Share this page
hula da rawanin su tana mai jujjuya su. Da sauri ta waigo ɓarin da suke tawowa, sabo da jin sautin takun tafiyar su da tayi. Washe baki tayi tun kafun su ƙaraso wurin, tukun daga bisani ta laɓɓan ta tana mai faɗin. "A'a ƴan samarin Mai Martaba kuce an futo shiryawar kenan." Ta ƙarasa maganar tana mai riƙe hannun Al'amin a lokacin da suka ƙarao wurin. "Ina yini Jakadiya." Yarima Asad da Al'amin suka haɗa baki wurin faɗi suna masu sakin murmushi. "Lafiya ƙalau shalelen Mai Martaba." Jakadiya ta faɗa tana mai shafa kan Yarima Asad, idanuwan ta ƙur akan sa. Yayinda su kuma suka juya cikin sauri suna masu shirin shigewa cikin ɗakin. Da sauri Jakadiya ta buɗe bakin ta tana mai faɗin. "Am nace ba..." Waigowa Yarima Asad da Al'amin suka yi a tare suna kallon ta, tare da jiran jin abun da zatace ɗin. Hakan da ta ganine ya sanya ta sake washe baki tana mai faɗin. "Idan kun shirya kun gama sanya kayan sai kuzo nan, ga wula da rawani na amsar muku, yau ni da kaina zan sanya muku su Ƴan gaban goshin Mai Martaba." Ta ƙarashe maganar da washe baki tana mai yi musu nuni da wular. Taɓe baki Yarima Asad yayi ba tare da yace komai ba, yana mai juyawa ya shige cikin ɗakin, domin kuwa shi ason samun sa yafi so mai Martaba ya sanya masa hular da rawani da kansa, kamar yacce yake sama sa su ako da yaushe. Yayinda shi kuma Al'amin ya amsawa Jakadiya da "tom", tukun ya juya yana mai shigewa cikin ɗakin shima. Murmushi Jakadiya tayi tana mai ɗan cije leɓen ta na ƙasa, tukun daga bisani ta koma jikin kujerar da take akai tana mai kishingiɗa. A ɓangaren su Yarima Asad kuwa suna shiga cikin ɗakin direct ya huce cikin bedroom ɗin Mai Martaba. Baiyi ko minti biyar da shigar tasa ba sai gashi nan ya futo daga shi sai farar sabuwar singilet tare da sabon farin boxer ajikin sa, yayinda hannuwan sa kuma suke rungume da kayan su waƴan da zasu sanya yanzu, kasancewar da ya shiga cikin baiga Mai Martaba ba sai dai motsin ruwa da ya jiyo a bathroom ɗin sa, shiyasa ya futo musu da kayan nan domin su shirya. Kan haɗaɗɗiyar doguwar kujerar da take a cikin fallon ya ƙarasa yana mai ɗora kayan a kan ta, tukun ya juya ɓarin da Al'amin yake zaune a kan ƴar ƙaramar kujera yana mai faɗin. "Wallahi idan na gama shiryawa ko kallon ka bazan ba, ballan tana na jiraka, tunda naga wuri ka nema kazauna ma." Ya faɗi maganar ƙasa-ƙasa yana mai juyawa ya fara ware kayan nasa. "To masifaffe ai sauƙin ta ma nima nasan wurin inka tafin." Cewar Al'amin yana mai tashi daga kan kujerar da yake ya fara zame kayan jikin sa shima. Yayinda shi kuma Asad ya cigaba da zura kayan sa ba tare da ya sake cewa komai ba. Blue ɗin shadda getzner ce da taji uban aiki irin na sarakai a jikin ta mai matuƙar tsada tana walwali, ɗinkin riga da wando tare da malum-malum suka sanya su a jikin su. Sosai sukayi bala'in kyau acikin kayan, musamman ma Asad shi da ya kasance farar fata. Wasu sababbin fararen takalma na fata suka sanya ƙafafun su a cikin su, tukun shi Asad ya ƙara ɗaukar farar alkyabbar da take a jiye a gefen sa yana mai ɗora ta akan kayan jikin sa. Yayin da shi kuma Al'amin yabar iya babbar rigar jikin sa kawai. "Ɗebo kayan ka muje ka a jiye, daga nan sai mu ƙara sa wani turaren." Yarima Asad ya faɗa yana mai nufar bedroom ɗin Mai Martaba, da niyyar yaje ya sake feso turare, duk da wanda ya fesa a jikin kayan kafun ya futo da su kuwa. Sun ɗauki tsayin mitina biyar zuwa shida a cikin ɗakin, tukun daga bisani sai gasu nan sun futo suna ta faman buga uban ƙamshi mai tsananin daɗi da sanyi. Shafa kai Yarima Asad yayi da tafin hannun sa yana mai sakin guntun tsaki ba tare da yace komai ba, hakan da Al'amin ya ganine ya sanya sa buɗe baki yana mai faɗin. "Mene ne kuma ya faru yanzu?" "Mtswwww! Da yanzu Abba ne zaisa mun rawani na, amma waccan Jadiyar ta ɗauke." Ya faɗa murya acunkushe yana mai fucewa daga cikin ɗakin. Binsa shima Al'amin yayi ba tare da yace komai ba. Suna futowa daga cikin ɗakin Jakadiya tayi saurin miƙewa daga kishingiɗen da take a kan kujera tana mai faɗin. "Kai Masha Allah ƴan samarin mai martaba, a gaskiya kunyi matuƙar yin kyau, dan haka ku maza ku matso nasa muku rawani kafun a fara hawa baku." Ta ƙarasa maganar baki a washe tana mai ɗauko hular ɗaya ta ɗora ta a kan al'amin daya ƙaraso gaban ta. Sanya masa hular da aka riga aka gama naɗa rawanin a jikin ta tayi ta zauna das akan sa, tukun ta buɗe baki tana mai faɗin. "Masha Allah ɗan saurayi ya futo, dan haka matsa a sawa ɗan Uwanka shima." Ta ƙarasa maganar tana mai ɗauko ta Asad ɗin idanuwan ta ƙur akan sa. Kallon ta shima Asad ya tsaya yi ido cikin ido daga wurin da yake ba tare da ya motsa ba. Hakan da ta ganine ya sanya ta buɗe baki cikin rawar murya tana mai faɗin. "Ya dai shalelen Mai Martaba, ko kuwa ka fasa yin hawan ne naga kaƙi ka matso, bayan kasan ƙila yanzu an farama." Ta ƙarasa maganar tana mai sakin wani irin murmushi, wanda za'a iya kiran sa da na yaƙe. Yayinda shi kuma Asad ya sauke wani ɗan gajeren numfashi yana mai janye idanuwan sa daga kanta, tukun daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai matsawa kusa da ita, sabo da jin furucin nata, kuma yana gudun kar a fara hawan babu shi. "Yawwa ko kaifa Autan Mai Martaba." Jakadiya ta faɗa tana mai fara ɗora masa hular a kan sa idanuwan ta ƙur a kan fuskar sa. Da ƙarfi Yarima Asad ya rumtse idanuwan sa, jijiyoyin kansa na futowa raɗa-raɗa a kan goshin sa, sabo da wani irin mahaukacin nauyi da yaji kan nasa yayi lokacin da Jakadiya ta ɗora masa hular, tukun daga bisani kuma ƙafafuwan sa suka fara wata irin kar-karwa suna rawa. Da sauri Jakadiya ta miƙe tsaye tana mai ƙara cusa hular da take haɗe da rawani cikin kansa idanuwan ta ƙur a kan fuskar sa, tukun ta buɗe baki tana mai faɗin. "Kuyi maza-maza ku tafi ga sautin bindiga can na jiyo, da alamun Mai Martaba ya futa ta ƙofar baya ne muna nan bamu sani ba." Jakadiya ta faɗa da matuƙar sauri tana mai girgiza Asad. Yayinda shi kuma ya taune leɓen sa na ƙasa da matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani ya fara bud'e idanuwansa da yake jin sun masa wani irin mahaukacin nauyi a hankali ahankali, harya buɗe su duka a kan fuskar Jakadiya. Da matuƙar sauri Jakadiya ta sake sa tana mai juyawa baya ta fara tafiya, bakin ta na furta kalmar. "Kuyi maza maza ku tafi kar ayi babu ku mana." Ba dan komai ta tafin ba kuwa sai dan yadda taga idanuwan Yarima Asad sun koma Jajahur yarce kasan garwashin huta, a lokacin da ya buɗe sun. Cigaba da tsayuwa Asad yayi a wurin yana mai jin jikin sa na wani rin ɗaukar zafi, yarce kasan ana zuba masa garwashi. Ganin da Al'amin yayi Asad bai motsa daga wurin da yake ba ne ya sanya sa buɗe baki yana mai faɗin. "Muyi sauri mutafi mana aboki, sabo da kaji fa Jakadiya tace amma fara." Ya ƙarasa maganar yana mai jan hannun Yarima Asad yayi gaba ba tare da ya tsaya kallon sa ba, ballantana ya lura da sauyawar da yanayin sa yayi. Jin hakan da Yarima Asad yayi ne da kuma yadda yaji Al'amin na ƙoƙarin jansa ne, yasan ya sa fara ɗaga ƙafafuwan sa da yake jin suna karkarwa yabi bayan sa cikin tsantsar azaba, domin kuwa shi kansa bazai so ace hawan nan da yayi mahaukacin tamasa ba ya huce sa. Tafe suke gumi na yanko masa ta tsakar kansa yana tsiyayowa ta cikin hular dake sanye a kansa zuwa kan fuskar sa sosai, amma a haka ya cigaba da bin bayan Al'amin da yake jan hannun sa ba tare da ya tsaya ba, duk da yadda kuwa yake jin jikin sa na sake ɗaukar zafi tamkar ana hura ta a cikin sa. Basu tsaya ba har sai da sukaje gaban Dokunan su da suke riƙe a hannun wasu mutum biyu daga cikin ƴan sulke, tukun Al'amin ya saki hannun Yarima Asad yana mai faɗin. "Ga naka nan ka hau, nima bari na hau nawa." Ya ƙarasa maganar yana mai matsawa kusa da danƙareren baƙin dokin da yake riƙe a hannun wani mutumi, ba tare da ya kalli fuskar Asad ba har lokacin. Yayinda shi kuma Asad ya sake rumtse idanuwan sa jikin sa na fara karkarwa, tukun daga bisani ya buɗe su a hankali, kana ya fara ɗaga ƙafafuwan sa da yake jin suna ƙara yin nauyi, yana mai matsawa zuwa gaban wani farin danƙareren doki da yaji uban ado ta ko ina a jikin sa, da alama dai shine Dokin nasa. Sosai dokin yake da matuƙar girma, ga kuma fatar jikin sa da takasance fara ƙal, babu ko ɗigon baƙi a jikin ta sai faman shigning da take tana ɗaukar ido, alamun ba ƙaramun hutu dokin yake ciki ba kenan. A hankali ya miƙa hannun sa da yake wata irin rawa yana mai riƙe linzamin dokin da shi, tukun ya fara ɗaga ƙafar sa ɗaya yana mai shirin hawa dokin, amma sai gaba ɗaya yayi baya yana shirin faɗuwa a ƙasa. Ganin haka da wannan mutumin da yake riƙe da dokin nasa yayi ne, ya sanya matsawa kusa da shi da matuƙar sauri yana mai tarosa a hannun sa, sannan ya ƙara cicciɓa sa yana mai ɗora sa a saman dokin ba tare da ya tsaya kallon fuskarsa ba, domin kuwa shi duk atinanin sa ko rashin sabo da hawan da baiyi bane da kansa ya sanya yanzun ma ya kasa hawa. Yayinda shi kuma Asad yana hawa saman dokin nan yaji kansa ya sake yin wani irin bala'in sarawa da matuƙar ƙarfi. Rumtse idanuwansa yayi yana mai ɗanyin zillo akan dokin tare da cije leɓen sa na ƙasa da bala'in ƙarfi, take kuwa leɓen ya futar da wata irin tsartuwar jini, alamun ya fashe kenan! Tukun daga bisani ya fara buɗe idanuwan sa a hankali yana mai jin numfashin sa na wani irin fuzga. Buɗe idanuwan nasa yayi dai-dai da lokacin da Al'amin ya riƙe linzamin dokin sa yana mai ɗan dukan jikin sa da hannu, take kuwa dokin ya zura a guje yana mai yin gaba, kamar yacce na Babban yaya ya riga yayi gaba tini. Ganin hakan da Asad yayi ne ya sanya sa shima miƙa hannun sa ɗaya yana mai damƙar linzamin dokin. Ai'ko kamar jira dokin yake yi ya riƙe sa yayi wata irin zabura yana mai sakin haniniya da matuƙar ƙarfi ya fara sakin gudu. A kuma dai dai lokacin jikin Yarima Asad ya fara wata irin bala'in karkarawa, numfashin sa na wani irin fuzga da matuƙar ƙarfi. Wata irin gigitattar ƙara Babban Yaya ya saki a dai-dai lokacin da ya juya dokin sa yana son yayi wani wasa da shi, sabo da yadda idanuwansa suka hango masa Yarima Asad ya saki linzamin dokinsa dokin na kan gudu, yana mai y....................✍ *A GASKIYA NA DENA SAKIN LINK NA GRUOP 'DINA, SABODA YAWAN B'ATA GARI DA WA'YAN DA BA KARATUN SUKE BA DA SUKE SHIGOWA, DAN HAKA GA DUK MAI SON KASANCEWA ACIKIN GROUP 'DIN B'AKAR MASARAUTA, AMMA FA IDAN YASAN YA IYA COMMENT DA SHARHI SAI KU TUNTUB'ENI TA NUMBER WHATSAPP 'DINA KAMAR HAKA. 08038135929. K'OFA ABUD'E TAKE GA MASU SO A TALLATA MUSU HAJARSU A DUNIYA KUMA ZAKU IYA TUNTU B'ATA TA NUMBER.* *BY* UMAR FARUQ*D* *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 19* Yin baya gaba ɗayan sa. Da matuƙar sauri Babban Yaya ya dire daga kan dokin sa, yana mai hankaɗe mutanen dake wurin yayi wurin da ƙanin nasa yake da bala'in gudu, kamar yadda mutane da dama suka juya wurin, ta sanadin ihun da yayi da yaja hankulan su zuwa wurin, amma sai dai kash, gaba ɗayan su sun makaro, domin kuwa tun kafin su isa wurin Yarima Asad ya faɗo ƙasa ta baya, kana dokin ya take ƙirjin sa da ƙafafuwan sa yana mai yin gaba! Wata irin zabura yarima Asad Yayi ƙirjinsa na ɗagowa sama adai-dai lokacin da dokin ya taka ƙirjin nasa, tukun daga bisani ya koma yana mai zubewa a ƙasa babu alamun numfashi tattare da shi! Wata irin mahaukaciyar ƙara Babban yaya ya buga alokacin da ya ƙarasa kusa da ƙanin nasa, sabo da yarce ya gansa a sassanƙare, gashi babu ko alamun numfashi tattare da shi, kana daga bisani ya zube guiwoyin sa aƙasa yana mai janyo Asad cikin jikin sa yana girgizasa, tare da kiran sunan sa. "Asad! Asad!! Asad!!!" Babban yaya yake faɗe cikin tsantsar ruɗu yana mai ɗan marin fuskar sa tare da girgiza sa, sabo da yadda yaga gaba ɗaya jikin sa ya sandare ya koma tamkar sanda, domin kuwa babu wata gaɓa da tayi saura wacce ke motsawa a jikin sa. Kafun kace tak tuni wurin ya cika da Al'umma tako ina ana kallon su. Yayin da shi kuma Babban yaya ya fashe da wani irin gigitaccen kuka jikin sa na rawa, gumi na tsattsafo masa cikin jikin sa. "Asad dan Allah ka temake ni ka tashi kar kamutu kabarmu kaji." Ya sake faɗa a gigice yana mai cigaba da girgiza sa. Acan ɓangaren Gimbiya Fulani cikin gida kuwa, tunda akayi sallahr la'asar ta futo daga cikin ɗakin ta tana me neman Asad, ba dan komai ba kuwa sai dan kawai ta sanya sa yayi azkar ɗin yamma, kamar yacce duk ranar duniya take sasu suke yin su, wato azkarul sabahu wal'masah, da suke a cikin hisnul muslim wanda Annabi yake yi ya kuma koyar. Amma sai dai har ta gama duba duk inda yake tsammanin zata gansa bata gansa ba, hakan ne yasata fahimtar yana hurin mai martaba ya tafi ya shirya, ba dan ranta yaso ba ta juya zuwa cikin ɗakin ta jikin ta duk ba daɗi, tana mai fatan Allah yasa yayi azkar ɗin da kansa, domin kuwa tasan sa da wasa muddin basa sa tayi ba haka yake cewa ya manta, ba kamar babban yaya ba da baya taɓa ƙinyi ko a ina yake kuwa, hakan yasa ko kaɗan bata da fargaba akan sa, domin kuwa tariga data sani muddin wani abun ya same sa to muƙaddari ne kawai daga Allah, ba wai dan rashin addu'a ba. Tana nan zaune a cikin ɗakin ta kan tsakiyar gado hannun ta riƙe da Baby, wata kuyanga ta faɗo cikin ɗakin bako sallama a bakin ta, sai faman haki da take ta saki kawai. Da sauri duka mutanen dake a cikin ɗakin suka kai idanuwan su gare ta, yayin da wasu daga cikin su kuma suka buɗe baki suna masu faɗin. "Ke ko lafiya kika faɗowa mutane cikin ɗaki a haka?" Bata iya basu amsa ba, sai gaba da ta cigaba dayi zuwa wurin da Gimbiya Fulani take cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali. "Yay...Yarima...ne ya faɗo...daga saman doki afil..." "Me kike son kice mun ne haka, shin wane Yariman ne ma ya faɗo daga saman doki?" Gimbiya fulani ta faɗa a haukace bayan ta diro daga kan gadon da take hannun ta riƙe da ƴar jinjirar ta. Yayin da sauran mutanen dake a cikin ɗakin ma duk suka miƙe tsaye hankula su a bal'in tashe. Da sauri Gimbiya Fulani ta ratsa ta cikin mutanen nan da suke a cikin ɗakin ta tana mai kama hanyar waje, ba tare data ɗau ko da mayafi ba, tsabar ruɗun da take a ciki, domin kuwa hankalin ta idan yayi dubu sai da duka ya tashi. Ganin hakan da sauran matan cikin ɗakin sukayi ne ya sanya su mara mata baya, suma duk hankulan su a matuƙar tashe. Ƙarasawar ta bakin ƙofar futa daga cikin fallon nata yayi dai-dai da lokacin da Babban Yaya ya danno kansa cikin falon, rungume da Asad a ƙirjin sa yana mai sakin wani irin kuka a matuƙar haukace. Take a wurin kuwa jikin Gimbiya Fulani ya ɗauki wata irin karkarwa, kana ta kasa yin gaba ta kasa yin baya, sai mamewa da tayi a wurin da take idanuwan ta ƙur akan Ƴaƴan nata guda biyu, yayin da zuciyar ta kuma ke wani irin gudu fiye da misali, fargaba da tashin hankalin abun da zata gani ta kuma ji sukayi matuƙar lulluɓe ta. "Mamy na dan Allah kicewa Asad kar yatafi ya barni, mamy kice masa ya tashi, dama ni sai da nace masa kar yahau doki bazai iyaba, amma yace ya iya kuma yana hawa ai dama, gashi kuma yanzu ya faɗo dokin ya taka ƙirjin sa." Babban yaya ya faɗa a wani irin haukace yana mai durƙushewa a gaban mamay'n tasu da ya ƙaraso, tare da sakin wani irin gigitacce kuka. Girgiza kai Gimbiya Fulani ta farayi tana mai zube guiwoyin ta a ƙasa Da sauri Hadima Larai ta ƙaraso wurin da take tana mai amshe baby'n hannun ta, sabo da yadda taga tana shirin yadda ta ba tare data sani bama. Cikin sauri ta miƙa hannuwan ta da suke bal'in rawa, tana mai janyo Asad daga jikin Babban Yaya ta dawo da shi kan cinyar ta. Kana ta ɗaga tafin hannun ta ɗaya tana mai ɗan marin fuskar sa, bakin ta na furta kalmar. "Zaki! Zaki!! Zaki!!!" Amma taji shiru ko alamun motsi babu tattare da shi. Hakan ne yasa ta janye tafin hannun nata daga kan fuskar sa tana mai matsar da shi zuwa wurin rawanin da yake sanye a kansa ta tunɓuke sa ƙasa, tana mai cusa ƴan yatsun hannuwan ta a cikin lallausar sumar kansa. Da sauri ta rumtse idanuwan ta tana mai janye ƴan yatsun nata daga cikin sumar sa, sabo da wani irin tururi da taji ya dake su mai tsantsar azabar zafi. "Ku bani ruwa! Ku bani ruwa!! Sun ƙone mun kan yaro da huta!"" Ta faɗa a wani irn haukace tana mai juyawa ta kalli dandazon jama'ar da suke zagaye da su. Cikin ƴan sakanni sai ga wasu mata nan har guda biyu sun miƙo mata ruwayen a cikin jarkokin su kamar yacce ta buƙata Da mtuƙar hanzari ta buɗe murfin jarkar bayan ta warce ta a hannun matar, tukun daga bisani ta ɗaga ta tana mai tsiyaya ruwan a tsakiyar kan Asad, tare da kai yatsun hannuwan ta cikin sumar tasa ta fara cuɗa ta hankali a bala'in tashe. A kuma dai-dai wannan lokacin Mai Martaba Sarki Abdallah ya faɗo cikin falon a matuƙar hargitse, ba tare da yayi ko sallama ba. *JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.* Yau take ranar sunan jinjirar da Gimbiya Kaɓel ta haifa, hakan ne yasa ko ina ka kalla a cikin Masarautar kake ganin jama'a iri-iri, tun daga kan Sarakai na wasu masarautun maƙotan su har zuwa hadiman gidan suna ta giftawa, yayin da gaba ɗaya fuskokin su suke ɗauke da tsantsar farin ciki da annashuwa. Tun bayan Sallah asuba aka yanka shanu har kimanin guda takwas narka-narka lafiyayyu a gidan, kana yarinya taci sunan Kakar ta, wato mahaifiyar Lamiɗo, amma za'ana kiran ta da HADDIYAL. Sosai akai shagali irin shagalin da ba ataɓa yin kamar sa ba a cikin gidan, kana aka baiwa jinjirar tsafuka kala-kala, a cewar su hakan shine ƙarshen gatan da zasu yi mata a duniya. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI MASARAUTAR WASAI.* Cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali mai martaba ya ƙaraso wurin da Gimbiya Fulani take riƙe da Asad, yana mai zube guiwoyin sa a ƙasa, yayin da sauran jama'ar dake wurin kuma suka bubbuɗa fili suna masu matsawa gefe. Janyo Asad yayi daga jikin Gimbiya Fulani yana mai rungume sa a jikin sa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin tsantsar tashin hankali yana mai faɗin. "Baba na! Baba na!! Baba na!!! Asad! Asad!! Asad!!!" Ya faɗa cikin ruɗu da firgici yana mai girgiza sa, gaba ɗayan sa shima ya ruɗe ya firgice yadda kasan ba namiji ba, namijin ma kuma Sarki. Amma sai dai Asad ko motsi baiyi ba, sai ma wata irin sandarewa da jikin sa yake sakeyi tamkar gawa, domin kuwa su kansu banda sunga zuciyar sa na bugawa da babu abun da zai hana suce ya mutu, sai dai kuma ga zuciyar tasa nan tana bugu da sauri da sauri kowa na gani, kasancewar babu kaya a jikin sa sai boxer kaɗai da yayi ragowa, domin kuwa duka sauran kayan Gimbiya Fulani ce ta cire masa su. Cicciɓar sa mai martaba yayi yana mai miƙewa tsaye da shi, kana ya mannasa a ƙirjin sa yana mai masa wata irin runguma, tukun ya juya baya cikin sauri tamkar ya kifa a ƙasa, yana mai fucewa daga cikin falon gaba ɗaya. Direct yayi part ɗin sa da shi yana mai zuwa ya kwantar da shi a kan tamfatse-tsen gadon sa na al'farma. Baifi mintina biyar ya ɗauka da shigowar sa ɗakin ba, sai ga Babban lilkitan su da yake duba su sun shigo cikin bedroom ɗin, tare da su Galadima da Waziri da kuma duk sauran ƴan uwan mai martaba manyan maza. "Yawwa likita matso-matso ka gaggauta dan Allah kayi sauri ka duba sa, bana son na rasa rayuwar Ɗana." Mai Martaba Sarki Abdallah ya faɗa cikin tsantsar ruɗu, yana mai ƙarasawa wurin da Doctor'n yake ya kamo hannun sa. Bai sakar masa hannun nasa ba har sai da ya kawosa gaban gadon da yarima Asad yake yashe akansa, tukun ya cika masa hannun yana mai komawa ɗayan ɓarin ya riƙo tafin hannun Asad ɗaya yana murza sa. Yayin da shi kuma doctor nan ya buɗe box ɗin sa cikin sauri, kana ya fara zaro abubuwan gwaje-gwaje yana mai fara yin abun da ya kamata yayi. Su kuwa su Galadima da sauran jama'ar gaba ɗayan su jugum-jugum sukai suna kallon Asad da yake kwance sheme akan gado yadda kasan gawa, zuciyoyin su cike da al'hinin wannan abu da ya faru lokaci guda, kana ko wanne daga cikin su da akwai abun da yake saƙawa a cikin zuciyar sa. Sai da likitan ya ɗauki kimanin mintina arba'in yana faman bincikar yaron. Kana daga bisani ya miƙe tsaye yana mai sharce gumin dake akan goshin sa, idanuwan sa akan fuskar mai martaba da shima yake kallon sa yana gumin, duk da sanyin A'C'n dake ratsa cikin ɗakin, amma hakan bai hana doctor'n haɗa zufa ba kamar yacce bata hana mai martana yin zufar fa shima. "Ya ake ciki ne doctor? Mene yake damun Asad ɗina? Shin dokin yay masa illa ne?" Mai Martaba ya watsowa likitan tambayoyi a jere a kuma tsantsar ruɗe duk a lokaci ɗaya. Yayin da shi kuma ya sake gyara tsayuwar sa a wurin da yake yana mai yin gyaran murya, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin. "Ina ganin wannan abun bazai yuwu anan cikin gida ba, dole sai mun dangana da Asibiti, sabo da acan ne muke da kayan aiki tare da kayan gwaje-gwaje waƴan da zasu taimaka mana wurin gano abun da ke damun sa, sabo da ni dai a yanzu gaba ɗaya ban fahimci komai ba dan gane da ciwon nasa, abu ɗaya kawai dana sani shine yana rayuwa har yanzu a doron duniya, but kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, insha Allah hakan ba wata matsala bace Babba." Ya ƙarasa maganar cikin sanyi. Gaba ɗayan su suma shiru sukayi babu wanda aka iya samu ya furta komai, domin kuwa ba ƙaramun sanyi jikin su yayi ba duka. Sun ɗauki tsawon minti na biyar a haka, tukun can mai martaba ya miƙe a wani irin zabure yana mai sake ɗaukar Asad, kana ya juya ya kama hanyar waje cikin sauri tamkar ya kifa a ƙasa, ba tare da yace musu komai ba. Hakan da suka ganine ya sanya suma gaba ɗayan su mara masa baya har likitan, suna masu fucewa daga cikin ɗakin. Cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙarasa cikin tamfatsetsen private hospital ɗin da yayi bala'in gajiya hurin haɗuwa, domin kuwa tsayawa faɗar kyawun asibitin shi kansa ɓata lokaci ne, amma sai dai kallo ɗaya mutum zai masa ya fahimci cewa ba wurin zuwan ko wane irin mutum bane ba, domin kuwa cikin masu kuɗin ma sai waƴan

Chapter 20 of 76