Share this page
ta kafesa da idanu cike da tsananin mamaki da b’acin rai tana masa kallon irin ‘kana hauka ne?’ D’innan. Shima d’in ita ya tsare da dogayen idanuwansa cike da kwarin guiwa ba tare da wani d’ar-d’ar ba. Ba ta shi take yi ba yanzun dan haka kawai sai ta zagayesa ta sake nufar wajen y’artata, amma sai ya kalli tulin Sojoji da Dogaran da suke tsaye a wajen ya ce musu “ku d’auketaa a nan!”. Ba su yi yadda ya ce ba sai da Gimbiya Mariya ta ce musu “ku d’auketa aka ce!!!” Tukunna wasu Sojoji guda biyu mata na masarautar suka nufeta suna zuwa d’ayar ta d’urkusa ta shiga k’ok’arin d’aukarta dan irin jibga-jibgan matan nan ne sojojin. “Hattara daiiii” Muryar wani Dogari wanda suka taho tare da Wambai da Waziri ta karad’e wajen Tsayawa kowa ya yi yana kallonsu, hankali ya koma kansu….. Suna k’arasowa wajen Wambai ya ce “kunce ta!” Jiki na rawa Dogarin nan ya nufi wajen amma sai matar (Gimbiya Mariya) ta daka masa tsawa “idan ka tsallake jan layin nan to ba zaka fito ba sai dai a fitar da gawarka dan tare za a jefe ku!” Sam Dogarin nan bai damu ba haka ya fara k’ok’arin shiga wajen dan ko a mutu ko a yi rai farin cikin ubangidan nasa shine a gabansa, dukda kuwa ya san wacece Gimbiya Mariya kuma ya san me shallake umarninta ka iya janyowa. Wambai d’in ne ya dakatar da shi sannan cikin b’acin rai ya kalleta ya ce “Saboda ba ki d’auki rai a bakin komai ba?…. Hala kin manta wacece wannan d’in ko kuwa dai kan ki ne ya juye.” Takowa ta yi ta zo gabansa ta tsaya ta ce “hattara dai Wambai! Ba kowacce magana ce idan ta taho maka za ka Furtata ga Gimbiya Mariya ba! Zan yi maka uzuri a matsayin mistake amma idan ka kuskura ka maimaita hakan a karo na biyu to zan hukunta ka hukunci mai tsanani dan ya zama ganganci, kuma Gimbiya Mariya ba ta d’aukar wargi.” A fusace Waziri ya yunk’uro zai yi magana Wambai d’in ya rik’e masa hannu da sauri. Sai da ya d’an daidaita fushinsa kafin ya ce “Mai ya faru?”. “Ba ni da lokacin da zan tsaya yi muku bayani! Sakina ta yi Laifi kuma zan hukuntata, that’s final!” Da kyar ya iya janyo numfashi ya fesar da bakinsa ya sake controlling kansa tukunna ya kalli Nuradden ya ce “mai ya faru?” A hankali ya jinjina masa kai sannan ya matso ya ce “bayan dogon bincike da nazari mun gano ita ce ta saka kayan tsafi a k’ark’ashin gadon mai martaba shekaru biyu da suka wuce, ga videon ta nan lokacin da take bawa Hadiminsa wanda aka kama da laifin dumu-dumu….” A take ya kunna ya mik’a musu wayar. Karb’a suka yi jikinsu har wani b’ari yake yi tsabar tashin hankali, gata nan tarr da murya da komai, dukda kuwa video d’in a karkace yake kuma dishi-dishi alamun an sha wahala wajen d’auka da nemosa amma kowa yana gani ya san Gimbiya Sakina ce. Turk’ashi!! Tabbas ko a cikin rami idan ka yi abu a cikin masarautar nan to sai ya fito! Duk wani abu na Makirci da zaka yi in dai ka barr wanda kuka yi tare da shi to sai ya fito, kai ko ka kashe ma tabbas sai an samu leakage daga wani d’an uwan wanda ya yi abun ko wani wanda ya sanshi! Dan da taimakon Oga kwata-kwata, k’ungiyar masu bincike ta masarautar take amfani shiyasa duk k’ank’antar evidence sai sun ganota sun yi amfani da ita ko da kuwa bata kai girman kwayar shinkafa ba. Tabbas shima yanzu ya sake tabbatar da ‘Oga kwata-kwata ba gaibu bane ba!’ Kamar yadda ake cewa (Astaghfirullah!!!)…. Wambai ya aiyyana hakan a cikin zuciyarsa hannuwansa suna karkawa! Ba su da ikon kub’utar da ita dama chan to yanzu kuma ga evidence! He really can’t believe wai yau shine zai nad’e hannu ya zauna a gaban idanunsa a jefe Gimbiya y’ar d’an uwansa! Dan ya san ko da ace Gimbiya Mariya bata da evidence to ba su Isa su hana ba ballantana kuma ga evidence. A hankali ya mik’awa Mai Babban D’aki videon d’in wadda ta matso kusa da su da kyar dan da kyar take iya jan numfashi ma….. Ta na gama gani duk wani k’ok’arinta na son ganin ta ci gaba da tsayuwa a kan kafafuwanta ta ceci y’artata ya sire! A take ta tafi ta sulale a wajen jinta ganinta tare da kuzarinta duk suka d’auke d’iff. A hankali Wambai ya matso ya ce “Tabbas maganar ki dutse! Amma duba da matsayin Gimbiya inaga wannan hukuncin ya yi mata tsauri…” Juyowa ta yi ta wani kallesa daga k’asa ta d’ebosa ta kai sama ta watsar, kamar baza ta ce komai ba sai kuma ta magantu ta ce “Inaga baka san matsayi da girman wanda ta yiwa laifin ba! Kuma ni a yadda na san tsarin masarautar nan in dai ba Sarki mace ta tab’a aura ba to tabbas hukuncin jifa bai sauk’a daga kanta ba!” A hankali Waziri shima ya matso ya ce ”mun ji kuma mun sani amma inaga gara a sakata a ‘kurkukun ban kwana’ ta mutu a chan a kan dai a jefeta! Gimbiya ce fa!! Sannan a gani na wannan hukuncin da kika yanke hukunci ne wanda ya kamata a ce an zauna an tattauna shi a Fada tukunna, tun da na san ba daga Sarki hukuncin nan ya taho kai tsaye ba! Idan kina yanke hukunci da kanki kai tsaye haka to mu meye amfanin mu? Kuma fa ki duba girman al’amarin a ganina ya kamata a tsaya a tattauna….” Shiru ta yi kawai ta na bin motar da ta shigo d’aukar Uwar Marayu, sai da aka zo aka d’auketa aka sakata a ciki aka wuce da ita tukunna ta kalli Fadawanta maza ta ce “su rufe mata gates d’in filin kar su bar kowa ya shigo! Dan ta san yanzu za a taru! Sannan ta juyo ta kalle sa ido cikin ido ta ce “Saifuddeen! Wallahi ko kaine ka aikata laifin yunk’urin tab’a mini Sarki to sai na kaika lahira at the very moment da na yi finding out tun kafin a shiga meeting a wanke ka ko kuma a kaika gidan Yarin da na san za a iya fito da kai daga baya.” Daga haka ta d’auke kai ta kalli bayin da suke wajen durk’ushe cikin tsawa ta ce “Ku jefe min ita na ce!! Ko sai raina ya b’aci?”. A hankali suka mimmik’e suka je suka tsaya a gaban uban tulin dutsunan suka fara d’auka suna jifanta da shi…… Sai da kanta ya fara lilo yana shirin barin gangar jikinta tukunna suka tsayar wanda abunda ba su sani ba tun a jifan farko da wani bafade ya yi mata yanzun zuciyarta ta bugu ta mutu! Barori ne ta koina zagaye da filin ta waje a durk’ushe suna kuka, hatta barorin da suka yi jifan suma akwai masu kukan a cikinsu, Barorin Gimbiya Mariya ne kawai suke farin cikin cika aikin uwargijiyar tasu da kuma wasu a cikin barori waenda Gimbiya Sakinar ta tarewa rawar gaban hantsi da kuma waenda suke jin haushinta…. Suna gama aikinsu suka bar wajen suka koma chan nesa suka zube a k’asa. Jikin Waziri har wani irin karkarwa yake yi! Tabbas ba su da amfani a masarautar nan he really can’t believe he’s this powerless da har ba zai iya sakawa a yi ba ko kuma ya hana a hanu ba. Kallon Nuraddeen kawai yake yi wanda ya matsa kusa da Gimbiya Mariya suna wani k’us-k’us, sosai ya k’ura masa ido yana mamakin sa kamar ba shine Gimbiya Mariyar ta disga a Fada satin da ya gabata ba! ‘Kalli fa hatta Ubansa Mahaifi bai sanarwa abunda take shirin aikatawa ba bayan gashi ga dukkan alamu shine ma a gaban komai, sai kawai gani Wambai d’in ya yi tare da kowa. Wanne irin kusanci ne haka a tsakaninsu sannan what are they up to? Dan tabbas Nuraddeen wanda ko a wajen Ubansa ba ya juyuwa bai kamata a ce ya tsaya suna had’in kai da Mariya ba ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Tabbas akwai wata a k’asa, ko kuma a tsakaninsu wani yana cin dunduniyar wani ne…” Ya aiyyana hakan a ransa….. Kai kana ganin fuskar Gimbiya Mariya ka san cewa she’s relax ta sauk’e wani nauyi. Ana gamawa ta gama magana da Nuraddeen d’in ta wuce bayan ta tamke fuska saboda kar ma wani ya ga rangwame a tare da ita. Bayanta kawai ya bi da kallo yana wani irin murmushi… ‘Tabbas matar nan sai na yi da gaske dan ta wuce tunani na!’ …Gimbiya Sakina yanzu haka shekarunta sun fi arba’in kuma ita ce za a ce Babba-Babba a cikin y’ay’a matan masarautar dan ko Giwar Mata maza ta dinga Haifa haka itama Mai Babban D’aki y’ay’a maza ta yi ta Haifa da farko-farko wannan dalili ya sanya da ta haifi Sakina sai duk ta girmewa ragowar y’ay’an matan Giwar Mata kuma bayan ita sai da ta haifi mata goma sha uku tukunna ta haifi maza biyu amma da ikon Allah yadda ya tsara mata ba ta tab’a ko auren fari ba! Wanda mutanen da basu gama yarda da k’addara ba suke cewa asiri ne aka yi mata. Masarautar ta KHAK’IL tana da collaborations da dayawan k’asashen nahiyoyin duniya wadda ita ce a sama-sama saboda girma da arzik’in k’asar wanda a yanzu haka power su take rawa sabida rashin capable leader! Dan kwata-kwata ko magana da iya tafiyar sarakuna Sarki ZainulAbiddeen bai gama iyawa ba ballantana azo kan mahimman aiyyuka, rannan da jirgin wasa d’an k’arami ya tafi fada ya manta yana mik’ewa jirgin ya fad’o kowa ya gani, da ikon Allah duk da girma ya riskesa amma har yanzun ya gagara ko da kamanta yi musu d’aya daga cikin abubuwan da suka kamata ne, dan ko baya ga k’arancin shekarunsa ma haka nan yake yin wasu abubuwan k’asa da shekarunsa. Wannan ya sanya ake tunanin nad’a Gimbiya Sakina a wasu fannukan kafin ya gama girma ta dinga wakiltar k’asar tunda ita ta yi karatu har PhD a k’asashe mabambanta kuma ta sassan mutane sannan she’s very social shiyasa aka bayar da shawarar a nad’a ta ko kuma su dinga wasu abubuwan tare kafin ya gama mallakar hankalin kansa, duk da kuwa ba a hakan amma a fara a kanta tunda ba su da yadda za su yi dan matan Sarkin sai da suka san yadda suka yi suka haramtawa Waziri da Wambai sarautar k’asar KHAK’IL. Nuraddeen ya je mata da tayin Soyayyarsa dukda kuwa ta girme masa sai dai shi sam bai damu ba dan a yadda ya ga ana shirin yi musu raba dai-dai ita da Sarki tabbas idan ta amince masa to kamar ta yi masa rabin aikin da ya tisa a gaba ne, amma sai ta yi fatali da shi har kusan sau uku wannan dalili ya sanya ya koma b’angaren Uwar Marayu wadda tunda aka fara batun ta rikice ta gigice dan ta san in dai aka fara hakan to suna iya janyowa sarautar ta bar hannun d’anta dad’in d’ad’awa ta fi so ta samu full control da power bata k’aunar sharing ko da d’igon girman kujerar ne da kowa. Wannan dalilin ya sanya ta had’a mata gadar zare ita kuma ta afka ba tare da ta sani ba! Wanda daga ita sai Nuraddeen d’in ne suka san kuma suka fusatata suka k’ulla mata abunda ya sanya dole sai da ta kai ga yunk’urin kashe k’anin nata! ***************** Jiya cikin dare har su Dije sun kwanta ta ji ana tab’a k’ofar d’akinsu dan Inna ta tafi d’akin Mallan. Tana bud’e k’ofar ta ga Sumayya da wasu k’awayenta y’an islamiyyar su a bayanta. Murmushi ta yi cikin sanyin da ba d’abiarta ba ta ce “Ashe da gaske kike” Daga haka ta bud’e musu k’ofar suka shigo ciki….. Dama Sumayya ta iya k’unshi sana’arta kenan, dan haka suna zama ta shiga zana mata jaa na gargajiya. Sai da ya yi ta cire ta saka mahallabiyya tukunna ta zana mata bak’i shima hannu da k’afa mai masifar kyau. Zuwan nasu ya taimaki Dije kam dukda babu abunda ya ragu na game da damuwar da take a ciki amma ta yi raha dan duk su ukun akwaisu da barkwanci. Ba su kwanta ba sai k’arfe uku dan haka suka d’an makara sallar asuba wanda kururuwa da koke-koken Kaka ne ma ya tashe su. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 17. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Cikin gigita duk suka yo waje wanda hakan ya yi dai-dai da k’arasa cikar tsakar gidan. Idanun Kaka suna sauk’a a kanta ta k’araso gareta ta na zuwa ta sa hannu ta shak’eta wanda ko yunk’urin kirki idan Dijen ta yi tsaff sai ta zubar da ita a wajen sakamokon rashin k’arfin jiki na tsufa da take fama da shi…. “Shegiya marar mutunci marar Imani!!!! Dama na san wallahi ke da d’an iskan kwarton kin nan ba za ku hak’ura ba! Yanzu ke kin fi son d’an daba akan mutum mai mutunci?? Da kika san ba zaki auresa ba ai da kin fito kin fad’a an hak’ura ba wai ki tura shi ya kashesa ba!” Salati tsakar gidan nasu ya d’auka yayinda yuuuuuu!! Wani irin jiri ya d’ebi Dije ta tafi zata zube a wajen su Sumayya suka ruk’o su ita da Kaka wadda ta biyo ta luu za ta fad’i itama. Da sauri Mallan ya k’araso wajen ya rik’e Kaka idanunsa jazir alamun ya ci kuka. A karo na ba adadi daga fitowar Kaka zuwa yanzu Asabe ta sake cewa “Kaka mai ya faru? Ya rasu fa kika ce, Yusufan ne ya rasu.” Cikin kuka mai cin rai Kaka ta ce “Wallahi Yusufa ya rasu Asabe ya riga mu gidan gaskiya sun kashe mini jikana!!” Sai kuma a fusace ta sake yin kan Dije Mallan ya yi saurin sake ruk’ota amma cha take “shegiya y’ar iska muguwa! Saboda son ranku gashi yanzu kin mayarda Y’ay’a takwas marayu mata biyu zawarawa, wannan wacce iriyar Annoba ce Allah ya sako min ita a cikin zuriata?? Mallan ka rabani da Yarinyar nan ta b’ace mini daga gani kafin zuciyata ta buga!” Sosai Kaka take kuka wanda tsaff idan ka ganta dole ta baka tausayi. “Shi kad’ai iyayensa suka haifa amma tsabar rashin imani saboda bin son zuciyarki ke da d’an iskan kwartonki d’an daba kun yi musu yankan k’auna…” A hankali Iyya ta matso ta ce “ki daina aibantata sannan kar ki d’aura zargi a mazaunin tabbataccen abu tunda baki da tabbas.” Cikin kuka Kaka ta kalleta idanunta jazir ta ce “Wallahi tallahi ba ni da tantama shi ne ya kashesa… A bud’e aka tarar da k’ofar gidan nasa da aka shiga kowa bacci yake yi mai masifar nauyi baccin da har yanzu da muke maganar nan da ke basu farka ba! Kinga kenan abu aka shak’a musu! Kuma aka tarar da shi da wuk’a chake a k’ahon zuciya da wata a yashe a kusa da matarsa inaga itama so ya yi ya kasheta watak’il ya ji motsi shine ya gudu! Ki gaya min wannan aika-aikar kisan gillar dana wa ya yi miki kama??? Wallahi wallahi bani da tantama shine! Kuma wannan” Ta yi maganar ta na mai nuna Dije kafin ta ce “da saninta aka yi komai. Ai ko Sagir shima na san k’are mata kallon da ya yi ne ya sanya data gaya masa aka kashe sa! In ba haka ba ai kaff samarin gidan nan duk sun fita mai yasa su bai kashesu ba sai shi?” Ta yi maganar har yanzun tana kallon Dije da rinannun idanunta da suke baiyyana tsana da tsantsar tashin hankali da b’acin rai. Basu ga k’arasowar Mahaifiyar Sagir ba sai sauk’ar ruwan dukan da ta shiga sauk’ewa Dije ne ya sanya aka ganta. Fad’i take “shegiya tsinanniya y’ar iska wallahi yau mai raba ni da ke sai Allah sai na kasheki in sha Allahu” Tashi d’aya matar ta sake hargitsa tsakar gidan ta sake gigita kowa gashi sai wani irin kuka take yi kamar ranta zai fita, sauk’inta d’aya ma Kubra bata ji ba dan an yi mata allurar bacci mai nauyi ne. Da kyar su Gwaggo suka janyeta Iyya ta ce “Ashe ba ki san k’addara ba? Ita har ta Isa ta kashe ko ta saka a kashe ba tare da izinin Allah ba? Daga an fad’i magana haka nan kawai tashi d’aya har kin hau kin zauna kin fara aiki da ita kina hauka ne???” Cikin kuka Maman Sagir ta ce “ai dan ba Kamal bane ba shiyasa kike da bakin magana! Na rok’i Ubangiji da ‘ya d’aura masa Irin k’addarar da kike ambatowa d’in’.” Duk da Iyya ta ji zafin maganar kuma abun ya yi mata ciwo amma sai kawai ta girgiza kai bata ce mata komai ba ta juya ta wuce d’aki. Abunda Kaka take yi bai gigita Dije ba kamar yadda Baba ya titsiyeta akan ‘sai ta gaya masa gaskiyar sun yi maganar Yusufa da Ma’a! Dan in ba haka ba to a Ina ya san har hanyar gidansa’ ba, A gaban mutane. Shiyasa ba ta san lokacin da ta durk’ushe a wajen kawai ta fashe masa da kuka ba. Wani irin kuka Dije take yi kamar ranta zai fita dan har wani shishshid’ewa take yi gashi ta k’i jin rarrashi, wanda hakan ya sanya jikinsa ya d’an yi sanyi kafin ya juya kawai ya bar wajen k’irjinsa yana dukan uku-uku. A hankali Inna ta k’araso ta mik’ar da ita suka wuce ciki Kaka tana zaginsu ta uwa ta uba kamar ba tsohuwa ba. Ba a yi minti ashirin ba suka shirya chap suka d’auki hanyar Getso har da Asabe da Zainab, ita Inna bama ta sani ba sai a bakin Minu ta ji wanda bai dad’e da dawowa daga asibiti ba. Bayan tafiyarsu ta gwada kiran Mahaifiyar Yusufa a waya ta yi mata ta’aziyya amma sai ta k’i d’agawa k’arshema sai ta dinga rejecting dan haka ta hak’ura ta bari akan washegari ta yi mata. Tunda Mallan yake bai tab’a shiga tashin hankali irin wannan ba dan ya ji mutuwar nephew d’in nasa gashi halin da ya ga d’an uwa da Mahaifiyarsa sun shiga ya sake kid’ima shi matuk’a. Kafin dare labari ya karad’e unguwa ya zama topic of the day ‘Ma’aah ya kashe wanda Dije zata aura, ba shi kad’ai ba ma hatta Sagir saboda ya ga yana sinsinar Dijen ne shiyasa ya kashesa ashe.’ Zuwa wannan lokacin kam kowa ya fahimci takurar Ma’ah ga Dije ashe so ne, dan haka labarin sai ya yi sauk’in fassaruwa aka dinga kasa shi a faranti dalla-dalla. Yayinda babban tashin hankalin Inna a yanzu ya zamto ‘waye zai auri y’arta?’ Dan ko ba d’an unguwa bane ba tabbas ta san idan ya zo yin bincike akan Dije wannan shine abu na farko da za’a fara fad’a masa…..duba da yadda a yanzu aka zuzuta abun a unguwar, ake ta shigowa ana jajantawa waenda bakinsu ba ya yin shiru ne suke fitowa su gaya mata halinda ake ciki yayinda waensu gulma da son sake gigitasu ne kawai yake kawo su. Zazzab’in da ya rufe Dije ya sanya dole sai da aka kirawo Sakina ta zo ta yi mata allurai itama tana yi tana tata gulmar….. Washegari da safe Ma’ah ya nemi number Mallan ya kira shi a waya ya yi masa ta’aziyyar rasuwar Yusufa! Wanda Mallan d’in ya rasa ma bakin magana, daga haka ya sanar masa ya tafi Abuja ana ta shirye-shirye za su wuce England za’a je a duba Mahaifiyarsa idan ya dawo zai zo ya same shi. Daga nan ya kashe wayar ya bar Mallan da waya kare a kunnensa! Tabbas idan zai mutu a yau to aurar da Dije will be the first thing to do in sha Allah a yau ba sai gobe ba. Sai dai kuma a kaff garin babu wanda ya karb’i shelar tayinsa dan ko an yarda idan aka ji ba’asin rasuwar Yusufa wanda nan d’in ma ya karad’e garin sai a ce an fasa…. Kwanan Mallan uku yana nemawa Dije Miji a garin Getso amma bai samo ba wanda hakan ya sake firgita shi matuk’a. Zuwa wannan lokacin kuma ya fahimci Kaka da Mahaifin Yusufa haushinsa suke ji ata dalilin rasuwar Yusufa saboda Dije wanda tun da aka yi rasuwar dama ya ga sun sauya masa to kuma tunda suka zo suka had’u da Anty d’in Kaka Iyya lami da Umma(Mahaifiyar Yusufa) abun nasu sai ya k’ara tsanani. Yau kam k’iri k’iri Kaka ta ce masa ‘ya nemi wajen kwana d’akin Baban Yusufa inda yake kwana ya cika taff da b’akin kunya da suka zo gari ya gari dan haka ya nemi wani wajen ko kuma ya koma Kano kawai.’ Shima dama abunda yake so d’in kenan dan ya lura zama a tsakiyarsu a haka ka iya janyo matsala, dan haka ya tattaro ya sake yi musu gaisuwa da sallama wanda Iyya lami da uwargidan Yusufan suka k’i amsawa sai amaryar tasa ce kawai ta amsa masa itama a kumbure. Su Kaka suma da kyar suke iya mayar masa da magana, shi dai ya yi musu duk wani abunda yake ganin ya dace daga haka ya wuto Kano da k’udirin aurar da Dije kafin ma ya shiga cikin Gidansa. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 18. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Yana karyo kwanar layin gidan nasa ya ci karo da Mallan Manniru. Ajiyar zuciya dattijon ya sauk’e wanda yake kusan tsara d’aya da Mallan d’in sannan ya mik’a masa hannu suka yi musabaha cikin jimami ya ce “Ashe haka ce ta faru kuma? Ya hak’uri?”. Jinjina kai Mallan ya yi tukunna ya ce “Hak’uri Alhamdulillah da godiya”. Fuskarsa na baiyyana rashin jin dad’i ya ce “Allah ya ji k’ansa ya gafarta masa”. Mallan ya ce “Ameen” Dan gaba d’aya jikinsa a sanyaye yake ga rashin lafiyar da take cinsa ba tare da kowa ya sani ba. Sai da ya d’an numfasa tukunna ya ce “haka kurum ya janyowa Yarinya bak’in jini!”. A hankali cikin sanyi Mallan ya d’ago daga kallon k’asan da yake yi ya kafesa da ido. Wanda hakan da ya yi ya sanya Mallan Manniru gyara tsayuwarsa ya ce “Ko dai baka san abunda yake faruwa a layin ba kwana biyu?” Bai jira an bashi amsa ba ya ce “Ai yanzu bak’in jinin Ma’ah gaba d’aya kan Dije ya komo, tunda suka fahimci yana k’aunarta shikenan sai suka d’auki karar tsana suka d’aura mata kamar ma ta riga da ta zama matarsa ne. A halin yanzu fa sun koreta daga makarantar islamiyya jiya Sumayya take gaya min, wai sun ce ‘saboda gudun kar a hukunta ta ko ta samu sab’ani da wani ko wata shi kuma ya zo ya kashe kowa!’ To d’azu ma dai har ta tafi bokon kuma sai na ga nan ma d’in ta dawo lokacin Ina shago kuma kamar ma kuka take yi, ta zo ta wuce gida alamun suma d’in dai korota suka yi.” Wani irin yawu mai tauri da d’aci Mallan ya had’iye da kyar! A hankali ya sake zuba masa idanunsa waenda suka fara rinewa ya ce “Mallan Manniru za ka iya auren Dije?” Rasss!! Gabansa ya yanke ya fad’i, sai kuma wani sanyi tare da fargaba suka rufe shi. A hankali Mallan ya ce “D’a na kowa ne Mallan Manniru, ka rufa mini asiri ka auri Yarinyar nan tun kafin fita ta gagareta, mutane sun yiwa abun hukunci da wuri wanda ba su da tabbacin Ma’ah d’in ne ya yi tunda ai bai ma san adreshin Yusufan ba ka ga kuma ba zai yiu ace ya nemo ya yi shiri ya je ya kashesa a cikin kwana d’aya tak! Da ya ji labarin auren nata ba.” Jinjina kai Mallan Manniru ya yi, duk da cewa Dije ta kasance k’awa, babbar k’awa ma kuwa ga y’ar sa har ga Allah dama ya dad’e yana harin Yarinyar. Yanzu kuwa ga dama ta samu, dukda kuwa wanchan al’amari da ya faru da Yusufa yana d’an firgita shi amma sai ya tuna ai basu da tabbacin hakan ne, dan haka ya d’ago ya kallesa ya ce “Na amince”. Jinjina kai Mallan ya yi cikin jin wani relief yana sauk’ar masa ya bashi hannu suka sake gaisawa ya ce “na baka Khadijah, kar ka damu da duk wata bidi’a sadakinta kawai za ka mik’o a d’aura muku aure yanzu. Bari in nemo shaidu sai a k’arasa masallacin” Murmushi Mallan Manniru ya yi irin ta jin kunyar surukantakar nan, sannan ya d’an sosa bayan kansa ya ce “da wuri haka Mallan…”. A hankali gaban Mallan yana fad’uwa dan so yake yi kawai ya ga ya d’aurawa

Chapter 14 of 23