Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels  🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *BAƘAR MASAURATA YASHA BAMBAN DA SAURAN LABARAN, LABARI NE IRIN WANDA BAKU TAƁA CIKIN KARO DA KALAR SABA.* *DUK ABUN DA ZAKU GANI ACIKIN LABARIN NAN ƘIR-ƘIRARRE NE, KAMA DAGA SUNAYEN GARURUWA HAR IZUWA NA MASARAUTU, KAMAR YACCE DUKA LABARIN YA KASAN CE ƘIR-ƘIRARRE.* *BAN YARDA WANI KO WATA BA SU JUYAMUN LABARI TA KOWACE SIGA BA TARE DA IZININA BA.* *PAGE 01* _SHIMFIƊA_ *ƘASAR HAUSA* Ƙasa ce mai tsantsar girma da faɗi, ƙasace wacce Allah ya azurta ta da mayawaitan al'umma, maban-ban ta ƙabilu da mazaunai daban daban, ƙasa ce mai ɗauke da jahohi 30 cif acikin ta, yayin da jahohin suka kasan ce ayanku na daban daban, ƙasa ce wacce ta kasan ce ƙasar hausawa, duk da dai basu kaɗai bane suka kasan ce acikin ta, sai dai kuma mafi yawan jahohin da suke acikin ƙasar yawan cin su duka na hausawa da fulani ne, wato dai sune masu ƙasar. *MASARAUTAR WASAI* Ɗaya daga cikin manyan masarautun da suke aƙarƙashin ƙasar hausa kenan. JAHAR WASAI Jahace mai matuƙar girma da faɗi, jahace wacce take ɗaya daga cikin manya-manyan jahohin da suke a ƙar-ƙashin ƙasar hausa, jaha ce ta musulunci da musulmai, jaha ce wacce take da manyan ƴan kasuwa tare da manyan kasuwani acikin ta, domin ko itace ta kasan ce cibiyar kasuwan ci ta ƙasar hausa. Yayin da ita kuma masauratar wasai ta kasan ce ɗaya daga cikin manya manyan masarautun da suke acikin ƙasar hausa, sannan kuma ta kasan ce masarauta ɗaya acikin jahar wasai, wato dai itace mamallakiyar jahar gaba ɗaya. Masarautar wasai masarauta ce mai tsantsar girma da ƙarfin mulki, masarauta ce wacce ta kafa tarihi acikin ƙasar hausa, masaurata ce mai ƙarfin mulki wacce ake ji da ita aduk faɗin ƙasar hausa harma da ƙasashen da suke maƙota ka da ƙasar. *** *JAHAR KAGUL* Itama dai jahar kagul ta kasan ce dlɗaya daga cikin manyan jahohi ne da suke aƙasar hausa, sai dai ita kuma jahar kagul tana ayankin yammacin ƙasar hausa ne, saɓanin jarah wasai da take a arewacin ƙasar hausa. Jahar kagul ta kasan ce jahar fulani ce ita, wato dai kusan duk mazaunan cikin ta sun kasan ce fulani makiyaya ne, sai dai ita kuma ta kasan ce ɗaya daga cikin jahohin da addinin musulunci baiyi zurfi acikin ta ba, domin kuwa mafiya yawan mazaunan cikin ƙasar ko karatun sallah basu iya ba bare aje ga sanin tauhidi da hadisai, kai ataƙaice ma dai sallahr duka bata dame su ba, domin ko hatta da gidan sarautar dake cikin ƙasar shima babu addinin acikin sa, dan kuwa babu abun da suka sanya agaba sai tsafi da harkar kula da dabbobin su, kasan cewar itace babbar jahar kiwo aƙasar hausa, domin kuwa kusan duk wasu shanu da ake kadawa acikin jahohi talatin da suke aƙasar hausa suna futowa ne daga jahar kagul. Hakan yasa ɗaukacin mutanen dake cikin jahar suka maida hankulan su akan kiwo da asirce asricen da zasu bawa dabbobin su kariya fiye da komai agidan duniya, ciki kuwa har da addinin su, wato dai in taƙaice muku zance jahar kagul itace cibiyar kiwo ta ƙasar hausa. *MASARAUTAR FULƊE* Masarauta ɗaya ƙwal dake acikin jahar kagul, wato dai itace mammallakiyar jahar gaba ɗaya. Masauratar fulɗe tana ɗaya daga cikin masarautu masu tarin dukiya da kafaffen tarihi acikin ƙasar hausa, masarauta ce ta fulani wacce ta kafa tarihi ta fannin harkar kiwo, domin kuwa duk wasu makiyaya da suke acikin ƙasar hausa kusan suna aƙar-ƙashin mulkin masarautar fulɗe ne. Masaurata ce wacce ta haɗa wasu irin mutane acikin ta, waƴan da ko kaɗan babu Allah azuciyar su, duk da dai suna iƙirarin su musulmai ne ako da yaushe, sai dai gaba ɗaya jama'ar cikin masarautar babu wanda zaka tambaye sa wani abu akan addini ya iya baka amsa, ciki kuwa har da sarki mai ci, bar su dai su ta fannin tsaface tsaface anan suka fi ƙarfi, domin kuwa hatta da ɗan ƙaramin yaro dake cikin masarautar zaka same sa ɗauke da tsafin sa ne, wato ya iya tsafuka kala kala ankoya masa an kuma basa tun yana ƙarami, ga su kuma da wata irin baƙar zuciya wacce bata tanƙwaru wa, wato dai idan suka ce hakan za suyi babu wanda ya isa ya canza su daga hakan, haka kuma idan suka ce baza suyi ba to fa babu wanda ya isa ya sasu suyi, sannan kuma basa yafiya ga mutumin da ya zalince su ko kuma yake shirin cutar da su, ko yake farautar wani abu nasu muddin suka gano sa. Hakan yasan ya babu wasu da suke iya shigo musu cikin ƙasa suyi musu satar dabbobi, duk da dai ansha kawo hara-hare daga jahohi daban daban, sai dai ako da yaushe idan ɓarayin sun shiryo sunzo babu wata riba da suke samu sai dai ma akarɓi ransu anan tsabar ƙarfin asirin su. Gaba ɗaya mutanen cikin jahar kusan sun kasan ce fararen fata ne, masu matukar kyawun hallitar jiki da fuska, tare da yalwataccen gashi, kama daga mazan su har matan su, hakan yasa masu kuɗin ƙasar hausa suke yawan zuwa jahar ta kagul neman aure cikin ta, sai dai kuma koda sun je ɗin duk da yawan dukiyar da suke da ita ba afiya basu ba, kasan cewar su mutane waƴan da basu fiye yadda da wani bare ba musamman ma bahaushen mutum, balle kuma har su sake da shi. **** *ƘASAR MALIN* YAN KIN JAHAR KARFUZ. Jahar karfuz ta kasance jaha mai matuƙar girma da faɗi, jahace wacce take aƙar-ƙashin ƙasar malin, jahace wacce Allah yayi ta da yawan manya-manyan ruwaye, tare da dogayen bishiyu da duwarwatsu, domin kuwa duk inda zaka bulla acikin jahar kusan zaka yanka ne ta tsakan-kanin dogayen korayen itatuwa tare da manya manyan ruwaye masu kwaranya. Ba afiya yi musu rana ba duka ajahar tasu, koma nace kusan aƙasar tasu ta malin baki daya, sai dai kuma aduk lokacin da aka tashi yi musu to bata zuwar musu da sauƙi, dan ko hatta futa ba kowa ke iyayi ba idan ba dare ne yayi ba a'irin yana yin. Ita dai jahar karfuz ta kasan ce jahar da babu musulunci acikin ta ko kaɗan, asalima gaba ɗaya basu san mene ne musuluncin ba, mutane ne su waƴan da suke bautar gumaka, huta, ruwa da rana, wato dai gaba ɗayan su basu san Allah ba. *BAƘAR MASARAUTA* Masarauta ɗaya ƙwal dake cikin jahar karfuz, masarautar da basu san Allah ba bare suyi aiki da faɗar sa, masarautar da basu mai da kisan rai abakin komai ba, masarautar da rashin imani da yahudanci ya tattaru ya ƙare acikin ta, masarautar da suka mai da zubar da jinin mutum tamkar zubar da jinin rago. Masarautar da take da matuƙar girma tare da ƙarfin mulki da iko, tsantsar zalunci da tarin yahudanci, dan ko ataƙaice su ko sallah ma basu san ta ba balle su san falalar ta har suyi ta. Wannan kenan. Tafe take cikin takun ta na tsantsar izza, isa tare da ji da kai. Kyakkyawa ce ajin farko, duk da dai bata kasance farar fata ba, sai dai kuma baƙin ta shima bai zamto na muni ba, irin baƙin nan ne wanda hausawa kewa laƙabi da wankan tarwatsa. Tana da tsayi tare da faɗi da tudun jiki dai dai misali irin wanda kowa ke so. Tana da manya manyan idanuwa farare masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, yayin da bakin ta kuma ya kasance ɗan tsukut da shi mai ɗauke da jajayen laɓɓa akan sa, sai dogon hancin ta siriri da yake tsaye cak akan fuskar ta yarce kasan ɗora sa tayi. Kai ataƙaice dai gaba ɗayan ta bata da makusa tako ina, dan ko hatta da gashin dake kan idanuwan ta idan ba ƙura mata ido kayi ba sai ka rantse kace ɗora sa tayi, sabo da yarce suke da matuƙar tsayi. GIMBIYA TASMIR kennan, ƴa mace ƙwalli ɗaya ƙwal ga sarki barbaru shugaban baƙar masarauta, gimbiya mai matuƙar kwarjini, wacce sautin takun ta kawai ke girgiza zuciyoyin bayi, gimbiyar da da zarar ta biyo hanya to babu wanda ya isa ya bayyana awurin idan aka cire ƴan rakiyar ta muddin bata kai ga wucewa ba tsabar ƙarfin ikon ta, gimbiyar da sautn muryar ta ke hautsina ƙwaƙwalen bayi, duk da dai ba fiye yin maganar tayi bama, dan azahirin gaskiya magana ma matuƙar wahalar da ita take yi, domin kuwa sai akawana atashi ba tare da ta furta koda kalma ɗaya ba ga kowa. Sanye take da wata doguwar riga baƙa mai matuƙar tsayi da faɗi, tayar ce har take sharar ƙasar duk wurin da ta taka, yayin wasu matasan ƴammata guda biyu suke riƙe da wasu yankuna na daga jikin rigar sabo da ta rage sharar ƙasa. Ɗaure suke da baƙin ƙyalle aƙugun su, wanda duka tsayin sa ya tsaya a'iyakar gwiwoyin su, sai wasu ƴan ɓingilallun fararen riguna na yadi masu matuƙar faɗi babu tsayi sanye ajikin su, yayin da jikin rigunan kuma daga gaban su suka kasan ce ɗauke da zanen tambarin masarautar tasu, wanda aka ɗinka sa da baƙin zare adai dai ƙirjin su, sai fuskokin su suma zane suke da tambarin masarautar da sukayi ado da kwalli ta ko ina. Yayin da gefe da gefen su harma da bayan su kuma wasu irin danƙara- danƙaran maza ke biye da su, hannuwan su ɗauke da zura zuran bulalai tare da takubbai soke aƙugunan su, wanda hakan ke nuni da sune dakarun ta, babu wanda ke sanye da riga ajikin sa, sai baƙin ƙyalle mai haɗe da gajeran wando iyakar gwiwa dake ɗaure aƙugun su, gaba ɗaya jikin su zane yake da tambarin masarautar tasu ta ko ina da akayi sa da baƙin fenti tun daga fuska har ƙafa. Kallo ɗaya zaka musu kayi matuƙar razana idan baka saba ganin su ba, sabo da yarce ƙwayoyin idanuwan su suka kasan ce jajaye, gasu su kuma baƙaƙe huluk dasu, duk wanda ya gansu ba sai anfaɗa masa ba zai san babu imani tattare da su, kai ataƙaice ma basu san saba ko kaɗan. Sosai wurin yayi tsit yarce kasan ba ataɓa hallitar mutum ba, kamar yacce kowane wuri yake kasan cewa aduk lokacin da ta kasan ce ashi, babu sautin da ake ji yana tashi sai na takun ta. Kallo ɗaya zaka mata ka fahimci ranta amatuƙar ɓace yake, sabo da yarce fuskar ta me ɗauke da zannen tambarin nasarautar su agaban goshin ta take amugun ɗaure, ko kaɗan babu alamun annuri tattare da ita, bare har asa ran samun rahama daga gare ta. Sun yi tafiya mai ɗan tsayi daga cikin gidan sarautar, tukun suka ɓulla cikin wani ƙaton wuri mai ɗauke da dogayen bishiyu da duwar-warsu zageye dashi. Kai tsaye ta doshi ƙofar dake kallo su idanuwan ta ƙur akan ta, yayin da suma dakarun nata ke biye da ita har suka ƙarasa bakin jibgegiyar ƙofar dake da matuƙar girma da kauri. Tsaye tayi cak daga gaban ƙofar ita batayi gaba ba sannan kuma ita batai baya ba, yayin da su kuma ƴammatan nan da suke riƙe da rigar ta sukayi hanzarin sakin rigar, suna masu zube gwiwoyin su tare da durƙusar da kansu ƙasa. Hannun daman ta tamiƙar tana mai buɗe tafin sa ba tare da tace ƙala ba. Dasauri ɗaya daga cikin jibga-jibgan mutanen nan da yake daga bayan ta ya juya baya, tukun ya fara tafiya da baya da baya yana mai yin inda take har sai da ya ƙarasa kusa da ita, kana ya zube gwiwoyin sa aƙasa tare da durƙusar da kansa ƙasa, sannan ya zaro wata zureriyar jar takobi ajikin sa yana mai miƙa mata ita, har lokacin kuma bai bari idanuwan sa sun kalli koda fuskar ta ba balle su shiga cikin nata. Ba tare da ta ɗago ta kalli inda yake ba ta ƙara ware tafin hannun ta, tukun shi kuma wannan ba dakaren ya ɗora mata takobin akan tafin hannun nata, kana tamai da yatsun ta tana mai dunƙule takobin acikin su. Dasauri badakaran ya ƙara juya mata baya, tukun ya miƙe yana mai cigaba da tafiya da baya da baya har ya koma inda yake, sannan ya ƙara tsayawa cak ya koma tamkar bishiyar da aka dasa. Rumtse idanuwan ta tayi da ƙarfi, tukun daga bisani ta buɗe su akan ƙofar dake kallon ta, kana ta ɗaga zureriyar jar takobin dake dunƙule atafin hannun ta tana mai nuna ƙofar da ita, tukun ta buɗe bakin ta cikin kakkausar muryar ta mai matuƙar sauti tana mai faɗin. "Gargabiluuuu!" Take jikin bayin nan mata ya ɗauki rawa yarce kasan mazari, gumi na yanko musu sabo da yarce sautin muryar ta ya daki zuciyar su ba tare da sunyi zato ba, yayin da su kuma jibga jibgan dakarun nan maza suka sake ƙamewa cak a'inda suke yarce kasan icci na. Ahankali -ahankali murfin ƙofar ya fara buɗewa har ya buɗe duka akan idanuwan ta, tukun daga bisani ta janye ƙwayar idanuwan nata daga kan ƙofar tana mai mai dasu kan tafin hannun ta da yake ɗauke da zureriyar jar takobin nan, sannan ta sake miƙar da hannun gefe ba tare da tace komai ba. Dasauri wannan badakaran da yakawo mata takobin ya sake tawowa da baya da baya har ya ƙaraso inda take, kana ya zube guiwoyin sa aƙasa, sannan ya miƙa hannu ya ɗauki takobin ba tare da ya kalli fuskar ta ba yanzu ma. Sake miƙewa yayi ya koma da baya da bayan sa kamar yacce yazo. Sai da ta ɗauki kimanin daƙiƙa goma atsaye awurin tana kallon ɗakin da yake kallon ta wanda yake baƙiƙƙirin da duhu, ba ahangen komai na cikin sa, tukun daga bisani ta fara ɗaga ƙafafuwan ta masu sanye da sarƙoƙin gwal ajiki waƴan da suke futar da sauti aduk lokacin da take tafiya, tana mai dosar ɗakin gadan -gadan. Cak ta tsaya adai dai bakin ƙofar ɗakin ba tare da ta shiga ciki ba. Dunƙule tafin hannun ta tayi tana mai yin wasu surutai, tukun daga bisani ta buɗe sa tana mai watsa wasu abubuwa da suka bayyana akan sa zuwa cikin ɗakin. Take kuwa haske ya bayyana acikin sa, tukun ta sake ɗaga ƙafafuwan ta tana mai tura kanta cikin sa. Ɗan ƙaramin ɗaki ne wanda idan da mutane zasu zauna aciki duka baifi yaci shimfiɗun mutum biyu ba zai cike, sai wasu kaskwayen huta (randina) da suke ajiye akowace kusurwa ta ɗakin huta na tashi daga cikin su, wacce tayi matuƙar zafafa ɗakin tako ina. Tsaye tai daga bakin ƙofa tana mai kallon yarce yake tsaye awurin, gaba ɗayan sa ya jiƙe sharkaf har yana ɗiga da gumi, kai idan baka sani ba zaka rantse kace daga cikin ruwa aka zarosa tsabar yacce ruwan ke sauka akowacce kafa ta jikin sa. Matashin saurayi ne mai kimanin shekaru talatin aduniya, ɗaure yake jikin wasu ƙarafa masu matuƙar girma, yayin da jikin sa ya kasan ce babu ko riga akai, sai ɗan ƙaramin farin yadi dake ɗaure aƙugun sa kawai. BEER Ahankali ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar inda yake idanuwan ta ƙur akan sa. Tun lokacin da ta ƙaraso bakin wurin yaji alamun zuwan nata ajikin sa kamar yacce yake ji aduk lokacin da sukai kusanci da ita, sai dai kuma ayarce kansa ke ɗage asama idanuwan sa na kallon rufin dake saman ɗakin kai bazaka taɓa cewa yasan da wanzuwar mutum awurin ba, domin kuwa motsi baiyi ba daga yarce yake tunda ta shigo balle har ya ɗago kai ya kalle ta. Cigaba da takowa tayi har ta ƙaraso kusa da inda yake, tukun taja ta tsaya tana mai kafe sa da manya manyan idanuwan ta ba tare da tace komai ba, yayin da har lokacin shima kansa ke ɗage asama ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba. Sai da suka ɗauki kimanin minti goma ahaka, tukun ta fara ɗaga laɓɓan ta cikin zazzaƙar muryar ta mai matuƙar kaushi tana mai faɗin. "Ina amsar tambaya ta?" Tukun ta ƙara mai da baki ta tsuke tana kallon sa. Sai da yay kamar bazai yi magana ba, domin ko ita kanta har ta fara fudda tsamannin zai bata amsa, tukun daga bisani ya saukar da kansa daga kallon saman da yake yana mai juyo da manya manyan idanuwan sa zuwa kan fuskar ta. Lumshe idanuwan sa yayi bayan ya kalle ta ba tare da yace komai ba, tukun daga bisani ya sake wara su yana mai watsa ƙwayoyin su acikin tsakiyar nata, kana ya gumtse baki yayi shiru ba tare da yace ƙala ba. Sosai ranta ya ƙara bala'in ɓaci ta dalilin banzan da ya mata, da kuma yarce ya tsaya ya kafe ta da idanuwa yarce kasan sa'ar sa. Cikin zafin rai da tafasar zuciya ta ƙara buɗe baki tana mai faɗin. "Nace maka ina amsa ta ƙasƙantacce!" Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai kallon cikin idanuwan sa. Murmushi gafen baki ya saki yana mai ƙare kafeta da dara -daran idanuwan sa, tukun daga bisani ya ɗaga laɓɓan sa cikin kakkausar muryar sa shima yana mai furta cewar. "Ke ɗin yarin ce har yanzu, shiyasa har kika gaza samun amsar tambayar ki ke da kan ki, amma ba damuwa, shima girman lokaci ne da shi, kuma ina mai tabbatar miki idam naki lokacin girman yayi keda kan ki zaki samo amsar ki." Ya faɗa cikin kaushi yana mai ƙareshe maganar tasa da sakin murmushi, har kuma lokacin ƙwayar idanuwan sa suna cikin nata yana aika mata da wani irin kallo. Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwan ta jikin ta na tsantsar rawa, tsabar yarce maganar sa tayi matauƙar ƙona mata rai, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai sake watsa su acikin nasa. Lokaci ɗaya duka idanuwan nata suka rikiɗe daga launin fari zuwa na ja, jan ma irin jajahur ɗin nan tsabar ɓacin rai, wani irin huci take futarwa daga cikin bakin ta yarce kasan wacce tayi tseren gudu, yayin da jijiyoyin kanta kuma suka futo sukai ruɗu-ruɗu agaban goshin ta duk ta sanadin furucin sa. Ta fannin sa kuwa har lokacin bai ɗauke idanuwan sa daga kan fuskar ta ba, kamar yacce bai dena jifan ta da kyakkyawan murmushin sa ba da yake yi, da alama dai shi ko kaɗan yana yin da ya ganta aciki bai razana saba, duk da dai kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar da ba ƙaramun jigatuwa yayi ba, koma ace yana kan jigatuwa sabo da yarce gumi ke tsattsafowa daga cikin gashin kansa yana dira akan kafaɗun sa da fuskar sa. "Tabbas azaba mai raɗaɗi zata hau kanka fiye da wacce kake ciki muddin ka bari daƙiƙa huɗu suka shige agaba ba tare da na jiyo abun da nake san ji daga gare ka b...." "Azaba? Shin dama har akwai wata azaba da zata zamto sabuwa gare ni ne acikin *BAƘAR MASARAUTA*? Shin koko kin manta ita kanta azabar acikin ta na taso na samu kaina ne?" Ya katse mata maganar da take kanyi da faɗin haka yana mai sakin numfarfashin wahala ba tare da ya bari yaji ƙarshen abun da zata faɗa ba, har lokacin kuma idanuwan sa suna acikin nata kamar yacce ita ɗin ma take kallon sa tana sakin huci da nata jajayen idanun. Harshe yasa ya kamo leɓen sa na ƙasa da shi, tukun ya sanya haƙwaran sa na sama dana ƙasa yana mai cige leɓen tare da sakin murmushi, har kuma lokacin bai bar kallon ta ba. Wani irin ɓacin rai gimbiya tasmir taji ya ƙara cakar zuciyar ta, lokaci ɗaya jikin ta ya fara rawa idanun ta na sake rikiɗewa suna yin ja. Cikin zafin nama ta ɗago tafin hannun ta na dama tana mai dunƙule ƴan yatsun ta cikin sa, sannan ta ɗaga ƙafar ta ta hagu tayi ball da kaskon hutar dake ci agaban ta ya tuntsire ƙasa ya fashe, kana ta rumtse idanuwan ta da ƙarfi tana mai buɗe baki cikin tsantsar sauti tace. "Rai Rai buuuu Hooo Reee!" Tukun ta wara tafin hannun nata bayan ta buɗe jajayen idanuwan ta tana mai watsa wasu abubuwa da suka bayyana acikin sa akan fuskar Beer. Wani irin baƙin hayaƙi ne ya tashi awurin yana mai lulluɓe masa duka jiki. Wata irin gigitattar ƙara ya buga wacce tasanya gaba ɗaya komai dake wurin amsawa. Juyawa tayi cikin tsantsar ɓacin rai tana mai dosar hanyar waje, banda sautin sarƙoƙin gwal ɗin dake sanye aƙafafuwan ta babu abun da akeji yana tashi awaurin. Tana fucewa waje gaba ɗaya dakarun nan dasu da ƴammatan bayin suka zube wanwar aƙasa suna masu yin ribda ciki. Ba tare da ta ɗaga kai ta kalli ko mutum ɗaya daga cikin su ba ta cigaba da tafiya har ta ƙarasa wurin da ta tsaya kafun ta shiga ɗakin nan. Sai da ta ɗauki tsayin minti biyar da tsayuwa, tukun dukan su suka mimmiƙe suna masu durƙusar da kansu ƙasa. Hannun daman ta ta miƙar gefe ba tare da tace tak ba. Kamar yacce ya faru ɗazu haka yanzu ma wannan badakaran ya tawo da baya baya har ya ƙarso inda take. Tukun ya zube guiwoyin sa aƙasa, sannan ya zaro takobin nan daga cikin jikin sa yana mai ɗora mata ita akan tafin hannun ta. Dunƙule ta

Chapter 1 of 76