Share this page
duk tsiya za su saka a yi masa sutura a binnesa….” Cikin tarar numfashinsa Scorpion ya ce “Baka gama fahimtar su waye mutanen nan ba har yanzu kai kenan ko?” Girgiza masa kai ya yi ya juyo da shi sosai suka fuskanci juna ya kama kafad’unsa ya ce “Scorpion Sarkin yawa ya fi sarkin k’arfi sannan power is everything!!! Idan muka tunkare su yanzu mu ne a ruwa, sannan Mama fa tana hannunsu!” Sai kuma ya d’an yi shiruu kafin ya ce “wai ta yaya ma aka yi kuka barta ita kad’ai har suka samu damar chanja mata waje?.” Cikin runtse ido dan sosai bullet d’in da ke mak’ale a d’antsen hannunsa yake dad’a azabtar da shi, Scorpion d’in ya ce “operation suka tura mu jiya tsakar dare, a chan ne ma muka ji komai ai, muna komawa kuma muka tarar da su tare muka ji conversation d’insu, to I think da suka ga mun ji kuma ranmu ya b’aci shine suka yi saurin ce mana sun turata England a cikin daren, which nake suspecting a tsakankanin lokacin ne suka tura aka chanja mata waje, dan muna fara nuna musu b’acin ranmu Alaji ya tashi ya fita da waya kare a kunnansa….to a wannan time d’inne inaga suka chanja mata waje saboda su yi amfani da ita against us tunda sun san mun fahimci komai. Ni dama tun shekaran jiya da Alaji ya ce mu dawo Kano gaba d’ayanmu ta nan jirgin zai tashi jikina ya fara bani akwai munafurci da b’oye-b’oye a al’amuransa.” Da k’arfi Ma’a ya damk’i bedsheet d’in gadon da yake a kai kansa yana wani irin juyawa tsabar bala’in da yake a ciki, idan ya ci gaba da zama a haka tabbas bak’in ciki zai iya kumbura masa zuciya ya mutu kafin ya yi abunda ya yi niyya, dan haka kawai ya juya ya bud’e drawer da ke a gefen gadonsa ya shiga dube-dube. Ba tare da ya kalli Scorpion ba ya ce “wuce ka tafi asibiti a rabaka da abun hannunka. Clinic d’in baya inda muke zuwa nan zaka je.” “Tam, Oga!” Scorpion ya ce da shi yana mai sara masa wata kwalla tana zubo masa dan ya san da tare za su yi masa hakan shi da Oscar, cike da alhini bak’in ciki da b’acin rai ya juya ya fice daga cikin d’akin dai-dai Ma’a ya gano abunda yake nema. Wata rikitacciyar kwayar gari ce ya d’auko. Ya kunna coal a kasko ya fara k’ok’arin zubawa a ciki, da sauri Tiger ya k’arasa garesa ya rik’e masa hannu ya ce “wai da wanne yaren kake so in yi maka bayani tukunna ka fahimce ni ne? Ka gaya mini ribar yin hakan idan ka yi, ka nutsu kar ka bari ka birkice na tabbata idan aka bincika watak’ilan ma Mama tana chan England d’in kamar yadda aka tsara, raina maka wayo kawai suke yi, ka tsaya ka nutsu mu san abun yi ba wai ka rikice mu rasa tudun dafawa ba.” K’uraa masa idanuwa ya yi kafin chaan ya ce “Maama ba ta chan basu kaita ba na gaya maka, Tiger treatment zamu je ba batun wasan y’ar tsana ba, ka gaya min ta yadda za su iya kammala duk wasu shirye-shirye su turata a cikin y’an kwanakin da suka gabata ana shirin…. Tabbas na tafka babban kuskure da na bar ragamar d’awainiyar kula da ita a hannunsu, dana sani da nayi mata iyakar iyawata na barwa Allah komai. On top of everything kuma jiya na sake barinta na tafi wani banzan operation!” Ya k’arashe maganar yana mai kama kansa kamar mai shirin fasawa, wani abu mai zafi yana dakar k’irjinsa, ji yake yi kamar ya kurma uban ihu! Bai ma san ta Ina ne zai fara ba gaba d’aya ya rikice, ashe shi kallon biri yake yi musu su kuma suna yi masa kallon ayaba, yana tunanin ya iya takunsa ashe suma akwai tasu manak’isar a k’ulle ba shi kad’ai ne yake ninke su ta bai-bai ba?? Ashe suma fuska biyu suka zo masa da ita….. A hankali ya sake yunk’urin kunna hayak’in Tiger ya rik’e masa hannu, cikin daka masa tsawa Ma’a d’in ya ce “wai baza ka bar ni in yi yadda nake so ba ne? Ka san Allah idan baka rabu da ni na yi baccin nan kwakwalwata ta nutsu ba har kai kanka sai ka bakwanci lahira a yanzu ba sai anjima ba! Ka bar ni in yi bacci in tashi tukunna na san abun yi tun ban aikata aikin dana sani ba!” Sosai tiger ya firgita ya tsorata da yanayinsa dan idanuwansa kad’ai idan ka kalla dole su firgita ka! Gashi ya birkice ya fito a asalinsa dan haka ya d’an jaa da baya ya sunkuyar da kansa ya ce “ka yi hak’uri. Bari in tafi zuwa anjima idan ka tashi sai ka nemeni.” ”Get out!.” Kawai ya ce masa har yanzu yana huci kamar wani zaki. A hankali ya juya ya fita zuciyarsa sam babu dad’i, shi kansa ya ji mutuwar Oscar wanda ya mutu a yau wajen k’ok’arin ganin sun (Shi da Scorpion) bawa Ma’ah d’in kariya wanda ya san harda hakan ne ya sake dulmiyasa cikin kogon k’unci da tashin hankali dan ko bai fad’a ba ya san cewa su Scorpion suna da special place a cikin zuciyar Ma’aruf d’in, ga kuma Mahaifiyarsa da mutanen chan suka rik’e suke k’ak’arin fara yin amfani da ita wajen ganin sun tilasta masa ya ci gaba da yi musu aiki, sannan ga Khadija wadda ya san yana matuk’ar so amma k’iri-k’iri an k’i a bashi aurenta! Tabbas dole ya shiga damuwa da k’unci mai tsananin hatsarin gaske….. Tiger yana fita Ma’a ya rufe d’akin ya yi masa turnuk’u ya d’auki wata kwaya itama ya kora da ita dan sosai yake buk’atar yin bacci mai nauyin gaske tun kafin ya yi b’arna ko kuma zuciyarsa ta buga ya mutu ya bar Mama a hannun waenchan munafukan, wallahi wallahi in dai ya haifu to sai ya nuna musu kuskuren su… Haka nan gaba d’aya daga jiya zuwa yau ana neman a haukatashi, duk da ya shaida d’ayar matsalar tasa ta kau amma har yanzu ya gagara daina ganin the worst scene da ya tab’a witnessing a rayuwar sa (jiya) a idonsa, da ya rufe ido kawai su yake gani. (MEANWHILE) Sama-sama take jin hayaniya kafin ta kai ga fara jinta tarr sosai. Ji ta yi inama ace bata farka ba dan muryar Kaka ta fara ji cikin hayagaga tana cewa “sai fa sun fita daga cikin gidan nan sannan daga cikin unguwar nan ma gaba d’aya dan wallahi tallahi mun gama zama da annoba!” Da alama a cikin d’akin take, kuma ga dukkan alamu b’arna take yi musu dan ta ji ana fatali da kaya sai dai ita ba wannan ce damuwarta a yanzu ba, ta yadda zata fara had’a ido da mutane shine matsalarta sannan mamakinta ya fi tafiya ga Ina Innar tasu take dan bata ji motsinta kwata-kwata a cikin d’akin ba illa muryoyin su Ramma ita da Gwaggo waenda suke ta faman k’ok’arin kwantarwa da Kaka hankali yayinda Maman Sagir Maman Fati da Asabe wadda bata ma san yaushe ta dawo ba suke sake zuzuta abun suna zuga Kaka. A hankali ta fara k’ok’arin bud’e idanuwanta…dishi-dishi ta fara gani kafin ta fara ganin su tarr sosai, ilai kuwa kamar yadda ta yi zato hatta y’ar guntuwar tvn su Kaka ta fanchakalar da ita a waje hatta labulen d’akin ta cisge ta jefa waje tare da duk wani kayan d’akin, wanda d’akin ya rage saura katifar da take ta faman kokawar ganin ta fitar da ita a yanzun ce kawai. Still har yanzu bata ga Inna ba, kuma kamar babu kowa a tare da ita. A hankali ta yunk’ura zata mik’e ta ji hannunta a rik’e cikin na mutum gamm!. Tana d’agowa ta ga Ya Aminu a zaune a saman kanta (gefe) idanunsa a kan Kaka kawai ba ya motsi amma yadda idanuwan nasa suka yi jaaa fuskarsa take karkarwa za ka san ransa ya kai k’ololuwa wajen b’aci!. Kallonsu kawai yake yi yana jira ya ga iyaka gudun ruwansu daga ita har Asaben. Cikin hayagaga ta ce “Asabe zo ki kama mini katifar nan mana! Wallahi na gama zama gida d’aya da annoba.” Yana kallon Asabe ta shigo k’ik’ik’ik’i ta kama mata suka fitar, suka yasar a waje. Sai gata ta dawo cikin d’akin ta fara k’ak’arin jaan k’afar Dije fad’i take yi “tashi annoba, tashi mai farar k’afa, tashi tsinanniya ki fice mini daga gidan d’a!” Shigowar Asabe wadda ta k’araso itama tana jaan d’ayar k’afar Dijen ta k’arfi da yaji ne ya basu damar fara janta a k’asa daga nan kan sallayar da aka d’aurata a kai. Har yanzu hannunsa yana a cikin nata bai cika ba dan har sun fara d’an motsi da shi shima, sunayen Allah kawai yake karantowa yana k’ok’arin danne zuciyarsa amma inaa ya gagara danneta! Bai san lokacin da ya mik’e ya k’arasa inda suke ba yana zuwa ya d’ago Asabe ya kifa mata wani gigitaccen Marin da sai da ta kifu a k’asa kan simintin d’akin. Duka Kaka ta rufesa da shi tana cewa “shege d’an iska tsinanne d’an tsinanniya! Wallahi yau ka tab’owa kanka tsuliyar dodo! Tunda ka tab’a ta zaka sha mamaki kuma har da kai za a bar gidan nan bari na har abada! Y’an iska shegu y’ay’an tsinanniya ballagaza in sha Allahu ko bayan barinku gidan nan sai dai ku wulak’anta ba za ku ga dai-dai ba wallahi sai kun tagaiyy….” Inaaaaa! Ba zai iya ci gaba da tolerating d’inta ba dan haka ya wani Irin juyowa a take ya damk’i wuyanta ya tafi da ita jikin bangon d’akin ya mak’ure ta cikin mad’aukakin b’acin rai ya ce “Enough! Enough!!Enough!!! Ya Isa haka, haukar ta ki ta Isa haka, k’iyayya da jahilcin na ki ya yi yawa haka. Kuma bari ki ji sai dai ke ki mutu a kai ki a binneki ki bar mu a gidan ubanmu wallahi ba ki Isa ki koremu ba nan gani nan bari, kin ji ko baki ji ba!?” Ya yi maganar cikin daka mata wata uwar tsawa kamar wani mahaukaci sabon kamu. Kaka ita kam zuwa yanzu bata ma san inda kanta yake ba dan har ta fara jiyo k’amshin barzahu. Sosai mutane suka taru a kansa har da su Usso ana ta kiciniyar k’ok’arin ganin an kwace wuyan Kaka daga hannunsa amma sam ba ya jinsu, kunnuwansu iyaka tsinuwa da zage-zagen ta a garesu kawai suke dad’a yi masa ringing a brain nasa shiyasa ya yiwa wuyan nata ruk’on life support dan haka sam suka gagara kwatar Kaka daga hannunsa. Babu wanda ya lura da shigowar Mallan wanda wani makwabcinsu ya je takanas ya d’aukosa daga asibiti dan hayaniyar ta cikin gidan ta fita har waje ana jiyosu tun d’azu….ba su ga shigowar sa ba sai gigitaccen marin da ya d’auke Minu da shi ne ya mayar da hankalin kowa a kansa. Still duk da hakan bai sanya Minu ya cika wuyan Kaka ba! Wata kalar tsanar matar ce take dad’a tasiri a cikin zuciyarsa da ya fuskanci tabbas bata da wani burin da ya wuce ta tarwatsa kawunansu gaba d’aya su d’aid’aice su wulak’anta, baya jin zai tab’a yiwa wani mahaluk’i a fad’in duniyar nan kalar tsanar da yake ji tana shigarsa a yanzu ta Kaka ba!…… “Aminu!!!!!” Mallan ya daka masa wata uwar tsawar da ta karad’e ilahirin cikin gidan. A hankali jikinsa yana wani kalar karkarwa ya cikata ta tafi yaraff!! Ta zube a wajen tana jan numfashi da mugun kyarrr! Da gudu Asabe ta durk’usa a kanta ta shiga yi mata sannu tana kuka. Baya-baya ya jaa a hankali yana tangad’i idanunsa har yanzu a kan Kakar sun yi wani irin jaaaa, sai kuma ya lumshe su wanda hakan ya bawa wasu zafafan hawaye masu tafe da k’unci da mad’aukakin b’acin rai damar zubowa daga cikin idanun nasa sai kuma ya durk’ushe a wajen ya fashe da kuka, tabbas inda ace ba don uban zunubin da ya san dole zai hau kansa ba wallahi wallahi da sai ya kashe matar nan a yau! Har lahira. Sosai jikin Mallan yake karkarwa zuciyarsa tana wani irin tsitstsinkewa. A hankali Kaka ta d’ago idanunta ta zuba su a kansa ta ga yadda ya kafe Minu da wani kalar kallon da idan ba gizo idanunta suke yi mata ba tou tabbas na tausayi ne! “Tashin balagar tsuntsaye ma kenan! Ban ga dalilin da zai sanya na yi sanya ba bayan ga dama nan na samu, ai Minu ya shak’e takardar lasisin zaman shi a cikin gidan nan yau in dai na haifu…..” Ta aiyyana hakan a cikin ranta. A zahiri kuma sai ta fashe da wani irin kuka. Da sauri Mallan ya juya gareta ya durk’usa k’irjinsa yana dukan uku-uku. “D’an kuka mai janyowa uwarsa jifa! Yau ga d’ana ya janyo mini an kusa kaini lahira ni Hadiza ina zan saka kaina” Ta fad’i hakan cikin hayagaga da kururuwa har da diddirza k’afafu a k’asa tana kuka kamar ranta zai fita. A hankali Mallan ya d’an juya ya goge hawayen da ya zubo masa, daga haka ya mik’e ya k’arasa ya kamo Minu ya mik’ar da shi ba tare da ya kallesa ba ya ce “tattare kayanka ka bar mini gidana!!!” Wani kalar sanyi Kaka ta ji ita da Asabe har ma da Maman Sagir! Kamar an yi musu bushara da gidan aljannah haka suka ji, amma dukda haka Kaka bata nuna ba still kururuwa ta ci gaba da yi tana cewa “Ni Khadija na haifi wanda ya haifo d’an da yake shirin zama ajalina, gashi kuma ba shi da niyyar yin komai game da hakan…” Shirun da Mallan ya ji ne ya sanya ya d’ago ya kalli Minu wanda yake nan tsaye idanunsa a kan Mallan d’in. Suna had’a idanu ya ce “Idan na tafi ka tabbata baza ka sake gani na ba!”. Da kyar Mallan ya iya controlling hawayensa ya hanasu zubowa ya kawar da kansa dan ba zai iya ci gaba da kallon Minun ba ya ce “ka tattara kayanka ka bar mini gidana na ce maka ko? Har sai na nemeka.” Still yanzu ma Minun sake ce masa ya yi “ka tabbata idan na tafi baza ka sake gani na ba! Dan haka ba sai ka neme ni ba.” Sosai jikin Mallan ya fara karkarwa yanzu dan hatta su Kaka sun yi la’akari da hakan dan haka ta sake zage dantse wajen kururuwa da borin k’aryar iskancin da take yi dan kar ma ya yi sanyi ya cewa Minu ya zauna. A hankali Mallan d’in ya ce masa “duniya tana da fad’i! Allah ya kareka a duk inda zaka shiga” Daga haka ya juya da sauri ya fice sakamokon kukan da ya ji ya na shirin cin k’arfin shi. Yana fita shima Minu bai tsaya bi ta kan Dije wadda ta rik’e masa k’afa tana kuka da magiyar kar ya tafi ya barsu ba ya fice fuuuu bayan ya fisge k’afarsa daga hannunta. Da gudu ta bishi, har cikin d’akinsu tana kuka tana magiya amma bai saurareta ba! Harhad’a kayansa kawai yake yi a fusace..wallahi yau ko duniya za ta tashi ba zai k’ara minti d’aya a cikin gidan nan ba. Su Usso har da Umar da Usama suma duk rarrashin suka biyosu suna yi masa amma bai saurari kowa ba. Ganin dai da gaske Ya Aminu tafiya zai yi ya barsu ya sanya ta koma cikin gidan da gudu neman Inna wadda bata san inda zata ganota ba. Kamar wata tab’abb’iya haka ta fito tsakar gidan wanda ya yi kacha-kacha da kayan d’akinsu ga uban jama’a wasu a d’akuna wasu a waje ta hau dube-dube har bayi amma bata ga Inna ba, tana fitowa daga bayan gidan wannan matar sabuwar zuwa ta ce mata “idan Innar ki kike nema ta na d’akin Iyya.” Ras! Gabanta ya yanke ya fad’i…gashi bata son ko had’a idanu ta yi da Iyya amma haka ta nufi d’akin, sai dai tun kafin ta kai ga shiga ciki ta hangi Inna kwance a sandare ana k’ara mata ruwa ga Iyya a gefe ita da wata mata waddda bata san wacece ba suna kuka suna karatun Alk’ur’ani, sai da ta lek’a cikin d’akin sosai tukunna idanunta suka sauk’a a kan gawar Ya Kamal wanda kamar har an shirya sa ma take gani (dan dishi-dishi ta fara gani a take) iyaka fuskarsa ce kawai a bud’e k’ofofin hancinsa da kunnuwansa kuma duk a toshe da auduga…… “Kenan da gaske Ya Kamal ya rasu??” Ta yi maganar a fili a hankali kamar wata gaula ba tare da ta san ta yi ba. ‘Tabbas Kaka dabba ce!! Yanzu ashe da gawa a cikin gidan amma ta yi wannan haukar!’ Ta aiyyana hakan a cikin ranta. A hankali muryarsa ta jiya da moments d’insu na jiyan suka shiga dawo mata kai, sai kuma suka fara yi mata guje-guje a ka suka fara shirin juyar mata da kai. A hargitse ta ga Mallan ya shigo cikin tsakar gidan Usso a tare da shi yana cewa “Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun Wallahi ban sani ba ni kawai ce min ya yi in zo gida babu lafiya.” Yana lek’awa cikin d’akin tun kafin ya shiga ya rafka salati sai kuma ya yi saurin durk’ushewa a wajen ya kama kansa……… Muryoyin mutanen wajen ne ta ji sun d’auke mata d’iff! A take ta daina jin k’arar komai sai na bugun zuciyarta. Fitowar Iyya ta na wani irin kuka ne ya sake dilmiya mata lissafi dan sosai wani irin tausayi da k’unci suka dirar mata a cikin zuciya suka samu mazauni, a take duniyar ta fara juya mata tana yi mata hajijiya sosai. A hankali ta fara jaa da baya ta koma d’akinsu Ya Aminu ta zauna ita kad’ai ta cusa kanta cikin cinyoyinta tana jin wani irin hajijiya kamar zata fad’i daga zaunen da take. Bata dad’e da zama ba da taimakon sunan Allahn da take ta jerowa ta ji muryoyin mutane sun fara dawowa (ta fara ji) duk da ba yadda ya kamata ba. Sosai ta ji gidan a cike ana ta nufanci da koke-koke wanda hakan ya tabbatar mata da y’an Minna d’inne suka iso. Tana ji su Gwaggo suna cewa “ai da kun bari an binneshi a nan, jigila-jigila da gawa babu dad’i.” Bata dai ji me suka ce ba ta ji koke-koke ya yi yawa daga nan ta ji gidan ya yi shiruuu kamar an yi ruwa an d’auke sai kuma ta fara jin tashin motoci. Sunanta ta ji ana ta kwala kira alamun nemanta ake yi, so take ta mik’e ko ta yi magana amma da ikon Allah sam sai ta gagara. Tana ji suna cewa “ai Innar tata itama ta ce ta bisu daga baya ko bayan sadakar bakwai ne sai ta dawo” Sosai take so ta mik’e ta je dan tana so ta sake kallon fuskar Ya Kamal d’inta tana so ta yi masa addu’o’i ta tofa masa amma sam sai ta gagara tashi. Haka nan su Gwaggo suka k’araci kiran sunanta suka gama suka hak’ura, daga nan ta ji d’ifff!! Komai ya d’auke mata. Ita dai bata san ko bacci ta yi ko suma ta yi ba, dan a kwance a d’akin ta farka ta ganta amma da alamu lokaci bai jaa sosai ba dan daga gani tun d’azun har zuwa yanzun data farka babu wanda ya shigo cikin d’akin. Zuwa yanzu duniyar ta daina juya mata, kuma tana jin murya sosai ba kamar d’azu da sai dai ta ji blank ko ta ji muryar kamar ta y’an cartoon ba. K’ok’arin mik’ewa ta yi ta ga da ikon Allah ta tashi dan haka sai ta yi yink’urin fita da sauri kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta ja ta tsaya chak. Yanzu ko da ace ta fita ba zata tarar da su Iyya ba! Ya Aminu ya tafi!! Innaa a kwance ga Ya Muhammad ba shi da lafiya sannan Mallan shima shi da kansa bashi da lafiya gashi an raba ta da Ya Kamal d’inta…. A hankali ta koma ta durk’ushe a wajen ta fashe da kuka ta shiga lissafin yadda komai yake ta jagwalgwalewa d’aya b’ayan d’aya kuma wai duk mutum d’aya tak ne silar jagwalgwala komai na rayuwarta hakan… Ta yaya ma za’a ce duk mutum d’aya ne ya yi sanadiyyar tarwatsa mata rayuwa haka kuma ta kasa yin komai ta zuba ido tana kallonsa yana ci gaba da aikata wasan kwaikwayo a cikin rayuwarta kamar wata y’ar tsana! A take shed’an ya samu damar aiyyana mata “to ki kashesa mana! Idan baki kashesa ba fa ba fasawa zai yi ba kuma babu wanda zai iya tsayar da shi a kaff fad’in duniyar nan.” Sosai kuwa maganar ta yi tasiri ta samu matsugunni a cikin zuciyarta. Dan a take babban burinta alokacin ya zamana bai wuce ta ga ta aika Ma’ah inda ya aika mata Ya Kamal d’inta ba. Zumbur!! Ta yi ta mik’e tana fesar da wani irin hucin da yake baiyyana k’unci da b’acin ran da take a ciki…da ikon Allah tana waiwayowa ta hango wuk’a an yanka lemon b’awo an bar d’aya ba a yanka ba. K’arasawa ta yi ta d’auka ta zira ta cikin rigarta ta soke da skirt d’in jikinta ta yi waje kamar wata mahaukaciya daga ita sai hula da d’inkin atamfa fitted da skirt k’afarta ko takalmi babu. Bata san awanni nawa ta yi a sumar ta na farko da wanda tayi a d’akin su Ya Aminu ba amma tabbas ta san ta dad’e dan tun kafin 8 ne yanzu kuwa gashi har an shiga masallacin sallar Magrib ma. Hakan ya taimaka mata ta k’arasa k’ofar gidan su Ma’a (ba tare da an ganta ba) wanda har yanzun yake a hargitse dan d’akinsa kawai aka kammala gyarawa amma cikin gidan da waje yana nan a k’ok’k’one gashi ya yi fad’a da Masu yi masa gyaran. Tabbas ta san shi ta gani jiya! Dan yanzu kam ta na da tabbacin yana nan..kuma ta ji ana labarin yadda aka gyara masa d’akin nasa har an kawo kayan kallo, d’azu da sassafe. Addu’arta d’aya kawai itace ta yi ido biyu da Ma’ah, in sha Allahu ita kuma idan ta haifu sai ta kaisa lahira da hannunta. Kamar wata wadda aka yiwa asiri gaba d’aya lissafinta ya kwance ko hukuncinta a musulunci ma kamar an saka cleaner an goge mata shi sam bata ganinsa babban burinta a wannan lokacin kawai shine ta ga gawar Ma’ah kwance a gabanta.. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 24. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Sai da Dije ta d’an jima da fita tukunna Inna ta farka da salati d’auke a bakinta. Sakina dama tana kusa dan haka ta shiga dubata su Ramma suna gefe suna hawaye suna bata Baki. Tabbas ita kanta Inna ta san ta dad’e bata yi kuka sannan ta shiga tashin hankali kamar na yau ba! Ji take yi inama sannan addu’a ta ke kawai a samu wani d’an albarkar ya tasheta daga wannan mafarkin tashin hankalin da take yi…tunda aka ce an tsinci gawar Ya Kamal a ruwan k’asan gadar Kaduna (river Kaduna) gaba d’aya ta ke jinta tana yawo a sama kamar leda, har aka shigo da gawar ta kasa gasgata hakan sosai take cikin rud’ani da mad’aukakin tashin hankali da fargabar amsar k’addarar y’artata wadda a yanzun ta fito muraran ba su Isa su ce zasu b’oye ba. Har da Mama ake zaune a d’akin jigumm! Kowa yana cikin alhini dan ko ba komai Ya Kamal mutum ne mai kyauta da mutunci da sanin ya kamata duk fad’ace-fad’acen y’an gidan nan ba’a tab’a jin hayaniyar sa da kowa ba shi ko Mahaifiyarsa. Sai da Sakina ta tabbata Inna ta dawo dai-dai tukunna ta mik’e ta ce “bari in je gida in shirya ina da night duty yau, idan ruwan ya k’are ki k’ok’arta ko chemist ne ki je a sauya maki wani, dan Allah.” Daga haka ta sake yi musu gaisuwa da addu’a ta tafi zuciyarta a cunshe babu dad’i. Kaka tana ganin fitar Sakina ta taso ta zo bakin d’akin ta tsaya ta kama k’ugu ta ce “oya oya fito tunda kin farka, fito kema ki wuce da ke da y’arki ku bi bayan Minu tun kafin farar k’afar ku ta sake dandalo mana wata masifar.” Inna bata damu da haukar Kaka na ‘sai ta fita daga gidan ba’ maganarta da ta yi a yanzun akan Minu ita ce ta jaa hankalinta ta kid’imata dan haka ta d’ago a gigice ta zubawa su Ramma idanu alamun tana buk’atar k’arin bayani. Kawar da kai Ramma ta yi dan bata san ta ina zata

Chapter 18 of 23