Share this page
sake sa suna masu barwa mutum d'aya shi. Shi kuwa wanda aka barwan da hannu d'aya yayi wani irin d'aga Bir sama, tukun ya fara d'aga k'afafuwan sa yana mai nufar bakin ruwan nan da shi, yayin da suma sauran y'an uwan nasa suka rufa masa baya, gaba d'ayan su suma ransu a b'ace da ganin kalar rashin kunyar da yayiwa uwar d'akin nasu. *K'ASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.* Rayuwa taja, a sannu-sannu kwanaki suka dinga zuwa suna wucewa, kana su koma satika, sannan satika suka koma watanni, yayin da watanni kuma suka dinga ninkuwa ahaka har suka zamto shekaru. Abubuwa da yawa sun faru acikin shekarun da suka gaba ta, cikin su kuwa har da haihuwar y'a macen da Gimbiya kab'el ta sake yi, yarinya taci sunan mahaifiyar Lamid'o Gimbiya Unau, amma suna kiran ta da Innahuro, ma'ana uwar masu gida a hausance kenan. Shekaru kusan goma shahud'u ke a tsakanin Gimbiya Haddiya da Inna huro, amma idan mutum yaga yadda Innahuro da take da shekaru biyar zuwa shida yanzu aduniya take yiwa Gimbiya Haddiyal sai ya d'auka baifi tsirayyar shekara d'aya ke tsakanin su ba, domin kuwa ko d'an kunne aka siyawa Haddiya to itama Innahuro sai tace asiya mata shi, wato ta mayar da ita tamkar kishiyar ta dai. Yayin da ita kuma Haddiyal take matuk'ar son k'anwar tata tamkar yadda sauran y'an gidan suke son ta, duk da dai ita Innahuro a kwaita da shegen surutu, ba kamar haddiyal ba da surutu bai dameta ba kwata-kwata. A yanzu haka Gimbiya Haddiyal tana da shekaru Ashirin ne a duniya. Sosai tayi girma ta k'ara yin kyau tamkar ita tayi kanta, domin kuwa babu ta inda Allah ya rage ta aduka hallitar jikin nata. Tini ta kammalla karatun secondry d'in ta a cikin wannan makarantar data farata tun farko, yayin da akai-akai da Lamid'o ya kaita k'asar waje ta cigaba da karatun ta amma gaba d'aya yace bai san da wannan batun ba, wanda tayi na bayan ma shima ya barta ne kawai dan an masa dole, amma bawai dan ransa yaso ba, hakan ne yasa yanzu take zaune a gida babu wurin da take zuwa, sai wurin tsuntsayen ta da tini suka dade da zamtowa abokan rayuwar ta, domin kuwa tsanin son da take yi musu ne ma da Lamid'o ya gani yasan ya ya nad'ata a matsayin sarauniyar su acikin duka masarautar, kana ya bata jagorancin kula da duk shanun da ake d'ibar madara a jikin su acikin masarautar, ta yadda muddin ana buk'atar madara sai an biyo ta wurin ta kafun asame ta. A b'angaren mafarkin ta da tayi na busar sarewa kuwa, haka kullum ta cigaba da yin sa a wancan lokacin, sai dai kuma har ta d'auki tsayin watanni shida tana mafarkin bata tab'a ganin mai busar ba, sai dai sautin ta kawai da take ji, kafin daga baya kuma mutumin dake busar ya bayyana acikin mafarkin nata, sai dai kuma ako da yaushe bata ganin fuskar sa, kawai dai tana ganin sa ne ya juya mata bayan jikin wani k'aton dutse da yake tsayuwa, sanye da shiga irin ta Sarakai a jikin sa, haka zataje ta samu wuri daga bayan sa ta zauna tana mai kallon sa, busar na ratsa ko wane lungu da sak'o na ilahirin jikin ta. A haka har aka shafe sama da shekaru biyu tana wannan mafarkin aduk daran duniya. Kwatsam rana d'aya sai taga mutumin dake busar ya sauya kalar shigar dake sanye a jikin sa ko da yaushe, amai-makon ta gansa da shigar sarauta, sai ta gansa sanye da d'an guntun bakin wando'n da tsayin sa bai huce iyakar guiwar sa ba ajikin sa, sai wani d'an kyalle kuma da yake yafe ajikin sa amai-makon riga, kana kuma babu abun busar rik'e a hannun sa tamkar yadda ta saba ganin sa ako da yaushe yana yin busar. Hakan ne yasa ta fara d'aga k'afafuwan ta cikin sanyi tana mai nufar wurin da yake. Tsaye tayi cak a bayan sa a lokacin da ta matsa dab da shi, tukun daga bisani ta bud'e baki cikin zazzak'ar muryar ta tana mai fad'in. "Yau kimanin tsawon shekaru kenan kullum kana zuwar mun da shigar Sarakai jikin ka, kana sautin daddad'ar busar ka na ratsa gangar jiki da jijiyoyin jiki na, ta yadda har take kwanciya acikin b'argo na. Amma kuma yau sai na ganka da sabon tufa ba waccan ba, kana kuma babu abun busar dake sanyaya mun zuciya ta. Shin ko zan iya sanin abun da ya hanaka zuwar mun da sarewa ta a yau, bayan kuma ka riga da kasabar mun da jin daddad'an sautin ta a cikin kunnuwa na?" Ta k'arasa maganar cikin sanyi, tana mai gyara tsayuwar ta a wurin da take. Amaimakon taji sautin muryar sa yana bata amsar tambayar da tayi masa, sai kawai taga ya fara juyowa gare ta ahankali-ahankali, har ya juyo duka b'arin da take yana mai fuskantar ta tare da jifan ta da wani irin sassanyan murmushin sa, abun da tunda take da shi bai tab'a yi ba kenan, wato juyowa gare ta balle har taga kamannin sa sai yau. Hakan ne kuwa ya sanya ta tayi suma tsaye a wurin da take tana mai binsa sa da dara-daran idanuwanta, kamar yadda taga shima yana kallon ta da nasa idanuwan, tare da sakar mata murmushi. Kyakkywa ne ajin farko, danko atak'aice tana iya cewa tunda take aduniya bata tab'a ganin mai kyan sa ba. Sun d'auki tsayin mintina goma ahaka suna kallon-kallon ba tare da wani daga cikin su yayi magana ba, sai kawai murmushin da suke ai'kawa junan su da shi. Kana daga bisani kuma Gimbiya Haddiyal ta fara d'aga k'afafuwan ta daga wurin da take tana mai sake nufar sa cikin tsantsar farin ciki. Tana dab da zuwa gare sa ne kawai ta farka daga baccin da take. Tun daga wannan ranar kuma take mafarkin sa acikin yanayi daban-daban. Yayin da zuciyar ta kuma ta kamu da wata irin mahaukaciyar k'aunar sa, ta yadda har sai da ko wane mutum na cikin gidan nasu yasan da labarin sa, kana kuma ta fara k'ok'arin ganin ta gano wurin da yake zaune ta hanyar tsafin ta, amma gaba d'aya abun ya cutura. Hakan ne yasa tasan ya d'aya daga cikin bayin gidan nasu data aminta da shi sosai ya fara yi mata bincike akan mutumin mafarkin nata, domin kuwa tun da suke had'uwa da shi tun lokacin data fara zama budurwa har kawo yau bai tab'a furta mata wata kalma ba sai dai kawai murmushi, yayin da ita kuma take zama tayi masa zuba acikin mafarkin nata. A lokacin da labarin mutumin mafarkin Gimbiya Haddiyal ya isa kunnen Lamid'o sosai hankalin sa yayi matuk'ar tashi, domin kuwa duk atinanin sa Aljanu ne suka shafi d'iyar tasa, hakan ne yasa ya fara nemar mata magun-guna gadan-gadan, kana kuma ta ko wacce hanya, amma kuma abanza, domin ko amaimakon abu yayi sauk'i sai haukacewa da kullum Gimbiya Haddiyal take k'arayi akan mutumin cikin mafarkin nata, wanda tai masa lak'abi da Gid'ad'on ta, wato Masoyin ta a harshen hausa kenan. Yanzu haka tsaye take a gaban had'ad'd'iyar wardrobe d'in k'arfen da take manne ajikin bangon d'akin ta, tana mai zaro kayan baccin ta, kasancewar tini dare ya fara nisa, domin kuwa har k'arfe goma ta gota. Cikin sauri ta fara ware had'ad'd'iyar jar doguwa rigar baccin da take rik'e a hannun ta, kafin daga bisani kuma ta zurata a jikin ta. Sosai rigar tayi mata mahaukacin kyau, abun ka da kyakkywar dama, kana ta d'auki hular ta tana mai sanya ta akan ta, bayan ta cusa mayawaicin gashin ta cikin ta. Tukun ta rufe murfin wadrobe d'in tana mai juyawa ta haye kan luntsumemen gadon k'arfen ta na alfarma, mai kalar ruwan zuma, tamkar yadda gaba d'aya sauran kayan d'akin suka kasace kalar. Da sauri ta lumshe idanuwan ta bayan ta janyo lallausan eskimon dake shimfid'e a gadon jikin ta. Tukun ta lumshe idanuwan ta tana mai fatan bacci ya d'auke ta a yanzu-yanzu, domin tayi arba da Gid'ad'on ta farin cikin ranta. Ai kuwa batai ko minti goma da kwanciyar tata ba wani nanauyan bacci mai matuk'ar dad'i ya sure ta. Cikin kyakkywan lambum da suka saba had'uwa da shi ta samu kanta. Sanye take da shigar su ta fulani da tayi matuk'ar amsar jikin, kana ta tai mata bala'in kyau tamkar koda yaushe. Tsaye ta hange sa jikin w...................✍ 08038135929 UMAR Faruq D *BAK'AR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 25* Wata k'atuwar bishiyar gwanda ya juya baya tamkar koda yaushe. Sanye yake da d'an guntun farin wando na yadi kamar yadda ta saba ganin sa ako da yaushe. Cikin tsantsar shauk'in da ta tsinci kanta a ciki ta cigaba da dosar wurin da yake tsaye, fuskar ta d'auke da tsantsar far'a. Jin ta take tamkar wacce aka yiwa bishara da gidan Aljanna aduk lokacin da zata ganta-gata gasa. Tana masa wani irin so irin wanda ita kanta ba zata iya misaltasa ba, tana mai jin sa tamkar yadda take jin rayuwar ta. Tsaye tayi daga bayan sa a lokacin da ta k'arasa wurin da yake, tana mai lumshe kyawawan idanuwan ta. Tukun daga bisani ta wara su a hankali akan farar-fatar gadon bayan sa da take a bud'e, kana ta bud'e baki cikin sanyi tana mai fad'in. "Tabbas rayuwar da babu kai tamkar mutuwa take a wurin Haddiyal Gid'ad'o am, domin ko zuciya da ruhi sun dad'e da yin nunk'aya a kogin k'aunarka. Ina maka so irin son da ban tab'a yiwa wani mahaluk'i makamancinsa ba a duniya. Kai ne na fara sani a duniyar soyayya, da kai zuciya tayi sabo, duk da a kullum rashin jin sautin muryar ka na matuk'ar rikitamun lissafi, kallon ka gare ni shi ne ya zamto farin ciki na. Shin har sai zuwa wane lokaci ne zaka bud'e baki kayi mun kwatan-kwacin irin kalaman da nake maka Gid'ad'o am? Domin kuwa zuciya ta tana gab da yin bindiga muddin za'a cigaba da tafiya a haka." Ta k'arasa maganar cikin sanyi, tana mai jin wani irin yanayi tattare da ita. Yayin da shi kuma ya fara juyowa a hankali, har juyo b'arin da take gaba d'ayan sa yana mai fuskantar ta, fuskarsa d'auke da tsantsar annuri. Sassanyan murmushin sa na ko da yaushe yake jifan ta da shi, yana mai d'an lumshe idanuwan sa, kana ya sake bud'e su akan ta. "Hak'ik'a ina sonka, kuma zan cigaba da sanka daga nan har zuwa ranar da numfashi na zai tsaya, sannan kuma har zuwa lokacin da zaka bayyana a gareni a zahiri, saboda ni d'in an halliceni ne domin ka, kamar yadda aka hallice ka domin ni." Ta k'arasa maganar itama tana mai jifan sa da nata kyakkyawan murmushin. Kana tana mai jin wani irin farin ciki mara misaltuwa na ratsa ilahirin sassan jikin ta, yana kwanciya a cikin b'argon ta. *JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Komai ya sauya a cikin masarautar wasai, tamkar yadda rayuwa take sauyasa ako da yaushe. Tini Gimbiya Fulani ta aurar da 'ya'yanta mata dukan su sai Baby auta kawai da tayi saura. A fannin Babban Yaya shima yayi aure tun yana da shekara ashirin da tara, ta yadda har ya ajiye 'ya'ya ukku yanzu, domin kuwa a yanzu haka shekarun sa sun kai talatin da tara zuwa arbai'n a duniya. A yanzu haka daga shi har mahaifiyar su Gimbiya Fulani basu da wata damuwa face ta hallayar Asad, a kullum basu da aikin yi wanda ya huce addu'oin da suke masa, suna masa fatan Allah ya shirye sa, domin kuwa ba k'aramun sosuwa ransu yake yi ba aduk lokacin da Asad yake gida. A b'angaren Mai Martaba kuwa shima sosai hallayar Asad d'in ke damun sa, domin kuwa bak'aramun d'aci ransa yake masa ba, idan ya tuna yadda suke yin shiga iri d'aya, tare da zama a wuri d'aya da shi da d'an nasa ada, suna hira a koda yaushe tare, amma yanzu gaba d'aya ya canza yak'i komai na baya, babu irin lallab'in da ba yayi masa akan yasa manyan kaya ya kumaje fada amma gaba d'aya a banza, domin kuwa babu abun da Asad ya tsana a halin yanzu irin Fada, yayin da su kuma manyan kaya yake musu kallon barguna. Godiyar sa d'aya ga Allah shine da yariga yasan duk iskancin Asad d'in baya shaye-shaye, sannan kuma baya wasa da Sallah ko kad'an, sai dai kuma bayan ita kuma babu wani abu da ya dame sa na addini. A fannin magautan su kuwa har kawo yau basu fasa jifan su da mugayen abubuwa ba, mussaman ma Babban yaya a yanzu, domin kuwa shi Asad suna ganin sun riga da sun gama da babin sa tun da ya kauce hanyar zama Sarki har abada. Hakan ne yasa suka duk'ufa akan Babban yaya ba dare ba rana, amma sai dai kullum yi suke tamkar basayi, domin kuwa har yau basu tab'a jin ance musu ko ciwon kai yayi ba, gashi har ya fara tara iyali shima, wanda hakan kuwa ba k'aramun k'ona musu rai yake yi ba. Tini Baby autar Gimbiya Fulani ta girma, dan ko a yanzu haka ma karatun degree d'in ta takeyi a cikin d'aya daga cikin k'asashen turawa, ita da 'yar gidan Waziri mai suna Fa'iza, domin kuwa a yanzu haka suna da shekaru goma shatara zuwa ashirin ne a duniya. Sosai Fa'iza take mutuwar san Yarima Asad tamkar ranta, amma sai dai kuma abun takaicin shi ko kallo bata ishesa ba, dan kuwa ko gaisuwar ta ma bako da yaushe yake amsawa ba, sai dai idan suna tare da Baby ne tun daga ranar da ya gane take-taken ta, domim kuwa a cewar sa Allah ya kiyaye ya kula wata daga cikin yaran gidan da sunan soyayya. Haka kuma ba ita kad'ai bace take son sa a cikin 'yammatan gidan nasu, sun kai su kusan Biyar, amma gaba d'ayan su babu wacce take samun darajar kallon arzik'i ma balle ya kulata. *UNGUWAR 'DAN TANKI.* Rayuwa ta canzawa su Aishatu da Iyalanta, ta sanadin aikin da Sheikh Ahmad ya samu na koyarwa a cikin jami'ar su a shekarar da ya gama. Kasancewar ya futa ne da first class, shiyasa makarantar tasu ta rik'e sa amatsayin malami, wato lecture, kana kuma suka basa damar k'aro karatu ta hanyar nauyin sa da duk suka d'auka, hakan ne yasa acikin shekarar da result d'in nasa ya futo ya sake neman gurbin karatun gaba anan cikin jami'ar tasu, wato masters, inda ya d'auki fannin Tauhid. Hakan kuwa ba k'aramun dad'i yayiwa mahaifan sa ba dama duk wani masoyan sa ma. Shekarar sa biyu da fara aikin kacal yayi musu sabon gida na gani na fad'a acikin wata unguwa da take a gaban unguwar su, wacce ta kasance ta masu kud'i, mai suna Babban Zaure Locus, duk da dai gidan nasu ba wai irin tank'ashe-shen nan bane, sai dai kuma a hakan ba k'aramar had'uwa yayi. Part biyu ne a gidan babba da k'arami, babban part d'in mai d'auke da d'akuna sama da k'asa da kuma k'atoton falo shi ya bawa iyayen nasa, yayin da k'aramin kuma da ya kasance plat building shi kuma ya zauna a cikin sa. Kasancewar shekara d'aya kawai su kai da komawa gidan shima yayi aure, inda ya auri d'aya daga cikin d'aliban sa na makarantar islamiyyar sa. A yanzu haka 'ya'yan su biyu shi da ita mace da namiji. Ishak' mai sunan baban sa shine babba, yayin da suke kiran sa da Dady, sai kuma Aishatu mai sunan maman sa da tazo ata biyu, bayan haihuwar Dady da shekara biyu da rabi, ita kuma suna kiran ta da Amira. Sosai sunan Sheikh Ahmad yayi matuk'ar shahara a cikin garin Wasai, domin kuwa a yanzu haka shine limamin juma'a na babban masallacin da yake a cikin garin wasai, idan aka cire na gidan sarki. Sosai girman sa da kwarjinin sa tare da haibar sa harma da kyawun sa suka k'ara futowa, kasancewar a yanzu haka yana da shekaru kusan arba'in ne a duniya. Yana da motocin hawa har guda biyu 'yan madai-daita masu kyau. Yayin da Mahaifin sa Ishak' ma yake da ita, wadda shine ya siya masa da kansa. A yanzu haka matsalar su d'aya ce kawai a gidan duniya, wacce kuma take matuk'ar nuk'ur-k'usar zuciya da ruhikan su, wato Aishatu, domin kuwa har kawo yau bata bar sanya damuwa a ranta ba, ta yadda har ta kamu da ciwon hawan jini mai tsanani, wanda aduk lokacin da ya tashi baya mata da sauk'i ko kad'an. Ako da yaushe sai tayi kamar ta dena tinane-tinanen, kwatsam rana d'aya kuma sai suga ta koma gidan jiya. Wannan damuwar da take ciki itace kawai take hana su sukuni gaba d'ayan su, domin kuwa hatta da kaka da d'akin ta yake anan k'asan bene ba k'aramun damuwa take da yanayin Aishatu ba, haka zata zauna wataran tai ta masifa tana fad'in, ta kasa d'aukar dangana sai kace ba musulma ba, kafin daga k'arshe kuma ta koma tai-ta rarrashin ta, wani lokacin ma har k'walla zakaga tana zubarwa. A fannin fad'an su da Sheikh Ahmad kuwa babu ranar banza da zata zo ta k'are ba tare da sunyi ba, barin ma da aka aurar da k'annen sa mata gaba d'ayan su, ya zamto su biyu ne kawai sukai ragowa shi da autan su mai shekar kusan ashirin da d'aya yanzu take gani, to kullum sai ta takali sheikk Ahmad sunyi ta, domin kuwa shi Auta tasu tazo d'aya da shi sosai, hakan yasa da wuya aji ta fad'i ai'bun sa. Yayin da Sheikh Ahmad kuma abun ya shafi har matar sa, domin kuwa kullum sai ta ai'bata ta tana kushe hallitar jikin ta, duk da kasancewar ta kyakkyawa sosai kuwa tamkar shi. Yanzu haka gaba d'aya Ishak' da Aishatu sun aurar da 'ya'yan su mata. Haka kuma bata sake haihuwa ba tun bayan haihuwar Auta. *ENGLAND* Da matuƙar ƙarfi Billy ta rumtse idanuwan ta sabo da abun da ta gani, jikin ta na wata irin karkarwa! Yayin da ita kuma wannan baturiyar ta k'ara bud'a tafukan hanneyan ta tana mai tallabo k'eyar Yarima Asad da su. Kana ta farasa harshen ta tana mai lasar saman jajayen lips d'in sa da suke matuk'ar birge ta da shi, kafin daga bisani kuma ta fara k'ok'arin tura harshen nata cikin bakin sa. A hankali ya d'ago tafukan hannayen sa duka biyu shima, yana mai dire su akan jan gashin dake kanta, kana ya tallabo k'eyar ta, yana mai zaro tongue d'in sa ya hard'o nata da shi, tukun sukayi wani irin had'e bakunan su wuri d'aya suna masu fara kissing d'in junan su da sauri da sauri. A kuma dai-dai lokacin Billy ta sake bud'e idanuwan ta akan su. Da matuk'ar sauri ta durk'ushe k'asa tana mai sa tafin hannun ta-ta toshe bakin ta da shi, sabo da wani irin azabbaben kuka mai cin rai da taji ya k'wace mata. Wani irin k'una take jin ranta da zuciyar ta suna yi mata. Lokaci d'aya idanuwan ta suka kad'a sukai jajajir yadda kasan gauta, yayin da jikin ta kuma ke wata irin karkarwa tamkar wacce aka sanya acikin ruwa. Cikin zafin rai tayi hurgi da jakar dake rik'e a hannun ta zuwa gefe, tukun ta fara dukan kanta da hannu bibbiyu, tana mai jin tamkar ta tashi taje ta shak'e wuyan baturiyar nan har sai taga ta dena numfashi, sabo da masifar kishin da yake caccakar zuciyar ta. Kana kuma ta k'udirtarwa ranta waji bine itama taje ta same sa daga yau, da ta tsaya tana kallon wasu matan banzan na mu'ama da shi akan idanuwan ta, sai dai kome zai yi mata yayi mata. A fannain su Yarima Asad kuwa cikin tsantsar shauk'i'n da suka tsinci kansu a ciki suka cigaba da abun da suke yi. Kafin daga bisani kuma ya janye tafukan hannayen sa daga saman gashin baturiyar yana mai mayar da su zuwa kan k'ugun ta. Kana ya fara zamar da jikin sa daga kan kujerar da yake yana mai d'an ture ta daga kan cinyar sa, tukun daga k'arshe ya jirkitar da ita ta koma k'asa, yayin da shi kuma ya d'ago zuwa saman ta yana mai yi mata rumfa da faffad'an k'irjin sa, suka cigaba da aikata abun su yadda kasan ba afili suke ba, domin kuwa ko kad'an babuwa ta kunyar tattare da su balle haf suji tsoron kar wani yazo ya gansu a haka. Zumbur Billy ta mik'e tsaye tana mai jujjuya kai, sabo da abun da idanuwan ta suka hango mata Yarima Asad yayi, kafin daga bisani kuma ta fara d'aga k'afafuwan ta cikin tsantsar zafin rai da k'unar zuciya, tana mai futa daga cikin wurin da ta lab'e ta doshi gun da suke gadan-gadan. Tana dab da zuwa wurin taja ta tsaya k'am a wuri d'aya, sabo da yadda taga Yarima Asad ya mik'e daga jikin baturiyar nan zumbur, yana mai yin wani irin jifa da ita a k'asa. Tukun ya fara sakin huci yana mai aika mata wani mugun kallo, da idanuwan sa da gaba d'aya suka riga suka canza launi. Kafin daga bisani kuma ya bud'e baki cikin cunkusassar muryar sa yana mai nuna baturiyar nan da yatsa, tare da fad'in. "How many time did i wand you akan karki k'ara kuskuren kai k'azamin hannun ki jiki na, ko kuwa na fad'a miki dan ina d'an tab'a jikin ki shine yake nufin zamu iyayin komai da ke? To bari kiji in fad'a miki, idan ma kina wannan tinanin, ina mai baki shawarar ki gaggauta kawar da shi a cikin zuciyar ki, because of jiki na ba irin jikin da kike tinanin zai iya kusantar ko wace kalar mace bane, kai impact ma babu ita, kuma ba ayi taba a duniya. Dan haka daga yau babu ni babu ke, ko a hanya kika ganni kikai gangancin nuna kin sanni sai na hulak'antaki. Stupid bitch kawai." Ya k'arasa maganar yana mai sakin nishi tamkar wanda ya futo daga filin dambe, ko kuma na tseren gudu, domin kuwa bai saba yin irin wannan doguwar maganar ba ko acikin sanyi, balle kuma yanzu da yayi ta a cikin zafin rai, hakan ne kuwa ya sanya sa yayi bala'in gajiya. Gaba d'aya yayi furucin nasa ne cikin harshen turanci. Kafin daga bisani kuma ya juya cikin tsantsar b'acinrai bayan yaja wani dogon tsaki, yana mai kama hanyar da zata sada sa da d'akin sa na cikin hotel d'in nan. Yayinda ita kuma baturiyar nan ta fashe da wani irin kuka cikin tsantsar tashin hankali, tana mai tsantsar nadamar abun da ta aikata masa, duk da dama tasan baya so, amma sai dai kuma ko kad'an batayi tinanin zai yanke hukuncin rabuwa da ita ba gaba d'aya a lokaci guda, dama ta gwada sa'ar tane ko Allah zai sa ta dace ayau ya yayada yayi mu'amala da ita, amma sai gashi nan kuma gaba d'aya ta kwafsawa kanta lokaci guda, ta yadda har garin neman gira ta rasa ido. Cikin tsantsar tashin hankali ta bud'e baki a lokacin da taga ya juya zai tafi tana mai fad'in. "Please Please Please Prince don't live me, don't live me, don't do this to me, i promise i will never do that again." Ta k'arasa maganar cikin matsanan cin kuka, tana mai rarrafawa da matuk'ar sauri ta kamo k'afar sa da hannun ta. Cak ya tsaya a wurin da yake zuciyar sa na tsantsar tafasa da k'una, tukun daga bisani ya funcike k'afar sa da k'arfi yana mai juyawa ya kwad'a mata wani irin mugun kallon da ya sanya cikin ta kad'awa, ta yadda har sai da taja baya da sauri, tukun daga bisani kuma ya juya yana mai cigaba da tafiyar sa ba tare da yace mata komai ba. Wani irin gigitaccen kuka ta saki tana mai nadamar abun da ta ai'kata masa a ranta. Abun da ya faru kuwa shine, a lokacin da Asad ya dawo saman ta, sosai ya fara aika mata da salon sa wanda yake matuk'ar gigita duk matan da yake mu'amala da su. Lokaci d'aya gaba d'aya taji ta rud'e ta gigice afagen buk'atar sa, sai dai kuma sanin halin sa da tayi ne na baya tab'a wuce hakan shi ya sanya ta biye masa suka cigaba da kssing d'in junan su, yayin da take jin notikan kanta na sake kwancewa, hakan ne yasa tace bara ta gwada sa'ar ta yau ko Allah zai sa ta dace, tunda taga shima d'in yayi nisa sosai a fagen. Hakan ne yasa ta janye tafin hannun ta d'aya a hankali daga gadon bayan sa, tana mai cusa sa k'ark'ashin ta, wato tsakanin jikin su. Tukun a hankali ta kife sa akan k'irjin sa tana mai fara shafawa, kana ta fara matsar da shi

Chapter 26 of 76