rayuwar Asad da Al'amin kenan._
_BAYAN SHUƊEWAR SHEKARU BAKWAI._
*KASAR MALIN JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*✍
*KUYI MANAGE BANDA CAJI NE YAU.*
*BAƘAR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 22*
Tafe Ƴar yarinyar take a cikin tsakiyar wasu garadan maza da suke riƙe da bulalai a hannun su, suna masu tunkarar wata kujera da take kafe a ƙarƙashin wata inuwar bishiya.
Yayin da gefe da gefen bishiyar kuma wani irin farin ruwa kar yay mata ƙawanya.
Sanye take da wata doguwar riga ruwan hanta mai matuƙar tsayi a jikin ta tana sharar ƙasa, yayin da kanta kuma yake ɗage a sama tana mai yin wani irin taku, babu alamun far'a a fuskar ta ko kaɗan, ƙafafuwan ta kuwa sanye suke da wani irin azababben takalmin fata, yayin da ƙaurikan ƙafafuwan ƙafar ta kuma suke sanye da wasu irin saraƙunan gwal, masu matuƙar ƙyalli da ɗaukar ido suna futar da sauti.
Gimbiya Tasmir kanen, Yarinya mai kimanin shekatu bakwai a duniya cif-cif yanzu kenan, Yarinyar da ta-taso da tsantsar Izza, girman kai tare da miskilanci, domin kuwa ba taƙi ta kwana kana kuma ta yini ba ba tare da ta furta komai ba, haka kuma muddin ta biyo hanya to babu wani mahaluki da ya isa ya gifta wannan hanyar, idan aka cire mutanen da suke tare da ita tun a yanzu da take ƴar ƙaramar ta, idan kuma har akayi rashin sa'a mutum bai lura da tawowar ta ba har ta ƙaraso wurin da yake, to fah ranar ya shiga ukku ya lalace, domin kuwa Dakarun ta da suke take mata baya a kowane lokaci take sanyawa su zane masa jikin sa tas sa bulalai.
Ko kaɗan bata da tausayi, kuma bata san-sa ba ma, kamar yadda ta taso taga ahalin gidan nasu suke.
Ƴar gatace lamaba ɗaya a wurin mahaifin ta Sarki Barbaru, tare da kuma Yayen ta Maza.
Duk abunda ta nuna tana so to komun wahalar sa sai an samo mata shi, haka kuma muddin tace bata son abu to fa bata son sa, kuma babu wanda ya isa ya sanya ta taso shi.
Ci gaba da tafiya tayi kanta ɗage a sama, yayin da mayawaicin gashin dake ɗauke akan ta kuma yake ta reto a gadon bayan ta.
Cak ta tsaya lokaci ɗaya a wurin da take ba tare da ta sake ɗaga ƙafar ta ba, ba wai kuma dan ta cimma wurin da take son zuwan bane, sai dan kawai motsin sautin tafiyar mutum da ta jiyo a cikin kunnuwan ta.
A hankali ta fara sauke kanta daga saman da yake, tukun ta juyar da shi ɓarin hannun ta na hagu, tana mai kai idanuwan ta zuwa wurin da take jiyo sautin nan.
Take kuwa idanuwan ta sukayi mata arba da matashiyar budurwar da take gudu amatuƙar firgice, tana neman wurin ɓuya, sanye take da kayan Bayi ajikin ta, da alama dai bata lura da tawowar tasu bane da wuri sai da har suka ƙaraso wurin da take, shi yasa ba tayi saurin ɓuya ba.
Da sauri dakarun nan suka juya ɓarin da su kaga Gimbiya Tasmir ta kai idanuwan ta, domin kuwa sun sani bata waige idan har tana tafiya, sai idan taji sautin motsin wani abun ne.
Take kuwa suma suka hango wannan baiwar da take ƙoƙarin ɓuya hankalin ta atsan-tsar tashe.
Ɗaga hannu Gimbiya Tasmir tayi, tana mai yi musu nuni da ita ba tare da tace komai ba, tukun daga bisani ta sauke hannun nata ƙasa, tana mai cigaba da ɗaga ƙafafuwan ta tayi gaba, yayin da su kuma waƴan nan dakarun nata su kayi wurin da suka hangi baiwar nan gadan-gadan.
Cikin sakwannin da basu gaza talatin ba duka suka cimmar wa wannan baiwar.
Ɗaya daga cikin sune ya miƙa hannun sa zuwa wurin da take yana mai riƙo hannun ta da matuƙar ƙarfi, tukun ya funciko ta yana mai janyo ta ta faɗi a ƙasa, kana ya fara janta a cikin ƙasar yana mai juyawa ya doshi wurin da Gimbiya Tasmir take, suma sauran duka suka take masa baya.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir cigaba da tafiya tayi har ta ƙarasa ƙar-ƙashin inuwar bishiyar nan, inda wannan haɗaɗɗiyar kujerar take ajiye a kafe.
Tsaye tayi a gaban kujerar tana kallon ruwan nan da yake zagaye da bishiyar, wata irin sassanyar iska mai matuƙar daɗi na dukan jikin ta.
Kana ahankali ta juyawa kujerar baya, tukun daga bisani ta zauna akan ta tana mai ɗaukar ƙafar ta ɗaya ta ɗora ta akan ɗayar.
Kana ta fara girgiza ta a hankali, tana mai lumshe dara-daran fararen idanuwan ta masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali .
Tukun daga bisani ta wara su akan wannan fuskar baiwar da aka janyo ta cikin ƙasa, jikin ta na wata irin kar-karwa.
"Tuba nake ranki ya dade, tuba nake ki mun ai'kin gafara ya shugaba ta."
Baiwar nan ta faɗa jikin ta na tsantsar kar-karwa, a lokacin da wannan badakaren ya durƙusar da ita a gaban Gimbiya Tasmir, Yarinyar da a haife ta haife ta.
Shiru Gimbiya Tasmir tayi ba tare da tace komai ba, sai kawai fitinannun idanuwan ta da ta ɗora su akan fuskar baiwar nan tana mai jifan ta da wani irin kallon ƙasƙan ci, tukun daga bisani ta janye su daga kanta tana mai kai su wurin farin ruwan nan da yake kwance a cikin tafkeken rami.
Kana daga bisani ta ɗaga yatsar hannun ta manuniya, tana mai nuna ruwan nan da ita ba tare da tace komai ba, sannan ta sauke hannun nata ƙasa tana mai sake mayar da idanuwan ta ta lumshe su.
Yayin da shi kuma wannan badakaran ya sake cafkar hannun bawair nan da matuƙar ƙarfi, tukun ya cigaba da janta a cikin ƙasa yana mai nufar bakin ruwan nan da ita.
Suna ƙarasawa wurin ya ya saki hannun baiwar yana mai damƙar gashin kanta ta da matuƙar ƙarfi, kana ya fara danna kanta a cikin ruwan, sai ya nutsa sa tas a ciki tukun yake zaro sa ya sake mayarwa, a haka har sai da yayi kimanin sau ukku, tukun daga bisani ya futar da ita yana mai yin cilli da ita gefe.
Da sauri ta kife a ƙasa tana mai fara tafiya da rarrafe, ta doshi hanyar da zata ɓatar da ita daga wurin tana sakin wani irin tari, yayin da idanuwan ta kuma suka kaɗa sukai jajajir tamkar gauta, alamun ba ƙaramar wuya taci ba kenan, a tsomen da aka mata a cikin ruwan.
A ɓangaren Bayi kuwa sosai Bir yayi matuƙar girma, kana ya fara zama saurayi, domin kuwa a yanzu yana da kimanin shekaru goma shabiyar ne a duniya.
Kyakkyawa ne lamba ɗaya, dan ko ataƙaice ma shine ya zamto mafi kyawun mutum a cikin duka Bayin dake a cikin Baƙar Masarauta.
Har kawo yau yana nan da maitar kwari da gwafar sa, domin kuwa akan ta baiƙi ya yini cir da yunwa ba, dan kuwa mafi akasarin lokuta ma idan ya futa da ita baya dawowa cin abinci, har sai Iyar Bayi ta bisa ta tattago sa.
A yanzu haka bashi da wani buri wanda ya huce na haɗuwa da Gimbiya Tasmir domin ya ganta, sabo da tun da yake a cikin Masarautar har yau Allah baisa sun taɓa cin karo da itaba a hanya, kai asalima ganin sa da ita duka sai ya irgu, shima kuma yana faruwa ne aduk lokacin da ake wani taron biki a cikin Baƙar Masarauta, amma bayan wannan bai taɓa cin karo da ita ba, sai dai yaji labarin cewar yau ta huce ta wuri kaza a wurin su Mauzum, haka kuma zai ga sunzo jikin su na tsantsar kar-karwa, kana a kullum sai yaji bayi na labarin kwarjinin ta da rashin tausayin ta, wannan shine kawai dalilin daya sa yaji yana matuƙar son ya haɗu da ita wataran shima, domin ya gwada tsayuwa a gaban ta yaga mai zata masa, ko kuma shima zata masa kwarjini kamar yacce mutane suke faɗin tana musu, kasancewar sa mutun mara tsoro da shakkar kowa, domin kuwa babu wanda bai sansa da wannan halin ba a cikin bayi, kai harma da wasu daga cikin dakarun dake zaune a Baƙar Masarauta, sai dai kuma babu yadda zasuyi da shi, sabo da koda an dake sa ba ya fasa yin abun da yake yi, wato yiwa dakarun rashin kunya, gashi kuma gaba ɗayan su Sarki Barbaru ya shimfiɗa musu sharuɗa akan sa tare da gargaɗi, kana suma dukan su sun san tarihin samuwar sa a cikin masarautar.
A kusan kullum sai ya ritsa Iyar Bayi yana mai tambayar ta su waye mahaifan sa, amma sai dai kuma aduk lokacin da ya taso mata da maganar sai yaga gaba ɗayan ta-ta rude ta fuce daga hayyacin ta, a ƙarshe ma sai dai ta-tashi ta basa wurin, ko kuma tai ta roƙon sa akan kar ya ƙara yi mata wanna batun, muddin ba gajiya yayi da ganin ta a duniya ba.
To da zarar fa tace masa hakan sai ya haƙura ya tashi yay gaba, amma bawai dan ransa yaso ba, kuma hakan baya hanawa washe gari ya sake taran ta da maganar ma.
*ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.*
Tun bayan haihuwar Gimbiya Haddiyal Gimbiya Kaɓel mahaifiyar ta bata sake wata haihuwar ba, yayin da ita kuma Gimbiya Mairamu ta sake yin wata haihuwar amma ɗa namiji, wato har yanzu dai Gimbiya Haddiyal ce kawai ƴa mace a gidan.
Yayin da take da Shekaru bakwai dai-dai a duniya yanzu kenan.
Sosai take da wani irin kyawu mai matuƙar ɗaukar hankali tare kwarjini da Izza.
Ko kaɗan magana bata dame ta, kamar yacce hayani kuma ke takura mata, domin kuwa hatta da yayyin ta maza idan suka haɗu wuri ɗaya suna hira takura take yi sosai, wannan dalilin ne yasan ya akoda yaushe take ware kanta ta tafi can lambun da jinsin tsun-tsayen masarautar Fulɗe suke rayuwa a cikin sa.
Yayin da wurin kuma yafi mata daɗi sama da kowane wuri dake a cikin gidan nasu, hatta da ɗakin ta kuwa, domin kuwa ba ƙaramun birge ta tsun-tsayen suke ba, haka ako da yaushe zata tafi cikin su tun tana da shekara huɗu aduniya ta zaune tana watsa musu gero, kana kuma tai ta kawo labarai tana basu ba tare da tana da tabbacin suna jin abun da take faɗen ba, domin kuwa muddin kana son jin sautin muryar ta to da zarar kazo wurin tsun-tsayen har dai ta kasance itama a wurin, to zakaji hirarar ta har ka gaji, yayin da acikin gida kuma take tamkar kurma a koda yaushe.
Ada idan taje wurin tsun-tsayen tun daga nesa suna jin motsin ta gaba ɗayan su suke tashi su gudu, amma a haka zata ƙarasa zuwa mazaunin ta wanda ta saba zama akai, ta zauna ɗauke da ƙwaryar hatsi a hannun ta.
Kana ta fara ciko tafin hannun ta tana wats musu shi.
Ai kuwa haka gaba ɗaya zakaga sun sauko ahankali-ahankali suna tsintar geron, yayin da ita kuma zata tai kallon su tana sakin mirmushi, tare da lumshe idanuwa.
Haka kullum take yi musu ba safiya ba rana, tun tsuntsayen suna guduwa idan tazo wurin, har ya zamto anzo lokacin da suka dena gudun ta gaba ɗaya, wato sun gane ba mai cutarwa bace gare su ita ɗin, domin kuwa gaba ɗaya dawowa sukai suna hangen ta zasu yo wurin da take a guje, kamar yadda dama can kaji da agwagi suka yi saurin sabawa da ita, kuma suke tawowa wurin ta a duk lokacin da taje wurin su, domin kuwa tsun-tsayen da suke a cikin masarautar Fulɗe sun kasance kaloli daban-daban ne, haka kuma babu wata kalar tsuntsuwa da kusan za'ace basu da ita.
A duk lokacin da tsuntsayen nan zasuga ta shigo wurin, to haka zasu tawo aguje suna masu yowa kanta ko wanne na sakin nasa kalar kukan, yayin da ita kuma zatai ta ɓaɓɓaka dariya tana mai shafa su tare da shawagi a cikin wurin, cikin tsantsar farin ciki da annashuwa, tukun a ƙarshe kuma ta koma kan shimfiɗar ta-ta zauna, kana suma duka su biyo ta suna masu sauka a gefen shimfiɗar, sannan ta fara ciko tafukan hannyen ta da gero tana watsa musu, tana yi tana basu labarai tare da dariya cikin tsantsar farin ciki.
Yayin da shi kuma malam buɗa mana littafi ya zamto abu na farko data fiso sama da komai arayuwar ta idan aka cire ahalin ta, domin kuwa shi yana ɗaya daga cikin abubuwan da suka zamto mahaɗi na tsafin da yake ɗauke a jikin ta, wato muddin tana buƙatar yin wani abun, to da zarar ta buga sandar tsafin ta, ko kuma taje wurin da ciyayi suke ta buge su, zakaga sun taso da yawan su masu tsanin kyau suna hawa kan tafukan hannyen ta, kana kuma idan har tana son su nuna mata wani abun, to da zarar ta faɗa musu buƙar ta zasu tashi su kaita har wurin da abun yake, sannan kuma zata iya cutar da mutum da su muddin taso yin hakan, sai dai kuma ita ɗin ta kasance babu ruwan ta ko kaɗan, domin kuwa ko bayin gidan su ba ƙaramun jin daɗin ta suke yi ba, kana kuma bata damu da sai an mata rakiya ba dan zataje wani wurin, asalima ita tafison tayi tafiyar ta ita kaɗai, sabo da a ganin ta duk ƙarin hayaniya ne dogarawan zasu sanya mata ba wai tsaro zasu bata ba.
Wannan dalilin ne ya sanya ko lambu idan zata tafi take tafiyar ta ita kaɗai ba tare da ta bari sun biyo ta ba.
Babu yadda ba ayi ba da Lamiɗo akan ya bari akai ta Makarantar Boko dake ac ikin Jahar Wasai ta kwana, wacce aka yita domin ƴaƴan sarakai da kuma ƴaƴan attajirai kawai, amma gaba ɗaya ya yaƙi amicewa, a cewar sa ba zai taɓa barin ta tayi nisa da shi ba amatsayin ta na ɗiyar sa ƴa mace ƙwalli ɗaya ƙwal da yake da ita a duniya, domin kuwa shi afannin sa har yau baiga wani amfani da karatun bokon yake da shi ba, suma kuma su Buba ya yadda an kaisu ne sabo da babu yadda zaiyi, gwamnati ce tace dole sai ya bayar, amma banda haka da ba zai bada su ba.
Haka dai akai ta takura masa da naci akan ya kaita amma yaƙi, domin kuwa shi ko karatun addini ma ba damun sa yayi ba balle kuma suce dole sai anyi na bokon, a ƙarshe dai da ƙyar aka samu aka shawo kansa ya bari aka kaita wata makarantar boko da take anan cikin Jahar Kagul, itama ɗin dai ta ƴaƴan masu kuɗin ce, sai dai kuma ya bari ne itama sabo da ance masa bata kwana bace ba, kullum yaro yake zuwa ya koma gida, hakan ne yasa ya tanadi lafiyayyan doki ma tsanin girma da kyawu ya bayar ake kaita akan sa, sannan ajira har a tashi, tukun a ɗakko ta a dawo da ita gida, yayin da masarrafin dokin kuma yake sarrafasa da hannu ɗaya, hannun sa ɗayan kuma yake zamtowa riƙe da lemar da take kare ta daga zafin rana, a haka zasuyi ta tafiya a hankali har sukai makarantar kullum.
Yanzu haka zaune take a gefen wani farin ruwa mai tsanin haske, ta zura ƙafafuwan ta biyu a ciki tana ta faman wawwantsala ruwan da su, yayin da gefe da gefen ruwan kuma ya kasance zagaye da wasu irin korayen ciyayi da furanni masu matuƙar kyau da ƙamshi, da suka yiwa ruwan ƙawan ya.
Sanye take da fararen kaya irin na fulani da sukayi matuƙar yi mata kyau da amsar jikin ta, yadda kasan dan ita kawai aka ƙir-ƙire su, yayin da gashin kanta kuma ya kasance tufke a wuri ɗaya yana ta faman ƙyalli da ɗaukar ido.
Gaba ɗaya gefe da gefen ta tsuntsaye ne a wurin dukan su a diddirƙushe suna kallon ta, yayin da ita kuma take wani irin lumshe idanuwan ta tana mai buɗe su, wani irin farin ciki mara misaltuwa na cigaba da gauraye ilahirin jiki da zuciyar ta, sabo da tino sautin daddaɗar busar sarewar da tayi mafarkin ta adaren jiya mai matuƙar zaki da take mata amsa kuwwa acikin kunnen ta.
Tun da take bata taɓa yin irin mafarkin da tayi jiya ba, hakan ne yasa ya mata arai har kawo yanzu ba tare da ya ɓace ba, kuma ba komai bane ya faru a cikin mafarkin nata sai wani irin saurtin daddaɗar busar sarewa, mai matuƙar zaƙi da ta dinga ji yana dukan dodon kunnen ta, yayin da tai ta faman laluben wurin da sautin yake futowa a cikin mafarkin amma bata gano sa ba har zuwa lokacin data farka daga baccin.
Shine fa yau tun da safe ana gama shiryata ta tawo wurin tsuntsayen ta tana mai basu labarin zaƙin busar da taji ɗin, wacce ta rasa gano ta inda take futowa, sai dai kuma ko yauma tana fatan ta sake mai-mata irin mafarkin nata na jiya.
*JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*
Tun bayan tafiyar su Asad da ƴan kwanaki sai hankalin Gimbiya Fulani ya kwanta sosai, sabo da labarin da sukaji na cewar tunda suka bar cikin Masarautar Wasai bai kuma koda firgita ba balle suma.
Hakan ne yasa daga ita har mai martaba sukayi matuƙar jin daɗi, sanan kuma hankulan su ya kwanta, domin kuwa ita Gimbiya Fulani dama damuwar ta tafi ƙarfi ne akan Asad, sabo da shi akafi sanyawa ido fiye da Babban yaya, sannan kuma shine mai wasa da azkar.
Tun da suka tafi basu zo ƙasar ba sai bayan cikar su shekara guda da barin ta.
Sai dai kuma sunzo ne da sabon salo tare da sabuwar al'ada cikin masarautar, domin kuwa ba ƙaramun rikicewa Gimbiya Fulani ta sake yiba alokacin da taga yadda Asad ɗin nata ya koma.
Gaba ɗayan sa ya canza ya koma wani irin miskili, ga wata irin sabuwar al'ada da suka ɗaukko acan garin ta sanya ƙananan kaya, gwanda-gwanda Al'amin ma da yazo yasa manyan kaya akan Asad, domin kuwa shi gaba ɗaya nunawa yayi bama zai iya sa su ba, sannan kuma gaba ɗaya tunda sukazo ɗin bai kalli ko hanyar fada ba, Asalima da Gimbiya Fulani tace suje su gaida mutanne fada nuna mata yayi shi bazai iya zuwa ba, sabo da yana zuwa zasu fara yi masa magana da ƙarfi a cikin kunne, haka tanaji tana gani yaƙi zuwa sai Al'amin ne kawai yaje.
Shi kansa Mai Martaba babu yadda baiyi ba da Asad akan yaje Fada, amma ya ƙeƙyashe idanuwan sa yaƙi, domin kuwa shi kansa sai zamtowa yayi idan yana son ganin sa sai dai yazo nan part ɗin Gimbiya Fulani ɗakin sa ya gansa, ko kuma shi Asad ɗin ya yaje part ɗin mai martaba, amma ba dai cikin fada ba.
Hankalin mai martaba bai sake tashi ba sai alokacin da ya kawowa Asad sababbun ɗinkunan da yayi musu tare, na wata haɗaɗɗiyar shadda ɗinkin riga da wando tare da malum-malum yace masa ya sanya su ranar wata juma'a.
Take a wurin kuwa Asad ya fara bin kayan da wani irin mugun kallo, tukun aƙarshe ya juyar da kansa gefe yana mai buɗar baki yace.
A gaskiya ni Abba bazan iya sa waƴan nan manyan kayan ba, haba dai, sai kace wani ɗan ƙauye, kuma mai ai idan nasa waƴan nan zafi ma kusa kashe ni zaiyi."
Ya ƙarasa maganar da juyar da kai gefe yana mai ture kayan daga kusa da shi.
Sakin baki Mai Martaba yayi yana kallon sa ba tare da ya iya cewa komai ba, tukun daga ƙarshe ya durƙusa a gaban sa yana mai dafa kafaɗun sa ya fara lallaɓa sa dan yasa kayan, amma ƙiri-ƙiri Asad ya nuna shifa bazai iya sasu ba, haka Mai Martaba yana ji yana gani dole ya haƙura ya barsa yasa ƙananan kayan sa.
Wata ɗaya cir sukayi a garin, tukun suka juya ƙasar Dubai, kasancewar dama hutun makaranta ne suka yi shiyasa har sukazo ɗin ma.
Haka dai abu yay ta tafiya duk zuwan da Asad zaiyi garin baya tabɓa sanya manyan kaya, sannan kuma baya wani shiga cikin mutane, Asalima ko da sunzo lokacin hawa to in'da ake hawan ma baya zuwa, balle har yace zaiyi sa kamar yadda yake maitar sa abaya, kai ataƙaice ma dai idan Al'amin yace masa yazo suje, haka yake cewa Allah ya kiyaye shi da ba bagidaje ba yaje wurin can, duka uwar me ma ake yi a wurin bayan harkar ƙauyanci da iface-iface.
A cikin duka abubuwan da ake gudanarwa acikin masarautar abu ɗaya ne kacal bai barsa ba, wato Doki, domin kuwa har yau idan yazo sai ya hau dokunan sa, kamar yadda yake da su acan ma gidan su na Dubai da Alahaji Abubakar ya siya musu su duka, sabo da masifar son sa da yake yi.
A ɓangaren Babban yaya sosai shima ya girma ya zama saurayi, domin kuwa ayanzu yana da kimanin shekaru Ashirin da biyar ne aduniya.
Yayin da afannin karatun sa kuma yake a matakin masters, kasancewar duka karatun nasa aƙasar turai yayi sa ne shiyasa yay masa matuƙar sauri.
A ɓangaren magautan Gimbiya Fulani su kuma sosai sukai farin ciki da yadda Asad ya dawo, domin kuwa sun riga da sun sani muddin ya ɗore a wannan halayyar da yake ta yanzu, to har Abada babu shi babu zama akan karagar kujerar sarki, hakan ko shine yasanya hankulan su sukayi matuƙar kwanciya ta fannin Asad, kana suka koma suka duƙufa akan Babban Yaya da kullum kuma suke abun baya cin sa.
Sai dai kuma suna ganin ayanzu an kusa azo lokacin da shima zai cisa, tun da yanzu sun riga da sun gama da babin Yarima Asad, to ko mai da zasuyi akan sa ne shi kaɗai yanzu, domin kuwa su dama burin su karsuyi mulki, kuma sun san Asad ayanzu yayi hannun riga da mulki har abada, tun da aikin su yaci akan sa.
*UNGUWAR ƊAN TAKI*
Abubuwa da yawa sun fara tun da ga kan marasa daɗi har zuwa kishiyar su, waƴan da cikin su kuwa suka haɗa har da mutuwar mahaifin Ishaƙ da yayi tsawon shekara guda yanzu kenan, da kuma auren Babbar ƴar Aishatu da Ishaƙ da akayi, wato mai bin Ahmad da yanzu kowa ya koma kiran sa da Sheik Ahmad a cikin unguwar su tasu harma da wajen ta, kasancewar sa na Babban matashin malami da ake ji da shi acikin unguwar, domun kuwa yanzu haka yana riƙe da har makarantun islamiyya biyu anan cikin unguwar tasu, yayin da yake koyar da manyan iyaye maza kuma aduk bayan sallar asubahin duniya.
A yanzu haka yana da shekaru Ashirin da biyar ne cif aduniya, amma idan mutum ya gansa muddin ba sanin adadin shekarun nasa yayi ba zai ɗauka ya kai irin ashirin da takwas ɗin nan ne, sabo da yadda yake da tsan-tsar nutsuwa, haiba tare da kamala tattare da shi, waƴan da kuma duk sun samu ne ta dalilin ilimin addinin da yake ɗauke da shi acikin kansa, kana kuma yake amfani da shi ako da yaushe.
Yayin da a karatun sa na boko kuma yake amatakin level 4 na jami'ar gwamnantin tarayya da take a nan cikin garin wasai.
Wato Federal University Wasai, inda ya fara karantar Islami study acikin ta, kafin daga bisani kuna ya koma Qur'anic Hadith, alokacin da yaje lavel 3.
Sosai yake da matuƙar ƙwazo fiye da duk sauran ɗaliban da suke a department ɗin nasu, domin kuwa akowane lokaci idan har aka kafe musu exarm makin sa yana fin na duk sauran ɗaliban, wato dai shine over roller na department ɗin nasu gaba ɗaya, wanda hakan kuma yasanya malamai da dama daga cikin malaman su suke bala'in ji da shi.
A ɓangaren Aishatu kuwa har kawo yau bata bar tinane-tinane ba tare da zaman cikin ɗaki, domin kuwa ko da tayi kamar zata dena da zarar ta kwanta bacci idan tayi mafatkin yaron nan da ta saba yi, wanda take ganin sa akullum yana ƙara girma, sai taji komai na dawo mata sabo, kana kuma har yau bata futar da tsammanin sake saduwa da ɗan na ta, da ta rabu da shi tun a wurin da ta haife sa, kamar yadda akullum zuciyar ta take bata cewar yana nan araye ba akashe sa ba shi.
A fannin kaka kuwa yanzu ta koma masifaffiya lamba ɗaya, domin kuwa a kullum sai tayi faɗa da jikokan nata musamman ma Sheikh Ahmad, kuma ba komai ne yake haɗasu ba sai tsohuwar da yaran suke ce mata, yayin da ita kuma ta tsani a kirata da tsohuwa, duk
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 76