Share this page
take yi musu nanny. Rakiya ta iya kitso amma har shi uwarta ta hanata yi a ganinta y’ay’anta suna da gata tunda suna da ita dan haka ba za su wahala ba. A kaff gidan za a iya cewa daga Inna sai Ramma a masifa! Irin masifaffun matan nan ne gata wata y’ar firit da ita sai shegen k’arfi da masifar d’aurawa kai…… Ba ta yi minti ashirin ba ta kammala kimtsa d’akin ta fito hannunta rik’e da tsintsiya da abunda ta kwaso shara a ciki. Ba ta kai ga kaiwa bolar ba ta hangi Asabe a cikin kitchen d’in ta bud’e mata tukunya tana ta d’ibar ruwa daga wani botiki tana zubawa a cikin tukunyar. A yadda ta bar tukunyar tata cike taff da ruwa ta san ko kofi d’aya ba zai yiu a k’ara a kai ba tukunyar za ta yi anbaliya amma gashi da ikon Allah Asabe ta kusa juye rabin bokiti amma tukunyar ba ta cika ba. Kwana ta yi ta nufi kitchen d’in hannunta har yanzu rik’e da tsintsiya da katin d’aurin auren da ta kwaso sharar d’akinta a ciki ta nufi kitchen d’in tana adduar Allah dai ya sa ba ruwan fankenta Asabe ta tab’a ba. Kasancewar gari bai fara yin haske ba ya sanya sai da Ramma ta shiga cikin kitchen d’in tukunna ta lura da Zainab d’aure da zani a tsaye tana rawar sanyi.. Tana shigowa Asabe ta d’ago a d’an zabure sai kuma ta dake ta ce “Au Ramma ke ce? Ruwan ki ne?” Zuwa yanzu Ramma ta gama gasgata tabbas ruwanta Asabe ta kandame yanzun kuma take mayar mata da mai sanyi dan haka ta gyara tsayuwarta ranta yana gama b’aci ta ce “A’a na uwarki ne!” Cikin tsananin fushi Asabe ta ce “durun uwa salatin arna, kina da isashshen hankali kuwa? A kan ruwan zafi za ki sako uwata a cikin shirmenki?” Ta yi maganar tana mai k’arasawa daff da ita tana dukan k’irjinta. Dai dai nan Iyya ta shigo cikin kitchen d’in hannunta rik’e da buta da fitila tana salati, cikin takun ta na tsoffi ta k’arasa kusa da su ta ce “haba mana Asabe me ye haka ne kuke yi, gari fa ko fara wayewa bai yi ba?” Cikin zafi masifa da d’acin zuciya Asabe ta ce “wai dan uban wannan matar har ita ta isa ta sako uwata a cikin haukan ta? Kin ga fa Zainab ce zazzab’i ya rufe cikin dare ta kwana tana amai jiya ita kad’ai a d’aki shine yanzu ina shiga na tsinceta kwance shame shame cikin k’azanta ga zazzab’i ruff a jikinta. Shine wai dan na tab’a ruwanta na yi mata wanka yanzu na mayar mata har take da bakin zagina! Dan ubanki kitchen d’in na Tanimu ne?” Salati Iyya ta yi sannan ta ce” Ramma ba ki kyauta ba iyaye sun fi k’arfin wasa sannann larura ce ta sanya ta tab’a miki ruwa ba son ranta ba, ke kuma Asabe dan girman Allah kar in sake ji kin sako mamaci a cikin fad’an ku hakan ba dacewa bane ba!…” Wani Irin huci Ramma ta ke yi zuciyarta tana wani irin tafarfasa, sai da Asabe ta kai aya tukunna ta saka dukkannin k’arfinta ta ingije ta cikin zafin nama ta isa inda Zainab ta ke ta d’aga gaba d’aya sharar d’akinta wadda ta kwaso a cikin katin d’aurin auren nan ta juyewa Zainab a cikin gashinta da jikinta sannan ta durk’usa ta dumbuzo rairayin k’asan kitchen d’in har da toka ta watsa mata a jiki. Kukan kura Asabe ta yi ta yo kanta dai dai nan Ramma ta yi saurin gocewa ta tafi ta afka kan tukunyar gaba d’aya ruwan ciki ya kelaye a kitchen d’in ya jik’a koina da duk wani icce dake cikin kitchen d’in, Allah ya so Asabe ruwan babu zafi amma fa ta k’one sangalalin hannunta da jikin tukunyar sannan zaninta har ya kama wuta nan ma Allah ya taimaka ruwan da ya zube ya jik’a k’oina ya kashe wutar jikin zanin nata wanda ta d’aura akan rigar baccin jikinta da ta murhun duk ya kashe. A zuciye ta yi kan Ramma za ta rufe ta da duka Iyya ta shiga tsakaninsu, tsabar bak’in b’acin rai Asabe bata san lokacin da ta ingije Iyya tana zage zage ta yi kan Ramma ba! Dai dai nan Ya Muhammad wanda tun d’azu yake ta jin hayaniya ya shigo cikin kitchen d’in wanda shigowar tasa ce ta sanya aka samu rangwamin bala’in da yake shirin faruwa dan a yadda Asabe take a zuciye haka itama Ramma shiyasa ta ja ta tsaya jira kawai take yi ta k’arasa inda ta ke ita kuma ta yi mata illa. Ba yadda ya iya ba dan ya so ba haka nan ya ruk’o hannun Asabe da kyar kuwa ya iya rik’e ta dan sai fisge fisge take yi tana zage zage kamar tab’ab’b’iya, sannan ya shiga tsakaninta da Ramma da suke ta jerawa junansu ashar ta uwa ta uba. Salati Kaka ta yi daga shigowarta kafin ta ce “ka cika mata hannu ko sai na ci ubanka? Kwartancin naka kuma yau ta nan ya biyo?” Da sauri Ya Muhammad wanda shi ya ma manta ya kamawa Asabe hannu ya cika ta sai kuma ya yi sauri ya fita ransa na gama b’aci dan ya san yanzu zata fara Inna kuma ba barinta za ta yi ba. Yana fita Asabe ta ce “Kaka wa’adin zaman matar nan a cikin gidan nan ya cika yau wallahi sai ta tafi, na gama yi mata kara.” Wata uwar gud’a Ramma ta rangad’a wadda ta tashi kusan kowa a cikin gidan, kafin ta ce “sai ki bari idan kin Isa da gidan da mai gidan tukunna ki yi magana! Banza wadda bata da k’ima a idon miji kawai! Allah na tuba kina borar ki da ke ke har kin Isa ki ce za ki sa a tashe ni a cikin gidan nan? D’azu fa Ina jinku ke da shi da kyar ya barki kika shigar masa d’aki alhalin duk ranar kwanan Halima tun bayan sallar isha take tafiya idan ba ta je ba kuwa nan zai fara jera mata d’an kira! Ai Wallahi kin yi asara, kamar yadda uwarki ta rako mata duniya kema haka nan kika rako mata duniya, borori kawai!.” Jikin Asabe ne ya fara rawa idanunta suka cicciko….ganin haka ya sanya Kaka ta yi saurin cewa “kar ki kulata, wuce ki tafi, bar ni da ita.” Dan ta fahimci yadda maganar ta daki Asabe tsaff tana iya zubar da hawaye a gaban Ramma da mutanen gidan da duk aka firfito suka yi cirko cirko, aje a sake rainata. Da sauri kuwa ta juya ta fita dan itama ta san ba zata iya rik’e kukanta ba. Tana shiga d’akinta kuwa ta sake shi marar sauti. Asabe tana fita Kaka ta cewa Ramma ‘ta tattara kayanta ita da y’ay’anta su bar gidan tun da ba ta san mutunci ba.’ Ramma kuma ta yi tsalle ta dire ta ce ‘Wallahi ko kud’in hayan da ta biya na shekara ya cika babu inda za ta je, sai ta samu wani gidan tukunna, ai ba haka ake yi ba .’ Nan da nan fad’a sai ya koma kan Kaka da Ramma..dama Kaka haushin Ramma ta ke ji saboda yadda take yawan zagi da gorantawa Asaben kamar ba a gidan Mijinta take haya ba. K’arshe dai Mallan ne ya zo ya raba fad’an dan tabbas Ramma ta fi Kaka gaskiya tunda ta bayar da kud’in haya kuma sun amshe sannan ya san yanzu haka idan Ramma ta tayar da balli ta ce a bata kud’inta ta tafi tabbas basu da kud’in da za su bata, kuma da ikon Allah Kaka ta san da hakan amma ta zage tana balli, kamar idan aka ce ta kawo zata kawo d’in. Bayan an lallab’a Kaka ta koma d’aki Ramma da Maman Kubra suka ce basu yarda da jik’a musu icce da Asabe ta yi ba dan kusan rabin iccen dake a kitchen d’in idan aka d’aga su tsiyayar ruwa ma suke yi, gashi gari babu rana alamun ma ruwa za a zuga yau d’in, ragowar kuma suka ce ba komai ai tsautsayi ne kuma za su ma iya yin amfani da waensu a hakan, Maman Kubra da Ramma kuwa sai da suka karb’i d’ari biyar biyar a hannun Baba kud’in icce tukunna hankalin su ya kwanta a cewarsu ba za su sha wahalar sha’ani da jik’akk’en icce saboda Asabe ba. Sai da k’ura ta lafa tukunna aka fara watsewa ana kafa layin band’aki domin kama ruwa da yin alwalla. Gidan su Suwaiba Ramma ta je ta samu ta d’aura ruwan da zata saka fanken nata a ciki, kafin ruwan zafin ya yi kuwa suka kafa dandalin munafurci kamar ba asubar fari ba. Allah ya taimaka allurar jijiya tana aiki a jikin Inna dan har aka gama budirin nan ba ta sani ba, da kyar Dije bayan ta dawo daga band’aki ta iya tashinta, ta tashi ta yi sallar asuba…….. Cikin wani d’an madaidaicin masallacin da ba zai d’auke sama da mutane hamsin ba! A tsare yake ga hasken lantarki dan solar ce da su Babba ba laifi. Layi uku ne a cikin masallacin inda na chan k’arshe yake cike da mutane na biyun ma haka yayinda ba farkon kuma (kusa da liman) ya kasance babu kowa a wajen tun daga farkonsa har k’arshensa…. Layin k’arshe shima ya cika dan haka wani magidanci wanda ya tare jiya a unguwar har ya zo zai shige aka ce masa ‘ai babu guri a cikin masallacin dan haka sai dai ya tada wani jam’in a kan simintin barandar masallacin.’ Da mamaki ya ke kallon saurayin da ya gama yi masa bayani kafin ya ce “Chan gaba ba sahu bane ba??” Dariya saurayin ya yi kafin ya ce “Eh akwai mai wajen ne” Daga haka ya juya dan har an tada ik’ama. Wani d’an gajeran tsaki magidanci ya ja kafin ya ce “mai waje kuma a masallaci? Wanne irin shirme ne wannan…”daga haka ya wuce ciki chan sahun gaba ya tsaya shi kwalli d’aya kwal ya tayar da ik’ama……. Ba a kai ga kaiwa ruku’u ba Ma’a ya shigo shi da Yaransa guda bakwai ta k’ofar da ya saka a ka bud’a masa dai dai saitin sahun farkon. Da mamaki yake kallon mutumin kafin kawai ya d’auke kanshi ya wuce bayan ya yiwa Yaran nasa alamar su kyalesa da yatsunsa uku. Ana idarwa aka fara watsewa..Mallan (Wanda ya kasance limami a masallacin) shima tunda ya waigo ya ga wani a sahun su Ma’a hankalinsa ya tashi dama chan a tashen yake. Kaff cikin masallacin mutun uku ne (Mallan sai wani tsoho da wannan mutumi na sahun su Ma’a) kawai suka tsaya yin addu’a amma ragowar duk guduwa suka yi. Wannan tsohon yana fita Ma’a ya kalli wani a cikin Yaransa ya ce “je ka siyo min kayan b’alli b’alli, kai kuma ka rufe min shi” Daga haka ya mik’e ya fita waje. Da sauri Mallan ya runtse idanuwansa da mugun k’arfi sai kuma ya juya gaba d’ayansa ya ci gaba da karatun Azkar d’in da yake yi, yana gamawa ya d’auki Al’qurani ya shiga karantowa…. Dai dai nan wannan mutumin ya mik’e ya nufi k’ofa dan gaba d’aya hankalinsa yana a kan wayarsa ne shiyasa bai ga lokacin da aka rurrufe k’ofofi uku na cikin masallacin ba. Kallon k’ofofin ya yi yana mamakin ya aka yi suka rufu kafin ya k’arasa jikin wadda take kallonsa ya gwada bud’ewa ai kuwa ilai ya tarar a gark’ame kamar yadda yake zato, gashi k’ofofin wasu irin k’ofofi ne kamar na tsoron prison dan sam ya kasa ganin ta Ina zai bud’e ta ciki. Da mamaki mutumin ya juyo ya kalli Mallan wanda ya kasa d’agowa sai kuma ya k’arasa inda yake ya ce “akaramakallahu Barkanmu da asuba” A hankali Mallan ya ce “Barka ka dai” Cikin nutsuwa mutumin ya ce masa “inaga Yara sun rufe mu fa ta baya, ko akwai yadda za a yi a bud’e ta ciki?” Mallan yana shirin yin magana Oscar wanda ya shigo yanzun ya k’araso wajen ya ce “mu ne muka rufeka saboda Oga yana da ganawa da kai ne a waje idan ka gama addu’ar, wuce mu je in kai ka wajensa.” Kallonsa mutumin ya yi wanda sai da gabansa ya d’an yanke ya fad’i dan ba Ma’a kad’ai ba hatta Yaran nasa abun tsoro ne, shiyasa mutane da yawa suke mamakin yadda sam Dije bata jin shakkarsa. Gyaran murya mutumin ya yi kafin ya ce “D’ana ka cewa Ogan naka za mu gana da shi anjima dan yanzu haka ko gida ba zan koma ba direct daga masallancin nan akwai in da zan je…..” Cikin katseshi Oscar ya ce “Oga ba ya jira! Idan Oga ya bada umarni dole a yi a lokacin!! Sannan Ma’a ba Oga na bane ba ni kad’ai, Ogan kowa ne har da kai da uwarka da ubanka dan uban babanka!” Cike da b’acin rai wanda tsoro ya hana shi yin tasiri har ya kai ga baiyyana kansa mutumin yake kallon d’an tsakurkurin d’an daban da yake tsaye a gabansa yana masa magana kamar wani ubansa! A yadda ya gansu gaba d’ayansu ya san ba hankali ne da su ba tsaff za su yi masa illa gashi sun tsattsare k’oina har da wani rufesa a ciki dan kar ya gudu, dan haka ya zab’i kawar da duk wani b’acin rai ya bi bayansa suka fita tare domin zuwa inda Ma’a d’in yake duk dan a zauna lafiya sannan ya samu su barshi ya tafi dan important abu ne a gabansa. A kishingid’e yake zaune a kan wata darduma a nan kan barandar gaban masallacin yana kallon gefe kamar wani mai tunani nan kuwa tun fitowarsa idonsa yake a kansa. Mutumin yana zuwa ya tsaya a tsaye ya ce “Oga an ce kana nemana gani nan na zo, na san watak’ila a kan tsayuwa a sahunku da na yi ne na b’ata muku rai, ka yi hak’uri amma wannan dokar taka ba dai dai bace ba, a d’akin Allah muke we are all equal….” Bai kai ga k’arasawa ba wani a cikinsu wanda k’arasowarsa wajen kenan ya k’araso yana zuwa ya tad’e shi da masifar k’arfi cike da mugunta wanda mutumin ya ji kamar an buga masa wani uban katako k’afar ta tsage! A take ya zube a k’asa wajen wanwar yana jin azaba tana ratsa sangalalin k’afarsa. Dariya gabaki d’ayansu suka kwashe da ita banda Ma’a wanda ya kafe mutumin da idanuwa kana ganinsa ka san ransa a b’ace yake. K’arasawa wanda ya tad’e mutumin ya yi kusa da Ma’a, yana zuwa ya durk’usa a kan guiwowinsa ya mik’a masa syring da reza kansa a k’asa ya ce “ka yi hak’uri Oga kar ka ga na dad’e, masu chemist da shagunan ne duk basu bud’e ba sai da na je na kira su.” Jinjina kai Ma’a ya yi daga nan ya had’e yatsunsa biyu manuniya da ta tsakiya ya yi masa alamun ya matsa, jikinsa na rawa ya matsa gefe yana mai kallon wannan mutumin da ragowar mutanen suke zaiyyane masa cewa ‘idan Ma’a yana tsaye rissinawa ake yi, idan yana zaune durk’usawa ake yi idan kuma yana kishingid’e to kwantawa ake yi……..’ Sun fi minti biyar suna yi masa rashin arzik’i! Daga wanda zai talle masa k’eya sai wanda zai hauresa da k’afa rashin mutunci dai kala kala tukunna da kyar Ma’a ya magantu kamar wanda aka yiwa dole ya ce “ku matso min da k’afafuwansa.” K’afafuwan nasa duk biyun kawai suka kama suka jaa shi sai da suka kai kusa da Ma’a tukunna suka cika k’afafuwan suka bugu a k’asa.. Cikin rashin jin dad’i da azab’a mutumin ya ce “Bawan Allah zaman lafiya nake nema! Kar ku yi abinda za ku yi dana sani, dan ina da masu bi mini hakkina, wanne irin wulak’anci ne wannan ku ke yi min?.” Sai a lokacin Ma’a ya d’ago kwayar idanunsa ya zubawa mutumin wanda hakan ya sanya mutumin saurin sunkuyar da kansa dan haka kurum ya ga ya yi masa wani irin mugun kwarjini!! Cike da d’aci da zafin zuciya yana kallon sa wanda shi a yanzu gefen k’afar wanda ya take masa kafad’a dan kar ya tashi zaune yake kallo! Ya ce “daga Abiya har zuwa Zamfara had’e da Abuja! Kai har ma da k’etare na k’asar nan na baka go ahead ka je ka kai k’arata mu ga uban da zai tsaya maka!!!” Cike da mugunta ya b’are allurar ya d’auko tsinin, da gudu Oscar ya zagayo ya zo ya durk’usa ya d’ago masa k’afar mutumin, ido cikin ido suka kalli juna shi da mutumin wanda zuwa yanzu hankalinsa ya gama tashi! Ga tsoro ga uban tozarcin da ake gwada masa. Gashi da ikon Allah wajen kamar an yi ruwa an d’auke babu motsin kowa, duk an gudu, ballanta a kawo masa d’ouki. Still yanzun ma shine ya fara d’auke kwayar idanunsa daga cikin ta Ma’a. A k’ufule Ma’a yana kallonsa ya ce “ka sanar mini idan na tab’o k’ashin k’asan tafin k’afarka!” Gaba d’aya mutumin sai ya zama confused! Bai gama fahimtar mai Ma’a d’in yake nufi ba ya ji ya zurmuk’a masa kusan duk tsinin allurar cikin tafin k’afarsa ta tsakiya cike da rashin imani da rashin tausayi… Jin ana shirin illata shi ya sanya ya kurma ihu sai kuma ya fara salati, dai dai nan Ma’a ya ce “Nop! Ban tab’o ba, ba nan bane ba” Sai kuma ya zaro allurar ya sake chakawa! A take Yaran nasa duk suka fashe da wata mahaukaciyar dariya. Mutumin bai so ya zage su ba amma abunda Ma’a ya ke yi masa ya sanya bai san lokacin da ya fara zabga maganganu yana kiransu da ‘jahilai marar sa hankali da Imani ba a guri a masallaci, waye waye…….’ Kallon Oscar Ma’a ya yi ya ce “saka mini shi a silent!” Mutumin ya gane mai suke nufi dan haka ya fara k’ok’arin kare fuskarsa sai dai bai kai ga rufe fuskar tasa da kan nasa ba Oscar ya bugu masa wani mahaukacin naushin da ya yi sanadiyyar d’aukewar jin sa da ganinsa da hankalinsa gaba d’aya na wucin gadi. Bai tashi farfad’owa ba sai da azabar asalin b’alli b’alli wanda Ma’a yake yi nasa da razor ta dawo da shi cikin haiyyacinsa. Shi dai ya dawo dai dai amma bai iya yin magana ba dan dukkan k’afafuwansa ciwo suke yi masa bawai iyaka tafin ba koina na abunda ya kama daga k’ugunsa zuwa k’asa azaba ce. Dishi dishi da sama sama yake ji, shi dai bai gama sanin abunda yake faruwa ba ya ga Ma’a ya mik’e tsaye ya tsaya a kansa yana goge hannunsa wanda ya yi kacha kacha da jini da wani kyalle, sai da ya gama gogewa tukunna ya kallesa ya ce “kasancewarka sabon zuwa unguwarnan ya sanya na yi maka rangwame, Idan Allah ya sanya k’afafuwan da suka kawoka sahun farko sun warke to ba wai iyaka sahun gaba ba ni Ma’a na haramta maka shigowa masallacin nan har abada.” Daga haka ya wuce Yaransa suka mara masa baya, duk suka bar wajen suka barsa kwance cikin mawuyacin Hali. Suna wucewa Mallan wanda kunnuwansa suke a wajen tun d’azu yake tsaye a tsakiyar masallacin ya fito da sassarfa ya k’arasa kan mutumin wanda har ya sake sumewa. K’arfe shida daidai, Dije ta sake yin juyi ta saki wani malalacin tsaki a karo na babu adadi! Daga yadda akuyar take yin kuka ta k’i shiru tun d’azu zaka fahimci yunwa take ji, gaba d’aya ta hana duk wani marar nauyin bacci yin bacci a safiyar yau da ta kasance ranar hutu. Wani kuka mai cin rai akuyar ta shiga yi dan haka Dije ta tashi ta zauna tana sake jan wani uban tsaki. Zaune ta ga Inna da Al’qurani a hannunta tana karatu dan haka bata gaisheta ba gudun kar ta katseta ta mik’e ta fice a fusace. Babu kowa a tsakar gidan dan garin ya yi matuk’ar yin dad’i sanyi da iska ta koina gashi a lumshe, gwanin ban sha’awa da dad’in bacci ga kowa banda su da Akuya ta addaba da koke koke. A bakin dakalin d’akin ta nemi waje ta zauna tana ta faman turo Baki tana kallon akuyar tana ji kamar ta je ta kasheta kowa ya huta, gata dai y’ar k’arama amma idan ta ware murya ta yi wani ihun sai ka ji kamar wata babbar Akuya ce ta yi. Tana nan zaune tana ta zabgawa akuyar nan harara Umar ya fito daga d’akin Mahaifiyarsa (Maman fati) hannunsa rik’e da kwano. Juyowa ta yi suka had’a ido, cikin tab’e baki ta ce “acici har ka zo ka fara sana’ar kenan!” Dariya ya yi ya ce “Akuya ce ta tashe ni shine na zo na d’auki ragowar abincina na jiya na cinye” sai kuma ya kalleta ya kalli inda take kallo kafin ya nemi waje a gefenta ya zauna ya ce “Yaya Dije kema akuyar nan ce ta taso ki ko? Wallahi muma y’an d’akinmu duk ita ce ta taso mu, su Ya Muhammad suma tun d’azu suke tsaki Mamana ma yanzu da na fito na barta zaginta take ta yi tana tsine mata.” Kallonsa ta yi sai kuma ta kalli k’ofar d’akin Asabe sannan ta d’an d’aga murya ta ce “shegiyar Akuya tsinanniya! Ko da yake ba laifinta bane ba yunwa take ji shiyasa, Allah na tuba dama ita kanta mai kiwon nata ma a karan kanta ta siyawa cikinta abun dad’i ta ci kyashi take yi ka ga kuwa Ina Akuya Ina ita Ina k’oshi?!” Dariya Umar ya yi ya gyara zama ya ce “babu kuwa” Kwafa Dije ta yi sannan ta ce “daga fa ganin Ya Aminu ya fara kiwon kaji shikenan aka tsiri kiwon akuyoyi tsabar gasa, ai kuwa alhaki kawai za a kwasarwa kai dan na san yunwa sai ta yi ajalinsu, kiwo dama ai ba na kowa bane ba, shi dai ya Aminu yana da arzik’in yin kiwo yana da sana’ar da zai ciyar da su shiyasa ya tsira su kuwa masu kiwon akuyoyi sai dai su yi ta d’aukarwa kai alhaki, yo ba ka da gashin wance ai dama ba ka yi kitso wance ba” Umar kuwa dad’in hirar yake ji dan haka ya biyeta tana yi yana tanka mata…Yaron kusan tsaran Zainab ne amma bashi da wayo sosai kuma jininsa ya mugun had’uwa da na Dije gashi ita ba ta ma wani cika kula shi ba dan duk Yaran gidan ba wasa take musu ba, shiyasa yau d’aya da ta biye masa ya ji abun kamar albishir, ita kuwa a halin yanzu da take neman magana ko jinjiri ne ya zo tayata yarda za ta yi. K’asa k’asa ta ce “Wallahi da Ina da salatip yau da sai na manne wa akuyar nan baki da shi kunnen kowa ya huta, shegiya tsinanniya.” Da sauri Umar ya ce ‘Ina da shi a d’akin mu bari…..” “Ku tashi dan ubanku masu neman fad’a” Cewar Kaka wadda muryar Dije ta taso ta daga barci. Dama Dije da biyu take ta hayagaga so take Asabe ko Kaka wani ya kulata ta rama abinda suka yiwa ya Muhammad d’azu da asuba! Ba ta san tak’ameme menene ya faru d’azun a tsakaninsu ba amma dai ta san a kan Asabe ne Kaka ta kira shi da kwarto. Cike da rashin kunya Dije ta ce “uban nawa dai d’an ki ne! Kinga kuwa idan kika zage shi kamar kanki ki ka zaga.” “Tabbas dama na san za ki aikata! Shegiya marar kunya fitsararriya, ai ba laifinki bane ba laifin uwarki ne da ta lalata ku yanzu gashi tun ba a je koina ba kuna shirin addabar al’umma!” Cewar Kaka. Mik’ewa tsaye Dije ta yi ta gyara d’aurin zaninta sannan ta ce “Wallahi kaff cikin mu babu wanda zai addabi al’umma, kaff cikin mu babu mai sata zina ko shaye shaye kinga kuwa mu ba abun gudu bane ba ita wacce kike son kai a kanta kike goyamawa baya ita ce take da wannan tambarin ba dai mu ba dan yanzu haka akwai d’an uwanta a hannun hukuma ya je ya yi shaye shaye ya yiwa al’umma b’arna, kinga kuwa itace mai kashi a gindi.. Mu kam in sha Allah abun alfahari zamu zama wallahi ki rubuta ki ajjiye in sha Allah sai mun yi suna wallahi sai mun baki mamaki” Cikin katseta Kaka ta ce “eh suna a gidan karuwai ba!” Wata mahaukaciyar dariya Asabe wadda ta fito yanzun da niyyar tankawa Dije ta yi kafin ta ce “ai dama baki ya san me zai fad’a amma bai san me za a mayar masa ba” Tab’e Baki Dije ta yi kafin ta ce “ai ba gaskiya ta fad’a ba! Mugun alkaba’i take yiwa mutane wanda in

Chapter 3 of 23