Share this page
gani tsaye su duba jikin ta. Sai da suka ɗauki kimanin daƙiƙa kusan arba'in suna abu guda, tukun suka gama da wannan jirgin ba tare da sun samu ko mai ciki acikin sa ba, sannan suka basa hanya ya wuce, kana suka koma kan na gaba da aka tsayar, kasancewar masu binciken daban suke, masu yawo acikin jirgin ruwan Baƙar Masarauta suna kaɗo jirgayen dake wucewa bakin ruwan, suma daban ne. *JAHAR RUMAN* Sai yamma liƙis Ishaƙ da Aishatu suka isa jahar ruman, cikin rugar da ahalin Aishatu suke rayuwa acikin ta, bayan kwana ɗaya da yini ɗaya da sukayi akan hanya. Gari ne mai tsantsar daɗi da ni'ima. Bukkoki ne tsalli-tsalli awurare daban daban da suke acikin rugar da suke. Tun daga nesa suka hango mutane da yawa zaune akan tabarmu, ƙarƙashin inuwar bishiyar darbejiya. Jiki asaɓule suka ƙarasa wurin, suna masu durƙusawa agaban tabarmun. Sosai suka yiwa junan su gaisuwa, tukun suka tashi gaba ɗayan su zuwa cikin gidan. _BAYAN SATI ƊAYA_ Yau ta kasance ranar Al'hamis, wacce tayi dai dai da cikar mahaifin Aishatu kwana goma da rasuwa. Tun jiya suka fara haɗa kayan su, kasancewar yau Al'hamis itace ranar da suka tsara zasu koma, amma zasubi jirgin ƙarfe goma na safe ne. Sosai dangin Aishatu suka haɗa musu tsaraba suka ƙulle ta wuri ɗaya. Gaba ɗaya kowa ka kalla dake cikin gidan jikin sa atsantsar sanyaye yake, domin kuwa har kawo yau mutuwar bata sake suba, jinta suke tamkar sabuwa, barin ma Aishatu da take jin jikinta na sake yin sanyi, wata irin kasala na rufe ta, tana mai jin tamkar su fasa tafiyar daga gobe, su bari sai wani lokacin, ga yarce gaban ta ke yawan faɗuwa tun bayan kwana biyu da suka huce, sai dai kuma babu wanda ta faɗawa kalar yanayin da take ciki, kamar yacce babu wanda ya tambayae tama, sabo da kowa na dan ganta sanyin nata ne da cewa mutuwar ce bata sake taba, yayin da ta fannin ta itama take ganin duk hakan ne. Acan Ɓakar Masarauta kuwa yau kimanin sati ɗaya cir kenan da fara binciken jaririn da sukayi abakin ruwa, ba dare ba rana kullum abu ɗaya sukeyi, domin kuwa ko runtsawa harta da shi sarki Barbaru, sabo da gudun karsu kwanta jirgin da jinjirin yake aciki yazo ya huce basu sani ba. Zuwa yanzu sun kashe jinjirayen mutane sama da ashirin da biyar, sabo da duk cikin yaran da suke samu har yau ba'a samu wanda ya tuntsirar da hutar kasko ba kamar yacce Boka mai hutar kasko yace jinjirin zaiyi. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Hadimai ne kawai ke giftawa ta ko ina acikin masarautar, wasu ɗauke da abubuwa a hannayen su, yayinda wasu kuma suke share-share da goge-goge. Aɓangaren sashin Gimbiya Huwaila, uwar gidan Sarki Abdallah kuma zaune take agefen gadon dake can cikin ƙuryar ɗakin ta. Kallon matar dake zaune aƙasan gado daga gaban ta tayi ido cikin ido, tana mai miƙa mata wani ƙullin tsuma dake riƙe ahannun ta. Miƙo tafin hannun ta matar mai kimanin shekaru hamsin tayi, itama ɗin idanuwan ta acikin na Gimbiya Huwaila. "Ina son ki buɗe kunnuwan ki ki saurareni Jakadiya, domin kuwa awannan karan ba lallai ne na sake yarda dake ba, muddin kika cemun an samu matsala kamar na baya." Ta faɗa tana mai cigaba da kallon ta. "Na ɗauki nutsuwa ta, hankali na, tare da kunnuwa na na miƙa su zuwa gareki yake Gimbiyar Masarautar Wasai, uwar Sarkin mu na gobe insha Allah, dan haka ki faɗi kome nene, ni kuma ina mai tabbatar miki da babu abun da zai hana sa yuwuwa awanan karan da izinin Allah." Matar data kira da Jakadiya ta faɗa tana mai gyara zaman ta awurin da take. Yayin da ita kuma Gimbiya Huwaila ta lumshe idanuwan ta tana mai sake dunƙule ƙullin tsumman ahannun ta, tukun daga bisani ta warasu akan fuskar Jakadiya, sannan ta buɗe baki tana mai yin ƙasa-ƙasa da murya, yadda kasan ba iya suka ɗai bane acikin ɗakin, wurin faɗin. "Wannan ƙullin da kika gani na baki, ba komai bane acikin sa face layoyi tare da garin magani, wanda nake son ayanzu-yanzu da zarar kin futa daga ɓangaren nan kije ki ai'watar dasu, domin kuwa Boka ya bani tabbacin cewa muddin anyi amfani da shi kamar yacce yace, to babu abun da zai hana duk abun da yake acikin cikin ta mutuwa ko mace ko namiji ne kuwa." Ta faɗa tana mai cigaba da kallon ta, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Layoyi ne tare da garin magani aciki, yadda zakiyi ai'kin shine, su layoyin zakije ki ajiye su ne aƙar-ƙashin makwancin ta, wato gadon da take kwana akai ita kaɗai, yayin da shi kuma ƙullin garin maganin, zaki zubasa aduk inda kika san zata taka, kuma ana son ya zamto ta takasa ne har kimanin sau ukku arana, wato safe, rana da kuma dare, muddin kikayi hakan dai-dai, ni kuma na miki alƙwarin mallaka miki kuɗi har kimanin Miliyan talatin, tare da sarƙar gwal babba, da kuma gidaje, kamar yacce na faɗa miki abaya." Ta ƙarasa maganar tana mai buɗe tafin hannun ta ta sakar mata ƙullin maganin acikin sa. "Ina son daga yanzu kisa aranki cewar gawace acikin Gimbiya Fulani, domin kuwa ina mai baki tabbacin babu abun da zai hana wannan abun faruwa, dan kuwa ayanzu haka da zarar na futa daga ɓangeren nan nata zan huce in ajiye layoyin, sannan kuma in barbaɗa wannan ƙullin maganin abakin ƙofar ta, kana kuma idan dare yayi in sake zubasa abakin ƙofar turakar mai Martaba, tunda kin san yau ɗin kwanan tane." Jakadiya ta faɗa tana mai sakin murmushi. "Yawwa bayan an gama da wannan aikin kuma, ki sani akwai wani sabo da zaizo, wanda za'ayi sa akan wancan ɗan iskan yaron da suke kira da Babban yaya, shima kuma ki sani farashin sa daban ne da wannan bawai duk ɗaya ba." Ta ƙarasa maganar da taune laɓen ta na ƙasa, tare da komawa jikin allon haɗaɗɗen gadon da yake acikin ɗakin nata ta jingi na. "Daga yau ina son ki fara kallon sa amatsayin gawa shima, domin kuwa muddin aikin yazo, babu wani abu da zaisa na kasa yinsa nima, dan haka yanzu ma bara na tashi domin naje na aiwatar da wannan ɗin." Jakadiya ta faɗa tana mai miƙewa tsaye. "Da gani sai ke ce maganar nan, bana son bayan mu wani yaji ta ko kuma ya ganta, dan haka sai ki kiyaye." Ta faɗa daga zaunen da take tana mai kallon ta. "Insha Allah Uwar Sarkin gobe." Jakadiya ta faɗa tana kallon ta, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Na barki lafiya." Kana ta juya tana mai fucewa daga cikin ɗakin. Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa, zaune take akan tattausan kafet ɗin da yake malale acikin bedroom ɗin nata, ta jingina da kujerar da take abayan ta tana mai ɗan cizon lip ɗin ta tare da ya ƙuna fuska, sabo da yarce take jin ciwon bayan data tashi da shi tun bayan tashin ta daga baccin safe na ƙara ƙaruwa fiye da baya, ga kuma yarce take jin marar ta na karta mata, hakan shine ma yasanya ta saukowa daga kan kujera ta zauna akan kafet, sai dai kuma babu wanda yasan halin da take ciki a masarautar, kasancewar babu wanda ta sanarwa. Tana cikin wannan yanayin ta jiyo sautin muryar jakadiya tana mai kwaɗo sallama daga bakin ƙofa. Dasauri ta gyara zamanta tana sakin fuskar ta sosai, tayarce koda jakadiya ta shigo ba zata fuskanci cewar bata da lafiya ba, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Wa'alaikumu salam, lale marhabun da Jakadiya." Ta ƙarasa maganar fuskar ta ɗauke da murmushi. Yayin da itama Jakadiya ta danno kanta zuwa cikin ɗakin bakin ta amatuƙar washe. Direct ta doshi bakin danƙararen haɗaɗɗen gadon dake cikin ɗakin yake. Wuri ta samu ta zauna tana mai facing ɗin Gimbiya Fulani, tare da jingina da katakon gadon da yake abayan ta, tukun ta buɗe baki cikin tsantsar far'ah tana mai faɗin. "Barka da hutawa Gimbiya Fulani, ɗiyar Sarki jikar Sarki, kana matar Sarki, sannan kuma uwar Sarkin gobe." Ta ƙarasa maganar tana mai kai hannun ta da yake riƙe da layoyin nan bayan ta ta kifesa aƙasan kafet ɗin nan. Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani tayi murmushi tana mai buɗe baki tace. "Jakadiyar Sarki kenan, amintacciya kuwa abokiyar shawarar Sarki, wato ke dai ako da yaushe bakya taɓa gajiya da fasawa mutane kai ko?" "Haba dai Gimbiyar mu, ai bawani fasa kai, duk wanda kikaji an faɗa masa to ya kai afaɗa masa ne dama, domin kuwa aduk faɗin gidan nan babu wata ƴar lele bayan ke a wurin mai Martaba, sabo da ke kaɗaice kika ajiye magajin sa acikin gidan nan, kinga kuwa yabo gareki ya zama dole." Jakadiya ta faɗa tana mai sake matsar da hannun ta baya fuskar ta ɗauke da murmushi, ba tare da ta bari Gimbiya Fulani ta lura da itaba ko kaɗan. Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani ta ɗan saki gajeran murmushi, sabo da jin kalamin Jakadiya da tayi, bayan kuma tasan da zata futa daga nan ɗin ta tafi wurin wata itama hakan zatai mata, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "To Jakadiya abar dai zancen haka kawai, atafi na gaba kuma." Murmushi Jakadiya tayi tana mai sake kai hannun ta baya tare da gyara zaman ta awurin, tayarce Gimbiya Fulani ba zata gane abun da take yi ba, tukun tace. "Dama mai Martaba ne ya turo ni gareki akan nazo na jiye masa lafiyar jaririn sa, domin kuwa akullum yana faɗin cewa mafarkin sa na nuna masa namiji ne ɗauke acikin ki wannan karan ma." Murmushi itama Gimbiya Fulani tayi tana mai lumshe idanuwan ta, domin kuwa harga Allah ta gaji da surutun Jakadiya, gaba ɗaya ma ta ƙagara ta tashi ta futa ko taji da abun da take ji, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan nata tana mai faɗin. "Hmmmm! Mai martaba kenan, to in kin koma sai kisanar dashi cewa, Baby na cikin ƙoshin lafiya." "Tom shikenan ni zan huce, na barki lafiya Uwar Magaji." Ta ƙarasa maganar tana mai hulla layoyin nan ƙarƙashin gadon da sauri, sannan ta miƙe tsaye fuskar ta ɗauke da tsantsar murmushi, tana mai sake faɗin sai da anjima." "Allah ya kaimu na gode." Gimbiya Fulani ta faɗa tana mai miƙar da ƙafafuwan ta akan kafet ɗin nan. Yayin da Jakadiya kuma ta huce ranta fal farin ciki, sabo da ganin da tayi ta samu nasarar aiwatar da abu ɗaya daga cikin abubuwan da zatayi cikin salama. Tana zuwa ƙofar ɗakin tayi sa'a kuwa babu ko mutum ɗaya dake cikin falon. Ganin hakan da tayi ne ya sanya ta fara waige-waige, sai da ta tabbatar da babu ko ƙuda dake kallon ta acikin ɗakin, tukun ta sanya hannun ta jikin haɓar zanin ta tana mai ciro ƙullin maganin nan daga cikin sa. Sake wawwaigawa tayi taga dai still babu kowa, sannan ta kwance sa cikin sauri tana mai zubasa abakin ƙofar ɗakin da matuƙar sauri, tukun ta juya tana mai yin gaba abun ta, bayan ta mayar da maganin cikin haɓar ta da zummar taje ta zuba abakin turakar mai martaba ma. *ƘASAR MALIN, JAHAR RUMAN.* Ƙarfe goma dai dai na safe jirgin su ya ɗaga ta cikin ruwa, yana mai ɗaukar hanyar da zata kaisa Ƙasar Hausa, bayan su Aishatu sun gama koke-koke ita da ƴan uwanta, kana suka mata fatan Allah ya sauke ta lafiya, tare da al'ƙawarin suna nan zuwa idan ta sauka. Sosai zuciyar ta ke cigaba da tsinkewa, gaban ta na wani irin faɗuwa, alokacin da jirgin su ya fara nitsawa cikin hanya. Jin ta take wani iri, gaba ɗaya jikin ta yayi matuƙar yin sanyi, ga kuma zuciyar ta dake cigaba da tsinkewa, yarce kasan ranar da aka sanar mata da mutuwar mahaifin ta. Addu'oi ta fara karantowa acikin zuciyar ta ba tare da ta sanarwa Ishaƙ halin da take ciki ba. Sai dai kuma shima ɗin duka yana lura da sauyawar tata, kasancewar akusa da shi take, amma sai bai kawo komai ba aransa, ya dangana hakan kawai da zafin rabuwa da ahalin tane ya sake sanyawa ta koma haka ba komai ba. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Ko da Jakadiya ta bar part ɗin Gimbiya fulani direct ta doshi turakar mai martaba, tayi sa'a kuwa babu wanda ta samu a wurin kamar yacce tai fata, hakan yasa ba tare da ta tsaya ɓata lokaci ba ta sake ciro ƙullin tsuman nan ta kwance sa, tana mai baɗasa abakin ƙofar, tukun tayi sauri ta koma baya cikin tsantsar farinciki. Aɓangaren Gimbiya Fulani kuwa, sosai ciwon da take ji ya cigaba da ƙaruwa, barin ma bayan lokacin da aka idar da sallahr magariba amasallacin dake cikin masarautar, amma duk da haka tai shiru da bakin ta ba tare da ta sanarwa kowa ba, haka kuma koda dare yayi bata tafi turakar mai martaba ba, duk da kasancewar itace da shi ɗin yau. Misalin ƙarfe goma ɗaya na dare ciwon naƙuda ya sake turnuƙe ta mai matuƙar tsanani, banda cizon leɓe tare da yarfa hannu babu abun da take ai'kin yi awannan lokacin. Tana cikin wannan yanayin ta jiyo sautin muryar hadimar ta, wacce ta kasance tamkar Uwa ga Ƴaƴan ta, kuma ta zamto aminiya agare ta, tana mai kwaɗo sallama abakin ƙofar ɗakin ta, kasancewar aduk lokacin da take da ciki dama haka Hadimar tata mai suna Larai take ziyarta ta duk dare, dan taga halin da take ciki, domin kuwa wani lokacin ma idan ta shigo sai dai ta juya ba tare da ta same ta ba, idan har ranar ta kasance tana turakar mai Martaba kenan, sannan kuma da zarar ta haihu to kula da yaron da komai nasa yake komawa wurin ta, haka duk ta raini yaran tun daga kan Babban yaya har zuwa Nafisat auta. Babu yarce magauta basuyi ba su janyo ta ajikin su, domin su samu damar kassara rayuwar Babban yaya cikin sauƙi, amma kwata-kwata taƙi, hakan ne yasa gaba ɗaya itama sukabi suka tsane ta, sannan kuma suke jin haushin ta, sai dai kuma babu yadda zasuyi da ita, domin kuwa Gimbiya Fulani ta daɗe da ƴanta ta. Macece mai kimanin shekaru arba'in da ƴan kai aduniya, Ƴaƴa huɗu duka ta haifa, daga nan kuma mahaifin su ya rasu. Tun bayan rasuwar sa bata sake yin wani auren ba, ataƙaice ma tana zaune ne anan ɓangaren Gimbiya Fulani itama data bata ɗaki. Da matuƙar sauri, sannan kuma cikin tsantsar tashin hankali ta ƙarasa wurin ta tana mai faɗin. "Subhanallahi haihuwar ce tazo kenan Mamy'n Yara." Ta ƙarasa maganar tana mai dafata, hankalin ta atsantsar tashe. Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani take ta cigaba da cizon yatsa, ba tare da tace mata komai ba. Dasauri ta juya tana mai shirin tafiya, bakin ta na faɗin. "Bara naje na sanarwa Jakadiya ta sanarwa mai Martaba, in yaso ko asibiti ne sai ataf... Caraf taji Gimbiya Fulani ta riƙo yatsun hannun ta, hakan ne yasata juyowa ɓarin da take tana mai kai idanuwna ta kanta. Ido huɗu sukai da junan su alokacin da ta juyo ɗin, tukun daga bisani Gimbiya Fulani ta buɗe baki cikin muryar ta da take nuni da halin da take ciki na tsantsar ciwo tana mai faɗin. "Kar kisanar masa, bana san wani mutum yaji labarin haihuwar nan ayanzu, domin kuwa kin san yarce wasu daga cikin mutanen gidan nan suke, dan haka ki barshi har zuwa nan da asuba muga yarce Allah zaiyi." Ta ƙarasa maganar da ƙyar tana mai cizon leɓe. "Tom shikenan, amma bara naje ɗakina na ɗauko wasu magun-guna dana tanade su sabo ds zuwan wannan ranar." Umma Larai ta faɗa ba tare data tsaya ja da maganar shugabar tata ba, domin kuwa sai dai ta bada labarin magautan cikin gidan nan, ba dai wani ya bata ba, tukun ta juya cikin sauri tana mai fucewa daga cikin ɗakin. *ƘASAR MALIN, CIKIN JIRGIN RUWA.* Dare ya tsala sosai, yayin da gari ya kasance baƙiƙƙirin da duhu, amma duk da haka jirgin nan bai tsaya ba, kasancewar ɗauke yake da futulu masu matuƙar haske tako ina ajikin sa, hakan yasa duk tsayin dare bai sanyawa direbobin su tsaya daga tuƙi, muddin ba abinci aka tsaya siya ba ko sallah. Tini suka daɗe da futa daga cikin Jahar Ruman, dan har sun shiga Jahar Karfuz ma. Tun da suka shigo jahar karfuz Aishatu taji jikin ta ya ƙara matuƙar yin sanyi, ga bugun zuciyar ta kuma da yayi matuƙar ƙaruwa, tayarce har take jin tamkar zata faso ƙirjin ta ta futo, tun tana addu'a acikin zuciyar ta har sai da ta dawo yin ta abayyane, sabo da yarce take jin yanayin na sake hau-hawa fiye da da, tayarce har Ɗan cikin ta shima keta motsi fiye da yarce ya saba yi. Ta fannin Ishaƙ shima sosai yake jin zuciyar sa na cigaba da dukan tara-tara, ga wani irin tsoro da fargaba da suka lulluɓe zuciya da ruhin sa, irin wanda bai taɓa tsintar kansa a makamancin su ba. Hakan ne yasa sa damƙe hannun Aishatu cikin nasa da matuƙar ƙarfi, yana mai karanto duk addu'ar da tazo zuciyar sa azuciyar sa shima. Misalin ƙarfe huɗu da ar'ba'in dai-dai na dare jirgin su ya danna kansa zuwa yankin da ya ratso ta cikin BAƘAR MASARAUTA, wanda shigar tasa kuma tayi dai dai da bugawar da ƙirjin Aishatu yayi da matuƙar tsanani fiye da da, yayin da zuciyar ta kuma ta cigaba da tsinkewa da matuƙar sauri. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Rabi da kwatan mutanen dake cikin jirgin suka furta cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali, sabo da yarce suka hango h.............✍ *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 15* Hasken futulu masu matuƙar ƙarfi an dallo idanuwan su tun daga can nesa da su. Take a wurin Aishatu ta sake matuƙar rikicewa, jikin ta na tsanstsar rawa da karkarwa, hakan da Ishaƙ ya gani ne ya Sanya sa sake damƙar hannun ta da matuƙar ƙarfi, bakin sa na furta duk addu'oin da suka zo cikin zuciyar sa cikin tsantsar tashin hankali, kamar yadda sauran ɗaukacin mutanen da suke a cikin jirgin suke. Yayinda tawagar mutanne Baƙar Masaruata kuma suka afka cikin jirgin ruwan su da matuƙar sauri, tukun suka doso inda suka hango jirgin su Aishatu, suna masu cigaba da dallewa direbobin tare da mutanen ciki idanuwa da hasken futulun su, bakin su kuma na aikin furta kalmar. "Gargabilu!" Da tsantsar ƙarfi. Cikin daƙiƙun da basu zarta huɗu ba suka ƙaraso wurin da jirgin da su Aishatu suke ciki yake. Ba tare da sun tsaya jan lokaci ba suka zare makaman su daga cikin jikin su, suna masu ɗaga su sama, tukun suka yiwa direbobin jirgin nuni da hanyar da zasu bi. Cikin tsantsar ruɗu kuwa matuƙarn jirgin suka nufi wurin da suke nuna musu hankulan su abala'in tashe, domin kuwa ba iya makaman su bane abun tsoro, su kansu mutanen da suke a cikin jirgin abubuwan firgici ne ga mutumim da bai saba ganin su ba. Yayin da jama'ar dake cikin jirgin kuma suka sanya ihu da matuƙar ƙarfi, suna masu faɗin sun shiga ukku cikin tsantsar tashin hankali. Afannin Aishatu kuwa kallo ɗaya tayiwa mutanen taji cikin ta yayi wata irin murɗawa, sabo da firgita, tukun daga bisani Ɗan cikin nata ya fara wani irin hutsul-hutsul da matuƙar sauri, tayarce har na kusa da ita zai iya lura da motsin sa muddin ya kalli cikin nata. Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwan ta, tana mai ɗaukar tafin hannun ta ta dafe cikin ta da shi, zuciyar ta na tsantsar bugawa, yayin da bakinta kuma ke ai'kin furta duk wasu addu'oi da sukazo cikin sa, ba tare da tasan tana yin suba ma. Basu dakata ba har sai da suka turasu gefen ruwan nan, inda su sarki Barbaru da Boka mai hutar kasoko, tare da sauran jama'ar su suke. Shimfiɗar fata ce ajiye daga gefen ruwan, wacce jikinta yake ɗauke da jini faca-faca, ɗauke take da kaskon wuta da yake matuƙar ci da wuta, yayin da gefen kaskon kuma aka aje wata irin kibiya mai matuƙar tsini, sai Boka mai wutar kasko da yake zaune daga gefen shimfiɗar, yayin da Sarki Barbaru kuma yake daga tsaye a bakin ruwan nan, gaba ɗayan sa a wani irin birkice, domin kuwa ko shigar da ke sanye jikin sa tun ta wancan satin ce, ranar da suka fara riskar tashin hankalin nan bai canza ta ba, asalima ko barin hurin kwata kwata baiyi ba har kawo yau, domin kuwa abinci ma a rana baifi sau ɗaya yake cinsa ba, shima sai yaji yunwa na shirin hanasa miƙewa tsaye. Sosai mutanen cikin jirgin nan suka sake matuƙar firgita, suna masu sakin ihu da salati, sabo da irin mutanen da suke sake arba da su agafen ruwan da suka iso yanzu. "Daƙiƙa ɗaya kawai na baku, ko wane mutum ya zamto ya kama bakin sa, muddin kuma kuka bari na sake jin ihun wani cikin kunnuwa na bayan giftawar daƙiƙun, to kusani sunan mutum gawa, ko waye ne shi kuwa." Sarki Barbaru ya faɗa cikin muryar sa mai matuƙar amo, yana mai kallon mutanen cikin jirgin nan. Take kuwa wurin ya ɗauki shiru gaba ɗaya, yarce kasan ba'a taɓa hallitar mutum ba, balle ayi zaton anan wurin ihun ya gama tashi. Yayin da Aishatu kuma ta taune leɓen ta na ƙasa da ƙarfi, tana mai dafe cikin ta da hannu ɗaya, sabo da yadda taji marar ta tayi wani irin kartawa, ga kuma bayan ta da taji lokaci ɗaya ya riƙe gam! Taune leɓenta ta cigaba dayi da ƙarfi, tana mai faman zare idanuwa tare da gumtse baki, gudun kar addu'ar da takeyi a zuciya ta suɓuce ta futo fili, Sarki Barbaru yaji, yayin da shi kuma Ishaƙ yake ta aikin shafa bayan ta a hankali, cikin tsantsar ruɗu shima. "Ku shiga cikin jirgin nan yanzu, ku bincika mana ko ina da ina, lungu da saƙo, ku futo mana da duk wani jinjirin yaro namiji da kuka samu." Sarki Barnaru ya faɗa cikin amo yana mai kallon wasu daga cikin dakarun nan nasu. Yayin da su kuma mutanen cikin jirgin nan hankulan su ya sake bala'in tashi, barin ma matan da suka san suna ɗauke da jariran Ƴaƴa. Dasauri wata mata da take ɗauke da jinjirin ta a hannunta, ta sake danna sa cikin hijabin ta jikin ta na tsantsar rawa, sabo da yadda taga mutanen nan sun tunkaro inda take gadan-gadan, kasancewar sun riga da sun hango ɗan nata tun farko, sabo riƙesan da tayi a hannun ta. Girgiza kanta ta farayi tana mai ja da baya daga zaunen da take, cikin tsantsar tashin hankali da firgici, yayin da su kuma waƴan nan dakarun suka cigaba da doso ta gadan-gadan. Ganin da tayi suna daf da isowa inda take ne, ya sanya ta miƙewa da sauri tana mai shirin rugawa baya, amma sai dai tana ɗaga ƙafarta ɗaya taji ta- ta kife kif a ƙasa, kanta na dukan katakon dake jikin jirgin da matuƙar ƙarfi, sabo da yadda ɗaya daga cikin dakarun ya sanya ƙafarsa ya tatsiye ta da ita. Gadan-gadan ya ƙarasa zuwa wurin da take yana maj sa hannu da niyyar funcikar Ɗan, amma sai tayi sauri ta ƙara ruƙun-ƙume sa acikin jikin ta, tana mai fashewa da wani irin gigitaccen kuka mai ban tausayi, take kuwa shima jaririn ya tsanyare da kuka da matuƙar ƙarfi, sabo da zafin matsar da yaji, wacce uwar tasa tayi masa gudun kar aƙawace mata shi. Tas! Tatas!! Tasss!!! Wasu irin ƙarar marika suka tashi a wurin da matuƙar ƙarfi, waƴan da suka sake sanya mutanen cikin jirgin ruɗewa da firgicewa, suna masu toshe bakunan su da hannu. Badakaran nan ne ya ɗauke matar da wasu gigitattun marika, sabo da yadda yaga yana miƙa hannu zai karɓi Ɗan tana kuma sake ruƙun-ƙume sa, tukun daga bisani ya ɗago tsaye yana mai funciko wata doguwar takobi daga ƙugun sa yayi kan matar da ita. Wata irin gigitattar ƙara matar ta saki, tana mai rumtse idanuwan ta da matuƙar ƙarfi. Funcikar Ɗan ya sakeyi da matuƙar ƙarfi, yana mai mayar da takobin cikin jikin sa ba tare da ya kaita jikin ta ba, sabo da yadda yaga riƙon da tayiwa yaron yayi sakwa-sakwa ta dalilin ihun da ta saki, tukun ya juya jinjirin riƙe a hannun sa, da yake tsala uban kuka yana mai ɗaga kafafuwan sa sama yayi gaba. Dasauri matar nan ta miƙe tsaye tana mai bin bayan sa cikin tsantsar ɗimaucewa. Ƙafar sa ɗaya ya

Chapter 15 of 76