu jin muryar Mahaifin nasa. Bayan ya gama yi masa oyoyo ya bashi jakarsa ya ce ‘ya kai masa d’aki ya dawo ya d’auki jakar bakkon da ya zo da ita itama ya kai masa ita ciki.’ Hakan kuwa aka yi sai da Yara da y’an matan suka gama yi masa sannu da zuwa tukunna ya kalli tsakar gidan ya sallami duk wani Yaro har su Rakiya duk ya ce su shiga ciki sannan ya kalli su Inna ya ce “Ya muka ji da hak’uri?” A take kamar masu jira duk suka fashe da kuka dan ya tab’o musu inda yake yi musu k’aik’ayi. Sai da ya barsu suka d’an rage nauyin dake a zuciyoyinsu ya yi musu ta’aziyya tukunna ya juya ya kalli Mallan idi ya ce masa “ilaika!” Sunkuyar da kai Mallan Idi ya yi sai kuma ya fashe da kukan da tun shigowarsa bai yi sa ba sai yanzu. Tsaki Asabe ta yi ta mik’e za ta bar wajen ta ji ya fad’i maganar da ta sanya ta ja ta tsaya babu shiri. “Tabbas zarginku gaskiya ne. Ina mai baku hak’uri d’ana shine ya aikata duk abunda kuke zargi, d’azu na ji yana waya… Dan Allah ku yi hak’uri Allah ya ji k’an waenda suka rasu.” Shiruuu duk suka yi har Kaka wadda ta fito da niyyar korarsa. Sai kuma suka hau kallon-kallo ita da Asabe kafin su mayar da hankalinsu ga Mallan Idi kacokam. Durk’usawa ya yi a kan guiwowinsa yana kuka ya had’e hannuwansa waje guda ya ce “da ni da Mahaifiyarsa muna yin iyaka bakin k’ok’arinmu amman abun ya fi k’arfinmu ne, tamu k’addarar kenan, ni kaina yanzu haka wasar y’ar b’uya nake yi da shi saboda Mahaifiyarsa ce kad’ai ta sanya ya barni da rai na dan tun wani fad’a da muka tab’a yi da shi lokacin yana Yaro shikenan tun daga nan ya k’ullace ni yanzu kuwa da babu idonta na san kashe ni abu mai sauk’i ne a wajensa dan ya ci alwashin yin hakan. Yanzu ma garin zan bari tunda Allah ya sa na warke har zuwa lokacin da Allah zai tashi kafad’unta tukunna in dawo, amma sai na ga bai kamata in wuce haka nan ba tare da na zo na sanar da ku abunda idanuna suka gane min kunnuwana suka jiye mini ba.” Sai da ya koma ya gyara zama ya jaa numfashi ya fesar tukunna ya ce “Na san kuna ta neman y’ar ku Khadija wadda yake ta faman kashe-kashe saboda ita ko?” A take hankalin kowa ya sake karkata garesa yayinda k’irjin Inna ya shiga dukan uku-uku numfashinta ya fara kakkatsewa ta shiga addu’ar Allah ya tsare ta da mugun ji da mugun gani dan tabbas ba ta jiyo k’amshin alkhairi a tattare da maganar da Mallan Idi ya kwaso ba. “Sai dai a yi hak’uri Halima dan mai afkuwa ta riga ta afku” Muryar Mallan Idi ta dirar mata kamar dirar Mikiya a k’ahon zuciyarta. Tsoro da tashin hankalin rashin jin k’arshen zancensa ne suka sanya kawai ta fashe da kuka, cike da fargaba Ramma ta ce “ka ga dalla chan Mallan idan zaka yi magana kanka tsaye ka bar kwana-kwana to ka yi!

Chapter 19 of 23