Share this page
ka akan kayi gaggawar komawa wurin waƴan da suka aiko ka zuwa gare ni kasanar musu da cewar banyi ba, domin ko bazan taɓa yi maka ba har abada, kamar yacce kaima bakai mun ba, kuma baka da abubuwan da zanyi tinanin zakayi mun ko agaba!" Ta ƙarsahe maganar ƙasa-ƙasa tana mai jifan sa da wani irin matsayacin kallo, tukun daga bisani ta juya tana mai sauka daga kan shmfiɗar, sannan ta sanya takalmam ta, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar hanyar da ta biyo ba tare da ta tsaya jin ta bakin sa ba. Yayin da shi kuma Yariman Yamma lokaci ɗaya yana yin sa ya sauya, kana gaba ɗaya annurin dake kan fuskar sa ya ɓace ɓat, idanuwan sa kuma suka kaɗa sukai jajajir yana mai kallon ta, kafin daga bisani kuma ya buɗe baki cikin kaushi yana mai faɗin. "Shin waya baki izinin tafiya ne da har kika juya kika tafi?" Cak Gimbiya Haddiyal ta tsaya daga inda take, sabo da furucin sa da taji ya daki dodon kunenn ta da ƙarfi, rumtse idanuwan ta tayi daga inda take ba tare da ta juyo ba, haka kuma bata cigaba da tafiya ba, sai zallar turiri kawai da take jin ranta na mata, tana mai tinanin kalar amsar da zata basa idan ta juyo. Yayin da shi kuma ya miƙe daga kishingiɗen da yake yana mai zuwa ya sanya takalman sa, tukun ya fara ɗaga ƙafa cikin takun sa na isa yana mai dosar inda take. Direct ya huce bayan ta yana mai zagayawa ya tsaya daga gaban ta gab da ita, tukun ya ranƙwafo da kansa yana mai rage tsayin sa ya zamto fuskar sa ta dawo saitin tata fuskar, tayarce har suke jin dirar numfashin junan su. Kallon-kallo suka fara aikawa junan su da shi ba tare da wani daga cikin su yace tak ba, tukun daga bisani shi Yariman Yamma ya buɗe baki cikin kakkausar muryar sa yana mai faɗin. "Ke atinanin ki har akwai wani jarumin ne bayan ni aduk faɗin jahar nan da ƙetaren ta, ko ko azaton ki akwai wani mutum wanda zai iya jure raɗaɗin tsumagiya ta? Shin shi ɗin ɗan wace masarauta ne ma da farko?" Ya faɗa ƙasa-ƙasa tayarce ita kaɗai ce zata ji yana mai kafeta da idanuwan sa, kamar yacce itama ta kafesa da nata, tukun daga bisani ya saki wani shu'umin murmushin da yayi ai'nahin futo da kyawun sa, sannan ya ɗora da cewar. "Agaskiya nayi matuƙar jin daɗin sauraron wannan labarin daga bakin ki, domin ko ada ina tinanin bani da abokin karawa wanda zamu gwada ƙwanji tsakanin ni da shi wurin neman ki, amma sai gashi yau naji cewar akwai sa daga bakin ki, hakan kuwa ki sani ba ƙaramun farin ciki ya sanya ni ba, sai dai kuma ina son ki shaida masa cewar ni Yariman Yamma, tun farkon kafuwar ahalin mu ba'a taɓa yin wani wanda yay bugun shaɗi ba tare da yayi nasara ba, dan haka sai shima ya ƙara shiri akan wanda yake yi, domin kuwa ke ɗin tawace ni kaɗai, kuma an halkice kine domin n... "Dakata Malam!" Ta faɗa da ƙarfi tana mai ɗaga masa hannu sama, tukun ta buɗe baki tana mai sakin wani irin wuci tare da faɗin. "Kar ka kuskura ka ƙara gigin furta kalmar cewar ni ɗin takace muddin baso kake na datse harshen ka ba kafun kabar wurin nan, domin kuwa wannan kalmar mutum ɗaya ne kawai ya halatta ya faɗe ta aduk faɗin duniya, kuma wallahi wallahi ni ɗin tasa ce kamar yacce shi ɗin yake nawa, bayan shi kuma babu wani agefen sa." Ta ƙarasa maganar tana mai juyawa daniyyar tafiya. Caraf taji Yarima ya cafki yatsun hannuwan ta adai dai lokacin da ta ɗaga ƙafa danniyar yin gaba. Cak ta tsaya ai'nda take ba tare data juyo ba ranta na tsantsar ƙuna, yayin da shi kuma ya saki yatsun hannun nata yana mai sake komawa daga gaban ta. Ɗauke kai tayi daga kansa tana mai kallon gefe tare da sakin huci, domin kuwa aduk lokacin da zata kalli fuskar sa ji take tamkar ta shaƙesa ya mutu dan baƙin ciki. "Ya da jin haushi haka kuma Gimbiya ta, ko kuwa har kin sare ne tun yanzu sabo da kin san nine dana sara?" Ya faɗa yana mai jifan ta da murmushi, tukun ya sake ranƙwafawa dai dai saitin fuskar ta yana mai yin ƙasa-ƙasa da murya tare da faɗin. "Ki sani ina sonki, kuma akan sonki babu abun da bazan iya ai'katawa ba dan ganin na mallakeki, dan haka ina mai sake sanar miki da ki shaidawa shi wancan ɗin ya fara shiryawa, domin ko haɗuwa ta da tasa bazata taɓa yin kyau ba, nima kuma da zarar na koma gida zan sanarwa da Lamiɗon mu cewa na samu abokin karawa." Ya ƙarasa maganar yana mai matsawa gefe ya bata hanya. Sai lokacin ta ɗago kai tana mai jifan sa da wani irin matsiyacin kallo. Wata irin tsanar sa take ji aranta irin wacce bata taɓa yiwa wani mahaluki ita ba aduniya, sabo da ganin sa da take amatsayin barazana gare ta akan soyayyar ra da Giɗaɗon ta, tukun daga bisani ta janye idanuwan ta tana mai ɗaga ƙafafuwan ta tayi gaba ba tare da ta sake tanka masa ba. Amai-makon tayi hanyar da zata sadata da gida sai kawai ta doshi hanyar wurin da tsuntsayen ta suke ranta atsantsar ɓace. Yayin da shi kuma Yariman Yamma ya juya yana mai komawa kan shimfiɗar nan ya zauna zuciyar sa na tsantsar tururi, sabo da ganin irin tarbar da tayi masa amatsayin sa na wanda zai zamto miji gare ta. Taune lips ɗin sa na ƙasa yayi da ƙarfi yana mai girgiza kansa tare da rumtse idanuwan sa, tukun daga bisani ya buɗe su yana mai buɗe baki yace. "Tabbas ko kai wane ne sai na sanya ka kayi nadamar soyayyar da ka fara da wacce nake muradin aure, sai nasa kayi dana sanin-sanin ta amatsayin ƴa mace balle har kasota, domin ko wallahi wallahi Haddiyal tawace ni kaɗai!" Ya faɗa cikin kaushi yana mai sake rumtse idanuwan sa, zuciyar sa na tsantsar tururi da ƙuna. *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ, CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Sosai shirye shiryen bikin godiya ga abun bauta Gargabilu da za'ayi ajibi ya kan-kama da gasken gaske acikin baƙar masarauta. Gaba ɗaya an sake sabon fenti akowane wuri tare da sabon tambari acikin masarautar, yayin da ko wane bawa da baiwa suka kasance suna ta shiri kuma har yau suna kan shirywa. Acan filin biki ma bayi ne suke ta aikin share share da jera kujeru acikin sa. Yayin da wasu kuma suke ta faman wucewa da wasu mahaukatan iccina ɗauke akafaɗun su suna masu kai su wani fili su aje. Acan wurin su Bir kuwa zaune yake agaban Iyar Bayi ya tanƙwashe ƙafafuwan sa suna tattaunawa. Sake matsawa kusa da Bir Iyar Bayi tayi tana mai miƙa yatsun hannun ta ta riƙo nasa da su. Ɗago idanuwan sa yayi ya kalleta kamar yacce ita ɗin ma take kallon sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Al'farma nake roƙo awurin ka Jarumi na, ina son gobe ka zamto yaro nitsats-tse kamar yacce sauran yara suke, kayi abun da yake agaban ka karka kuskura ka kalli ko inda Gimbiya take balle har kaje wurin ta kajawa kanka bala'i kaji." Uhm! "Iya ta kenan, to ni dama ai bawai ina zuwa wurin ta bane, itace dai take biyowa hanyar data kasance hanyar mu, ni kuma abu ɗaya dana sani shine banga abun da yake tattare da itaba wanda har zai firgita dan tazo wuri in gudu in ɓuya, wannan dalilin ne yasan ya aduk lokacin da tazo giftawa nake ƙara matsawa inda take domin naga ƙarshen ikon ta." Bir ya faɗa yana mai sakin murmushi idanuwan sa akan fuskar Iyar Bayi, yayin da ƙwaƙwalwar sa kuma ke hasko masa kyawun fuskar Gimbiya Tasmir tare da kyawun surar jikin ta. "To wa gari ya waya kuma, wane yake wahala bayan kai Jarumi?" Iyar Bayi ta faɗa tana mai cigaba da kallon sa, tukun ta daga bisani ta ɗora da faɗin. "Tun kafuwar tarihin BAƘAR MASARAUTA ba ataɓa yin zamanin da ɗan sarki ko sarki yake zuwa giftawa ta wuri ba, asamu wata hallita da ke kasancewa awurin ba tare da sun gudu ba bayan ƴan rakiyar su kawai sai akan ka Jarumi, shin kai ɗin me zai hana kazamto kamar sauran ƴan uwanka bayi ko domin lafiyar ka Jarumi, domin ko kasan akan wannan abun da kake ai'katawa tsaf har ranka kana iya rasawa acikin BAƘAR MASARAUTA." "Iya ta kenan, bazaki fahimci yarce nake ji bane kwata-kwata, sai dai kuma abun da zan faɗa miki shine, wallahi bazan iya nisantar ta ba, bazan iya jurewa jin sautin taba ba tare da na ɗaga ido na kalle ta ba." Bir ya faɗa yana mai kallon Iya, yayin da ita kuma Iya ta saki baki cikin firgici tana mai zaro idanuwa waje, tukun daga bisani ta fara ɗaga laɓɓa bakin ta na tsantsar rawa tana mai faɗin. "Shin kasan abun da kake faɗe kuwa Jarumi? Shin wai anya ma kana cikin hankalin kane Jarumi, to wai ma mekake nufi da bazaka iya jure jin sautin taba ba tare da ka ɗaga ido ka kalle ta ba?" Iyar bayi ta watso masa tambaya amatuƙar ruɗe tana mai futo da idanuwa waje. "Shiyasa tun farko nace miki bazaki fahimta ba Iya, amma ba komai kawai ki kwantar da hankalin ki akwai lokacin da bake kaɗai ba hatta da sauran mutanen dake cikin masarautar nan zaku fahimta." Ya faɗa yana mai lumshe idanuwan sa, tukun daga bisani ya wara su yana mai zame ƴan yatsun hannuwan sa daga cikin na Iyar Bayi da ta saki baki take aikin kallon sa, kana ya miƙe tsaye yana mai juyawa zai tafi. "Jarumi!" Iyar Bayi ta faɗa tana mai miƙewa tsaye itama. Cak Bir ya tsaya a'inda yake ba tare da ya juyo ba, yayin da ita kuma Iya ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai nufar inda yake. Gaban sa ta ƙarasa ta tsaya tana mai kallon fuskar sa. Lumshe idanuwan sa yayi agaban Iya ba tare da yace komai ba, domin ko yasan duk abun da zata faɗa masa ayanzu bama fahimta zai ba. "Na roƙe ka Jarumi badan ni ba, na roƙe da abun bauta Gargabilu ka futa daga harkar Gimbiya Tasmir, domin ko tsaf ana iya fille kanka muddin irin wannan furucin da kayi ayanzu zai cigaba da futa daga cikin bakin ka acikin BAƘAR MASARAUTA." Hmmmm! "Ki kwantar da hankalin ki Iya ta, ni da kaina na faɗa miki babu damuwa, sannan kuma babu abun da zai faru." "To idan har hakane da gaske ina son yanzu kamun al'ƙwarin babu abun da zai haɗaka da Gimbiya Tasmir gobe." Iya ta faɗa tana kallon sa. "To ai dama Iya ba daga ni bane matsalar, tambaya ce kawai take mun akan rayuwar ta ni kuma nake yarce naso da ita ta hakan, wannan fa shine kawai abun da ke faruwa." "To amma mai zai hana ka bata amsar tambayar da taimakan idan ka sani ko domin hutun ka?" "Iya kenan, shiyasa tun farko nace miki bazaki fahimta ba, amma ba komai yanzu dai na miki al'ƙwarin bazan ko kalli inda take ba gobe balle har wani abu ya shiga tsakanin mu Iya ta." Ya faɗa yana mai juayawa ya cigaba da tafiyar sa hankali kwance, yayin da ita kuma Iya ta juya tana mai komawa ta zauna tare da buga uban tagumi da hannu bibbiyu. Acan ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa sosai ake shirya ta tun yau, wani irin gyara ake yiwa gashin kanta, yayin da ƙafafuwam ta da hannuwan ta kuma aka ƙunshe su da ƙunshi irin na jan lalle da yay tsananin yi mata kyau. Zaune take akan wata kujerar ƙarfe mai azabar kyau ana mata gyaran gashi. Sosai ta ƙagara ranar gobe tazo, domin kuwa gobe ne take ganin ranar da zata wuce duk baƙin cikin da wancan ƙas-ƙantaccen bawan ya ƙunsa mata cikin sauƙi! *ƘASAR HAUSA JAHAR WASAI, CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Misalin ƙarfe goma na safe dai dai Babban yaya ya tura kansa cikin ɗakin Asad bakin sa ɗauke da sallama. Kwance ya hange sa akan gado gaba ɗaya ya ƙudun dune jikin sa da eskimo, sai fuskar sa kawai da ya bari awaje yana shara-rar bacci. Kallon haɗaɗɗen agogon bangon da yake manne ajikin bangon ɗakin Babban yaya yayi, sabo da ganin da yay har yanzu Asad bai tashi ba. Girgiza kai yayi bayan ya janye idanuwan sa daga kan agogon, tukun ya cigaba da takawa yana mai dosar bakin bed ɗin. Wuri ya samu daga gefen gadon ya zauna, tukun yakai tafin hannun sa zuwa jikin Yarima Asad yana mai ɗan bubbugasa, bakin sa na furta kalmar. "Kai Asad! Asad!! Asa..." "Wai kai dallacan me yasa mugun jarababben mutum ne kai!" Yarima Asad ya faɗa aharzuƙe yana mai buɗe idanuwan sa tare da miƙewa zaune. Ƙam ya tsaya ayarce yake yana mai zaro idanuwa tare da buɗe baki, sabo da fuskar da yay araba da ita wacce ko kaɗan bai kawo cewar itan zai gani ba, kafin daga bisani kuma ya fara ɗan sosa ƙeya yana mai sakin yaƙe tare da faɗin. "Ashe Babban yaya nane ban sani ba." Uhm! Babban yaya ya sauke ɗan gajeren numfashi yana mai kafesa da idanuwa. Sake sosa ƙeya yayi, sabo da yarce yaga yaƙi ya ɗauke ido daga kan sa, tukun daga bisani yace. "Kayi haƙuri Yaya na wallah na zata wancan masifaffen al'amin ɗin ne yazo, shiyasa kaji na faɗi haka." Taɓe baki babbayn yaya yayi ba tare da yace komai ba, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ina fatan dai kayi sallah, ba wai sai yanzu ka tashi ba ko?" "Haba dai ai acikin masallaci nai sallah ma Babban Yaya." Asad ya faɗa yana mai gyara zaman sa, tukun daga bisani ya ɗora da faɗin. "Ina kwana Yaya na." "Alhamdulillah." Babban Yaya ya faɗa yana mai miƙewa tsaye, tukun ya sake fuskantar ƙanin nasa yana mai faɗin. "Dama zuwa nai na sanar maka ka kasance cikin shiri, gobe misalin ƙarfe tara na safe zakamun rakiya zuwa MASARAUTAR FULƊE ta cikin JAHAR KAGUL." "Amma Yaya masarautar fulɗe?" Yarima Asad ya faɗa yana mai sosa kai, kana far'ar kan fuskar sa na gushewa, tukun daga bisani ya ɗora da faɗin. "Da kuma akawai wani wuri da zamuje gobe ni da Al'amin fa Yaya." "Sai ku ɗaga taku tafiyar zuwa jibi idan mun dawo, domin kuwa wannan tare na shirya mana ita ku duka biyun, kuma har mai martaba ma yasan da shirin." "Kuma shima Abban ya yadda atafi dani?" Yarima Asad ya faɗa yana mai ɗan zaro idanuwa, sabo da sanin mahaifin nasa da yay baya taɓa yanke masa hukunci sai ya fara tambayar sa yaji yana son abun ko ko, badan komai ba kuwa sai dan kawai tsananin ƙaunar da yake mai, wanda hakan yana ɗaya daga cikin abubuwan da sukayi sanadin ƙara lalata sa. "Kai Asad wannan fa umarni ne nake baka ba shawara ba da har kake shirin cika ni da tambayoyi, dan haka katabbatar gobe kun shirya da wuri daga kai har Al'amin ɗin tun kafin na futo." Babban Yaya ya faɗa yana mai ɗan ɗaure fuska, sabo da ganin da yay sakin fuskar tasa na shirin sanyawa yace bazai bisa ba, domin ko ya riga daya sani muddin yaje ya samu mai martaba ya faɗa masa baya son zuwa to shikenan fa zuwan ya fasaya sa shi. "Tom shikenan Allah ya kaimu Yaya na." Yarima Asad ya faɗa badan ransa yaso ba. Yayin da shi kuma Babban Yaya ya juya yana mai dosar waje bakin sa na furta cewar. Katabbatar kuma ka futo kayi break, sannan kaje ka nagaisar da Mamy yanzu." "Oh shirt!" Yarima Asad ya faɗa yana mai dukan fillow alokacin da ya tabbatar da Yayan nasa ya futa, tukun daga bisani ya ɗora da faɗin. "Aiko wallahi babu wanda ya isa yasan ya ni nasa blanket ajiki sai dai afasa zuwan dani." Tukun yasa hannu yana mai yaye eskimon dake jikin sa zuwa gefe, sannan ya zuro dogayen fararen ƙafafuwan sa da suke lulluɓe da kwantaccen baƙin gashi akan su zuwa ƙasa. Babu komai a jikin sa sai ɗan ƙaramin boxer da ya tsaya masa asaman guiwoyin sa. Janyo takalman dake ajiye agafen gadon yayi yana mai zura kafafuwan sa acikin su, tukun ya miƙe tsaye duka yana mai dosar hanyar toilet cikin takun sa wanda shi kaɗai ke zautar da Ƴammatan dake binsa. *GIDAN GWAMNAN JAHAR WASAI.* Tunda Billy ta baro Asadullah palace har kawo yau bata bar ƙunci ba tare da jin takaicin abun da Yarima Asad yayi mata. Sanye take cikin engilsh wear na black ɗin wando jeans da yayi matuƙar kama jikin ta ƙam-ƙam, sai ƴar ƙaramar jar riga mai ɗan guntun hannu da take sanye ajikin ta wacce ta zamto kusan da ita da babu duk ɗaya, domin kuwa bata hana komai bayyana ba na daga surar jikin ta. Yayin da kanta kuma yake ɗauke da farin gashin atarch ta tufkesa, sai wani uban hill shoe da yake sanye aƙafar ta tana mai sakkowa daga kan stairs. Direct ta doshi dining area ɗin da mahaifin ta da kuma mahaifiyar ta suke zaune akan kujeru, da alamun ita ɗin suke jira ta ƙaraso dama. "Morning Dad! Morning Mom!" Ta faɗa tana mai jan kujera ɗaya sannan ta zauna akai. "Morning daughter, fatan kin tashi lafiya." Mom ɗin tata ta faɗa tana mai bubbuɗe kulolin da suke agaban ta waƴan da suke ɗauke da kala-kalan abinci cikin su danniyar tayi serving ɗin su. Yayin da shi kuma Dad ɗin nata ya bita da idanuwa kawai ba tare da ya amsa gaisuwar da ta masa ba. Mai da idanuwan ta tayi kan wayar ta dake riƙe ahannun ta tana mai fara shafata. "Dear meke damun daughter ne, gaba ɗaya tun jiya naga duka yanayin ta ya sauya, kwata-kwata bata walwala kamar yacce ta saba, shin meke faruwa ne mara daɗi da bansan da shi ba?" Mahaifin nata ya faɗa yana mai kallon mahaifiyar tata alamun ita ɗin yake tambaya ba ƴar ba. Uhm! Ta sauke ɗan gajeren numfashi, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "To gatanan dai, sai dai yanzu kaima ka ɗora daga inda na tsaya, domin kuwa tun jiya data fuce daga gidan nan ita kaɗai ba tare da guard's ba ta dawo gaba ɗaya abirkice, kuma babu kalar tambayar da ban mata ba akan ta faɗamun abun da ke faruwa amma tace mun wai babu, shi yasa na rabu da ita da zummar yau idan kai ka tambaye ta ta faɗa maka muji." Mom ɗin tata ta faɗa tana mai kallon sa. "Subhanallahi, wai dama ba na hanaki futa bane ke kaɗai daughter, shin mene ne ma yafaru ajiyan, wane ya taɓaki kuma mai yay miki, sannan waye ubansa afaɗin Jahar Wasai?" Dad ɗin nata ya faɗa ahargitse yana mai kallon ta. Ajiye wayar dake ɗauke ahannun ta tayi akan table ɗin dake gaban ta tana mai shash-shake fuska ba tare da tace komai ba." "Kwantar da hankalin ki daughter ki yimun bayanin damuwar ki, ni kuma na miki al'ƙawarin muddin bata ƙarfi na ba zan yaye miki ita ayau yau ɗin nan." Ya faɗa yana mai miƙa hannu ya riƙo tafukan hannayen ta cikin nasa. "Yarima Asad ne Dady!" "Yayi miki me? Ba dai ya sake wulaƙanta ki bane kamar yarce kika faɗamun ya miki a kwanaki ba ko?" "Ai da Dady da kalar na kwanaki ne ma dako sani ba zakuyi ba, domin ko shi ba komai bane akan wanda yamun jiya." "Dukan ki yay ko ko zagin ki yay ne?" Mahaifin nata ya faɗa da ƙarfi yana mai miƙewa tsaye jijiyoyin kansa na futowa raɗa-raɗa akan goshin sa. "Kusan hakan Dad, domin kuwa har hankaɗe ni yay na faɗa cikin swimming pool, dan bada ban Allah yasa na iya ruwa ba da shikenan sai dai akawo muku gawata!" Ta faɗa tana mai matso ƙwalla daga cikin idanuwan ta. "Ina!!! Ai ko wallahi sai yayi nadamar abun da ya ai'kata, zanje in samu uban sa ayau yau basai gobe ba domin ajasa masa kunn... "A'a Dad ba haka nake so ayi ba." Ta katse baban nata da faɗin haka ba tare da ta bari yakai ƙarshen maganar saba. "Kamar ya ba haka kike so ayi ba daughter, ko ko kina nufin kice mun na barsa ne awannan karan nan gaba kuma ya illatamun ke yacuce ni, shin shi agidan ubanwa aka faɗa masa haka ake soyayya, ko kuwa haka yaga ubansa nawa uwarsa tsawa da duka, to wallahi daga yau anyi an gama kema, dan ke kanki bazan saurare ki ba ballan tana har ki sanyani na yafe masa." "Nima bawai ina nufin ayafe masa bane Dad." Ta faɗa tana mai kallon mahaifin nata. "To ya kike so amasa ne daughter?" Ya faɗa shima yana mai komawa ya zauan akan kujerar da ya tashi, yayin da ita kuma mahaifiyar tata tai shiru ba tare da tace komai ba, sai abincin ta da take ci kawai tana kallon su. "Wani shegen murmushi Billy ta saki tana mai ɗan tane lower lips ɗin ta, tukun daga bisani ta buɗe baki bayan ta miƙa hannu ta riƙo hannun mahaifin nata cikin nata tana mai faɗin. "S................✍ 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *FREE PAGE 08* "So nake abi masa ta hanyar da bai taɓa zato ba Dad, ma'ana kawai ka samu iyayen sa kayi musu magana akan auren mu, nasan idan akayi hakan dole ya dena mun hulaƙacin da yake yi mun, kamar yacce nasan babu tayarce za'ai mahaifin sa yaƙi yin komai kace yayi." Ta faɗa tana mai kallin baban nata, yayin da shi kuma yayi shiru ba tare da yace komai ba, sai kansa da ya ɗaga sama yana mai kallon haɗaɗɗen rufun dake cikin ɗakin, tukun daga bisani ya sauke kan nasa ƙasa yana mai watsa ƙwayar idanuwan sa akan fuskar ƴar tasa, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Tabbas na gamsu da zancen ki ɗari bisa ɗari my Daughter, Dan haka ayau yau ɗin nan zan turawa mahafin nasa da saƙon zuwa na gare sa, domin kuwa agobe-goben nan nake son ayi duk mai yuhuwa, sannan kuma aƙarshe in faɗawa mahaifin sa aja masa kunne, sabo da ya kiyaye kar bayan anyi aure ya cigaba da abun da yake yi yanzu." Ya faɗa still idanuwan sa akan fuskar ƴar tasa. Yayin da ita kuma tayi wata irin miƙewa tana mai matawa kusa da shi, tukun tayi hugging ɗin sa daga zaunen da yake da matuƙar ƙarfi tana mai faɗin. "Yess my Dad, that's why akullum nake ƙara son ka, sabo da kaima kana son abun da nake so." Ta ƙarasa maganar da sakar masa kiss akan goshin sa, tukun ta juya aguje tana mai kama hanyar stair's cikin tsantsar farin ciki. Yayin da shi kuma mahaifin nata ya bita da idanuwa fuskar sa ɗauke da yalwataccen murmushi shima. *WASHEGARI* ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA. Tun daga bakin tafkeken ruwan da yayiwa jahar karfuz ƙawanya mutum zai fahimci yau ɗin ana wani gagarumin taro ne acikin sa basai an faɗa masa ba, sabo da yarce jama'a na garuruwa daban- daban suke ta shigowa suna wucewa, wasu akan dokuna, yayin da wasu kuma suke akan ƙafafuwan su, ga kuma yarce akabi aka zagye gefen ruwan da yake abakin garin, wanda dole sai mutum ya tsallake sa kafin ya shiga jahar karfuz da wuta acikin kaskwaye tanaci bal-bal-bal! Acan cikin Baƙar Masarauta kuwa ban da sautin kiɗa babu abun da akeji yana tashi, domin kuwa tun cikin dare aka gama shirya filin biki tas, sannan kuma aka zageye sa da kayan kiɗa masu matuƙar sauti, tare da kaskwayen Huta waƴan da suke ɗauke da iccina suna ci acikin su.

Chapter 8 of 76