Share this page
Hausa zuciya na zafi da ƙuna. *** Kwanaki sunja watanni sun zo sun shuɗe, tun ana sa ran Yarima Asad zaiyi magana a cikin ƴan satittika sai gashi har ya ɗauki tsawon wata tara ba uhm ba uhm-uhm sai dai kallo da idanuwa kawai. Gaba ɗaya sun fara futar da tsammanin zai sake magana, duk da har lokacin basu bar ƙasar London ba, kwatsam rana ɗaya kawai a daren ranar da zai cika wata goma da fara rashin lafiyar tasa, suna zaune tare da Mai Martaba da ya dawo daga Ƙasar Hausa aranar, kawai sai jin muryar Asad yayi tana dukan kunnen sa ahankali. Da farko basarwa yayi ba tare da ya juyo ɓarin da yake ba, domin kuwa duk atinanin sa amsa kuwwa ne kunnen sa yake masa na muryar tasa kamar yadda ya saba yi masa a kusan kullum. Amma sai yaji Asad ya sake faɗin. "Abba na!" Hakan ne yasa sa juyowa ɓarin da yake da matuƙar sauri, yana mai kallon sa baki buɗe. Yayin da shi kuma Yarima Asad ya lumshe idanuwan sa a hankali, tukun daga bisani ya sake buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin. "Abba na." Zumubur Mai Martaba ya miƙe daga kan kujerar da yake, yana mai nufar wacce Asad yake a kai cikin tsantsar aljabi. Yana ƙarasowa gaban kujerar da yake ya durƙushe a ƙasa yana mai zama akan guiwoyin sa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin rawar murya idanuwan sa akan fuskar Asad, yana mai faɗin. "Shin da gaske ne abun da kunnuwa na suka jiyo mun, kai ɗin ne kake magana da kanka Baba na?" Mai Martaba ya faɗi haka cikin sauri, yana mai kamo tafukan hannayen Yarima Asad duka biyu ya riƙe su da nasa. Yayin da shi kuma Asad ya sake mayar da idanuwan sa yana mai lumshe su, tukun daga bisani ya jin-jinawa Mai Martaba kai alamar Eh. Girgiza kai Mai Martaba ya fara yi yana mai faɗin. "A'a Baba na ba da kai nake son ka amsa mun ba, muryar taka nake son sake ji tamkar yacce naji ta yanzu." "Abba na!" Yarima Asad ya sake faɗe yana mai kallon mahaifin nasa. Yayin da shi kuma Mai Martaba ya buɗe baki cikin tsantsar farin ciki yana mai faɗin. "Shin tun yaushe ne ka fara magana Baba na ban sani ba, ko kuwa dama can kanayi-yin ne baka yi Baba na?" Ya faɗi maganar cikin rawar murya, yana mai shafa lallausar sumar da take kwance sunƙum akan Asad. "Yanzu nima naji nayi maganar." Asad ɗin ya faɗa yana mai sake yin shiru. Da wani irin sauri Mai Martaba ya janyo sa jikin sa yana mai rungume sa ƙam-ƙam a ƙirjin sa yarce kasan zai mayar da shi ciki. Tukun daga bisani ya buɗe baki cikin muryar tsantsar farin ciki, hawaye na tsiyayowa daga cikin idanuwan sa, ya fara faɗin kalmar. "Alhamdulillah." Ba ƙaƙƙautawa. Suna a wannan yana yin ne Sheikh Yaƙub ya danno kansa cikin ɗakin, bakin sa ɗauke da Sallama. Hango su da yayi a hakan ne yasan ya sa ƙarasawa ciki da matuƙar sauri, yana mai faɗin. "Subahanallahi, meke faruwa ne yallaɓai na ganku a haka?" Ya ƙarasa maganar yana mai ƙarasowa gaban su ya tsaya. Yayin da shi kuma Mai Martaba ya saki Asad da sauri yana mai miƙewa tsaye ya rungume Sheikh Yaƙub. Shi kuwa Asad mayar da idanuwan sa yayi ya lumshe su ba tare da yace komai ba, domin kuwa hakanan kawai yaji ko kaɗan baya son yin maganar, amai-makon ace yayi ta yin ta amatsayin sa na wanda ya daɗe bai furta koda kalmar A ba. "Allah ya amshi addu'ar mu ya Sheikh, yau dai Asad ɗina yamun magana, ya kirani ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba." Mai Martaba ya faɗa cikin matsanan ciyar murna. Yayin da shi kuma Sheikh Yaƙub ya furta kalmar. "Alhamdulillah." Cikin tsantsar farin ciki, yana mai sake rungumar Mai Martaba shima, tukun daga bisani ya sake sa yana mai yin wurin da Asad yake, bakin sa ɗauke da tsantsar murna. Zube guiwoyin sa shima yayi a gaban sa yana kallon sa. Tukun daga bisani ya buɗe baki cikin tsantsar farin ciki yana mai faɗin. "Asad! Shin da gaske na kayi magana?" Jin-jina masa kai Asad yayi, tukun daga bisani ya buɗe idanuwan sa da suke a lumshe yana mai faɗin. "Eh nayi magana Ya Sheikh." Ya faɗi hakan cikin sanyi. Yayin da Sheikh Yaƙub kuma yayi saurin janyo sa cikin jikin sa yana mai godiya ga Allah. Haka dai sukai ta farin ciki suna sake sanya Asad yana magana, duk da yadda baya son yin nata shida ko kaɗan. Aranar Mai Martaba ya farayi musu cuku-cukun juyawa Ƙasar Hausa a gobe shida Asad. Ko da dare yayi sosai Mai Martaba yayi bacci har da munshari, irin wanda ya jima baiyi kamar saba, domin kuwa rabon sa da cikakken bacci tun ana gobe Asad zai kamu da ciwon nan, wato tsawon wata goma yanzu kenan. Washe gari kuwa tun da sanyin safiya suka tafi airport. Ƙarfe takwas na safe dai-dai na agogon ƙasar jirgin su ya ɗaga zuwa sararin samaniya. Yayin da Sheikh Yaƙub kuma da Iyalan sa da suka yo musu rakiya suka juya cikin jin kewar tafiyar tasu, suna masu komawa gida. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Lokacin da labarin dawowar Mai Martaba a yau ya fasu a cikin Masarauta Wasai, ba ƙaramun mamakin abun da zai sanya sa dawowa yau bayan kuma kowa yasan jiya ya tafi bane ya lulluɓe su. Take kuwa maganar ta bazu ako ina dake cikin Masarautar, yayin da jama'a da dama dake cikin Masarautar sukai tinanin ko Asad ɗin ne ya rasu, dan kuwa babu wani wanda yay tinanin ko warkewa yayi ne. Tini kuwa murna ta cika zukatan magautan su gaba ɗaya da tinanin da sukeyi na ko Asad ɗin ne ya rasu, kasancewar Mai Martaba bai sanar da kowa dawowar tasa ba har sai da ya sauka a cikin Wasai Internationl airport, tukun ya sanar musu domin azo atafi da su, amma bawai ya faɗa musu dalilin dawowar tasa bane, sabo da yadda yake son yayi suprising ɗin su. Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa tana zaune akan kujera sanye da hijabi a jikin ta tana taz'bihi, ɗaya daga cikin Hadiman ta da suke anan part ɗin nata ta faɗo cikin falon da sauri. Da idanuwa Gimbiya Fulani ta bita bayan ta amsa mata sallamar da tayo, har ta ƙaraso bakin kujerar da take zaune akai. Durƙusar dai ƙasa Hadimar tayi bayan ta zauna akan ƙafafuwan ta, tana mai buɗe baki tace. "Barka da hutawa ranki ya daɗe." "Yawwa barkan ki dai Talatu." Gimbiya Fulani ta faɗa tana mai cigaba da kallon ta. Yayin da ita kuma ta ɗan fara mustu-mutsu a wurin da take tana mai son buɗe baki tayi magana, amma tana tsoron tayarce Gimbiya Fulani zata ɗau zancen, sabo da sun sani gaba ɗayan su bata son gulma, asalima babu abun da ta tsana face mutum ya jiyo wani labarin na wani a cikin gidan yazo yace zai sanar mata, hakan yasa gaba ɗaya ta kasa buɗe baki tayi maganar kai tsaye. "Alamun ki sun nuna akwai magana ɗauke abakin ko, shin meke faruwa ne to?" Gimbiya Fulani ta faɗa tana kallon ta, sabo da lura da tayi da ita tana son yin maganar amma kuma tana shakkar yi. Jin da Hadima Talatu tayi Fulani ta bata dama ne, ya sanya ta ɗago kai cikin rawar murya tana mai faɗin. "Dama wai yanzu ne muma mukejin labarin dawowar Mai Martaba ayau, domin kuwa ance har ya sauka ma an tafi ɗakko sa" Ta ƙarasa maganar da sosa ƙeya. Yayin da ita kuma Fulani tayi suman zaune a wurin da take gaban ta nayin wata irin gigitacciyar faɗuwa, sabo da jin furucin Hadima Talatu da tayi na cewa Mai Martaba ya dawo, sabo da jiya kafun ya tafi ita da kanta ta tambaye sa sai kuma yaushe zai dawo, amma yace mata bai sani ba shima sai yadda hali yayi, sai dai kuma yana tinanin zai ɗauki tsawon sati biyu zuwa ukku kafun ya dawo ɗin, sai gashi kuma yanzu labarin isowar sa yazo kunnen ta. Zumbur ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take jikin ta na rawa, yayin da ita kumavwannan hadimar tayi saurin ja da baya daga zaunen da take, sabo da a zaton ta tashi tayi ta make ta ne, duk da dai tasan hakan ba halin ta bane, amma sai taga ta kama hanyar waje cikin ɗimuwa, bakin ta na furta kalmar. "Innalillahi wa'inna ilahir raj..." Cak maganar ta tsaya daga cikin bakin ta tana mai ƙamewa wuri ɗaya, ƙirjin ta na cigaba da dukan tara-tara, sabo da yadda muryar mai martaba ta daki dodon kunnuwan ta yana mai doko sallama shima. Tukun daga bisani sai gashi nan ya danno kansa cikin falon. Kana sai ga Asad nan kuma ya tako masa baya sanye da ƙana nan kaya a jikin sa. Take a wurin Gimbiya Fulani ta fara zare idanuwa jikin ta na cigaba da kar-karwa, yayin da idanuwan ta kuma suka kasance ƙur akan fuskar Asad da tayi arba da shi tana kallon sa. Itama wannan Hadimar tare da su Babban Yaya da sauran ƴan uwan su gaba ɗayan su ƙamewa sukayi a wuri ɗaya suna kallon Asad cikin tsantsar mamaki, ba tare da an iya samun ɗaya daga cikin su ya matsa wurin da yake ba. Yayin da Mai Marataba dake riƙe da hannun Asad kuma yayi tsaye yana kallon Gimbiya Fulani, fuskar ɗauke da wani irin yalwataccen murmushi. Tukun daga bisani ya mayar da idanuwan sa kan fuskar Asad da yake ta faman naniƙe sa, tun lokacin da suka shigo Masarautar, domin kuwa sai da suka ƙaraso ɓangaren Gimbiya Fulani ne ma tukun ya ɗan ware. Fuska ɗauke da murmushi Mai Martaba ya buɗe baki yana mai faɗin. "To Baba na aje a gaida Mamy ko?" Ya ƙarasa maganar yana mai shafa kansa, tare da ɗan turasa gaba. Cikin sanyi Yarima Asad ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai tunkarar inda mamy'n tasu take. Ba zato ba tsammani sai jin sautin muryar Asad Gimbiya Fulani da gaba ki ɗaya sauran mutanen dake a cikin falon sukayi yana mai faɗin. "Ina yini Mamy na!" Tukun daga bisani ya faɗa jikin ta yana mai rungume ta. Da sauri itama ta durƙushe a ƙasa tana mai rungume sa ƙam-ƙam a cikin jikin ta, tukun daga bisani ta fashe da wani irin kukan farin ciki wanda batan da tawowar sa ba, sai futowar sa da taji kawai, tana mai faɗin. "Shin da gaske ne ba mafarkin dana saba yi bane nake yi kaine nake jin muryar ka Zaki na?" Ta ƙarasa maganar tana mai ɗago kansa ta kalle sa. Jin-jina mata kai yayi ba tare da yace komai ba. "A'a my Zaki ba da kai nake son ka amsa mun ba, bakin ka zaka buɗe ka sake yi mun magana, hakan shine zai sa na tabbatar da ba mafarki nake yi ba." Ta faɗa tana mai ɗan girgiza sa da hannuwan ta biyu. "Ba mafarki kike ba, Mamy na nine a gaban ki nake magana." Asad ya faɗa yana mai sake faɗawa jikin ta yayi wani irin lafewa. "Alhamdulillahi rabil alamin, Alhamdulillahi rabi samawati wal'ard." Gimbiya Fulani ta faɗa cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa. Yayin da su Baban Yaya da sauran ƴan uwan sa kuma suka saki wani irin ihun murna da matuƙar ƙarfi, suna masu tawowa zuwa wurin da suke aguje. Suna isowa gaba ɗayan su suka faɗa jikin Asad da Mamy'n tasu suna masu rungume juna ƙam-ƙam. Haka dai sukai ta farin ciki suna sanya Asad yana maganar da baya son yin ta ko kaɗan. Barin ma da suka iso cikin gidan, gaba ɗaya sai ya jisa a wani irin takure, ga kuma ƙirjin sa dake ta faɗuwa tunda suka doso Masarautar a mota, wannan dalilin shine ya sanya sa kasa sakewa ko da ƴan uwan nasa. Suna a cikin wannan yana yin na farin ciki sai ga Al'amin nan ya faɗo cikin falon aguje bako sallama a bakin sa. Da matuƙar sauri suka rungume juna shi da Asad suna masu sakarwa junan su murmushi. Tukun Al'amin ya buɗe baki cikin tsantsar murna yana mai cewa. "Yi mun maganar mana inji idan da gaske ne abun da jummai tazo ta faɗa." Al'amin ya faɗa yana mai shafa kan Asad. Yayin da shi kuma ya ɗaure fuska yana mai ture sa daga jikin sa, tare da faɗin. "Bazan yi ba ɗin, dallacan ɗaga ni daga zuwa na har zaka fara danne ni." Ya ƙarasa maganar da hararar Al'amin. Wani irin ihu Al'amin ya saki yana mai faɗin. "To jarabbaben banza ai kayi ma maganar baka sani ba, kuma wallahi bazan ɗaga kan ba." Ya ƙarasa maganar yana mai sake hayewa kansa. Yayin da shi kuma Mai Martaba ya juya yana mai fucewa daga cikin ɗakin cikin tsantsar farin ciki, sabo da ganin da yayi gaba ɗaya sun manta da shi ma. Kafun kece me tini labarin dawowar Asad yana magana ya baza ko na- na cikin Masarautar. Hakan kuwa ba ƙaramun daɗi yayiwa masoyan su ba, yayin da maƙiyan su kuma sukaji tamkar su cinnawa zuciyar su huta dan baƙin ciki. Abu fa kamar wasa na faɗuwar gaban da Asad yake ji, sai gashi yana shirin zamtowa Babba. Domin kuwa bayan Fulani tayi masa wanka yaci abinci sun shirya, sai ga saƙon Mai Martaba nan ya iso wurin sa, na cewar ya tawo faɗa suyi hira idan bai gaji ba. Ai kuwa take awurin Al'amin ya miƙe tsaye yana mai jan hannun sa tare da faɗin. "Taso muje kaji." Kasancewar a lokacin suna zaune ne babu abun da suke yi. Miƙewa Asad ɗin yayi yana mai bin bayan Al'amin suka fuce, sai dai kuma sun dosar hanyar fada yaji gaban sa yayi wata irin mahaukaciyar faɗuwa. Da ƙarfi ya rumtse idanuwan sa yana mai ɗaukar tafin hannun sa ya dafe ƙirjin sa da shi, tukun daga bisani ya cigaba da dɗaga ƙafafuwan sa cikin ƙarfin hali irin nasa suna masu dosar fadar. Adadin yadda yake ɗaga ƙafafuwan nasa yana cigaba da tunkarar Fada, haka adadin faɗuwar da gaban sa yake yi take ƙaruwa. Yayin da Al'amin kuma yake ta masa zuba yana basa labaran abubuwan da suka faru a lokacin da baya nan, ba tare da ya lura da halin da yake ciki ba, ahaka har suka ƙarasa bakin fada. Suna shiga cikin fadar Yarima Asad yaji kansa yayi wata irin mahaukaciyar sarawa, kana daga bisani kuma wata irin hajijiya ta fara ɗibar sa, tukun ya tafi luuu yana mai zubewa a ƙasa sumamme! Cikin tsantsar tashin hankali da firgici daga Mai Martaba har sauran mutanen da suke zaune a cikin fada suka taso suna masuyowa kansa. Yayin da Al'amin kuma ya fashe da wani irin gigitaccen kuka yana mai durƙusawa sa a ƙasa ya fara girgiza sa tare da kiran sunan sa. Da wani irin gudu Mai Martaba ya ƙaraso wurin yana mai h................✍ *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 21* Hankaɗe mutanen da suke tsaye a gaban sa, ya durƙusa ƙasa yana mai ɗaukar Asad ya ruƙunk'ume sa a jikin sa. Kana daga bisani ya buɗe baki cikin tsantsar tashin hankali, ruɗu had'i da firgici yana mai faɗin. "Baba na! Baba na!! Baba na!!! Asad! Asad!! Asad!!! Zaki! Zaki!! Zaki!!!" Ya dinga kiran sunayen da duk ake faɗa masa a matuƙar ruɗe yana mai girgiza sa. Kafin daga bisani kuma ya miƙe tsaye zumbur ɗauke da shi a hannun sa. Zagaye ya farayi da shi a cikin Fada'r yana mai girgza kansa, gaba ɗayan sa ya ruɗe ya rasa yadda zaiyi, tukun daga bisani kuma ya juya da sauri yana mai fucewa ya kama hanyar pary ɗin sa direct ɗauke da shi a hannun nasa. Yayin da Al'amin kuma ke biye da su a baya cikin tsantsar firgici shima yana kuka. Shimfiɗe sa Mai Martaba yayi akan haɗaɗɗen gadon sa, yana mai cigaba da girgiza sa tare da kiran sunan, kafin daga bisani kuma ya sake miƙewa zumbur yana mai matsawa gaban freezer dake kafe a cikin ɗakin. Buɗe ta yayi yana mai ɗauko ruwa mai sanyi a cikin jarka daga cikin ta, kana ya juyo da sauri yana mai dawowa wurin da Asad yake ya buɗe jarkar ruwan, yana mai fara tsiyaya masa shi akan fuskar sa. Wasu irin ƙarfa-fan ajiyar zuciya Asad ya fara saki da sauri da sauri, tukun daga bisani kuma ya buɗe idanuwan nasa duka akan fuskar Mai Martaba da yake tsaye a gaban sa. Da sauri Mai Martaba yayi cilli da jarkar ruwan da take riƙe a hannun sa a ƙasa, kana ya durƙuso zuwa kan gadon yana mai janyo Asad cikin jikin sa. Da wani irin ƙarfi Asad ya rungume sa jikin sa na rawa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin muryar tsoro yana mai faɗin. "Ina Mamy na Abba na, ni zan tafi wurin Mamy na, ni bana son wurin nan." Ya ƙarasa maganar yana mai shirin zame jikin sa daga cikin na Mai Martaba ya tafi. "Meke damun kane Baba na, me yasa ba zaka zauna anan wuri na ba?" Mai Martaba ya faɗa cikin rawar murya, yana mai sake rungume ɗan nasa da yake jin tamkar shi kaɗai ya haifa a duniya. Wani irin kuka Asad ya fashe da shi jikin sa na matuƙar karkarwa, tukun daga bisani ya fara ƙoƙarin ɓan-ɓare jikin sa daga cikin na Mai Martaba yana mai faɗin. "Abba na mutafi daga gidan nan, mu koma gidan Sheik yafi nan daɗi." Ya ƙarasa maganar yana mai funcike jikin sa daga na Mai Martaba. Yayin da Al'amin kuma keta aikin kuka yana mai riƙe da tafin hannun sa. Ganin hakan da Mai Martaba yayi ne ya sanya sa miƙewa tsaye shima yana mai sake riƙo ɗan nasa, tukun ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin. "To muje in kaika wurin Mamy'n taka Baba na." Kana suka juya suna masu kama hanyar da zata sadar dasu ɓarin Gimbiya Fulani, ta cikin wata ƙofa da suka bi da take anan cikin part ɗin su duka ukkun, har zuwa lokacin kuma jikin sa bai bar rawar da yake yi ba. Suna shirin shiga cikin falon sukaci karo da Gimbiya Fulani bako mayafi a jikin ta tana shirin futa cikin tsantsar firgici. Da sauri taja da baya ta tsaya, sabo da jin da tai kanta ya daki ƙirjin mutum, tukun daga bisani ta ɗago kan nata tana mai sauke idanuwan ta akan fuskar Mai Martaba, kafin daga bisani kuma ta sake yin ƙasa da kanta nata, idanuwan ta na dira akar fuskar ɗan nata. Da matuƙar sauri tayi wurin da yake tana mai durƙusawa a ƙasa ta janyo sa cikin jikin ta. Wani irin ƙan-ƙameta shima yayi da matuƙar ƙarfi, jikin sa na karkarwa. "Zaki na aka cemun baka da lafiya, ka sake sumewa a cikin Fada" "Mamy na mutafi-mutafi, ki mayar dani gidan ya Sheikh ni bana son gidan nan." Asad ya faɗa cikin tsantsar ruɗu yana mai fashewa da kuka, ba tare da ya bata amsar tambayar da tayi masa ba. Take kuwa a wurin hankalin su daga ita har Mai Martaba da Babban yaya da ya ƙaraso wurin yanzu yayi bala'in tashi. Da sauri Gimbiya Fulani ta cicciɓe sa a jikin ta tana mai miƙewa tsaye ɗauke da shi, tukun ta juya tana mai kama hanyar bedroom ɗin ta cikin tashin hankali. Rufa mafa baya su Mai Martaba sukayi suma, gaba ɗaya shi yanzu ma ya rikice ya rasa mai ya kamata yayi, domin kuwa gaba ɗaya kansa ya riga da ya gama kullewa da yanayin yadda yaga Asad ɗin ya koma yanzu. Shimfiɗe sa tayi akan gadon ta tana mai fara tofa masa addu'oi. Ƙarasowa su Mai Martaba sukayi ciki suma suna masu hayowa kan gadon, tukun dukan su suka haɗu suna masu karanto addu'oi suna tofa masa. Ba suyi minti biyar da fara addu'oin ba ya fara sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya ajere-ajere, kana daga bisani kuma wani irin bacci ya fizge sa. A tare daga Gimbiya Fulani har mai martaba suka sauke nannauyar ajiyar zuciya, tukun suka juya suna masu kallon junan su cikin tsantsar aljabi da firgicin abun da ke faruwa. Zaune sukai a wurin gaba ɗayan su jugum-jugum ba mai tankawa wani, sai faman kallon Asad da suke ta ai'kin yi da idanuwa kawai. Acan cikin Masarautar kuwa tini labarin sake suman Asad ya baza ko ina da ina na cikin ta. Sosai kuwa abun yayi matuƙar ɗaurewa jama'a da dama kai, yayin da wasu kuma hakan yayi musu tsantsar daɗi, wasu kuwa gaba ɗaya suma sun firgita da lamarin ba kaɗan ba. Ko da dare yayi ma haka Asad ya farka yana surutai tare da zabure-zabure akan cewa dole sai ya koma wurin Sheikh Yaƙub, shi baizai ƙara zuwa fada ba baya sonta. Sosai hankalin su Mai Martaba ya sake matuƙar tashi, haka su kai ta aikin tofa masa addu'oi da shi da Gimbiya Fulani har su samu yayi bacci kafin ya sake farkwa, kai ataƙaice dai ranar kwanan zaune sukayi dukan su, har Babban Yaya da sauran ƴan uwansa masu girma, domin kuwa shi kansa Al'amin sai bacci ɓarawo ne ya sace sa anan cikin ɗakin Gimbiya Fulani, amma bai koma part ɗin su ba. Washe gari kuwa misalin ƙarfe ɗaya na rana, Abokin Mai Martaba kuma ɗan uwan sa mai suna Alhaji Abubakar ya duro cikin Masarautar Wasai, domin taya murnar samun lafiyar Asad da yaji labari jiya. Alhaji Abubakar nabban ɗan kasuwa ne wanda sunan sa yay shuhura aduniya, domin kuwa ataƙaice dai yanzu haka ma yana Dubai dukan sa da zama da shi da iyalan sa. Sun taso tare da Mai Martaba a matsayin aminai tun suna yara, kasancewar shima ɗin Asalin mahaifin sa ɗan nan cikin Masarautar Wasai ne. Yana shigowa gidan shima ya riski wannan rikicin da ake ta fama da shi na Asad, domin kuwa har kawo yanzu kuka yake yana cewa bazai zauna a cikin Masarautar ba. Shima ɗin shigowa falon Gimbiya Fulani yayi yana mai zama a kusa da kujerar da Mai Martaba yake zaune akai riƙe da Asad. Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani take zaune a gefen Mai Martaba, gaba ɗaya idanuwan ta a kumbure, alamun ba ƙaramun kuka taci ba kenan. Ko da Alhaji Abubakar yaga abun Asad ɗin da gaske ne ba wasa ba, sai ya gyara zaman sa akan kujerar da yake yana mai yin gyaran murya. Sautin gyaran muryar sa da su Mai Martaba sukaji ne ya sanya su juyowa ɓarin da yake dukan su suna kallon sa. Fuskantar su shima ɗin yayi sosai, tukun ya buɗe baki cikin nutsuwa yana mai faɗin. "To ni a gani na Alhaji, tunda abun nan yazo da haka shi yaron yana ta faɗin bazai zauna ba, mai zai hana abani shi in tafi da shi can wuri na, in yaso sai ya cigaba da karatun sa acan kafin zuwa wani lokaci muga yarce hali zaiyi." Ya ƙarasa maganar yana mai binsu da idanuwa daga shi har Fulani. Yayin da su kuma gaba ɗayan su sukayi shiru ba tare da wani yace komai ba, tukun daga bisani Fulani tayi ƙarfin halin buɗe baki cikin sanyin murya, tana mai faɗin. "Tabbas hakan ma yayi, domin kuwa ni kaina tun ɗazu tunanin yadda zamuyi da shi nake, sabo da gashi nan daga jiyan da ya dawo zuwa yau har ya rame, dan haka ni na amince ku tafi tare muddin zai samu nutsuwa acan ɗin, in yaso daga baya sai muga yadda za'ayi." Ta ƙarasa maganar cikin sanyi tana mai jin ranta na ɗaci da ƙuna. Jin hakan data faɗa ne ya sanya Mai Martaba shima amicewa, amma bawai dan ransa yaso da hakan ba ko kaɗan, sai dai shima ɗin zai so yaga ɗan nasa ya samu nutsuwa bawai ya cigaba da rayuwa ahaka ba. Hakan ne yasa ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin. "Tom shikenan Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, amma ni ina ganin idan kun tashi tafiyar sai ahaɗa har da Al'amin ku tafi tare duka, domin kuwa in bahakan akai ba shima bazai taɓa sakewa anan ɗin ba, duba da yadda ya koma alokacin da muke acan London sabo da rashin abokin nasa, kuma shima Asad ɗin zaifu samun sakewa acan ɗin idan suna tare." "To masha Allah hakan ma yayi sosai, Allah kuma ya ƙara masa lafiya." Cewar Alhaji Abubakar cikin sanyi shima. Haka dai ranar ma suka yini cir jugum-jugum sai sallah ce kawai ke tayar da su, domin kuwa ko Fada ma Mai Martaba bai leƙaba kwata-kwata, ahaka har dare ya riske su suna a hakan. Washe gari kuwa tun da sanyin safiya aka shirya Al'amin da Asad tas, misalin ƙarfe goma na safiya aka musu rakiya Airpot, kana ƙarfe shaɗaya na safe dai-dai jirgin su ya ɗaga zuwa ƙasar Dubai, ba tare da sun ɗauki ko da ƙyalle ba na sutura, sai waƴan da suke sanye a jikin su kawai. _Musababbin canzawar

Chapter 22 of 76