Share this page
zamuyi in biyo ka ko?" Uhm! "To ai yanzu ma bata baci ba idan naje inda zani na tsaya sai ka futo kasamu mota ka juya, domin kuwa kasan ni dai bazan tsaya akan hanya ba, kuma kasan bazan iya zama acikin gidan can ba ana waƴan can kaɗaɗe da bushe -bushen banzan can na gidadanci." "To karka tsaya ɗin mana ɗan iskan banza kawai." Al'amin ya faɗa cikin zafi yana mai buga ƙwafa, yayin da shi kuma yarima Asad yay shiru yana mai mai da hankali akan tuƙin haukar da yake hankali kwance. *ASADULLAH PALACE* Shi ne sunan da aka rubuta daga saman azababben building ɗin daya tunkara da motar tasa wanda get ɗin wurin kaɗai abun kallo ne bama ginin ba. Tun daga nesa ya danna horn ɗaya daga nan kuma bai sake yin wani ba. Da sauri wani matashin saurayi ya wangale tamfatse-tsen get ɗin yana mai kauce wa. A hankali ya fara taka motar yarce kasan ba zai tafi ba yana tunkarar cikin wurin, kai idan har ba sani kayi ba ka gansa akan titi yanzu kuma akace maka shine yake irin wannan tafiyar sai ka rantse da Allah kace ƙarya ne, domin kuwa ko mutum dake tafe aƙafa sai ya hucewa sa sosai a'irin yarce yake taka ta yanzu! *JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE* Da gudu ƴar ƙaramar yarinyar mai kimanin shekaru bakwai aduniya ta afka cikin ɗakin tana ta faman numfar-fashi, alamun ba ƙaramun gudu tayi ba kenan. Durƙushewa tayi akan guiwoyin ta tana ta faman zare ido tare da sakin numfar-fashi. Ahankali kyakkyawar budurwar da take zaune agefen wani azababben gadon ƙarfe mai matuƙar kyau, wasu matasan ƴammata guda biyu da suke sanye da kayan fulani na tufke mata uban gashin da yake ɗauke akan ta mai tsananin yawa, tsayi da baƙi ta ɗago dara-daran fararen idanuwan ta tana mai watsa su akan ƴar yarin yar data shigo aguje. Kallon yarin yar tafarayi tun daga sama har ƙasa ba tare da tace komai ba. Yayin da ita kuma ƴar yarinyar har lokacin take durƙushe aƙasa tana sakin nishi. Ɗaya daga cikin ƴammatan da suke gyarawa budurwar nan gashi ne ta ɗago kai tana kallon yarinyar fuskar ta ɗauke da murmushi, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin harshen fulatanci tana mai faɗin. "Shin me ya faru ne uwar gijiya ta beldo?" Ɗago kai yarinyar tayi tana mai kallon ta, tukun tace. "Ba hulin ki nazo ba." Kana ta mai da idanuwan ta kan fuskar budurwar da ake gyarawa gashi tana mai cewa. "Adda ta gote ki duka sun tashi sun gudu, yanzu naje ansho fulata wani ya kal-kaɗamun jelar sa afuska ta ya tashi sama, kinga kenan gwalo yayi mun ko?" Yarinyar ta faɗa tana mai kallon budurwar bayan tazaro manya manyan idanuwan ta waje, alamun dai abun ba ƙaramun firgita ta yayi ba. Yayin da waƴan nan ƴammatan bayin guda biyu suka tuntsire da dariya suna kallon ta. Ita ko uwar gayyar wacce aka kawowa labarin taɓe baki tayi tana kallon ƴar yarinyar, kana daga bisani ta ɗaga laɓɓan ta cikin zazzaƙar muryar ta mai matuƙar daɗi tana mai faɗin. "To uwar shirme ni wuce ki bani wuri." Ta faɗa tana ɗauke kai daga kan yarinyar, yayin da ita kuma yarin yar ta ɗaure fuska tana mai miƙewa tsaye ranta aɓace ta juya ta tafi, sai da taje bakin ƙofar futa daga ɗakin, tukun ta juyo tana mai kallon yayar tata, sannan daga bisani ta buɗe baki tana cewa. "Bama zan ƙala baki labari na ba, kuma Allah yasha kalsu dawo ma." Ta ƙarashe maganar da murguɗa baki, tukun ta juya tana mai fucewa daga cikin ɗakin. Murmushi dukan su su ukkun sukayi har ita ba tare da sunce komai ba. Sun ɗauki dogon lokaci suna gyaran gashin tukun suka kammala. Gefe guda suka koma suka tsaya kawunan su durƙushe aƙasa, ko wacce hannun ta riƙe da cumb. Gyara zaman ta tayi akan gadon da take, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Kuna iya tafiya sai na sake neman ku kuma." Ta faɗa tana mai miƙewa daga kan gadon. "Tom ranki shi daɗe Allah ya ƙara lafiya." Suka haɗa baki wurin faɗin haka, tukun suka juya suna masu fucewa daga cikin ɗakin. Tafiya tayi zuwa bakin mudubin da yake maƙale ajikin bangon ɗakin, wanda gefe da gefen sa yake ɗauke da ƙarafa masu adon flawoyi kalar ruwan zuma, kamar yacce duka kayan ɗakin suke. Tsaye tayi agaban sa tana mai kallon kanta acikin madubin. Sanye take da kayan fulani irin na sarauta, riga da zani ne farare masu ɗauke da adon ja da koren zare ajikin su, sai ƙafar ta kuma da take sanye da plat farin half cover shoe na fata mai ɗauke da adon gashi ajikin sa mai tsananin kyau, yayin da kanta kuma ya kasan ce abuɗe ba ɗankwali akai, sai uban gashin da aka gama gyarawa da aka rabasa gida biyu, aka kikkitse jelolin suka zubo har kan cikin ta baƙiƙƙirin dasu gwanin ban sha'awa. Farace tas kamar ataɓa ta jini ya ɓullo, tana da tsayi tare da ƴar ƙiba dai dai misali, irin waƴan da ake so mace ta kasan ce dasu, tana da dara daran idanuwa masu ɗauke da blue black ɗin ƙwaya acikin su, sai siririn hancin ta da yake zaune daram akan fuskar ta wanda baza'a kira sa da dogo can ba kuma baza ace nasa ɗan guntu ba, yayin da bakin ta kuma ya kasan ce ɗan tsukut dashi ɗauke da pink lips akan sa suna ta faman ƙyalli. Ba wata kwalliya ce ɗauke afuskar ta ba sai kawai zallar powder data shafa, daga nan kuma bata ƙara komai akai ba sai suturar dake sanye ajikin ta da sukayi matuƙar zama das da su. GIMABIYYA HADDIYAL kenan. Ƴa mace ta farko ga Lamiɗon masarautar fulɗe, gimbiya ƴar gata wacce ake tsananin ji da ita, gimbiyar da take da matuƙar izza da kwarjini irin na ƴaƴan sarauta. Gimbiyar da ta maida tsun-tsaye da shanaye abokan rayuwar ta fiye da komai acikin masarautar tasu, hakan ya sanya har mahaifin ta Lamiɗo ya bata sarautar tsun-tsaye ta duka masarautar. Lumshe idanuwan ta tayi agaban madubin fuskar ta ɗauke da sassanyan murmushi, babu abun da take hange acikin idanuwan ta sai kyakkyawar fuskar sa yana aiko mata da sassanyan murmushin sa kamar yacce take ganin sa aduk lokacin da taso ganin sa muddin ta kulle idanuwa ko kuma ta kwanta bacci. Ta ɗauki tsayin mintina biyar rufe da idanuwan tana sakin murmushi, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai sake duban kanta ajikin madubin, kana ta juya tana mai dosar ƙofar da zata sadata da waje cikin takun ta wanda yake nuni da ita ɗin wata ce basai anfaɗa ba. Wani danƙareren fallow ne mai tsananin kyau, wanda aka ƙawa tasa da kujerun ƙarafa masu ruwan zuma ta ɓulla cikin sa. Gaba ɗaya bangon fallow'n zagaye yake da adon ja da bluen stara masu tsananin kyau, yayin da daga saman starorin kuma aka kafe wasu haɗaɗɗun ƙwarare da luwade harma da faifayen kaba kala kala akan su. Kallo ɗaya mutum zaiwa wurin ko da bai san saba yasan tabbas ya shigo cikin babbar masarautar fulani waƴan da suke ji da Al'adun su, sabo da yarce aka ƙawata ko ina da kayan ado irin na fulani. Kai tsaye ta tunkari inda wata farar dattijuwar mace mai kimanin shekaru hamsin da ƴan kai take, kishingiɗe take akan tabarmar kaba wacce saman ta take ɗauke da lallausar sarrafaffar fata akai, sai wasu tum-tum da suke ajiye agefe da gefen shimfiɗar, yayin da ita kuma matar take kishingiɗe akan tum-tum ɗin ta miƙe ƙafafuwan ta duka akan kafet ɗin. sanye take da kayan fulani farare kar da su, sai al'kyabba wacce itama take ta mahaɗin kayan fara mai adon baƙi sanye ajikin ta. Kallo ɗaya zaka yiwa matar ka gane itace ta haifi Gimbiya Haddiyal, sabo da tsananin kamar da suke yi, riƙe take da wani haɗaɗɗen kofin silba ahannun ta, wanda cikin sa ya kasan ce cike danƙam da madarar shanu mai matuƙar dumi tana sha. Sai daga can wuraren ƙafafuwan ta kuma wata dattijiwar mata ce mai kimanin shekaru kusan hamsin da biyar aduniya take riƙe da ƙafafuwan ta tana ta aikin mammatsa su. Tunda ta hango tawowar ƴarta ta take ta faman sakin murmushi tana kallon fuskar ta har ta ƙaraso wurin da suke. Cire takalman dake sanye aƙafafuwan ta tayi, tukun ta hau kan kafet ɗin tana mai zama ta tanƙwashe ƙafafuwan ta akai. Dasauri wannan dattijuwar matar dake aikin lallatsa ƙafafuwa ta buɗe baki har tana ɗan ranƙwafa jiki wurin faɗin. "Barka da futowa ranki ya daɗe." "Yawwa barkan ki dai Iya." Gimbiya Haddiyal ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi, tukun ta juya ɓarin da mahaifiyar tata take tana mai buɗe baki cikin sanyi, bayan ta durƙusar da kanta ƙasa tace. "Barka da hutawa dadde na." Janye kofin madarar da takai baki tayi bayan ta ɗan kurɓe ta, tukun ta miƙawa dattijuwar matar nan da take zaune tana matsa mata ƙafafuwa shi. Dasauri matar ta karɓa tana mai ajiye kofin agefe bayan ta rufe sa da murfin sa. Lumshe idanuwan ta tayi, kana ta buɗe su akan fuskar ƴar tata, tukun daga bisani ta buɗe baki fuskar ta ɗauke da murmushi tana mai faɗin. "Yawwa Bello (kyakkyawa) ta." Tukun daga bisani ta ɗora da cewar. "Me ɗazu Innahuro ta tamiki da kika mata rashin mutunci, tazo tashe mun bazata ƙara kula ki ba ta dena baki labari daga yau babu ruwan ta dake." Mahaifiyar tata ta faɗa har lokacin tana kallon fuskar ta. Zaro idanuwa Gimbiya Haddiyal tayi tana sakin murmushi, tukun daga bisani tace. "Wai haka tashe miki kenan, barni da ita Dadde na ita da kanta zata zo har inda nake da anjima." Ta faɗa tana mai miƙewa tsaye. "To yanzu kuma sai ina?" Mahaifiyar tata ta faɗa tana kallon ta. Zan zaga bayan nan ne."Cewar Gimbiya Haddiyal" tana mai sanya takalman ta aƙafa. "To adawo lafiya." Mahaifiyar tata da dattijuwar matar nan suka haɗa baki wurin faɗin haka. Juyawa Gimbiya Haddiyal tayi tana mai kama hanyar waje. Tsaye tai daga bakin ƙofa bayan ta futa tana mai kallon ɗirka ɗirkan shanun da ake shigewa dasu ta gaban ta. Gaba ɗaya ginunuwa ne irin na fulani masarautar gare ta, ko ina ka kalla share yake ƙal babu alamun datti ko kaɗan. Sai da har tagama kallon shigewar shanayen nan tukun ta sauka daga kan daɓen part ɗin nasu tana mai kama wata hanya ta miƙe ta samɓel tana tafiya. Tafe take tana lumshe idanuwan ta tare da sakin murmushi akai akai, sabo da yarce take ganin fuskar sa aduk lokacin data lumshe idon, ga kuma yarce take jin daɗin yana yin garin nayau da ya kasan ce babu rana ko kaɗan, sai wata irin sassanyar iska dake kaɗawa tana dukan jikin ta, tayar ce har jelar gashin dake kitse kwance akan cikin ta suke juyawa. Sai da tayi tafiya mai nisa daga cikin gidan sarautar tasu, tukun ta ɓulla cikin wani tafke-ken wuri wanda yake ɗauke da bishiyu kala-kala acikin sa, sosai wurin yake da tsananin kyau, sabo da yarce aka ƙawata sa da itatuwa iri daban daban akuma jere atsare, ga wata irin sassanyar iska da take kaɗawa mai matuƙar ƙamshin ganyaye tana dukan fuskar ta. Wuri ne mai matuƙar girma, domin kuwa aƙalla idan akace mutun ya zagaye sa ataiƙace zaiyi tafiyar kusan awa biyar aƙafa kafun yaje ko ina na ciki. Banda sautin kukan tsuntsaye iri iri babu abun da akeji yana tashi awurin. Kai tsaye ta doshi wani wuri da yake daga can gaba wanda aka zagaye sa da iccina, mai ɗauke da haɗaɗɗun bishiyu acikin sa. Lumshe idanuwan ta tayi abakin wurin tana mai sakin murmushi, badan komai ba sai dan kawai sautin kukan abubuwan data fiso da taji yana dukan kunnuwan ta. Ahankali ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana dosar cikin wurin bayan ta buɗe idanuwan ta, har kuma lokacin bata fasa sakin murmushi ba. "Shale am!" (tsun-tsaye na). Ta faɗa cikin zazzaƙar muryar ta da matuƙar ƙarfi. Aiko ko minti ɗaya batayi ba da rufe baki sai ga dan-dazon tsun-tsaye nan da matuƙar gudu sunyo wurin da take ko wanne na kalar kukan sa. Tsaye sukai asaitin ta wasu daga bayan ta wasu kusa da fuskar ta, yayin da wasu kuma suke daga saman kanta kowanne da kalar kukan da yake, suna yi suna kar-kaɗa jela da fuka fukai, alamun suna farin ciki da zuwan nata kenan. Lumshe idanuwan ta tayi cikin tsantsar shauƙin da take ji, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai sakin murmushi, kana ta ɗaga laɓɓan ta cikin yin ƙasa -ƙasa da murya tana mai faɗin. "Kun san me, yau akwai babban labari da zan baku, labari ne mai daɗi wanda yafi duk na baya daɗi akan Giɗaɗo am." Ta ƙarashe maganar cikin murmushi tana mai girgizawa tsun-tsayen nan kai, take awurin ko suma suka ƙara sautin kukan su suna masu cigaba da karkaɗa jelina da sauri da sauri alamun farin ciki kenan. Tukun ta juya tayi gaba suma duka suka biyo ta abaya da matuƙar yawan su, sannan kuma kaloli daban- daban. Bata tsaya ba har sai da taje wani haɗaɗɗen wuri wanda yake ɗauke da ruwa mai matuƙar girma acikin sa, tukun taja ta tsaya agaban wata shimfiɗar fata mai ɗauke da tum-tum da take agaban ruwan, yayin da cikin ruwan kuma ya kasan ce ɗauke da agwagi kala kala suna ta faman iyo aciki. Suna ganin zuwan ta suma gaba ɗayan su sukayo bakin ruwan da gudu suna ta faman yin kuka tare da luma kawunan su acikin ruwa, wanda hakan ke nuni dasu ɗin ma farin ciki suke kenan. Tukun daga ƙarshe kuma sai ga dan-dazon kaji masu tsantsar kyau gaba ɗayan su jikin lukui-lukui dasu sunyo inda take suma suna nasu kukan. Cire takalman ta tayi tana mai hawa kan shimfiɗar nan ta kishingiɗa akan tum-tum. Dasauri tsun-tsaye nan suka mar-matso saitin shimfiɗar suna masu maƙal ƙalewa ajikin itatuwan bishiyun da suka yiwa ruwan da shimfidar rumfa gaba ɗayan su, sai ɗawisu kuma guda ɗaya babbar cikin su da ita kuma ta haye kan tum-tum ɗaya wanda yake kusa da wanda Gimbiya Haddiyal ta kishingiɗa tana mai ƙure ta da idanun ta. Yayin da su kuma agwagi nan suka jajjeru acikin ruwan daga bakin sa, suma cikin su akwai wata fara da tafi duk sauran kyau da take agaban su, sai kuma sauran duka suka hau layi abayan ta. Sai daga gefen shimfiɗun kuma kaji ne jera reras mazan su da matan su duk sun duddurƙusa suna kallon ta, suma acikin su akwai wacce take agaba fara, sai sauran abayan ta ajere. Wato dai waƴan nan na gaban sune shuwagabbanin da Gimbiya Hadiyyal ta naɗa acikin iyalan nata, kuma ako da yaushe hakan suke idan har zasu gana da ita. Lumshe idanuwan ta tayi bayan ta ɗaga kai sama tana mai sakin murmushi, yayin da su kuma tsuntsayen nan duka sukayi shiru tsit suna kallon ta, tukun daga bisani ta sauke kan nata ƙasa tana mai wara idanuwan ta akan tsun-tsaye nan, kana ta buɗe baki cikin zazzaƙar muryar ta, har kuma lokacin tana sakin murmushi tana mai faɗin. _"Babban wuri ne mai tsananin girma da kyawu, zagaye yake da korayen furanni masu matuƙar ƙamshi da ƙyalli, yayin da jinsin kyawawan tsun-tsaye suka kasan ce kewaye da wurin mazan su da matan su ko wanne yana harkokin sa, sai sassanyan ruwa fari kar dashi yana kwaranya acikin rami. Zaune yake acikin ruwan yana ta faman ɗaga sa sama da hannun sa, sannan sai ya watsa sa ajikin sa, yayin da ni kuma na kasan ce zaune agefen ruwan ina shan madara idanuwa na akan sa, ban an'kara ba banyi tsammani ba sai jinai an watso mun ruwa akan fuska, ina ɗago kai dan naga ko waye sai nayi ido huɗu da shi agabana yana sakar mun murmushin sa mai tsananin kyau, murmushin nima nayi masa ina mai ɗaukar yatsa ta na dunguri dogon hancin sa da shi, kana daga baya na buɗe baki ina mai cewa. Ina sanka Giɗaɗo na._ _Murmushi shima yayi mun, tukun ya sake komawa cikin ruwan yana mai yin nitso ya cigaba da wankan sa ba tare da ya bani amsa ba, daga nan kuma sai na tashi daga bacci na."_ Ta ƙarashe maganar idanuwan ta akan tsun-tsaye, kaji da agwagin nan, yayin da su kuma gaba ɗayan su suka fara sakin kuka suna masu jujjuya jiki alamun suna taya uwar ɗakin nasu farin ciki kenan. "Tom kunji inda labari na na yau ya tsaya, sai kuma gobe idan na dawo zan baku sabon da zanyi yau, dan haka kowa yana iya komawa wurin sa masoya na." Ta faɗa tana mai miƙewa tsaye daga kan shimfiɗar. Sosai tsun-tsaye suka rikice da ihu suna ta faman shawagi akan ta, wasu har suna dan gwalar ta da jelar su, tukun sai suyi gaba, suma kaji juyawa sukai agurguje suna masu komawa wurin da suke, yayin da agwagi ma suka sake yin nutso cikin ruwa suna cigaba da harkokin su. Zura ƙafafuwan ta tayi cikin tattausan takalmin fatar ta, tukun ta juya tana mai sake ɗaukar wata hanyar duk acikin wurin. Tayi tafiya mai nisa, kana ta isa bakin wani farin ruwa da yake wucewa ƙal-ƙal da shi, yayin da gefe da gefen ruwan kuma wasu irin korayen ciyayi suka masa ƙawanya yayi gwanin ban sha'awa. Zama tayi agefen ruwan kan ciyayin tana mai cire takalman dake sanye aƙafar ta, tukun ta zura ƙafafuwan nata cikin ruwan tana mai kar-kaɗa su tare da lumshe idanuwa, kana ta ɗaga laɓɓan cikin sanyi tana mai faɗin. "Shin sai yaushe ne zaka bayyana gare ni, sai yaushe ne zan ganka azahiri kaima ka ganni, nayi iyakar yina akan ka amma na kasa, sai dai ina so kasani muddin rai da numfashi suna tattare agangar jikin Gimbiya Haddiya, to soyayyar kama tana nan daram, haka kuma muddin zuciya na cigaba da bugu aƙirjin Haddiyal, to kasani koda yaushe ƙaunar ka na sake sambun ta ne. Kamatso gare ni ya kai masoyi na, ka tawo gare ni yakai abun ƙauna ta, shin sai yaushe ne zan ganka ka ganni Giɗaɗo na? Ban sanka ba, ban taɓa ganin ka azahiri ba, amma na kamu da ƙaunar ka azuciya ta. Shin kai ɗin ma kasan da zama na ko ko ni kaɗai ce nake hauka akan ka? To kasani koda baka san dani ba babu wata mace da ta isa ta kasance agefen ka bayan ni! Har yau ba ahallici wacce zata soka ba bayan ni! Mutane na cewa kai ɗin ba mutum bane, amma ni na daɗe da sanin kai ɗin mutum ne kuma na daban acikin mutanen ma, ina son kaso ni kamar yacce na soka Giɗaɗo na, jiki na na bani zan ganka na kusa na sadu da kai nan kusa ba da daɗe wa ba." Ta ƙarashe maganar ƙwalla na tsiyayowa ta gefen idanuwan ta, tukun daga bisani ta wara idanuwan ta tana mai sakin murmushi, kana ta zare ƙafafuwan ta acikin ruwan tana mai miƙewa tsaye. Takalmanta ta sanya aƙafa, sannan ta sake yin wurin wasu korayen ganye har lokacin fuskar ta ɗauke da murmushi. Tsaye tai agaban su tana mai sanya hannu ta fara bubbuga ganyayyakin. Take kuwa Malam buɗa mana littafi (buterfly) suka mimmiƙe daga kan ganyayyakin masu tsananin kyau kala kala suna hawa kan jikin ta. Dariya ta kwashe da ita tayarce har sai da sautin ta ya ɗan futo, tukun ta buɗe tafin hannuwan ta duka biyun, yayin da su kuma birbillo nan (malam buda mana littafi) suka hau kan tafin hannuwan nata suna ta jujjuyawa. Zagaye ta farayi awurin tana hajijiya tare da sakin dariya mai sauti, tukun daga bisani ta tsaida dariyar tana mai faɗin. "Kuyi haƙuri masoya na, ban so nayi muku kishiya ba, sai dai kuma nima ban san lokacin da soyayyar sa ta hudan zuciya ba, abu ɗaya kawai dana sani shine amafarki nasan sa, kuma amafarki nake gannin sa, amma sai da ina mugun kaunar sa, dan haka kuma ina san kuso sa masoya na, na muku al'ƙawarin kune na biyu acikin zuciyar Gimbiya Haddiyal daga ku babu ƙari." Ta faɗa tana mai cigaba da shawagi da dariya ahaka har ta koma bakin ruwan nan data taso. *ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFUZ, CIKIN BAƘAR MASARAUTA* Cikin tsantsar fushi da tafasar rai ta ƙarasa bakin ƙofar dake sada mutum da cikin gidan nasu. Tsaye tayi ƙam abakin wurin, yayin da su kuma waƴan nan ƴammatan bayin da dakarun sukayi saurin zube guiwoyin su aƙasa. Miƙar da hannun ta tayi gefe ba tare da tace komai ba, yayin da idanuwan ta kuma da ɓacin rai ya mayar dasu ja suka kasan ce kafe akan ƙofar dake kallon su. Dasauri wannan badakaran ya tawo da baya da baya har ya ƙaraso inda take, tukun ya zube gwuiwoyin sa aƙasa yana mai durƙusar da kai ƙasa, kana ya sanya hannu ya zaro takobin nan tata yana mai ɗora mata ita akan tafin hannu. Damƙeta tayi da ƙarfi fiye da irin riƙon da take mata abaya, yayin da shi kuma wannan badakaran yayi saurin miƙewa yana mai juya baya ya koma inda yake ya tsaya. Cikin tsantsar izza ta fara ɗaga ƙafafuwan ta da suke futar da sautin gwalagwalai tana mai dosar ƙofar dake kallon ta. Cak ta tsaya adai dai lokacin data ɓulla cikin tafkeken falon da yake zagaye da kayan alatu tare da Tambarin masarautar tasu tako ina acikin sa, sabo da abun da idanuwan ta suka gane mata daga shigar tata. Sosai kanta ya kulle, mamaki da tinanin abun da ya kawo sa cikin falon su awannan lokacin yayi matuƙar ɗaure mata kai, tayarce har ta kasa buɗar baki tayi magana kamar yacce ta kasa ɗaga ƙafa tai gaba. Cikin tsantsar fushin da bata taɓa ganin sa acikin sa ba tun lokacin da tazo duniya tagan sa adai dai lokacin da ya juyo ɓarin da take yana mai watsa jajayen idanuwan sa cikin nata! Wata irin faɗuwar gaba ta samu kanta aciki, sabo da tunda take bata taɓa ganin idanuwan sa sun sauya haka ba, yayin da shi kuma ya fara tinkaro inda take cikin takun sa wanda yake nuni dashi ɗin ko waye fuskar sa amatuƙar ɗaure. Rawa jikin ta ya kamayi sabo da yarce taga ya nufo ta gadan gadan, abun da tunda take bata taɓa tsintsar kanta aciki ba, wato tsoron da ya ziyarci zuciyar ta yanzu! Cak ya tsaya agaban ta yana mai ɗan ranƙwafowa ya rage tsayin sa fuskar sa ta kasan ce dai dai tata fuskar, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. "Sh.............✍ 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 03* "Shin ashe dama har akwai lokacin da zaizo wanda ƴa zata yaƙi ubanta! Wato ke yanzu har kinyi girman da zaki iya ja dani, sannan ki rushe mun ginin da na ɗauki tsawon shekara da shekaru ina yin sa! Shin kin san kalar hanyar dana bi kuwa kafun na samu wannan mafutar da ke kike shirin wargazata yanzu?" Ya faɗa cikin ƙaraji jajajyen idanuwan sa duk sunyo waje yana mai kafe ta da su. Yayin da ita kuma jikin ta ya ɗauki wata irin kakkarwa, hankalin ta idan yay dubu sai da duka ya tashi, domin ko ko kaɗan bata fahimci inda maganar mahaifin nata ta dosa ba balle har ta gano kalar laifin data aikata masa. Sake gyara tsayuwa yayi agaban ta yana mai sake fuskantar ta fuskar nan tasa babu alamun rahama tattare da ta, tukun daga bisani ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Labarin dogo ne, tarihin murɗaɗɗe ne, al'amarin kuma mai girma ne, sannan kuma rikitacce ne wanda yafi ƙarfin iko na! Tsahon shekara talatin kenan da Ubangiji mai girma Gargabilu ya samar mun da mafuta, amma sai gashi rana tsaka ƴata ta ciki na tana shirin rushe duk mafutar da aka samar tun kafun wanzuwar cikin ta

Chapter 3 of 76