Share this page
muni da ƙuna a cikin rayuwar su. Acan ɓangaren su Sarki Barbaru kuwa kai tsaye suka doshi ɓangaren bayi. Tafe suke suna masu furta sunan Gargabilu da matuƙar ƙarfi, yayin da jinjirin nan kuma yake ta cigaba da sakin kuka, har lokacin kuma Sarki Barbaru bai ajiye sa ba. Suna zuwa ɓangaren bayi suka tsaya dukan su a wuri ɗaya, tukun daga bisani wani Bafade ya buɗe baki cikin sauti yana mai faɗin. "Kuna inane ne Ƴaƴan matsiya ta ƙasƙantattu? To kufur-futo ga Uba ga kowa nan ya ƙaraso, ku fur-futo ga bujimin mazaje nan ya ƙaraso, ku fur-futo ga zakin duniya nan na jiran ku." Tun kafin ya kaiga rufe bakin sa sai ga su nan suna futowa da baya da baya daga cikin ɗakunan su na iccina, da matuƙar yawan su mazan su da matan su a guje kuma. Sanye mazan su suke da ƴan gajerun fararen wandina na yadi, babu ko riga ajikin su, yayin da matan su kuma suke ɗaure da wani ɗan guntun baƙin ƙyalke a ƙugun su, tare da wata wargajejiyar rigar yadi ajikin su, gaba ɗayan su babu mai takalmi a ƙafar sa. Da baya da baya suke ƙarasowa har wurin da su Sarki Barbaru suke a tsaye jikin su na karkarwa, tukun sai su juyo ta gaba suna masu zubewa rufda ciki a ƙasa wanwar gaban su Sarki Barbaru. "Ina Iyar Bayi take?" Sarki Barbaru ya faɗa cikin muryar sa da take matuƙar firgitar da su yana kallon su. Wata mata ce mai kimanin shekaru arba'in ta miƙe daga kwancen da take tana mai futowa jikin ta na tsantsar rawa da karkarwa, yayin da kanta kuma yake durƙushe a ƙasa, ta ƙaraso gaban Sarki Barbaru tana mai zube guiwoyin ta a ƙasa. "Tsaye zaki miƙe nan." Sarki Barbaru ya faɗa cikin muryar sa mai firgitarwa yana mai kallon Iyar Bayi da take durƙushe a gaban sa. Yayin da ita kuma ta miƙe tsaye cikin sauri ƙafafunwan ta na wani irin rawa tana mai jin kamar ba zasu ɗauke ta ba, sabo da fargabar laifin da za'ace ta ai'kata da tayi matuƙar lulluɓe ta, domin kuwa ko kaɗan bata lura da ɗan da yake riƙe a hannun Sarki Barbaru ba, duk da kukan da yaron yake tsalawa kuwa tsabar tsoro. Miƙa mata jinjirin dake tsala kuka Sarki Barbaru yayi. Hannuwan ta da suke tsantsar rawa ta miƙa masa su idanuwan ta akan jaririn, tukun shi kuma ya Sarki Barbaru ya ɗora mata Ɗan akan hannun sa. Take kuwa yaron yayi tsit yana zuwa hannun ta, yayin da ita kuma ta zuba masa idanuwan ta tana mai kallon sa tare da yaba kyawun hallitar sa a cikin zuciyar ta. Lokaci guda taji yaron yayi matuƙar shiga ranta, ga kuma wata irin soyayyar sa da taji ta lulluɓe zuciya da ruhinta, tayarce har take jin sa tamkar ita ta haife sa. Sosai ta shagala da kallon sa tana mai ɗan sakin murmushi, domin kuwa ganin kyakkyawan yaron ya sanya ta manta ko a gaban suwa take duka ma. Yayin da shi kuma Sarki Barbaru ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ga sabon Ɗa nan na kawo miki shi da kaina, shi kuma wannan jinjirin da kika gani ba kowa bane face rayuwar mu mu dukan mu kamar yadda kukaji labari, hakan yasa nazo da kaina har inda kike na baki shi, dan haka saiki kula mana da Rayuwar mu." Muryar Sarki Barbaru ta daki dodon kunnen Iyar Bayi, wacce tai sanadin dawowa hayyacin ta daga duniyar kallon jinjirin data tafi tana mai faɗin. "Tabbaci tare da alƙawari gare ni zuwa ga kai ya shugabana, babu wani abu da zai faru da wannan yaron, zan kula da shi tamkar yacce na saba kula da sauran Yaran da yardar Ubanguji Gargabilu." Ta ƙarasa maganar muryar ta a ƙasa. Yayin da shi kuma Sarki Barbaru ya juya yana mai tafiya ba tare da yace komai ba. Binsa a baya suma mutanen sa da suka zo tare sukayi. Yayin da su kuma bayin nan duka suka miƙe daga kwancen da suke suna masu yowa wurin da Iyar Bayi take a tsaye, hannun ta ɗauke da jinjirin kowa na kallon sa. Murmushi Iyar Bayi ta sake yi a lokacin da Ɗan ya ƙara tsanyara kuka yana wawurar yatsun sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Wayyo yunwa ma yake ji, dan haka bara naje na haɗa ruwan zafi nai masa wanka, in yaso sai asamo mun madara na basa yasha." Ta ƙarasa maganar tana mai yin gaba zuwa wurin da ɗakin ta yake. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Shigar mai martaba part ɗin yayi dai -dai da lokacin da Hadima Larai ta dawo hannun ta ɗauke da jinjirin. Da sauri ta zube guiwoyin ta a ƙasa tana mai faɗin. "Barka da futowa Al..." "Bani, bani shi, taso ki bani Baba na na gansa." Mai martaba ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi, yana mai miƙa mata hannu ba tare da ya tsaya amsa gaisuwar ta ba. Hakan da taji ne ya sanya ta tashi fuskar ta ɗauke da murmushi, sabo da jin da tai har mai martaba ya basa suna, wato sunan mahaifin sa kenan, tana mai miƙa masa Ɗan a hannu. "Masha Allah! Alhmdulillahi Alhamdulillah!." Ya faɗa cikin tsantsar farin ciki yana mai kai hannun sa zuwa kan fuskar Ɗan dako wanka ba'a yi masa ba, ya shafi kumatun sa, tukun daga bisani ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Babban Yaya na biyu kenan ko, wato ita Fulani kawai masu kama da ita take haifowa tsabar san kai kenan." Ya faɗi maganar fuskar ɗauke da murmushi yadda kasan ba Sarki ba, domin kuwa shi kansa bazai iya musalta kalar farin ciki da yake ciki ba, haka kuma yana jin bazai taɓa iya ɓoye saba, koda yana cikin fada ne kuwa. Kallo ɗaya yayiwa jinjirin yaji wata irin soyayyar sa ta lulluɓe duka zuciya da ruhin sa, tayarce har yake jin tamkar bai taɓa haihuwa ba sai akansa, kai ataƙaice dai kallon farko da yayi ga yaron yaji ya shiga ransa fiye duk sauran yaran nasa, har Babban Yaya da yake Ɗan farko namiji gare sa kuwa. "Yanzu ina ita Fulanin take ne?" Mai martaba ya faɗa yana mai miƙawa Hadima Larai jinjirin, sabo da jin da yay ana tada sallah a cikin masallacin Masarauta. "Tana cikin ɗaki lafiya ƙalau." Gimbiya Larai ta faɗa tana karɓar Yaron. "Tom shikenan ki mata sannu yanzu in kin shiga, ni na tafi masallaci bayan an idar da Sallah zan dawo, domin kuwa ban gaji da kallon wannan babbar kyautar da Ubangji yayi mun ita ba." Ya ƙarasa maganar yana mai juyawa yayi gaba. Yayin da ita kuma Hadima Larai ta ƙame a wurin ɗaya tana mai bin bayan mai martaba da kallo, sabo da yadda taji ya tsaya a gaban ta yana dogon surutu, abun da bata taɓa ji ance yayi ba ballan tana kuma ta gani, domin kuwa iyakar su da shi gaisuwa ce kawai ke haɗasu, amma sai gashi yau ya tsaya gaban ta yana zuba da nuna farin ciki, yadda kasan a yanzu aka fara masa haihuwa. "Tabbas ko a kwai badaƙala a cikin gidan nan, muddin mai martaba zai cigaba da rawar ƙafa akan yaron nan ba ƙarama bama kuwa, dan sai dai kawai muyi fatan Allah ya kare." Ta faɗa tana mai yin gaba ta doshi ɗakin Fulani, domin taje ta gyara wurin da a kayi haihuwar da kuma shi kansa jinjirin. Acan ɓangaren Gimbiya Huwaila kuwa tana shirin fucewa daga cikin falon ta sukaci karo da Jakadiya, ita kuma tana danno kanta domin ta shigo, har lokacin takalman ta riƙe suke a hannun ta, da alamun bata sanya su ba a haka ta tawo tun daga can ɗakin ta har nan. Da sauri Jakadiya ta miƙa hannu tana mai riƙo hannun Gimbiya Huwaila, sabo da ganin da tayi tana shirin fucewa kamar bata ganta ba. Janta Jakadiya tayi cikin sauri suna masu nufar ɗakin ta, ba tare da tace mata komai ba. Suna shiga cikin bedroom ɗin Jakadiya ta saki hannun Gimbiya Huwaila tana mai juyawa ta rufe ƙofar bedroom ɗin, tukun ta sake juyowa ga Gimbiya Huwaila data ɗora tafin hannun ta akan goshin ta tana mai sakin numfarfashi, tare da rumtse idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su akan fuskar Jakadiya, lokaci ɗaya duka sun canza launi sunyi jajahur yacce kasan gauta. "Shin meye hakan ya faru Jakadiya? Tayaya ma za'a ce Fulani ta haihu, haihuwar ma kuma Ɗa namiji, Ɗa namijin ma kuma mai rai, tayaya hakan ya faru ne Jakadiya?" Gimbiya Huwaila ta faɗa a wani irin haukace tana mai zagaya cikin ɗakin nata. "Nima abun da ya ɗaure mun kai kenan, ya kuma rikita ni Uwar Sarkin Gob..." "Dakata haka Jakadiya!" Gimbiya Huwaila ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai ɗagawa Jakadiya hannu, tare da rumtse idanuwna ta, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai faɗin. "Akan me zaki cigaba da kirana da wannan sunan kina samun rai, bayan kuma kin san duk ƙarya ne hakan kuma, bayan kuma keda kunnuwan ki kinji kalar sautin da tamabari ya futar yanzu, bayan kuma wanda ya futar shekaru goma da suka huce baya." Ta ƙarasa maganar da sakin numfarfashi. Yayin da ita kuma Jakadiya ta buɗe baki tana mai faɗin. "Karki fara faɗin haka yake Shugabata, kar kiyi kuskuren cewa zaki sare tun yanzu, domin kuwa haihuwar Yara biyu maza bashi ke nufin an haifo Sarki cikin su ba, dan kuwa sanin kanki ne hawa karagar Sarki sai wanda ya cancanta ko cikin Ƴaƴan Sarkin, sai kuma ya a jiye abubuwa da yawa, tukun yake da damar hawan ta, kinga kenan tunda har akwai waƴan ka'idojin, to ko ba mutuwa kina iya zamtowa Uwar Sarki muddin kin haifo Ɗa namiji kema." Jakadiya ta faɗa tana kallon Gimbiya Huwaila. Yayin da ita kuma tayi shiru tana mai lumshe idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai girgiza kanta, kana ta sake buɗe baki tana mai faɗin. "To duk naji wannan kuma na amun ta da hakan Jakadiya, amma kafun nan, wai taya ma akai hakan ta faru, taya ya za'ace Yaron yazo da rai, bayan kuma kince mun kinyi duk yadda nace kiyi tun a jiyan?" "Ta sanadin ikon Allah mana, domin kuwa cikin duka abubuwan da kika sani babu wanda banyi sa ba, sai dai kuma ko idan ita ɗin ce bata kwanta akan gadon ba, sabo da dama lokacin da naje ɗakin nata na same ta ne zaune agefen kujera kamar yacce na faɗa miki tun jiya, kuma ma ba wannan ba, shin wai kin manta ne haka kikece sai an baɗa mata maganin har kimanin sau ukku arana, sannan kuma ta kwanta aƙar-ƙashin layoyin tukun Ɗan zai mace?" Jakadiya ta faɗa tana kallon ta, yayin da ita kuma Gimbiya Huwaila ta dafe goshin ta da tafin hannun ta tana mai faɗin."Kashhhh!" Tukun ta tafi da baya da baya tana mai zuwa ta zauna yaraf akan gado, tare da cije leɓen ta na ƙasa da ƙarfi. "Ina da wata shawara, wacce nake ganin ko ita kawai akabi zamu cimma burin mu." Jajadiya ta faɗa daga inda take a tsaye, idanuwan ta akan fuskar Gimbiya Huwaila. "Mene abun tsayawa ɓata lokaci, bayan kuma kin san yana gab da ƙare mana, kawai faɗe ta kai tsaye inji ta mana, idan zatayi mai zai hana abita." Gimbiya Huwaila ta faɗa tana kallon Jakadiya. Hmmmm! "To ai sirri ne abun shugabata." Jakadiya ta faɗa bayan ta saki wani shegen murmushi, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai matsawa kusa da Gimbiya Huwaila. Sai da taje har gab da ita, tukun ta ranƙwafa tana mai kai bakin ta dai dai kunnen Gimbiya Huwaila da suke ɗauke da haɗaɗɗen ɗan kunnen gwal, tukun ta fara yi mata raɗa a cikin kunnen nata. Ta ɗauki kusan mintina biyar zuwa shida tana mata raɗan, tukun daga bisani ta janye bakin ta daga kan kunnen ta tana mai miƙewa tsaye fuskar ta ɗauke da murmushi tace. "To ya kika ji?" Shiru Gimbiya Huwaila tayi tana mai ɗan taune lowar lios ɗin ta, ba tare da tace komai ba, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mi faɗin. "Hakan ma tabbas zai yin, amma si dai ina son mu fara yin wanda na faɗa miki, idan baiba sai mubi ita wannan hanyar ɗin." Ta ƙarasa maganar itama da sakin murmushi. Haka dai duka haihuwar Ɗa namijin da Fulani tayi ta girgiza gaba ɗaya magautan su na cikin gidan, tare da ɗimauta su, sannan kuma ko wanne ya fara ɗaura ɗamarar sake sabon taku, wurin ganin sun kawar da duka yaran biyu, daga Babban Yaya har shi sabon Jinjirin da aka haifa yau. Yayin da masoyan su kuma murna da farin ciki suka cika su, har suka ransa inda zasu sa kansu, tun kafin agama idar da Sallah Asuba part ɗin Gimbiya Fulani ya fara cika da jama'a, masoya da ma maƙiya, sai dai kuma kowanne da manufar da yake zuwa da ita, su masoya domin taya ta farin ciki, yayin da su kuma maƙiya suke zuwa domin su fara ai'watar da aikin su. _BAYAN KWANA BAKWAI_ *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA* Tun daga bakin get ɗin gidan Bayi mutum zai fahimci yau ɗin suna wani gagarumin shagalin ne a ciki, sabo da yadda kiɗa ke tashi da matuƙar sauti tare da daɗi a ɓangaren Bayin, ga kuma manya manyan tukwane da aka ɗora akan duwar-watsu ana aikin basu huta sosai, kasancewar yau ɗin ta kasance sati ɗaya dai-dai da samuwar jinjirin nan, kuma dama a ƙa'idar Baƙar Masarauta koda Bayi ne suka haihu to ana barin su suyi shagalin suna ya junan su, a kuma cikin wurin su, hakan ne yasa tun jiya kuwa suke ai'yika, domin yau ɗin ce takasance ranar sunan sabon yaron da aka kawo musu. Sosai suke cikin farin ciki daga mazan su har matan su, kasancewar sai a irin wannan ranar ta suna idan tazo musu ne kawai suke samu suyi nishaɗi, ayi dariya, a kuma yi kiɗa ai rawa cikin farin ciki da junan su, ba tare da an daki kowa ba a cikin su. Acan ɗakin Iyar Bayi zaune take agefen shimfiɗar ta, rungume da ɗan jaririn a hannun ta tana mai muts-tsika masa mai a jiki, kasancewar yanzu ta gama yi masa wanka, domin kuwa ko ruwan zafin da tai masa wankan da shi ma ba'a janye sa daga wurin ba. Sai da ta gama shafe sa da mai tas, sannan ta ɗauki hoda ta shafa masa akan fuskar sa, tukun ta miƙa sa zuwa hannun wani mutumi da yake zaune a gefen ta shima da irin shigar su ta Bayi. Karɓar yaron yayi a hannun sa, sannan ya juya ɓarin sa na dama yana mai janyo wata ƴar ƙaramar roba a kusa da shi, tukun ya buɗe murfin robar. Wani baƙin abu ne mai kama da baƙin fenti a cikin ta, sai kuma tambarin Baƙar Masarauta ɗan ƙarami na soso, da yake a cikin baƙin fentin. Hannun sa na hagu yasan ya a cikin robar yana mai zaro soson, sannan ya futo da shi waje yana mai manna sa akan farar fatar jinjirin. Take kuwa tambarin masarautar tasu ya futo ɗas a jikin sa baƙiƙƙirin da shi, haka mutumin yay ta manna masa tambarin a fatar sa har kan fuskar sa, sai da ya tabbatar da ko ina tambarin ya futo, tukun ya janyo wani ɗan mitsitsin baƙin wando na yadi irin na jarirai, yana mai ɗago jinjirin, sannan ya sanya masa shi a jikin sa, kana ya buɗe baki yana mai faɗin. "Daga yau za'ana kiran sa da suna BIR, domin kuwa shine sunan da aka raɗa masa." Ya ƙarasa maganar yana mai miƙawa Iyar Bayi shi. Miƙo hannun ta tayi ta karɓe sa fuskar ta ɗauke da tsantsar far'a, tukun ta janyo wani sabon farin yadi tana mai sanya sa a ciki, ba tare da tasa masa ko riga ba, kamar yadda sauran bayi mazan wurin suke duka, babu mai riga a jikin sa. Kallon yaron tayi tana mai sakin murmushi, yayin da shi kuma yake ta faman yin wutsi-wutsil da ƙafafuwan sa, yana mai kallon wurare daban-daban, alamun yana cikin ƙoshin lafiya kenan. Sosai yaron ya ƙara girma da wayo a sati ɗayan da yayi kawai a duniya, ko kaɗan basa da damuwar komai, domin kuwa da zarar yayi kuka Iyar Bayi take ɗaukar madara ta basa, sannan kuma tasa zani ta goye sa a bayan ta idan ya gama sha. Fari ne kar yadda kasan a taɓa sa jini ya ɓullo, kyakkyawa ne sosai, domin kuwa ko kaɗan basa da makusa ta ko ina jinjirin, hakan yasa su kansu sauran Bayin suke matuƙar sonsa, sannan kuma kowa yake mararin ɗaukar sa. Miƙewa Iyar Bayi tayi tsaye da ɗan a hannun ta, tana mai faɗin. "Suna yayi daɗi, dan haka bara muje ashelan tawa jama'a, a kuma shiga tsakiyar fili ai rawar suna da jinjiri." Ta ƙarasa maganar tana mai fucewa daga cikin ɗakin. Kai tsaye ta doshi wurin da sautin kiɗa ke tashi, kasancewar anan ne ta hango dan-dazon jama'a maza da mata suna rawa. Itama rawar ta farayi tun daga wurin da take tana tafiya, a haka har ta ƙarasa cikin filin hannun ta riƙe da Ɗan. "Kai ku gafara nan gamu nan mun iso, suna ya raɗu yaro zama *BIR*." Ta faɗa tana mai kutsawa cikin filin rawar. Take kuwa a wurin kiɗa da rawar da ake suka sauya salo, yayin da jama'ar wurin kuma keta sakin tafi da rawa suna zagaye Iyar Bayi da jinjirin a tsakiyar su, bakunan su na furta. "Barka da zuwan BIR! Marhabun da zuwan BIR." Haka suke ta faɗe suna zagaye Iyar Bayi da jinjirin da matuƙar ƙarfi, sunayi suna sakin tafi. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Yau take ranar suna a cikin Wasarutar Wasai, hakan yasan ya ko ina ka kalla a cikin Masarautar kake ganin jama'a tun daga kan hadimai, kuyangu suna ta giftawa ta ko ina. Yayin da sautin bushe bushen sarewa, algaitu, kakaki, kiɗan ƙwarya, harma da tambura keta tashi a cikin wurare daban daban na masarautar. Ga kuma yadda bayi keta wucewa da niƙi-niƙin abinci kala-kala afarantai ta ko ina, sannan ga mutane da suke ta hucewa akan dawakuna sunci uban kwaliyya a jikin su, kamar yacce suka tsan-tsarawa dokunan nasu kwalliya. Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa, tun daga harabar part ɗin nata zakaci karo da maroƙa suna ta faman sakin kiɗa tare da kirare-kirare da matuƙar ƙarfi. Faɗi suke. "Allah ya raya mana Ahmad ɗan gidan Abdallah jikan Ahmadu, ɗan gidan sa'a haihuwar sa'a jikan sa'a, fari farar aniya, jinin sarauta kafu ƙarfin raini, Ɗa ga gimbiyar mata, shugabar kyawawa kuma uwar Sarkin gobe, Ahmadu jinin alkhairi haihuwar nasara, ƙani ga Sarkin mu na gobe Usmanu Babban Yaya. Allah ya raya mana Ahmadu Asadullahi Zakin Allah, mai Kakkani da yawa, mai Iyaye lodi-lodi, mai Yayye bila adadin. Kakan ka Ɗan Sarki Ubanka Ɗan Sarki, Mamar ka Ƴar Sarki kaima kuma Ɗan Sarki." Haka suke ta sakin kirari da bushe-bushe da matuƙar ƙarfi, kasancewar an riga da an raɗa suna tun asubahi, yaro yaci suna Ahmad, wato sunan Mahaifin mai martaba, hakan yasa tun a wurin mai martaba ya ƙara masa da wani sunan akai wanda za'ana faɗa masa, wato ASAD, ma'an ZAKI kenan. Hakan kuwa ba ƙaramun tafasa zuciyar magautan su ya sakeyi ba, barin ma yadda suka ga mai martaba na wani irin farin ciki da samuwar yaron, yadda kasan akan sa aka farayi masa haihuwa, ga kuma labarin da suka ji yana yawo, na cewar mai martaba da kansa yace yau akwai hawa irin hawan da ba'a taɓa yin sa ba a suna, za'ayi kilisa kalar kilisar da ba'a saba yin ta ba yau da yamma. Hakan kuwa ba ƙaramu sake lona musu rai yayi ba, sannan kuma suka ɗauki alwashin ganin bayan jinjirin nan kota halin ƙaƙa ne. Acan cikin ɗakin Gimbiya Fulani kuwa zaune take a gefen gadon ta taci uban Ado mai tsananin kyau da ɗaukar hankali da abubuwan kuɗi. Sanye take da wani ɗan ubansu farin less, mai ratsin adon baƙi a jikin sa da yayi matuƙar amsar jikin ta, dinƙin riga da zani da ɗan kwali, sai wasu irin saraƙunan gwal da suke manne a jikin kunnuwan ta da wuyan ta, suna ta faman ɗaukar ido, ga wani irin azababben ƙamshin turarruka masu matuƙar daɗi da suke futa daga cikin jikin ta. Yayin fa shi kuma Ɗan jarari Asad yake riƙe a hannun Hadima Larai, da itama taci uban Ado tana mai sake canza masa wasu kayan, sabo da futar da za'a sake yi da shi, harma da Gimbiya Fulani, sabo da yanzu aka aiko cewar mai Martaba yace su shirya su futo harabar gida za'ayi musu hotuna a tare. Hakan yasa ake canza masa wasu sababbun kayan, duk da dai waƴan can na jikin nasa da aka cire masa suma basu fi minti goma ba duka da sanya masa su ɗin. Sosai yaron ya ƙara girma da kyawu asati ɗayan da yayi a duniya. Kamar shi ɗaya sak da mahaifiyar sa, basu da bam-banci ko kaɗan. Cikin ƴan sakanni ta gama sanya masa kayan tas har takalmi, tukun ta ƙara fashe sa da wani haɗaɗɗen turare mai tsananin ƙamshi na jarirai. Tukun ta miƙowa Gimbiya Fulani shi, da itama ta miƙe tsaye tana mai yafa wani haɗaɗɗen mayafi a jikin ta. Karɓar sa tayi a cikin lafiyayen showel ɗin sa, tukun ta fara takawa tana mai dosar hanyar waje. Tana futa tabi wata ƙofa dake a cikin ɗakin nata, wacce zata sadata da part ɗin mai Martaba kai tsaye, domin kuwa da aka tashi tsara ginin gidan, sai da yasa akayi masa hanyoyin da zasu kaisa duka ɓangaren matan nasa ukku daga cikin part ɗin sa, ba tare da ya futa ta babbar ƙofa ba. Baifi minti goma tayi ba da shigar ta, sai ga sunan sun futo a jere ita da mai Martaba, ga kuma Babban yaya da yake daga bayan su da irin shigar mai martaba sak a jikin sa. Sanye suke da farar shadda mai tsananin kyawu da tsada, banda ƙyalli da ɗaukar ido babu abun da take yi, yayin da kawunan su kuma suke ɗauke da baƙaƙen tare da farin rawani, kamar yacce takalman ƙafafuwan su suka kasance baƙaƙe suma, sai kuma wata haɗaɗɗiyar baƙar al'kyabba mai adon fari da take sanye a jikin su, su duka biyun. Haka suka cigaba da takowa mai Martaba rungume da Asad a hannun sa. Suna shigowa Babban falo gaba ɗaya matan dake zaune a cikin sa suka rangaɗa wata mahaukaciyar buɗa mai tsananin ƙara, suna masu miƙewa tsaye. Yayin da masu hotuna kuma suka fara ɗaukar su tun daga nan tare da video, a haka har suka ƙarasa harabar gidan. Suna futowa maroƙa da fadawa sukayo kan su gaba ɗaya, ko wanne da kalar kirarin da yake yi gare su. "Barka da futowa Asadullahi, barka da isowa Zakin Allah, barka da isowa Yariman Wasai! Yarima Damisan Yan Sarki, Yarima Ɗan masu gari, Ɗan bakin ruwa da ciyawa, Ɗan uban gabasawa." Gaba ɗaya maroƙan dake wurin suka faɗa a tare, suna masu sakin kiɗa duk alokaci ɗaya, yayin da su kuma Fadawan Sarki da suke tsaye a harabar wurin suka matso gare su da sauri, suna masu zagaye su, bakunan su na futar kalmomin. "Barka da futowa Sarkin Sarakai, barka da futiwa toron giwa! Sakaka Baban baƙo! Uban gabasawa! Taka lafiya barden mahadi! A Lafiya bahau da wani ba saukan wani! Lafiya hana kangara! Lafiya bango madafar Bayi! Lafiya hadarin ƙasa maganin mai kabiɗo! Lafiya dubu jiran mutum ɗaya! Lafiya gagara gasa! Uban Yarima Usmanu, Uba ga Asadullahi sabon yaro, miji ga kyakkyawar Gimbiya mahaifiyar Sarkin mu na gobe. Taka a lafiya jinjirin wata shakallo." Fadawan keta faɗe suna masu binsu a baya, a haka har suka ƙarasa wurin da za ayi musu hotunan, tukun suka kauce suka bada wuri aka dinga musu hotuna kala-kala, sannan kuma da mutane daban -daban, domin kuwa harda su Gimbiya Huwaila da Gimbiya Amina sai da akayi musu hoton tare, duk da dai ko kaɗan bawai dan ransu yana soba suka tsaya akai hoton, sunyi ne kawai gudun kar suƙi zuwa mai Martaba ya zargi wani abun, kasancewar shi da kansa ya aika a kira su suzo ayi hoton. Haka dai aka yini shan-shagalin suna a cikin gidan har zuwa yamma. Tukun aka sake sabon shiri, sabon wanka, sannan kuma a kayi sabuwar futowa ana tafiya filin Hawa, kasancewar dama da yamna aka tsara za'ayi Hawan sunan. Sosai akayi Hawa a kai wasa da dokuna irin wanda ba'a taɓa

Chapter 17 of 76