ga dogon lokaci ba ba tare da anyi sa ba, tunda har su yaran sun samu fahimtar juna." Suka sake faɗe fuskar su ɗauke da murmushi.
Yayin da shi kuma mai martaba ya sake gyara zaman sa akan kujera, kana daga bisani yayi gyaran murya, tukun ya buɗe baki cikin yanayin sa wanda baka isa kace fariciki yake ba ko kuwa akasin sa, yana mai faɗin. "Masha Allah, naji duk abun da aka tattauna akai, kuma nayi farin ciki da jin hakan, dan haka yanzu sai muyi fatan Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ya ƙarasa maganar da sakin murmushin yaƙe, domin kuwa haka kawai yaji bai wani amunta da zancen su mai girma Gwamna ba, na cewar Yarima Asad na san Bilkisu, gashi shi kuma aransa yana mai jin bazai taɓa iya yiwa ɗan nasa mafi soyuwa acikin ransa auren dole ba, sai dai kuma yasan tunda abun ya zamto ahaka to koda tinanin sa ya zamto gaskiya na Asad baya son yarinyar babu yarce zasuyi daga shi har Asad ɗin dole suyi haƙuri ayi, domin ko shi dai bazai iya buɗar baki yace bazai haɗa jini da mai girma Gwamna ba, hakan shine ya sanya gaba ɗaya yaji yana yin sa ya sauya, sannan kuma ya ƙudiri aniyar samun Asad da maganar dan yaji ta bakin sa ayau yau ba sai gobe ba.
Ta fannin Alhaji Saleh kuwa cikin farin ciki ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amin Amin."
Yayin da shi kuma mai girma Gwamna yake ta sakin murmushi ba tare da yace komai ba, duk da yarce yake son tun ɗazu ya buɗe baki yayi wa mai martaba bayanin abun da Yarima Asad yake yiwa Bilkisu tare da kashedin ajamasa kunne, sabo da jin da yay Alhaji saleh baiyi magana akan hakan ba, sai dai kuma da zarar ya kalli mai martaba danniyar ya buɗe baki yay masa magana akan hakan sai yaga ya masa wani irin kwarjini acikin idanuwa, hakan yasa yake ta ruƙon maganar acikin sa tun ɗazu duk da yarce yake son ya furta ta ba tare da yayin ba.
Sun ɗauki kimanin mintina talatin zuwa arba'in suna tattaunawa, tukun daga ƙarshe suka yiwa juna sallama su mai girma Gwamna suna masu miƙewa suka doshi hanyar waje.
*JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.*
Cikin sauri Gimbiya Haddiyal ta ƙarasa cikin ɗakin ta, direct ta doshi ƙofar ɗakin da kayan tsafin ta na gado suke aciki, tana mai zuwa ta buɗesa, tukun ta mayar da sandar nan tata awurin data ɗauke ta tana mai ɗaukar farin ƙyallan da ake rufe ta da shi ta lulluɓe ta, sannan ta sake juyawa cikin sayri tana mai fucewa daga cikin ɗakin, kana ta doshi hanyar da zata sadata da fallo dan taje ta sanya atatso madara.
"Barka da futowa yake kyakkyawar Gimbiya." Wata matashiyar Baiwa da take share cikin tafkeken falon ta faɗa tana mai ajiye tsintsiyar hannun ta ƙasa tare da zube giuwoyin ta aƙasa alokacin da Gimbiya Haddiya ta futo daga cikin ɗaki.
"Am, kiyi maza yanzu-yanzu ki tashi ki tafi wurin majiaɗin shanu, ki sanar da shi cewar ina buƙatar sabuwar madara cikin ƙwarya ukku kafun nan da giftawar da ƙiƙa talatin gaba." Gimbiya Haddiyal ta faɗa tana mai kallon Baiwar dake durƙushe agaban ta ba tare data amsa gaisuwar da tai mata ba.
Yayin da ita kuma baiwar ta miƙe da sauri tana mai nufar hanyar da zata sadata da waje.
Tukun ita kuma Gimbiya Haddiyal ta juya tana mai komawa cikin ɗakin ta.
Tana shiga ta huce gaban wata wadrobe ta ƙarfe mai azabar kyau ruwan zuma da take ajikin bangon ɗakin.
Hannu tasa ta buɗe ta tana mai zaro wani farin towel mai ɗauke da lallausan gashi jikin sa, tukun ta maida murfin ta rufe sa, kana ta juya tana mai dosar hanyar da zata sadata da bathroom ɗin da yake acikin bedroom ɗin nata ba tare da ta tsaya cire kayan jikin ta ba, gaba ɗaya tana komai ne cikin sauri duk da yarce ranta yake amatuƙar cunkushe da baƙin ciki.
*****
Misalin ƙarfe shaɗaya da rabi na safe motocin su Babban Yaya suka shigo cikin Masarautar Fulɗe, kasancewar gudu sukayi bana wasa ba, domin kuwa tafiyar kusan awa biyar ce har da rabi, amma su sukayi ta acikin awa biyu da ƴan mintinu.
Tunda suka shigo garin Yarima Asad yake aikin yamutsa fuska tare da wurga kallon ƙasƙanci acikin sa, domin kuwa gaba ɗaya ji yay bazai taɓa iya rayuwa acikin wannan bagidajen garin ba, wanda ya kasance babu wasu wayayyun mutane acikin sa.
Banda aikin yamutsa fuska da taɓe baki babu abun da yake yi, yayin da shi kuma Al'amin yake ta sakin zuba yana mai faɗin. "Agaskiya garin nan yayi, domin kuwa ba ƙaramar ni'ima Allah ya wadata su da ita ba, kaga fa yarce suke da wata irin daddaɗar iska, ga ruwaye da suke ta faman gudu, tabbas mutum na garin nan dole ma fatar jikin sa tai ta ƙare kyau akoda yaushe, domin kuwa daga gani su basu san mece rana bama." Ya faɗa idanuwan sa akan hanyar da suke wucewa yana mai kallon ta ta cikin glass.
Yayin da shi kuma Yarima Asad ya rumtse idanuwa yana mai jin tamkar ya mammake Al'amin dan takaicin furucin sa, sabo da shi kwata kwata baiga wani abu da ya birge sa acikin garin ba, sai zallar haushi da ya basa ma, domin kuwa ya fuskanci hatta da mutanen cikin sa kusan dukan su duk ƙauyawa ne.
Aƙarshe ma da ya gaji da jin surutun Al'amin earpiece ya zaro acikin aljihun sa yana mai sanya ta cikin kunnuwan sa ya doɗe su da ita.
Ahaka har suka ƙarasa cikin Masarautar Fulɗe wacce take cike da abubuwan burgewa da kyan gani acikin ta, sai dai ta fannin Asad kuma har yanzu bai ga abun da ya burge saba acikin Masarautar.
Tun daga bakin ƙofa wasu dogarawa suka tarbe su cikin tsantsar girmamawa, sanye suke da kayan fulani, hannuwan su kuma riƙe da sandina, daga nan kuma suka yi musu jagora zuwa fadar Lamiɗon Masarautar Fulɗe.
Kallo ɗaya Yarima Asad yayiwa mutanen nan da suka zo tarbar su, daga nan kuma ya ɗauke idanuwan sa akan su ba tare da ya sake kallon wani daga cikin suba, dan ko gaba ɗaya ƙyanƙyamin su ma yaji shi, sabo da suturar dake sanye ajikin su, wacce yayiwa laƙabi da ta mahaukata ayanzu daga kallo ɗaya da yayi musu acikin zuciyar sa.
Dasauri Babban Yayan su Gimbiya Haddiyal wanda ake kira da Jauron masarautar Fulɗe yazo ya tarbe su cikin tsantsar mutun tawa, tukun daga nan ya shige gaba suna masu dosar cikin fada da take ɗauke da kayan ado na fulani tako ina gadan gadan.
Sosai Masarautar tayi matuƙar birge Al'amin, tayarce har yake jin ina ma ace sai sun kwana biyu tukun zasu barta, yayin da shi kuma Yarima Asad yaji gaba ɗaya wurin ya gundure sa, kana ko kaɗan bai ga wani abun burgewa ba acikin sa sai zallar ƙauyanci da yake gani.
Iso akayi musu har gaban Lamiɗo da yake zaune akan wata irin kujerar Al'farma ta ƙarfe mai azabar kyau, sanye yake da kaya irin na fulani, amma na sarauta tare da Alkyabba wacce ta kasance ta fulani ɗauke ajikin sa, sai farin rawani da yake ɗaure akansa, farine tas da shi yarce kasan ataɓasa jini ya ɓullo, kamar yacce duka ƴaƴan sa suka kasance suma.
Yayin da gefe da gefen sa kuna da gaban sa mutanen fada suka kasance zaune awurin.
Zama su Babban yaya sukayi akan shimfiɗar kafet ɗin da take agaban su suna masu kwasar gaisuwa awurin Lamiɗo.
Cikin mutun taka da far'a ya amsa musu fuskar sa ɗauke da tsantsar annuri, sannan daga ƙarshe suka sake gabatar da abun da yake tafe da su.
Gyaran murya mai martaba Lamiɗo yayi, tukun ya furta munji komai kamar yacce kuka faɗa arubuce, dan haka yanzu kai Jauro ka tashi ka kai su wurin cin abinci, inyaso idan sun gama sun huta sai su dawo ayi ciniki." Ya faɗa yana mai kallon Babban ɗan sa wanda zai kai kusan shekaru arba'in aduniya.
Amsa masa yayi da tom shima, tukun ya miƙe suma su Babban Yaya da su Yarima Asad da yake ta faman yamutsa har lokacin suka take masa baya.
Suna futa waje Jauron Masarautar Fulɗe ya hangi ƙanin sa mai suna Habu, mai kimanin shekaru talatin aduniya, wato sa'an su Yarima Asad dai.
Ƙwalla masa kira yayi da ƙarfi, cikin sauri Habu ya ƙaraso wurin da suke yana mai faɗin. "Barkan ku da zuwa baƙi." Fuskar sa ɗauke da murmushi yana mai kallon su Yarima Asad.
Idan ka gansa kai bazaka taɓacewa ɗan nan cikin Masarautar bane, domin kuwa sosai yake awaye shima, kasancewa yayi karatun boko har matakin degree shi.
"Yawwa."
Babban yaya da Al'amin suka faɗa cikin far'ah, yayin da shi kuma Yarima Asad ya faɗa ƙasa ƙasa ba tare da ya kalle sa ba.
"Yawwa Habu ga abokai nan kaja su ku tafi cikin lambu, sannan ka tabbatar an samar musu abinci da madara yanzu yanzu"
"Tom shikenan Hamma." Habu ya faɗa yana mai sake miƙa musu hannu suka sake yin musabaha, tukun yace ku tawo muje ko.
Jerawa sukai suka tafi suna tafiya suna hira da shi da Al'amin cikin raha, yarce kasan sun san juna dama. Yayin da shi kuma Yarima Asad yayi shiru yana sauraran su kawai ba tare da yace komai ba, ahaka har suka ƙarasa cikin wani ni'imtaccen lamubu mai ɗauke da korayen ciyayi tare da sanyi acikin sa.
Direct sukayi kan wata shimfiɗar Al'farma ta fata da take ɗauke da tum-tum akan ta daga can nesa.
Tunda suka shigo masarautar Fulɗe Yarima Asad baiga wurin da ya burge saba sai wannan kaɗai, hakan yasa ya jujjuya yana mai kai idanuwan sa ko wane sashe dake cikin wurin, tukun ya maida idanuwan sa kan shimfiɗar da suka ƙarasa gaban ta yana mai cire takalman dake sanye aƙafar sa ya hau ya zauna, kamar yacce Al'amin da suke uwar hira da Habu suka zauna.
Kishingiɗa yayi jikin tum-tum ɗin dake gaban sa yana mai lumshe idanuwan sa ba tare da yace komai ba.
Kallon sa Habu yayi fuskar sa ɗauke da murmushi, tukun daga bisani ya buɗe bakin sa yana mai faɗin. "Shin wai kai ɗin Bebe ne amma ko?" Ya ƙarasa maganar cikin raha.
Wara idanuwa Yarima Asad yayi akansa yana mai sakar masa murmushin yaƙe, still ba tare da yace komai ba, yayin da shi kuma Al'amin ya buɗe baki yana mai faɗin. "Bebe ko kuma miskili ba."
Ya faɗa yana mai hullawa Yarima Asad da ya zaro wayar sa yana shafawa harara.
Yayin da shi kuma Habu ya saki dariya yana mai faɗin. "Any way, ga dai abinci nan yanzu kuci tukun sai acigaba da hirar."
Ya faɗa yana mai fara buɗe haɗaɗɗun kwanukan da suke jere akan tray.
Farfesun naman ciki ne dana kaji da suka gaji da haɗuwa suna ta faman tashin turiri da ƙamshi acikin kwanika biyu da suke daga farko, sai kuma wani haɗaɗɗen kwandon kaba da yake ɗauke da Tufa, Inibi, Ayaba, Lemo, acikin sa da matuƙar yawa.
Bubbuɗe kwanukan duka yayi yaga babu madara kwata- kwata awurin.
Hakan ne yasa sa miƙewa yana mai kallon su tare da faɗin. "So sorry dan Allah fa, ashe wai basu kawo madaraba, but please ku ɗan jirani yanzu bara naje naji dalilin da yasa ba akawo ba." Ya faɗa yana mai miƙewa ya juya ya tafi ba tare da ya tsaya jin ta bakin su ba.
Bai tsaya ako ina ba sai acikin ɗakin Haddiyal da take zaune agaban madubi tana mutsikka mai afatar ta.
Da sauri ta juyo bayan ta tana mai kai idanuwan ta bakin ƙofa sabo da motsin da taji.
"Mai ya hana kisa akaiwa baƙi madara amatsayin ki na shugabar shanu, bayan kuma nasan an sanar miki da zuwan su tun kafin yau?" Ya faɗa yana mai kafeta da idanuwan sa.
"Kayi hakuri dan Allah Hamma, wallahi na sha'afa ne, amma nasa atatso ta tun ɗazu, kuma yanzu haka nasan an gama ma ƙila ma sun shigo da ita, dan haka bara na sanya kaya sai naje nasa akai madarar." Ta faɗa tana mai miƙewa ta doshi gaban wadrobe ɗin ta.
"A'a kawai ke yanzu abun da za'ayi shine, idan kin sa kayan kije ki ɗauki madarar ki kaita lambun gaban sa, ni kuma yanzu bara naje na ɗauka na kai lambun yamma inda su Hamma Jauro suke, domin kuwa har baƙin sunzo tun ɗazu gashi ba akai musu madara ba." Ya faɗa yana mai juyawa.
"Tom shikenan Hamma Habu." Gimbiya Haddiyal ta faɗa tana mai sanya hannun ta acikin wadrobe ɗin ta.
"Ki fa yi sauri, sabo da sun riga sunzo harma sun zauna." Ya faɗa yana mai ƙarasa fucewa daga cikin ɗakin.
Yayin da ita kuma ta fara sanya kayan da ta zaro farare na fulani, amma bawai na sarauta ba cikin sauri.
Tukun ta ƙarasa gaban mudubi tana mai kama uban gashin kanta da yake baƙiƙƙirin atsafe ta tufke sa wuri ɗaya, sannan ta ɗauki man leɓe kaɗai ta goga akan pink lips ɗin ta.
Sosai tayi matuƙar kyau yarce kasan sarauniyar kyawu ta duniya, duk dama ba wata kwalliya ce ke ɗauke afuskar ta ba, yayin da gashin kanta da ta tufke sa kuma ya zubo har gadon bayan ta ya kwanta.
Cikin sauri ta juya tana mai kama hanyar da zata sadata da waje, bayan tasanya wani plat shoe aƙafar ta ba tare data ɗaura ɗankwali ba.
*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*
Ahaka suka cigaba da shigowa cikin filin kafaɗun su ɗauke da iccina masu matuƙar yawa, suna masu dosar wurin da abun bauta Gargabilu yake.
Ahaka har akazo kan Bir da ya shigo shima kafaɗar da ɗauke da nasa iccinan da baya da baya, yana mai faman ɗirkar rawa daga shi sai farin ƙyalle ɗaure aƙugun sa.
Wani irin murmushi Gimbiya Tasmir ta saki alokacin da taga shigowar Bir cikin filin, tana mai cije leɓen ta na ƙasa.
Yayin da su kuma bayin nan daga mazan su har matan su suka cigaba da nufar wurin da abun bauta Gargabilu yake suna masu faɗin. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Da matuƙar ƙarfi.
Duk wanda yaje gaban daɓen da abun bauta Gargabilu yake akai durƙusawa yake kansa sun kuye aƙasa yana mai faɗin. "Godiya ta tabbata gareka ubangjin mu daka nuna mana wannan rana." Sanna su sake yin juyi agaban sa suyi rawa iyakar rawa, tukun su huce zuwa cikin filin nan suna masu dosar inda Sarki da Iyalan sa suke, domin su kai gaisuwa, har lokacin kuma hannuwan su suna riƙe da kaskwayen hutar nan ne.
Dasari Gimbiya Tasmir ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take alokacin da taga bayin nan sun fara doso hurin da suke, kamar yacce yayin ta biyu maza suma suka miƙe.
Tukun suka doshi wurin da wasu irin zura-zuran bulalai suke masu matuƙar tsayi da kauri cikin wani ruwa, suna masu sa hannu suka ɗauke su, sannan suka juyo suna masu dawowa tsakiyar filin nan ta ɓarin da bayi maza suke tawowa suka tsaya cirki cirko.
Ahaka har bayin nan suka fara isowa zuwa wurin da suke.
Ɗaga bulalun nan suka farayi cikin tsantsar ƙarfi, suna masu antaya musu ita agadon bayan su da ya kasance ko riga babu akansa!
Ana zubawa mutum bulalar yake rumtse idanuwan sa da ƙarfi jikin sa na tsamtsar karkarwa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin ƙaraji yana mai faɗin. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!! Godiya muke!"
Sannan ya huce gaba, shima ɗayan da yake agaba ya sake yi masa irin wacce na gaban sa yay masa, kana su huce gaba inda Gimbiya Tasmir take tsaye itama ta yi musu kamar yacce yayin ta sukai musu ba tare da tausayi ba ko kaɗan aranta, ahaka har aka ƙaraso kan Bir da yake ɗauke da iyayen iccina akan sa, jikin sa na rawa da ɗigar gumi.
Haka duk yayyen Gimbiya Tasmir suka masa bulalar nan kamar yacce suka yiwa duk waƴan da suka zo kafin shi, sannan ya huce gaba wurin da Gimbiya Tasmir take idanuwan sa durƙushe aƙasa, aƙoƙarin sa na ganin ya cikawa Iya alƙawarin da ya ɗaukar mata na bazai kalli Gimbiya ba, duk da kuwa yarce yake jin wani irin abu na fusgarsa akan ta, amma ahaka ya daure ba tare da ya ɗago ya kalle taba, ahaka har ya ƙarasa gaban ta.
Yayin da ita kuma tayi wani irin rumtse ido da matuƙar ƙarfi tana mai yin wasu irin surutai ahankali, bayan ta dunƙule tafin hannun ta, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan nata tare da tafin hannun nata tana mai kaisa kan bulalar dake riƙe ahannun ta ta shafeta da shi.
Take awurin bulalar ta ƙara wata irin miƙewa tare da banƙarawa tana motsi yarce kasan abu mai rai, tukun Gimbiya Tasmir ta ɗaga ta da matuƙar ƙarfi bayan ta cije leɓen ta na ƙasa idanuwan ta akan Bir, tana mai zambaɗa masa ita agadon baya!
Da ƙarfi ya rumtse idanuwan sa jikin sa na tsantsar rawa da karkarawa, sabo da tsantsar azabar da yaji ta ratsa jikin sa wacce bai taɓa jin makamanciyar ta ba, yayin da jini kuma yayi wani irin tsartuwa daga cikin jikin sa yana mai tsalle aƙasa.
"Gargabilu! Gargab..." Maganar ta ɗauke daga cikin bakin yana mai sakin ihu lasa-ƙasa, tayarce ya zamto ita kaɗai taji sabo da yarce ta ƙara zambaɗa masa bulalar agadon bayan sa!
Wani irin feshin jini jikin sa ya sake futarwa yarce kasan wanda aka tsaga da reza!
Tukun daga bisani ya ɗago kansa amatuƙar firgice yana mai watsa manya-manyan idanuwan sa cikin na Gimbiya Tasmir.
Ƙara ɗaga bulalar tayi da iyakacin ƙarfin ta tana mai sakar masa ita asaitin wuyan sa, tare da sakar masa wani irin murmushin mugun ta.
Amma amai-makon taji yayi ihu kamar yacce yayi ɗauzu sai kawai taga ya dake yana mai sake watsa ƙwayoyin idanuwan sa da suka canza launi daga fari zuwa ja cikin nata, tare da sakar mata wani irin shegen murmushi shima, tukun daga bisani ya lumshe idanuwan sa yana zaro harshen sa ahankali ya lashi gefen bakin sa da shi, sannan ya sake buɗe idanuwan sa akan ta yana mai sake jifan ta da kyakkyawan murmushin sa!
Wani irin baƙin ciki ne taji yazo ya caki zuciyar ta da matuƙar ƙarfi, take awurin kuwa ranta yayi matuƙar ɓaci, tayarce har idanuwan ta suka fara canza launi daga fari zuwa ja, tukun daga bisani ta rumtse tafin hannun ta tare da rufe idanuwan ta tana mai buɗe baki tace. "Rai Rai Rai Buuu Hooo Reee!" Kana ta buɗe sa tana mai watsa masa wasu abubuwa da suka bayyana acikin tafin hannun nata akan jikin sa tare da yin gefe da shi.
Take ya fara yin wani irin layi awurin yana mai shirin zubar da iccinan da suke ɗauke akafaɗun sa, tukun daga bisani ya fara tafiya adurƙushe cikin tsantsar azabar dake ratsa jikin sa yana mai fucewa daga cikin filin ya doshi wata hanya can daban, har lokacin ƙafadar sa ɗauke da iccinan yana layi, ganin hakan da Gimbiya Tasmir tayi ne ya sanya ta juyawa itama cikin tsantsar ɓacin rai tana mai nufar hanyar da yabi gadan-gadan!
*ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.*
Tana futa daga cikin babban falon nasu taci karo da wata baiwa, hannun ta ɗauke da wata haɗaɗɗiyar ƙwarya wacce take rufe da fai-fan kaba tare da ludayin duma har guda biyu akan ta.
Dasauri Baiwar taja baya tana mai faɗin. "Tuba nake ranki ya daɗe, ban san da zuwan ki ba shiya sa na sanyo kaina ciki."
Hannu kawai ta miƙa mata tana mai karɓar ƙwaryar ba tare da ta tanka mata ba, tukun ta juya tana mai dosar hanyar da zata sadata da lambun gabas.
Tafiya take iska na kaɗa jikin ta, tayarce har gashin ta yake reto agadon bayan ta, sai dai kuma yau ɗin gaba ɗaya bata jin daɗin yana yin garin ko kaɗan, sabo da yarce take cikin tsantsar baƙin ciki, wanda ba komai ne yasan ya ta cikin sa ba sai zuwan Yariman Yamma jiya wurin ta, da kuma mafarkin ta na yau, tare da abun da ta gani alokacin da tayi bincike.
Gaba dayan ta jinta take asaɓule yarce kasan babu laka ajikin ta, ahaka har ta ɓulla cikin lambun gabas ba tare da tasan ta shigo sa bama, sabo da yare tayi nisa aduniyar tinanin hanyar zatabi wacce zata sadata da Giɗaɗon ta.
Afannin su Yarima Asad suma dukan su babu wanda ya lura da shigowar ta wurin, domin kuwa shi Al'amin farfesun naman cikin nan kawai yake ci yana lumshe idanuwan sa, yayin da shi kuma Yarima Asad har lokacin kansa yake durƙushe idanuwan sa akan wayar sa da yake aikin shafawa.
Tafiyar ta ta cigaba dayi cikin sanyi ba tare da tasan taƙamai mai cikin wurin da take bama, ahaka har ta ƙaraso gab da shimfiɗar da suke bata lura da suba, kamar yacce suma ɗin babu wanda ya lura da ita.
"Ashhh!" Ta faɗa da ɗan sauti cikin zazzaƙar muryar ta, sabo da yarce taji tayi tuntuɓe da wani abu wanda batasan ko menene shi ba, ga kuma yarce ƙwaryar madarar da take ɗauke ahannun ta mai ɗumi ta suɓuce daga kan hannun nata duka.
Atare dukan su suka ɗago kawunan su, shi Yarima Asad cikin tsantsar zafi da ƙuna rai, sabo da yarce ta kifo masa ƙwaryar madara akan duka cinyar sa, yayin da ita kuma ta ɗago domin taga abun da ya tokare ta ta faɗi, suna masu sanya ƙwayoyin idanuwan su cikin na juna!
Ƙurr sukayiwa juna da ido ba tare da wani ya iya ƙiftawa acikin su ba, barin ma Yarima Asad da gaba ɗaya yanayin sa ya sauya, tayarce har idanuwan sa suka farayin ja, yayin da ita kuma take kallon sa tana mai jin wata irin tsanar sa da haushin sa na lulluɓe ilahirin jiki da ruhinta, wacce bata san dalilin taba.
Ahankali ya janye idanuwan sa daga kan nata yana mai mayar dasu zuwa kan jikin sa da yayi faca-faca da madarar shanu, tukun daga bisani ya sake ɗago su yana mai sake kafeta da su, kamar yacce har lokacin itama take kallon sa cikin wani irin yana yi, yayin da shi kuma Al'amin ya saki baki tare da ajiye naman dake hannun sa yana mai aikin kallon wannan, sannan ya koma ya kalli wannan ba tare da ya iya furta komai ba!
*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*
Gaban wani tafkeken dutse Bir ya watsar da iccinan, yana mai komawa jikin sa daga gefe ya durƙushe aƙasa tare da rumtse idanuwan sa da tsantsar ƙarfi.
"Shin ka shirya faɗamun amsar tambaya ta ayau, ko kuwa har yanzu taurin kan naka bai ƙare ba ƙasƙantaccen Bawa mara galihu!"
Sautin muryar ta ya daki dodon kunnen sa ba tare da yay zaton jin saba.
Take awurin kuwa yaji wata irin jarumta ta zomasa agaba ɗaya ilahirin jikin sa.
Ahankali ya fara ɗago ƙwayar idanuwan sa yana mai sauke su akan fuskar ta, tukun daga bisani ya mayar dasu zuwa kan ɗan ƙaramin bakin ta da take futar da munanan kalamai akan sa daga cikin sa.
Wani irin abu yaji yana fuzgar sa zuwa gare ta wanda bai taɓa jin makamancin sa ba, hakan ne yasa ya sake kafe ɗan ƙaramin bakin ta da idanuwan sa yana mai cigaba da kallon yarce take motsa su, tare da yarce jajayen laɓɓan dake akan su suke futar da ƙyallin man leɓen da aka shafa musu alokacin da ake mata kwalliya.
Ko kaɗan bai san lokacin da ya fara yunƙurin miƙewa ba, sai dai kawai jin sa da yayi tsaye akan ƙafafuwan sa, sabo da yarce yake jin wani irin abu na fuzgar sa zuwa gare ta, ta sanadin jajayen laɓɓan ta da yake kallo.
Ahankali ya fara ɗaga ƙafafuwan sa da suke tsartuwa jini yana mai dosar inda take.
Yayin da ita kuma ta kafe sa da idanuwa tana mai yin shiru dan taga abun da zai aikata da ya miƙe yayo kanta
Ganin da tayi yana gab da haɗe jikin ta da nashi ne ya sanya ta fara ja da baya da baya ba tare da tasan lokacin da ta fara yin hakan ba tana mai kallon cikin idanuwan sa.
Yayin da shima ya cigaba da biyo ta har lokacin idanuwan sa ƙur akan laɓɓan ta, ahaka har ta ƙarasa jikin bango.
Cigaba da matsawa yayi gare ta gadan -gadan.
Dasauri ta kalle sa tun daga saman sa har zuwa ƙasa, tukun ta sake sauke idanuwan ta akan faffaɗan ƙirjin sa da yake cike da yalwatacce gashi akan sa,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 76