Share this page
buɗe baki cikin daddaɗar muryar ta tana mai faɗin. "Yau dai gani gaban ka Giɗaɗo am, ubangijin shanu da mutane ya yayin sanadin haɗuwar mu da juna yau. Ta ƙarasa furucin cikin wani irin shauƙi wanda bata taɓa tsintar kanta amakamancin sa ba, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Tabbas yau ɗin ta kasance rana ta musamman gareni ni Gimbiya Haddiyal, yau ɗin ta zamto rana ta daban daga cikin ranakun da nayi arayuwa ta, dan haka juyo ka ganni na ganka Giɗaɗo am, juyo gani masoyi na, juyo kayi arba da wacce aka hallita domin kai, juyo kaga kyakkyawar hallitar da ta daɗe tana tsumayin ganin ka." Ta faɗa fuskar ta ɗauke da murmushi, yayin da shi kuma yayi shiru ba tare da yace komai ba, sai tsayawa da yayi da busar da yake yi. Sake gyara tsayuwa tayi tana mai ɗorawa da faɗin. "Ka sani na soka fiye da kowa da komai dake cikin duniyar nan, na soka kuma ina kan sonka fiye da yarce nake son kaina Giɗaɗo am! Ka sani kai ɗin nawa ne ni kaɗai kamar yacce na kasance taka kai kaɗai kaima, dan haka juyo ka ganni na ganka masoyi na!" Ta ƙarasa maganar still fuskarta ɗauke da tsantsar murmushi. Ahankali shima ya fara juyowa gare ta fuskar sa ɗauke da tsadadden murmushin sa da yayi matuƙar ƙara masa kyau. Kallon ta ya farayi yana mai jifan ta da murmushin sa ba tare da yace mata komai ba. Yayin da ita kuma ta lumshe kyawawan idanuwan ta tana mai cigaba da sakin murmushi, tukun daga bisani ta fara buɗesu ahankali-ahankali, tana mai jin sun nata wani irin nauyi, sai dai kuma suna gama buɗuwa amai-makon taga Giɗaɗo am ɗin ta sai kawai tayi arba da fillown da ta ɗora kanta akan sa tun kafin tayi bacci! Zumbur ta miƙe zaune daga kwancen da ta ka tana mai ɗaukar tafin hannun ta ta dafe goshin ta da shi cikin tsantsar takaici da haushi, sabo da fahimtar da tayi na duk abun da ya faru ba gaske bane ba mafarki ne irin wanda ta saba yin sa akoda yaushe tayi. Ta ɗauki kimanin mintina biyar ahaka tana mai cizon leɓen ta na ƙasa, tukun daga bisani ta janye hanun nata daga kan goshin ta tana mai matsawa bakin gadon tare da zura ƙafafuwan ta ƙasa. Sannan ta miƙe tsaya tana mai yin taku biyu daga inda take, tukun taja ta tsaya tana mai rumtse idanuwan ta da ƙarfi, kana daga bisani ta buɗe su tana mai faɗin. "Wato idan na fahimci dai dai, wannan mafarkin na nufin sandar tsafi na ta gado ce zata nuna mu hanyar da zanbi in gano ka Giɗaɗo am kenan." Ta ƙarasa maganar tana mai girgza kanta tare da sakin murmushi, tukun ta cigaba da ɗaga ƙafafuwan ta cikin kuzari tana mai dosar wani ɗan ƙaramin ɗaki da yake acikin ɗakin baccin nata. Hannu tasa tana mai janyo ƙofar dake wurin, tukun ta danna kanta zuwa cikin ɗakin. Ɗan ƙaramin ɗaki ne sosai, domin ko ko mutum ɗaya bazai ɗauka ba da sunan kwanciya acikin sa. Ɗauke yake da wasu kayan kari-kitai kala kala acikin sa, sai kuma wata doguwar sanda irin ta fulani da take jingine ajikin bango an yafa mata wani farin ƙyalle akan ta. Hannu tasa tana mai janye ƙyallen dake kan sandar, sannan ta damƙe ta cikin tafin hannun ta na hagu da matuƙar ƙarfi, tukun ta ɗago ta tana mai juyowa tayo waje da ita. Hannun daman ta ta sanya ta rufe ƙofar ɗakin da shi, tukun ta juyo tana mai dosar wata ƙofa dake manne jikin bangon ɗakin gadan -gadan. Buɗe ƙofar tayi itama, kana ta zura kanta tana mai dosar cikin wurin. Tafkeken filine mai matuƙar girma da faɗi ya bayyana, ashe wai nan ɗin ma hanya ce wacce take sadar da mutum wani shashi na daga cikin sashikan dake cikin gidan cikin sauƙi. Ɗaukar sandar nan tayi tana mai rataye ta akan kafaɗar ta, tukun ta fara ɗaga ƙafa cikin sauri tana mai dosar wata hanya. Sai da tayi tafiya mai ɗan nisa daga cikin ɗakin ta data futo, kana ta bayyana gaban wani tafkeken farin ruwa wanda ko ƙarshen sa ba ahange. Tsaye tayi agaban sa tana mai rumtse idanuwan ta da matuƙar ƙarfi, tukun ta fara ɗaga laɓɓan ta cikin kakkausar murya wacce batai kama da tata ba tana mai faɗin. Zaibaaaa!!!" Tukun ta ɗaga sandar nan tana mai bugata acikin ruwan da matuƙar ƙarfi, kana ta sake rumtse idanuwan tana mai sake faɗar kalmar Zaiba da matuƙar ƙaraji, tukun ta wara idanuwan nata tana mai kaisu kan ruwan nan gaba ɗaya, sai dai kuma me, take awurin taga gaba ɗaya kalar ruwa na sauya daga farin da yake zuwa baƙiƙƙirin yana wani irin tsalle. Dasauri taja baya tana mai girgiza kai tare da sakin sandar ta aƙasa, tukun daga bisani wasu irin hawaye masu matuƙar gudu suka ɓalle daga cikin idanuwan ta suna dira akan kuncin ta. Ba ta ita ta tsaya da ja da bayan da take ba har sai da ta jita jikin wata tafkekiyar bishiyar ɗorawa, tukun ta jingina da ita tana mai buɗe baki cikin kuka tace. "Shin me yasa irin hakan ke faruwa akowa ne lokaci ne? Shin ita ɗin ƴar gidan uban wace da har take mun katanga da ganin ka Giɗaɗo am? Nayi iya yina, nayi duk abun da zanyi domin na sameka amma duk abanza. Shin wane dalili ne ya sanya akowane lokaci ruwan ke canzawa daga kalar sa zuwa Baƙar kala." Ta faɗa tana mai ɗagowa daga jikin bishiyar da ta jngina, tukun ta farayin taku daga inda take tana mai komawa wurin ruwan nan da taga yana juyawa yana komawa asalin kalar sa. Tsugunnawa tayi awurin da ta yarda sandar tsafin ta tana mai ɗaukar ta ta riƙe acikin tafin hannun ta, tukun ta ƙurawa ruwan nan idanuwa tana mai ɗaure fuskar ta tamau, kana daga bisani ta buɗe baki cikin wata irin kakkausar murya tana mai faɗin. "Ina mai rantsuwa da ubanginin da yay ruwan dake cikin wurin na tare da bishiyun da suke cikin sa sai na tagyaraya ki ko ke ɗin wacece kuwa, tunda har kike ƙoƙarin shiga tsakanina da Giɗaɗo am, domin kuwa an hallice sane domin ni kaɗai badan wata ba, dan haka Wallahi tallahi sai na sanya ki kiny nadamar sanin sa da kikayi arayuwa, domin ko bincike na ya fahimtar dani cewar yana tare da wata ɗiya mace ce bani ba, bayan kuma gaba ɗayan sa anhallice sane domin mukasance atare mu biyu kawai." Ta ƙarasa maganar tana mai sake rumtse idanuwna ta zuciyar na tsantsar ƙuna da ciwo, tukun daga bisani ta warasu da sauri tana mai ɗora hannun ta akan goshin ta ta dafe sa, sabo da tino saƙon mahaifin ta da aka sanar da ita na cewar ta sanya asamar da madara da kayan itatuwa, sabo da baƙi da zasuyi yau daga Masarautar Wasai ta cikin jahar wasai, gashi kuma gaba ɗaya ta manta bata sanya an tatso madarar ba sai yanzu kawai abun ya faɗo mata. Hakan yasa ta janye hannun nata daga kan goshin ta tana mai fara ɗaga ƙafafuwan ta ta doshi hanyar da ta biyo cikin sauri, hannun ta riƙe da sandar ta domin taje ta sanya asamar da madara kafin lokacin zuwan baƙin yayi. *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Misalin ƙarfe tara dai dai na safe tawagar Sarki Barbaru tare da iyalan sa suka doso cikin filin bikin da yake cike maƙil da jama'a. Banda sautin kiɗa da bushe-bushe babu abun da ake ji yana tashi awurin. Sanya yake da wa..................✍ 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 https://chat.whatsapp.com/BhlmHQbDexzCA2fi7K6Jtu _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 10* Sanye da wasu jibga-jibgan riguna ajikin sa, yayin da ƙafafuwan sa kuma suke sanye cikin wani irin halp cover takalmi irin na sarakai mai azabar kyau, fuskar sa kuma zane take da tambarin masarautar tasu. Sai Iyalan sa kuma da suke daga gefen sa sun sanya sa atsakiya. Ɓarin daman sa da hagun sa matan sane biyu suma cikin shigar su ta alfarma, sai daga bayan su kuma Gimbiya Tasmir ce sanye da wata doguwar riga mai azabar kyau data futar da surar jikin ta tana jan ƙasa sosai, sai daga bayan ta kuma Yayyan tane maza guda ukku, suma dukan su sanye da shigar alfarma tare da alkyabba yafe asaman jikin su. Gaba ɗayan su babu wata alamun rahama tattare da fuskar su. Yayin da wasu irin danƙara danƙaran mutane da suke sanye da wani baƙin gajeran wando bako riguna ajikin su, hannun su riƙe da wasu irin zura zuran bulallai sukayi musu ƙawanya, gaba ɗaya jikin su zane yake da tambarin masarautar wanda akayi sa da baƙin fenti. Tafe suke cikin takun su wanda shi kaɗai ke hautsina cikin mutanen da suke ƙarƙashin mulkin su, suna masu dosar ƙarshen filin nan inda yake jere da kayan ƙawa tare da wasu irin azababbun kujeru masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Kai tsaye suka fara zarcewa tsakiyar filin, suna masu tsayawa daga gaban tafkeken daɓen da abun bauta Gargabilu yake akai. Yayin da dakarun nan kuma dukan su suka zube wanwar aƙasa suna masu yin ribda ciki, tukun su kuma tawagar slSarki Barbaru suka juya baya dukan su, kana suka fara ɗaga ƙafafuwan su suna masu fara taka matattakalar da zata sada su da saman daɓen nan da baya da baya, kawunan su durƙushe aƙasa. Ahaka har suka ƙarasa wurin da abun bauta Gargabilu yake, tukun suka zube wanwar aƙasa gaba ɗayan su hatta da shi Sarki, suna masu rumtse idanuwan su tare da buɗe bakunan su atare suna faɗin. "Godiya gare ka yakai abun bauta Gargabilu, godiya gareka ya kai jagoran rayuwar mu, godiya gareka yakai madubun dubawar mu." Kana sukai shiru dukan su aduk lokaci ɗaya, tukun daga bisani suka buɗe idanuwan su akan abun bautar tasu. Sannan suka ɗora da faɗin. "Haska mana gaban mu yakai jagoran mu, godiya muke gareka da ka sake mai-maita mana wannan rana mai albarka." Suka ƙarasa faɗe suna masu mimmiƙewa tsaye daga kwancen da suke. Tukun Sarki Barbaru ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai ƙarasawa kusa da abun bauta Gargabilu, sannan ya sanya hannun sa ɗaya acikin aljihun alkyabbar dake jikin sa. Wata irin haɗaɗɗiyar sarƙar gwal ya zaro wacce take sarƙe da fulawoyi ajikin ta, tukun ya ɗan durƙusa agaban abun bauta Gargabilu yana nai sanya masa sarƙar awuyan sa, kana daga bisani ya ɗago yana mai haɗe tafukan hannayen sa biyu ya ɗora su akan ƙirjin sa, tukun ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Godiya muke ubangijin mu maji ƙanmu." Sannan ya juya yana mai komawa wurin da ya baro, tukun matan sa guda biyu suma suka tawo atare suna masu yin kamar yacce mijin nasu yayi, tare da ajiyewa gunkin nasu kyaututtuka, kana suka juya suka koma suma. Haka duka Iyalan nasa suka dinga zuwa wurin abun bautar tasu suna gaishe sa tare da basa kyaututtuka, kana su koma wurin da suke ahaka har kowa yaje. Tukun suka juya da baya da baya suna masu dosar hanyar matattakalar nan, domin su sauka daga kan daɓen. Acan gefen daɓen kuma daga ƙasan sa wani tsohon mutum ne tukuf zaune akan wata shimfiɗa mara kyan gani, daga shi sai ɗan guntun ƙyalle ɗaure aƙugun sa bako riga ajikin sa. Yayin da gefe da gefen sa kuma aka ajiye wasu kaskwayen wuta, ya zamto atsakiyar su suna ta faman bal-bala da huta. Daga gaban sa kuwa akan shimfiɗar da yake wasu irin karikitai ne akan ta kala-kaka, kai ataƙaice dai gaba ɗayan sa basa da kyan gani ko kaɗan, domin kuwa idan mutum ya kalle sa har dai ba sanin ko waye shi yayi ba babu abun da zai hana ya kirasa da mahaukaci tuburan, sabo da yarce jikin sa yake ɗauke da zanen tambarin Baƙar Masarauta ta ko ina, ga kuma wasu irin layoyi da suke rataye awuyan sa, da hannuwan sa harma da ƙafafuwan sa. BOKA MAI HUTAR KASKO KENAN. Suna sauka daga kan daɓen nan suka tsaya cak a'inda suke, yayin da su kuma dakarun nan da suka zuzzube aƙasa suka miƙe da sauri dukan su suna masu fara tafiya da baya da baya, ahaka har suka koma bayan su. Sannan Sarki Barbaru ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai yin gaba, kana suma Iyalan nasa suka bisa suna masu dosar wurin da kujerun nan suke. Suna ƙarasawa gaban kujerun gaba ɗaya dakarun nan suka yi sauri suka tsaya daga gaban su, suna masu juya musu baya tare dayi musu rumfa, ya zamto sun rufe su bamai ganin su kwata -kwata, tukun sarki Barbaru ya zauna kan wannan azababbiyar kujerar da ta gaji da haɗuwa, yana mai kamewa wuri ɗaya, kana suma matan sa suka zauna akujerun da suke ajiye jikin wacce ya zauna, tukun ƴaƴan sa maza guda ukku suka zauna, akan waƴan da suke ajiye agefen wacce Iyayen nasu suke akai, sai wata ƴar ƙarama kuma mai azabar kyau, wacce aka ajiye ta daga gaban na iyayen nasu hatta da ta shi sarki Barbaru, da take ɗauke da fulawoyi akan ta, Gimbiya Tasmira ta doshi inda take cikin takun ta wanda yake futar da sautin ƙarar sarƙoƙin gwal ɗin da suke maƙale ajikin ƙafar ta aduk lokacin da ta ɗaga ta ta dire aƙasa. Tsaye tai agaban ta tana mai lumshe idanuwan ta, wani irin nishaɗi take ji aranta wanda ta gaza misalta kalar sa, badan komai ba kuwa sai dan kawai ganin da take yauce ranar da zata yiwa ƙasƙantaccen fitsararren bawan can azaba mai raɗaɗi, agaban dubban jama'ar da suke cikin filin nan, kasancewar aduk rana irin wannan dama su Ƴaƴan Sarki suna da ikon yin duk yarce suka so suyi akan kowane Bawa, sabo da girman ranar agare su, domin kuwa azamanin baya da ya shuɗe, a'irin wannan ranar ce ake kashe duk wani mutum da ya can-can-ci kisa acikin Baƙar Masarauta gaban dubban jama'a. Sai da ta ɗauki kimanin mintina kusan huɗu lumse da idanuwna ta, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai komawa ta ɗaure fuska tamau, duk da dama can ɗin ba dariya take ba, sai dai kuma baza'a ce fuskar ta ɗaure take ba, sannan ta zauna akan wannan haɗaɗɗiyar kujerar tana mai ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya, tukun ta ɗago dara-daran fararen idanuwan ta tana mai ɗora su akan hanyar da bayi zasu biyo su shigo filin bikin, kasancewa acikin duka filin babu wani Bawa suna can sashin su suna shiryawa suma. Tana zama akan kujerar salon kiɗan dake tashi acikin wurin duka ya sauya, wani irin kiɗa makaɗan sukeyi da gangunan dake ɗauke ahannun su da tsantsar ƙarfi idanuwan su arufe. Tukun can sai ga Bayi mata nan sun fara shigowa alayi ta wata hanya da baya da baya suna ta faman ɗirkar rawa, yayin da tafukan hannayen su kuma suke ɗauke da kaskwayen wuta waƴan da suke ta faman ci da huta! Wata irin rawa suke yi suna masu shigowa akan layi da baya da baya, bakunan su kuma na aikin furka kalmar. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Da tsantsar ƙarfi. Ɗaure suke da wani baƙin ƙyalle na yadi ɗaure aƙugun su wanda ya tsaya iyakar guiwoyin su, sai wata ƴar ɓingilar riga da tsayin ta ya huce kan cibin su da kaɗan mai tsantsar faɗi fara ajikin su, gaba ɗaya rigar zane take da tambarin masarautar kamar yacce duka fuskar su take zane da shi, wanda ake bugasa da baƙin fenti, yayin da ƙafafuwan su kuma suka kasance ko takalmi babu akan su, sai uwar ƙura kawai da suke ɗiba. Haka sukai ta shigowa cikin filin suna masu dosar inda abun bauta Gargabilu yake, hannuwan su riƙe da kaskwayen huta da suke ta faman jujjuya sa, alamun ba ƙaramun zafi yake musu ba, domin kuwa kusan dukan su tafukan hannayen su sunyi jajajir yarce kasan zasuyi tsartuwar jini. Ba tare da sun gama shigowa ba suma bayi maza suka fara shigowa da baya da baya akuma kan layi, su kuma ɗauke da damin iccina masu matuƙar yawa akan kafaɗun su, suna ta faman rawa tare da faɗar kalmar. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Da tsantsar ƙarfi yarce kasan zasu tsaga wurin, ga kuma uban sautin kiɗan ganguna da suke tashi awurin mai matuƙar dadi. Sanye suke su kuma da fararen wandina na yadi masu matuƙar faɗi iyakar guiwoyin su, yayin da gaba ɗaya jikin wandinan kuma suka kasance ɗauke da zanen tambarin masarautar tasu da akayi sa da baƙin fenti, sai fuskar su da fatar jikin su da ta kasance zane da tambarin masarautar tako ina, kasancewar babu wanda yake sanye da riga acikin su. Gaba ɗaya suma nufar hanyar wurin da abun bauta Gargabilu yake sukayi da baya da baya, hannuwan su ɗauke da iccina suna faman aikin dilliƙar rawa, yayin da gumi kuma ke yanko musu ta koce kafar gashi dake jikin su sabo da wahala. ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI. Acikin masarautar wasai kuwa tun kafin gwamna da tawagar sa su ƙarasa fada masu tarbar su suka ƙaraso inda suke, kasancewar an riga ansan da zuwan su tun jiya. Cikin girmamawa wasu daga cikin fadawan mai martaba Sarki Abdallah suka da aka turo su tarbar mai girma gwamna suka durƙusar da kai agaban su suna masu miƙa gaisuwar su gare sa. Yayin da shi kuma gwamna da yake zaune agidan baya cikin azababbar motar da suke ke ciki ya sanya drivern sa ya sauke masa glass ɗin motar ƙasa, tukun shima ya ɗagawa dakarun hannu yana mai sakar musu murmushi alamar amsawa kenan, sannan suka juya suna masu dosar hanyar da zata sada su da fada aƙafafuwan su, yayin da suma motocin su gwamna da escort ɗin sa suka bisu abaya, bayan driver'n shi ya mai da glass ɗin motar ya rufe. Ko da suka ɗauki hanyar fada amai-makon su shiga cikin ta sai suka ɗauke hanya suna masu yin wata hanyar wacce zata kai su zuwa ga gidan da mai martaba Sarki Abdallah yake ganawa da manyan baƙin sa, kasancewar tun jiyan da mai girma gwamna ya aiko da saƙon zuwan sa sai da yasa sanarwa da mai martaba cewar babbar magana ce zata kawo su wurin su, sai dai amma ba wacce ta shafi Jaha bace, magana ce wacce ta kasance family issue. Hakan yasa mai mairataba Sarki Abdallah bai sa akai su fada ba sai yace awuce dasu zuwa masaukin baƙin sa direct. Gaban wani haɗɗaɗen plat building fadawan sarki suka tsaya, sannan suma motocin su gwamna akayi parking ɗin su awani wuri da yake ajikin gidan, wanda anyisa ne sa domin aje motocin dama. Dasauri escort ɗin da suke acikin motocin waƴan da suke sanye da uniform kala kala ajikin su suka buɗe murafan motocin su su suna masu furfutowa waje, tukun suka fara ɗaga ƙafafuwan su suna masu dosar wurin motar da mai girma gwamna tare da aminin sa suke aciki, cikin takun su dake nuni da su ɗin cikakkun jarumai ne, yayin da hannuwan su kuma suka kasance riƙe da manya-manyan bindigu. Mutum biyu suka matsa jikin ƙofofin motar suna masu sanya hannu suka buɗe su, yayin da suran escort ɗin kuma sukayi tsai-tsaiye abakin motar cirko-cirko. Ƙafar sa da take sanye da wani azababben cover shoe mai matuƙar kyau da tsada ya fara zurowa waje, tukun daga bisani ya sanyo gangar jikin sa waje yana mai futowa duka. Sanye yake da wata arniyar getzner shadda ash color da take matuƙar ƙyalli da ɗaukar ido, ɗinkin babbar riga ajikin sa. Aɓangaren abokin nasa shima futowa yay yana mai dawowa ɓarin da mai girma gwamna yake, shi ɗin ma sanye yake da shiga ta alfarma ɗinkin babbar riga ajikin sa. Tukun suka fara takawa suna masu dosar ƙofar dake manne jikin haɗaɗɗen building ɗin nan, yayin da suma escort ɗin suka bisu abaya suna ta faman bubbuɗawa. Cak fadawan nan suka tsaya daga bakin ƙofar suna masu komawa gefe suka buɗawa mai girma gwamna wuri. Suna zuwa bakin ƙofa ya ɗagawa escort ɗin dake binsu hannu ba tare da yace musu komai ba. Cak sukai tsaye awurin daga bakin ƙofar suna masu gyara riƙon bindigun dake hannuwan su. Yayin da su kuma su gwamna suka danna kawunan su zuwa cikin ƙofar. Tamfatse-tsen fallo ne wanda ya gaji da haɗuwa da kayan ƙawa da alatu yarce kasan babu mutuwa. Tsit fallon yake babu kowa cikin sa sai sautin futar ac kawai dake tashi acikin sa, tare da wani irin ni'imtacce ƙamshi. Kan wata mayyar royal chair dake zagaye da fallon mai girma gwamna da aminin sa suka samu wuri suka zauna. Yayin da daga gaban kujerar kuma wani tamfatse-tsen center table yake cike maƙil da kayan ciya-ciye, irin su ruwa, fruits, naman kaji, dana rago wanda aka sarrafa sa kala-kala jere akan wani ƙaton tray. Basu jima da zama awurin ba sai ga Waziri da Galadima nan sun futo ta wata ƙofa da take acikin fallon bakunan su ɗauke da sallama. Ƙarasawa sukayi zuwa kan kujerar da take facing ɗin wacce su mai girma gwamna suke akai, tukun suka zauna suna masu fara gaisawa cikin mutunta juna da girmamawa. Zaman su baifi da minti biyar ba sai ga mai martaba Sarki Abdallah nan ya futo ta cikin ƙofar dasu galadima suka futo bakin sa ɗauke da sallama shima. "Wa'alaikumu salam." Gaba ɗayan su suka amsa masa suna masu kai idanuwan su kansa. Sanye yake da shigar sa irin ta koda yaushe, wato manyan kaya tare da alkyabba mai azabar kyau da rawani ɗauke akan sa. Ƙarasawa yayi zuwa gaban kujerar da su mai girma gwamna suke yana mai miƙa musu hannu sukayi musabaha cikin mutunci da girmamawa, kana ya juya yana mai komawa kan kujerar da take agefen wacce su Waziri suke akai ya zauna, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Bismillah ga abinci nan ku taɓa mana." Ya ƙarasa maganar yana mai musu nuni da tray'n dake cike da kayan abinci kala kala akan sa da yatsar sa manuniya. "Alhamdulillah! Alhamdulillah wallahi!!" Suka haɗa baki wurin fadɗe suma fuskar su ɗauke da murmushi. Shiru ne ya biyo baya ba tare da wani ya ƙara cewa komai ba acikin su. Tukun daga bisani aminin mai girma gwamna mai suna Alhaji Saleh yayi gyaran murya yana mai ɗago kai ya fuskanci su mai martaba, tukun daga bisani ya fara ɗaga laɓɓan sa yana mai faɗin. "To ataƙaice dai ba komai ne yasan ya mu muka buƙaci zama daku ba sai akan wani muhimmin abu da yake atsakanin yaran mu duka, wanda afannin mu mu muke masa kallon abun alkhairi tare da alfahari garemu gaba ɗaya idan har muka samu ya tabbata." Ya faɗa yana mai gyara zaman sa akan kujera, yayin da su kuma su mai martaba suka zuba masa ido suna masu kallon su tare da sauraran sa fuskar su ɗauke da murmushi, ba tare da sunce komai ba. Tukun shi kuma ya ɗora da faɗin. "Ba komai bane ba kuwa face soyayyar dake atsakanin yarinyar wurin mu, wato bilkisu ƴar wurin mai girma Gwamna, da kuma yaron wurin ku Yarima Asad." "Asad kuma!" Suka haɗa baki su duka ukkun suna masu faɗin haka fuskar su cike da tsantsar mamaki, domin kuwa cikin su duka babu wanda bai san halin Asad ba na rashin son aure, dan kuwa babu yarce ba'ayi ba da shi akan su futar da matan aure amma shi yaƙi sai Al'amin ne kawai ya futar da tasa. "Tabbas kuwa Asad naku da Bilkisu, dan kuwa ataƙaice sun ɗauki tsawon shekaru kusan huɗu suna atare, hakan yasa mukaga amai-makon su zauna suna ta abu ɗaya gwanda ace kawai anyi mai duka kowa ya huta, wannan shine dalilin da yasa muka buƙaci zama daku." Yaƙarasa maganar yana mai sakin murmushi. "Masha Allah! Masha Allah!!" Galadima da Waziri suka faɗa gaba ɗayan su fuskar su ɗauke da murmushi, tukun daga bisani suka sake buɗe baki atare suna masu faɗin. "Haƙiƙa munyi matuƙar jin daɗin wannan labari daga bakin ku, kuma insha Allah abun bazai ɗauke mu

Chapter 10 of 76