nan ɗin shine ya kasance vip na cikin wurin, ga kuma yadda wata irin sassanyar iska mai matuƙar daɗi take dukan jikin sa, ta yadda har kwantaciyyar baƙar sumar da tayiwa hannuwan sa da ƙauri-kan sa ƙawanya take kaɗawa.
Billy na tsaye awurin nan taga giftawar wata baturiya da taci uban ado ta gaban ta, hakan ne yasa ta bita da kallo domin taga wurin da zatayi, ai'kuwa direct taga ta doshi wurin da Prince Asad yake cikin yauƙi.
Take kuwa a wurin Billy taji gaban ta yayi wata irin mahaukaciyar faɗuwa, kana taji wani irin abu ya caki zuciyar ta, bata gama jin wannan baƙin cikin ba idanuwan ta suka hango mata wannan baturiyar a gaban Yarima Asad.
Take kuwa jikin ta ya fara wata irin karkarwa, idanuwan ta na canza launi.
Yayin da ita kuma wannan baturiyar da ta ƙarasa gaban Yarima Asad, ta miƙa hannun ta ahankali zuwa kan mug ɗin da yake riƙe a hannun sa, tukun ta amshe sa tana mai ajiye sa akan plate ɗin da yake akan table ɗin dake a gaban sa.
Yana jin duk abun da take yi kuma ya gane ta, amma yaƙi daga kai ya kalle ta.
Yayin da ita kuma ta sake matsawa gare sa, tana mai ɗaukar hannun ta-ta ɗora su akan kafaɗun sa, tukun ta farayin ƙasa da kanta a hankali, tana mai kai fuskarta kan tasa.
"Hlo Baby!"
Ta faɗa ƙasa-ƙasa tana mai busa masa iskar bakin ta akan fuskar sa, tukun ta cigaba da matsar da fuskar ta zuwa ga tasa tana mai haɗe tsinin hancin ta da nasa, kana ahankali ta juya mazaunan ta tana mai zama akan cinyar sa, tukun ta haɗe lips ɗin ta da nasa wuri ɗaya.
Da matuƙar ƙarfi Billy ta rumtse idanuwan ta sabo da abun da ta gani, jikin ta na wata irin karkarwa..!
*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*
Abubuwa da yawa sun faru a cikin shekarun da suka gifta, na daɗi dana kishiyar sa a cikin masarautar.
A yanzu haka Bir yana da shekaru Ashirin da takwas zuwa da tara ne a duniya.
Sosai yake da tsananin kyau mai matuƙar ɗaukar hankalin duk wanda ya gansa, duk da kasancewar sa Bawa.
Fari ne kar tamkar a taɓa sa jini ya ɓullo, yana da manya-manyan fararen idanuwa masu ɗauke da baƙar ƙwaya wulik acikin su, yayin da karan hancin sa kuma ya kasance dogo, da yayi matuƙar ƙara ƙawata fuskar tasa, sai kuma ɗan ƙaramin bakin sa da yake ɗauke da jajayen laɓɓa akan sa, yayin da fuskar tasa kuma duka ta kasance zageye da wani irin baƙin saje mai tsananin laushi, da yayi masifar yi masa kyau.
Kana yana da wata iriyar suma mai matuƙar yawa da laushi, ga kuma baƙi, duk da dai bata kasance tana samun wani gyara ba, amma a hakan ba ƙaramun kyau take masa ba, domin kuwa tsabar yawan ta har kan kafaɗun sa sai da ta sakko.
Har kawo yau yana nan da maitar kwari da gwafar sa, kana kuma afannin taurin kansa ma babu abun da ya sauya.
Tun a wancan lokacin na shearun baya da Gimbiya Tasmir ta fara tasawa yake son su haɗu gaba da gaba ita, amma har kawo yau da ita kanta take da kusan shekaru Ashirin a duniya Allah bai haɗa su ba, gashi kuma a yanzu yana jin labarin abubuwan da takeyi da suka ninka na da, hakan ya sanya a kullum yake burin haɗuwar sa da ita gaba da gaba, domin yaga abun da zatayi akan sa.
Wannan dalilin ne ma yasan ya-ya samu abokan sa da suke tare ya tambaye su wuraren da take zuwa acikin masarautar, ba dan komai ba kuwa sai domin yaje ya tsaya akan hanyar da take wucewar, kasancewar kusan kullum a daji yake yini wurin harbe-harben sa, shi yasa bai taɓa cin karo da ita ba, sai dai idan ana wani biki acikin masarautar ya ganta, hakan yasa gaba ɗaya ya dena futa daji a ƴan kwanakin -nan, yake zaman sa a wurin su Mauzum, kullum yana hanyar da take bin domin su haɗu, sai dai kuma har kawo yau ita kuma bata biyo hanyar ba, da alamun dai ta kwana biyu bata futo shan'iska ba kamar yadda ta saba.
Zaune yake a gaban Iyar Bayi cikin ɗakin ta na iccina ya tanƙwashe ƙafafuwan sa yana kallon ta.
Yayin da ita ɗin ma take zaune a gaban sa tana kallon sa, gaba ɗayan ta duk a wani rikice, da alamun dai babu natsuwa tattare da ita a yanzun ko kaɗan.
Sake mirginar da kai Bir yayi gefe, yana mai yin narai-narai da idanuwan sa, tukun daga bisani ya ɗaga tafukan hannayen sa duka biyu yana mai haɗe su wuri ɗaya, idanuwan sa akan fuskar Iyar Bayi.
Kana ya buɗe baki cikin muryar roƙo yana mai faɗin.
"Ki temake ni Iya ta, ina mai tabbatar miki da babu wani abun da zai faru dake.
To waima wane ne zai sani bayan daga ni sai ke a cikin wurin nan, ballantana har akai rahoton da kike gudun akai."
Girgiza kai Iyar Bayi tayi tana mai rumtse idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su akan sa tana mai kallon sa, kana ta buɗe baki cikin muryar raɗa tana mai faɗin.
"Amma me yasa kake son dole sai ka sani ne Jarumi?
Shin me ma sanin zai amfana maka, bayan kasan ba zaka taɓa ganin su ba, asalima ni ɗin kaina ban san komai ba dan gane da su Jarumi."
Girgiza kai shima Bir yayi yana mai ɗan taune leɓen sa na kasa, tukun daga bisani shima ya buɗe baki cikin yin ƙasa da murya, kamar yadda suke yi ako da yaushe idan suna irin wannan batun yana mai cewa.
"Kawai ina son jin tushe nane nima, badan komai ba kuwa sai dai in tabbatar da ni ɗin ƙas-ƙantaccen Bawa ne kamar yadda mutane suka sha faɗamun hakan.
Ina son ki faɗa mun da gaske ne tsinto ni akayi Iya ta."
Bir ya ƙarasa maganar yana mai sauke tafukan hannayen sa daga haɗen da suka ya miƙa su yana mai riƙo na Iyar Bayi a cikin nasa, ya damƙe su wuri ɗaya, yana mai kallon ta da jajayen idanuwan sa.
Yayin da Iyar Bayi kuma ta furzar da wata zazzafar iska daga cikin bakin ta, tana mai jin gaban ta na duka tara-tara, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin matuƙar sanyi, tana mai faɗin.
"Kayi haƙuri Jarumi, haƙiƙa a yanzu bakina bazai taɓa iya furta abun da kunnuwan ka suke son jiba, sai dai kuma ina son kasani akwai lokacin dana tanada domin na faɗa maka, duk da dai zanyi hakan ne ba ason raina ba, dan haka na maka al'ƙwarin muddin lokacin nan yayi to babu abun da zai hana ni baka tsakuren tarihin ka, sai dai kuma ina son kasani, sannan kuma kasa aranka, wannan ranar da bakina zai furta maka labarin da kake son ji, itace kuma zata zamto rana ta-ta ƙarshe a gidan duniya."
Ta ƙarasa maganar tana mai zame hannayen ta daga cikin na Bir, kana daga bisani ta miƙe tsaye a hankali tana mai fucewa daga cikin ɗakin, ba tare da ta tsaya jin ta bakin sa ba.
Shi kuwa Bir gaba ɗayan sa mutuwar zaune yayi a wurin da yake, sosai yake matuƙar gigicewa aduk lokacin da yaji Iya tayi irin wannan furucin, kana kuma yake jin yana matuƙar ƙara son jin labarin nasa, domin yaji dalilin da ya sanya iyar bayi take tsoron faɗa masan, duk da dai shima ɗin yana matuƙar firgita idan ya tuna da magan-ganun ta, sa yake cewa zata mutu akan tarihin nasa.
Ya ɗauki tsawon mitina goma shabiyar zaune a wurin yana mai faman tinane-tinane, tukun daga bisani da yaga abun bazai yi masa ba ya miƙe tsaye cikin sanyi yana mai fucewa daga cikin ɗakin.
Dogo ne sosai lamba ɗaya, yana da ƙiba dai-dai misali tare da murɗaɗɗen jiki irin wanda kowa ke so ya kasance da shi.
Sanye yake da ɗan gajeran baƙin wandon sa babu riga a jikin sa kamar yadda suka kasance ako da yaushe, duk tsanin sanyi da damina kuwa.
Gaba ɗaya ƙirjin sa cike yake da uwar gargasa mai matuƙar laushi da duhu, amma ahaka yake tafiyar sa baya jin kunyar kowa ya gansa, kasancewar hakan al'adar masarautar tasu ta koyar da su, kuma haka ko wane Bawa yake kasancewa a cikin ta.
Kai tsaye ya doshi hanyar da aka faɗa masa Gimbiya Tasmir nabi ta ita idan zataje wurin hutun ta.
Tafe yake cikin sanyin da kalaman Iyar Bayi suka haifar masa, kansa durƙushe a ƙasa.
Yayin da a cikin zuciyar sa kuma yake fatan haɗuwa da Gimbiya Tasmir a futowar tasa ta yanzu.
Ai'kuwa ba zato ba tsammani ya jiyo sautin gudun mutane rada-da-da-da ta ko ina, hakan ne yasa sa ɗago kansa cikin sauri domin yaga abun da ke faruwa.
Bayi ne suke gudu iyakar ƙarfin su, kama daga mazan su har mata suna masu neman hurin ɓuya.
Cikin tsantsar mamaki ya fara waige-waige yana bin su da kallo, domin kuwa shi bai taɓa ganin ana irin wannan gudun ba tun da yake acikin masarautar sai yau.
Tsaye yayi a wuri ɗaya yana waige-waige, sabo da yadda yaga cikin ƴan sakanni duka bayin dake a wurin sun ɓace-ɓat.
Yana shirin janye idanuwan sa daga kan hanyar da yake kallo ya hangi tawowar mace sanye da wata irin blue'n doguwa riga mai azabar kyau a jikin ta, wacce take manne da adon duwatsu a jikin ta tana jan ƙasa, yayin da wasu irin danƙara-danƙaran mutane waƴan da ba yau ya fara ganin su ba acikin masarautar, amma sai da ya saba ganin su ne aduk lokacin da ake yin hukunci akan wani, dan shima yasha shiga hannun su, suna biye da ita hannuwan su riƙe da mugayen bulalai tare da makaman su.
Da sauri ya janye kansa daga wurin da yaga suna tawowa, yana mai yin tamkar bai san da zuwan su ba, ya cigaba da ɗaga ƙafafuwan sa yana tafiyar sa, yayin da a ƙasan zuciyar kuma yake jin wani irin tsoro sama-sama, ga kuma ƙirjin sa dake ɗan bugawa, sabo da sanin muguntar dakarun nan da yayi, sai dai kuma neman fitina irin tasa gaba ɗaya ta sanya ya kasa guduwar shima.
Acan kuwa ɓangaren su Gimbiya Tasmir cikin takun ta na tsantsar Izza, wanda shi kaɗai ke nuni da ko ita ɗin wace-ce, ta cigaba da takowa wurin dakarun ta na biya da ita.
Sosai tayi matuƙar kyau cikin shigar dake sanye a jikin ta, abunka da mai kyau ɗin dama, shiya sanya duk irin sitirar da tasa a jikin sa sai tayi mata kyau.
Kanta ɗaga asama tana kallon hanya fuskar nan tata babu alamun annuri tattare da ita ta cigaba da dumfarar wurin nan.
Lokaci ɗaya ta tsaya cak a wurin da take adai-dai lokacin da suka ƙaraso saitin wurin da Bir yake, sabo da motsin sautin tafiyar mutum da taji acikin kunnuwan ta.
A ɓangaren Bir kuwa shima ya lura da isowar su wurin da yake ɗin, hakan ne yasa sa durƙusawa ƙasa jikin wata bishiya da take a gefen sa, yana mai ɗaukar wani icce ya fara kakkarya sa ba tare da ya ɗago ya kalli wurin da suke ba.
Tsayuwa Gimbiya Tasmir ta cigaba dayi a wurin tana mai jiran taji ƙarar sautin gudu a kunnuwan ta, amma sai dai har ta ɗauki tsawon daƙiƙa ukku a wurin bataji ba, kai asalima sai daina jiyo sautin tafiyar tayi, sai kawai ƙarar karya iccina, wanda hakan kuma ya tabbatar mata da cewar akwai mutum a wurin.
Take kuwa ranta yayi matuƙar ɓaci lokaci guda, domin kuwa tunda take futowa ba'a taɓa yi mata haka ba sai yau.
Hakan yasa cikin tsantsar ɓacin ran da ya lulluɓe ta lokaci guda ta fara juyar da kanta ɓarin da take jiyo motsin ahankali.
Karaf kuwa idanuwan su suka haɗu da na juna, adai-dai lokacin da ya ɗago shima domin yaga ko sun kauce.
A hankali ya janye idanuwan nasa daga cikin nata yana mai yin tamkar bai ganta ba, ya cigaba da karya sandar dake riƙe a hannun sa.
Yayin da ita kuma ta kafesa da nata idanuwan da suka fara sauya launi tsabar ɓacin rai, tana mai mamaki tare da tinanin abun da ya taka da har ya hanasa guduwa a lokacin da ta tawo, bayan kuma ta tabbatar da yaga lokacin da sauran ƴan uwan sa bayi ke gudu, kana kuma duk wannan laifin da yayi bai ishesa ba sai da ya ƙara sanya idanuwan sa a cikin nata, abun da ba ataɓa samun wani yayi ba bayan ahalin ta a duniya.
Cikin tsantsar ɓacin rai ta ɗago hannun ta da yake wata irin kar-karwa tsabar ɓacin rai, tana mai nuna sa daga wurin da take, tukun daga bisani ta ɗaga laɓɓan ta a hankali cikin muryar ta da kafun ajita ake yarawa, tana mai faɗin.
"Waye shi ɗin, mai kuma ya taka da har zai ganni ya zauna?"
Ta ƙarasa maganar da sakin huci ba tare da ta janye yatsar tata daga nuna san da take yi ba, yayin da shi ɗin ma yake lura da duk abun da take yi ta ƙasan ido da yake kallon ta, kana ta sake buɗe baki cikin fushi tana mai faɗin.
"Ina buƙatar ganin sa durƙushe a gabana kafun nan da giftawar daƙiƙa daya kacal".................✍
*BAK'AR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 24*
Ta k'arasa maganar cikin zafi tana mai sakin huci, tukun ta fara d'aga k'afafuwan ta tana mai dosar wurin da kujerar nan take cikin tsantsar zafin rai.
Yayin da su kuma dakarun nan sukayi kan Bir aguje ransu atsantsar b'ace da abun da sukaga yayiwa uwar d'akin nasu, domin kuwa zasu iya cewa tun da suke da ita basu tab'a ganin ranar da ranta ya b'aci ba irin na yau.
Ko kad'an Bir bai lura da isowar su ba, sai dai kawai hannun sa da yaji an funcika da wani irin k'arfi tamkar za'a cizge sa, ta yadda har sai da ya kife ak'asa wanwar kansa na gwaruwa da wani dutse dake a kusa da shi.
Yayin da shi kuma wannan badakaran da ya funcike sa yana mai fara jansa a k'asan wurin da yake d'auke da duwar-watsu da matuk'ar k'arfi.
Rumtse idanuwa Bir yayi da k'arfi yana mai jin yadda kansa ke had'uwa da duwar-watsun kan hanyar.
Suna k'arasawa gaban kurar da Gimbya Tasmir take a k'ark'ashin bishiyar nan, ya durk'usa yana mai sannu hannu ya damk'o huyan Bir da matuk'ar k'arfi, tukun daga bisani ya d'agosa yana mai durk'usar da shi a kan guiwoyin sa.
Yayin da ita kuma Gimbya Tasmir take zaunu akan wannan kujerar ta-ta, ta d'ora k'afa d'aya akan d'aya tana mai girgiza ta.
Gaba d'aya babu alamun rahama ko kad'an tattare da fuskar ta.
Wani irin abu take ji mai kama da icce na tokare mata k'awon zuciya, aduk lokacin da tuna da yadda Bir ya kalli cikin idanuwan ta.
A hankali ta fara sauke idanuwan ta k'asa tana mai kaisu b'arin wurin da Bir yake.
Yayin da shi d'in ma kuma adai-dai lokacin ya d'ago nasa idanuwan yana mai kaisu kan fuskar ta.
Take kuwa idanuwan su suka sark'e cikin na juna.
Yayin da zuciyoyin su kuma sukayi wata irin bugawa a lokaci guda, tukun daga bisani gudun su ya k'aru fiye da yadda suke ada.
Cikin wani irin yanayi wanda Gimbiya Tasmir bata tab'a tsintar kanta acikin sa ba ta ji ta, ta sanadin had'uwar da idanuwan nasu sukayi wuri d'aya, ga kuma zuciyar ta dake wani irin bugu da matuk'ar k'arfi, abun da tun da take arayuwar ta bata tab'a sanin sa ba.
Wata irin tafar-fasa zuciyar ta take jin tana yi mata, sabo da yadda Bir ya kafeta da tsumammun idanuwan sa baya ko k'itawa.
Ita kanta so take ta ja ye nata idanuwan daga cikin nasa, ko ta samu damar yin tinanin kalar hukuncin da ya kamata tayi masa, amma gaba d'aya taji ta kasa, sabo da wasu irin abubuwa da take ganin suna futowa daga cikin idanuwan nasa suna fad'awa cikin nata.
A fannin Bir kuwa ko kad'an bai d'aga kansa ba da niyyar ya kafeta da idanuwan sa tamkar yadda yayin, sai dai kuma d'ago idanuwan nasa keda wuya suka fad'a cikin nata, wanda kuma a take a wurin yaji zuciyar sa tayi wata irin matsananciyar harbawa .
Yaso ya janye idanuwan nasa daga cikin nata, amma gaba d'aya yaji ya kasa yin hakan kwata-kwata, kai asalima ya kasa koda k'ifta su ne daga kan nata, yadda kasan mayen k'arfe da k'arfe ne suka had'u, domin kuwa wani irin haske yake ganin yana futa daga cikin idanuwan nata yana jonewa da nasa idanun, ta yadda har ya manta matsayin wacce yake durk'ushe a gaban nata, domin kuwa tun da ya taso yayi wayo bai tab'a tsintsar kansa a cikin yanayi mai kama da irin wannan d'in ba.
Jini ke tsiyayowa ta cikin gashin kansa sa yana gangarowa ta gefen idanuwan nasa, ta sanadin kansa da ya fashe a lokacin da badakaran nan ke jansa acikin kwazazzaban nan, amma ko kad'an bashi da alamun zai goge sa, gudun karya shigar masa idanun, sai kallon tsakiyar idanuwan Gimbiya Tasmir da ya cigaba dayi zuciyar sa na wani irin bugu da matuk'ar sauri, yayin da tsigar jikin sa kuma ke wani irin tashi, yana mai jin wani irin yanayi a gaba d'aya sassan jikin sa wanda bai saba da shi ba.
Cikin tsantsar k'unar rai Gimbiya Tasmir ta cigaba da kallon tsakiyar idanuwan sa, tana mai jin wani rin mugun bak'in ciki na tokare mata zuciya.
So take kawai ta janye idanuwan nata daga cikin nasa, amma gaba d'aya taji ta kasa.
Babu abun da yafi b'ata mata rai ma sai irin yadda taga shi d'in ma yak'i ya janye nasan, ga kuma zuciyar ta dake wani irin bugu duk ta sanadin kallon-kallon da suke yiwa junan su, abun da bata tab'a jiba kenan dan ta kalli wani mutumin, asalima babu mai iya had'a idanuwa da ita balle har aje ga irin haka.
Lokaci d'aya ta mik'e tsaye zumbur daga kan kujerar da take, tana mai tsayawa akan k'afafuwan ta, tukun daga bisani ta fara d'agasu cikin zafin rai, suna masu futar da sautin k'arar gwala-gwalan da suke manne akan su, ta doshi wurin da Bir yake a durk'ushe, har lokacin kuma idanuwan ta na-nan cikin nasa.
Ko da ta mik'e'n tsaye amai-makon Bir ya hak'ura dakallon ta tunda tai masa nisa, amma sai ya sake d'aga kansa sama yana mai sake danna idanuwan sa cikin nata.
Sai da tazo dab da shi tukun taja ta tsaya tana mai sakin numfarfashi, yayin da zuwa lokacin kuma idanuwan ta suka kad'a sukai jajajir tsabar b'acin rai, duk a tinanin ta idan yaga ta mik'e tsaye zai janye idanuwan nasa daga cikin nata, amma sai taga ya sake d'aga kansa sama yana mai mayar da su ciki, hakan da yayin kuwa ba k'aramun sake dagula mata lissafi yayi ba, kana kuma ranta ya k'ara kaiwa k'ololuwa wurin b'aci, sannan ta fara tinanin to wai shi d'in uban waye ne ma da har zai tsaya a gaban ta yana kallon ta ido cikin ido, sannan kuma mai ya taka da har dan ta kalle sa bugun zuciyar ta ke sauyawa, bayan a yadda ta gansa tariga da tasan Bawa ne k'ask'antaccen mutum gare ta.
Hakan ko shi yayi matuk'ar k'ara harzuk'ata, ta yadda har k'wak'walwar ta ta gaza sanar da ita abun da ya kamata tayi masa.
Cigaba da kallon sa tayi daga tsayen da take, kafin daga bisani kuma ta durk'ushe a k'asa tana mai cake guiwar k'afar ta d'aya a cikin k'asa, yayin da d'ayar kuma ta dire tafin ta akan k'asa, kana ta dafa k'asa da hannun ta d'aya, yayin da d'ayan kuma ta dunk'ule sa da k'arfi, tana mai cigaba da kallon cikin idanuwan Bir, kamar yadda shim yake kallon nata, zuciyoyin su na wani irin bugu atare, ta yadda har kowanen su ke iya jiyo sautin bugawar zuciyar d'an uwan sa.
Bud'e bakin ta tayi tana mai furzar da wata irin zazzafar iska daga cikin sa akan fuskar Bir.
Da sauri ya lumshe idanuwna sa ba tare da ya shirya yin hakan ba, sabo da iskar bakin ta mai matuk'ar turiri da ta daki k'wayoyin idanuwan nasa, yayin da ita kuma ta fara d'aga lab'b'an ta cikin kausassar muryar ta da take futa k'asa-k'asa, tana mai fad'in.
"Shin waye kai?
Waye ubanka?
Me kuma ka taka acikin Bak'ar Masarauta?"
Ta k'arasa maganar da k'yar, tana mai sakin numfarfashi, gaba d'aya alamun gajiy sun bayyana k'ara-ra akan fuskar ta, kasancewar bata saba yin doguwar magana irin wannan ba aduk lokaci d'aya, sai dai kuma a yadda take jin zuciyar ta na zafi akan wannan mara kunyar Bawan na gaban ta, zata iyayin fiye da haka ma.
A hankali Bir ya sake bud'e idanuwan sa akan fuskar ta, tukun daga bisani ya mayar da su ya lumshe yana mai sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, tamkar yaron da yaci kuka ya more, kana daga bisani ya sake bud'e su akan fuskar ta yana mai sake watsa su cikin nata da yaga gaba d'aya sun canza launi, daga farin kar d'in da ya gansu d'azu zuwa jajawur yanzu.
A hankali ya fara d'aga lab'b'an sa idanuwan sa acikin nata tamkar zaiyi magana, tukun daga bisani kuma ya b'ige da aika mata da wani irin sassanyan murmushi, kana a k'arshe ya k'arasa rufe bakin nasa da hura mata sassanyar iskar dake cikin sa shima, yana mai jin wani irin abu tamkar mayen k'arfe na fuzgar sa zuwa gare ta.
Da sauri Gimbiya Tasmir ta lumshe idanuwan ta tana mai sakin wata irin ajiyar zuciya da ko kad'an bata shirya ma yin ta ba, sabo da yadda taji saukar sassanyar iskar bakin sa mai matuk'ar k'amshi akan fuskar ta, ta yadda har sai da ta daki k'wayoyin idanuwan ta.
Wanda hakan kuma ba k'aramun sake b'ata mata rai yayi ba.
Yayin da su kuma dakarun nan nata gaba d'ayan su sukayi suman tsaye a wurin da suke suna masu bin su da idanuwa, yayin da mamakin k'arfin halin Bir kuma gaba d'aya ya cika zuciya da ruhin su, domin kuwa kosu tun da suke da ita tun tana y'ar k'aramar ta ba a tab'a samun wani ya kalli cikin idanuwan ta ba ko da na second d'aya kuwa, tsabar kwarjinin da take yi musu, amma sai gashi yau sun gani akan idanuwan su wani Bawa wanda ko su suka fisa galihu ya kafe ta da nasa idanuwan.
Wata irin kar-karwa jikin Gimbiya Tasmir ya farayi sabo da tsantsar b'acin rai, tukun daga bisani kuma ta wara idanuwan nata tana mai mik'ewa tsaye zumbur tamkar wacce aka tsikara.
Kana kuma ta d'aga k'afar ta-ta dama tana mai harbin Bir da ita da matuk'ar k'arfi, ta yadda har sai da yayi baya taga-taga yana shirin fad'uwa akan wani dutse, amma sai yayi sauri ya dafe wani k'aton icce da ya gani agaban sa yana mai sake cake guiwoyin sa acikin k'asa, tukun daga bisani ya d'ago kansa yana mai sanya idanuwan sa a cikin nata, tare fa sakar mata wani irin murmushi mai tafe da ma'anoni da yawa a cikin sa.
Da k'arfi Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwan ta da tafukan hannayen ta duk alokaci guda, tukun daga bisani ta bud'e su tana mai juyawa bayanta ta fara waige-waige, tana mai tinanin kalar hukuncin da ya dace da shi.
Juyawa tayi b'arin da farin ruwan nan wanda yake zagaye da su yake tana mai kai idanuwan ta kansa, tukun daga bisani kuma ta janye su daga kan ruwan tana mai girgiza kai.
Kana ta sake juyawa tana mai kai idanuwan ta kan dakarun nana nata da suke a tsaye cirko-cirko tamkar bishiyu.
Sannan ta bud'e baki cikin wata iriyar murya wacce take d'auke da tsantsar b'acin rai a cikin ta tana mai cewa.
"Ku d'auke shi ku tafi da shi, a masa azaba mafi muni daga cikin azabobi, a masa azaba irin azabar da baku tab'a yiwa wani makamacin ta ba a duniya, kana idan an tabbatar da jikin sa ya nuna azo asanar mun kafun asake sa."
Ta k'arasa maganar tana mai sakin wani irin huci, tukun daga bisani ta juya tana mai fara d'aga k'afafuwan ta cikin sauri, ta doshi hanyar da suka biyo alokacin da suke zuwa wurin.
Yayin da su kuma way'an nan dakarun sukayi kan Bir gadan-gadan gaba d'ayan su.
Tamkar zasu kacaccala sa suka kai hannuwan su jikin sa, ko wanne daga cikin su yana mai damk'ar wani sassa daga cikin sassan jikin sa.
Kana daga bisani sauran suka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 76