sha Allah a kanta zai tsaya ita kad’ai”
Sai kuma ta juya ga Kaka ta ce “wannan rashin sanin ya kamatan naki da aiki da kike yi da k’aramar kwakwalwarkin nan ne ya sanya ko kad’an ba na respecting d’inki wallahi! Allah na tuba in banda rashin man kai wacce
kalar Kaka ce za ta yi wannan furucin ga jikarta??”
Cikin fushi Kaka ta taho tana cewa “Asabe rik’e min Yarinyar nan yau sai na koya mata hankali wallahi, rik’e min ita in daki banza, ya kamata ta san har yanzu Inada ragowar k’arfi na! Shegiya kayan banza”
Nan kuwa Asabe ta shiga k’ok’arin rik’o ta ita kuma tana zillewa tana cewa “Wallahi mai dukana sai ruwan sama”
Dai dai sun rutsa ta a lungu Asabe ta tare hanya Kaka kuma ta taho da sassarfa har da had’awa da gudu ita kuwa Dije ta yi wani tsalle ta bi ta kan kejin kajin Ya Aminu ta tsallake Asabe yayinda Kaka ta je ta gwaru da garu ji kake k’ummm!!! Ta gwara hannu da Kai nan take ta zube a wajen bayan kanta ya bugu sangalalin hannunta kuma ya ce wani ‘k’asss!’
Salati Asabe ta kurma ta fashe da kuka tana cewa “shikenan za ta k’arasa mana ita! Mallan! Mallan!! Mallan!!!!”
Ita kuwa Dije ko d’arr ba ta ji dan dama ita da tsoro sun yi hannun riga, cike da gadara ta ce “gobe kya sake zagin mu… ai mu Allah muka ce shiyasa duk wanda ya tab’o mu yake ganin ba daidai ba.”
Ba ta san lokacin da Ya Muhammad ya shigo tsakar gidan ba sai “wuce ki tafi d’aki” d’in da ya ce mata ta ji.
Tana waigowa ta ganshi a tsaye ransa a d’an b’ace abunda ba ta saba gani ba dan haka ta juya simi simi ta wuce ciki zuciyarta fess!!
Har ga Allah ba ta tausayi ko jin k’an Kaka saboda yadda sarai kuma k’iri k’iri tshohuwar take nuna musu k’iyayya ko kara babu, ta tabbata in da ace babu zunubi tsaff Kaka sai ta kashesu one by one….haka nan suke rayuwarsu su da ita kamar Annabi da kafiri.
A zaune ta tadda Inna tana yankan farce, sai da ta durk’usa tukunna ta ce mata “Inna Ina kwana, ya jikin?”
Dukda ta san Inna ba lalle ta yi mata magana ba tunda ba wani namijin ta kula ko ta yi dambe da shi ba amma sai da ta ji d’ar-d’ar…
Ilai kuwa kamar komai bai faru ba Inna ta d’ago ta kalle ta ta ce “Alhamdulillah.
Ki je ki d’aura mana ruwan d’an wake”
Ajiyar zuciya Dije ta sauk’e kafin ta ce” su Ramma sun jik’a duk itacen kitchen d’in wasu har d’igar ruwa suke yi ragowar kuma ba za su ci da wuri a yi girkin a gama da wuri ba, za su bada wahala su b’ata lokaci. Ko a siyo y’ar tsala
kawai ko?”
Tab’e baki Inna ta yi ba tare da ta damu ta ji mai ya faru ita da waye ba ta ce mata “ki d’auki itacen namu ki kai kan simintin waje ki shanya su, daga nan sai ki biya ki siyi y’ar tsalar ki tahowa Muhammadu da shayi.”
Ta yi maganar tana janyo
purse d’inta ta zaro d’ari shidda ta bata.
Karb’a ta yi ta ce “to” daga nan ta mik’e ta d’auki Hijabin ta har za ta fita sai kuma ta juyo ta ce “Inna in fitar da har murhun in d’aura a kan kejin Ya Aminu ko? Komai na kitchen d’in ya jik’e”
“Eh”
Kawai Innna ta ce mata daga nan ta ci gaba da yankan farcenta.
Tana fitowa ta tarar an kinkimi Kaka an wuce an fita da ita da alama asibiti za su kaita.
Ai kuwa ilai tana fita ta ga anata k’ok’arin dannanta a motar Manager. Ko sake kallon inda suke bata yi ba kamar ba ita ce musabbabin komai ba haka nan ta wuce ta barsu suna ta hayya hayya.
Dije bata dad’e da fita ba, Umar ya fito hannunsa rik’e da wani k’aton salatip fari, kasancewar kusan kaff gidan aka tafi kai Kaka asibiti dan wasu ma a napep suka bisu ya sanya gidan ya zamana shiruuu, tsakar gidan shima ba kowa.
Wani murmushi Umar ya yi ya k’arasa inda akuyar nan take wadda ta ci kuka ta galabaitu zuwa yanzu kukan nata ma da kyar ya ke fita.
Yana zuwa ya nemo kan salatip d’in ya d’agosa ya warwaro ya dedeta bakinta ya mannna mata, a take ta fara kiciniyar kwacewa amma ya danneta ya shiga nad’a mata salatip d’in nan kamar an aiko sa….Umar d’in Yaro ne gashi dukda kasancewar sa Yaron still shekarunsa sun fi wayonsa yawa sosai, gashi so yake yi ya burge Dije idan ta dawo ta tarar ya toshewa Akuya Baki ta daina kuka ya san za ta ji dad’i, dan haka ya had’e har da hancin akuyar ya rufe koina ruff da salatip d’in nan ba tare da ya lura ba.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 04.
Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.
****************
…..SOMEWHERE IN AFRICA…..
Dukda kasancewar garin a waye yake hakan bai sanya d’igon haske ya ratso ta cikin d’akin ba! Ga wanda bai san inda kansa yake ba tsaff zai iya cewa duhun daren wata mai kwana d’aya ko biyu ne, amma a zahirin gaskiya k’arfe goma da rabi ne na safe.
Wata dakakkiyar murya aka yi amfani da ita wajen cewa “ki tabbata idan aka samu matsala wannan karon ranki ne fansa tare da na y’ay’ank’i guda uku!”.
Wani yawu mai tauri d’aci da zafi ta had’iye sannan ta ce “na yi dukkannin abinda ya dace, bani da tantama wannan karon bai isa ya tsallake ba”.
“Ki tabbata idan aka samu matsala wannan karon ranki ne fansa tare da na y’ay’ank’i guda uku!”.
Aka sake maimaita mata maganar ta farko.
Ta san idan ta bari aka maimaita har sau uku hukuncin ta mai tsanani ne dan haka ba dan ranta ya so ba ta ce “Na amince!”
Muryarta na rawa.
Marik’in k’ofar wadda ta kasance ta jar k’asa mai shegen nauyi aka kama aka jaaa k’ofar ta bud’u wanda hakan ya bawa haske damar wanzuwa a cikin d’akin tarr! Har sai da ta yi saurin runtse idanuwanta sakamokon sabawar da ta fara yi da duhun d’akin.
Ficewa aka yi aka barta ita d’aya kwal aka mayar da k’ofar aka rufe duhun nan ya sake mamaye koina..wani Irin kuka ta fashe da shi jikinta yana karkarwa tashin hankali yana sake lullub’e ta, ta san cewa ta yi dukkanin abubuwan da aka sanya ta amma Mai Martaba Sarki ZainulAbidden ba k’aramin d’an baiwa bane ba shiyasa ta ke cikin matsanancin tashin hankali! Ba zata iya k’irga adadin tarkunan da ya shallake ba kama daga haihuwar sa zuwa yanzu ba! Ta yadda aka yi aka haifesa d’a Namiji ma kuma ya rayu a cikin masarautar kanshi abin mamaki tsoro da al’ajabi ne!
Kamar wata zararriya haka ta fara magana tana hawaye ga gumi kamar ana dafata sakamokon rashin b’ulin da iska ko d’aya zata shigo cikin d’akin. “Kaicona! Ina zaune a matsayina cikin kwanciyar hankali tare da uwargijiyata gashi kwad’ayin k’arin matsayi tare da son abun duniya sun janyo min bala’i”
Numfashinta ne ta ji ya fara sark’ewa sakamokon rashin iska dan ta jima a d’akin ta galabaitu, a hankali ta ce “Ya Allah ko da ace wa’adi na ya zo k’arshe ka kub’utar min da y’ay’ana”
Dukda kuwa ta san rayuwarsu a cikin masarautar ba tare da ita ba bala’i ne gasu duk k’ananu amma gara dai su rayu d’in akan su mutu tare da ita….
A hankali ta fara lullumshe ido daga nan ta silale daga zaunen da take ta sume a wajen….
Bayan kamar awa d’aya, ta ji an shek’a mata ruwa!
Haske ta gani tarr! An bud’e k’ofar Fadawa wajen su biyar suna tsaye a kanta. Kukan babbar y’arta ta ji mai kimanin shekaru goma a duniya. Da k’arfi kuma da sauri ta runtse idanuwanta bata kai ga bud’ewa ba aka ce mata “Mai Martaba Sarki ZainulAbidden yana a cikin k’oshin lafiya bayan karin kumallo da ya yi da shayi da dambun naman da kika yi masa”
Bulala arba’in ta hau kanki tare da y’ay’anki bayan nan kuma
Rayukan ku ne fansa!!”
Bud’e Baki ta yi zata fara magiya aka yi saurin toshe mata bakin ta bayanta da wani kyalle haka suma y’ay’an nata….
Ko wannensu sai da Fadawan nan suka yi masa bulala arba’in d’innan kamar yadda suka furta da wata mahaukaciyar bulala wanda tun a bugu na uku da aka yiwa y’ar autarta mai Shekaru hud’u da ita Yarinyar ba ta sake shurawa ba!
Jina jina haka nan suka yi musu tukunna suka fita suka barsu da Baki a toshe gashi babu ko d’igon iska a cikin d’akin da ya kasance na jar k’asa wanda ta waje aka yi masa kamar plasta da langa langa.
Dukda bata gani sosai suna fita ta rarrafa kansu inda take jin nishi sama sama…
Da kyar hannunta yake iya lalubo mata su, ko da ta duba ta k’arshen ta rasu haka shima na biyun babbar y’arta ce kawai ta yi saura, dan haka ta jawo ta ta rungume suna wani irin kuka mai cin rai.
Bayan kamar awa d’aya lokacin da rana ta kwalle numfashi ya yi bankwana da jikin babbbar y’ar tata, lokacin itama ba ta cikin haiyyacinta ta yi sumar wucin gadi, sai da ta farfad’o sannan ta fahimci rumgume take da gawa……Rashin ventilation ga uban warin gawarwakin da wasu suke ta tsutsa da bak’in ciki da azabar radad’in ciwukan da suka jijji mata yayin dukansu da bulalar doki! Ne suka taru suka sanya itama ta ji zuciyarta ta yi wani irin hantsilawa sai kuma ta bada dummm!!! Daga nan ta ce ga garinku nan.
****************
Mallan bai samu ya koma gida ba sai wajajen k’arfen goma na safiyar ranar sakamokon suntumewar da k’afar wannan bawan Allah wanda Ma’a ya yiwa b’alli b’alli a masallaci ta yi, dan sai da ta kaisu ga danganta shi da asibiti yanzu haka ma yana chan an dai yi dressing an nad’e k’afar ana kan bincike.
Yana shigowa tsakar gidan ya hango gawar Akuyar Asabe yashe a tsakar gidan baki a nannad’e!
Dukda ya san ba lalle Dije ta aikata wannan d’anyen aiki ba amma sai ya tsinci kanshi da fara adduar Allah ya sa babu hannunta a ciki, a zuciyarsa.
D’akin Kaka ya nufa da niyyar gaida ita kamar yadda ya saba kullum sai dai kuma ko da ya Isa bakin k’ofar ya kwankwasa sai ya ji shiru, bai wani jima a tsaye ba Inna ta fito tana gyara d’aurin d’ankwalinta, suna had’a ido da shi ta d’an saki fuska ta ce “Ashe kai ne” Sai kuma ta d’an rissina ta gaida shi dukda wadda suka yi a waya ba da jimawa ba.
Cikin kulawa ya amsa mata ta tambayesa mai jiki ya ce mata “da sauk’i” daga nan ya fara rarraba ido ya na k’arewa tsakar gidan kallo….
Sai a yanzu ya lura da yadda gidan ya ke shiruu kamar ma babu kowa, dan in banda Umar da ya gani a kan yashi suna wasa da Yara to bai ga kowa ba kuma bai ji motsin kowa ba bayan Halima da suke gaisawa da ita yanzun, sai ko Rakiya da ya hanga a kitchen tana shan ruwa.
Gyaran murya ya yi bayan ya gama waennan lissafe lissafen ya ce “ina ta kiran wayar Kaka tun d’azu bata d’auka, tana ciki kuwa? Allah dai ya sa lafiya”
Ya jero mata tambayoyin idanunsa a cikin nata.
Numfashi ta fesar ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kafin ta ce “Ka yi hak’uri Mallan, Kaka Dije ta biyo d’azu wai za ta daketa ita kuma ta zille shine ta k’ume da bango ta suma, Aminu kuma yanzu ya fita yake ce min har da gocewar k’ashi a hannu”.
Lumshe idanuwansa ya yi ya fara k’ok’arin controlling temper d’insa, sai da ya samu ya d’an daidaita kansa da kyar! Tukunna ya ware murya ya shiga kwala kiran “Dije! Dije!!”
Cikin kwantar da murya Inna ta ce “tun d’azu na aiketa siyo y’ar tsala ka ga har yanzu ba ta dawo ba babu ita ba abun karin, sai Aminu na bawa ya je ya siyo mana k’osai ga naka a d’aki naga Asabe bata nan”
Shiruu ya d’an yi kafin ya juya a
fusace da niyyar fita suka yi kicib’is da Dije ta kawo kai, bud’ud’u da ita kamar wadda ta yi burgima a cikin yashi..
Da mamaki suke kallonta fuskarnan ta yi jaa idanunta sun firfito waje alamun ta ci kuka.
Baba ya tab’u kwarai da yanayin nata amma hakan bai hanasa d’aga hannu ya d’auketa da wani irin gigitaccen Mari ba!
Cikin karsashi ya ce “duk haukarki ta tsaya iya kan mutanen gida amma ko da wasa kar in sake jin fad’a tsakaninki da Kaka!”
Kamar zai wuce ta ya fita sai kuma ya ce “mai ya sameki kika yi kacha kacha haka? Ko kema kan yashin kika hau?”
Sai a lokacin hawayen bak’in ciki da takaici suka b’alle mata tana yi tana jaan ajiyar zuciya a jejjere…
Sai da Inna ta daka mata tsawa “ba tambayar ki ake yi ba!!!” Tukunna ta magantu ta ce “Ma’a ne ya d’aure mini k’afafuwa da hannnu a lungun mal.mai kanti wai sai dai in taho gida a haka kamar tsutsar caterpillar, kuma suka dinga yi min dariya…”
Rasss!!! Gaban Inna ya yanke ya fad’i, a ranta ta shiga had’a kalmomin tana yi musu fashin bak’i a cikin kanta….Ma’a kuma ya d’aure ta a lungu!! “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” ta shiga nanatawa a cikin ranta sai kuma ta jaaa hannunta suka shige d’aki ta ma manta da Mallan a wajen wanda shima ya yi mutuwar tsaye daga jin zancen…tun kwanakin baya ya cewa Kaka yana so su tashi daga Unguwar amma tunda ta ji saboda Dije ne yake so a tashi d’in nan ta yi tsalle ta dire ta ce ‘ba za su tashi ba, ko dai ta kama kanta ko kuma ta zubar ita ta sani amma ba za a wani tashi saboda ita ba kuma in aka sake yi mata maganar sai ta tsinewa mutum.’
Suna shiga cikin d’akin Inna ta hau duddubata sai kuma ta yi cupping fuskarta a cikin tafukan hannayenta ta ce “ki gaya min gaskiya mai ya faru??”
Cikin sheshshek’ar kuka dan sosai abun ya b’ata mata rai, wai kamar ita Babba da ita za’a d’aure kuma ta gagara guduwa…ta ce “D’azu ne da na dawo daga siyian y’ar tsala wai dan in yi sauri sai na biyo ta lungun malan mai kanti, sai da na kusan kaiwa k’arshen lungun tukunna na lura da su a zaune Yaransa suna ta shaye shaye. Wari gaba d’aya lungun shine na toshe hanci wallahi ko kallonsu ban yi ba ya taso ya zo da kanshi ya saka igiya ya d’aure mini hannu da sauri ta baya sannan ya saka d’ankwalin Oscar ya d’aure min k’afafuwana wai dole in tsaya in shak’i warin da nake toshe hanci shine garin guduwa na fad’i na kasa tafiya wai in yi irin ta cartapillar kawai in k’arasa gida a haka.
suka dinga yi min dariya, na dad’e ina ta k’ok’arin tafiya na kasa har rana ta zo kaina shi yana tsaye a kaina su kuma suna gefe suna ta hira, shine yana gani na fara kuka kuma sai ya yi saurin kunce ni ya ce “in tafi, wai ashe ni marar kunyar k’arya ce.”
Ajiyar zuciya Inna ta sauk’e kafin ta ce “kin tabbata shikenan? Daga haka shikenan?”
Zuwa yanzu Dije ta gane me innar ta ke nufi dan haka ta ce “ko da ya zo d’aurenima ni ban ji ya tab’a ni ba.”
Sosai Inna ta sake sauk’e ajiyar zuciya sai kuma ta koma ta zauna a kan gadonta ta dafe kai.
***
Matsakaicin gida ne (a layin su Dije) mai d’auke da d’akuna uku da babban band’aki da kitchen sai d’aki mai bayi a soro shima Babba.
A d’an hargitse ya shigo cikin gidan yana rarraba ido, idanunsa suna sauk’a a kanta ya k’arasa ya zare silifas d’insa ya zauna a kan tabarmar nan kusa da ita inda take zaune tana tankad’e….
Murmushi ya yi kafin ya ce “uwargida kuma amarya sarautar mata, barka da gida”
Murmushin itama ta mayar masa kafin ta yi masa barka da shigowa sannan ta fara k’ok’arin mik’ewa tana cewa “bari in kawo maka abinci”
Da sauri ya rik’o hannun nata ya ce “A’a ba abinci ba tukunna zauna mu yi wata y’ar magana….a cikin ajiyar da aka baki jiya nake so ki d’an bani rance”.
A take annurin fuskarta ya d’auke, ba ta zauna d’in ba ta ce “dan Allah ka rufawa kanka asiri, ni da ace ina da nawa wallahi da na baka ka sani. Kud’in nan da ka gani ya bani jiya yau fa yace min zai karb’a…”
Cikin katseta ya daka mata wata uwar tsawa yana cewa “ke dalla malama rufewa mutane Baki! Ba wani dogon zance na nemi ji a wajenki ba kud’i kawai za ki ranta min. Kin san ni yau nawa na kashewa b’arnar da ya yi d’azu da asubah a masallaci?…… Ki d’auko mutane zan biya bashi na gaya miki zan mayar kafin ya karb’a.”
Ya yi maganar yana mai matse tafin hannunta wanda yake a cikin nasa..
Azaba sosai take karb’a dan kamar zai karya mata hannun haka yake yi mata cike da mugunta, cikin dauriya ta ce “Allah wannan karon idan ya zo kai tsaye zan ce masa kai ne ka karb’a ba zan sake rufa maka asiri ba..”
Cikin tsananin b’acin rai ya fincikota kuma ba kansa ba gefen taburmar ya zubar da ita sannan ya ce “idan kin fasa!! Ki tashi ki d’auko min kud’i na ce” Ji ta yi kamar mutum a kansu dan haka ta d’ago ta kalli direction d’in aikuwa a take idanunta suka sark’e a cikin nasa, da mugun k’arfi gabanta ya yanke ya fad’i karkarwar da jikinta ke yi ya k’aru gashi babu damar wayancewa dan da gani ya dad’e tsaye a wajen….
Tana shirin yiwa Mallan Idi magana ko ta yi masa inkiya ta ji an fincikesa kamar wanda aka jaaa da mashin hakanan kafin k’iftawar ido ta hangesu ya buga shi da bangon gabas ya shak’esa yana huci!!!
Cikin mad’aukakin tashin hankali ta k’arasa garesu da gudu ta fara k’ok’arin b’amb’are hannunsa daga wuyansa amma ko gezau, tsabar bala’i jikinsa har wani karkarwa yake yi yana huci gashi ya kafesa da idanunsa waenda suka rine da b’acin rai.
Zuwa yanzu idanuwan mallan idi har sun fara k’ak’k’afewa!!
So yake yi ya basa hak’uri amma ya k’i ma ya bashi damar yin hakan, ganin yana shirin aika sa lahira a take ya sanya ta daga hannuwanta duk biyu kawai ta rufesa da duka sai kuma ta fashe da kuka ganin ba ma dukan yake ji ba ta durk’ushe a wajen tana cewa “ka rufawa kanka asiri so kake tsinuwar Allah ta tabbata a kanka ne???”
Sautin kukan ta ne ya d’an fara dawo da shi cikin haiyyacinsa, a hankali ya juya ya kalli yadda ta durkush’e a wajen tana kuka, cikin wani irin rauni ya ce “ki daina kuka!”
Ganin ta yi nasarar karkarto da hankalinsa ne ya sanya kawai ta mik’e ta shige d’aki still tana kukan, ba ta da tantama yanzu zai biyo ta………
Ko gama zama ba ta yi ba ya d’aga labulen d’akin ya shigo fuskarsa a hargitse, cikin rashin jin dad’i ya k’arasa inda take ya zauna ya kamo hannunta.
Fisgewa ta yi cikin kuka ta ce “tashi ka fita”
Cikin rauni dan sam ba ya k’aunar kukan nata ya ce “Mamaa”
A fusace ta juyo tana kallonsa ta ce “me za ka ce min? Ma’aruf ubanka ne fa shi!! Idan ba ka tsoron mutane zuciyarka ta k’ek’ashe ai ya kamata a ce kana jin tsoron mahallicin ka! Ka san me ake nufi da iyaye kuwa? So kake yi Allah ya yi fushi da kai ka sake tab’arb’arewa??? Kalli rayuwarka Ma’aruf ko kishin kanka ba ka yi? Ba aiki ba sana’a ba aure ba girma? Ko wannan fadanci da ake yi maka ganinsa ka ke yi a mazaunin girma? Ka yi karatunka ka je ka nemi aiki ko ka ci gaba da karatun ko ka kama sana’a wannan rayuwar da ka zab’awa kanka ba fa mai b’illewa bace ba, mai ya sa su y’an siyasar ba sa saka y’ay’ansu yin ta’addancin sai kai?….”
Yadda ya runtse ido ya fara haki ne ya sanya ta fahimci ransa ya kai k’ololuwar b’aci, dan haka kawai sai ta kawar da kai ta k’i ci gaba da cewa komai………
A hankali ya zame hannunsa da ke a cikin nata ya ce “dan Allah ki daina kuka”
Daga haka ya mik’e ya juya ya fice fuuu kamar zai tashi sama.
Inda ya bi ya fita ta juya ta bi da kallo zuciyarta sak’e sak’e kala kala…ba ta san wasu ba amma ita dai tunda ta ke ba ta tab’a ganin mutum mai saurin fushi rik’o da taurin zuciya da masifar taurin kai had’e da zafin kai kamar d’anta Ma’aruf ba! A lokacin da ta haifesa bayan ta farfad’o daga suman wucin gadin da ta yi ungozoma hud’u ta tarar a kansa suna ta duba shi dan ya k’i yin kuka sam! Ga dai idanunsa a bud’e yana kallon jama’a amma bai ce uffan ba, k’arshe sai hak’ura suka yi suka ce ta kaisa ya ga Likita….
Sai da ya kai shekaru uku tukunna ta fahimci halayensa tsaff waenda suke matuk’ar d’aure mata kai wasu lokutan..
Tun haihuwarsa Mahaifinsa Mallan idi ya ke jinyar karaya, dan haka ita take fita ta je ta yi aikatau ta nemo musu abinci, barinsa da Ma’a da take yi ne ya bashi damar cin zalin Yaron kamar ba shi ya haifesa ba dan har da molestation
yake had’awa wanda sai da Ma’a d’in ya kai shekaru goma sha biyu tukunna ya gane cutarwa ne ake yi masa kuma abun bai dace ba..shi d’in ya kasance Yaro mai tsananin so da yiwa Mahaifiyarsa biyayya to a duk lokacin da ta dawo gida ya tambayeta me ye hukuncin wanda ba ya yiwa iyayensa biyayya sai ta ce masa “d’an wuta ne” to top it all ya ga ita kanta da ya ke matuk’ar so da girmamawa tana jin tsoron uban, ga uwar wahalar da yake gana masa idan ba ta nan waennan su suka taimaka wajen sake saka tsoronsa a cikin zuciyarsa. Tsoro azabtarwa da wahalhalun da Mallan idi yake basa ne suka bada gudummawa wajen jefasa a hali na damuwa sannan zuciyarsa ta tab’u.
Bak’in Hali da miskilancinsa da ba sa barinsa ma ya shiga cikin Yara ya sanya bai fahimci komai ba sai da Mahaifiyar sa ta harhad’a kud’i da kyar ta saka shi a makaranta lokacin shekarunsa goma sha biyu…….
Musu suke yi shi da wani Yaro Antynsu ta ji shi Ma’a ya ce ‘ko menene idan iyaye suka ce a yi dole a yi’ shi kuma Yaron ya ce masa ‘ban da sab’on Allah.’
Dan haka ta kirasu ta faiyyace masa komai ta yi masa bayani dalla dalla. Ko da ya je islamiyya nan ma same thing Malamin su ya gaya masa dan haka kawai ya samu Mama da maganar kai tsaye.
Da farko ba ta yarda ba sai da ta d’ana tarko ta kama Mallan Idi da kanta tukunna.
Ita sam maganar wanki da ragowar wahalhalun ba su dame ta ba kamar molestation…Yanke jiki ta yi ta fad’i sai a asibiti ta tsinci kanta. Ko da ta farfad’o a take ta ce ba aure! Shi kuma ya ce bata isa ba
Ganin y’an unguwa suna shirin maida su su zauna ne ya sanya ta tatttara kayanta suka gudu ita da Ma’a.
Sai bayan shekaru goma sha d’aya tukunna da kyar aka gano inda suke, ya tattaro mutane har da k’aryar ciwo ya na kuka aka lallab’a ta koma ba dan ranta yana so ba sai dan ba yadda ta iya dan har zuwa wannan lokacin ya ce shi fa bai saketa ba.
Ko da suka dawo ita kanta Mama sai da ta yi mamakin yadda kwata kwata Ma’a bai nemi d’aukar fansa ba gashi a lokacin ya zama rik’ekk’en d’an daba… sai da aka yi watanni tukunna ta fahimci ashe petir yake bashi kullum cokali biyu kuma ya hanashi fad’a, a cewarsa sai ya kashe sa silently kamar yadda ya yi masa… Allah ya taimaki Malan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 23