wata irin murya, wacce take nuni da tsantsar kalar b'acin ran da take a cikin sa, ta yadda har iskar bakin ta da ke futowa tana dukan fuskar sa a lokacin da take furucin ta zamto zazzafa matuk'a.
Lumshe idanuwa Bir yayi yana mai d'an juyar da kai gefe ya fesar da iska daga cikin bakin sa, kana ya sake juyowa b'arin da take yana mai d'an dage mata girar sa d'aya, alamun yana jin ta to.
Yayin da ita kuma ta d'ora da fad'in.
"Tunda na taso a rayuwata, ban tab'a sanin wani abu wai shi tsoro ba, sannan kuma ban tab'a sanin b'acin rai ba, kana bansan meye fad'uwar gaba ba, kasan ko me yasa?
Sabo da na taso cikin tsaro da kariya, sannan kuma na taso cikin gata.
Amma tun a karo na da kai na farko komai nawa ya fara sauyawa, b'acin ran da ban san sa ba kasa nasan sa a ranar, fad'uwar gaban da ban santa ba kasa naji ta a ranar, magana da yinta ke wahalar dani kasa ta zamto abaryina ta dole.
Dan haka ayau yau d'in nan, a kuma yanzu-yanzun nan nake son sanin abun da ka taka."
Ta fad'a cikin wani irin yanayi, tukun ta fara d'an d'aga k'afafuwan ta tana mai zagayasa a wurin da yake, kana ta sake dawowa gaban sa ta tsaya, tana mai watsa jajayen idanuwan ta a cikin nasa, ta dora da cewar.
"Shin me ka taka? Wane kalar sihiri kake tattare da shi ne? Ya sunan bokan daya baka shi?
Sannan kuma akan me bugun zuciya ta yake sauyawa a duk lokacin da nayi gamo da kai!!! ?"
Ta k'arasa maganar cikin k'araji tana mai d'aga k'afar ta d'aya ta dire ta a k'asa, kana ta d'ora da sakin numfar-fashi idanuwan ta k'ur akan Bir.
Shi kuwa Bir wami irin farin ciki mara misaltuwa ne yaji ya lullub'e zuciya da ruhin sa, sabo da fahimtar da yayi ba shi kad'ai bane ya afka kenan.
Tabbas sunan da iya ta sanya masa yana gab da zamtowa na gaskiya, wato Jarumi, domin kuwa ya riga da ya sani muddin Gimbiya ta zama tasa to idan da akawai abun da yafi Jarumi ma za'a kira sa da shi.
Hakan ne yasa sa sakar mata murmushi kawai, yana mai sake kafeta da tsumammun idanuwan sa da suke d'auke da wani irin sinadari a cikin su amai-makon ya bata amsar ta.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir yadda kasan saukar tafasash-shen ruwan dalma akan ta haka take jin saukar murmushin sa a cikin jikin ta.
Lokaci d'aya jikin ta ya k'ara d'aukar kyarmar b'acin rai, sabo da ganin da tayi tamkar yana shirin raina mata hankali, tunda gashi nan amai-makon ya bata amsar ta sai kafeta da yayi da idanuwan sa yana aiko mata da murmushi ma.
"Wallahi! Wallahi Azaba mai rad'ad'i zata hau kanka, irin wadda tun da kazo gidan duniya baka tab'a jin labarin ta ba balle har ka ganta muddin kayi wasa da kalami na, dan haka ka gaggauta bani amsar tambaya ta tun kafin raina ya k'arasa dagulewa, hukunci na ya hau kanka."
Gimbiya Tasmir ta sake fad'awa Bir, jijiyoyin kanta na k'ara futowa rad'a-rad'a akan goshin ta.
"To idan kuma ban shirya fad'ar amsar ba fa, ko kuma nima nace ban santa ba fa?"
Bir ya fad'a cikin tsantsar farinciki, yana mai lumshe idanuwan sa.
"Tabbas ko hakan tamkar dai-dai yake da ka kira mutuwar ka kai da kanka zuwa gare ka domin ta d'au ranka, domin kuwa azaba ta ta huce gaban kwatance, dan haka dak'ik'a d'aya kawai na baka, ka gaggauta bani amsa ta ko kuma komai ma ya faru da kai k'ask'antacce mara galihu."
"To banda amsar nace miki 'yar gata."
Bir ya fad'a yana jifan ta da murmushin sa tamkar ba zagin sa ita tayi ba.
Wani irin juyi Gimbiya Tasmir tayi daga wurin da take, tukun ta mik'a hannun ta-tana mai kamo linzamin dokin ta, kana ta d'ane kansa tana mai rumtse idamuwan ta, tare da mik'ar da takobin ta-ta saita Bir da ita.
Wasu irin surutai tayi da matuk'ar k'arfi, tana mai nuna Bir da takobin nan tata.
Kana ta daki cikin dokin nata da k'afar ta tana mai nuna masa hanyar da zasu bi.
Wata irin iska mai matuk'ar k'arfi Bir yaji ta dake sa, kana ta k'udun-dune sa acikin ta, tukun ta fara wani irin fuzgar sa a cikin k'asa, ta yadda kawai yaji sa yana bin bayan dokin Gimbiya Tasmir daga kwancen da yake a guje.
Sosai take gudu akan dokin nata tana mai nutsawa wata hanya.
Yayin da Bir kuma ke biye da ita abaya iska na jansa da matuk'ar k:arfi, sosai kansa da wasu wurare na jikin sa duk suka farfashe, sabo da duwatsun da yake cin karo da su akan hanyar.
A haka har suka b'ulla gaban wani gini wanda yake d'auke da wata irin k'ofa a jikin sa, wato d'akin Azaba.
Cak dokin Gimbiya Tasmir ya tsaya a gaban k'ofar d'akin nan.
Shima kuwa Bir adai-dai wurin yaji iskar nan ta dena funcikar sa, amma kuma bawai sakin sa tayi gaba d'aya ba, har yanzu dai yana k'udun-dune a cikin ta ne.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir cikin wani irin yanayi ta duro daga kan dokin nata, tukun ta juya b'arin da Bir yake tana kallon sa, kana ta bud'e baki cikin kaushi tana mai fad'in.
"Shin ka shirya bani amsar tambaya ta yanzu ko k..."
Maganar ta-tace ta katse, sabo da yadda taga Bir ya girgiza mata kai yana sakar mata murmushi a yadda yake tun kafin takai k'arshen zancen nata ma, alamun bai shirya ba d'in kenan.
Hakan ne yasa ta juyawa b'arin da k'ofar nan take da wani irin sauri, kana ta d'aga takobin ta sama tama mai nuna k'afor da ita, sannan ta bud'e baki cikin k'araji, tana mai fad'in.
"Gargabiluuu!!!"
Take kuwa a wurin k'ofar ta fara bud'ewa har ta bud'e duka.
Kana ta sake juyawa b'arin da Bir yake tana mai sake yin wasu surutan.
Ai kuwa tini iskar nan ta sake d'ibar sa a guje zuwa cikin d'akin da ya kasance d'an k'arami da shi, mai zagaye da kaskwayen huta a cikin sa suna ta faman ci.
D'aga k'afafuwan ta ita tayi tana mai bin bayan sa.
Shi kuwa Bir iskar nan bata sake sa ba har sai da ta dangana da shi gaban wasu irin k'arafa, tukun ya jisa sakayau gaba d'ayan sa, ta yadda har ya samu damar mik'ewa tsaye yana mai kallon ciwu, kan jikin sa, amma sai dai kuma ko gama mik'ewar baiyi ba yaji wasu irin k'arafa sun tawo daga sama sun d'ad'd'aure sa gagam a jikin su.
Cikin wani irin yanayi na tsantsar firgici da tashin hankali ya d'ago idanuwan sa yana mai watsa su akan fuskar Gimbiya Tasmir da take tsaye a gaban sa, sabo da yadda yaji k'asusuwan jikin sa tamkar zasu warwatse.
"Rai Rai Rai Buuuu Hooo Reeee."
Gimbiya Tasmir ta fad'a tana mai nunasa da takobinta.
Take kuwa yaji wani irin bala'in zafi, irin wanda bai tab'a riskar saba tun da yazo gidan duniya ya lullub'esa, ta yadda har bai san lokacin da ya saki wani irin gigitaccen ihu ba.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir tana jin ya saki ihun nan ta juya tana mai fara d'aga k'afafuwanta ta doshi hanyar waje.
Wasu surutan ta sakeyi a lokacin da ta futa bakin k'ofar d'akin.
Ai kuwa take wani irin bak'in duhu ya mamaye gaba d'aya ilahirin cikin d'akin.
Tukun ta juya tana mai hayewa saman dokin ta.
Sannan ta sake nuna k'ofar da takobin ta tana mai kiran sunan Gargabilu.
Take kuwa k'ofar ta koma ta rufe gam.
Sannan ta damk'i linzamin dokin ta tana mai juyawa suka doshin hanyar da zata mayar da ita gida da tsananin gudu.
_CIGABAN LABARI_
*K'ASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.*
Kallon kallo Yarima Asad da Gimbiya Haddiyal suka cigaba da jifan junan su da shi.
Yayin da Al'amin kuma ya saki baki yana kallon su, zuciyar sa cike da fargabar abun da Yarima Asad zeyiwa Gimbiya Haddiayl, sabo da yadda yaga gaba d'aya cinyoyin sa sun b'aci da madarar shanun nan.
Shi kuwa Yarima Asad a hankali ya k'ara janye idanuwan sa daga kan fuskar ta yana mai sake kallon jikin sa, kana ya k'ara d'agowa yana mai k'ara kafeta da su.
Yayin da yake jin zuciyar sa na wani irin bugu da matuk'ar sauri, abun da tun da yake a rayuwar sa bai tab'a ji ba kenan dan ya tsaya da wata yarinya.
Ita kuwa Gimbiya Haddiyal haka nan taji wani irin haushin sa ya lullub'e gaba d'aya ilahirin jiki da zuciyar ta.
Amai-makon ta basa hak'uri a matsayin ta na wacce tai masa laifi sai tak'i yin hakan gaba d'aya, a karshe ma sai idanuwanta da ta janye daga cikin nasa a hankali.
Kana ta mik'e ta juya tana mai fara d'aga k'afafuwan ta da niyyar komawa.
Amma sai ji tayi an cafki yastun hannuwan ta da matuk'ar sauri.
Cak ta tsaya a wurin da take tana mai rumtse idanuwan ta, sabo da yadda taji wani irin abu ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har izuwa 'yantsun k'afafuwan ta a lokacin da ya rik'o yatsun hannun nata.
Kafin daga bisani kuma ta fara juyowa gare sa fuskar nan ta ta a matuk'ar d'aure.
Ido hud'u suka suka sakeyi da shi yana mai cigaba da kallon ta da tsumammun idanuwansa.
'Dauke nata idanuwan tayi daga kan fuskar sa, tana mai mayar da su kan 'yantsun hannuwan sa da suka kasance had'e da nata wuri d'aya.
'Dan taune leb'enta tayi na k'asa da d'an k'arfi, tana mai jin wani irin mugun bak'in ciki da takaici na cakar ta, kafin daga bisani kuma ta janye idanuwanta daga kan 'yantsun nasu, tana mai mayar da su kan fuskar Yarima Asad.
Hakan da Yarima Asad ya gani ne ya sanya sa sakin hannun nata da sauri.
Yayin da ita kuma ta hurga masa wani irin kallo, kafin ta juya tana mai kama hanyar da ta biyo tazo wurin, ba tare da ta d'auki ko k'waryar ta ba.
Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi, yana mai jin yadda tsigar jikin sa ke mimmik'ewa, ga kuma yadda yake ganin kyakkyawar fuskar ta a cikin idanuwansa, zai iya cewa tun da yake a rayuwa bai tab'a cin karo da mai kyawun ta ba ko a cikin larabawan da yayi rayuwa da su kuwa.
Lokaci d'aya yaji gaba d'aya komai nasa ya sauya a kanta, kayan da suke sanye a jikin ta da yake musu kallon na mahaukata a lokacin da suka shigo cikin masarautar yaga masu su, yanzu kuma sai yaga sunyi bala'in kyau a jikin ta ita.
Ko da ba a fad'a masa ba yasan ita d'in bagidajiya ce, duba da yadda yaga yanayin mutanen garin nasu suke, ga kuma kalar shigar da ya gani sanye a jikin ta.
To amma mai yasa ta kasa basa hak'uri bayan tasan itace tayi masa laifi.
Ya raya haka a cikin ransa yana mai sake d'aga idanuwansa yabi bayanta da kallo.
Kafin daga bisani kuma ya mik'e tsaye zumbur daga kan shimfid'ar da yake, yana mai shirin bin bayan ta.
Da sauri Al'amin ya mik'a hannun sa yana mai kamo tafin hannun Yarima Asad da shi.
Hakan da Yarima Asad yaji ne ya sanya sa dakatawa, yana mai juyowa ya watsa idanuwan sa akan fuskar Al'amin.
Girgiza masa kai Al'amin yayi yana mai masa alamar da ya dawo ya zauna da idanuwansa.
Yayin da a zuciyar sa kuma mamakin Asad ya gama rufe sa gaba d'aya, domin kuwa k'wayoyin idanuwan sa kawai ya kalla ya fahimci yanayin da yake a ciki.
Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi ba tare da ya iya cewa Al'amin komai ba, tukun daga bisani ya dawo jiki a sanyaye yana mai komawa wurin da ya tashi ya zauna.
Kana ya k'ara bin hanyar da Gimbiya Haddiyal tabi da yanzu har an den hangon ta ma da idanuwan sa.
Sosai hoton kyakkyawar fuskar ta ya zauna daram a cikin idanuwan sa, ta yadda har yake jin tamkar har yanzu tana zaune ne a gaban sa.
A hankali ya durk'usar da kansa k'asa yana mai k'ara kallon madarar da take kwance akan sitirar jikinsa, kana ya d'an d'aga lab'b'ansa yana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa.
Yayin da shi kansa yake mamakin abun da ya hanasa hukunta wannan bagidajiyar bak'auyiyar yarinyar, akan wannan laifin da tayi masa har ta juya ta ta tafi.
Wai yau shi Asad ne mace tayi masa laifi kuma ya barta ta juya ta tafi ba tare da ta basa ko hak'uri ba, laifi ma babban laifi ba k'arami ba.
Shi da mata suke hauka akan sa, suke kuka tare da kaff-kaffan abun da zai b'ata masa ransa, suke jin dad'i aduk lokacin da ya daga ido ya kalle su.
Mata masu aji masu ilimi, kana wa'yan da sukafi k'arfin kud'i, amma sai gashi yau wata can 'yar k'auye ta b'ata masa jiki ya kasa yin komai akan ta, asalima ko wani haushin ta baiji ba a ransa, sai zallar kyawun hallitar ta da ta tafi ta barsa da ita a cikin idanuwan sa.
Suna a cikin wannan yanayin Habu ya dawo fuskar sa d'auke da murmushi.
Amma sai dai kuma yana zuwa gaban shimfid'ar da suke zaune akai yaja ya tsaya cak, murmushin kan fuskar tasa na gushewa, yayin da idanuwan sa kuma suka kasance k'ur akan k'waryar madarar nan, tare da jikin Yarima Asad da ya gansa a b'ace.
"Shin meye hakan nake gani?
K'waryar madara ta kife a jikin ka?
Kar dai kuce mun ba Haddiyal bace ta kawo madarar nan da kanta, wata ta sanya ta kawo muku har tazo ta kifa maka ita a jiki."
Habu ya fad'a ransa a tsantsar b'ace.
Kafin daga bisani kuma ya fara k'ok'arin juyawa da sauri, da niyyar yaje ya samu Gimbiya Haddiyal dan yaji bayanin abun da ya faru.
Amma sai dai ko sauke k'afar sa d'aya da ya d'aga bai kaiga yiba Yarima Asad ya mik'a hannu da sauri yana mai cafko 'yan yatsun sa.
Hakan da Habu yaji ne ya sanya sa juyowa gare sa yana mai zuba masa idanuwan akan fuskar sa.
Shi kuwa Yarima Asad girgiza masa kai yayi yana mai d'an sakin murmushi, kana ya bud'e baki yana mai cewa.
"To yanzu da ka juya cikin fushi ina zaka kenan?"
"Zanje wurin ta ne, domin tamun bayanin yadda akai hakan ta faru, bayan ni da kaina nace mata ta amsa ta kawo muku da kanta."
Ya k'arasa maganar har lokacin ransa a b'ace, yana shirin zare yasun hannun sa daga cikin na Yarima Asad.
Ganin hakan da Yarima Asad yayi ne ya sanya sa sake damk'ar yastun nasa da k'arfi.
Tukun ya girgiza masa kansa fuskar sa d'auke da murmushi, kana ya d'aga lab'b'an sa yana mai fad'in.
"To idan ita d'in ce ta kawo da kanta kuma fa?"
"Ok kana nufin kace mun ita Haddiyal d'in ce ta kifo maka madarar da kanta tsabar tana hauka ko?"
Habu shima ya fad'a idanuwan sa akan Yarima Asad.
Yayin da shi kuma Yarima Asad ya lumshe nasa idanuwan, yana mai jin gaba d'aya yanayin sa na sauyawa.
Kana daga bisani ya sake wara idanuwan nasa akan fuskar Habu, sannan ya bud'e baki yana mai fad'in.
"To yanzu dai idan ma hukunci kake son kayi ba kowa ya kamata kayiwa ba face ni, domin kuwa ita har sai da ta juya ta tafi ma tukun na kifar da k'waryar madarar, ta hanyar zamewar da tayi a hannu na a lokacin da na d'auko ta domin nasha."
Yarima Asad ya samu kansa da fad'awa Habu haka, ba dan komai ba kuwa sai sabo da yadda yaga ransa ya b'aci, kuma ya fahimci muddin yaje wurin ta bazai mata da sauk'i ba.
Wanda sai bayan ya gama fad'ar hakan tukun mamakin abun da yasa sa yayi k'aryar akan waccan kucakar da tayi masa laifi ya lullub'e sa.
"To mema ya dameni ne ni, koda kashe ta ma zaiyi idan yaje d'in da har na rufa mata asiri?"
Yarima Asad ya fad'i haka a cikin ransa bayan ya gama yiwa Habu bayanin nan.
Yayin da Al'amin kuma yayi suman zaune a wurin da yake, idannwan sa akan fuskar Yarima Asad.
Gaba d'aya mamaki ya gama cikasa, ko a mafarki akace masa Yarima Asad zai aikata abun da ya aikata yau wallahi tallahi bazai tab'a yadda ba, amma sai gashi nan akan idanuwan sa komai ya faru.
Hakan ne yasa sa jinjina kan sa yana mai cigaba da bin Yarima Asad da idanuwa, wanda shi kuma zuwa yanzu ya saki yantsun Habu da ya rik'e yana mai lumshe idanuwan sa.
Shi kuwa Habu jinjina kansa yayi yana mai yadda da abun da Yarima Asad ya fad'a masa, domin kuwa ko kad'an dama shi da farko bai kawo k'anwar tasa ce ta kifar da madarar ba, sabo da yadda ya santa da tsantsar nutsuwa.
Hakan yasa ya d'an sakin murmushi, kana ya bud'e baki yana mai fad'in.
"To yanzu abun da za'ayi shine, tashi zakuyi mutafi part d'in mu sai kayi wanka ka canza kaya, in yaso sai akawo muku wata madarar bayan ka shirya kusha ko."
Ya fad'a yana mai rik'o hannun Al'amin.
Ba tare da Yarima Asad yace komai ba gaba d'ayan su suka mik'e suna masu bin bayan sa.
A b'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa, cikin tsantsar k'unar rai ta k'arasa cikin d'akin ta.
Direct ta wuce bathroom d'in ta da yake a cikin d'akin.
Tana mai zuwa ta kunna ruwa, bayan ta shafe dai-dai saitin wurin da Yarima Asad ya rike na hannun ta da sabulu ta dinga dirzar sa.
Tana yi hawayen bak'in ciki na tsiyayowa daga cikin idanuwan ta suna wanke kaykkyawar fuskar ta.
Tabbas Yarima Asad ya shigo cikin sahun mutanen da tafi tsana a rayuwa ta sama da komai, ta yadda har ya zamto mutum na farko daga cikin su.
Yayin da shi kuma Yariman Yamma ya zamto na biyu.
Ba dan komai ba kuwa sai sabo da yadda gaba d'ayan su suka rik'e hannun ta, wanda ko kad'an basu cancanci su zamto wa'yan da zasu kalli ko da fuskar ta ba, hakan yasa take jin tamkar ba tayiwa Gid'ad'on ta adalici ba da ta bari hakan ta faru.
A yanzu tafi jin haushin Yarima Asad ma akan Yariman Yamma.
Sabo da shi kallo d'aya tayi masa ta fahimci gaba d'ayan sa zubin 'yan iskan samarin nan gare sa, duba da irin sitirar da ta gani sanye a jikin sa, wacce ko kad'an batayi kama da ta d'an musulmi ba, musulmin ma kuma wai hausa fulani, hausa fulanin ma wai d'an Sarki.
Wannan dalilin ne ya sanya ta k'arajin haushin sa fiye da yadda take jin na Yariman Yamma, domin kuwa ita ta tsani mu'amala da 'yan iskan mutane a rayuwar ta.
Ba ita ta bar dirzar hannun nata ba har sai da taji ya fara yi mata rad'ad'i, tukun ta hak'ura ta barsa haka tana mai juyawa ta doshi k'ofa, yayin da har lokacin kuma idanuwan ta suke cigaba da zubar hawaye.
Bata tsaya ba har sai da ta dangana da gaban dressing mirrow d'in ta, kana taja ta tsaya a gaban sa tana mai kallon kanta a cikin sa.
Kafin daga bisani kuma ta rumtse idanuwan ta da matuk'ar k'arfi, sannan ta bud'e su tana mai d'aga lab'b'an ta cikin sanyi tace.
"Shin har sai zuwa wane lokaci ne zaka bayyana a gareni Gid'ad'o am? Har tsawon wane lokaci zan cigaba da zaman jiran ka?
Ka taimake ni, ka taimaki rayuwa ta ka bayyanar mun a zahiri Gid'ad'o am, domin kuwa rashin ganin ka a zahiri tamkar barazana da rayuwata ce a gidan duniya, rashin bayyanar ka ya sanya har wasu mutane can suke k'ok'arin rik'e wani sassa daga jiki na, bayan kuma kai kad'ai ne mutumin da ya dace da rik'e su, domin kuwa kaine kad'ai mammalikin su.
Tabbas zuciya ta na gab da tarwasewa muddin rayuwa zata cigaba da had'ani da irin wa'yancan mutanen, wannan dalilin yasa naji na tsane su fiye da yadda na tsani mutuwa ta, domin kuwa ni d'in gaba d'aya na takace, tamkar yadda kaima ka zamto nawa ni kad'ai."
Ta k'arasa maganar tana mai durk'ushewa akan guiwoyin ta ta cigaba da sakin kukan ta har da su shash-sheka.
Yayin da fuskar Yarima Asad kuma tak'i b'acewa daga cikin idanuwan ta, wanda harda hakan yasa take k'arajin tsanar sa fiye da wacce take yiwa Yariman Yamma, sabo da ada fuskar Gid'ad'on ta kawai ce ke mata gizo acikin idanuwan ta, amma sai gashi yau fuskokin sun zama biyu, wato ta gid'ad'o'n ta da kuma ta waccan mutumin mai siffa da 'yan iska da suka had'u.
*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*
Sosai hawaye suke kwaranya daga cikin idanuwan Gimbiya Tasmir tana tafiya.
Wani irin rad'ad'i da suya take jin zuciyar ta nayi mata, idan ta tuna yadda wancan k'ask'antaccen bawan ya had'a jikin sa da nata.
Ji take inama ace Ubangiji Gargabilu ya d'auki rayuwar ta tun kafin zuwan wannan ranar, ji take inama ace baya na komowa, tabbas da babu abun da zai sa tayi gigin cewa zata dake sa a yau, ballan tana har azo ga wannan d'anyen iskancin da fitsarar daya aikata a mata.
Wai ace kamar ita, kamar ita Gimbiya Tasmir, yarinya mai tsantsar kwarjin da Izza, aka samu bawan da ya iya tsayawa a gaban ta ya kalli cikin idanuwan ta, sannan kuma bai ma tsaya a iya kar kallon cikin idanuwan nata ba har sai da ya dangana da had'a jikin sa da nata wuri d'aya.
"Inaa! Wallahi hakan bazai yuwu ba!
Nayi rantsuwa da Ubangiji Gargabilu sai naga bayan ka, sai dai duk abun da zai faru ya faru, domin kuwa bazan tab'a barin ka ba kaci banza."
Gimbiya Tasmir ta fad'a da wani irin k'araji, tana mai durk'ushewa a kasa akan guiwoyin ta, yayin da ruwan hawaye kuma suke cigaba ambaliya daga cikin idanuwan ta tamkar an bud'e famfo.
"Shi me yasa rayuwa zakiyi mun haka? Me yasa duniya zaki juyamun a lokaci guda? Me yasa izza ta, kwajini na tare da k'arfin ikona zasu nemi tarwatsewa a lokaci guda? Shin wane laifi na aikata maka Ubangiji Gargabilu da har zaka hukunta ni ta hanyar turo k'ask'antacce bawa gare ni? Me yasa, me yasa zaka hanani hukun tasa Baba?
Me yasa hakan zata faru dani?"
Ta k'ara fad'a cikin k'araji, hawaye na cigaba da tsiyayowa daga cikin idanuwan ta, abun da ita kanta bazata ce tasan lokacin da ta d'auka rabon ta da kuka ba, sai gashi yau tana yin sa har da k'araji ta sanadin Bawa, Bawan ma kuma k'ask'ancce wanda ko shi kansa bai san suwaye iyayensa ba, Bawan ma d'an tsuntuwa.
Kafin daga bisani kuma ta sake mik'ar da takobinta tana mai fad'in.
"Shairamaaa!!!"
Ta fad'a da wani irin k'araji bayan ta rumtse idanuwan ta.
Take kuwa wannan dank'areriyar macijiyar tata ta bayyana tana mai karkad'a harshen ta.
Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir ta k'arasa gaban ta da sauri, tana mai durk'usawa k'asa ta damk'i kanta da matuk'ar k'arfi.
Tukun daga bisani ta bud'e baki cikin tsantsar kuka tana mai fad'in.
"Shin ina taimakon da akace zaki yimun a rayuwa Shairama? Ina Garkuwar da akace zaki zame mun a gidan duniya Shairama? Kana ina hasken da akace zakina haskan gaba na da shi Shairama?
Shin wai meye amfanin ki ma agare ni Shairma, bayan gashi nan kina gani ana hulak'anta ni ana take izza ta da kwarjini na akan idanuwan ki ba tare da kin iya komai ba?
Shin taya ya zansan dalilin da yasa Baba ya hanani hukunta wancan matsiyacin Bawan, wane irin k'ulli ne yake ak'asa da har hakan zata kasance? Wata irin alak'a ce take a tsakanin su da har take shirin ta ture wacce take tsakani na da shi?
Tabbas zan binciko, kuma kome yene amsar muddin na gano sa to sai na tarwatsa sa!"
Ta k'arasa maganar tana mai sakin kan macijiyar da ta damk'a tare da sake mik'ewa tsaye zumbur.
Kana ta d'ora da fad'in.
"Baki da amfani a gareni Shairma, ba kiyi mun komai ba a rayuwa, kana ban ga amfanin zaman ki a tare da ni ba tun da har kin kasa bani kariya akan wancan dak'ik'in Bawan!
Tabbas baki da amfani, ki tafi bana bukark'i bana buk'atar ki tattare dani yanzu Shairama."
Gimbiya Tasmir ta fad'a da wani irin k'araji tana mai shurin macijiyar nan da k'afa.
Take kuwa a wurin ta b'ace b'at tamkar ba'a tab'a yin ta.
Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir ta fara d'aga k'afafuwan ta tana mai dosar hanyar da zata sadata da part d'in su ta baya, ba tare da ta koma filin bikin nan ba.
Acan cikin filin biki kuma sosai hankalin Iyar Bayi yayi bala'in tashi, jikin ta ya dinga wata irin karkarwa, gumi na yanko mata daga can wurin da take a tsaye, domin kuwa akan idanuwanta komai ya faru na abun da Gimbiya Tasmir tayiwa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 76