Share this page
ka na ƙarshe acikin duniyar BAƘAR MASARAUTA, muddin har zaka ƙara kuskuren shiga gona ta, domin kuwa ina mai rantsuwa da ubangiji Gargabilu sai na lalata maka wannan koɗaɗɗen jikin naka. Sai na kassara rayuwar ka, ta yadda ko gobe ance ka sake tsayawa akan hanya ta ba zaka yi ba, wannan alƙawari ne na ɗaukarwa kaina akan ka ƙasƙantacce." Ta ƙarasa maganar da ɗan sauti, tana mai danna kanta zuwa cikin tanƙashshen falon su na alfarma. Tayi sa'a kuwa babu kowa acikin falon tamkar yadda tayi fata, hakan ne yasa ta kama hanyar da zata sadata da corridor ɗin da zai kaita ɗakin ta cikin sauri, gudun kar wani ma ya ganta a cikin yanayin da take yanzu. Ko da dare yayi haka tai ta juyi akan tamfatsen-tsen bed ɗin ta bacci yaƙi ya dauke ta, sabo da baƙin cikin abun da yayi mata da yake cigaba da sukar zuciyar ta. Tun da take arayuwar ta bata san wata aba mai suna damuwa ba sai yau, bata sai meye tinanin ba sai yau, haka bata san ɓacin rai ba sai yau data haɗu da wancan ƙasƙantaccen fitsararren bawan mara kunya, hakan yasa take jin ƙarin tsanar sa na ƙara turnuƙe zuciya da ruhin ta aduk bayan wanzuwar wata daƙiƙar. Ba ita ta samu bacci ya ɗauke taba sai misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, bayan ita ada ƙarfe takwas da ƴan mintuna ma tayi bacci. Haka kuma ko da ta tashi a yau da tinanin abun da yay mata a zuciyar ta tashin. Hakan ne yasa gaba ɗaya yau ɗin taji bata sha'awar futa ko daga cikin ɗakin ta ko kaɗan, balle har ta sake arba da wata fuskar ta ƙarasa tarwatsa mata zuciya da baƙin ciki. Wannan dalilin ne yasa koda Bir yaje kan hanyar ya zauna har ya shafe sama da awa biyar ba tazo ba. Hakan ne yasa ya miƙe cikin sanyi riƙe da kwari da gwafar sa a hannun sa zuciya duk ba dadi, yana mai komawa ɓangaren su. *ENGLAND* Cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa Billy ta tura kanta zuwa cikin ɗakin su. Hango Zee da tayi zaune akan kujera ne ya sanya ta sakin ihu da matuƙar ƙarfi, tana mai yin kanta a guje tare da faɗawa jikin ta tamkar zata karya ta. Da matuƙar sauri Zee ta ɗago gare ta tana mai faɗin. "A Beb meye haka? Lafiyarki ɗaya kuwa da kike shirin karyawa Dady da Momy Autar su?" "Ke Beb i got him! I got Prince Asad! Finally he is my own know!"............... ✍ _CIKIN ABU UKKU TABBAS DAYA ZAI FARU, WATO DAI KO KU GYARA KU DINGA COMMENTS DA SHARHI, KO KUMA BAKAR MASARAUTA BOOK 2 YA ZAMTO NA KUDI, KO NA DENASA GABA DAYA, SABODA HAR YANZU LABARIN BAI DAU ZAFI BAMA, DAN HAKA ZABI YA RAGE GAREKU. KO A ADENA GABA DAYA, KO KUMA YA SAKE KOMAWA NA KUDI, KO KU FARA COMMENTS DA SHARHI_ *GA MASU BUKATAR SHIGA CIKIN GROUP DIN DA AKE POSTING, COMMENT DA SHARHI SAI KU TUNTUBENI TA WHATSAPP NMBER TA KAMAR HAKA. 08038135929* *BY* UMAR FARUQ*D *BAK'AR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 28* "Kamar ya kin same sa? Waye kike nufin ya zama naki? Please kiyi mun bayani yadda zan gane, saboda kwata-kwata ban fahimci abun da kalamanki suke nufi ba." Zee ta fad'a cikin wani irin yanayi mai nuni da zallar mamaki da aljabin da suka rufe ta, tana mai sa hannu ta d'ago Billy daga jikin ta, tare da kafe ta da idanuwa. Hakan da Billy taji ne ya sanya ta bud'e zip d'in jakar ta cikin sauri, tana mai zaro d'an katin da Yarima Asad ya hullo mata. Kana ta mik'awa Zee shi ba tare da ta furta komai ba, sai zallar farin cikin da yake kance akan fuskar ta ta yadda har ya gaza b'oyuwa a fili. Cikin sakin baki Zee ta mik'a hannu jiki a matuk'ar sanyaye, tana mai amsar katin ta rik'e sa acikin tafin hannun ta, yayin da idanuwan ta kuma suka kasance k'ur akan katin, kafin daga bisani kuma ta d'ago tafin hannun ta tana mai kai sa kan idanuwan ta ta murza su sosai, a cewar ta ko idanuwan nata basu gane mata rubutun da tayi arba da shi ba akan katin dai-dai, domin kuwa ko a mafarki bata tab'a tinanin Billy zata samu karb'uwa a wurin Yarima Asad ba, duba da irin yawan 'yammatan da suke hauka akan sa, amma ko kallo basu ishe sa ba. Sai dai kuma koda ta sake bud'e idanuwan nata bayan ta janye hannun ta daga kai, da abun da ta gani a farko ta sake yin arba. Wato Sunan Yarima Asad akan katin, tare kuma da jerin numbobin sa. Hakan ne yasa ta juyawa b'arin da Billy take cikin sauri, bakin ta har yana rawa wurin fad'in. "Ya akai hakan ta faru ne Beb? Ya ki kai? Me kuma kika basa da har ya baki katin sa? Kai anya ma kuwa da gaske nasan ne Billy?" Zee ta fad'a cikin tsantsar mamaki, yayin da har lokacin kuma take kallon katin nan tana sake juyawa sa a cikin hannun ta, kana kuma ta sake d'ago kai ta kalli tun daga sama har k'asa. Ita kuwa Billy wani irin murmushin farin ciki ta saki, kafin daga bisani kuma ta bud'e baki tana mai fad'in. "Kamar ya anya ma kuwa na san ne? To na tambaye ki mana, dama akwai wani Prince Asad d'in ne bayan shi wanda kika sani." Girgaza kai Zee tayi idanuwan ta akan fuskar Billy, tukun daga bisani ta bud'e baki cikin sanyi tana mai fad'in. "Shi d'in ne dai kawai." "To kinga kenan babu wani zancen kokwaton shine ko ba shi bane ba, kuma ma wai mantawa kikayi da abun da na fad'a miki ne tun a ranar dana fara ganin sa." Billy ta fad'a tana mai gyara zaman ta tare da sake fuskantar Zee sosai. Tukun ta d'ora da cewar. "Idan baki manta ba dama na fad'a miki cewar ni d'in ban tab'a neman abu na rasa sa ba tunda nazo duniya, haka kuma dan wasu sunyi sun kasa ba shi ne yake nufin nima zan kasa ba, domin kuwa kowa yana buga kalar nasa salon wasan ne, wanda kuma gashi naje na bugo nawa, sannan nayi wining acikin sa, dan haka ina san ki cire duk wani mamakin dake a cikin ranki ki fara kira na da Billy'n Asad, domin kuwa ya riga da ya zamto nawan." Ta k'arasa maganar da sakin murmushi, tare da dafa kafad'un Zee. Yayin da ita kuma Zee ta girgiza kanta tana mai sakin murmushi, tukun daga bisani tace. "Tabbas na yadda da batun ki, ke d'in ta daban ce Beb, domin kuwa samun kallo daga wurin Yarima Asad ma kad'ai ba abu bane mai sauk'i, amma sai gashi ke yau daga had'uwar farko kin tawo hadda phone number's d'in sa, dan haka Congratulation Friend." Zee ta k'arasa maganar fuskar ta d'auke da murmushi, kana tana shafa kiston dake d'auke akan Billy, tukun daga bisani ta d'ora da fad'in. "To wai in tambaye ki mana, dan Allah ke kuwa Billy wani irin salo ne kika jewa Prince Asad da shi da har ya bada kai haka da huri. Please kiyi sauri ki fad'a mun na k'agu naji yadda labarin yake." Ta k'arasa maganar tana mai k'ara gyara zaman ta akan kujera. Yayin da itama Billy ta janye cinyoyin ta daga kan na Zee da ta danne ta, tana mai zama sosai akan kujerar ta fuskan ci Zee sossi. Tukun ta fara jero mata duk abun da ya faru tun daga A har Z. Kana tayi shiru tana mai sakin murmushi. "A gaskiya kam da gaske ke d'in 'yar sa'a ce wallahi Beb." Zee ta fad'a tana mai mik'awa Billy hannu suka tafa. Sannan suka d'ora da hirar su cikin tsantsar farin ciki, domin kuwa ko ita Zee tayi natuk'ar taya Billy murna, sabo da yadda taga ta kamu da mahaukacin son sa, sai dai kuma a k'asan zuciyar ta tana mai tausayin irin yadda zata gwaru a wurin Asad, dan kuwa babu labarin da bata sani ba na wahalar da 'yammatan sa suke akan sa, amma kuma dai-dai da kalmar so babu wadda ya tab'a furtawa a cikin su. A cikin hirar tasu ne Zee take cewa Billy. "To yanzu kuma yaushe ne zaki koma wurin nasa?" Shiru Billy tayi tana mai d'aga kanta sama, kafin daga bisani kuma ta sauke sa tana mai watsa idanuwan ta akan fuskar Zee. Sannan ta bud'e baki tana mai fad'in. "Ina ganin kamar nan da kwana ukku zuwa hud'u masu zuwa gaba kenan, duk da dai da son samun abun da zuciya take so ne to yanzu ma bata k'i a sake ganin sa ba, sai dai kuma a yadda naji labarin sa tabbas idan na nuna masa maita-ta tun farko zai watsar da ni, domin zaiga kamar nayi mahaukaciyar damuwa da shi, hakan yasa zan bari har sai zuwa nan da 'yan kwana ki sai in koma, in yaso tunda ina da number sa a hannu na yanzu sai nai ta tura masa da message's na fatan Al'khari harma da kira kafin ranar." "Tabbas hakan ma yayi sosai kuwa, domin kuwa kina komawa gobe ma zai iya fara tinanin ko dama can kin saba mu'amala da maza sosai, da ganan kuma zai fatattake ki, dan kuwa babu abun da ya tsana a rayuwar sa face amasa kishiya, wato kina tare da shi ki kuma ki kula wanin sa, dan haka sai ki kiyaye." Zee ta fad'a tana mai mik'ewa tsaye. Itama Billy mik'ewa tayi tsayen tana mai d'aukar jakar ta-ta doshi hanyar bedroom d'in ta, bakin ta na furta kalmar. "Ai nama kiyaye na gama Beb." *BAYAN SATI 'DAYA.* *K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.* Tun bayan had'uwar da Bir yayi da Gimbiya Tasmir har yau Allah bai sa sun sake cin karo ba, duk da yadda yake aikin ziryar bin kan hanyoyin ta ako da yaushe, domin kuwa ba k'aramun matsuwa yayi da ya sake ganin fuskar ta ba, ta yadda har sai da ya d'an fara, sabo da yadda kullum yake yini da tinanin ta, ga kuma mafarkin ta da yake yi a cikin yana yi daban-daban a duk lokacin da ya kwanta bacci. Gaba d'aya ya dena zuwa ko ina hatta da daji wurin harbo abubuwan da ya saba, sabo da yadda yake yini ko da yaushe akan hanyar Gimbjya Tasmir. Babu yadda iya batayi ba da shi akan ya fad'a mata abun da yake damun sa a 'yan kwanakin nan, sabo da ganin da tayi yana ta ramewa, ga kuma yadda ya sake komawa shiru-shiru fiye da da, duk da dai dama shi can ba mutum bane mai hayaniya, amma sai dai kuma a yanzu ya ninka bayan nesa ba kusa ba. Amma Bir yak'i fad'a mata, sai dai yace mata ba komai kawai, sabo da sanin da yayi na muddin taji silar komawar sa hakan to ba k'aramun tashin hankali zata shiga ciki ba, wanda shi kuma bazai tab'a son haka ya faru da ita ba. Wannan dalilin ne ya sanya sa b'oye mata gaskiyar damuwar sa, duk da yadda ya saba fad'a mata komai nasa kuwa. Tsaye yake jingine jikin wata bishi da take akan hanyar da Gimbiya Tasmir take bi lumshe da idanuwan sa. Yayin da yake hangen ta a cikin idanuwan sa tana mai jifan sa da wani irin kyakkyawan murmushi wai. Yana a cikin wannan yanayin ya fara jiyo sautin gudun jama'a acikin kunnuwan sa tamkar a mafarki. Hakan ne yasa sa bud'e idanuwan sa cikin sauri, yana mai bin Bayin da yaga suna aikin gudu da kallo. Kafin daga bisani kuma wani irin murmushin farin ciki ya sub'uce masa daga cikin baki, sabo da fahimtar da yayi na Gimbiya ce zata huce. Take kuwa yaji gaba d'aya zuciyar sa na yin sanyi, ga wani irin nishad'i da yake lullub'e sa ta ko ina. Amai-makon shima ya gudun sai ya koma bayan bishiyar nan da yake jingine da ita, yana mai lab'ewa a jikin ta, ta yadda baza su tab'a hango sa ba a lokacin da suke tawowar har sai dai idan sun k'araso wurin da yake. Yayin.da shi kuma ya tsara abun da zai aiwatar a cikin zuciyar sa kafun su iso gare san. Wannan dalilin shine ya sanya sa b'oyewar. A b'angaren su Gimbiya Tasmir kuwa tun bayan waccan had'uwar tasu ba ta sake futowa tayo nan ba, sabo da ganin da take a kullum tamkar zata gansa ne idan ta futon, hakan yasa gaba d'aya ma ta dena bin hanyar, sai yau data tawo domin zuwa kan kujerar nan tata. Sanye take da irin shigar ta-ta koda yaushe, wato doguwar riga mai jan k'asa, amma ta yau d'in ta kasance blue ce mai azabar kyau. Yayin da gashin kanta kuma ya kasance a bud'e an tufke sa wuri d'aya, sai wasu irin takalman fata da suke sanye a k'afafun ta blue suma, duk da dai ba ganin su ake iya yi sosai bama, sabo da yadda rigar nan ke bin k'asa, a hakan ma wai dan wa'yan nan 'yammatan bayin na rik'e da wani sashi na daga jikin ta ne. Zane fuskar ta take da tambarin masarautar tasu yau da akayi sa da k'walli, sai dai kuma ba k'aramun kyau yayi mata ba. Ko kad'an babu alamun rahama tattare a fuskar ta-ta tamkar ko da yaushe. Cikin takun ta na tsantsar nuna isa da izza tare da tak'ama ta cigaba da tafiya kanta d'age a sama. Yayin da dakarun nan nata na ko da yaushe kuma suke biye da ita a bayan ta. Acan b'angaren Bir kuma ta gefen Bishiyar nan yake ganin su, hakan ne yasa yana ganin sun kusa k'arasowa wurin kawai ya futo kai tsaye yana mai dumfaro inda suke. Ita kuwa Gimbiya Tasmir ba zato ba tsammani taga bayyanar mutum a gaban ta kawai yana tafiya, domin kuwa kwata-kwata bata lura da lokacin da ya tawo ba sai dai kawai ganin sa da tayi. Cak ta tsaya a wurin da take zuciyar ta na wani irin bugu da matuk'ar k'arfi, tamkar yadda ta Bir take yi shima, sabo da idanuwan su da ya sark'e cikin na juna a lokacin da ta kai duban ta gare sa. Wani irin kallon-kallo suka fara aikawa junan su da shi, zuciyoyin su na wani irin gudu a d'ari-d'ari, ta yadda har suke jin tamkar sa fasa k'irji nansu su futo waje. Da k'arfi Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwanta gumi na fara tsats-tsafo mata akan goshin ta. Ga wani irin sarawa da taji kanta yayi lokaci guda, bayan kuma azababbaben b'acin rai mara misaltuwa da ya game ko ina na jikin ta. Lokaci d'aya jikin ta ya d'an fara karkarwa, gumi na cigaba da tsats-tsafo mata akan goshin ta, kafin daga bisani kuma ta sake bud'e idanuwan ta akan fuskar Bir suna masu cigaba da kallon-kallo. Kana ta bud'e bakin ta cikin wata irin murya wacce take k'unshe da b'acin rai a cikin ta, tana mai fad'in. "Kai ne yauma?" Ta k'arasa maganar tana mai cigaba da kafe sa da idanuwan ta da suka canza launi. Yayin da dakarun nan nata kuwa gaba d'ayan su suma sukayi tsaye cirko-cirko suna masu jiran ta basu umarni su far masa. A hankali Bir ya d'an jujjuya kansa, kana daga bisani ya lumshe idanuwansa, sannan ya sake bud'e su akan fuskar Gimbiya Tasmir da yake ganin yau ta k'arayi masa kyau fiye da yadda ya ganta a baya. Kana ya d'an zaro harshen sa yana mai lasar busassun lab'b'an sa da yajisu sun bushen take yanzu, sannan ya d'an jujjuya k'wayoyin idanuwansa. Kana wani irin murmushin farin ciki ya sub'uce masa, yana mai cigaba da kallon fuskar ta, yayin da yake jin zuciyar sa na wani irn sanyi. Tukun daga bisani ya d'an d'aga lab'b'an sa a hankali bayan ya langwab'ar da kansa gefe, idanuwan sa akan ta, yana mai fad'in. "Tabbas nine d'in dai kuwa Gimbiya, kinga yau ma mun sake had'uwa ko. Amma fa kin san me?" Ya fad'a yana mai cigaba da jifan ta da kyakkyawan murmushin sa, wanda ita kuma take jin sa tamkar futar wuta daga cikin bakin sa zuwa zuciyar ta, tsabar yadda take sake tafar-fasa. Kana ya sake lumshe idanuwan sa, sannan ya d'ora da cewa. "Hak'ik'a ke d'in kin kasance ta daban acikin duka matan duniya, domin kuwa kyawun ki ya zarc...." "Dakata! Dakata mun haka k'ask'antacen Bawa mara galihu!" Gimbiya Tasmir ta katse sa da fadin haka cikin wani irin lafazi mai matuk'ar kaushi da sauti, ta yadda har sai da hurin gaba d'aya ya amsa a lokacin da tayi furucin. Yayin da jijiyoyin kanta kuma suka futo sukai rud'u-rud'u akan goshin ta, ga wani irin gumi da ya cigaba da tsats-tsafo mata, ta yadda zuwa yanzu har ya fara d'iga, kana idanuwanta sukayi wani irin jajahur tamkar gauta. Bud'e idanuwanta data rumtse su a lokacin da take furucin tayi akan fuskar sa. Kana daga bisani ta fara d'aga k'afafuwanta da suke futar da sautin sarak'aunan gwal tana mai dosar wurin da yake, cikin wani irin taku wanda shi kad'ai ya isa ya kad'a hanjin cikin matsoraci, amma shi kuwa Bir wani irin farin ciki ne yaji ya sake ziyartar sa a lokacin da ta doso wurin da yaken. Yayin da yake ganin fuskar tasa ta na sake yi masa kyau acikin idanuwansa fiye da baya, ta yadda har yake ganin tamkar canzawa take aduk bayan wasu lokutan. Lumshe idanuwansa yayi adai-dai lokacin da yaji ta iso dab da shi. Kana ya d'ago tafin hannun sa yana mai d'orasa adai-dai saitin zuciyar sa ya dafe ta. Sannan ya bud'e idanuwan nasa wanda hakan kuma yayi dai-dai da tsayuwar ta cak a gaban sa. Cikin muryar ta mai futar da amon b'acin rai ta bud'e baki tana mai fad'in. "Hak'ik'a yau zan tabbatar maka da kayi gangancin shiga gona ta, zan tabbatar maka da ni d'in ko wacece, zan sanya ka ka bambance tazarar da take a tsakanin ni da kai matsiyacin Bawa, domin kuwa nayi rantsuwa da Ubangiji Gargabilu akan sai nasa an maka ninkin ba ninkin abun da akai maka waccan ranar." Ta k'arasa maganar tana mai sakin wani irin huci, ta yadda hucin ke dukan fuskar Bir. Amai-makon taga tsoro ya bayyana akan fuskar Bir sai kawai taga ya sakar mata kyakkyawan murmushin sa yana kallon ta, tukun daga bisani ya bud'e baki yana mai fad'in. "Dama har akwai azaba wacce za'a fad'e ta da har zata firgita Bawan da ya tashi cikin BAK'AR MASARAUTA Gimbiya? Shin wai kin san ma me kuwa iyata take kirana da shi? To bara kiji in fad'a miki. Jarumi shine sunan da iyata ta mun lak'abi da shi tun ina cikin tsumma na. Shi kuma Jarumi kin san ako da yaushe ba raggo bane shi d'in, dan haka ina mai farin cikin sanar miki da cewar Jarumi yana mai maraba da duk wata wahala da zata b'ullo muddin daga gareki ne, domin kuwa ta kan juyawa ta koma dad'i ne, tare da farin ciki a cikin zuciyar Bir." Ya k'arasa maganar da busa mata sauran iskar bakin sa akan fuskar ta, yana mai sakin murmushi mai sauti. Take kuwa a wurin ta lumshe idanuwan ta tana mai sakin ajiyar zuciya. Sosai Bir ya k'yalk'yale da dariya, yana mai d'aga yatsar sa ya nuna ta da ita. Yayin da ita kuma ta bud'e idanuwanta tana mai jin tamkar ta kashe kanta dan bak'in ciki. Cikin wani irin yanayi ta mik'ar da hannunta gefe, tana mai bud'e tafin hannun ta da yake wata irin karkarwa ba tare da tace komai ba. Da sauri badakaran da ke rik'e da takobin tsafinta ta gado ya fara tawowa da baya da baya, yana mai yowa wurin da take. Zube gwuiwoyinsa yayi a k'asa yana mai durk'usar da kai k'asa, tukun daga bisani ya d'ora mata zureriyar takobin nan akan tafin hannun ta. Damk'eta tayi da matuk'ar k'arfi, tare da rumtse idanuwan ta, kana daga bisani kuma ta bud'e su akan fuskar Bir dan taga yadda yanayin sa ya koma. Amma amai-makon taga ya tsorata yanzu sai taga dai still yana cigaba da jefo mata murmushin sa ne. Hakan yasa tayi wani irin ja baya daga wurin da take tana mai nuna sa da takobin nan. Kana ta bud'e baki cikin muryar ta mai matuk'ar amo tana mai fad'in. "Rai Rai Rai Buuuu Hoooo Reeee!" Sannan tayi wani irin kautar da takobin daga kansa tana mai matsar da ita jikin wata bishiya da take a gefen su. Fittt! Kakajein k'arar wucewar Bir asama, yadda kasan wanda iska ta d'auke sa yana mai zuwa ya manne a jikin bishiyar nan. Kana wasu irin igiyoyi suka futo suna masu d'ad'd'aure sa a jikin bishiyar. Sosai gaba d'aya dakarun nan sukayi matuk'ar firgita da abun da suka gani, yayin da su kuma 'yammatan bayin nan jikin su ya kama wata irin karkarwa tsabar tsoro. "Shairamaaa!" Gimbiya Tasmir ta fad'a da k'arfi tana mai nuna gefen bishiyar nan. Take kuwa dank'areriyar macijiya ta bayyana a wurin, tana mai kad'a harshenta. Sake d'aga takobin tayi ta nuna jikin Bir da ita, tana mai fadin. "So nake ki bambance masa tsakani na da shi Shairama." Ai kuwa take wannan macijiyar tayi kansa gadan-gadan. Da matukar k'arfi Bir ya rumtse idanuwansa yana mai jin bugun zuciyar sa na k'aruwa. Yayin da ita kuma wannan macijiyar ta cigaba da tunkarar sa. Tana dab da zuwa gare sa Gimbiya Tasmir ta sake kiran sunan ta da matuk'ar k'arfi, tana mai nuna can gefe wurin da ta baro. Yayin da take sakin wani irin nishi, tamkar wadda taga zaki ko kuma aka biyota za'a kasheta ta samu ta tsira. Ita kuwa wannan macijiyar da wani irin sauri ta juya tana mai komawa wurin ta na farko. Kana daga bisani kuma ta b'ace-b'at, yadda kasan bata tab'a bayyana a wurin ba. Hakan da Gimbiya Tasmir ta gani ne ya sanya ta juyawa b'arin da dakarun ta suke, sannan ta bud'e baki cikin wani irin sauti tana mai fad'in. "Kutsamamamun jikin sa, ta yadda zaiji ina ma baizo duniya ba yanzu-yanzu." Aiko da wani irin sauri suka tunkare sa gaba d'ayan su, suna masu zare bulalan su. Yayin da ita ma ta fara d'aga k'afafuwan ta tana mai nufar bakin bishiyar nan. Su kuwa dakarun nan suna k'arasawa gaban bishiyar suka fara dukan Bir ta ko ina, tamkar suna dukan bishiyar. Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir tayi tsaye a gaban sa tana mai sakin wani irin murmushi aduk lokacin da taji ya saki ihu, sabo da wani irin farin ciki da take jin yana lullub'e zuciya da ruhin ta da ganin sa a hakan da tayi. Su kuwa 'yamnatan bayin nan wata irin karkarwa jikin su yake daga wurin da suke a tsaye. Sosai suka toshe kunnuwan su suna masu durk'usar da kawunan su k'asa, sabo da kar kallon Bir da kuma jin sautin ihun su ya sanya su zubda hawaye, daga nan suma kuma su had'u da nasu hukuncin wurin Gimbiya Tasmir. Basu suka dakata da dukan sa ba har sai da sukaga gaba d'aya ya dena numfashi, a lokacin kuma tini suka huce awa guda da fara dukan sa. Ganin da Gimbiya Tasmir tayi kansa ya tuntsire yayi gefe ne, ga kuma jinin dake tsiyayowa ta ko ina daga jikin sa, tun daga tsakar kansa har zuwa tafukan k'afafuwan sa ne, ya sanya ta dakatar da su. Kana kuma taji bugun zuciyar ta ya sake sauyawa fiye da baya, ga wani irin tsoro da bata san kona mene ne ba da taji ya lullub'e ta, sai dai kuma duk maitar mutum bai isa ya gano halin da take ciki ba dan ya kalle ta. Da wani irin sauri ta d'aga takobin ta tana mai nuna sa da ita, kana ta furta kalmar. "Gargabilu!" Take kuwa igiyoyin nan suka tsits-tsinke gaba d'ayan su, Bir na fad'owa k'asa jikake Tim. Sannan ta juya tana mai nufar hanyar da zata mayar da ita gida ba tare da ta kula wa'yan nan dakarun nata ba. Da sauri suma suka take mata baya suna masu bin ta. Suna b'acewa daga wurin sai ga dan dazon bayi nan hankulan su atsantsar tashe sun yi kan Bir gadan-gadan. Yayin da Iyar Bayi kuma da wasu daga cikin Bayin suke wani irin kuka na tausayin halin da suka samu Bir a ciki. Da k'arfi Mazum ya shek'awa Bir ruwan da yake d'auke a hannun sa a gaba d'aya jikin sa. Take kuwa a wurin yaja wata irin doguwa ajiyar zuciya, yana mai bud'e idanuwansa da sukayi matuk'ar kumbura a hankali. Yayin da bakin sa kuma ke furta kalmar. "Gimbiyata!!!" Ganin jama'ar da yayi zagaye da shi ta ko ina ne ga Iyar Bayi da ta durk'uso gare sa tana rusar kuka ne ya sanya sa yin shiru, yana mai mayar

Chapter 29 of 76