da suka amasa sunan su na masu kuɗi, wayan da futa ƙasar waje ma ba tai musu huya.
Cikin tsantsar hanzari mai martana dake riƙe da Yarima Asad har lokacin a jikin sa ya furo daga cikin motar da wani Bafade ya buɗe masa ita.
Ba tare da ya tsaya ɗora sa akan gadon marasa lafiyan da wasu nurses suka kawo wurin ba ya huce gaba rungume da abun sa, ganin hakan da doctor'n yayi ne ya sanya sa bin bayan sa cikin sauri shima.
Ko da aka zo shiga da Asad da ya zamto tamkar gawa ɗakin da za'ayi masa gwa-gwajen, dagewa mai martaba yayi yace sai ya shiga shima, amma likitan yay ta basa haƙuri yana mai basa tabbacin zai tashi insha Allah, har ya samu ya shawo kansa ya haƙura da shigar, ta sanadin bakin da ƴan uwan sa suka sanya akan yayi haƙurin.
Tukun ya juya yana mai zuwa ya zauna akan kujerar da take a bakin ƙofar ɗakin, tare da ɗaga kansa sama ya lumshe idanuwan sa, yana mai jin zuciyar sa na tsantsar tafasa da ƙuna.
Yayin da su kuma likitocin suka shige cikin ɗakin dukan su, domin su fara ai'watar da abun da ya kamata suyi.
Acan cikin masarauta kuwa, ɓangaren Gimbiya Fulani, gaba ɗaya mutanen da suke a cikin falon jugum-jugum sukayi a lokacin da Mai Martaba ya fuce da Yarima Asad, yayin da Gimbiya Fulani kuma take wani irin kuka tana mai yiwa ɗan nata addu'oi, domin kuwa ba ƙaramun firgita tayi ba da halin da tagan sa a ciki, barin ma kuma da taji wannan azababben zafin da yake futa daga cikin jikin sa.
Shima Babban yaya gefe ya koma ya zauna yana mai aikin rusar kuka, domin kuwa shi duk a tinanin sa ƙanin nasa ya riga da ya mutu.
Suna cikin wannan halin sai ga Jakadiya nan ta afko cikin falon a matuƙar ruɗe, tana mai yowa wurin da suke.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, yau nayi mummunan ji, naji labarin da ya hargitsa ƙwa-ƙwalwa ta, shin ina ma shi shelelen yake ne yanzu?" Jakadiya ta faɗi haka a hargitse, hannun ta dafe da kanta.
Shiru gaba ɗaya mutanen dake wurin sukayi ba tare da wani ya tanka mata ba, jin hakan da tayi ne ya sanya ta sake buɗe baki cikin muryar ta da take tsantsar rawa, alamun kuka na shirin ƙwace mata tace.
"Dan Allah kuyi mun magana mana, ku faɗumun inda Shalelen Mai Martaba yake tun kafin zuciyata tai bundiga."
"Kiyi haƙuri Jakadiya, Mai Martaba ya ɗauke sa sun tafi asibiti ance."
Ɗaya daga cikin matan da suke zaune a wurin jugum-jugum ta faɗa, tana mai dafa kafaɗar Jakadiya da tashin hankali ƙarara ya bayyana akan fuskar ta.
Acan Asibiti kuwa sai da har likitocin suka ɗauki tsawon awa ɗaya suna binciken abun da ke damun Asad, amma basu gano komai ba da zasu iya cewa shi yayi sanadin sa-sa sumar, domin kuwa ko ƙirjin nasa da akace doki yabi takai su ba suga wani abun da ya same saba kwata-kwata, wato dai normal ƙirjin nasa yake kamar na kowa, sai dai kuma zuwa yanzu sun samu numfashin sa na futa dai-dai, ta sanadin oxygen da suka sanya masa, kana kuma bugun zuciyar tasa shima ya koma ya saitu kamar yacce yake a baya, sai dai kuma zafin jikin nasa ne har yanzu babu abun da ya ragu a kan na baya, sai ma sake ƙaruwa da yake yi fiye da da.
Jiki a tsantsar saɓule Doctor Muhammad ya juya yana mai kama hanyar futa daga cikin room ɗin.
Yayin da sauran Nurses ɗin kuma suka samu wuri suna masu zama akan kujeru, kamar yacce tsarin Asibitin yake, wato su da kansu suke jinyar patiant ɗin su ba wai ahalin mutum bane zasu zauna masa, sai dai kuma idan mutum ya takura akan shi zai zauna suna barin sa, tun da dai su baza a fasa basu kuɗin su ba cas, kamar yacce kowa ke bayarwa.
Doctor Muhammad na tura kai waje Mai Martaba da yake zaune akan wata haɗaɗɗiyar kujera da take abakin ƙofa anyi-anyi ya shiga office amma yaƙi, ya miƙe tsaye zumbur yana mai faɗin.
"Ya jikin nasa doctor, ina fatan dai yaro na yaki sauƙi yanzu ko?"
Ya watso masa tambayoyin a jera, sannan kuma a matuƙar ruɗe.
"Kayi haƙuri mu ƙarasa zuwa cikin office ranka ya daɗe."
Cewar Doctor Muhammad yana mai ɗan durƙusawa ya rage tsayin sa a gaban Mai Martaba, kamar yacce ya saba a koda yaushe.
Yayin da shi kuma Mai Martaba ya rumtse idanuwan sa yana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa, tukun daga bisani ya buɗe su akan fuskar doctor ba tare a yace komai ba.
Ganin hakan da Doctor Muhammad yayi ne ya sanya sa yin gaba yana mai faɗin.
"Bismillah'n ku to."
Gaba ɗayan su miƙewa sukayi suna masu bin bayan sa, ko wanne a cikin su zuciyar sa cike da son jin abun da ke faruwa, yayin da wasu daga cikin su kuma suke murna da jin daɗi, tare da fatan Allah yasa mutuwa yaron yayi, idan kuma bai ba zaiyi, wato magautan su kenan, munafukai masu fuska biyu, su kuwa masoyan su cike suke da fargabar jin abun da Doctor zai ce.
Tamfatse-tsen office ne mai matuƙar girma da kyan tsari.
Jere yake da wasu haɗaɗɗun kejeru masu tsanin kyau da taushi acikin sa, yayin da daga can gefe ɗaya na cikin office ɗin kuma wani haɗaɗɗen table yake kafe a wurin, sai daga bayan table ɗin kuma kujera ce mai tsantsar kyau irin wacce ke juyawa da mutum idan yana kai, yayin da saman teburin kuma yake ɗauke da takaddu tare da system akan sa.
Direct doctor muhammad ya huce zuwa kan table ɗin, yayin da su kuma su Mai Martaba suka zazzauna akan kujerun nan suna masu fuskantar sa.
Gyaran murya yayi yana mai sa yatsun hannun sa ya cire maɓalli ɗaya daga cikin maɓallayan dake jikin gaban rigar sa.
Kana daga bisani ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin.
"Haƙiƙanin gaskiya dai shi ne, munyi iyakar yin mu, sannan kuma munyi amfani da duk abun a ya kamata muyi, domin mugano abun da ke damun sa, amma sai dai kuma gaba ɗaya binciken da mukayi babu wanda yay mana nuni da wata matsala da take tattare da shi, asalima duka result ɗin suna nuna negative ne na duka tests ɗin da mukayi masa, sai dai kuma munyi nasarar dai-dai ta numfashin sa tare da bugun zuciyar sa, but yanayin zafin jikin nasa ne har yanzu babu abun da ya ragu, sannan kuma shima ɗin bai farfaɗo ba."
Doctor Muhammad ya ƙarasa maganar cikin sanyi, domin kuwa ya yi iyakar yin sa amatsayin sa na cikakken Medical Doctor, amma bai gano komai na dan gane da abun da ke damun yaron ba, kuma baya tinanin ko sun bar nan sunje wani wurin za adace ɗin, domin kuwa gaba ɗaya kayan ai'yukan da yake amfanni da su a cikin asibitin nasa duk irin na ƙasashen turawa ne, wato irin waƴan da ake amfanni dasu acan ɗin ma idan an kai mutum, kasancewar sa mutum wanda yake da kuɗi, sannan kuma ya taso cikin ruwan kuɗi a gidan su, domin kuwa shi kansa duka karatun nasa ba a Ƙasar Hausa yayi sa ba, hatta da primary kuwa.
Wani irin zazzafan numfashi Mai Martaba ya fesar, yana mai jin kansa na sara masa, ga kuma idanuwan sa da sukayi jajajir, alamun ba ƙaramun tashin hankali yake ciki ba.
Galadima ne ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin.
"To yanzu mene abunyi kuma a gaba Doctor, bi ma'ana me kake ganin zaku iya sake yi masa, ko kuma wane wurin kake tinanin zamuje bayan nan wanda suke da kayan aikin da sukafi naku?"
Girgiza kai Doctor Muhammad yayi yana mau ɗan yin shiru, tukun daga bisani ya buɗe baki bayan ya ɗago ya kalle su, yana mai faɗin.
"Haƙiƙa bazance kuma ga wurin dana sani ba wanda nake da tabbacin yafi nan, domin kuwa a duk faɗin Jahar Wasai babu wani Asibiti da ya kai namu, sabo da mu kaɗai ne muke amfani da kayan aiki irin waƴan da ake afanni da su a Asibitocin mu na ƙasashen waje, amma sai dai kuma ni atawa shawarar sai nake ganin mai zai hana a gwada na Islamic chemist, wato na musulunci ko Allah zai sa adace."
Ya faɗa yana mai kallon su.
Yayin da su kuma dukan su sukayi shiru ba tare da wani ya iya furta komai ba.
Sun ɗauki tsayin mintina biyar a hakan, tukun daga bisani mai martaba ya buɗe bakin sa bayan yasa yatsun hannuwan sa ya sharce gumin dake tsats-tsafowa akan goshin sa, yana mai faɗin.
"Ina ganin shawarar taka ita zamubi Doctor, dan haka tun yanzu nake tinanin zamu shirya tafiyar, domin kuwa akwai wani Babban malami na da yake zaune a London, malami ne masanin Al'qur'ani tare da litattafai, da kuma magun-guna irin na Islamic, domin kuwa a wurin sa nayi karatu na a lokacin da nayi zaman Saudiyya, to daga baya ne yanayin ai'ki ya mayar dashi can ƙasar London, dan haka ayau-yau ɗin nan zamubi Private Jet mu tafi."
Ya ƙarasa maganar yana mai miƙewa tsaye.
Hakan da suka ganine ya sanya su suma dukan su suka miƙe tsayen har doctor, tukun suka juya suna masu fucewa aga cikin ɗakin.
Tamkar gawa haka Mai Martaba ya sake ɗakko Asad a hannun sa bayan anyi dischargen nasu, domin kuwa kwata-kwata yaƙi ya bari aɗora sa akan gadon marasa lafiya, shi da kansa yake ɗaukar abun sa.
A haka duk suka shige cikin motocin su da dogarawa suka yi musu ƙawanya, tukun matuƙan ciki suka jasu suna masu fucewa daga cikin hospital ɗin.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka fara cuku-cukun tafiyar su Mai Martaba Kasar London.
Misalin ƙarfe goma na dare dai-dai Private Jet ɗin da suka kama wanda ya zamto su biyun ne kawai acikin sa, wato daga Mai Martaba sai Asad ɗin, ya ɗaga zuwa sararin samaniya.............✍
_Kadanba na gaji haka_ 😟
*BAƘAR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 20*
Sosai Gimbiya Fulani da duk wani makusancin ta masoyin ta kuma suka shiga cikin matsanan ciyar damuwa, jin abun take tamkar Al'mara, domin kuwa lafiya ƙalau Asad ya bar wurin ta alokacin da aka kira sallahr la'asar, suka tafi masallaci tare da Al'amin, ba tare da yace mata yana ko ciwon kai ba.
Kusan duk jama'ar dake cikin masarautar sun shigo sun mata jaje, sai ƙalilan ne kawai basu shigo ba, irin su Gimbiya Huwaila da kuma Gimbiya Amina kishiyoyin ta.
Sai dai kuma ko kaɗan abun bai dama ta ba da rashin zuwan nasu, sannan kuma bai bata mamaki ba, domin kuwa tariga da ta daɗe da sanin babu wata mai ƙaunar ƴaƴan nata a cikin su,.
Hakan yasa ta duƙufa kaiwa Allah kukan ta, tana mai roƙon sa akan ya tada kafaɗun Ɗan nata.
_LONDON_
Sai a washe garin ranar da suka isa, tukun mai martaba ya fara bincikar gidan Sheikh Yaƙub, wato malamin nasa, bai wani sha wata wahala ba wurin neman gidan ya gano sa, sabo da dama ba wannan bane zuwan sa na farko.
Cikin girmamawa tare da mutun-tawa sheikh Yaƙub ya tarbi Mai Martaba da hannu bibbiyu a cikin falon sa da yake sauke baƙin sa cikin sa.
Bayan sun gama gaisawa ne Sheikh Yaƙub ya buɗe baki idanuwan sa akan Asad da yake kwance a kan cinyar Mai Martaba, tamkar yadda yake jiya yana mai faɗin. "Yaron ba lafiya ne, ko kuwa bacci yayi maka a hanya ne?"
Girgiza kai Mai Martaba yayi yana mai kai idanuwan sa kan fuskar Asad ɗin da yayi wata mahaukaciyar rama daga jiya zuwa yau a hakan da yake, tukun daga bisani ya ɗago kai idanuwan sa akan fuskar Sheikh Yaƙub, yana mai faɗin. "Lafiyar ce dai babu Ya Sheikh, domin kuwa tasanadin ta mukazo nan wurin naka ma." Mai Martaba ya faɗa murya asanyaye, cikin harshen larabci kamar yadda suke maganar da shi dama.
"Subahanallahi! Meke damun sane haka to?"
Shikh Yakub ya tambaya yana mai miƙewa tsaye daga kan kujerar da yake ya nufi wurin su mai martaba.
Gyaran murya mai martaba yayi, tukun ya fara bawa Sheikh Yaƙub labarin duk abun da yasan ya faru har zuwa asibitin da sukayi, da kuma shawarar da likitan su ya basu na cewa su haɗa da maganin addini.
Girgiza kai Sheikh Yaƙub yayi alokacin da ya gama jin bayanin Mai Martaba, hannun sa riƙe da ƴan yatsun Asad.
Tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Tabbas kuwa ba abun mamaki bane hakan ya kasance, domin kuwa mutum babu abun da bazai iya ba, amma in banda rashin imani ma duka-duka nawa wannan yaron yake, me yasa ni ne ma da har za'a cutar da shi irin haka, but ba damuwa insha Allah zai warke tas nan kusa bada jimawa ba."
Sheikh Yaƙub ya faɗa yana mai sa hannu ya ɗauki Asad daga kan cinyar mai martaba, tukun ya juya yana mai dosar wata ƙofa da take a cikin fallon, bayan ya cewa Mai Martaba ya biyosa zuwa ciki.
Ɗan madai-daicin ɗaki ne mai matsakaicin girma.
Ɗauke yake da magun-guna kala-kala irin na addini, tun daga kan na ruwa har zuwa na gari, da suke aje akan kantocin da suka yiwa ɗakin ƙawanya.
Yayin da daga ɓari ɗaya kuma aka ajiye wani ɗan gado irin na Asibiti.
Direct Sheikh Yaƙub ya huce da Asad zuwa gaban wannan gadon na cikin ɗakin, tukun ya ɗorsa akan sa, kana ya juyo ɓarin da mai martaba yake yana mai masa nuni da wata kujera da take ajiye a gefen gadon, yace ya zauna a kanta.
Hannu mai martaba yasa ya matsar da kujerar bakin gadon, tukun ya zauna akai, yana mai riƙo tafin hannun Asad cikin nasa yana murzawa.
Sosai yake jin tausayin ɗan nasa na ratsa ko wane lungu da saƙo na jikin sa, yana kwanciya a ɓargon sa.
Kana yana mai jin a ransa muddin abun nan ya zamto gaskiya, wato asirin akaiwa ɗan nasa, kuma ya zamto ya gano wanda ya ai'kata masa hakan, to kowaye shi sai yaga ƙarshen fushin sa, sai ya masa hukunci na dai-dai laifin da ya ai'kata masa.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba Sheikh Yaƙub ya fara haɗa magun-gunan sa, tukun ya matso gaban gadon da Asad yake hannun sa riƙe da wata ƴar kwalba, wacce take ɗauke da wani kalar mai a cikin ta.
Dangwalar man ya dinga yi yana mai shafa sa asaman goshin Asad da kuma kan ƴan tsunsa na ƙafa, tukun daga bisani ya juya bayan ya gama shafa masa, yana mai ɗauko wani turare ya zubasa a cikin electric burner ta turaren wuta, bayan ya maƙala ta a jikin socket.
Take kuwa ɗakin ya turnuƙe da wani irin hayaƙi mara daɗi ko kaɗan.
Ajiye sa yayi agefe yana mai juyawa ya tsiyoyo wani ruwa da yake a cikin jarka a cup, kana ya dawo gaban Asad yana mai zuba ruwan atafin hannun sa, tukun ya yarfa masa shi akan fuskar sa, sannan aƙarshe ya koma ya juye masa ruwan duka a fuska, ɗan sauran da yayi ragowa a cikin kofin kuma ya sanya mai martaba ya ɗago masa da kan sa tare da buɗa masa bakin sa, tukun ya tsiyaya masa shi a ciki yana mai hucewa cikin-cikin Yaron.
Yayin da hayaƙin nan kuma ke cigaba da tashi har lokacin yana bugun fuskar Asad.
Ruwan na gama shiga cikin-cikin sa ya fara ɗan jujjuya kai idanuwan sa na motsawa, amma bawai sun buɗu bane ba.
Ganin hakan da mai martaba yayi ne yasan ya sa zaro idanuwa da sauri, sannan kuma cikin tsantsar farin ciki, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Malam kagani fa yana motsi da kai yanzu, kuma ma naga kamar idanuwan nasa yake shirin buɗewa.
Baba na! Baba na!! Baba na!!! Buɗe idanuwan ka kaganni kaji."
Mai Martaba ya faɗa cikin sauri yana mai cigaba da murza tafin hannun Asad.
"Hakan shike nuna tabbacin sihiri ne akai masa, kuma Insha Allah ba zaiyi wahalar samun sauƙi ba, amma sai dai kuma wannan motsin da yake bashi ke nufin zai buɗe idanuwan nasa yanzu ba, dan haka ina son ka kwantar da hankalin ka, insha Allah zai warke a nan kusa."
Cewar Sheik Yaƙub yana mai dafa kan Mai Martaba da shima duk ya zurma sosai, sabo da tashin hankali da fargabar kar ya rasa ɗan nasa.
Jinjina kai Mai Martaba yayi yana mai faɗin.
"Allah ya basa lafiya to."
"Amin! Amin!!" Sheikh Yaƙub ya faɗa yana mai komawa ya cigaba da haɗa magun-gunan sa.
Har suka ɗauki tsawo sati ɗaya da zuwa dai-dai Asad bai buɗe idanuwan sa ba, sai dai kuma akullum motsin sa na ƙara ƙaruwa fiye dana da daga kwancen da yake, domin kuwa yanzu har hannun sa yana ɗagawa ya ɗorsa akan ƙirjin sa, hakan yasa Mai Martaba yake ƙara kwantar da hankakin sa, sabo da cigaban da yake gani shida kansa a kullum.
Yayin da shi kuma Sheikh Yaƙub ya duƙufa wurin nemawa yaron magani da gasken-gaske.
Acan Ƙasar Hausa kuwa, a Jahar Wasai cikin Masarautar Wasai.
Sosai Gimbiya Fulani tayi wata irin kwantsamewa, ta jeme ta rame ta kuma yi duhu, sabo da tsan-tsar fargabar da take ciki, ga abinci da bata iya ci, sannan kuma ga rashin samun ishash-shen bacci, domin kuwa kwanan tsaye take tana kaiwa Allah kukan ta.
A ɓangaren Babban Yaya da sauran ƙannen sa suma sosai suka rame suka kwantsa me, barin ma Babban Yaya da shima bai fiye yin wadataccen bacci ba, sabo da yadda yake raba dare yana yiwa ƙanin nasa addu'oi cikin sallolin da yake yi.
Fannin Al'amin shima kullum rana sai yayi kukan rashin abokin sa, domin kuwa gaba ɗaya ma baro part ɗin su yayi ya dawo wurin Gimbiya Fulani, acewar sa da zarar su Asad sun dawo shi zai fara ganin sa.
Hakan da Gimbiya Fulani ta gani ne yasa tasanya akayi musu visa ta zuwa London su ukku, wato ita, sai Babban Yaya, sai kuma shi Al'amin ɗin, yayin da jirgin nasu zai tashi a sati mai zuwa, wato rana ita yau.
Har yau cikin duka kishiyoyin nata biyu babu ɗaya data zo mata jaje, hakan ne yasa gaba ɗaya ta ɗiga alamar tambaya akan su, wato take zargin sune suke da sa hannu akan ciwon ɗan nata, sai dai kuma babu wanda ta faɗawa hakan, kana kuma koshi mai martaba tace bazata faɗa masa basu zo ɗin ba.
_BAYAN SATI ƊAYA_
Yau ta kama sati biyu da fara yiwa Asad magani kenan, amma sai dai kuma har yau bai buɗe idanuwan sa ba, sai dai kuma a kullum jikin nasa na ƙara yin kyau daga kwancen da yake, sannan kuma zuwa yanzu gaba ɗaya zafin da jikin sa keyi ya ɓace tas, wato tempreture sa ta dawo dai-dai tamkar ta kowa.
Misalin ƙarfe ukku na rana an agogon nan london, su Gimbiya Fulani suka ƙaraso cikin gidan Sheikh Yaƙub, ta sanadin driver'n sa da yaje ya ɗauko su a airport.
Sosai dattijuwar matar Sheik Yaƙub ta musu tarbar mutunci cikin sakin fuska.
Basu iya cin wani abun kirki ba daga cikin lodin abubuwan da aka ajiye musu a gaban su, suka miƙe tsaye suna masu faɗin wazai kai su wurin su Asad ɗin, kasancewar suna can cikin ɗakin maganin har shi Sheik Yaƙub.
Ita da kanta ta sanya hijab ɗin ta tana mai shiga gaba tace su biyo ta.
Shigar su cikin ɗakin tayi dai-dai da lokacin da Asad ya fara wani irin girgiza kai da matuƙar ƙarfi, yana mai ƙiƙƙifta idanuwan sa, sabo da wani tirare da Sheikh Yaƙub ya shaƙa masa a cikin hancin sa.
Da sauri dukan su suka ƙarasa zuwa gaban gadon suna masu tsayawa cirko-cirko, yayin da wasu irin hawaye masu mugun gudu suka ɓalle daga cikin idanuwan Gimbiya Fulani suna tsiyaya akan kuncin ta, sabo da yadda taga gaba ɗaya ɗan nata ya rame yayi baƙ,i yarce kasan ba kakkyawan Asad ɗin ta ta ɗan gayu ba.
Ahankali ya fara buɗe idanuwan sa har ya buɗe su duka akan fuskar jama'ar dake wurin, tukun daga bisani yayi saurin mayar dasu ya rumtse yana mai kai tafin hannun sa ya shafe su, sabo da wani irin haske da ya dalle masa idanuwan alokacin da ya buɗe sun.
Yayin da su kuma duka jama'ar a suke wurin suka buɗe baki cikin tsanrsar farin ciki, suna masu faɗin.
"Alhamdulillah."
Kana Gimbiya Fulani ta ɗaga ƙafafuwan ta cikin sauri tana mai zuwa ta zauna abakin gadon, tukun ta kamo tafin hannun Asad ta riƙe sa a cikin nata tana murzawa, bakin ta na furta kalmar.
"Zaki! Zaki!! Zaki!!! Buɗe idanuwan ka ka ganni kaji."
A hankali ya fara buɗe idanuwan nasa har ya sake buɗe su tas akan fuskar Mamy'n tasa.
Gaba ɗayan su murmushi suka saki suna masu matsowa gaban gadon cikin tsantsar farin ciki.
Da sauri Mai Martaba ya matsa kusa da shi yana mai miƙa hannun sa ya riƙo ɗayan tafin hannun Asad da shi, tukun ya buɗe baki cikin farin ciki shima yana mai faɗin.
"Baba na! Baba na!! Barkan ka da tashi kaji."
A hankali Asad ya sake juyawa yana mai kai idanuwan sa kan fuskar Mai Martaba.
Yayin da shi kuma Mai Martaba ya sakar masa murmushi yana mai faɗin.
"Sannu kaji Baba na."
Amma sai dai kuma gaba ɗaya Asad ɗin baice komai ba tun da ya buɗe idanuwan, sai kallon kawai da yake binsu da shi gaba ɗayan su.
Yayin da su kuma suke ta sake matsawa gare sa duka har Al'amin, kowa na yi masa magana.
Sai da suka ɗauki tsayin mintina goma suna abu ɗaya amma Asad bai tankawa kowa ba, ganin hakan da Sheikh Yaƙub yayi ne ya sanya sa cewa su ɗan matsa daga bakin gadon su basa wuri.
Take kuwa duk suka jajja baya, sai Mai Martaba ne kawai bai kauce ba.
"Ina yini malam."
Gimbiya Fulani da su Babban Yaya suka faɗa, kasancewar basu samu damar gaishe saba la okacin da suka shigo, sabo da murnar ganin Asad da sukayi ya buɗe musu ido data ɗauke musu hankali.
"Lafiya ƙalau, fatan kuma kun iso lafiya."
Sheikh Yaƙub ya faɗa yana mai zama abakin gadon.
Da lafiya ƙalau suma suka amsa masa, yayin da shi kuma ya miƙa hannun sa ya mai riƙo tafin hannun Asad ɗaya da yake ta kallon sa da shi.
Tukun ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin.
"Asad! Asad!"
Ƙala Yarima Asad bai ce masa ba, sai idanuwa kawai da yake binsa da su.
"Asad kayi magana mana, ya jikin naka ne?"
Sheikh Yaƙub ya sake faɗe yana mai ɗan girgiza sa, amma still dai shiru sai kallon kawai, hakan da ya gani ne yasa ya ɗago sa daga kwancen da yake, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin.
Sauko ƙasa to kaji."
Take kuwa Asad ya fara zuro ƙafafuwan sa ƙasa, amma baice komai ba, ganin hakan da yayi ne yasa yace masa koma kazauna to basai ka sakko ɗin ba kaji."
Komawar yayi ya zauna kuwa, yana mai jin gina da bango ya cigaba da binsu da idanuwa.
Yayin da shi kuma Sheikh Yaƙub ya juyo gare su, gaba ɗayan su da duk sunyi shiru, yana mai kallon su murya asanyaye yace.
"To duk da haka dai Al'hamdullilah zamuce, domin kuwa munga sauƙi sosai fiye da baya, tun da gashi nan yanzu yana ganin kowa kuma yana jin muryar kowa, sannan kuma yana iya motsawa har tafiya ma zaiyi, sai dai kuma inda matsalar take a yanzu itace rashin magana, wato dai a gaskiya baya magana, kuma ba zai iya magana ba a yanzu, sai dai ko a nan gaba."
Sheikh Yaƙub ya ƙarasa mganar cikin sanyi.
Yayin da su kuma dukan su sukayi shiru, sai hawaye da suka ɓalle daga cikin idanuwan Gimbiya Fulani.
"To Alhmdulillah, hakan ma ai yafu da sosai, kuma maganar ma insha Allah muna saran zaiyi ta a nan kusa."
Mai Martaba ya Faɗa cikin sanyi yana mai murza hannun Asad ɗin.
Yayin da shi kuma Shekh Yaƙub ya miƙe tsage yana mai juyawa ya fuce daga cikin ɗakin da shi da matar sa, sabo da su basu damar tattaunawa.
Abu fah kamar ƙarami sai gashi yana shirin zamtowa Babba, domin kuwa har kawo yau da su Gimbiya Fulani suka cika sati ɗaya da zuwa kuma suke shirin juyawa a yau ɗin, Asad baiyi magana ba, wanda hakan kuma ba ƙaramun tayar musu da hankali yayi ba, domin kuwa iyakar su da shi kallo ne kawai.
A haka dai rai babu daɗi suka rabu, driver'n Sheikh Yaƙub ya kai su airport, domin su koma Ƙasar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 76