wasu ƴaƴan har guda ukku, amma su kuma duk mata ne. Bilkisu, Maimuna sai kuma ƙaramar su Ruƙayya. Dukan su suna da tazarar shekara bibbiyu har da rabi-rabi ne tsakanin junan su.
Afannin iyayen Aishatu kuwa tunda suka koma Kasar Malin yankin Jahar Ruman basu kara canza wuri ba, kasancewar nan ɗin sun same sa da tsantsar ni'ima ga kuma wadatar abincin dabbobi acikin sa, sannan kuma mutanen garin mafi akasarin su Musulamai ne masu san ƴan uwan su musulmai, ba kamar yankin Jahar Karfuz ba.
Sau ukku Aishatu da Ishak suna zuwa garin abayan komawar su, domin kuwa zuwa na ƙarshe ma har da ɗan su mu'allim da yake da shekara bakwai da rabi yanzu suka je.
JAHAR KAGUL, MASARAUTAR FULƊE.
Lamiɗo Sulaiman mahaifin Gimbiya Haddiyal shine sarki na goma acikin Masarautar Fulɗe, yana da mata biyu tare da Ƴaƴa biyar.
Matar sa ta farko itace Gimbiya Kaɓel, tana da ƴaƴa ukku, na farko shine Ummaru wanda sukewa laƙabi da Jauron Fulɗe, daga nan kuma bayan shi da shekara huɗu ta sake haifo wani ɗan namiji yaci suna Halilu, amma suna kiran sa da Bammi, bayan shi kuma sai Abubakar wanda suke kira da Buba.
Yayin da ita kuma matar sa ta biyu take da suna Gimbiya Maraimu, ita kuma tana da ƴaƴa biyu ne duk maza suma, Habibu shine ɗan ta na fari wanda suke sa'nni da Jauro Ummaru, bayan shi kuma ta sake haihuwar wani yaron mai suna Harisu wanda suke sa'anni da Buba, domin kuwa duka tsiran su baifi tazarar wata ukku ba.
Sosai Lamiɗo yake matuƙar son samun ƴa mace, hakama kuma afannin matan nasa da ƴaƴan sa suma duk suna son sugan su da yarin ƴa mace, amma sai dai Allah bai basu ba duka yaran maza ne.
Ita dai Masarautar Fulɗe ta kasance masarauta ce wacce ko kaɗan mutanne cikin ta basu da ilimin addini, duk da suna ikirarin su ɗin musulmai ne ako da yaushe, sai dai kuma ko kaɗan basa amfani da faɗar Allah, ataƙaice ma ko tauhidi basu sani ba, dan kuwa sun mayar da tsafi ba komai ba awurin su, domin kuwa babu wani Ɗa dake tasowa acikin gidan sarautar harya girma ba tare da ya iya tsafi kala-kala ba, a cewar su wannan itace kaɗai hanya wacce zasu iya kare kansu daga kowanne irin mugun mutum cikin sauƙi.
Basu damu da sai sunyi karatun boko ba, domin kuwa ada kwata-kwata ma basu yarda da ita bokon ba, sai daga baya ne abayan haihuwar Buba da Harisu aka samu wasu turawa tare da haɗin goyon bayan gwamnati sukazo har cikin Masarautar suka ƙarayi musu bayani akan boko tare da muhimmancin sa, kuma Alhamdulillahi alokacin sunyi sa'a, Lamiɗo ya aminta da zancen su duk da kasancewar sa mutum mai kafiya da tsayawa akan magana ɗaya.
Hakan yasa koda Habu da Harisu sukai wayo aka ɗauke su aka kaisu wata makarantar kwana, wacce ake biyan maƙudan kuɗaɗe suka fara tun daga farko anan.
SHEKARA TALATIN BAYA.
1991..........✍
*SHARHI DA TURAWA NAKE BUƘATA DAGA GAREKU FANS, HAKAN SHI ZAI BANI ƘWARIN GWIWAR CIGABA DA RUBUTO MUKU.*
*BAƘAR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 12*
*1991*
ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.
Gudu suke tun ƙarfin su yadda kasan waƴan da sukai gamo da mutuwa, banda faman sakin haki babu abun da suke yi, ga kuma wani irin gumi dake yanko musu ta kowace ƙafar gashi dake jikin su.
Ƴammata ne guda biyu da suke ɗaure da wani ɗan guntun baƙin ƙyalle tare da ƴar ƙaramar riga ajikin su, wato dai sanye suke da shigar su irin ta bayi ajikin su.
Gudu suke sosai tun ƙarfin su suna yi suna kallon sama, ahaka har suka ƙarasa cikin Masarautar tasu, amma duk da haka basu dakata da gudun da suke ba sai da har suka sada kansu da cikin fada.
Da matuƙar sauri fadawan Sarki Barbaru da yake zaune akan wata arniyar kujera, sanye da wasu irin manyan kaya ajikin sa suka miƙe tsaye suna masu dakawa ƴammatan nan da suka faɗo cikin fadar arikice wata irin gigitattar tsawa.
Amma sai dai ko inda suke Ƴammatan nan basu kalla ba sai da har suka dan gana kansu da gaban kujerar da sarki Barbaru yake zaune akai, tukun suka durƙushe aƙasa suna masu sakin haki da tari.
Dasauri Fadawan nan suka sake yowa kansu gadan-gadan cikin tsantsar ɓacin rai, amma sai dai tun kafin su ƙaraso wurin kowanne daga cikin su ya ƙame awurin da yake cak, sabo da yarce Sarki Barbaru ya ɗaga musu hannu sama ba tare da yace ƙala ba, yayin da idanuwan sa kuma suka kasance ƙur akan Ƴamnatan bayin nan, yana mai mamakin abun da ya kawo su cikin fadar sa a irin wannan yanayin.
Tafukan hannun su suka sanya suna masu dafe ƙirjin su da shi, tukun daga bisani suka sake sunkuyar da kansu ƙasa idanuwan su akan shimfiɗar kafet ɗin da take awurin, kana suka buɗe baki cikin muryar su wacce take ɗauke da tsantsar tashin hankali suna masu faɗin. "Tuba muke ranka ya daɗe, tuba muke da labarin da bakin mu zai furta, domin kuwa mu kan mu mun san bamai daɗin ji bane." Suka faɗa jikin su na tsantsar rawa.
Yayin da wani bafade da yake tsaye agefe ya buga musu wata gigitacciyar tsawa yana mai faɗin. "Ku ƙaz....."
Tsit yay da bakin sa ba tare da ya ƙarasa furucin nasa ba, sabo da yarce Sarki Barbaru ya sake dakatar da shi ta hanyar hannun da ya sake ɗaga masa.
Komawa bafadan yayi zuwa wurin da yake yana mai tsayawa, yayin da su kuma waƴan nan Ƴammatan suka sake buɗe bakin cikin rawar murya suna masu faɗin. Haƙiƙa labarin ba zaiwa kunnuwa daɗin saurara ba, kamar yacce bai mana kyan gani a idanuwan mu muma ba, hakan yasa muke neman gafara gareka ya shugaban mu, domin kuwa ayau ɗin, akuma yanzu munyi mummunan gani ne, irin wanda bamu taɓa yin sa ba!" Suka ƙarasa maganar da sakin haki kansu durƙushe aƙasa, tukun daga bisani suka ɗora da faɗin.
"Munga sama ta juye daga fari zuwa wasu kalolin, giza-gizai na juyewa daga kalar su ta farare suna komawa zuwa jajaye da baƙaƙe, gari nayin duhu tayarce har ba'a iya hangen abun da ke agaba, yayin da ruw...." "Kaiiiii!" Sarki Barbaru ya faɗa da matuƙar ƙaraji yana mai miƙewa tsaye daga kan kujerar da yake cikin tsantsar firgici da ruɗu, yayin da su kuma jikin Ƴammatan Bayin nan ya ɗauki wata mahaukaciyar kyarma, tukun daga bisani ya fara ɗaga laɓɓan sa yana mai faɗin. "Shin me hakan ke nufi kenan? Wane irin mummunan laifin aka aikata da har Ubangiji Gargabilu yake shirin yi mana hukunci ta hanyar juyar da mu?" Ya faɗa da wani irin ƙarfi idanuwan sa duk sun futo waje, tukun daga bisani ya sake buɗe baki cikin ƙaraji yana mai faɗin. "Daƙiƙa ukku kacal na baku, kar ku kus-kura ku bari takai huɗu ba tare da kun samo mun tabbacin labarin nan ba." Ya ƙarasa naganar yana mai watsa idanuwan sa akan fadawan sa da suke tsaye cirko-cirko suma duk arikece, tukun ya sake juyawa ɓarin da Ƴammatan nan suke yana mai faɗin. "Ku sani muddin labarin ya suya daga yarce kunnuwa na suka jiyo sa daga bakunan ku, to awannnan karan ni da hannu na zan luma takobi acikin cikkunan ku!" Ya faɗa cikin ƙaraji, tukun ya juya cikin tsantsar sauri yana mai fucewa daga cikin fadar duka, ya ɗauki hanyar da zata sadasa da wurin Boka mai hutar kasko, domin yaji ko yana da masaniya akan zancen, sabo da shi dai tunda yazo duniya bai taɓa jin wani labari makamancin wannan ba.
Yayin da su kuma Ƴammatan Bayin nan hankulan su ya sake bala'in tashi.
Da matuƙar ƙarfi suka ruƙun-ƙume junan su kamar zasu shige cikin jikin su, suna masu fashewa da wani irin gigitaccen kuka!
ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTA WASAI.
Tun bayan haihuwar Nafisat Gimbiya Fulani bata sake haihuwa ba, sai yanzu da take ɗauke da tsohon ciki mai kimanin watanni takwas har da sati Biyu ajikin ta.
Sosai hankalin magautan ta ya sake matuƙar tashi, fargaba da tsoron karta sake haihuwar Ɗa namiji suka cika zuciya da ruhin su, domin kuwa yanzu hakama kullum ƙoƙarin su shine suga bayan Babban yaya, sai dai kuma har kawo yau da yake da kimanin shekara Goma cif aduniya Allah bai basu nasara ba, wanda hakan kuma ba ƙaramu firgita su yayi ba, domin kuwa babu kalar asirin da basuyi masa ba, amma duk abanza bayaci, danko ataƙaice ma sai kyau da farin jini tare da tsantsar hankali yaron yake ƙarawa awurin jama'a.
Tun daga lokacin da cikin jikin Gimbiya Fulani ya bayyana gaba ɗaya hankulan magautan su ya sake tashi, domin kuwa ko kaɗan babu wanda yasan da cikin sai dai kawai lokaci ɗaya suka wayi gari suka gansa ya futo, hakan yasa suka sake bazawa wuraren Bokayen su, domin ganin sun lalata cikin tun kan yazo duniya, sabo da atsoron su kar suje namiji ne ba mace ba, sai dai kuma duk abun da sukayi abanza, ko kaɗan baici ba, domin kuwa gashi nan zuwa yanzu har an fara tsumayen ranar haihuwa.
UNGUGUWAR ƊAN TANKI.
Zaune Aishatu take akan kujera gaban murhu ɗauke da ƙaton ciki jikin ta tana tuƙin tuhu.
Yayin da daga can gefe kuma mu'allim da kakar sa mahaifiyar Ishak suke zaune akan tabarma suna hira tana yanke masa farce.
Ayanzu haka yana da shekara goma ne cif aduniya, yayin da ƙannen sa mata suma duka sukai girma tare da wayo sosai sosai, sai dai kuma tun daga kan ƴar ƙaramar su Ruƙayya, Aishatu bata sake haihuwa ba, sai yanzu da take ɗauke da ciki mai kimanin watanni takwas ajikin ta.
"Anya kuwa lafiya kike Aishatu, domin kuwa gaba ɗaya tun daga jiya nake lura dake duk kin canza, shin ko dai haihuwar ce ta tawo ne?"
Kaka ta faɗa tana mai janye ƙafar Ahmad da take akan cinyar ta tana yanke masa farce daga jikin ta, tare da kai idanuwan ta kan Aishatu da take tuƙin tuwon amatuƙar sanyaye.
Murmushi Aishatu tayi tana mai cigaba da tuƙin tuwon ta, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Wata irin haihuwa kuma Baba, cikin da dukan sa yanzu ya shiga wata na takwas ma, kawai dai gaba ɗaya jikina ne nake jin sa ba daɗi tun jiya, ga kuma zuciya ta da take ta yawan tsinkewa." Ta ƙarasa maganar cikin sanyi sosai.
"To ai dama jin daɗin jiki ga mata irin ku sai ahankali, tun...." "Assalamu alaikum." Suka jiyo sautin sallamar Ishaƙ wacce ta sanya gaban Aishatu wata irin muguwar faɗuwa, tayarce har sai da ta rumtse ido, yayin da ita kuma kaka tayi shiru da abun da take faɗe ba tare da takai ƙarshe ba.
"Wa'alaikum Salam." Suka faɗa atare cikin sanyi, suna masu binsa da idanuwa, sabo da yarce suka gansa ya shigo ba'a irin yana yin da ya saba shigo musu ba.
Yayin da shi kuma Ahmad ya miƙe da sauri yana mai ƙarawa kusa da shi ya riƙe yatsun hannun sa, tare da faɗin. "Sannu da zuwa Abba na."
Damƙe tafin hannun Yaron Ishak yayi ba tare da ya amsa masa ba kamar yacce ya saba, sai jansa da ya cigaba dayi har zuwa kan tabarmar da Kaka take azaune da yayi.
Cire takalman sa yayi agefen tabarmar, tukun ya hau kai ya zauna yana mai lumshe idanuwan sa ba tare da yace komai ba, yayin da Aishatu kuma da kaka suka juyo ɓarin da yake suna masu zuba masa ido, gaba ɗayan su sun kasa yi masa koda sannu da zuwa, sabo da yarce sukaji wata irin fargaba ta lulluɓe su, sabo da ganin sa da sukayi ahaka.
Sai da ya ɗauki kimanin mintina biyu rufe da idanuwan nasa, tukun daga bisani ya buɗe su yana mai juyawa ɓarin da Kaka take ya kalle ta, sannan daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ina yini Umma ta."
"Shin meke faruwa ne ɗan nan?" Kaka ta faɗa ba tare data amsa masa gaisuwar da yake mata ba.
Lumshe idanuwan sa ya sakeyi ahankali, tukun daga bisani ya buɗe su yana mai kaisu ɓarin da Aishatu take zaune, kana ya buɗe baki cikin sanyi ba tare da ya bari ya kalli idanuwan ta ba yana mai faɗin. "Tawo baro gaban murhun nan, ga huri kizo nan ki zauna Maman Ahmad." Ya ƙarasa maganar cikin sanyi yana mai ɗaga ido ya kalle ta.
Wani sanyi taji jikin ta duka ya mata lokaci ɗaya, yayin da ƙafafuwan ta kuma da suke akan kujera taji sun fara mata karkarawa, tayarce har ta kasa tashi daga kai duk da ƙoƙarin yin hakan da take yi.
Ganin hakan da Ishaƙ yayi ne ya sanya sa miƙewa tsaye cikin sanyi, yana mai yin wurin da take.
Ahankali ya miƙa hannuwan sa yana mai riƙo tafukan hannayen ta duka biyu da su, tukun daga bisani ya ɗagota yana mai miƙar da ita tsaye, sannan ya saki hannun ta ɗaya yana mai riƙe ɗaya sukayi gaba.
Zama yayi akan tabarmar dai dai wurin da ya tashi, yayin da ita kuma Aishatu ta zauna daga gaban sa kusa da Kaka, ya zamto suna facing ɗin junan su da shi.
Sake miƙa hannuwan sa yayi ya riƙo nata da su, tukun daga bisani ya buɗe baki cin sanyi idanuwan sa akan ta yana mai faɗin. "Shin wane ke bayarwa Aishatu?" Ya jefo mata tambaya yana mai kallon ta.
Yayin da ita kuma ta lumshe idanuwan ta tana mai jin zuciyar ta na wata irin tsinkewa, tukun daga bisani ta wara su akan fuskar sa ahankali tana mai faɗin. "Allah mana." Ta faɗa ƙasa-ƙasa jikin ta na ƙara mutuwa.
Yayin da shi kuma Ishaƙ ya girgiza kansa alamar na'am, tukun daga bisani ya ɗora da faɗin. "Nasan dukan mu nan mun san mutuwa gaskiya ce, sannan kuma ko wane rai da yake cikin duniya sai ya ɗan ɗane ta, walau yaro, walau babba, tosho da tsohuwa, haka kuma babu wanda yasan lokacin da tasa zata riske sa, da...." "Haƙiƙa ni ɗin musulmace, wacce ta yadda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, dan haka kawai faɗamun kai tsaye, insha Allah zan jure suraron koma mene ne, sannan kuma zan rungumi ƙaddara ta da hannu bibbiyu." Ta katse sa daga maganar da yake da faɗin haka jikin ta na tsantsar rawa, dan kuwa ji tai gaba ɗaya bazata iya jiran sa ba har zuwa lokacin da zai gama bayanin sa.
Lumshe idanuwna sa ya sake yi yana mai ƙara damƙar tafin hannun ta, tukun daga bisani ya buɗe su, sannan yayi gayaran murya, kana ya buɗe baki yana mai faɗin. "Allah yayiwa Baffah Rasuwa a shekaran jiya da daddare!" Ya faɗa yana mai yin shiru ba tare da yace komai ba, sai idanuwa kawai da ya bita da su yana mai kallon ta, kamar yacce itama take kallon sa idanuwan ta duka awaje, ba tare da tace masa komai ba, domin kuwa gaba ɗaya ma jitai duka natsuwar ta da komai nata sun ɗauke, ga wani irin dum da taji kunnuwan ta da kanta sun mata, ɗan cikin ta kuma na juyawa.
Yayin da Kaka kuma ta buɗe baki tana mai faɗin. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un. La'ilah Haillalahu Muhammadu Rasulullahi Sallalawu Alaihi Wassallam." Tukun daga bisani kuma wasu irin hawaye suka ɓalle daga cikin idanuwan ta da matuƙar gudu, kana ta sake buɗe baki cikin kuka tana mai faɗin. "Shin a'ina ka jiyo wannan labarin ne Ishaƙ?"
"Ɗazu nima ina zaune akasuwa, ɗaya daga cikin mutanen da suke can ƙasar tare yazo mun da labarin, domin kuwa yace ma tun a jiya da sassafe bayan anyi jana'izar sa ya tawo, wuri na ya fara sauka."
To yanzu yana ina ne shi ɗin?" Cewar Kaka tana kallon sa.
"Na ajiye sa ne a shagon ƙofar gida, sabo da da haka yace ayau zai juyama nine na hana sa tafiya, nace ya bari zuwa gobe sai mu tafi tare."
Shiru sukai dukan su ba tare da sunce komai ba, sai uban tagumi da kaka ta buga tana kallon Aishatu data zamto tamkar mutun-mutumi awuirin da take, domin kuwa tun daga lokacin da taji furucin sa na farko bata sake iya motsawa daga yarce take ba, asalima gaba ɗaya bata ji sauran bayanan nasa ba ko kaɗan.
Sai da ta ɗauki kimanin mintina kusan goma ahakan, tukun daga bisani ta ɗago afirgice tana mai kai idanuwan ta kan fuskar mijijn nata, sannan ta buɗe baki cikin rawar murya tana mai faɗin. "Shin dagaske ne Baffah na ya rasu Abban Ahmad?" Ta ƙarasa maganar wasu irin hawaye masu matuƙar gudu suna ɓallewa daga cikin idanuwan ta.
Miƙewa Kaka tayi tsaye tana mai nufar cikin ɗakin ta, hakan da ishak ya gani ne ya sanya sa miƙewa tsaye shima, tukun ya kamo hannun Aishatu yana mai janta sukayi part ɗin su.
ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.
Cikin tsantsar tashin hankali Sarki Barbaru ya doshi hanyar da zata kaisa wurin Boka mai hutar kasko.
Sai dai kuma tun kafin yayi nisa ya hango dan-dazon jama'a na ɓullowa hankali atsan-tsar tashe, ga kuma wani irin sauyawa da yaga sama nayi tana rikiɗewa kamar yacce Ƴammatan Bayin nan suka faɗa.
Hakan da ya ganine ya sanya sa juyawa baya da matuƙar sauri yana mai dosar wurin da dokunan su suke.
Ko daƙiƙa biyu ba baiyi ba daga wurin da yake zuwa ma'ajiyar dokunan.
Wani irin tsalle ya buga tun daga nesa, yarce kasan bashi bane jibge-gen mutumin nan, yana mai hayewa saman wani baƙin doki, tukun ya damiƙi linzamin sa da matuƙar ƙarfi yana mai sa hannu ya daki bayan sa da shi.
Wata irin haniniya dokin ya saki da ƙarfi, kana ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai fucewa daga cikin wurin da tsantsar gudu.
Gudu dokin yake yarce kasan zai tashi sama, yayin da jama'a ke cigaba da furfutowa bakunan su ɗauke da ihu tare da kiran sunan Gargabilu.
Cikin daƙiƙun da basu zarta ukku ba duka dokin ya ɓulla kwanar da zata kai sa wurin Boka mai hutar kasko.
Da matuƙar sauri Sarki Barbaru ya dire daga kan dokin ba tare da ya tsayar da shi ba, hankalin sa na sake matuƙar tashi, sabo da yarce ya hango B.............✍
By
UMAR FARUQ*D*
*BAƘAR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 13*
Boka mai wutar kasko ya futo daga cikin ɗakin sa amatuƙar ruɗe, yana mai kallon sama, ga kuma yarce garin ke sake rikiɗewa yana yin duhu.
Da matuƙar sauri ya dire daga kan dokin, yana mai yin wurin da ya hangi Boka mai hutar kasko.
"Shin meke shirin faruwa damu n ya kai Boka?" Sarki Barbaru ya watsowa Boka mai hutar kasko tambaya cikin kakkausar muryar sa, hankalin sa atsantsar tashe.
Yayin da Boka Barbaru kuma ya cigaba da juyi yana kallon sama, ba tare da ya kalli ko inda Sarki Barbaru yake ba, ballan tana ya tanka masa.
"Na roƙeƙa da abun bauta Gargabilu ka tsaya kai mun bayanin ta inda mafuta take." Sarki Barbaru ya sake faɗa adai dai lokacin da ya ƙaraso gaban Boka mai hutar kasko.
"Ni kai na bansan ta inda zan fara ba, domin kuwa lamarin yazo mun alokacin da ban tsammace sa ba, sabo da ko kaɗan abun bauta Gargabilu bai sanar mun da faruwar hakan ba, gashi kuma afahimta ta ta yanzu naga kamar garin ake shirin rusawa tare da jama'a..." Dakata Boka!" Sarki Barbaru ya katse sa da faɗin haka cikin tsawa, hankalin sa na sake bala'in tashi, tukun daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai ƙara matsawa kusa da Boka mai hutar kasko, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Mafuta nake son ka samar mana Boka, ba wai bayanin abun da yake shirin faruwa damu ba, domin ko tun lokacin da wannan labarin ya iso kunnuwa na na fahimce cewar mun aikata babban laifin ne ga Ubangiji Gargabilu, shiya sa har yake shirin hukun tamu ta wannan hanyar, dan haka duk yanzu ba lokacin dogon jawabi bane, kamata yayi ace ko da na ɓullo wurin nan in hangeka agaban Huta da Ƙasa kana ƙoƙarin nemar mana afuwa ba anan ba." Ya ƙarasa maganar da sakin huci.
Yayin da Boka mai Hutar kasko kuma ya buɗe baki cikin zafi shima yana mai faɗin. "Haƙiƙa al'amarin ya huce duk yarce kake.zato, domin kuwa cikin duka abubuwan daka lissafo ayanzu babu ɗaya da ya rage banyi sa ba, amma duk basuyi aiki ba, sabo da ita kanta Hutar kasko Bama ta koma, tana futar da jan hayaƙi, wanda hakan ke nuni da cewar kamar wasu al'ummar ne daga wani yankin suke shirin kawo mana farmaki, wannan dalilin shine ya sanya kazo ka sameni awurin nan, sabo da in duba ne dan na gano ta yadda zan ɓullowa al'amarin!" Boka mai hutar kasko ya ƙarasa maganar yana mai kallon cikin idanuwan Sarki Barbaru.
Yayin da shi kuma ya juya yana mai kaiwa iska naushi, tare da faxin. "Kai, kai, kai inaaa! Hakan ba zata taɓa faru dani ba wallahi." Ya faɗa da ƙarfi yana mai juyawa ya fara taku daga inda yake zuwa gaba cikin tsantsar sauri, tukun daga bisani kuma ya sake juyowa ahaukace yana mai dawowa gaban Boka Gargabilu, kana daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "To yanzu meye mafuta kenan Boka?"
"Zan koma ciki a yanzu domin nayi ƙoƙarin ganin mun sadu da ubangiji Gargabilu ayanzu-yanzu, duk da yau ɗin bata kasance ranar saduwar mu ba, amma sai dai kuma babu yarce zamuyi dole zanje nabi wata hanya, domin ganin na sadu da shi, sabo da ya samar mana da mafuta."
"To muje mana kawai kafara Boka, domin kuwa na sani ubangiji Gargabilu bazai taɓa barin mu mutaɓe ba, sabo da mun kasance masu ƙoƙarin yin duk wani abu da ya sanya mu muyi." Sarki Barbaru ya faɗa yana mai bin bayan Boka mai hutar kasko da yayi gaba.
Ɗakin iccina ne mai ɗan girma dai dai misali, zagaye yake da bakin ƙyalle wanda aka buga tambarim Baƙar Masarauta tako ina na jikin sa da farin fenti, ga kuma kaskwayen wuta da suke ajiye a kowace kusurwa ta cikin ɗakin suna ci da huta, sai kuma wasu uban kayan kari-kitai kala kala marasa kyan gani da suke ako wane wuri dake cikin ɗakin.
Yayin da daga can jikin bango kuma akayi wani ƙaton daɓe mai matuƙar tudu, domin kuwa harda matattakalar hawa manne ajikin sa.
Daga saman daɓen kuma Sassaƙen gunkin nan wanda suke kira da abun bautar su ne kafe awuri ɗaya, ɗauke yake da kayan ado kala kala manne ajikin sa, sai daga can gefen sa kuma aka ajiye wata shimfiɗar fata tafkekiya, yayin da kowacce kusurwa dake kan shimfiɗar kuma ta kasance ɗauke da kaskwayen Huta waƴan da suke matuƙar ci da huta, sai dai kuma kamar yacce Boka ya faɗa gaba ɗaya hutar suna futar da jan hayaƙi ne, yayin da kalar hutar kuma ta kasance baƙa!
Acan kuwa tsakiyar shimfiɗar mazaunin Boka mai hutar kasko ne awurin.
Gaba ɗaya layayoyi ne da ƙulluka kala-kala zagaye da mazaunin nasa, yayin da daga gaban sa kuma aka ajiye wata randa da take faman ci da huta itama, sai akusa da ita kuma aka ajiye wani ƙaton faranti da yake ɗauke da farin yashi acikin sa mai matuƙar yawa.
"Shin yanzu ka fahimci abun da nake sanar da kai ko, kaga yadda kalar Hutar kasko ta koma, abun da bai taɓa faruwa ba tun kafuwar mu duniya, wato canzawar Hutar kasko." Boka mai hutar kasko ya faɗa afirgice yana mai kallon Sarki Barbaru.
"Tabbas ko al'amari nada matuƙar ruɗarwa, dan haka na roƙe ka da abun Bauta Gargabilu kayi gaggawar fara aikin nan, tun kafin ƙwaƙwalwar kaina ta tarwatse, domin kuwa al'amarin baƙaramun ruɗar dani yayi ba." Cewar Sarki Barbaru awani irin hargitse.
Dasauri Boka mai hutar kasko ya cigaba da tafiya yana mai nufar kan daɓen nan.
Take masa baya shima Sarki Barbaru yayi cikin sauri.
Cikin hanzari yasa hannu yana mai fara fincikar wasu layoyi daga cikin layoyin da suke awurin da matuƙar yawa, adai dai lokacin da ya zauna awurin.
Yayin da Sarki Barbaru ma ya samu wuri akan shimfiɗar ya zauna, yana mai cigaba da bin hutar kasko da idanuwa.
Wasu manya- manyan layoyi ya ɗauko har
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 76