Share this page
ni ba ma izinin fara zance da ita ko wani abu makamancin hakan na zo nema kad’ai ba! Na zo ne in gabatar maka da kaina a matsayin wanda yake neman auren y’arka Khadijah kuma Mijinta har a aljannah in sha Allah.” Har ga Allah tsabar yadda Mallan ya shiga mad’aukakin tashin hankali da rud’ani wallahi shi manta ma ‘wacece Khadijar’ ya yi! Sai da ya dedeta kanshi da taimakon addu’o’i tukunna da mugun kyar ya samu ya iya had’a 1+1. Wani Irin gumi ne ya shiga tsattsafo masa ta koina, da ya bud’e Baki zai fara magana sai bakin ya hau karkarwa ya ji ya gagara furta komai! D’agowa ya yi ya d’an kallesu ya ga Ma’ah ya kafesa da rikitattun rinannun idanunsa babu alamar annuri rahama ko sassauchi a kan fuskarsa. Da sauri ya kawar da kansa gefe yana mai jin yadda zuciyarsa take wani irin hantsilawa kamar za ta fashe ne. Cikin magagin buguwa Oscar wanda suma duk sun zuba masa idanune ya ce “Baba ya na ga ka shiga trembling ne? Mu fa nan da ka ganmu ko a yanzu a shirye muke da sadakin mu a hannu, idan kuma kana buk’atar preparation to sai a saka sati d’aya ko biyu, saboda Mai gida za su tafi k’asar turawa ne jinyar Mama kuma da ita yake so ya tafi…” Cikin bayarda umarni Scorpion ya ce “ka yanke komai mu gama magana yanzu, kawai dai ka tabbatar ka yi abunda mukeso, dan ko baka yi ba ranka ne zai b’aci amma dole za a d’aura da izinin Allah, saboda Oga shine Mijinta har a gidan Aljannah” A tare duk suka ce “in shaa Allah”. “Ikon Allah, Allah shine mai aljannar amma Astaghfirullah yanzu suma waennan ashe suna saka ran shiga aljannah??” Kawu Isah ya yiwa kansa tambayar a cikin zuciyarsa ba tare da ya san mai bashi amsa ba. Sunkuyar da kai Mallan ya sake yi a karo na babu adadi! Bai riga da ya d’aura auren Dije da Ma’aruf ba kuma ya san kansa a gabas ba zai tab’a d’aurawa ba amma the fact that ‘wai Ma’aruf d’an daba wanda yake yiwa kallon the most useless human being a duniya a idanunsa! Wai yau shine ya zo yana neman auren y’arsa’ hakan ya sanya wasu hawayen bak’in ciki da tashin hankali suka zubo masa…shi musulmi ne kuma mutum ne mai addini ya san cewa kyamatar d’an uwa musulmi bai dace ba amma tabbas a yadda yake jin kyamar Ma’aruf wallah idan aka ce yau ya auri Khadija to sai ya had’iyi zuciya ya mutu har lahira!. D’agowa ya yi suka had’a ido da Ma’ah wanda har yanzun shi yake kallo ba ya ko k’yafta idanu. Ganin yana ta faman dibi-dibi akan abunda ko hauka suke yi ba za su tab’a k’ullawa ba ya sanya Kawu Isa ya kalli Ma’ah ya ce “Mallan Ma’aruf ko?” Bai jira ya bashi amsa ba ya ce “asalin gaskiya shine gobe iwar haka ma Dije tana a matsayin matar wani idan Allah ya yar.” “To ai da sauk’i! Tunda gobe ka ce ba yanzu ko jiya ba, kawai yanzu abunda zai faru shi ne..a d’aura musu auren ma yanzu tunda ga abunda na ji kun fara cewa saboda gudun samun matsala, dan a zauna lafiya.” Scorpion ya zaiyyane musu hakan cikin katse shi fuskarsa tana mai chanjawa zuwa wani yanayi na daban. “Ina ga kamar baka fahimce ni ba….mun riga mun bayar da ita ga d’ana d’an uwanta, kuma na san ka san cewa neman aure cikin aure haramun ne ko?” Cikin tarar numfashinsa Oscar ya ce “mun fahimci abunda kake nufi mana kwarai! Abunda muma muke so ku fahimta shine ku chanja tsari a bawa wanchan hak’uri a mayar masa da kud’insa dan mu bamu san mu ce muna son abu a ce mana A’a ba! Kune iyayenta kune magabatanta dan haka chanja hakan a wajenku na tabbata abu ne mai sauk’i…..” Shi dai Mallan bai ce komai ba Ma’ah kawai ya tsurawa ido wanda ya kawar da kansa gefe guda! Ya lura hatta naman kumatunsa wani irin karkarwa yake yi alamun bala’i yana cin sa. Oscar yana dire aya Ma’a ya mik’e tsaye kawai! A hankali ya ce “Baba a duba lamarin nan saboda Allah.” Daga haka ya wuce ba tare da ya k’ara ce musu komai ba….. Sai da su Oscar suka gama treatning su Mallan kamar ba surukan da suke saka ran auren y’arsu ba! Tukunna suka mik’e suka fita Scorpion yana ta bala’i kamar zai ari harshe…………….. Yau dai Mallan ya shirya tunkarar Inna a yita ta k’are dan tabbas shirunta ya fara yi masa illah! Ya shirya zai shiga d’akin ya rutsata idan za su shekara ba zai fita ba har sai ta kula shi. Sai da ya kira Usama ya bashi tofin da ake bawa Kubra (wadda take neman haukace musu a gidan, dan har ta fi Mahaifiyar Sagir d’in gigicewa) ya ce a mik’a mata Yaron ya karb’a ya shiga d’akin da sallama, tukunna shima ya yi sallama kafin ya tura k’ofar d’akin na su Dije ya shiga. Suna zaune tana cikin yiwa Dije nasiha Mallan d’in ya shigo. A hankali cikin nutsuwa Dije ta gaida shi ya amsa idanunsa a kan Inna. Waje ya nema ya zauna a gefensu still yana kallonta ita kam ko inda yake bata kalla ba. Ba dan tana so ba sai dan ba zata iya ba ya sanya ta ce masa “Ina wuni” Still ba ta kallesa ba. A hankali ya sauk’e numfashi idanunsa a kanta ya ce “Alhamdulillah, ya jiki da gida?.” “Da sauk’i” kawai ta ce, daga haka d’akin ya kasance shiruu.. Mik’ewa Dije ta yi za ta fita ya ce “dawo ki zauna” Cikin kasala da mutuwar jiki ta koma ta zauna kanta a k’asa tana mai k’ok’arin danne kukan da yake ta faman taso mata. Gaba d’aya tunda aka ce za a aurar da ita yau kwana uku kenan bayan fitar uzuri sau uku kawai ta fita daga d’akin nasu, na farko zuwa asibiti emergency na biyu duba Ya Muhammad sai na uku d’azu da rana da ta fita ta tuk’a musu tuwo amma ko girki Inna ce take yi y’an gidan kansu ta yi musu yaji sun daina ganinta! Ita ganin abun ma take yi kamar a mafarki wai ita Dije za a aurar auren ma na dole duk a ta sanadiyyar Kaka! Gashi abun ya had’e musu da alhini dan haka k’uncin sai ya assasa. Tabbas tsakanin shekaran jiya da yau Kaka ta sha zagi da tsinuwa tare da Allah ya Isa a wajen Dije ya fi cikin kwando! Ba ta tab’a jin takaicin rashin dangin da Innarsu ta tsinci kanta a ciiki ba sai a yau! Dan wallahi da gidan d’aya a ciki za ta gudu ta b’oye sai an manta an hak’ura da maganar tukunna za ta dawo…… “Dije, Ba ni da niyyar yi miki dole, ba ni da niyyar aurar da ke yanzu sannan ban so na kai ki ki yi rayuwa a k’auye ba amma an fi k’arfina ta koina ba ni da yadda zan yi ne shiyasa…. Tun ba yau ba saboda Ma’aruf na so a ce mun bar Unguwar nan duba da yadda ya tasoki a gaba amma Kaka ta k’i aminta da hakan! Kina da hakk’i a kaina haka zalika itakuma nata matsayin mafi girmane, duk yadda zan fasalta miki mafi k’ololuwar darajar da ake so ka kamanta wajen mu’amalantar iyayenka da hakan ya yi kad’an! Amma duk da hakan na san kuna ganin yadda nake iyaka bakin k’ok’arina wajen kareku a duk lokacin da aka wuce layi duk da kuwa ko musayar yawu ba a so ka dinga yi da iyaye!. Ina so ki san cewa tun kafin ki kai haka kawunki Isa yake nema wa d’ansa Yusufa aurenki. Bayan ku da Kaka da Isa su kad’ai gareni a kaff fad’in duniyar nan sai ko iya lami. Kaka tana ik’irarin tsinemin shi kuma ya zo min da wannan maganar wadda ita ce mafitar dukkannin matsalata ya kike so in yi? Duk da haka ban so kaina ba dan inda ace ba dan kariyarki ba to da ba zan fake a bayan inuwarki in ceci kaina ba! Dije baki ya yi yawa a kanki, Kaka Asabe y’an gidan nan duk sun sakoki a gaba wanda ban san dalilinsu na yin hakan ba kowa so yake yi ya ga bayanki. Harshe yana da kaifi su kuma a ko da yaushe idan suka bud’u Baki basu da abun fad’e na alkhairi a kanki sai sharri! Wanda Allah kad’ai ya san kalar tashin hankalin da nakan shiga a duk lokacin da na ji Irin haka. Abu na biyu shine Ina so ki san cewa idan Allah ya k’addara Yusufa ba Mijinki bane ba to babu ta yadda za a yi ki auresa ko da kuwa abunda yake a tsakanin ku da d’aurin auren naku bai rage girman kwayar zarrah ba! Haka zalika idan Allah ya k’addara Mijinki ne shi to ko da ace babu mu kuma ba ku san juna ba babu wata dangantaka a tsakaninku ke kina China shi yana Getso Dije sai kin auresa! Dan haka ki saka a kanki aurenki da shi abunda Allah ya tsara ne ba wai ni ko a ta silar Kaka ba. Sannan mutum yakan iya barin k’auye ya dawo birni ko kuma na birni ya koma k’auye wannan duk tsarin Allah ne kuma in har ya k’addara to sai an yi ko da kuwa Sarki za ki aura to idan ya k’addara a k’auye za ki rayu sai fa kin rayu a k’auyen nan. Abu na k’arshe kuma da nakeso ki saka a kanki shine da mai kud’i da marar kud’i da d’an k’auye da mai ilimi da marar ilimi duk Ubangiji ne ya yi su! Bawa kuma bai Isa ya shallake k’addararsa ba! Dan haka ki rungumi ambaton sunan Allah ki yi ta addu’a na rantse miki baza ki tab’e ba!” Maganata ta gaba itace tun ba yau ba na lura da take-taken Ma’aruf wanda ba zan b’oye miki ba har da hakan ya sanya na amincewa kawunki dan gara Yusufa sau dubu a kan Ma’aruf wanda na san in har ya furta yana son ki to akwai matsala! Dan ni kad’ai na san me na hanga.. Kuma Dije da in bar ki ki auri Ma’aruf ki yi rayuwa da shi gara ace babu ke!… Ilai kuwa sai gashi yau ya zo neman aurenki a wajena yanzunnan muka rabu da shi.” A firgice duk suka d’ago suna kallonsa. Jinjina musu kai ya yi sannan ya ce “dan haka dan Allah ku bani had’in kai a samu a yi auren nan Dije ta tafi ta tare a gidanta tun kafin ya b’allo mana wata b’arnar… D’azu Minu har kuka ya yi mini a d’aki dan Allah Halima ki taimaka ki taya ni fahimtar da shi, Mun yi magana da Yusufa ya ce in sha Allah zai san yadda zai yi ta ci gaba da karatu ko da hakan yana nufin ya mayar da ita madobi ko kura ta samu ta yi polytechnic dan shima dama kasuwancinsa a tsakankanin nan d’in ne. Ya ce min in sha Allah har aiki Dije sai ta yi amma yanzu a jira a fara yin auren dan idan ya tsame ta daga cikinsu yanzun tashi d’aya to akwai matsala, itama amaryarsa yanzu haka waec take rubutawa Uwargidan kuma ita ce ta k’i shiyasa, dan haka kinga ba ta da matsalar karatu sannan ya ce a gida daban zai ajjiyeta yanzun ma, ba zai had’ata da su ba. Ku kwantar da hankalinku ku taya ni kwantar mata a samu a yi abunnan mu rufawa junanmu asiri dan Allah. Idan Allah ya yi za ta yi karatu ko a k’ark’ashin rami ta ke za ta yi….” Na san na gaza miki a matsayin uba amma nima abubuwan sun fi k’arfina ne, da ke da y’an uwanki da mahaifiyarku na san duk na gaza muku, ku yi hak’uri ba ni na zab’i hakan ba a haka tawa kaddarar ta zo, ku yi hak’uri dan Allah ku yafewa Mahaifinku Halima ki yafewa Mijinki ki taimaka ki ce wani abun ki bani amsa dan Allah ki yi min magana.” Ya k’arashe maganar yana mai had’e hannuwansa waje guda abun tausayi. Zuciya da abunda take so gaba d’aya tashi d’aya duk sai Inna ta yi sanyi. Sai da ta saka hannu ta sauk’e masa hannunsa daga alamar rok’o da ya yi tukunna a hankali ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kafin ta ce “tun a ranar da ka ce ka bayar da ita ba ni da jaa a kan hakan Mallan dan na yarda ba zaka cutar da ita ba kuma na yarda da k’addara, sannan kamar yadda ka fad’a Allah shine ya yi kowa duk d’aya muke babu wanda ya fi wani kuma kamar yadda ka fad’a idan Allah ya yi zata yi karatun to fa ko a k’ark’ashin dutse take sai ta yi, idan kuma ya rubuta ba zata yi ba to ko a bakin makarantar gidanta yake ba zata yi ba! Sannan ni kaina shaida ce kuma na yarda da k’aunar da Yusufa yake yi mata. Sannan rayuwarma da ake ta buri a kanta dududu nawa take? Mu da ma bamu san wa’adin mu ba. Dan haka na amince d’ari bisa d’ari yanzu haka ma da ka shigo ka ganmu nasiha nake yi mata. Kuma maganr Ma’aruf ba kai kad’ai ba har ni nan kaina na fara fahimtar hakan, kuma har ga Allah ba k’aramin dad’i na ji ba da ya kasance sai da aka gama maganar aurenta tukunna shi ya zo daga baya, ka ga dole ya hak’ura kenan.” Jinjina kai Mallan ya yi yana mai fitar da wani huci mai zafi, sai kuma ya d’ago ya kalleta yana murmushi….Ba k’aramin dad’i ya ji ba dan sai da ya yi hawayen farin ciki, sannan ya shiga jero mata albarka da addu’o’i masu tarin yawa…… A tsari dama sai an d’aura aure da sati d’aya tukunna za su tare, dan yanzu haka ma ginin gidan nata inda za ta zauna flasta ake yi ba a kai ga yin ko fenti ba, shima kuma Mallan dama ya ce musu su bashi sati d’aya ya yi siyayya. Ya san dan sati d’aya dai Kaka zata yi hak’uri ta k’ara musu, za a sha daru kam amma ya san za ta k’ara musu kuma ma Mahaifiyar Yusufa ta ce tun ana i saura kwana biyar d’aukar amaryar za ta taho dan haka ya san ba shi da matsala tunda ba laifi suna shiri da matar idan ta ga dama. Adduarsa d’aya Allah ya basu zaman lafiya Allah ya bawa Dije farin ciki ya had’ata da marar adadin alkhairi. Ba laifi Inna ta d’an sake dan sai da suka gama lissafin komai har aka kusa shiga sallah, suka shirya akan gobe zata je ta siyo komai na kayan d’aki tukunna ya mik’e ya nufi k’ofa yana mai ci gaba da saka musu albarka, sosai ya ji kaso hamsin na damuwar da yake a ciki ya yaye da ya samu Inna ta kulashi kuma ta bashi goyon baya. Ta so ta yi masa maganar k’in d’aukar wayarta da replying message d’inta da yayi kuma mai ya sa ya turo mata Asabe amma kawai sai ta basar dan kwana biyun nan komai ya sure mata a ka ga rashe-rashen da aka yi sun sake sanyayata….. D’azu da Mallan ya zo shiga d’akin Inna bayan ya shiga sai ya mayar da k’ofar ya rufe, wannan dalili ya sanya har ya taso ya iso bakin k’ofar ya sa hannu ya bud’e sam Asabe da Kaka basu san ya k’araso ba. A mugun zabure suka d’an matsa da suka ga an bud’e k’ofar sai kuma suka d’ago a tare wanda hakan ya janyo suka k’ume k’ummm!!! A gigice Kaka take sosa wajen tana kallonsa yayinda Asabe ta kawar da kanta gefe ta shiga kame-kame. Yatsine fuska ya yi cike da kalar tausayi irin mai yasa kike haka d’innen yana daff da yin magana cike da borin kunya ta ce “dan ubanka to ba lab’e muka yi ba!” Ya riga ya makara sosai dan gashi ma ya ji har wani ya fara kiran sallah dan haka ya wuce da sauri yana mai cewa “ni ban ce komai ba Kaka, bari in tafi masallaci na makara. Yana fita Dije ta fashe da wani irin kuka, sosai Inna take jin tausayinta kwana biyun nan dan haka ta janyota jikinta ta rungume ta shiga lallashinta..wanda sai da ta yi da gaske tukunna aka samu ta yi shiru. Wai yau ita Dije ce zata auri Yusufa mutumin da ko muryarsa ba ta son ji! Ai kuwa d’an halak d’in nata a take kiran wayarsa ya shigo wayar Inna dan ita bata da waya. D’auka Inna ta yi suka gaisa daga nan ya fara kame-kame, murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi kawai ta mik’awa Dije wayar ta mik’e ta fita dan ta je ta yo alwallah, ai kuwa ko gama fita ba ta yi ba Dijen ta kashe wayar kamar yadda ta yi jiya da shekaran jiya, Allah ya sota Innar ba ta ganta ba ta k’arasa fita daga cikin d’akin abunta. Bayan fitar Inna Yusufa ya kira ya fi sau goma amma ta k’i d’agawa kuma ta goge misscalls d’in k’arshema kashe wayar ta yi gaba d’aya da Innar ta dawo ta ce mata chaji ne babu. Bayan ta je ta yi alwallah ta dawo, a hankali ta koma ta kwanta ta lumshe idanunta a take lissafin Ma’ah ya fad’o mata….”Mugu kawai!” Ta fad’i hakan a ranta tana shafa hannunta dai-dai inda ya tab’a rik’ewa kwanaki wanda sai da wajen ya yi kwana uku ciff yana yi mata zafi-zafi!!… “Haka kurum na aure shi ya kakkarya ni! Mtswwww ta Yaya ma zan auri wannan tshohon, kuma d’an daba Allah ya Isa ma ni da ya ce yana so na, marar kunya ko a gidan wa aka ce masa mutum yana zuwa neman aure da kansa oho masa!!!!” Ta yi maganar duk ita kad’ai a cikin ranta. A hankali kwakwalwarta ta shiga zoomo mata ranar nan ita da shi a asibiti! “Ba zan tab’a cutar da ke ba Khadijah!!” Maganarsa ta dawo mata tarr kamar yanzun yake fad’a! Da k’arfi ta runtse idanunta sakamokon yadda ta ji ilahirin jikinta ya amsa. A hankali ta shiga sauk’e ajiyar zuciya sai kuma ta yi tsaki ta ce “cutarwa kuma ta nawa!!mugu kawai, har da had’in guiwarka ne ya sanya za a yi min aure” Daga haka ta runtse idanunta ta shiga neman bacci afujajan tana mai sake danna tsana da kyamar Ma’ah a cikin zuciyarta. Tausayin Mama ne ya fad’o mata dan ko d’azu sai ta ji ana fad’ar halin da take ciki, a hankali ta ce “Allah ya baki lafiya, Albasa ba ta yi halin ruwa ba.” Dan Mama tana da kirki kuma tana sonta, tun bata kai haka ba in dai suka had’u ta gaisheta sai ta bata alawa ko kud’i, tun ba ta karb’a har ta zo ta fara karb’a. Matar tana da kyauta ba ita kad’ai ba hatta Yaran layin haka nan duk take yi musu alkhairi. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 16. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. **************** A rikice sannan hankali a masifar tashe Gimbiya Sumayya ta shiga sashen Mahaifiyarta gudu-gudu sauri-sauri. A babban parlournta inda ta saba zama ta amshi gaisuwar kowa ta tadda ita… Yadda take tafiya kamar zata kifa jikinta yana wani irin masifar karkarwa ne ya sanya Mahaifiyar tata ta mik’e tsaye tun kafin ta k’araso ta ce “Gimbiya Sumayya kanki akwai motsi ne??? Kalli yadda kike tafiya kamar baki san matsayinki ba?”. A take duk bayin da suka rakota waenda suka sha gudu garin binta suka zube k’asa suka sunkuyar da kawunansu k’as, haka suma ragowar bayin da suka tadda a wajen (duk suka sussunkuyar da kawunansu k’asa)… Karkarwa take yi jikinta yana kyarma har yanzu ta gagara furta komai. Da kyar ta iya cewa “Gimbiya Mariya..” Tana magana tana nuna waje da hannunta ba tare da ta kalli wajen ba, ta d’aura da cewa “ta tara mutane a babban filin rabo wai za’a jefe Gimbiya Sakina!”. Wani irin mahaukacin bugawa k’irjin Gimbiya Mai Babban d’aki ya yi wanda hakan har sai da ya sanya ta durk’usa ta kai k’asa tsabar yadda abun ya daketa. A take duk bayin suka sake yin k’asa da kawunansu yayinda hadimanta guda biyu makusantanta suka k’arasa da sauri suka d’agota. D’ayar ta fara k’ak’arin zaunar da ita yayinda d’ayar ta shiga yi mata fifita tare da fad’in maganganu masu sanyaya ruhi. Mik’ewa ta yi kawai ta wucesu ta zo ta wuce Sumayyar hankalinta a masifar tashe….’Tabbas yau kam sai dai a tsireta amma sai ta nunawa Mariya matsayinta! Yo hauka ake yi? Sakina fa y’ar Sarki ce jikar Sarki gaba da baya da zata ce zata jefeta tana shaye-shaye ne? Ta yaya ma zata zuba ido ta bari a jefe mata y’arta kamar wata baiwa? Wanne irin sharri ne haka aka yi mata da har zai sanya wachchar mahaukaciyar ta yi yunk’urin jefeta?’…..Tana waennan lissafe-lissafen ta zo ta wuce Sumayya fuuu kamar zata tashi sama. A take bayinta suka mara mata baya ita kuma Sumayya wadda ta sulale a wajen nata suka durk’usa suna kururuwa gashi basu da ikon tab’ata. A chaan babban filin rabo… Tun kafin ta k’arasa ta hango Gimbiya Sakina d’aure jikin wata k’atuwar bishiya jikinta babu komai sai doguwar shimi har k’asa fara tas dan hatta d’ankwali babu a kanta sannan duk wani abun ado kama daga y’an kunne zobuna suma duk babu gasunan ajjiye gefe guda tare da kayanta yashe a gefe alamun yanzun ne aka cire mata. Dishi-dishi Gimbiya Mai Babban d’aki ta fara gani tsabar mad’aukakin tashin hankali da b’acin ran da ya sake rufe ta! ‘Wai yanzu y’arta ce d’aure jikin wannan k’ask’antacciyyar bishiyar a gaban bayi haka tsaye chak a kan k’afafuwansu? Sannan on top of everything wai shirin jefeta ma ake yi!?’ Tana cikin wannan tunanin ta k’arasa inda Gimbiya Mariya take tsaye tana zuwa bata yi wata-wata ba ta sa hannu ta juyo da ita ta d’auketa da wani irin mahaukacin Marin da ya sanya kowa durk’usawa a wajen kawunansu a k’asa suka shiga cewa “tuba take yi! Uwar sarki matar sarki a yi mata aikin gafara hannunta ne ya sub’uce!”. A tsawace ta juyo ta ce “ku rufewa mutane Baki!” Sai kuma ta juya ta kalleta ta ce “Garr nake ganinta kuma ban tuba ba dan ubanki!” Rikicewa wajen ya yi yayinda wasu a cikin mutanen wajen suka fashe da kukan an zagi uwar sarki. Cikin b’acin rai ta ce “wasa ya wuce wasa amma ban da tsole idon uwar Miji da tab’arya! Dan ni duk haukan nan da kike yi tun daga ranar da aka nad’a Yareema a matsayin Yareema har ya kawo Sarki wallahi a matsayin wasan Yara na d’aukesa, dak’ik’iya wadda bata san inda yake yi mata ciwo ba!” A hankali wani Bafade ya k’araso wajen shi da waensu sojoji guda biyu ya ce “Gimbiya Mai Babban d’aki ki gafarceni, amma maganganunki sun yi tsauri ga Gimbiya Uw….” Tass!! Ta d’aukesa da Mari ta ce “ku kuke ganinta a matsayin Gimbiya Uwar Sarki ni har gobe a matsayin k’ask’antacciya y’ar talakawa nake kallonta!”. D’iff! Haka wajen ya yi ba ka jin komai sai sheshshek’ar kuka, sai kuma suka ci gaba da cewa “Allah ya huci zuciyar Gimbiya Uwar kowa” Wata nannuyar ajiyar zuciya Gimbiya Mariya ta sauk’e, tabbas sai ta gasa mata aya a tafin hannun da ya mareta, amma ba yanzu ba zata samu lokacin ta ne. Dan haka kawai sai ta juya ta kalli jama’ar da ta tara a wajen ta ce “Bismillah, za ku iya fara aikin lada” Ta yi maganar ko kallon gimbiya Mai Babban d’aki bata yi ba. Dai-dai nan Nuraddeen ya k’araso wajen yana wani bubbud’awa… Nufar bishiyar Gimbiya Uwar Marayu ta yi yunk’urin yi amma Sojojin nan suka hanata shallake jan layin dake zagaye da bishiyar ballanta ta k’arasa ga Sakina wadda duk dauriyarta zuwa yanzu ta fara kuka. Cike da Isa da izza Nuradden ya k’arasa inda take ya ce “kin kuwa san me ta yi? Ko dai bakinku d’aya? Ki rufawa kan ki asiri ki bar nan tun kafin a had’a da ke!” Cikin fushi ta juyo za ta d’aukesa da Mari shima amma sai ya yi saurin rik’e hannuwan nata cikin b’acin rai ya ce “kar ki kuskura” tukunna ya yarfe hannun nata da k’arfi dan har sai da ta tafi ta yi tangal-tangal kamar za ta fad’i kafin ta d’ago

Chapter 13 of 23