ɗaga yana mai harbin ta da ita ta baya, hakan yasa ta tafi taga taga tana mai kifewa a ƙasa kanta ya sake dukan wani icce, tayadda har sai da ya fashe jini ya futo, amna a haka ta sake miƙewa tana mai sakin kuka
Yayin da shi kuma wannan badakaran ya cigaba da tafiyar sa babu ko ɗigon imani tattare da shi, yana mai fucewa daga cikin jirgin.
Kai tsaye ya doshi kan shimfiɗar nan mai ɗauke da huta a kanta.
Miƙawa Boka mai hutar kasko jinjirin dake tsala uban kuka yayi, yayin da daga can bakin jirgin kuma wani badakaran ya tare wannan matar uwar jinjirin, da take shirin futowa yana mai sanyata ta duƙushe akan guiwoyin ta, tana hangen Ɗan nata daga nesa.
Matsawa Sarki Barbaru yayi zuwa gaban kaskon huta shima, yayin da Boka mai hutar kasko kuma ya tashi daga hurin da yake zaune, hannun sa riƙe da jinjirin, yana mai matsawa gaban kaskon nan, tukun ya durƙusa yana mai kwantar da shi a kusa da kaskon.
Hutsil-hutsil yaron ya farayi yana mai cigaba da tsanyarewa da kuka, sai dai kuma har bayan shuɗewar daƙiƙa goma ko kaɗan ƙafarsa bata taɓa jikin kaskon nan ba, balle harya tuntsirar da shi, hakan da suka ganine yasan ya Sarki Barbaru buɗe baki cikin muryar sa mai matuƙar amo da firgitarwa, yana mai faɗin. "Bashi bane wannan ma, dan haka matso ka caka nasa kibiyar shima." Ya ƙarasa maganar da kallon wani badakare da yake tsaye agefe.
Wata irin ƙara Uwar jinjirin nan ta saki, sabo da jin abun da Sarki Barbaru ya faɗa da tayi, ga kuma ganin da tayi badakaran yayi wurin jinirin gadan-gadan.
Da sauri wannan badakaran da yake tsaye a gaban ta ya damƙi tsintsiyar hannun ta, sabo da yadda yaga tana shirin fucewa daga cikin jirgin.
Yayin da shi kuma wancan da Sarki Barbaru yayiwa magana ya ƙarasa gaban Jinjirin nan, tukun ya durƙusa ƙasa yana mai sa hannu ya ɗauki kibiyar da take ajiye kusa da kaskon huta, sannan ya ɗago tsaye yana mai ɗaga ta sama, tukun yayi ƙasa da ita yana mai cakata a dai -dai ƙawon zuciyar jaririn!
Wata irin gigitattar ƙara Uwar jinjirin nan ta saki, tana mai zubewa a ƙasa sumamma, sabo da yadda taga an yiwa jinjirin nata da bai san hawa ba bare sauka, wanda bashi da haƙƙin kowa a kansa kisan gilla akan idon ta.
Yayinda Aishatu kuma ta saki wani irin salati da matuƙar ƙarfi, wanda ya janyo hankalin duka mutanen wurin, tunda ga kan su Sarki Barbaru har zuwa mutanen cikin jirgin nan da suke tare, tana mai rumtse idanuwan ta tare da yarfa hannun ta, sabo da wani irin mugun murɗawa da taji cikin ta yayi, ga kuma bayan ta daya riƙe gam, banda jujjuya kai tare da sakin nishi babu abun da take iyayi.
Gumi ke yanko mata ta kowace kafar gashi dake jikin ta, sabo da yadda ciwon naƙuda ya taso mata gadan-gadan, a kuma lokaci ɗaya.
Da sauri Ishaƙ ya dafa bayan ta yana mai girgiza kai, hankalin sa a bala'in tashe, kafin daga bisani kuma wasu irin hawaye masu matuƙar gudu suka ɓalle daga cikin idanuwansa suna tsiyaya akan kuncin sa.
Yayin da Sarki Barbaru kuma ya buɗe baki cikin amo yana mai faɗin.
"Ga wata nan zata haihu yanzu, dan haka ku shiga ciki ku anso mana sauran yaran kafun muga wanda zaizo natan."
Ya ƙarasa maganar da kallon dakarun nan nasa.
Take kuwa suka tafi zuwa cikin jirgin, domin su anso sauran yaran da suke a ciki, yayin da ita kuma Aishatu take cigaba da sakin nishi, hannun ta dafe da ƙasa tayi durƙushe, yayin da ɗayan hannun nata kuma ya kasance dire akan cikin ta da take jin abun cikin na motsawa, yana neman hanyar futa.
Cikin sauri Ishaƙ ya fara buɗe jakar kayan ta da take ajiye a kusa dasu idanun sa na zubar hawaye, nadamar barin Aishatu tazo gaisuwar mahainfin ta na cika zuciya da ruhin sa.
Zannuwa ya ɗauko har kimanin guda huɗu.
Ninka guda biyu yayi yana mai shimfiɗa su aƙasa, tukun ya sanya hannu yana mai matso da Aishatu da zuwa yanzu bata fahimtar komai, sabo da tsantsar azabar ciwon da take ji zuwa kan shimfiɗar, sannan ya ware guda biyu yana mai miƙewa tsaye ya fara ƙoƙarin yin dabara wurin ganin yayi mata rumfa da zannuwan, ganin hakan da matan cikin jirgin sukayi ne yasan ya wasu daga cikin su har kimanin mutum huɗu sukayo wurin da suke, gaba ɗayan su hankulan su a tsantsar tashe, yayin da idanuwan su kuma ke tsiyayar da ruwan hawaye yadda kasan an buɗe famfo.
Karɓar zannunwan matan sukayi a hannun Ishaƙ, tukun biyu daga cikin su suka buɗasu suna masu zagaye Aishatu da shi daga tsaye, ya zamto sun mata ɗan ɗaki kenan, yayin da biyu daga ciki su kuma suka shiga cikin dan ɗakin zannuwan, sabo da su taimaka mata.
Acan ɓangaren dakarun nan kuwa, cikin rashin imani suka sake ƙwato wasu yaran har guda biyu a cikin jirgin a hannun iyayen su, suna tsantsar kuka.
Ɗaya jinjirin duka watan sa biyu aduniya, yayin ɗayan kuma yake da wata ukku aduniya.
Suma ɗin tawowa sukayi da su zuwa kan shimfiɗar nan, tukun aka ajiye na farko a gaban kaskon huta, amma sai dai shima har bayan wucewar daƙiƙa goma da ajiye sa bai bige kaskon nan ba, hakan ne yasa Sarki Barbaru ya sanya aka luma masa kibiyar nan a ƙawon zuciya shima.
Wata irin gigitattar ƙara uwar jinjirin ta saki, tana mai miƙewa a zabure zata afka cikin ruwa, amma sai wasu maza guda biyu da suke a gafen wurin da take sukayi saurin kamata suna masu kaita ƙasa, yayin da ihun da ta saki kuma ya daki kunnuwan Aishatu da matuƙar ƙaraji, wanda ya ƙara sanya cikin ta ya ƙara wata irin murɗawa fiye da baya sosai.
Cikin tsantsar zafin ciwon da takeji ta sanya hannun ta tana mai dan buɗe zanin da ake zagaye ta da shi, tukun ta zura kanta waje tana mai kai idanuwan ta zuwa wurin da su sarki Barbaru suke, wanda hakan kuma yayi dai-dai da lokacin da wannan badakaran ya sake ɗaga kibiyar nan yana nai cakawa ɗayan jaririn aƙawon zuciya shima, kasancewar bai bige kaskon nan ba shima ɗin.
Wata irin gigitattar ƙara Uwar jinjirin tare da Aishatu suka saki a lokaci guda, tukun daga bisani kuma sai ga kukan jinjiri nan ya biyo baya da matuƙar ƙarfi...!
*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*
Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa sosai take jin jiki, yayin da hadimar ta Larai kuma ke tsaye akan ta tana ta faman yi mata sannu, tare da sharce mata gumin dake tsats-tsafowa akan goshin ta.
Kiran sallah'r da aka kwaɗa a cikin masallacin masarautar yayi dai-dai da bayannar kukan jinjiri da matuƙar ƙarfi.
"Alhamdulillahi rabil alami." Gimbiya Fulani ta faɗa tana mai mayar da numfashi, tare da lumshe idanuwan ta, kasancewar abun da ke cikin nata na faɗowa itama mabiyar ta biyo sa.
"Ayiri-yiri-yiririiiiiiiiiiiiii!"
Hadima Larai ta saki wata mahaukaciyar buɗa mai matuƙar sauti a lokacin data kai idanuwan ta kan gaban jinjirin, sabo da yadda idanuwan ta suka mata arba da santalelen jinjiri Ɗa namiji.
Ƙara sakin buɗa tayi da matuƙar sauti, tukun daga bisani ta durƙusa ƙasa tana mai yankewa yaron cibi, sannan ta ɗauke sa tana mai naɗe sa acikin wani lallausan showel, tukun ta juya cikin sauri tana mai kama hanyar waje hannun ta riƙe da yaron.
Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani ta matsa daga hurin da take tana mai mayar da numfashi, tare da lumshe idanuwan ta.
Kai tsaye Hadima Harai ta doshi waje hannun ta ɗauke da jinjirin, sannan kuma har lokacin bata bar sakin buɗar da take yi ba, bakin ta na furta kalmar.
"Masha Allahu! Masha Allahu!! Masha Allah da zuwan ka duniya Ɗan albarka!!! Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai mai kowa mai komai.
Yau ranar tamuce mu mutanen gida, domin kuwa ƙaruwar tamuce tazo, ƙaruwa irin wacce aka daɗe ana mararinta da jiran ta.... Haihuwar Ɗa namiji ba kowa ba a wanga gida, haihuwar namiji sai ɗiyar sa'a a wanga gida, zama Uwar Sarki sai Ƴar Sarki Jikar Sarki, sannan kuma Matar Marki."
Hadima Larai take ta faɗa da tsantsar ƙarfi tana mai cigaba da tafiya tare da sakin buɗa.
Yayin da ɗaukacin jama'ar dake rayuwa a ɓangaren Gimbiya Fulani kuma suka furfuto daga cikin ɗakunan su da tsantsar gudu, domim kuwa koda basu san meke faruwa ba muryar hadima Larai kawai ta sanar da su.
Aɓangaren Hadima Larai kuwa cigaba da tafiya tayi tana mai sakin kalamai iri-iri, hannun ta ɗauke da jinjirin da yake ta aikin tsala kuka ko wanka ba ayi masa ba, tana mai nufar hanyar da zata sadata da wurin buga Tambarin murna, kasancewar haka al'adar gidan sarautar nasu take, muddin wata daga cikin matan gidan suka haihu, to da zarar an yanke wa abun da aka haifa cibi za'a ɗauke sa a tafi da shi wurin buga Tambari, shi kuma wannan Tambarin shine ke sanar da duk jama'ar dake cikin masarautar haihuwar, sabo da tsananin ƙarar sa, sannan kuma bawai kai tsaye ake bugasa ba da zarar an kai jinjiri, a'a sai sun fara dubawa sun ga namiji ne ko mace, tukun a ɗauki makaɗi a fara bugasa, kasancewar kowane jinsi yana da kalar bugun da ake masa, tayarce da zarar an buga sa mutanen dake cikin gidan suke fahimtar jinsin dlƊan da aka samu, mace ko namji ta hanyar kiɗan.
"Ayiri-yiri-yiririiiiiiiiiiiiiii."
Hadama Larai ta sake rangaɗa buɗa a dai-dai lokacin da ta shiga wurin, tana mai girgiza jinjirin da yake ta ai'kin tsanyara kuka shima.
Kafun kace tak, tuni mutnen da suke zaune cikin wurin sun futo da tsantsar gudu.
Tun kafin su ƙaraso wurin da take ta yaye showel ɗin dake ƙudun-dune a jikin jinjirin, tana mai ɗaga jaririn sama tayi musu nuni da shi.
Take kuwa wani dattijon tsohon mutum da yake sanye da babbar riga a jikin sa ya juya yana mai dosar wurin da wasu manyan ƙarafuna suke a kafe jikin bango, wato Tambarin murna.
Durƙusawa yayi ƙasa yana mai sa hannu ya ɗauki wani ƙarfe mai kama da taɓaryar ƙarfe, amma sai da shi wannan dogo ne sosai, tukun ya ɗago yana mai ɗaga sa ya fara dukan Tambarin farko da yake a ɓangaren wurin da yake a tsaye, wato na namiji kenan.
Take kuwa wani irin sauti mai daɗi ya fara tashi da matuƙar ƙarfi, tayarce har sai da ya karaɗe ko ina na cikin masarautar, yayin da su kuma mutanen dake cikin wannan hurin suka toshe kunnuwan su suna rawa tare da kaɗa manyan rigunan su, sabo da yadda sautin yake ratsa har cikin kwanyar su.
Ita kuwa Hadima Larai cigaba da ɗaga Jinjirin nan sama tayi tana mai rawa a tsakiyar filin hurin, yayin da shi kuma jaririn keta aikin tsanyara kukan sa.
A ɓangaren Gimbiya Huwaila kuwa tashin ta kenan daga kan gado taji sautin bugun tambarin samuwar yaro namiji na dukan kunen ta.
Wata irin zabura tayi tana mai miƙewa zaune daga kwancen da take akan gado, tukun daga bisani ta fara girgiza kanta tana mai faɗin.
"Inaaa bazai yuwu ba Wallahi Tallahi, shin me bugun tambarin Ɗa namijin da kunnuwa ne suke jiyo mun yake nufi kenan?"
Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai miƙewa tsaye, tukun ta duro daga kan gadon da take yarce kasan wata zararriya.
"Ɗa namiji acikin gidan nan kuma? Shin dama akwai wata mai cikin ce bayan Fulani agidan nan ne da har kunnuwa ne suke jiyo mun sautin bugun tambarin Ɗa namiji?"
Ta sake faɗa tana mai juyi acikin ɗakin nata cikin tsantsar tashin hankali.
"A'a, babu wata bayan ita dake da ciki a cikin gidan nan, kenan hakan na nufin itace ta haifo Yaro namiji kuma yazo da ransa?
Inaaaa!!!! Hakan bazai yuwa ba, Wallahi Tallahi ƙarya ne..."
Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai kama hanyar waje!
Ɓangaren Gimbiya Suwaiba matar mai martaba ta biyu kuwa, futowar ta kenan daga cikin bathroom bugun tambari samuwar yaro namiji acikin masarautar tasu ya daki dodon kunnen ta.
Da matuƙar sauri ta dafe bangon ɗakin ta, sabo da yarce taji ƙafafuwan ta sun zame tana shirin kifawa ƙasa, tukun daga bisani ta koma tana mai zama yaraf a ƙasa, wato zaman daɓaro, tare da ɗora hannuwa biyu aka.
A ɓangaren Jakadiya kuwa tamkar a mafarki taji bugun tambarin samuwar Ɗa namiji na dukan kunnuwan ta, kasancewar ita bata kaiga tashi ba a lokacin.
Ahankali ta fara buɗa idanuwan ta tana mai yamutsa fuska, kafin daga bisani kuma tayi wata irin miƙewa tsaye daga kwancen da take zumbur tana mai zaro idanuwa waje, tare da dafe ƙirjin ta da hannu, sabo da yadda ta jiyo sautin na dukan kunnen ta da matuƙar ƙarfi, alamun ba mafarki take ba a zahiri abun ke faruwa kenan.
"Ɗa namiji?...Gimbiya...Fulani?..ta sake haihuwar sa yanzu ma?"
Ta faɗi magan-ganun a rarrabe, sannan kuma ta sigar tambaya, tana mai zaro idanuwanta waje, tukun daga bisani ta juya tana mai miƙa hannun ta ta janyo mayafin ta da tsantsar sauri, sannan ta durƙusa ƙasa tana mai ɗibar takalman ta a hannu ba tare data tsaya sanya su ba, ta doshi hanyar waje tamkar ta kifa a ƙasa sabo da saurin da takeyi.
A ɓangaren mai martaba kuwa futowar sa kenan daga bathroom ya ɗauro alwala, sautin bugun tambarin samuwar Ɗa namiji ya daki dodon kunnwan sa.
Cak ya tsaya a inda yake yana mai sakin baki da kunnuwa, kai harma da hanci, sabo da yarce yaji abun tamkar al'mara a kunnuwansa, yayin da shi kuma sautin nan ke cigaba da tashi da matuƙar ƙarfi ko kaɗan ba'a da niyyar denawa.
Sai da ya ɗauki kimanin mintina tsawo biyar yana tsaye a wuri ɗaya, tukun daga bisani yayi firgigit ya dawo hayyacin sa yana mai furta kalmar.
"Al'hamdulillah! Alhamdulillahi!! Alhamdulillah!!!"
Kafin daga bisani kuma ya durƙusa ƙasa yana mai kai goshin sa ƙasa yayi sujudu shukur ga rabbil izzati, sannan bayan ya gama ya ɗago idanuwan sa na zubar da ƙwallar murna, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Masha Allah, ashe nima ina da rabo sake haihuwar Ɗa namiji a duniya, ashe wannan dalilin ne ya hana Fulani zuwa wurina jiya bayan nasa jakadiya ta kira ta, kai Alhmadulillahi rabbil alamin."
Ya faɗa cikin tsantsar murna yana mai miƙewa tsaye ya doshi hanyar waje, daga shi sai jallabiya ajikin sa ko al'kyabba bai yafaba kamar yacce ya saba ako da yashe, sabo da tsantsar farin cikin da ya tsinci kansa aciki wanda ya mantar da shi wata alkyabba ma.
*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*
Da matuƙar sauri Sarki Barbaru ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Ta haihu, dan haka kuyi maza maza ku shiga ciki ku anso mun shi tun kafin ta fara sabo da shi, domin kuwa wannan Yaron badan ita Ubangiji Gargabilu yayo saba, yayo sane domin mu."
Atare mutanen cikin jirgin suka fashe da kuka hatta da mazan dake ciki, sabo da jin furucin Sarki Barbaru da sukayi yana yi akan Ɗan da ya diro duniya yanzu -yanzu.
Yayin da shi kuma jaririn ke aikin tsanyara kuka da matuƙar ƙarfi yana mai ciccila ƙafafuwan sa sama.
Cikin sauri matan nan suka fara ƙoƙarin gyarawa Aishatu jikinta, sabo da jin furucin Sarki Barbaru da sukayi, domin kuwa sun san da zarar mutanen sun iso zasu kwaye zannuwan da sukai mata sutura da su.
Yayin da ita kuma Aishatu ta miƙa hannu da sauri tana mai shirin ɗaukar ƙatoton farin jaririnta mai tsananin kyau a ƙasa, wanda ada duk suke tinanin cikin sa bai huce wata takwas ba, sai kuma gashi a yanzu take ganin girman Ɗan yafi ƙarfin a kira sa da Ɗan wata twakas.
Hannuwan ta suna tsantsar rawa, kamar yadda jikin ta ke rawa ta miƙa su tana shirin ɗaukar jaririn dake cigaba da tsanyara kuka tare da cilla ƴan ƙafafuwa sama, amma sai dai kuma hannun nata yana daf da kaiwa jikin Ɗan taji ansa ƙafa an make sa da matuƙar ƙarfi, tayarce har sai da ta tuntsira baya tana mai faɗawa jikin Ishaƙ da yayi saurin tarota, kasancewar babu ƙwari jikin nata ko kaɗan.
Wani danƙareren baƙin badakare ne da yake riƙe da zureriyar takobi a hannunsa, yasa ƙatuwar ƙafar sa ya bige hannun nata da ita, tukun ya durƙusa ƙasa yana mai sa hannu ɗaya ya tallabo jinjirin da yake ɓace da jini zuwa jikin sa.
Wata irin gigitattar ƙara Aishatu ta saki tana mai miƙewa tsaye tayi kan mutumin nan, tare da buga tsalle ta shaƙi wuyan sa yadda kasan ba itace ta haihu yanzu ba, domin kuwa lokaci ɗaya gaba ɗaya taji ciwon da takeji a jikin ta ya ɓace ɓat, sai ma wani irin ƙarfi da taji yazo mata, tayarce har take jin zata iya yaƙar uban kowa akan jinjiri nata.
Guiwar hannun sa badakaran nan yasa yana mai dukan cikin ta da ita.
Take kuwa ta saki wuyan sa tana mai yin baya luuu ta kifa akan jikin Ishaƙ da yayi saurin matsawa wurin da take, a lokacin da take shirin faɗuwa.
Banda aikin kuka tamkar ransa zai futa babu abun da yake iyawa, yayin da ita kuma Aishatu ta faɗa jikin sa tana mai wani irin zare idanuwa, tare da taunar leɓen ta da matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani ta saki leɓen nata tana mai buɗe baki tana wuri-wuri da idanuwa, gaba ɗayan ta ta fuce daga hayyacinta, sabo da yadda cikin ta yayi wata irin ƙullewa ta sanadin dukan da mutumin nan ya mata.
Banda koke-koke babu abun da ke tashi a cikin jirgin, domin kuwa zuwa yanzu babu wani mahaluƙi dake cikin jirgin da ya iya cigaba da riƙe kukan sa.
Wata irin ƙara Aishatu ta ƙara saki tana mai sake miƙewa zumbur, a lokacin da idanuwan ta suka hango mata badakaran nan yana tafiya ɗauke da jinjirin ta a hannu da yake ta tsala kuka.
Da sauri Ishaƙ ya miƙe tsaye shima yana mai shirin riƙota, amma tuni ta funcike hannun ta tana mai fara ɗaga ƙafafuwan ta a guje ta nufi hurin da ta hangi mutumin nan.
Da sauri wani badakare ya tare ta ta hanyar tsayawa a gaban ta, tare da babbake wurin da yayi.
Yayin da shi kuma wannan badakaran da yake riƙe da jaririn ya fuce daga cikin jirgin duka yana mai dosar shimfiɗar da Boka mai wutar kasko tare da Sarki Barbaru suke, hakan da Aishatu ta gani ne yasan ta ya ta sake sakin wata irin ƙara mai matuƙar ƙaraji tana mai girgiza kanta, tukun daga bisani ta ɗaga ƙafar ta ɗaya daniyyar ta sake zurawa a guje, amma sai gaba ɗaya ta koma tayi baya luuu, tana mai zubewa a ƙasa sumamma!
A wani irin haukace Ishaƙ yayi kanta yana mai sakin wani irin gunjin kuka mai tsantsar sosa rai da ban tausayi, gumi na yanko masa ta ko ina na jikin sa, tayadda har ya jiƙa sa duka sharkaf yadda kasan wanda ya shiga ruwa.
Acan ɓangaren badakaran nan kuwa yana ƙarasawa kan shimfiɗar ya miƙawa Boka mai hutar kasko jinjirin.
Kallon sa boka mai wutar kasko ya tsaya yi daga tsayen da yake, yana mai yaba kyawun halittar yaron da ya gani aransa, tukun daga bisani ya matsa kusa da kaskon nan dake ci da wuta acikinsa, yana mai ajiye jinjirin da yake tsirara jikin sa ɓace da jini a gaban kaskon, kana yaja baya yana mai komawa ya zuba ido akan sa kamar yadda duka sauran mutanen dake wurin suka zuba nasu idanun.
Yana diresa a wurin kuwa jinjirin ya ƙara tsanyarewa da kuka, yana mai kai hannun sa baki ya fara wawurar sa, tukun daga bisani ya fara hahaura ƙafafuwan sa yana mai cillasu sama cikin kukan da yake, hakan da suka gani ne ya sanya su sake zuba idanuwan su akan sa.
Yayinda shi kuma jinjirin ya cigaba da harba ƙafafuwan sa har suka dako kaskon wutar nan.
Take kuwa a wurin kaskon ya tungule ƙasa yana mai rabewa gida biyu dai-dai.............!!!✍
_KUNA MUGUN SON KARARU TA YADDA HAR IDAN KUKAJI SHIRU BAKWA IYA HAKURI SAI KUN TAMBAYA, AMMA KUMA COMMENT NA KANKANIN LOKACI NA MUGUN YI MUKU WUYA. TO BANA TINANIN ZAKU SAKE GANIN WANI PAGE DIN DAGA WANNAN MUDDIN BANGA COMMENTS DA SHARHI SOSAI BA GASIYA._
*BY*
UMAR FARUQ*D*
*BAƘAR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 16*
Wani irin ihu su Sarki Barbaru suka saki cikin tsantsar farinciki suna masu ɗaga hannuwansu sama, tare da faɗin.
"Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!"
Sabo da yadda suka ga gaba ɗaya kaskon nan ya dare gida biyu, kana wutar cikinsa ta mace tas, kamar yadda boka ya faɗa, yayin da su kuma mutanen dake cikin jirgin nan suka sake fashewa da kuka mai sosa rai, shi ko Ishaƙ banda faman girgiza Aishatu yana kiran sunan ta, bayan ya watsa mata ruwa a fuska babu abun da yake iya yi.
Wani irin kuka yake jikinsa na tsantsar rawa tamkar ƙaramin yaro.
Sarki Barbaru da kansa ya durƙusa a ƙasa, yana mai ɗaukar jaririn dake ta aikin tsala kuka har yanzu a hannun sa, tukun ya buɗe baki cikin muryar sa mai futar da amon sauti, yana mai kallon dakarun sa tare da faɗin. "Ai'ki kuma ya ƙare daga yau, domin ko Ubangiji Gargabilu ya yaye mana wahala, ya aiko mana da mafutar mu, yanzu rayuwar mu zata dawo kyakkyawa ba tare da fargabar komai ba, tamkar yadda muka kasance ada, dan haka ku koremun waƴan nan mutanen, tare da jirgin su gaba ɗaya daga cikin ƙasa ta."
Sarki Barbaru ya faɗa yana mai nuna Jirgin su Aishatu.
Tukun ya juya ɗauke da Ɗan a hannun sa.
Da wata irin gigitattar ƙara Aishatu ta farka da ita tana mai faɗin. "Ɗana! Ɗana!! Ɗana!!! Kuyi haƙuri! Kuyi haƙuri karku kashemun shi, kuyi haƙuri kubani shi ko ɗaukar sa ne nayi, kumun afuwa kubarni inji ɗumin sa yaji ɗumin jiki na shima, kumun gafara ku barni nayi rayuwa da jinjiri na!" Ta faɗa a wani irin haukace tana mai funcike jikin ta daga riƙon da Ishaƙ yayi mata ta sake yin bakin Jirgin aguje tana shirin fucewa, sabo da yadda ta hango Sarki Barbaru ya juya yana tafiya riƙe da jinjirin nata, ga kuma yadda kukan jaririn ke dukan dodon kunnuwan ta.
Da sauri wani Badakare da yake abakin hanyar yasan ya hannun sa yana mai hankaɗata baya ta faɗi ƙasa.
Tukun suka ƙara zare mahaukatan makaman su suna masu saitawa direbobin jirgin hanya, tare da basu umarnin suyi gaggawar yin gaba tun kafin su canza shawara duka suka kashe su suma.
Jin hakan da matuƙan Jirgin nan sukayi kuwa ba ƙaramun sake hatsina musu ƙwaƙwalwa yayi ba, domin kuwa sun tabbatar da babu abun da mutanen nan zasu ce zasuyi sa suka sa yin sa, hakan yasa cikin gaggawa ko wanne ya koma wurin sa, tukun suka sake yin gaba suna masu ɗaukar hanyar su, yayin da suma mutanen Baƙar Masaruta suka ƙara shigewa cikin jirgin su suna masu binsu abaya domin suyi musu rakiya.
Tunda wannan Badakaran ya sake hankaɗa Aishatu ta faɗi a ƙasa, sai Ishaƙ ya sake zuwa ya riƙe ta gam, irin riƙon da bazata taɓa iya ƙwatar kanta ba, domin kuwa ya sani muddin zata cigaba da haka to Ba ƙaramun aikin su bane su kashe ta duka itama.
Sosai take kuka na tashin hankali mai tsanin ban tausayi daga kwancen da take acikin jirgi, banda raɗaɗi da suya babu abun da take jin zuciyar na nayi mata, tayi nadamar zuwan ta Jahar Ruman gaisuwar mahaifin ta tafi sau dubu, taji inama ace tabi maganar mijin nata tayi haƙuri tabar zuwan, tabbas da tasan babu wani abu wanda zai rabata da Ɗan ta a lokacin da ta haife sa.
Sosai take hango kamannin yaron a cikin idanuwan ta, sabo da yarce suka zauna mata a cikin idanuwan nata das, wato kamannin ta kenan sak kamar yacce ta gani akan fuskar jinjirin.
Sai da har suka rakasu ƙofar futa daga cikin Ɓakar Masarauta duka, tukun suka juyo da kan nasu Jirgin hankulan su akwance babu damuwar komai tattare da su, yayin da su kuma mutanen cikin Jirgin su Aishatu suka sake fashewa da wani irin azababben kuka, musamman ma waƴan da aka ƙwacewa Ƴaƴa, suna masu kallon hanyar garin, hanyar da suka raɗa mata suna Bakar Hanya, kamar yacce suka raɗawa wannan rana ta Alhamis suna Baƙar Rana, mai tsantsar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 76