Share this page
dole ya mata ba ta kulasa, kai ak'arshe ma shine yake yin fushi, ta tadda har sai taci wuya tukun take samu ta shawo kansa. Har kawo yau bai tab'a yadda ta kwana a wurin sa ba, duk da yadda take mutuwar son yin hakan kuwa, domin kuwa acewar sa bai ga uban da zata zauna tayi masa ba tun da ba wani babban abu yake da ita ba, asalima kuma shi ba d'an iska bane ba, sabo da tun da yake a rayuwar sa har yau baisan wani abu sex ba. B'angaren su Al'amin kuwa sosai suma suka cin karen su ba babbaka, domin kuwa su mai gaba d'aya ma suke yi babu ruwan su da tinanin lahira, a haka har Allah yasa suka kamalla karatun su na master's gaba d'aya, a lokacin kuma itama Billy saura shekara d'aya ta gama degree d'in ta. Haka su Yarima Asad suka tattaro komai nasu suka dawo Ka'sar Hausa, Jahar Wasai Cikin Masarautar su. Inda sukazo suka tarar da ko wanne an sake tsara masa mazaunin sa acikin part d'in mahaifiyar sa, wanda hakan kuma ya zamto duk aikin mai martaba ne, domin kuwa ba k'aramun farin ciki yayi ba da kammala karatun d'an nasa mafi soyuwa a ransa ba, sabo da sanin da yayi na yanzu shikenan ya dawo gaban sa, babu kuma zancen sake yin nisa da shi anan kusa, dan kuwa yace koda zai barsa yayi Phd to sai bayan ya tabbatar da ya nutsu ya dawo tamkar yadda Babban Yaya yake, tukun zai barsa ya k'ara yin nesa da shi, domin kuwa sun d'aura d'amarar ganin sun dawo da shi kan hanya daga shi har Fulani, kai harma da Babban yaya. Watan su biyu da dawowa dai-dai mai martaba da waziri harma da galadima suka same su da zancen aure. Take a wurin Al'amin ya gabatar musu da budurwar sa wadda suka had'u da ita acan school d'in, amma ita yanzu take kanyin degree d'in ta, wato dai mate d'in Billy ce, duka-duka ba zasu k'ara ko shekara d'aya a school d'in ba suma zasu kammala. Yayin da shi kuma Asad ya nuna musu cewar bai san wannan batun ba kwata-kwata, kai atak'aice ma a k'arshe haka yace shi har yau baiga wacce tayi masa ba. Hakan ne yasa waziri ya yanke masa lokaci zuwa nan da shekara d'aya a wadace kenan, sannan yace masa muddin lokacin kuma ya cika bai futar da matar aure ba to ya sani su da kansu zasu zab'a masa cikin 'yammatan su na nan gida da sukaji labarin suna haukar son sa, kana a ka'rshe suka sallame su gaba d'ayan su, bayan sun yanke hukuncin zuwa su nemar wa Al'amin auren yarinyar da yace yana so. Ko kad'an Yarima Asad bai d'auki maganarsu da muhimmanci ba, sai ma ya watsar da ita a wurin da suka gama yinta, tukun ya taso ya baro wurin. _BAYAN SHU'DEWAE WASU WATANNI._ Sosai Yarima Asad yake buga tsiyar sa yanda ransa yake so. Yayin da Babban Yaya, Gimbiya Fulani da Mai Martaba suke k'ok'arin ganin ya dawo kan hanya a kullum amma a banza. Tini Billy sunyi graduation harma ta dawo gida, ta yadda har suka d'ora da mu'amalar su daga wurin da suka tsaya ita da Prince d'in ta. Yayin da sunan Yarima Asad kuma ya karad'e kunnen ko wane mutum da yake da kusanci da Billy, ciki kuwa har da mahaifin ta mai girma gwamna, sai dai kuma har kawo yau bai tab'a zuwa gidan su ba, sai dai ita tazo ta same sa a cikin Asadullah Palace. Yayin da Al'amin kuma akayi maganar auren sa harma da sa rana, inda za'a had'a bikin nasa dana 'yammata da yawa da suke a cikin Masarautar Wasai, cikin su kuwa har da masu hauka akan Yarima Asad da suka gaji suka hak'ura, sabo da ganin da sukayi baya ta su ko kad'an. Yayin da ita kuwa Fa'iza k'awar Baby da suka kammala degree d'in su yanzu take tsantsar haukar sonsa, amma sai dai kuma ko darajar kallo bata samu daga gare sa. Sosai Yarima Asad yayi k'aurin suna acikin garin wasai fiye da duk sauran yaran cikin gidan sarautar, haka kuma kowa yasan halin sa, sabo da yadda ko titi idan ya futo baya sassautawa mota, kamar yadda bai yadda wani ya tuk'asa ba muddin ba tafiyar nesa zaiyi ba. Yayin da motocin sa kuma suka kasance har guda goma shabiyu, gaba d'ayan su masu azabar kyau da tsada na zamani. Ko wacce tana d'auke da number ta mai suna Prince Asad ajikin ta, tun daga kan number 1 har zuwa 12 ta k'arshe. Sosai yake matuk'ar birge Matasa, sannan kuma suke mutuwar son sa da san salon sa, barin ma idan ya futo akan doki, kasancewar har yau yana hawa doki, kana kuma yana da su kusan har guda shida, gaba d'ayan su lafiyayyu k'osassu. Yayin da manyan mutanen da suke a kusa da gidan sarki kuma suke alawadai da hallayar sa, wasu kuma suke masa fatan shiriya, sabo da kowa yasan yadda yake gudun al'adun hausawa yanzu, su kuwa manyan babu abun da suka tsana face irin shigar da yake yi, da kuma yadda suke jin labarin sa a gari na cewar yana da huraren shak'atawa da yake had'a 'yammata da samari kala-kala suna iskancin su. Wannan dalilin ya sanya baya birge su kwata-kwata. Mutuwar Ciroman gida wanda ya kasance k'ani ga mai martaba da yayi bayan wasu 'yan watanni ne ya sanya ake ta shirin nad'a Babban yaya a cikin satin nan, domin ma har an tsaida ranar da za'ayi nad'in, sabo da dubawar da akayi a kaga shine kawai ya cancanta da kujerar, dama kuma ita sarautar ciroma sarauta ce wacce ake bawa 'ya'yan sarki ita. Wannan dalilin ya sanya aka futar da shi a matsayin wanda za'a d'ora akan karagar ta ciroman gida, wanda za'ayi bikin nad'in nan da sati d'aya mai zuwa. *BABBAN ZAURE LOCUS* Tsaye suke a cikin compound d'in gidan nasu, Sheikh Ahmad na furfuto da kayan da suke acikin boot d'in motar tasa irin su fulo, capet, buta, tare da kulolin abinci, wanda hakan ke nuni da cewar sun dawo daga asibiti ne, kuma da alamun sun d'an kwana biyu ne acan d'in da. Yayin da matar sa kuma take rik'e da Aishatu, da yanzu ta koma hajiya Aishatu da sukaje saudiyya sukayi aikin hajji da ita da Ishak', harma da tsohuwa kaka a shekarar da ta huce, wanda Sheikh Ahmad ne ya biya musu gaba d'ayan su kuma, domin kuwa a yanzu sai dai suce Alhmadulillah, sabo iyakar rufin asiri na duniya Allah yayi musu shi, sai dai kawai suyi fatan da cewa da na lahira. Da alamun dai itace mara lafiya da aka dawo da ita daga asibitin, duba da yadda tayi matauk'ar kwantsamewa, sai kuma Alhaji Ishak' mahaifin Sheikh Ahmad da shima ya futo daga gidan gaba. 'Dibar kayan sukayi suna masu shigewa da su cikin gidan gaba d'ayan su. A d'an madai-daicin falon nasu da ya gaji da had'uwa da kayan ado, suka zube akan tausasan kujerun da suke a cikin sa wa'yan da suka kasance na k'asar turkey. "Barka! Barka!! Barkan ku da isowa." Muryar kaka ta ratsa dodon kunnuwan su a lokacin da take futowa daga cikin d'akin ta. "Yawwa Kaka barkan ki da gida." Sheikh Ahmad da matar sa suka fad'a suna masu kallon ta. Yayin da Ishak' da Aishatu kuma suka had'a baki wurin gaishe ta cikin tsantsar ladabi da biyayya. Amsa musu kaka tayi tana mai zama akan kujerar da take facing d'in wacce Aishatu take zaune akai. Kana ta bud'e baki idanuwan ta akan Aishatu tana mai fad'in. "To ya kuma k'arfin jikin naki yanzu 'yannan?" "Alhamdulillah." Aishatu ta fad'a tana mai kallon ta itama. Yayin da ita kuma Kaka ta k'ara gyara zaman ta, tukun ta d'ora da fad'in. "Har yau na rasa gane wace irin macece ke Aishatu, tun kina bani tausayi ina zubar miki da hawaye ada har gashi yanzu kin fara bani haushi. Haba, ace mutum kwata-kwata ya kasa yadda da k'addarar da Allah ya d'oro masa. Yau kimanin kusan shekara talatin da faruwar wannan abun, tun kina da yarinta a jikin ki gashi nan har girma ya fara zuwar miki, amma kullum kina mayar da abu tamkar yanzu yake faruwa, bayan kuma kin san hakan babbar illace gare ki, domin kuwa gashi nan yanzu har likita yace kina gab da kamuwa da ciwon zuciya, bayan kuma tsinannen hawan jinin nan mara imani da yayi miki mugun kamu. To ina ranar damuwar da kike sawa aranki?" Kaka ta fad'a cikin fad'a fad'a tana mai hararar Aishatu. Ita kuwa Aishatu lumshe idanuwan ta tayi tana mai jin furucin kaka na dukan zuciyar ta. Ji take inama ace zata iyayin yadda suke so tayi, tabbas da babu abun da zai hana ta yin hakan, domin kuwa tafi kowa cutuwa da kalar halin da take ciki na yanzu. Amma sai dai kuma ita kanta ta sani babu wanda zai tab'a fahimtar ta, sabo da shekara talatin ba kwana talatin bace ba. Sai dai kuma ita a yanzu ma gaba d'aya ta fara futar da ran sake yin wani murmushi agidan duniya. Sabo da mafarkin matashin kyakkyawan yaron da take yi a yanzu cikin mugun yanayin da yafi na baya sosai sosai, wanda hakan kuma shine musababbin tashin ciwon nata har ya kaita da kwanciya a asibiti na tsawon sati biyu yau kenan. Sai dai kuma tasan babu mai fahimtar halin da take ciki kota fad'a yanzu, sabo da koda ita d'in ce ma ba lallai ta fahimta ba. Sai dai kuma ta riga tabarwa Allah komai nata yanzu, babu abun da take aikin yi face addu'ar Allah yaye mata wannan damuwar, ya sanya mata dangana ko domin farin cikin ahalin ta. Shi kuwa Sheikh Ahmad gyara zaman sa yayi akan kujerar da yake zaune akai yana mai karkata kansa, kana ya watasa dara-daran fararen idanuwan sa akan fuskar Kaka. Sannan ya bud'e baki yana mai fad'in. "Kuji tsohuwar nan dan Allah, to yanzun da kika sata a gaba kina ta masifa dame kike so taji kenan, bayan kuma duk kema kina d'aya daga cikin zamtowa silar abun da ya faru." Ya k'arasa maganar k'asa-k'asa yana mai d'an watsa mata hararar wasa. "Yau na shiga ukku na lalace, yanzu Ahmadu ni kake zagi a haka akan idanuwa na sabo da nayiwa Uwarka fad'a. To Ishak'u kana jifa fitsararren d'anka yana zagi na, amma kayi shiru kana kallon sa. Innalillahi ke duniya ina zaki damu, yau naga abun da yafi k'arfin gani na, sannan naji kalamin da suke shirin toshe mun kunnuwa na." Kaka ta fad'a da k'arfi tana mai fara k'wak'ulo- k'walla a cikin idanuwan ta tana goge ta a hab'ar zanin ta da ta kwanto sa, sabo da Ishak' yayiwa Sheikh Ahmad fad'a. Ai kuwa ta samu yadda take so. Domin kuwa cikin tsantsar zafi Ishak' ya juyo b'arin da Sheikh Ahmad yake yana mai cewa. "Kai dan Ubanka meye hakan kakeyi, bana son shirmen banza da wofi fa, ko kuwa ita d'in tsarar kace da zaka tsaya kana fad'a mata magan-ganu, to kasani har dai zaka iya yi mata rashin kunya nima tsaf zaka yi mun, domin kuwa itace komai nawa a duniyar nan." Ishak ya fad'a cikin zafi yana mai kallon fuskar Sheikh Ahmad. Shi kuwa Sheikh Ahmad kansa ya durk'usar k'asa yana mai d'an murza yatsun hannuwan sa. Yayin da yake jin duk zuciyar sa babu dad'i, sbo da ran mahaifin nasa da yaga ya b'aci. Hakan ne yasa cikin sanyi, kana cikin yin k'asa da murya ya bud'e baki yana mai fad'in. "Kayi hak'uri Abba ka gafarce ni, insha Allah irin haka bazata sake faruwa ba." "Hhhhhhhhhh! Kaji d'an kan Uba ko, ai wallahi ni d'in dai-dai nake da duk wani d'an banza a gidan nan." Kaka ta kwashe da dariya tana mai kallon Sheikh Ahmad, yayin da take jin zuciyar tayi haske k'al. Kana daga bisani kuma ta mayar da idanuwan ta kan matar Sheikh Ahmad da take zaune mai tana fad'in. "Ke kuma lafiya kika zubo mun wa'yan nan mayun idanuwan naki, ke wai a dole mai miji kinji haushi an masa fad'a ko, to ai sai ki matso ki dake ni shine zan san ranki ya b'aci mara kunya matar fitsararre kawai. Malaman k'arya malaman bogi." Durk'usar da kai tayi tana mai d'an sakin murmushin yak'e, kana ta bud'e baki tana mai fad'in. "Allah ya baki hak'uri kakus, ni ba haka nake nufi ba." "Dallacan ni rufemun baki gafara kawai. Kai Allah Sarki Huzaifah na, Allah ya nuna mun taka matar, kai daga gani nasan kyakkyawa 'yar gayu zaka zab'o mana ba irin su d'an ware ba, domin kuwa dama kowa yana d'auko kalar sane." Ta k'arasa maganar tana mai sahafa kan Auta tare da hararar Sheikh Ahmad daga wurin da take zaune. Shi kuwa Sheik Ahmad inda take bai d'ago ya kalla ba, saboda lura da yayi da neman rigima kawai take yi yau d'in, gashi kuma yaji Abban nasa ya biye mata, hakan ne yasa sa kama bakin sa yayi gum da shi ba tare da ya furta komai ba. *JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.* Babu daren duniyar da zaizo ya tafi ba tare da Gimbiya Haddiyal tayi mafarkin Gid'ad'on ta ba har yau. Yayin da soyayyar sa kuma ta k'ara mamaye gaba d'aya zuciya da ruhin ta, ta yadda har take jin komai zai iya faruwa da ita idan ta rasa sa. A kullum bata da wani labari face nasa, babu abun da tafi son gani face kyakkyawar fuakar sa, hakan yasa ko da yaushe take cikin lumshe idanuwan ta dare da rana, domin kuwa da zarar ta lumshe sun take ganin sa tsaye a gaban ta yana mata murmushin sa. Bata da abokan hira wa'yan da suka huce tsuntsayen ta, domin kuwa sune kad'ai take zama ta bawa labarin Gid'ad'on ta kuma su saurare ta har su taya ta farin ciki. Yayin da sauran mutane kuma suke mata kallon wacce ta fara zaucewa, ta yadda har ake ta aikin samar mata da maganunuwa amma a banza. Sosai ta duk'ufa wurin binciken ganin ta gano mazaunin sa, amma a kullum abun baya yihuwa. Tana da amintaccen Bawa wanda take kiran sa da Buba, wato amintacce ta kenan da fulatanci. Shine kad'ai ya tabbatar da Gid'ad'on ta mutum ne ba aljan ba, sannan kuma ya duk'ufa wurin ganin ya taya ta cimma burin ta. A yanzu haka tana da shekaru Ashirin da biyu ne aduniya, yayin da kyawun halittar ta kuma ako da yaushe yake k'ara bayyana, ta yadda babu mai iyayi mata kallo d'aya ya janye idanuwan sa ba tare da ya sake ba, tun daga kan mace kuwa har namiji. Duk da secondry d'in da tayi batasa ta bar al'adun su na fulani ba da shigar su, kamar yadda ta taso ta ganta acikin ta. Domin kuwa haka masarautar tasu take tafiya har kawo yau da al'adun ta, wannan dalilin ne ma ya sanya ko wasu kayan daban Gimbiya Haddiyal bata sanyawa sai nasu na fulani, duk da kuwa ba su d'in ne kad'ai suka zamto kayan ta ba, domin kuwa Habu da kansa yake siyo mata English wear tare kuma da atamfofi da leces, amma ko kallo basu isheta ba. Iyakaci idan kaga tasa wasu kayan daban to lokacin bacci ne, shine take sanya sleeping dress a jikin ta. Yayin da su kuma kayan nata na fulani suka zamto kala-kala, kana masu matuk'ar yawa, ta yadda har idan tasa wani sai ta shafe sama da wata ukku ba tare da ta zagayo kansa ba, kai wani lokacin ma har mantawa da wasu takeyi. *K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA* Tun bayan karon da Gimbiya Tamir da Bir da sukayi na biyu da har yau basu sake gamuwa ba, tsawon watanni da yawa kenan, kuma hakan ya faru ne ta dalilin rok'on sa da iyar bayi tai-tayi har da su k'wallar ta akan kar ya k'ara shiga sabgar Gimbiya. Amma sai dai kuma ba k'aramar cutuwa yayi ba da rashin ganin tan da bayayi, domin kuwa babu ranar da zata zo ta shige ba tare da yayi tinanin ta ba, haka kuma aduk daren duniya yana aikin mafarkin ta. Sosai kuwa ya rame kana gaba d'ayan sa ya k'ara komawa shiru-shiru. Haka kawai kwanan nan yaji aduk duniya babu abun da yake son gani sama da fuskar ta, ta yadda har yake jin baik'i ba ace ko kashe sane tasa ayi muddin ya riga ya ganta. Wannan dalilin yasa sa k'udirtawa ransa cewar yau duk runtsi duk huya sai ya isa gare ta, sai dai duk abun da zai faru ya faru bayan ya gantan. Ita kuwa gimbiya Tasmir a b'angaren ta sai da ta d'auki kusan wata tana jin bak'in cikin abun da yayi mata, kafun daga baya kuma komai ya huce. Babu abun da yafi damun ta sai idan ta tuna da yadda bugun zuciyar ta ke sauyawa aduk lokacin da suka had'u. Hakan yasa ta k'udiri aniyar cewa muddin suka k'ara yin gamo da shi sai yayi mata bayanin dalilin da yasa take jin fad'uwar gaba idan ta kasance a gaban sa, sabo da tana zargin ko wani asirin gare sa akan ta, sai dai kuma tun bayan waccan had'uwar tasu ba ta k'ara ganin sa ba. Hakan yasa ta gane cewa ya bam-bance tsakanin ta da shi kenan, shiyasa bai k'ara biyo hanyar ta ba, wanda hakan kuma ba k'aramun dad'i yayi mata ba. Yanzu haka zaune take akan d'irkeken bak'in dokin ta sanye da shigar ta-ta yau da kullum. Yayin da hannun ta d'aya kuma yake r................✍ *AMIN AFUWA ZAKUGA SUNAN MAHAIFIN SHEIKH AHMAD YA CANZA DAGA ABDULKARIM DA NACE A PAGE NA UKKU ZUWA ISHAK', HAKAN YA FARUNE TA DALILIN MANTUWAR DA NAYI.* SAI KUMA NA BIYU YAYAN GIMBIYA HADDIYAL HABU SUNAN SA, BUBA KUMA SUNAN AMINTACCEN BAWAN TANE, SHIMA ABAYA NAYI MISTAKE NA CEWA HABU BUBA, WANDA SAI DAGA BAYA NA FAHIMTA.* UMAR FARUQ.✍ 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 πŸ‘‘πŸ‘‘ πŸ¦‹ πŸ¦…πŸ•ŠπŸ¦† πŸπŸŽ πŸ„πŸΉ _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 30* _END OF BOOK 1_ Rik'e da zureriyar takobin ta, d'ayan hannun ta kuwa rik'e yake da linzamin dokin ta. A hankali dokin ya fara tafiya, yau da alamun ita kad'ai kawai take sha'awar yawon, duba da yadda babu wani da ya biyo ta a cikin dakarun nata. Tafe suke a saman dokin fuskar ta d'auke da annuri, sab'anin sauran ranakun da ko da yaushe take a d'aure. Yau tun da ta tashi daga bacci take jinta cikin wani irin farin ciki. 'Daga kanta tayi sama tana mai kallon yadda giza-gizai suke a ko ina, ga kuma yadda garin nasu yayi luf-luf tamkar koda yaushe, kana ga wata irin sassanyar iska mai matuk'ar dad'i da take busata ta ko ina, ta yadda har uban bak'in gashin kanta yake d'an d'agawa sama. Ga kuma yadda iskar ke kad'a rigar da ke sanye a jikin ta, tana ta faman bud'ewa, wannan dalilin shine ya sake sanya ta cikin annashuwa sosai. Acan wurin Bir kuwa cikin wani irin yanayi na tsantsar buk'atar ganin fuskar Gimbiya da yaji shi a cikin sa ya mik'e daga bakin bishiyar da yake zaune. 'Daga tafin hannun sa yayi yana mai shafa lallausar sumar dake d'auke akan sa mai matuk'ar yawa. Kafin daga bisani kuma ya d'an saki murmushi, yana mai fatan ya had'u da itan idan ya tafi. Kana ya fara d'aga k'afafuwan sa cikin wani irin kuzarin da yake ji a tattare da shi, yana mai dosar hanyar da yake tsammanin zai iya cin karo da Gimbiyar tasa acan. Sosai yake jin wani irin farin ciki mara misaltuwa tattare da shi. A lokaci d'aya gaba d'ayan su bugun zuciyar su ya sauya, suka fara jin tamkar yadda suke ji aduk lokacin da sukayi kusanci da junan su. Cak Bir ya tsaya a wurin da yake yana mai lumshe idanuwan sa, kana daga bisani ya d'ago tafin hannun sa yana mai dafe saitin zuciyar sa da shi. Yayin da yake jin wani irin farin ciki mara misaltuwa nayi masa bargo a gaba d'aya ilahirin jiki da zuciyar sa, sabo da fahimtar da yayi na tabbas Gimbiyar tasa tana kusa da k'arasowa wurin da yake d'in, wato dai yau yayi futowar sa'a. Kana daga bisani ya cigaba da d'aga k'afafuwan sa yana mai cigaba da bin hanyar, kansa sun kuye a k'asa, acewar sa yana son ta fara kallon sa ne kafin shima ya kalle ta. Ita kuwa Gimbiya Tasmir lokaci d'aya yanayin ta ya sauya, gaba d'aya annurin dake akan fuskar ta ya gushe, ta yadda har launin idanuwan ta suka fara d'an sauyawa, ba dan komai ba kuwa sai sabo da jin da tayi bugun zuciyar ta gaba d'aya ya canza, k'irjin ta na wani irin bugun tara-tara, wanda hakan yasa ta fahimci abun da ke shirin faruwa, wato dai yau ma batayi futowar sa'a ba, tayi gamo da k'ask'antaccen Bawan ta. 'Dan rumtse idanuwan ta tayi da k'arfi, tana mai tinanin kalar hukuncin da zatayi masa idan har bai bata amsar tambayar da zatayi masa yau ba, domin kuwa ta k'udiri aniyar jin dalilin da ya sanya take samun fad'uwar gaba aduk lokacin da zai-zo gare ta. Cikin wani irin yanayi na tsantsar b'acin rai ta sake damk'ar linzamin dokin. Ai kuwa take a wurin ya k'ara gudun sa akan wanda yake yi na baya. Ba zato ba tsamnani kawai sai ganin su sukayi a gaban juna. Ita tana daga saman doki idanuwan ta akan sa. Yayin da shi kuma yake daga k'asa gaban dokin idanuwan sa a cikin natan. Kallon-kallo suka fara jifan junan su da shi daga wuraren da suke tamkar ko da yaushe. Yayin da bugun zuciyoyin su kuna suke sake tsanan ta, ta yadda har suke jin tamkar zasu hudo k'irjin su su futo. Cikin wani irin yanayi Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwan ta, tana mai jin tabbas wannan bawan yana shirin zame mata masifa a rayuwa, kafin daga bisani kuma ta fara aikawa kanta da tambayoyi. "Shin mene yasa bashi da tsoro ne ma shi, wato kenan yana nufin yace duk wahalar da yasha a wancan lokacin bai daddara ba, tun da gashi nan yau ma ya tsare ni agaba yana aiko mun kallo da wa'yan nan mayun idanuwan nasa, tabbas yau d'in kuwa dole ne na san dalilin da yasa kallon sa yake sanya mun fad'uwar gaba." Ta fad'i haka a cikin ranta, kana daga bisani ta bud'e idanuwan nata akan fuskar Bir. Sannan tayi wani irin durowa daga kan dokin, tana mai fara d'aga k'afafuwan ta-ta doshi wurin da yake takobin ta rik'e a hannun ta. A hankali Bir ya d'an fara d'aga k'afafuwan sa yana mai ja baya daga wurin da yake, sabo da yadda yaga ta nufo kansa gadan-gadan. Yayin da har lokacin kuma idanuwan su suke sark'e a cikin na juna. Ba shi ya dakata da ja da bayan da yake ba kamar yadda itama d'in bata daina biyo sa ba, har sai da ya dan gana da jikin wata k'atuwar bishiya, kana ya jingina da ita yana mai lumshe idanuwan sa. Yayin da ita ma ta tsaya cak a wurin, tana mai jin zuciyar ta na cigaba da gudu a d'ari, ga kuma wani irin b'acin rai da tsantsar tsanar wannan bawan na gaban ta da suke taso mata tun daga k'asan zuciyar ta. A hankali Bir ya bud'e idanuwan sa yana mai watsa su akan fuskar ta, kana ya d'an saki murmushin sa mai matuk'ar kyau, ta yadda har sai da fararen hak'waran sa suka bayanna, tukun ya d'an d'aga lab'b'an sa cikin yin k'asa da murya, yana mai fad'in. "Hak'ik'a idanuwa na sunyi kewar ganin wannan kyakkyarwa fuskar taki, mai cike da abubuwan kallon akan ta Gimbiyar mu. Shin wai me...." Maganar tasa ce ta yanke, sabo da yadda yaga lokacin d'aya jikin ta ya d'auki wata irin rawa, ga kuma idanuwanta da ta zuba su akan sa da suke k'ara rikid'ewa suna yin ja, jan ma irin jajahur d'in nan. Yayin da jijiyon kanta kuma suka futo sukai rud'u-rud'u akan goshin ta. "Zan tambaye ka, sai dai kuma kafun nan ina son kasani bana son k'arya, asalima na tsani duk wani mak'aryaci a rayuwata, dan haka amsar tambayata kawai nake buk'atar ji daga gare ka a yau d'in." Gimbiya Tasmir ta fad'a cikin

Chapter 31 of 76