da ita da kanta tasan tsufan yazo mata.
*DUBAI*
Tun bayan komawar Asad da Al'amin ƙasar Dubai gaba ɗaya komai nasu ya sauya, domin kuwa ko ɗaki da aka tashi basu ko wanne guda ɗaya tafkeke aka basa, kamar yadda sauran yaran gidan suka kasance kowa acikin nasa ɗakin.
Yayin da aka zube musu ruwan kuɗi kuma suke duk yadda ransu yake so da su, ba tare da kwaba ko hantara ba.
Kwanan su biyu kacal da zuwa Alhaji abubakar ya ɗauke su ya kai su wata makarantar miliyoyin kuɗi da kansa.
Inda anan ɗin kuma suka haɗu da yaran manya irin su, kama daga kan larabawa har zuwa baƙar fata irin su.
Satin su ɗaya da fara zuwa sukayi wasu abokai a cikin class ɗin nasu ƴaƴan larabawa, irin waƴan da babu kwaɓa tattare da su ko kaɗan, duk da kasancewar su musulmai kuwa, wato Suhaib da Safuwan.
Akullum abun da suke so shi suke samu acikin gidan, haka kuma babu wani mai kwaɓar su da sunyi abun da bai kamata ba, kamar yadda sauran yaran gidan suka kasance, kasancewar su Alhaji Abubakar suna irin rayuwar nan ce wacce turawa da wasu daga cikin larabawa sukeyi agidajen su, wato babu kwaɓa kowa yayi harkar gaban sa.
Wannan saken da su Yarima Asad suka samu shine ya sanya akullum suke abun da ransu yake so, ga yawon bala'i daga yau suje wancan park ɗin gobe kuma sai su tafi wancan joint ɗin, ta hanyar abokan su guda biyu da suke biye musu amotacin gidan su su tafi.
A yanzu haka daga Yarima Asad har Al'amin ko wanne yana da motar sa ta hawa, mai tsananin kyau da tsada da Alhaji Abubakar ya mallka musu su alokaci guda, tare da ɗan sa mai suna Huzaifah, wanda yake sa'an su shima.
Zaune suke akan wasu haɗaɗɗun kujerun silver, masu azabar kyau da suke a cikin wani haɗaɗɗen joint su duka biyar ɗin.
Wato Yarima Asad, Al'amin, Huzaifah, Suhaib, da kuma Safwan.
Yayin da ga gaban kujerun kuma wani irin tafkeken swimming pool yake.
Sosai wurin yake da bala'in kyau da girma, domin kuwa tsayawa faɗin yadda tsaruwa wurin yake kawai ɓata lokaci ne.
Ƴammata ne da Samari suke ta giftawa ta ko ina, ko wanne da kalar shigar da take sanye a jikin sa.
Yayin da daga cikin swimming pool ɗin nan kuma wasu fararen Ƴammata masu matuƙar kyau suka kasance acikin sa, daga su sai ɗan guntun wando tare da brezia ajikin su, yayin da wasu daga cikin su kuma ya zamto pant ne ajikin nasu ma ba gajeren wando ba.
Kusan dukan su tare suke da samarin su acikin ruwan, suna abun da ransu yake so.
Yayin da gang ɗin su Asad kuma da dukan su ba zasu haure shekara goma shabiyar ba, suka kasance zaune akan waƴannan haɗaɗɗun kejerun da suka yiwa swimming fool ɗin ƙawanya suna musu hira.
Shi kuwa Asad kansa durƙushe yake aƙasa, idanuwan sa akan ƴar wayar sa da aka siya musu ita kwanan-nan, yana aikin latsa ta.
Wasu irin haɗaɗɗun Ƴammata ne da suke sanye da ƙananan kaya, da suka futar da siffar jikin su tas su biyu suka zo wuce ta gaban kujerun da su Asad suke zaune akai cikin tsantsar yauki.
Take kuwa a wurin idanuwan su gaba ɗaya suka koma kan Ƴammatan nan, banda Asad kawai da kansa yake durƙushe aƙasa yana aikin latsar wayar sa.
"Wow!"
Safuwan ya faɗa yana mai janye idanuwan sa daga kan Ƴammatan nan ya juya ɓarin da Asad yake.
Kana ya buɗe baki cikin zaƙuwa yana mai faɗin.
"Hay Prince! Please look at that fine girls."
Ya ƙarasa maganar yana mai taɓo Asad ɗin, tukun ya juya yana mai mayar da idanuwan sa kan Ƴammatan nan da suke cigaba da tafiya, kamar yadda su Al'amin ma duk suke kallon sa.
Yayin da Asad kuma ya janye idanuwan sa daga kan wayar da yake aikin latsawa, tukun ya fara ɗago kansa ahankali yana mai kai idanuwan sa zuwa wurin da Safwan ya nuna masa.
Kallo ɗaya yayiwa Ƴammatan ya janye idanuwan sa daga wurin, yana mai mayar da su kan su Safwan gaba ɗayan su.
Kana daga bisani ya buɗe baki cikin muryar sa, wadda yake magana da ita tamkar an masa dole, yana mai faɗin.
"Haba dai guys, ku yanzu dan Allah ina abun kallo yake ajikin waƴan nan da duk kukabi kuka zuba musu idanuwa haka, salon kawai ku zubar mana da mutunci."
Ya ƙarasa maganar yana mai taɓe baki, kana ya mayar da idanuwan sa kan wayar sa.
Da sauri gaba ɗayan su suka zuba masa idanuwa baki a sake, sabo da jin furucin sa da sukayi akan Ƴammatan da duk kyawun mutum yayi kaɗan ya kira su da munana, tukun daga bisani Huzaifah ya buɗe baki cikin tsantsar mamakin halin Asad yana mai faɗin.
"Haba guy, anya kuwa kagan su sosai, da har zakace basu kai a kalle su ba."
Sake ɗago kai Asad yayi yana mai zuba mayatattun idanuwan su akan su, kamar yadda suma ɗin suke kallon sa, kana daga bisani ya janye su ahankali daga kansu yana mai mayar da su kan hanyar da matan nan suke tafiya, tukun ya sake ɗauke idanuwan sa daga wurin su, yana mai sake watsa su akan abokan nasa, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Uhm! Ku kalle su da kyau guys, both of them are bicths fa."
Ya ƙarasa maganar yana mai juyar da kai gefe ya tofar da yawu, tukun ya sake mayar da idanuwan sa kan wayar sa.
Yayin da Al'amin kuma ya buɗe baki cikin sauri yana mai faɗin.
"Kai Asad, wallahi koda suke bitch ƙaryar mutum yace dai basuyi ba, kuma-ma mu dai sun birge mu."
Da sauri Asad ya ɗago kansa daga kan wayar da take ahannun sa, sabo da jin furucin da Al'amin yayi yana mai watsa masa wani matsiyacin kallo, tukun daga bisani ya ɗaga laɓɓan sa cikin kausassar murya, yana mai faɗin. "Bu...............✍
*BAK'AR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 23*
"But you know ko da iskancin zanyi nafi ƙarfin na kula bitch ko, ƙazama sauran wani, tirr Allah ya kiyaye."
Ya ƙarasa maganar yana mai sake jifan su da wani ɗan iskan kallo, tukun daga bisani ya miƙe tsaye yana mai ɗaukar key'n motar sa ya dumfari parking space.
Binsa sukayi da idanuwa gaba ɗayan su ba tare da wani ya iya furta komai ba.
Yayin da shi kuma ya shige cikin motar sa yana mai bata huta yayi gaba, ko inda suke bai ƙara kallowa ba.
"A gaskiya Prince ɗan iskan gaye ne, ku duba fah ku gani tsabar rainin hankali muzo wuri tare, amma ya tashi yayi tafiyar sa shi kaɗai."
Cewar Suhaib yana mai kallon su Al'amin.
Yayin da shi kuma Huzaifa ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Kaɗan daga cikin rashin mutuncin Asad kenan, kuma fa wai shi fa nan yana nufin yaji ne haushi an haɗa sa da bitch, bayan kuma akullum su ɗin yake kallo yana jin daɗi."
"Kai guys wallahi ba gida Asad ya tafi ba yanzu, ko kuwa kun manta da yaune birthday ɗin Taslim."
Al'amin ya faɗa yana mai kallon abokan nasu, fuskar sa ɗauke da murmushi.
Yayin da Safuwan kuma ya buɗe baki cikin tsantsar mamaki yana mai faɗin.
"Amma gaskiya kuwa idan haka ne Prince ya raina mana hankali, shegen kullum yay ta nunawa baya son ta, yana faɗin Allah ya kiyaye yaso wata yarinya a cikin class, to yanzu uban mene zai kaisa wurin ta."
"Hhhhhh! Lallai ne guy's, wato wai ku haryau baku gane halayyar Prince bane ba ko, to bari kuji in faɗa muku, shi fa ya yadda aso-sa, amma shi ɗin ne dai bazai ce yana so ba, sabo da yana ganin hakanin tamkar zubar da mutuncin sa ne, sannan kuma ya yadda da yayi abota da yarinya, muddin ta kasance kyakkyawa kuma mai tsafta, kana ƴar gayu, dan haka Taslim ma ita take son sa bashi yake sonta ba."
Huzaifah ya faɗa yana murmushi.
"To kuma uban mene zai kasa wurin taron ta idan haka ne?" Cewar Suhaib yana kallon huzaifah.
"Haba dai guy, ya keke irin wannan batun ne tamkar wani villager, kai da kanka kasani ko ba soyayya ai zai rage zafi a wurin."
Safuwan ya faɗa yana mai ɗan kashe masa ido ɗaya.
Gaba ɗayan su yara ne ɗanyu shakaf, amma sai dai kuma idanuwan su sun riga da sun gama buɗewa da iskanci, ta yadda har suke yiwa kansu kallon cikakkun samari.
Ayanzu haka suna ss 1 ne anan makarantar su wacce sukeyi, yayin da Alhaji Abubakar kuma yayi musu Al'ƙawarin kaisu Oxford University Ingla suyi degree ɗin su acan.
"Any way, ku tashi kawai mubi bayan ɗan iska, domin muga abun da zai ai'kata da idanuwan mu, ta yadda koda yazo yana cika mana baki zamu samu abun faɗe."
Al'amin ya faɗa yana mai miƙewa tsaye.
Kana gaba ɗayan su suma suka miƙe tsayen suna masu tunkarar wurin da suka ajiye motocin su.
*BAYAN SHUƊEWAR WASU SHEKARU.*
Abubuwa da yawa sun faru acikin shekarun da suka gabata waƴan da baki bazai iya furta adadin yawan su ba.
Yayin da su Asad kuma suka zama cikakkun samari masu kimanin shekaru Ashirin da takwas zuwa da tara aduniya.
Ayanzu haka suna karatun master's degree ɗin su ne a Oxfort University dake Engila, kamar yadda sukayi degree ɗin acan ma.
Har kawo yanzu suna nan da hallayar su wacce suka taso da ita, koma ace fiye da waccen ta baya, domin kuwa a yanzu haka har neman matan banza dukan su sunayi, sai dai shi kuma Asad har yau bai taɓa yin zinaba, saɓanin su Al'amin da suka mayar da ita ba komai ba.
Shima ɗin kuma bawai yaƙi ta bane sabo da gudun saɓon Allah, a'a kawai dai bai yarda da yin bane, sabo da kallon abun da yake amatsayin ƙazanta, wato ƙyanƙyamin sa da yake mahaukacin yi, abun da kawai ya yadda da shi shine romancing, shima kuma bada ko wace yarinya ba, sai wacca yasan bata mu'amala da wani namijin bayan shi, to fah a wannan fagen ne yayi mugun ƙwarewa, domin kuwa shi ta wannan hanyar yake biyawa kansa buƙatar sa aduk lokacin da yaji ta taso masa, yayin da Ƴammata da dama kuma suke hauka akan sa, tunda ga kan turawa, larabawa, har zuwa hausawa irin sa ƴaƴan attajirai da suke karatu a school ɗin tasu, sai dai kuma shi a wurin sa ko kallo basu ishesa ba, asalima babu wadda tafi cin wuya a wurin sa face wacce zata nuna tana son sa, sabo da ya faɗa ya kuma faɗa har yau ba a haifi yarinyar da takai matsayin ya so ta a cikin zuciyar sa ba, balle kuma har yayi mararin auren ta.
Ansha raba Ƴammata faɗa akan sa ba sau ɗaya ba-ba kuma sau biyu a cikin school ɗin tasu.
Jin sa yake tamkar yafi kowa aduniya, sabo da azababben kyawun da yaje taƙama da shi, wanda ko su larabawan baza su nuna masa shi ba, ga kuma Uwa Uba giyar ruwan kuɗin da take ɗibar sa, domin kuwa ba ƙaramun kuɗi Alhaji Abubakar da Mai Martaba suke sakar masa ba, kana suma zuwa yanzu duk suna da sanao'in su, yayin da Asad yake da super market's da dama acikin ƙasar Dubai, da kuma cikin ƙasar sa ta haihuwa, wato Ƙasar Hausa, ga kuma wuraren shaƙatawa da yake da su suma, kuma gaba ɗayan su yana sa musu suna Asadullahi ne, kamar irin su Asadullah Palace, da ya gina sa acikin Ƙasar Hausa a Jahar su da wasu Jahohin da suke a cikin ƙasar, da kuma Asadullah Boutique, da shima yake da shi acikin Dubai da Kuma cikin ƙasar hausa, kana ga Asadullah Shoping Mall dukan su a wurare daban-daban.
Uwa uba kuma ga jinin Saurata da yake gudanya acikin jinin sa, wanda ta sanadin sa ne kuma ako da yaushe yake ƙara jinsa asama fiye da kowa, domin kuwa ako ina baya ɓoye shi ɗin ko wane ne, duk da dai ayanzu haka babu abun da ya tsana sama da al'adun gidan su, amma sai dai kuma yana jin daɗin a kirasa da Prince ako da yaushe, domin kuwa hakan ba ƙaramun fasa masa kai yake yi ba.
Tun lokacin da suka gama Degree ɗin su na farko basu ƙara komawa Dubai da zama ba duka, kamar yadda suke acan ɗin da, sai dai suje ta da ziyara, wato dai yanzu sun koma ƙasar sune, wanda hakan kuma aikin mai martaba ne da Gimbiya Fulani, ba dan komai ba kuwa suka dawo dasu nan ɗin, sai sabo da yadda sukaga gaba ɗaya rayuwar su ta sauya, duk babu wata sauran tarbiyya tattare da su, hakan yasa suka zauna suka tattauna da Alhaji Abubakar, sannan aƙarshe aka gyara musu ɗakunan su na nan, aranar da sukayi graduation Mai Martaba da yazo suka juya tare da su, da kuma Alhaji Abubakar da yayi musu rakiya.
A fannin su suma ba siji wani rashin daɗi ba da komowar tasu gidan su, sabo da sun riga da sun san sun dafa ƙasa a yanzu, ko wace ƙasa sukai niyar zuwa zasu tafi aduk lokacin da suka gadama, kana kuma idan duk sati sukayi niyyar zuwa Dubai ɗin to fah zasu je, ba tare da sun cewa wani ya ɗau wani abun ya basu ba.
Yanzu hakama cigaban karatu ne ya sake dawo dasu Engila.
Zaune yake akan ɗaya daga cikin kujerun da suka yiwa haɗaɗɗen swimming pool ɗin dake wurin ƙawanya.
Sanye yake da wani ɗan guntun wandon jeans da tsayin sa ya tsaya masa a iyakar kan guiwoyin sa, yayin da rigar dake sanye ajikin sa kuma ta kasance mara hannu, ta yadda har ake ganin fareren damtsen hannayen sa afili.
Sosai baƙar lallausar sumar dake ɗauke a kansa, tare da sajen dake zagaye a fuskar sa suke futar da wani irin ƙyalli suna ɗaukar ido, kallo ɗaya zaka musu kasan ba ƙaramun kuɗi suke ciba.
Riƙe yake da mug ɗin copy a hannun sa ɗaya yana siping ɗin sa, yayin da ɗayan hannun nasa kuma ya kasance riƙe da wayar sa ƙirar Iphone 12, yana aikin shafata, idanuwan sa ƙur akan ta.
Sosai Ƴammata keta giftawa ta gaban sa, ko wacce da kalar shigar dake sanye ajikin ta, kuma duk suna yin hakan ne ko Allah zaisa su dace ya taya, domin kuwa suna tsoron zuwa gare sa kai tsaye, sabo da kowa yasan halin sa na dizga Ƴammata muddin kasan sa.
Yayin da shi kuma ko da wasa bai ɗaga kai ya kalle su ba, sai aikin shafa wayar sa kawai da yake yi, yana sipping ɗin copy ɗin sa.
Tun misalin ƙarfe huɗu take zaune a wurin tana jiran zuwan sa, domin kuwa ayau ta ƙudiri aniyar zuwa gare sa ta furta masa abun da ke ranta akan sa, ko Allah zai sa ta dace, amma sai dai kuma yana zuwa ya zauna a wurin gaba ɗaya taji ta kasa tashi daga wurin da take zaunen, balle har ta kai ga ƙarasawa gare sa ta furta masa abun da ke ranta, sabo da tsabar kwarjin da taga ya ƙara yima ayau fiye da kullum da take ganin sa daga nesa.
Bilkisu Abubakar Sardauna kenan.
Bahaushiya yarinya y'ar gata wacce ta futo daga gidan kud'i, domin kuwa mahaifin ta shine gwamnan da tainuwar sa take ci a cikin Jahar su ta Wasai yanzu.
Tana d'aya daga cikin fresh studen d'in da akayi admiting d'in su a wannan shekarar a cikin school d'in.
Yarinya ce sangartatta lambar d'aya, kasancewar ita kad'ai ce 'ya mace a wurin mahaifin ta.
Satin ta ukku da zuwa makarantar taci karo da Asad a cikin wannan wurin hutawar, da k'awarta ta janyo ta a ranar suka fara zuwan sa, domin suyi wankan ruwa.
Sai kuma akayi rashin sa'a adai-dai lokacin da suka shigo idanuwan ta suka yi mata arba da Yarima Asad yana shirin futa daga cikin wurin, domin kuwa acikin wurin Yarima Asad yafi zama sama da ko ina acikin k'asar, dan kuwa har d'aki na mussaman ya kama wanda yake hutawa acikin sa aduk lokacin da yazo, kasancewar wurin Babban wuri ne wanda ya had'a masaukin bak'i da kuma wuraren shak'awa da nishad'i acikin sa, sai dai kuma anan k'asar ma ba kowa ke iya zuwan sa ba, sai wanda ya amsa sunan sa na mai kud'i, domin kuwa wuri ne special wanda babu ruwan wani da wani, kana babu hayani acikin sa kowa na harkar gaban sa ne, kuma mafi akasarin mutanen da suke zuwa wurin duk matasa ne da ga mazan har matan.
Cak Billy ta tsaya a wurin da take tana mai bin bayan mayyar motar da ta hango wani had'ad'd'en gaye zaune acikin ta ya fuce daga cikin wurin.
Jin shirun da abokiyar tafiyar Billy tayi ne ya sanya ta juyawa b'arin da take, dan taga abun da ya sanya ta yin shirun.
A hankali ta janye idanuwan ta daga kan Billy tana mai bin hanyar da taga tana kallo da nata idanuwan, domin taga abun da take kallo wanda har ya janye mata hankali haka.
Amma sai kuma taga ba taga komai ba, sai shimfid'ad'ar kwaltar da wasu irin had'ad'd'un furanni suka yi mata k'awanya a wurin.
Hakan ne yasa ta sake janye idanuwan ta daga wurin, tana mai mayar da su kan k'awar tata, tukun daga bisani ta d'aga hannun ta tana mai kaisa jikin Billy, bakin ta na fad'in.
"Hey Billy!"
Ta fad'a tana mai d'an girgiza kafad'ar ta.
Firgigit Billy ta juyo b'arin da take tana mai dawo da idanuwan ta kanta, da alamun dai gaba d'aya hankalin ta baya hurin ma da.
Yayin da ita kuma k'awar tata ta d'ora da fad'in.
"Lafiya kuwa Beb, meke faruwa ne haka?"
Ta fad'a tana kallon ta.
Lumshe idanuwa Billy tayi tana mai bud'e baki ta fesar da wata sassanyar iska daga cikin sa, tukun daga bisani ta wara idanuwan ta akan fuskar k'awar tata tana mai bud'e baki tace.
"Waye shin d'in Zee?"
Shiru Zee tayi tana mai kallon Billy tare da d'an cizon lips d'in ta na k'asa a hankali, tukun daga bisani ta sake juyawa bayan ta tana mai k'ara kai idanuwan ta zuwa kan hanyar da taga hucewar Yarima Asad alokacin da suke shigowa, kana ta janye idanuwan nata daga kan hanyar, tana mai sake juyowa ta kalli Billy.
Tukun ta bud'e baki tana mai fad'in.
"Wai Prince Asad kike nufi?"
"Zata iya yuwuwa shi ɗin ne, duk da dai ni ban san sunan saba, amma dai shine guy ɗin da ya fuce a cikin mota alokacin da muke shigowa."
Billy ta faɗa idanuwan ta ƙur akan fuskar Zee, tana mai jiran jin amsar ta, kasancewar ita Zee a level 2 take ne yanzu tafi Billy sanin wurin, domin kuwa abotar su tazo ɗaya ne ma sabo da kasancewar Zee ita ƴar shugaban Ƙasar Hausa, yayin da ita kuma ta zamto ƴar Gwamnan Jahar Wasai, kuma jam'iyar iyayen nasu ɗaya, shi yasa tun can suka san juna ma.
"Prince Asad kenan."
Zee ta faɗa tana mai sake taune leɓen ta na ƙasa, idanuwan ta akan fuskar Billy tana jiran taji abun da zata faɗa.
"Ok Prince ne ma kenan?"
Cewar Billy fuskar ta ɗauke da murmushi.
"Tabbs kuwa, kuma Prince ɗin ma na cikin Jaharku, wato ɗan gidan Sarki Abdallah ne, Sarkin Wasai."
Zeee ta faɗa tana mai cigaba da kallon Billy.
Yayin da ita kuma ta buɗe baki fuskar ta ɗauke da murmushi, tana mai faɗin.
"Kice abun zai zamto mai sauƙi ma a gare ni.
To duk ba wannan ba ma, koma waye ne shi ɗin, to yana gab da zama nawa, domin kuwa kallo ɗaya nai masa ya tafi da komai nawa, kuma ayanzu haka ina jin zan iyayin komai akan sa."
Wani irin kallon rainin hankali Zee tabi Billy da shi baki asake, tukun daga bisani ta saki wani shegen murmushi, irin wanda ma'anar sa take nufin da wanda aka yiwa shi ɗin bai san kansa ba, wato shi da mahaukaci duk ɗaya suke.
Kana daga bisani ta tsaya da murmushin da take tana mai buɗe baki, idanuwan ta a cikin na billy tace.
"Shin kin san abun da kike faɗe kuwa Billy?
Ko da yake bazan ga laifin ki ba dan kinyi irin wannan furucin akan Asad, sabo da ke ɗin sabuwa ce baki san komai daga cikin halayyar saba, amma shawarar da zan iya baki a yanzu ita ce, ki gaggauta kawar da wannan abun daga cikin zuciyar ki tun kafin yayi zurfi, domin kuwa dubun ki sunyi irin haka, koma nace fiye da haka, kuma har yanzu suna kanyi amma har yau babu nasara akan Prince."
Zee ta faɗa babu alamun wasa a cikin magan-ganun nata idanuwan ta a cikin na Billy.
Yayin da Billy kuma ta rumtse idanuwan ta da matuƙar ƙarfi tun lokacin da Zee tace akwai dubbanta, kana yanzu ta buɗe su har sun ɗan sauya launi daga fari zuwa ɗan ja, sannan ta buɗe baki cikin muryar gaskiya da gaskiya, tana mai faɗin.
"Please Zee daga yau karki ƙara danganta sa da wasu matan muddin ina tsaye a wuri, domin kuwa ni ɗin nan da kika gani ina da zazzafan kishi akan abun da nake so, kana kuma dan su sun buga sun kasa ba shi ke nufin nima zan kasa ba, domin kuwa sunbi nasu salon ne, haka nima zanbi nawa salon wanda kuma ba lallaine ya zamto ɗaya da wanda suka bi ba.
Abu ɗaya kawai da zan sake mai maita miki shine, na gansa ina son sa, kuma wallai tallahi sai na bar tarihi tunda har ance wasu sun kasa."
Billy ta faɗi haka da tsantsar gaskiyar ta tana mai kallon Zee.
Yayin da ita kuma Zee ta fara girgiza kai tana mai jifan Billy da kallon tabbas bakya cikin hayyacin ki, domin kuwa babu wata hallayar Asad wadda bata san labarin ta ba, kana tasan Ƴammata da dama waƴan da sukafi Billy komai da komai da suke hauka akan sa, amma ko kallo basu ishe sa ba, hakan yasa ta buɗe baki tana mai faɗin.
"Shin kin san inkiyar sa ma kuwa?"
Ta faɗa tana mai ƙara sakin murmushin rainin wayo, tukun ta ɗora da cewar.
"Baka so sai dai asoka! Haukata Ƴammata su yini su kwana suna dambe! Sanya ƙawa da ƙawa gaba!
Wannan shine iƙirarin da abokanan sa hausawa suke masa a cikin school ɗin nan."
"Tabbas kuwa lokacin ɓacewar sunayen ne yazo, domin kuwa tabbaci nake baki akan sai ya koma na Billy bada kan ka asar..."
"Hhhhhhhhhhhhhh!" Zee ta kwashe da wata mahaukaciyar dariya wacce ta sanya Billy dakatawa da maganar da take kanyi dan dole tana kallon ta, ba tare da ta kai ƙarshe ba.
Tukun daga bisani kuma ta gimtse dariyar ta lokaci guda, kana ta ɗaga kafaɗun ta sama tana mai taɓe baki tace.
"Any way naji yanzu kuma zanjira lokaci, dan haka please let us go ko mayi abun da ya kawo mu."
Zee ta faɗa tana mai yin gaba.
Girgiza kai Billy tayi tana mai bin bayan Zee da kallo, domin kuwa ba ƙaramun shaƙa tayi ba da dariyar da tai mata, tukun daga bisani itama ta ɗaga ƙafafuwan ta tana mai rufa mata baya.
Tun daga wannan ranar ta fara bin diddigin Yarima Asad, ya zamto duk wuraren da yake zuwa itama tana nan, haka zataci uban ado da ƙana-nan kaya tazo wurin daniyyar ta tun kare sa da batun abun da ke cikin ranta, amma sai dai kuma har kawo yau da aka ɗauki tsawon wata ɗaya da haɗuwar su ta farko bata iya zuwa ta tsaya ko agaban sa ba, ballan tana ta kaiga faɗar abun da take son faɗen, sabo da wani irin kwarjini da take ganin yana mata akullum idan ta ƙudir ta zuwa gare san.
Cigaba da tsayuwa tayi a wurin da take tana mai kallon sa, wata zuciyar nace mata taje kawai koma mai zai faru ya faru, yayin da wata zuciyar kuma take tunasar da ita kalaman Zee akan hallayar Asad da kullum take faɗa mata.
Sanye take da black jeans tare da wata ƴar red top ajikin ta, sai wani mahaukacin red hill shoe mai matuƙar tsini da yake sanye aƙafar ta, yayin da gashin atach ɗin da yake tufke akan ta kuma ya kasance zube agadon bayan ta.
Yafe take da wani ɗan mitsi-tsin mayafi da ya tsaya iya kar kan ƙirjin ta akan ta, sai ƴar ƙaramar jakarta wacce ta kasance ta mahaɗin takalmin ƙafar ta da take riƙe a hannun ta.
Acan kuwa ɓangaren Asad hankali kwance yake sipping ɗin copy ɗin sa, yana yi yana latsa wayar sa, sosai yake matuƙar jin daɗin wurin, sabo da yadda ya kasance tsit babu hayaniya, domin kuwa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 76