Share this page
tayi gam acikin hannun, tukun ta miƙar da ita tana mai nuna ɗakin da huƙar, kana daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Gargabiluuu." Ahankali ƙofar ta fara rufewa har ta rufe gaba ɗayan ta, sannan ta ƙara miƙar da hannun ta gefe shi kuma wannan badakaran ya miƙa hannu ya ɗauki takobin. Tashi yayi ya koma inda yake da baya da baya kamar yacce yazo. Juyi tayi cikin zafin nama ba tare da ta kalli kowa acikin su ba, har lokacin bata bar sakin huci ba tana mai kallon hanyar da suka biyo sukazo wurin. Dasauri waƴan nan ƴammatan bayin suka mimmiƙe daga durƙushen da suke suna masu kama wasu sashika daga jikin rigar dake sanye ajikin ta, sannan ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar hanyar da suka biyo sukazo cikin sauri. Gaba ɗaya suma dakarun nata rufa mata baya sukai cikin sauri suna binta. *ƘASAR HAUSA CIKIN MASARAUTAR WASAI* Tun daga bakin masarautar mutum zai fahimci yau ɗin ana wani gagarumin bikin ne aciki basai an faɗa masa ba. Sabo da yarce sautin kaɗe-kaɗe da bushe-bushen algaitu, sarewa, kakaki, tambura, kalangu, harma da kiɗin ƙwarya ke tashi awurare daban daban acikin masarautar, ga kuma yarce jama'a keta kai kawo, wasu asaman doki, wasu akan motocin su, yayin da wasu kuma suke tafe akan ƙafafuwan su. Ko ina ka kalla hadimai ne da sarakai kawai suke giftawa kowanne da kalar shigar dake sanye ajikin sa. Tsaya yake gaban tamfatsetsen mudubin dake manne jikin bangon ɗakin wankan nasa yana mai kallon fuskar sa ta cikin sa. Ɗaure yake da towel aƙugun sa bako riga jikin sa, yayin da hannun sa kuma ya kasance riƙe da wani ɗan ƙaramin towel ɗin yana tsane lallausar sumar dake kwance akansa tana ɗigar ruwa. Ya ɗauki kimanin minti goma tsaye gaban mirrown yana kallon kansa, tare da cigaba da tsane sassan jikin sa da towel ɗin dake ɗauke ahannun sa ba tare da ya gama ba. Ahankali ya juya bayan sa yana mai kai fararen ƙwayoyin idanuwan sa kan ƙofar bathroom ɗin, sabo da yarce sautin noking keta tashi ta yarce har ya fara takura masa, domin kuwa an ɗauki tsayin minti huɗu ana yin sa kenan. Mtseww! Yaja ɗan ƙaramin tsaki yana mai yamutsa fuska, tukun daga bisani ya janye idanuwan sa daga kan ƙofar ba tare da ya tankawa mai ƙwan-ƙwasowar ba, sai ma juyawa da yayi yana mai zuwa ya ya saƙale ɗan ƙaramin towel ɗin dake riƙe ahannun sa ajikin ƙarfen saƙale kaya, kana ya juya yana mai komawa ɗayan ɓarin inda wata azababbar wadrobe mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali ke manne ajikin bango take, ya tsaya gaban ta yana kallon ta, tukun daga bisani ya lumshe fararen idanuwan sa, kana ya buɗe su yana mai saka zara-zaran yatsun hannun sa masu ɗauke da kwantaccen gashi akan su, ya dire su akan murƙar jikin wadrobe ɗin, kana ya bude ta. Gida ukku wadrobe ɗin ta kasu. Gida na farko gaba ɗayan sa ɗauke yake da designers bathroob jere aciki kala-kala masu masutuƙar kyau, sai gida na biyu kuma jere yake da designers boxers da singlet gaba ɗayan su sababbi fidigil suma, sai kuma side na ƙarshe da ya kasance ɗauke da haɗaɗɗar loka mai zaman kanta, wacce take ɗauke da haɗaɗɗen murfin roba fari ƙal da aka ƙawata sa da zanen flower's akan sa. Sake kai yatsun sa yayi kan murfin lokar yana mai buɗe ta. Gaba ɗayan ta cike take da tooth brush sababbi fidigil acikin kwalayen su tare da maclean masu matuƙar tsada. Hannu yasa ya ɗauki brush ɗaya tare da maclean, tukun ya maida locar ya rufe, kana ya mai da murfin wadrobe ɗin ya rufe ta duka, sannan ya juya yana mai yin wurin wani haɗaɗɗen sink bathroom da yake manne akan canter yana facing ɗin wadrobe ɗin nan, yana tafiya yana yage kwalin brush din dake ɗauke ahannun sa. Cilla kwalin brush ɗin yayi cikin dustbin ɗin da yake ajiye awuri ɗaya daga can gefe, tukun ya buɗe sabon maclean ɗin da ya ɗauko ya matsa sa ajikin brush ɗin, kana ya ƙarasa yana mai sa hannu ya kunna tap ɗin da yake manne jikin sink ɗin bayan ya aje maclean ɗin gefe. Ya dauki kimanin minti shida zuwa bakwai akan brush ɗin kawai yana ta dirzar haƙwara yarce kasan wanda zai canza su, tukun daga ƙarshe yasa ruwa ya ɗauraye bakin sa da shi, sannan ya juya ɓarin da kwandon sharar nan yake yana mai cilla brush ɗin da ya gama amfani da shi aciki, tukun ya juya yana mai dosar ƙofar da zata futar dashi daga cikin toilet ɗin wacce ake ta faman ƙwan-ƙwasawa tun ɗazu, cikin takun sa na tsantsar isa da izza, wanda yake nuni da shi ɗin cikakken jinin sarauta ne. Ɗan gajeran tsaki ya sake ja yana mai ɗan cije lower lips ɗin sa ahankali, tukun daga bisani ya ɗora hannun sa akan jamlock ɗin jikin ƙofar yana mai murɗa sa ta buɗe. Tunda yaji motsin sa abakin ƙofar yana shirin futowa ya ɗaure fuska, kana ya ture sistem ɗin dake ɗauke akan cinyar sa yana opereting ɗin ta zuwa kan kujera, tukun ya kafe ƙofar da kallo yana mai jiran futowar sa. Koda ya futo daga bathroom ɗin inda yake bai kalla ba ya doshi bakin dressing mirrow, kai bakace yasan da wanzuwar mutum ba ma acikin ɗakin, sabo da yarce bai ko kalli kujerar da yake zaune akai ba balle har ya tambaye sa yaji dalilin da yasa yake ƙwan-ƙwan sa masa ƙofa. Yana ƙarasawa gaban mirrow yaja kujera ya zauna akai, tukun ya sanya hannu yana mai janyo haɗaɗɗen man da yake shafawa, wacce robar sa kaɗai ma abar kallo ce, ya fara matsar sa atafin hannun sa yana murza sa, sannan ya shafe akan lallausar fatar jikin sa, wacce take lulluɓe da kwantaccen baƙin gashi akan ta hankali kwance. Ƙwafa saurayin dake zaune akan kujera ya buga da ƙarfi, cikin jin haushin yarce abokin nasa ya nuna halin ko inkula dashi da yay, bayan yasan tun ɗazu shi yake ta zaman jira acikin ɗakin, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amma dai gaskiya guy baka da mutunci ko kaɗan wallahi, wato tsabar iskanci tun ɗazu ina nan zaune ina zaman jiran ka, amma ka futo shine ko darajar kallo ma bazan samu daga gare kaba balle harka tanka mun ko?" Ya ƙarashe maganar yana mai sake buga ƙwafa tare da buga masa harara ta cikin mirrow, duk da dai shi har yanzu bai nuna yasan da shi bama. Inda yake bai ɗago ya kalla ba balle harya samu ya tanka masa, cikin kwanciyar hankali ya cigaba da shafa mai asassan jikin sa ba tare da ya juyo ba. Sai da ya gama mutssike ko ina na jikin sa da mayukan, sannan ya janyo body spray ya shafe ko wanne lungu da saƙo na jikin sa da shi, tukun ya mai dasu ya aje akan mirrown kamar yacce suke tun farko, kama ya miƙe daga kan kujerar da yake azaune yana mai juyawa ya doshi bakin tamfatsetsen royal bed ɗin da yake kwance atsakiyar ɗakin mai tsananin kyau, har kuma lokacin bai juya ya kalli wurin saurayin nan ba balle ya kula sa. "Please ASAD kayiwa Allah kai maza ka shirya, ko mayi mu ƙarasa cikin fadar nan muma, dan nasan yanzu duk kowa na can mu kaɗai ne bamu ƙarasa ba." Cewar matashin saurayin nan yana mai kallon Yarima Asad, tare da haɗe tafukan hannuwan sa wuri ɗaya alamun roƙo, domin ko yasan har dai ba lallaɓa sa yayi ba to bazai taɓa yin sauri ya shirya ba kamar yacce idan zai kwana yana masifa bazai nuna yasan yana wurin ba balle ya tanka mai. "Kash!" Yarima Asad ya faɗa yana mai yamutsa fuska tare da dago idanuwan sa ya watsa su akan fuskar abokin nasa, tukun daga bisani ya ɗaga laɓɓan sa cikin muryar sa wacce har dai ba mugun nutsuwa kayi ba ka saurare sa ba zaka taɓa jin abun da yake faɗe ba yana mai cewa. "Uhmm Al'AMIN kake da suna kowa ma? Shi wai na tsare ka ne anan ɗin, ko kuwa nace maka kajira ni ne da zaka tsaya kana mun ihu acikin kunnuwa tun ɗazu." Ya faɗa yana mai janye idanuwan sa daga kan fuskar sa, tukun ya cigaba da dosar bakin bed ɗin nan inda ya hango kaya ajiye awurin, alamun Abokin nasa ne ya zaɓo masa su amatsayin waƴan da zai sanya. "Ɗan iska mara mutunci, haka ma zakace kenna ko?" Abokin nasa ya faɗa yana mai ɗaure fuska takaici fal ransa. Ko kallon sa Yarima Asad bai ba ya ƙara sa bakin bed ɗin yana mai bin kayan da ya gani ajiye akai da idanuwa. Tattausan farin yadi ne ƙal mai matuƙar kyau, wanda yake ɗauke da irin aikin da ake yiwa rigunan sarakai da baƙin zare mai matuƙar kyau, kai ko baka san kaya ba idan ka kalli wannan yadin tare da aikin dake manne ajikin gaban rigar sa zaka san ba ƙananan kuɗi aka ɓatar ba kafun asamar da shi, agefen yadin kuma wata azababbar alkyabba ce fara mai matukar kyau da ɗaukar idanu, sai baƙin takalmi sandal tare da baƙar hula wacce take ɗauke da sirkin farin zare ajikin ta, waƴan da suma basai an faɗa maka ba kana kallon su zaka san bana ƙananan mutane bane, bayan su kuma sai farin rawani da yake ajiye agefe gaba ɗayan su anjere su akan gadon ne gwanin sha'awa da su. Wani irin matsiyacin kallo Yarima Asad ya dinga bin kayan da shi yana mai yaƙuna fuska yarce kasan wanda yaga kashi, tukun daga baya ya ɗago kai yana mai watsa idanuwan sa ɓarin da Al'amin yake zaune, wanda shima ɗin shi yake kallo yana mai addu'a Allah yasa ya sanya kayan nan acikin ransa. Danna lower lips ɗin sa yayi cikin baki yana mai taune sa da haƙora tare da lumshe idanuwa, tukun daga bisani ya wara su akan fuskar Al'amin yana mai buɗe baki yace. "Ina fatan dai ba wai ka ajiye waƴan nan shirgin bane anan wurin, da nufin nine zan sanya su ajiki na ko?" Ya faɗa yana mai sake yamutsa fuska tare da mai da idanuwan sa ya sake lumashe su. "Dan Allah Yarima Asad ka daure yau kaɗai ka taimaka kasanya kayan nan muje fada please." Al'amin ya faɗa yana mai haɗe tafukan hannuwan sa wuri ɗaya tare da kallon fuskar Yarima Asad a marai-raice. "Uhm! Amma gaskiya ina ganin da alamu kafara samun taɓin hankali ne guy, imagin ni Asad kake cewa in sanya waƴan nan kayan, ni, ni Asad zan sanya waƴan nan blankets ɗin ajiki na. Tirr god forbid." Ya faɗa yana mai sake juyawa ɓarin da kayan suke ya watsa musu wani matsiyacin kallo. "Haba Asad, koda baka son irin waƴan nan kayan bai kamata ace a irin rana tayau da ake bikin naɗa babban Yaya Ciroman gida ka ƙisu, domin ko kasan duk masarautar nan babu mai maka irin son da yake ma ko? Dan haka ni a gani na ya kama ta ace wannan ce irin shigar da zakayi ayau kaɗai domin ka taya masoyin ka farin ciki." Al'amin ya fada cikin sanyi yana mai fatan Allah yasa Yarima Asad ya fahimce sa yasan ya kayan nan acikin ransa. Mtswww!!! Yarima Asad yaja dogon tsaki yana mai wucewa gaban wadrobe ba tare da ya sake tankawa Al'amin ba. Buɗe wadrobe ɗin yayi yana mai zaro wani black creazy jeans, tare da farar long sleev t shirt sababbi gadagal ya aje akan bed ɗin, tukun ya sake sa hannu ya zaro wani farin ƙyalle mai kama da hirami yana mai diresa akan bed ɗin shima, kana ya rufe nan yana mai juyawa zuwa inda wata ƴar ƙaramar loka take manne ajikin bango ya buɗe ta. Wasu irin azababbun agoguna ne masu matuƙar kyau da sarƙoƙin huya suka bayyan aciki, hannu ya sanya ya ɗakko wani baƙin agogo tare da sarƙa mai matuƙar ƙyalli aciki, tukun ya mai da lokar ya rufe ta, kana ya juya zuwa inda kayan suke ba tare da ya sake ɗaga kai ya kalli Al'amin ba yana mai ware su ya fara sanya su ajikin sa. Cikin mintinan da basu huce biyar ba duka ya sanya creazy jens ɗin tare da farar rigar da tayi matuƙar kama jikin sa, tayarce har ta bayanna hallitar ƙarfin sa, domin kuwa ko singlet bai sanya aciki ba zallar rigar kawai ya ɗora. Ɗaukar hiramin nan yayi yana mai ware sa ahannun sa, tukun daga bisani ya lanƙwasa sa yana mai nin kasa gida biyu, kana ya ɗago sa yana mai dire sa akan sa ya haɗa da kunnuwan sa ya ɗaure sumar tas, wato dai ya ɗaure kan yarce kasan ɗan kwali, kana ya sake buɗe wata loka yana mai janyo wasu sababbin fararen boot masu matuƙar kyau da girma ya sanya fararen ƙafafuwan sa acikin su, kana ya ɗago yana mai hucewa gaban mirrow hannun sa riƙe da silin sarƙar nan. Buɗe bakin ta yayi, tukun ya ɗora ta akan huyan sa, kana ya maida bakin nata ya haɗe, sannan ya sake ɗaukar parforms ya feshe ko ina na jikin sa da su, tukun ya juya ɓarin da Al'amin yake zaune sake da baki yana mai karkace kai, tare da ƙanƙantar da idanuwa akan sa yana kallon sa. Farine ƙal yarce kasan ataɓa sa jini ya ɓullo, faffaɗa ne mai matuƙar tsayi da kauri dai dai misali, yana da doguwar fuska wacce take ɗauke da siririn dogon hanci tare da ɗan ƙaramin baki akan ta, sai fararen idanuwan sa da suka kasan ce su ba manya can ba, sannan kuma su ba ƙanana ba, yayin da gefe da gefen fuskar tasa kuma take ɗauke da kwantaccen baƙin gashi da yabi har ta tsakan-kanin saman bakin sa zuwa haɓar sa, mai matuƙar taushi da yayi matuƙar ƙara haska ka fuskar tasa, sosai sajen nasa yasha gyara yay gwanin ban sha'awa, kai kana ganin sa kasan ba ƙaramun ji yake da sajen ba, sabo da yarce yake futar da wani irin walwali da sheƙi akan fuskar tasa. Cikin tsantsar ɓacin rai Al'amin ya buɗe baki yana mai faɗin. "Am............✍ *FOLLOW ME ON WATPPAD @umarfaruqD pls.* *#COMMENTS* *#VOTE AND SHARE FISABILALLAH* 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 02* "Amma kai da kanka kasan hakan da kai bai dace ba ko Asad, domin ko hatta mai martaba idan ya ganka acikin wannan shigar arana irin tayau wacce sarakunan garuruwa da dama suka halarci gidan nan kasan ransa ba ƙaramun ɓaci zai yi ba ko, ina ma laifin ace kasanya iyakar manyan kayan basai kasa alkyabbar ba, in yaso bayan an gama shagali sai kazo kacire su ka maida irin wanda kake so ko." Al'amin ya ƙarashe maganar cikin sanyi kamar bashi ne ya fara ta cikin fushi ba, domin ko yasan har dai bata lallami yabi Abokin nasa ba to ko kallo ma bai ishesa ba balle har yayi amfani da abun da yake faɗe . Kallon sa Yarin Asad ya cigaba dayi har sai da ya bari ya kai ƙarshen maganar sa, tukun ya ɗan taɓe baki yana mai juyawa ya doshi bakin bed ba tare da ya tanka masa ba. Nannauyar ajiyar zuciya Al'amin ya sauke yana mai sakin murmushi, sabo da yarce yaga Yarima Asad ya nufi inda waƴan can kayan suke, amma sai dai ko gama murmushin nasa bai ba ya koma ya ɗinke fuska yana mai bin Asad da ido, sabo da yarce yaga ya huce ta gaban kayan ko kallon su baiyi ba balle ya dauka ya sanya. Direct yayi saitin inda pillow'n sa yaka yana mai zuwa ya ɗauki makullin motar sa tare da wayar sa ƙirar iphone 13 pro max ya riƙe, tukun daga bisani ya juya yana mai dosar ƙofar da zata sadasa da waje ba tare da ya sake kallon inda Al'amin yake ba, yayin da shi kuma Al'amin har lokacin yake binsa da kallo yana mai jin-jina girman rainin hankalin Asad acikin ransa. Sai da yaje har bakin ƙofa tukun ya tsaya yana mai juyowa ya sake jifan kayan nan da kallon ƙas-ƙanci, tukun daga bisani ya janye ƙwayoyin idanuwan sa daga kansu yana mai -mai dasu kan kujerar da Al'amin yake zaune yana kallon sa baki sake shima. "Katabbatar ka kwashe waƴannan shirgin banzan naka kafun na dawo, and then idan ka gama abun da kake kana iya rufe mun ɗaki ka ƙara gaba." Ya faɗa yana mai juyawa ya sanya kai ya fuce ba tare da ya tsaya jin abun da Al'amin zai ce ba. "Kuttt, Amma wallahi sai kaci ubanka Asad, yanzu duk awannin dana ɓata ina jiran ka kagama shiryawa mutafi tare shine har zaka huce ka barni, to dan uwarka baza a kwashe kayan ba kayi duk abun da zakayi." Al'amin ya faɗa da ƙarfi yarce Asad ɗin zai jiyo sa yana mai miƙewa cikin jin haushin sa yabi bayan sa. "Barka da futowa yaya." Wasu kyawawan ƴammata da suke zaune akan haɗaɗɗun kujerun da suke jere acikin tamfatse-tsen fallon suka faɗa, suna masu kallon Yarima Asad da ya futo daga ɓarin sa. "Ina mamy take ne?" Ya faɗa idanuwan sa akan waya ba tare da ya amsa gaisuwar da sukai masa ba. Da sauri ɗaya daga cikin su ta buɗe baki tana mai cewa. "Mamy na part ɗin ta, amma bari baby taje ta kira maka ita." Ta ƙarashe maganar cikin wani irin salo wanda yake nuni da tayi hakan ne domin ya ɗago ya kalle ta, amma sai dai ko motsi bai canza ba daga kalar wanda yake yi balle har ya kallo tan, yayin da ita kuma wacce aka kira da baby ta miƙe tsaye da sauri tana mai faɗin. "Ok bara nayi sauri." "To yaya ga wuri kazauna mana, kafin mamy'n ta ƙaraso ko." Ta faɗa tana mai far-fara idanuwa tare da ɗan buɗa space akusa da inda take idanuwan ta akan fuskar sa. Taune lips ɗin sa na ƙasa yayi yana mai yamutsa fuska ba tare da yace tak ba, domin kuwa ita bata sani ba ba ƙaramun takura masa tayi ba da surutun da take tayi ma. Ba tare da ya ɗaga kai ya kalli ko kujerar da take zaune akai ba duk da yarce take ta faman gyara zama tana kwar-kwasa kala kala ya juya yana shirin fucewa daga cikin falon, akuma lokacin ne Al'amin ya ƙaraso falon yana ta faman masifa. Baice ƙala ba duk da yaji abun da Al'amin ke faɗa, sai ma taɓe baki da yayi yana mai cigaba da tafiyar sa hankali kwance. Yana fucewa daga cikin part ɗin nasu ya tsaya cak abakin ƙofa, yana mai kallon yarce jama'a keta hucewa cikin irin banzar shigar da Al'amin ya aje masa da sunan yasa ta shima. Tsaye yay awurin yana mai ƙan-ƙantar da idanuwan sa tare da kar-katar da kai yana mai bin duk masu hucewa da kallo, yi yake yana taɓe baki tare da yamutsa fuska, ji yay gaba ɗaya bazai iya zama acikin gidan ba idan har baza'a dena waƴan nan kaɗaɗen ƙauyen cin da ake yi ba, domin ko shi ba ƙaramun takura masa sukayi ba, gaba ɗaya bai ɗauki irin waƴan nan bushe bushen ba amatsayin abubuwan nishaɗi, sai zallar gida danci da rashin waye wa kawai yake gani. "Kai yanzu dan Allah mutanen nan da suke hucewa cikin shigar nan basu burge kaba?" Al'amin ya faɗa alokacin da ya ƙaraso wurin yana kallon sa. Uhm! Yace kawai yana mai yin parkin space. Da sauri zagagen da suke tsai-tsaye a area wurin suka taso suna masuyo kan su. Tun daga nesa suka fara faɗin. "Barka da futowa ɗan sarki jikan sarki, takawar ka lafiya bujimin maza, takawar ka lafiya jinin mulki, gaba salamun baya salamun Asadullahi ikon Allah, ɗa ga sarki Abdallah, shalele wurin sarauniya kuma gimbiyar matan hausa, jika ga sarki Ahmadu ƙani ga ciroma uban.... Cak suka tsaya a'inda suke suna masuyin shiru dukan su, sabo da yarce ya ɗaga musu hannu sama yana mai dakatar dasu, ba tare da ya waigo ya kalli ko mutum ɗaya daga cikin su ba. Juyawa suka farayi suna masu komawa wuraren da suke, yayin da shi kuma ya cigaba da takawa cikin takusan sa da shi kaɗai ke hautsina ƙwaƙwalen ƴan mata su muto akan sa, yana mai dosar inda wata azababbar farar mota take, wacce take ɗauke da number mai suna YARIMA ASAD 08 sabuwa fidigil da ita. Tun daga nesa ya sanye remote ya buɗe ta, shi yasa yana ƙarasawa wurin ya sanya hannu ya buɗe murfin yana mai shigewa ciki ya zauna akujerar direba. Da sauri shima Al'amin ya ƙaraso wurin yana mai buɗe murfin ya shiga. Lumshe ido Yarima Asad yayi yana mai ɗora tafukan hannayen sa akan stiyarin motar bayan yayi mata key. "Wai yana ga kayo nan ne Asad, bayan kuma kasan fada zamuje ko?" Al'amin ya faɗa yana kallon fuskar sa. Ƙala bai ce masa ba sai ma buɗe idanuwan sa da yayi yana mai janyo wayar sa ƙirar iphone 13 pro max ya fara shafawa. "Da kai fa nake Asad kamun banza." "To kai ɗin ubane ne da bazan ma banza ba, ko kuwa na maka dole ne akan sai ka biyo ni inda zani." Ya faɗa ƙasa ƙasa yana mai cigaba da danna wayar sa ba tare da ya ɗago ya kalle sa ba. "Me kake nufi da hakan? Idan na fahimta kamar kana so kace ba fada mukai daga nan ba ko?" "Kai ka juyo kuma." Yarima Asad ya faɗa yana mai danna giyar motar bayan ya rufe motar gam. Da wani irin mahaukacin ƙarfi ya take ta yana mai lailaya kanta atsakan-kanin wurin da suke ya juya ta. Tukun ya ɗebe ta atamanin yana mai ɗauke hanyar da zata sada sa da main get, ko mutanen da suke faman kai kawo aharabar gidan nasu bai lura dasu ba. "Wai dallacan Asad me kake shirin yi haka ne?" Al'amin ya faɗa cikin ƙaraji yana mai dukan kujerar motar ransa amatuƙar ɓace. Inda yake Asad bai ɗago ya kalla ba balle ya tanka masa, saima sake take motar da yayi ahaukace yana cigaba da dosar get ɗin da zai sada su da wajen gidan sarautar. "Kaga malam dallacan samu wuri ka sauke ni anan." Al'amin ya sake faɗa cikin fushi yana mai jin kamar ya mammake fuskar Yarima Asad tsabar takaici. "Ai kana iya buɗewa ka futa yanzu ma tunda ba ɗaure ka nayi ba, kuma da kake cewa na tsaya na sauke ka ai ina ce da ɗin bani na ɗora ka aciki ba ko?" Yarima Asad ya faɗa adai dai lokacin da ya shilla kan motar sa titi aguje. Gaba ɗaya mutanen dake abakin titi harma da waƴan da suke acikin motocin su bin motar Yarima Asad sukayi da idanu, manya banda zagin sa da shegan tasa babu abun da suke yi, yayin da matasa kuma keta faman kambaba sa suna faɗin guy ɗin na burge su, sabo da yarce yayi matuƙar iya hannun sa. Acan cikin mota kuwa Al'amin ne ya kalli Yarima Asad yana mai faɗin. "Amma Asad kai atinanin ka hakan da kayi ka kyautawa babban yaya kuwa?" Murmushi Yarima Asad yayi wanda yayi matuƙar ƙara masa kyau, tukun daga bisani ya lumshe idanuwan sa ko damuwa bai ba da cewar kan titi yake duk da uban gudun da yake kwara-rawa, kana ya wara su daga baya yana mai buɗe baki yace. "Shin wai dan Allah ni nace ka biyo ni ne guy, koka na buɗe baki nace Al'amin kar kaje fada kallon naɗi ne?" Ya faɗa yana mai sake sakin murmushi hankali kwance. Yayin da shi kuma Al'amin yayi matuƙar ƙulewa, sabo da yarce yaga shi ko ajikin sa bai damu bama. "Amma dai ai kasan ban san nan kayo ba da babu abun da zai sa inbar hawan da

Chapter 2 of 76