Yayin da daga can gefen filin kuma wani tamfatsetsen farin ruwa mai wucewa yake.
Sosai aka ƙawata wurin da ado kala-kala, yayin da tambarin masarautar tasu kuma ya kasance manne akowane wuri, acan ƙarshen filin kuwa daga jikin bango wata irin haɗaɗɗiyar ƙatuwar kujerar ƙarfe ce aka jere awurin, yayin da gefe da gefen ta kuma aka aje wasu ƙananan kujerun masu azababben kyau suma na ƙarfe masu dauke da tambarin baƙar masarauta ajikin su, yayin da tsakiyar filin kuwa aka ƙawata sa fiye da yarce aka ƙawata ko wane wuri.
Wani tafkeken daɓe (floor) ne akayi awuri mai matuƙar tudu da tsairs ajikin sa, gaba ɗayan sa zage yake da randinan da suke ɗauke da Huta acikin su suna matuƙar ci sosai, yayin da saman daɓen kuma aka ajiye wani danƙareran gunkin da akayi sa da taɓo da basa da kyan gani ko kaɗan, yayin da gefe da gefen sa kuma ya kasance ɗauke da fulawoyi zube aƙasa zageye da shi masu matuƙar yawa da wal-wali, sai kuma tambarin baƙar masarauta da aka bi aka manna sa aduka ƙasan daɓen.
Acan ɓangaren bayi kuwa ko wanne shiryawa yake cikin kalar shigar sa.
Yayin da ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa ta kasance zaune akan wata ar'niyar kujerar ƙarfe mai azabar kyau da sheƙi acikin ɗakin ta, yayin da wasu ƴammata da suke ɗaure da ɗan guntun baƙin ƙyalle iya guiwar su tare da ƙatuwar farar rigar yadi ajikin su mai ɗauke zanen tambarin masarautar tasu suke aikin tsan-tsara mata wata irin azababbiyar kwalliya mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, kallo ɗaya zaka musu katabbatar da amatuƙar tsorace suke, sannan kuma ko kaɗan basa cikin nutsuwar su, sabo da yarce suke aikin wasu sassa na jikin su na kar-karwa.
Yayin da ita kuma ta kasance lumshe da idanuwan ta tana mai ɗan taune leɓen ta na ƙasa ahankali, tare da ɗan sakin murmushi lokaci bayan lokaci, wanda yayi matuƙar bawa ƴammatan da suke yi mata kwalliya mamaki, domin kuwa zasu iya cewa tunda suke da ita basu taɓa ganin ta tana murmushi irin haka ba sai yau, duk da dai dama bawai suna iya kallon fuskar ta bane ba ada, yanzun ma dan suna mata kwalliya ne shiyasa har suka samu wannan damar kallon ta, amma sai dai tun da suke basu taɓa jin ko alabari ba ance tayi murmushi sai yau da suka gani azahiri .
Afannin ta kuwa ba komai ne ke sata murmushi ba sai tunawa da take yi yauce ranar da zata koyawa ƙasƙantaccen ƙazamin bawan can Bir da yake ganinta tamkar tsaran sa hankali, domin kuwa ta tanadi azabobi kala kala waƴan da zata yi masa su ayau fiye da duk sauran da ta masa abaya muddin bai bata amsar tambayar ta ba.
Sanye take da wata doguwar riga mara kafaɗa wacce ta kasance ruwan ƙasa mai duhu sosai, yayin da kanta kuma ya kasance ɗaure da abun ɗaurin ɗan kwali kalar ruwan zuma da aka mata ɗauri irin mai hawa hawa da shi, sai sarƙar goshi mai azababben kyau ta goal da take zagaye akan ta. Yayin da ƙafafuwan ta da hannuwan ta harma da wuyan ta suka kasance ɗauke da sarƙoƙin goal masu matuƙar kyau da tsada suna ƙyalli.
Sosai tayi matuƙar kyau tana ta faman sheƙi ta ko ina.
Acan ɓangaren su Bir kuwa tun cikin dare Iyar Bayi ta sake zaunar da shi tana mai sake roƙon sa akan karya ko kalli fuskar Gimbiya Tasmir, balle har tai masa wani abun.
Da tom ya amsa mata shima yana mai ƙudurtawa ransa cewar zaiyi yarce Iyar tasa ta roƙe sa yayi ko domin farin cikin ta, amma bawai dan yana tsoron wani abu da Gimbiya Tasmir zata masa ba, asalima yasan sai yayi tsantsar kai zuciyar sa nesa, tukun zai iya haƙura ya kasa ɗaga kai ya kalle ta muddin sukai kusanci da juna, gashi kuma yasan wajibine suyi kusancin, tunda akwai gaisuwa ta daban da Bayi suke kaiwa ahalin Sarki aduk irin wannan ranar.
*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*
Tun misalin ƙarfe takwas da minti arba'in Yarima Asad ya gama shirin sa tsaf kamar yacce Babban yaya ya umarce sa akan ya shirya da wuri.
Sai dai kuma irin shigar da yay ta yau tafi ta kusan koda yaushe muni, domin ko sanye yake da wani farin wando three quarter wanda yake akekkece daga saitin cinyoyin sa, tayarce har ake hangen farin net boxer ɗin dake sanye jikin sa, wato crazy, sai wata baƙar t shirt mai ɗan guntun hannu da take sanye ajikin sa da tayi matuƙar kama jikin sa, tayarce har ta bayyana gaba ɗaya murɗaɗɗiyar surar sa.
Yayin da sumar dake ɗauke akansa sa mai tsananin yawa kuma ta kasance atsage gida biyu, banda wal-wali da sheƙi babu abun da take yi, sabo da ruwan mayukan da ya mulketa dasu har zuwa ƙasumbar sa, sai wuyan sa kuma da yake ɗauke da wani silin sarƙar goal mai matuƙar ƙyalli, yayin da hannun sa ɗaya kuma ya kasance ɗaure da wani azababben baƙin agogo yayi matuƙar ƙara haskaka fatar hannun, sai kuma ɗayan hannun da ya bisa da wasu abun hannuwa na roba suma baƙaƙe. Banda faman ciccin magani yana kumbura babu abun da yake aikin yi, donin ko koda Al'amin yazo yana masa magana ma ko kai bai ɗaga ya kalle sa ba balle ya tanka masa, hakan da Al'amin ya gani ne, sannan kuma ya fahimci dalilin fushin nasa ya sanya yake ta faman tsokanar sa yana sheƙar uwar dariya, domin ko shi sanye yake da manyan kaya ɗinkin riga da wando na shadda.
Ƙarasawa yayi zuwa inda takalman sa suke yana mai sa hannu ya ɗauko wani sabon baƙin boot yana mai sanya ƙafafuwan sa acikin su, tukun ya janyo wayar sa ya riƙe ahannun sa yana mai komawa gefen bed ɗin sa ya zauna tare da mai da idanuwan sa kanta.
Ko minti biyu baiyi ba da zama sautin ringing ya fara tashi daga cikin wayar tasa.
Yamutsa fuska yayi yana mai sake ɗaure fuska, sabo da sunan da yaga yana yawo akan screen ɗin wayar tasa, wato Yaya na. Tukun daga bisani yayi picking yana mai kai wayar kan kunnen sa.
Lumshe idanuwan sa yayi yana mai ɗan taune lower lips ɗin sa da haƙora ba tare da yace komai ba, da alamun dai yana sauraran abun da ake faɗe ne daga can, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Tom shikenan gamunan." Daga can ƙasan makoshin sa, kana ya janye wayar daga kan kunnen sa yana mai miƙewa tsaye.
"Ka taso Malam ana jiran mu." Ya faɗi haka yana mai yin gaba.
Murmushi Al'amin yayi ba tare da yace komai ba shima, tukun shima ya miƙe yana mai bin bayan sa.
Acan ɓangaren Babban yaya kuwa sanye yake da manyan kaya harda alkyabba ajikin sa.
Tsaye suke agaban wasu arnayen motoci da suke ta faman ɗaukar ido, tare da dogaran sa da suke sanye da uniform da zura zuran bulalai riƙe ahannun su, suna masu kallon hanyar da su Yarima Asad zasu ɓullo, alamun su ɗin kawai suke jira kenan.
Al'amin ne ya fara ɓullowa tukun Yarima Asad ya biyo bayan sa, tun daga nesa Babban yaya ya saki baki tare da zuba idanuwa akan ƙanin nasa saboda shigar da ya hango sanye ajikin sa, yayin da suma dakarun nan gaba ɗaya suka bisa da kallo, duk da dai hakan ba sabon abu bane awurin su, sai dai amma gaba ɗaya cikin su babu wanda yay zaton ganin sa ahaka yau, duba da wurin da suka san zasuje.
Tafe suke babu mai cewa wani ƙala daga shi har Al'amin, dan shi Yarima Asad ma kansa sunkuye yake aƙasa, ahaka har suka ƙaraso bakin motocin nan.
"Ina kwana Yaya." Al'amin da Yarima Asad suka faɗa adai dai lokacin da suka ƙaraso gaban Ciroma.
"Da alamu ka manta sunan wurin dana faɗa maka zamuje ne, ko kuma ka kurmance alokacin da nake faɗa maka jiya, shiyasa har ka sanyo waƴan nan ƴan iskan kayan ajikin ka ko?" Babban yaya ya faɗi haka ransa aɓace ba tare da ya amsa gaisuwar da suka masa ba, sai idanuwa kawai da ya kafe yarima Asad dasu yana kallon sa.
Yayin da shi kuma ya sake gyara tsayuwar sa awurin da yake yana mai ɗaure fuska tare da ɗaukar yastun hannuwan sa ya kai kan ƙeyar sa yana sosawa ba tare da yace komai ba.
"Wai ba magana nake maka bane da kamun shiru kana bina da idanuwa?" Babban Yaya ya faɗa da ƙarfi ransa na ƙara tafar fasa.
Yayin da shi kuma Yarima Asad ya rumtse idanuwan sa da ƙarfi yana mai danna lower lips ɗin sa cikin baki ya cije su, sabo da tsawar da yayan nasa yamasa ransa na ɓaci shima, tukun daga bisani ya buɗe baki still yana sosa ƙeya tare da faɗin. "Am dama Yay.... "Kamun shiru, bana son jin duk wani shirmen banzan da zai futo daga bakin ka, dan haka yanzu yanzu ka huce kaje ka canzo kayan nan kasanya kayan mutunci, minti biyar kawai na baka ina jiran ka anan." Ya katse sa da faɗin haka cikin tsawa ba tare da ya bari yaji ƙarshen abun da zai ce ba.
"Girgiza kai Yarima Asad yayi tare da sake rumtse ido ransa na ƙara ɓaci, domin kuwa aduk duniya idan da akwai wani abu da yafi tsana to ya biyo bayan tsawa da takura, hakan yasa lokaci ɗaya yaji gaba ɗaya tafiyar ta gama fuce masa arai, tayarce har ya ƙudiri aniyar cewa muddin ya koma to wallahi babu abun da zai sanya sa ya dawo, domin kuwa bazai taɓa sanya barguna ajikin sa ba, sai dai komai zai faru ya faru.
Yayin da shi kuma Babban Yaya ya buɗe murfin motar dake gaban sa yana mai shigewa ya zauna ransa na tsantsar ɓaci.
Sai da ya ɗauki kimanin minti biyu daga tsayen da yake rumtse da idanuwan sa, tukun daga bisani ya buɗe su gaba ɗaya har launin su ya fara sauyawa daga fari zuwa ja, kana ya juya yana mai dosar hanyar da suka biyo suka zo daniyyar ko yaje bazai dawo ba wallahi.
Acikin mota kuwa cikin tsantsar takaicin hallayar ƙanin nasa da yake ji aƙasan ransa ya lumshe idanuwan sa, yana mai jingina da jikin kujerar tare da ɗaga kansa sama, kafin daga bisani kuma ya miƙe zumbur yana mai gyara zaman sa akan kujerar, sabo da tino wasu daga cikin shawar-warin Sheikh Ahmad da yayi da yake cewa muddin yana son buƙatar sa ta biya ta ɗora ƙanin nasa akan hanyar dai dai, to dole sai yana binsa ahankali, domin kuwa idan har yace zai masa ta zafi ko kuma yace zai na cewa yayi komai kai tsaye, to bazai taɓa samun yarce yake so ba, face shaƙuwar dake tsakanin su ma ta samu tangarɗa, dan haka muddin yana son yay abun da yake so, to dole sai yana jan sa ajiki tare da lallaɓa sa.
Hakan da ya tina ne kuwa ya sanya sa miƙewa zumbur daga kishingiɗen da yake jikin kujera, tukun daga bisani ya miƙa hannu yana mai janyo wayar sa da take ajiye agefen sa, sannan ya shiga contacts yana mai nemo number ƙanin nasa da ya rubuta My Asad ajiki da ɓaro-ɓaron baki ya doka masa kira, tare da karata akan kunnen sa.
Aɓangaren Asad kuwa yana shirin shiga cikin apartment ɗin nasu yaji sautin wayar sa dake riƙe ahannun sa.
Bai ɗago ta ba balle ya kalle ta har tai ringing ɗin ta ta gama tas.
Ko minti ɗaya batai da katsewa ba sai ga wani kiran nan ya sake shigowa.
Mtswwww! Yaja wani dogon tsaki yana mai dakatawa awurin da yake tare da lumshe idanuwan sa, tukun daga bisani ya warasa yana mai ɗago hannun sa yakai idanuwan sa kan wayar tasa.
BIG BROS
Shine sunan da ya gani yana yawo akan screen ɗin wayar ɓaro-ɓaro da manyan baki.
"What againe kuma?" Ya faɗa yana mai taune lowar lips ɗin sa tare da yamutsa fuska, tukun daga bisani yay pickin ɗin call ɗin lokacin da yake dab da katsewa yana mai kai ta kan kunnen sa.
Shiru yayi ba tare da yace komai ba, sai faman hanci da yake hurawa kawai.
Yayin da acan ɓangaren Babban Yaya kuma yayi gyaran murya yana mai yin shiru ba tare da yace komai ba shima.
Sun ɗauki kimanin mintina biyu ahaka sai sautin futar numfashin junan su da suke ji kawai, tukun daga bisani shi Babban Yaya ya buɗe baki cikin sanyin murya yana mai faɗin. "Ƙanina." Kana yay shiru ba tare da ya ƙara furta komai ba.
"Uhm!" Kawai Asad ya faɗa ba tare da yace ƙala ba.
Murmushi Babban Yaya yayi daga can ɓarin da yake sabo da fahimta da yay ƙanin nasa na fushi da shi ne, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Kana ina ne ƙani na?"
"Cikin ɗaki." Ya faɗa acan ƙasan maƙoshi tayarce shi kansa Babban Yaya sai da ƙyar ya iya jiyo sautin furucin nasa.
"Ka cire kayan naka ne?" Ya sake faɗa agajarce har lokacin muryar sa ɗauke da murmushi.
"A'a." Yarima Asad ya faɗa still daga can ƙasan maƙoshi.
"To kawai kabar abun ka basai kacanza ba, nima sai bayan ka tafi naga ne ba ƙaramun kyau kayi ahakan ba, dan haka yanzu kayi sauri katawo mutafi kai kaɗai muke jira." Baban Yaya ya faɗa ahankali muryar sa ɗauke da murmushi har lokacin.
Yayin da shi kuma Yarima Asad yayi wani irin haɗ..................✍
*SAI DA NA GAMA TYPPING ƊIN 6K WORDS (READ MORE GOMA) INA EDITING DUKA YA GOGE, SO KUYI HAƘURI DA WANNAN KUYI MANAGE, INSHA ALLAH IDAN NA SAMU LOKACI ZA KUGA PAGE 9 ZUWA DARE.* 😭
🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹
_*NA*_
UMAR FARUQ*D*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
*FREE PAGE 09*
Haɗe rai yana mai ɗaukar tafin hannun sa ya kaisa kan goshin sa ya dafe sa tare da rumtse idanuwan sa da ƙarfi, yana mai jin takaicin kiran sa da yayan nasa yayi, tukun daga bisani ya buɗe idanuwan nasa yana mai juyawa ya koma hanyar da ya biyo.
Yana ƙarasawa wurin da suke, suka buɗe murafan wata haɗaɗɗiyar mota ba wacce Babban Yaya yake aciki ba shi da al'amin suna masu zama daga gidan baya.
Tukun matuƙan motocin sukayi musu key suna masu ɗaukar hanyar da zata futar dasu daga cikin masarautar.
Ƙarasawar su bakin get yayi dai dai da isowar motocin Gwamnan Wasai tare da tawagar sa, ba tare da sun tsaya sauraran junan su ba bare su gaisa ko wanne yayi gaba, su suka shilla zuwa kan titi, yayin da motocin da gwaman da ƴan rakiyar sa suke aciki su kuma suka hulla kan motocin su zuwa cikin masarautar.
*JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FULƊE*
Tun daga lokacin da tayi arba da fuskar Yariman Yamma take cikin baƙin ciki tare da ƙunci, tayarce har takasa sanya komai acikin ta, domin kuwa ko alamun yunwa bataji ba balle har tayi ƙoƙarin cin abincin, duk da yarce aka jere mata su kala kala agaban ta kuwa, sabo da tsantsar baƙin cikin da take ciki.
Babu abun da yafi ƙona mata rai da sanyawa ta sake jin ta tsanar sa fiye da kowa, sai irin kalaman da ya dinga faɗa mata na cewar ita ɗin tasace.
Koda ta kwanta bacci cikin dare mafarki tayi wai gata kan saman wani tafkeken dutse. Yayin da ƙasan dutsen kuma ya zamto zagaye da wani farin ruwa mai matuƙar girma da haske, sai daga can gaban ruwan kuma ta dinga jiyo wani irin sautin busa mai tsantsar daɗi da kwanciya arai yana tashi.
Hakan yasa tai ta shawagi akan dutsen fuskar ta ɗauke da murumushi, yayin da idanuwan ta kuma suka kasance kafe akan ruwan nan tana mai tinanin ta hanyar da zatabi ta tsallake sa, domin ta ƙarasa wurin da daddaɗan sautin da ke dukan kunnen ta yake.
Sanye take da kayan fulani bana sarauta ba yau, wato irin waƴan da kowa ke sanyawa farare ajikin ta, yayin da kanta kuma ya kasance ɗauke da wasu manya manyan kitso guda biyu ƙwal akai, sai sandar gadon ta ta tsafi da take riƙe ahannun ta tana mai cigaba da juyi asaman dutsen nan.
Babu abunda yafi mata daɗi awurin sai yarce wata irin sassanyar iska mai matuƙar daɗi take tashi tana dukan jikin ta awurin, ga kuma ƙamshin korayen ciyayin da suke dashe agefen dutsen, waƴan da suka ƙara sanya ta cikin shauƙi.
Ta ɗauki kimanin daƙiƙa kusan talatin asaman dutsen tana mai neman hanyar da zata sauka daga kansa, domin tabi ta cikin ruwan nan ta ƙarasa wurin da take jiyo sautin busar, amma bata samu ba.
Lokaci ɗaya yanayin ta ya fara sauyawa, gaba ɗaya jikin ta ya farayin sanyi, sabo da rasa hanyar da zatabi ta sauka daga kan dutsen da tayi, sai can taga wasu kyawawan tsuntsaye guda biyo sun tawo aguje suna masu zuwa suka gogi gefen fuskar ta da fuka-fukan su, tukun daga bisani suka ƙara yin gaba suna masu tsayawa asaitin fuskar ta tare da karɗada jelinan su.
Wani irin murmushi ne ya suɓuce mata take awurin, sabo da ganin tsuntsayen nan da tayi, tukun daga bisani ta gayara tsayuwar ta awurin tana mai ɗaukar sandar dake riƙe ahannun ta ta maƙale ta akan ƙafadar ta, sannan ta buɗe baki cikin tsantsar shauƙi tana mai faɗin. "Barkan ku da zuwa gareni masoya na." Ta faɗa tana mai sakin murmushi tare da lumshe kyawawan idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai ɗorawa da cewa. "Dama ni nasan bazaku taɓa barina cikin wani hali ba, duk inda mafuta take zaku samo mun ita Shale am, dan haka idan kun shirya nima na shirya, muje ku nuna mun hanyar da zata kaini wurin wancan daddaɗan sautin."
Ta faɗa tana mai sake gyara tsayuwar ta tana kallon su tare da sakin murmushi, yayin da suma ɗin suka juyo ɓarin da take suna masu shawagi akan ta tare da sakin kuka, alamun suna amsa batun ta kenan, tukun daga bisani suka juya atare suna masu dosar wata hanya dake akan dutsen.
Bin su itama tayi abaya cikin takun ta wanda shi kaɗai ke ɗaukar hankulan jama'u akan ta.
Wata hanya suka ɓulla da ita akan dutsen wacce ta kasan ce gangare ce, tukun suka sauka daga sama suna masu sauka akan dutsen, suka fara ɗan tsallawa da ƙafafuwan su suna masu sauka daga kan dutsen.
Binsu itama tayi abaya idanuwan ta ƙur akan hanyar da take jiyo sautin busar nan cikin tsantsar farin ciki, ahaka har suka sauka daga kan tafkeken dutsen nan dukan su suna masu tsayuwa agaban makeken ruwan nan, tukun daga bisani tsuntsayen suka ƙara tashi sama suna masu dawowa dai dai saitin fuskar ta, sanann suka karkaɗa mata jelolin su tare da shafar gefen fuskar ta da fuka fukan su.
"Shin ina kuma zaku tafi kubarni ba tare da kun nuna mun hanyar da zanbi in tsallaka wannan ruwan ba." Ta faɗa tana mai marai-raice fuska idanuwan ta akan su.
Cigaba da zagaya ta sukayi suna masu sakin ɗan kuka, tukun daga bisani suka tashi sama gaba ɗayan su atare suna masu yin gaba suka barta awurin.
Lumshe idanuwan ta tayi tana mai shaƙar sassanyar iskar dake wurin, tare da ƙamshin turare.
Ta ɗauki kimanin mintina biyu ahaka, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan ta fuskar ta ɗauke da tsantsar murmushi, sabo da tinawa da tayi da Birbillon ta (malam buda mana littafi)
Hakan yasa ta juyawa da sauri tana mai dosar wurin da wasu korayen ciyayi suke dashe agafen ruwna nan, fuskar ta ɗauke da murmushi, yayin da har lokacin hannun ta yake riƙe da sandar nan ta.
Durƙusawa tayi aƙasa gaban furannin bayan ta aje sandar ta agefen ta, tukun ta lumshe idanuwanta tana mai kai tafin hannun ta ta bugi korayen ciyayin nan da shi, tukun ta buɗe tafin hannun tana mai ɗora sa akan ciyayin.
Take wasu irin kyawawan malam buɗa mana littafi kala-kala suka taso suna masu yin shawagi adai dai saitin fuskar ta, tukun sai su koma su haye kan tafin hannun ta.
Ahakan har sai da suka cika duka tafukan hannayen ta biyu da ta buɗe, tukun daga bisani ta wara fararen idanuwan ta masu ɗauke da blue black ɗin ƙwayar ido akan su.
Miƙewa tsaye tayi cikin tsantsar farin ciki tana mai sakin dariya, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Barkan ku da zuwa Birbillo am masoya na." Ta faɗa tana mai cigaba da sakin dariya, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Shin ta wata hanyar kuke ganin zanbi domin na tsallake ruwan nan?" Ta ƙarasa maganar tana mai tsayawa awuri ɗaya tare da zuba idanuwan ta akan su.
Rufe bakin ta keda wuya gaba ɗayan su suka tashi daga kan tafukan hannuwan nata suna masu komawa kan sandar ta da take ajiye agefe, tukun suka ƙara tashi daga kan sandar suna masu tafiya zuwa saitin ruwan nan sukayi kamar zasu nutsa cikin sa, sannan suka sake juyawa suna masu sake hayewa kan tafukan hannuwan ta.
"Godiya nake masoya na, bada ban kuba da bansan yacce zanyi in tsallaka ruwan nan ba." Ta faɗa tana mai sakin murmushi, tukun ta daga bisani ɗora da cewar. "To sai da anjiman ku masoya na, ni zan ƙarasa wurin Gidado am."
Tashi sukayi dukan su suna masu komawa cikin ciyayin nan, yayin da ita kuma ta durƙusa ƙasa tana mai sa hannu ta ɗauki sandar ta dake ajiye aƙasa, tukun ta ɗago ta tana mai riƙe ta ahannun ta, ta miƙar da ita tare da zuba mata idanuwan ta, kana daga bisani kuma ta buɗe baki tana mai faɗin. "Na dogara dake sandar gado ta, dan haka ina fatan bazaki bani kunya ba, kamar yacce akace ba zaki taɓa bani kunya ba arayuwa, zaki kaini zuwa ga Giɗaɗo am." Sannan ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar bakin ruwan nan gada-gadan.
Tana zuwa gaban sa ta sake dunƙule sandar nan tata da matuƙar ƙarfi acikin tafin hannun ta, tukun ta ɗaga ta tana mai buga ta acikin ruwan nan da matuƙar ƙarfi.
Take kuwa ruwan ya dare gida biyu gaba ɗayan sa. Yayin da ta sake jiyo sautin busar nan da matuƙar ƙarfi na cigaba da dukan kunnen ta.
Ba tare da ta tsaya wata -wata ba ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar hanyar da take atsakiyar ruwa kai tsaye.
Sai da tai tafiya mai ɗan tsawo, tukun ta fuce daga cikin ruwan, kana hanyar ta koma ta haɗe gaba ɗayan ta ta zama ruwa kamar da.
Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal tayi tsaye a'inda take tare da buɗe kunnuwa tana mai sauraran sautin busar nan, dan ta fahimci ta inda yake futowa.
Murmushi ta saki tana mai lumshe idanuwan ta, tukun daga bisani ta warasu tana mai fara ɗaga ƙafafuwan ta ta doshi hanyar da take tinanin anan zata tarar da mai busar nan.
Miƙaƙƙar hanyace mai ɗauke da farin yashi mai matuƙar laushi akan ta, cigaba da tafiya tayi har ta ɓulla zuwa wani ƙaton fili mai ɗauke da duwar-watsu tare da da ƙananan ruwaye zagaye da shi.
Zagaye ta farayi aɗan rukunin wurin da take tana mai wara idanuwan ta, domin ta hango ta inda mai busar yake.
Tsaye ta hange sa acan bayan wani dutse ya juya baya yana mai karkaɗa kai, tare da cigaba da sakin busar sa da take jin daɗin ta na ratsa har cikin kwanyar ta.
Lumshe idanuwan ta tayi awurin da take tana mai sakin murmushi, tukun daga bisani ta sake buɗe su akan bayan sa, kana ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar wurin da yake.
Tsaye tayi abayan sa tana mai jin wani irin shauƙi na ɗibar ta. Yayin da shi kuma yake cigaba da sakin busar sa hankali kwance ba tare da yasan da tsayuwar ta ba awurin ma.
Gyara tsayuwar ta ta sake yi awurin tana mai ɗora sandar ta akan kafaɗar ta, tukun daga bisani ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 76