ya zagayo."
Ɗaya daga cikin matsan da suke dafe da Bir waƴan da zasu iya yin sa'anni a shekaru ya faɗa suna masu cigaba da dosar inda wasu ɗakuna da aka haɗasu da iccina suke jera da matuƙar yawa.
"Ai dama ka dena wahalar da bakin ka ɗan uwa Mauzum, domin kuwa duk abun da zakace akan Bir ya dena shish-shigewa Gimbiya kayi abanza ne, dan ko ba saurara yake ba balle harya dauka ma, shiyasa ni yanzu tsakani na dashi kawai idone babu ruwa na, sabo da karma ya gogamun laifin da ban janyo ba." Cewar ɗayan yana mai kallon ɗan uwan nasa.
Yayin da shi kuma Bir ya lumshe dara daran idanuwan sa yana mai yin shiru ba tare da ya tanka musu ba, duk da dai yana jinsu sai aikin kawai taunar leɓan ƙasan bakin sa da yake yi da haƙoran sa ahankali, ahaka har suka ƙarasa wurin da ɗakunan itacen nan suke ajere re-ras ta kowanne ɓangare.
Sai da suka shigar dashi har cikin wani ɗan ƙaramin ɗaki dako daɓe babu akasan sa, sai ƙasa da kuma shimfiɗun tsummokara waƴan da suke kwanciya akan su, tukun suka ajesa. Miƙewa tsaye sukai suna kallon sa, yayin da shi kuma yake akwance rigin-gine idanuwan sa na kallon iccinan da aka jera asama wurin rufin ɗakin.
"To Bir bara mu muje musanarwa Iya cewar kadawo, domin kuwa tun lokacin da Gimbiya ta rufeka hankalin ta yake atashe ko abinci bata ƙara ciba." Suka faɗa suna masu juyawa suka fuce daga cikin ɗakin.
Ahankali Bir ya miƙe daga kwancen da yake yana mai taune laɓen sa tare da yamutsa fuska, alamun har yanzu jikin nasa nayi masa ciwo kenan.
Waige waige ya farayi acikin ɗakin nasu har idanuwan sa suka sauka akan wasu curin kaya da suke ƙulle wuri ɗaya.
Jan jiki ya farayi har ya ƙarasa inda kayan suke, tukun ya sanya hannu yana mai bubbuɗasu, kana ya janyo wata ƙatuwar kwari da gwafa daga cikin kayan yana mai riƙe ta ya jujjuya ahannun sa yana kallon ta, tukun ya miƙe tsaye ahankali yana mai dafa katakwayen da suka kasance bangon ɗakin, kana ya fara ɗingisa ƙafafuwan sa yana mai dosar hanyar waje.
Yana futa ya ɗauki hanyar dake kallon kudu yana mai miƙar ta, tafe yake yana dingishi tare da cije lips ahanka har yayi tafiya mai nisa daga inda yake, tukun ya ɓulla wani huri wanda za'a iya kiran sa da daji sabo da bishiyun da suka kasance awurin masu matuƙar yawa ta koina, banda sautin kukan tsunysaye babu sautin da akeji yana tashi awurin.
Jingina yayi jikin wata bishiya yana mai ɗaga kansa sama tare da lumshe idanuwan sa. Kana ya ɗaga laɓɓan sa ahankali yana mai faɗin. "Iya tace ba'a taɓa yin nasara daga zaune, sannan kuma daɗi bai zuwa sai bayan ansha gumurzu, dan haka na ɗauri aniyar zama jarumi har zuwa lokacin da zancimma buri na, zan jure kowace kalar wahala daga gareki yake Gimbiyar BAƘAR MASARAUTA, zan ɗauki ko wane kalar wulaƙanci da ƙasƙanci muddin zan samu abun da zuciya ta take muradi agaba, zan tabbatarwa duniyar BAƘAR MASARAUTA cewa Iya batai ƙarya ba data kirani da suna JARUMI." Ya ƙarashe maganar yana mai buɗe idanuwan sa tare da sauke kansa ƙasa, tukun yakai duban sa kan tafin hannun sa da yake riƙe da kwari da gwafa, sannan ya matsa daga jikin bishiyar nan yana mai ɗaukar kwarin ya maƙala sa ajikin gwafar, tukun ya saita wata shirgegiya bishiya da take nesa dashi sosai, yana mai jan gwafar tukun ya sake ta.
Fit!!! Kake jin sautin futar tsinken daga jikin gwafar da matauƙar gudu yana mai zuwa ya cake cak ajikin bishiyar.
Cigaba da saki yayi baji ba gani yana yi yana tangaɗi tare da buɗe baki, sabo da yarce yake jin wata irin hajijiya na ɗibar sa, amma duk da haka ko kaɗan bashi da alamar zai tsaya.
Kallo ɗaya zakai nasa ka fahimci ba'a ƙaramun jigace yake ba, sabo da yarce gumi ke cigaba da tsiyaya daga jikin sa da yake tsantsar rawa, ga laɓɓan sa da sukayi matuƙar buahewa tare da yin baƙi, alamun ba ƙaramar ishirwa yake ji ba kenan!
"Kai Jarumi! Jarumi!! Jarumi!!! Shin meye hakan kake yi?" Sautin muryar iyar bayi ya daki dodon kunnen sa cikin firgici, amma duk da haka bai waiga ya kalli inda yajiyo sautin ba balle harya tsaya daga abun da yake, sai uban tangaɗi da yake yi kawai!
Da gudu Abokan nan nasa guda biyu da suka kai sa ɗaki suka ƙaraso inda yake suna masu sanya hannu suka rirriƙe sa, tukun Mauzum ya anshe kwari da gwafar daga hannun sa yana mai dire su aƙasa.
"Shin me yasa zaka baro ɗaki kayo nan, bayan kasan ɗauke kake da raunika ajikin ka Jarumi?" Cewar Iyar bayi tana mai durƙusawa ta aje ƙatuwar ƙwaryar dake rumgume ahannun ta agefe, tukun ta matsa inda su Mauzum suke zaune aƙasa, rungume da Bir da yake ta faman sakin numfarfshi idanuwan sa na kakafewa ahannun su.
Zama tayi tana mai tanƙwashe ƙafafuwan ta agaban sa, tukun ta tallabo kansa tana mai ɗora sa akan cinyar ta, kana ta buɗe tafin hannun ta tana mai ɗan marin fuskar sa sama-sama bakin ta na furta kalmar. "Kai Jarumi! Jarumi!! Jarumi na!!!" Amma sai dai ko kallon ta baiba sai idanuwan sa da suke cigaba da kakkafewa numfashin sa na fuzga da ƙarfi.
"Kai Mauzum maza yi sauri ka miƙo mun ƙwaryaccan." Iyar Bayi ta faɗa hankali tashe tana mai cigaba da marin fuskar Bir tare da faɗin Jarumi.
Dasauri suka mike su duka biyun har suna gware da juna wurin tashi, tukun Mauzum yay maza yaje ya ɗauko ƙwaryar da take cike da ruwa tare da kofi acikin ta yana mai zuwa ya ajeta agaban Iyar Bayi.
Dasauri ta sanya hannu ta ɗauki moɗar dake cikin ruwan tana mai kwaso ruwan da shi, tsiyaya sa tayi atafin hannun ta, tukun ta yarfawa Bir shi akan fuska tana mai cigaba da kiran sunan sa.
Ajiyar zuciya ya fara saukewa akai-akai yana mai lumshe idanuwan sa.
Hakan da Iyar Bayi ta gani ne yasan ya ta sa hannu ta ɗago kansa, tukun ta ɗora masa moɗar ruwan akan laɓɓa tana mai faɗin. "Sha ruwa Jarumi na."
Bai musa mata ba ya buɗe bakin sa ruwan ya fara wucewa da sauri da sauri.
Tas ya shanye ruwan yana mai buɗe idanuwan sa, sake maida moɗar ruwan tayi cikin ƙwaryar ta ƙara kamfato sa, tukun ta ƙara ɗora masa akan baki ya shanye sa tas.
Sannan ya sake maida kansa kan cinyar Iya yana mai lumshe idanuwan sa.
"Shin sai yaushe ne zake dena shigewa Gimbiya Jarumi? Kullum abun da nake gudar ma kenan amma ko kaɗan bakaji, to yanzu wagari ya waya kenan, gashi kuma kasan Jibi ne bikin ranar zagayowar godiya ga abun Bauta Gargabilu, amma kuma babu abun da ka tanada, ko iccen da zaka ɗauka baka tanada ba, kuma kasan ko awane irin hali kake ciki babu wanda zai yarje maka sai ka futo kaima." Iyar bayi ta faɗa tana mai bin fatar jikin sa da tayi wani irin dabbara-dabbaran baƙi da ja yarce kasan wanda ya ƙone da idanu. Yayin da shiko Bir har lokacin yake lumshe da idanuwan sa ba tare da yace mata komai ba.
Hannu tasa ahaɓar zanin ta tana mai ciro wani ƙullin tsuma, tukun ta fara kwance sa bayan ta sake matso da ƙwaryar ruwan nan gaban ta.
Ƙullikan wasu tsummokaran ne har guda biyu acikin babban ƙullin.
Ɗaukar na farkon tayi ta fara kwance sa. Gishiri ne ya bayyana acikin sa, buɗe tafin hannun ta tayi tana mai tsiyaya gishirin da yawa akan sa, tukun ta juye sa acikin ruwan ƙwaryar, sannan ta sake kwance ɗayan ɗaurin wanda yake ɗauke da garin magani acikin sa.
Shima ɗibar sa tayi ta zuba acikin ruwan, kana ta sake ƙulle su tana mai mai dasu jikin haɓar zanin ta ta ɗaure, tukun ta sanya hannun ta cikin ruwan tana mai jujjuya sa.
Kana ta tsunduma kofin nan tana mai kamfato ruwan da shi, tukun ta juye sa ajikin Bir.
Rumtse idanuwan sa yayi da ƙarfi yana mai taune leɓen sa na ƙasa, sabo da yarce ruwan yake ratsa ciwukan dake jikin sa yana kwanciya.
"Ina mai roƙon ka da abun bauta Gargabilu ka taimake ni ka kuma taimaki kan ka futa daga harkar Gimbiya, muddin baso kake muyi kukan rashin ka ba nan kusa." Iyar bayi ta faɗa tana mai cigaba da watsa masa ruwan ajiki.
Sai da ta gama sanya masa ruwan ta tabbatar da ya taɓa ko ina na jikin sa, tukun ta miƙe tsaye tana mai gyara ɗaurin baƙin ƙyallen da yake aƙugun ta, kana ta kalle su tana mai faɗin. "Yanzu ba zama zakuyi ba, ku tashi ku kama Jarumi kutaya sa yo nasa itacen ɗaukar shima, dan ko muddin bakuyi hakan ba to ni nasan wannan azabar tayau ba komai bace akan wacce Boka mai Hutar Kasko zai sa ayimasa aranar Biki." Ta ƙarasa maganar tana mai juyawa ta doshi hanyar data biyo.
"Shin har sai zuwa wane lokaci ne zaki cikan alk'warin da kika d'aukar mun ne Iya?" Bir ya fad'a da k'arfi yana mai mik'ewa tsaye, tukun ya fara d'aga k'afafuwan sa yana mai dosar inda iyar bayi take. Yayin da ita kuma Iyar Bayi ta tsaya cak ai'nda take jikin ta na matuk'ar rawa ba tare data iya furta komai ba, tukun daga bisani ta fara waige- waige tana mai duba gabas da yamma, kudu da arewa, domin taga ko akwai wani wanda yaji furucin Bir bayan su.
Sai da ta tabbatar da babu wani mahaluk'i dake wurin bayan su, tukun ta juyo inda Bir yake takowa da d'an gyashi jikin ta na tsantsar karkarwa.
"Shin mene zai sanya kayi irin wannan furucin awuri irin wannan jarumi?" Iyar Bayi ta fad'a k'asa k'asa tana mai matsawa inda Bir yake ta dafa kafad'ar sa.
"To iya s.... "Shiiiit!" Iya ta fad'a tana mai d'ora yatsa akan baki tare da zaro idanuwa, jikin ta na tsantsar rawa, yayin da shi kuma Bir ya bita da idanu yana kallon ta, tukun daga bisani ta janye yatsar ta daga kan la'b'ban ta tana mai bud'e baki ahankali tace. "Muddin baso kake in bak'unci k'asa ba ayau, to na rok'eka da abun bauta Gargabilu ka temakeni karna sake jin makamancin furuci irin wannan anan wurin."
"Amm..." "A'a Jarumi kawai kayi abun da na sanya ku, ka tafi, ka tafi kuje kufara samo icci na." Cewar iyar bayi jikin ta na tsantsar kyarma.
Yayin da shi kuma Bir ya rumtse idanuwan sa da matuk'ar k'arfi tare da taune leb'en sa na k'asa, tukun ya juya yana mai fara d'aga k'afafuwan sa ya doshi inda ya baro ba tare da ya sake cewa komai ba.
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Iyar bayi ta saki tana mi dafe k'irjin ta da hannu, tukun itama ta juya cikin tsantsar sauri tana mai dosar inda ta futo, har lokacin kuma jikin ta bai bar kyarmar da yake yiba.
Acan b'angaren Gimbiya Tsamir kuwa cikin zafin rai ta damk'i kan macijiyar nan da ke karkad'a harshen ta bayan ta durk'ushe agaban ta tare da rumtse idanuwan ta da k'arfi.
Tukun daga bisani ta bud'e baki cikin kaushi tana mai fad'in. "Shin meke shirin faruwa dani ce Shairama? Wane laifi nayiwa abun bauta Gargabilu da har yake shirin hukunta ni ta wannan hanyar? Kamar ni! Kamar ni!! Ni Gimbiya Tasmir har zan yiwa wani can k'as-k'antanccen bawa hukunci asa na sake sa! Shin ina k'arfin iko na ya tafi ne? Me Baba yake nufi dani ce akan wancan k'ask'antaccen banzan mara galihu Shairma?" Ta fad'a da k'araji tana mai sakin kan macjiyar ta mik'ewa tsaye.
Taku ta farayi daga inda take zuwa gaba, sai da tayi taku ya kai biyar, tukun taja tsaya tana mai sakin wasu irin numfar-fashi, kana daga bisani ta juyo tana mai dawowa wurin yashin da ta cake takobin ta ta funcike ta da matuk'ar k'arfi.
Sake d'aga k'afafuwan ta tayi tana mai yin wurin da macijiya nan take akai.
Tana k'arasawa wurin ta zube gwiwoyin ta tare da cake Takobin da matuk'ar k'arfi ak'asa idanuwan ta akan macijiyar nan da take kallon ta, tukun daga bisani ta bud'e baki tana mai fad'in. "Ina mai rantsuwa da Gargabilu sai naga bayan sa Shairama, ina mai rantsuwa da gargabilu sai ya fuskanci azaba irin azabar da bai tab'a fuskantar makamanciyar taba aduniya tunda harya bud'e baki yace mun wace kalar azaba ce bai santa ba acikin BAK'AR MASARAUTA!
Zan masa azaba da ruwa, sannan kuma zan masa azaba da k'asa, kana kuma in masa azaba da huta muddin ban samu amsar tambaya ta daga bakin sa ba!
Zanyi amfani da ranar jibi wacce ta kasance ranar godiya gare ka abun bauta Gargabilu, wurin gana masa azaba mafi muni daga cikin azabobi na!
Tabbas ranar jibi zata zamto rana irin wacce baka tab'a yin taba agidan duniya k'ask'antacce! Tabbas ranar jibi zata kasance rana mafi k'uncin rana gareka gidan duniya, tunda har kasanya mahaifina yamun tsawa ayau! Daga rana ta jibi zan kawo k'arshen rashin kunyar ka ta hanyar gille sauran lalatacciyar rayuwar ka agidan duniya! Wannan alk'wari ne na d'aukarwa kaina, kuma nayi rantsuwa da ubangiji Gargabilu sai na cika sa Shairama kece sheda ta kuma!" Ta k'arasa maganar cikin k'araji, kana da matuk'ar sauti.
Tukun ta sake mik'ewa tsaye tana mai matsawa gaban ruwan nan ta kafesa da dara-daran idanuwan ta da suka koma jajajir dasu, sabo da b'acin rai, sannan ta k'ara bud'e baki tana mai fad'in. "Tabbas kome zai faru sai dai ya faru, danko bazan tab'a iya barin wannan lalataccen bawan yaci banza ba, shine na farko da aka fara samu acikin BAK'AR MASARAUTA! Dan haka nayi rantsuwa da Gargabilu bazan tab'a barin sa shi kansa yay k'arko ba balle har asamu na biyun sa agaba!" Ta k'arasa maganar da matuk'ar k'araji tana mai juyawa ta doshi wurin da takobin ta take acake gaban macijiyar nan. Hannu tasa tana mai funcikar ta daga cikin k'asa, tukun ta juya tana mai dosar inda dokin ta yake atsaye da matuk'ar sauri.
Tsalle ta buga adai dai lokacin da taje gaban sa tana mai hayewa kansa, tukun ta damik'i linzamin sa da hannu hagunta da matuk'ar k'arfi, kana ta mik'ar da takobin nan ahannun ta tana mai nuna macijiyar nan da ita, sannan ta bud'e baki cikin sauti tana mai fad'in. "Shairama!!!" Take awurin macijiyar ta b'ace bat kamar ba atab'a yin taba awurin, yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir ta saki linzamin dokin tana mai dukan cikin sa da matuk'ar k'arfi.
Haniniya dokin ya saki da k'arfi, tukun ya zabura da mugun gudu yana mai dosar hanyar daya biyo sukazo wurin.
*K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI*
*ASADULLAH PALACE.*
Ba zato ba tsammani yarima Asad ya jisa tujum acikin swiming pool din nan!
Yayin da ita kuma Billy ta sake damk'ar lips d'in sa da matuk'ar sauri tana tsotsar su tare da dannan tongue d'in ta cikin asalin bakin sa kamar mayya.
Ta fannin Yarima Asad kuwa damƙar gashin atach d'in dake kanta yayi da matuk'ar k'arfi yana mai ɗago da fuskar ta sama, bayan ya zame lips ɗin sa daga cikin bakin, yayin da ɗayan hannun nasa kuma yake dafe da ƙugunta yana mai kallon cikin idanuwan ta, kamar yacce itama take kallon nasa, tukun daga bisani ya fara matsar da fuskar sa yana mai dosar tata, tayar ce har kowanne daga cikin su yake jin dirar numfashin ɗan uwansa akan fuskar sa.
Cikin tsantsar shauƙin da Billy ta tsinci kanta aciki tayi wani irin lumshe idantuwa ta, tana mai jiran taji saukar lips ɗin sa akan nata, amma sai jitai ya sake damƙar gashin kanta yana mai ma.................✍
🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹
_*NA*_
UMAR FARUQ*D*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
*PAGE 06*
Yana mai masa wata irin cakuma, tukun daga bisani ya funcikesa da matuƙar ƙarfi yana mai hullata cikin ruwan, ji lake tunjum! Ƙarar faɗawar ta.
Wata irin gigitattar ƙara Billy ta saki sabo da azabar da taji ta ratsa har tsakiyar ƙwaƙwalwar ta asanadin fuzgar gashin kanta da yay, yayin da shi kuma ya juya ba tare da ya tsaya duban halin da take ciki ba yana mai kama ƙarfen dake manne jikin ramin ya futo waje.
Ƙarasawa yay gaban ɗan gadon nan da yake daga bakin ruwan yana mai sa hannu ya ɗauki wayar sa, tukun ya juya yana mai dosar haɗɗaɗen building ɗin dake cikin wurin hankali kwance.
Yayin da ita kuma Billy tayi suman tsaye daga cikin swimming pool ɗin ba tare da ta iya futowa ba, tana mai bin bayan sa da kallo, kafin daga bisani kuma wasu irin hawaye masu matuƙar gudu suka tsinke daga cikin idanuwan ta suna dira akan kuncin ta.
Sai da har taga shigewar sa duka, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta jiki asaɓule tana mai yowa bakin ruwan.
Wucewa tayi gaban gadon nan, tukun tasa hannu tana mai ɗaukar hand bag ɗin ta da wayar ta, banda ɗigar ruwa babu abun da jikin ta yake yi.
Juyawa tayi ɓarin da building ɗin da da Yarima Asad ya shiga tayi tana mai kafe haɗaɗɗiyar ƙofar dake wurin da idanuwan ta da suke tsiyayar hawaye har lokacin, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin kaushi tana mai faɗin. "Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Sai nasa kayi nadamar hulaƙanta ni da kake yi Prince Asad, sai nayi fatali da duk wani jiji da kai tare da izzar da ka, sai na maida kai bawa gareni mai mun bauta, sai na nuna maka bam-bancin dake tsakanin girman kujerar Gwamna da ta Sarki!
Zanyi amfani da ikona da matsayi na na ƴar Gwamana kuma ƴar gata wurin ganin na mallakeka Prince Asad, sannan aƙarshe in rabaka da duk wata ɗiya mace da ka kasance kana da kusanci da ita, domin ko an halliceka ne domin ni kaɗai Asad, an halliceka ne sabo da kazamto miji gareni ni kaɗai, dan haka babu tayarce za'ayi ka iya gujemun Prince Asad!
Wallahi dani kake wasan ne Prince, kai ka fara amma nice zan ƙarashe sa. Yarima Asad kake ɗan Sarki Abdallah jikan Sarki Ahmadu agarin Wasai, ni kuma Bilikisu Abubakar Sardauna nake ɗiyar Gwamnan Wasai, dan haka muzuba mugani ni da kai ɗan halak kafasa! Ta faɗa cikin kaushi tana mai taune leɓen ta na ƙasa da ƙarfi, kana ta janye idanuwan ta daga kan mofar tana mai juyawa ta doshi parkim space cikin sauri.
Bata damu da yarce ruwa ke ɗiga ajikin ta ba ta buɗe murfin motar tata tana mai faɗawa cikin ta, tukun tayi mata key tana mai lailaya kanta acikin wurin ta juya ta, kana ta take ta aɗari da ashirin tana mai dosar bakin get ɗin nan atsiyace.
Da gudu get man ɗin dake zaune abakin wurin ya miƙe yana mai wangale mata get ɗin, tukun ya kauce da sauri sabo da yarce yaga tana shirin bi takansa.
Gaba ɗaya ɗaukacin mutanen da suke aɗayan wurin nan na farko bin motar Billy sukayi da ido baki sake, sabo da yarce suka ga ta futo amugun tsiyace, anan ɗin ma tun kafin ta ƙaraso aka wangale mata get ɗin, tukun tazo ta huce tana mai hayewa kantiti aguje ba tare da ta tsaya duban hanya ba.
Acan cikin Masarautar Wasai kuwa, tun acikin fada lokacin da ake naɗi Babban Yaya yake ta ɗaga idanuwa yana mai wurga su awurare daban -daban domin ya hango ƙanin nasa. Amma sai dai har akai naɗi aka gama baiga ko Al'amin ba ballantana yasa ran ganin sa, hakan ko ba ƙaramun sosa masa rai yayi ba.
Koda aka gama naɗi mimmiƙewa akayi domin aje afara aiwatar da shagul gulan da aka shirya kamar yacce aka saba.
Sosai taro yay taro, wuri ya cika da manya manyan Sarakai, masu kuɗi, harma da Gwamnoni na garuruwa daban-daban, ko wanne da kalar shigar dake sanye ajikin sa.
Yayin da shi kuma Ciroma, wato Babban yaya yake sanye da wani ɗanyen farin yadi mai matuƙar taushi da haske, anyi masa ɗinkin doguwar riga tare da dogon wando, ɗauke yake da wata azababbiyar hula baƙa mai sirkin adon fari ajikin ta, yayin da daga saman hular kuma aka bita da naɗin farin rawanin da yayi matuƙar ƙarawa shigar tasa kyau, sai takalmin dake sanye aƙafar sa da ya kasance half cover shoe baƙi irin na Sarakai, yayin da tsintsiyar hannun sa kuma take ɗaure da wani ɗan ubansun agogon fata mai tsananin kyau, sai wata uwar baƙar Al'kyabba mai ɗauke da adon fari da take sanye ajikin sa tana ta faman walwali da ɗaukar ido.
Dogon mutum ne sosai kanar yacce Yarima Asad ya kasance dogo, sai dai shi kuma yayi biyun Yarima Asad ajiki, kamar yacce ya basa tazarar shekaru goma a haihuwa, domin ko shi ayanzu yana da shekara arba'in ne aduniya, tare da mata ɗaya da kuma yara huɗu, maza biyu mata biyu, yayin da shi kuma Yarima Asad yake da shekara talatin da ƴan watanni aduniya.
Kamar su ɗaya sak da Yarima Asad, bam-bancin su kawai shine shi Babban yaya bai kai Yarima Asad haske ba, duk da dai shima bai zamto baƙi ba, amma bayan wannan basu da wani bam-banci sai na shekaru, dan ko hatta da sajen dake ɗauke ahaɓar su duk iri ɗaya ne.
Tafe suke suna masu dosar inda dawakai suke, kasancewar yanzu ne lokacin da za'a fara hawa. Zagaye yake da maroƙa da zagage suna ta faman yi masa kirari tare da kaɗa-kaɗe da bushe-bushe, suna masu faɗin.
"Ciroma Sarki!
Ciroma Yarima!
Gagayya Ciroma!
Yarima damisan Ƴan Sarki!
Ɗan uban gabasawa!"
Sai wasu irin bushe-bushe da kaɗa-kaɗe kawai ke tashi awurin, yayin da shi kuma ko kaɗan baya tasu, sai aikin wurga idanuwa da yake tayi awurare daban daban dan yaga ta inda zai hango ƙanin nasa.
Dum! Dum!! Dum!!! Kakejin sautin ƙarar harbin bindigu na tashi da matuƙar ƙarfi, kasancewa tawowa da Sarki yayi tare da tawagar sa.
Zagaye yake atsakiyar Fadawa da Dogarai, hannuwan su ɗauke da wasu irin zura-zuran bulalai suna ta aikin buɗa hanya, tare da hankaɗe duk wani wanda ya kasance tsaye agaban su. Yayin da fadawa kuma ke aikin sakin kirari da matuƙar karfi yarce kasan zasu tsaga wurin, suna masu fadin.
"Takawarka lafiya garƙami wandon ƙarfe!
Lafiya jinjirin wata shakallo!
Lafiya jijjigen Addini!
Lafiya maida garin wani kango!
Lafiya darzaza amalen Sarakuna!
Lafiya bango madafar Bayi!
Lafiya mai kiran gabas da yamma ta amsa!
Lafiya numfashin duniya!
Lafiya ubangijin Bawa da Baiwa!
Sannu alafiya Alfanda bawanda!
Sannu alafiya Amalen Sarakuna!
Sannu Alafiya toya matsafa!
Lafiya mai ado da kurar yaƙi! Lafiya mai ado da kurar yaƙi!! Lafiya mai ado da kurar yaƙi!!!
Amin zulillah!
Amin kigon gabas maci yammawa!
Lafiya mai shari'ah daf da wuya!
Hifzullahi na Allah!
Kanzullahi bawanda!
Amincinka yafi ga linzami!
Ciki sannu alafiya uban gyayya!"
Haka suke ta aikin yi masa kirari da matuƙar ƙarfi suna masu dosar hanyar futa daga cikin fada. Yayin da maroƙa suma keta aikin sakin kiɗa da busa suna masu faɗin.
"Abdullahi jikan Abdullahi!
Majina gishirin yaro!
Dariyanka kukan yaro!
Tsawa mai ratsa gidan Arna!
Dan Ahmadu Autan Abdullahi!
Balaraben sarakuna jikan Abdullahi!
Ɗan Massalacin juma'a jikan Massalacin juma'a!"
Haka suma suke ta faɗe suna masu busa algaitu da kakaki. Yayin da shi kuma Sarki Abdallah yake tafe atsakiyar su jikin sa sanye da wata azababbar alkyabba ruwan ƙwai mai matuƙar kyau, sai kansa da yake ɗaure da farin rawanin da yayi matuƙar ƙara futo da kwarjinin sa. Shi kansa hulla idanuwan sa yake acikin jama'a duk da gaba ɗaya fadawa da dogarai sun zagaye sa, dan yaga ta inda zai hango ɗan nasa mafi soyuwa aransa.
Ahaka suka ƙarasa bakin ƙofa gaban wasu danƙara danƙaran dawakuna da suka gaji da jin Ado ajikin su. Tukun fadawan nan suka baza rigunan su suna masu sake rufe sarki tare da faɗin. "Bisa haikawa da alheri, bisa dafkawa, bisa maikawa."
Basu dena faɗe ba har sai da suka tabbatar da ya hau kan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 76