guda ukku yana mai ajesu agefe, tukun daga bisani ya juya ɓangaren da wasu karikitai suke yana mai sa hannu ya ɗauki wani ƙaton ƙullin tsumma ya a jesa agefe, sannan ya juya yana mai kai idanuwan sa tare da yatsun sa zuwa cikin farantin dake agaban sa.
Akan yashin dake cikin farantin ya ɗora yatsun sa biyu, tukun ya fara wasu zane zane akan yashin yana mai furta wasu kalmomi da ƙarfi, bayan ya rumtse idanuwan sa.
Ya ɗauki kimanin daƙiƙa kusan ukku ahaka, tukun ya buɗe idanuwan sa yana mai kaisu kan zanen da yayi.
Jijjiga kansa yayi, sabo da ganin da yay abun ya masa kamar yacce yake so, tukun daga bisani ya juya ɓarin da ya ajiye wannan ƙullin tsuman yana mai ɗaukar sa, tare da layoyin da ya aje agefe, tukun ya miƙe tsaye cak yana mai tsayawa agaban hutar dake ci acikin kasko.
Kwance ƙullin tsuman nan yayi yana mai riƙe sa da hannu ɗaya, yayin da ɗayan hannun nasa kuma ya danƙule layoyin da ya riƙe acikin sa da matukar Ƙarfi, sannan ya kuma ya rumtse idanuwan sa da ƙarfi, kana ya buɗe baki yana mai fara yin wasu irin surutai, tare da fara tsiyaya wannan garin da yake cikin tsumman sa acikin hutar kasko.
Yana fara tsiyayawar gaba ɗaya hutar cikin kaskwayen dake cikin ɗakin duka suka mutu atare!
Wata irin gigitattar ƙara Sarki Barbaru ya saki da ganin hakan, wacce tayi sanadin da yasa Boka mai hutar kasko ya buɗe idanuwan sa da tsantsar sauri.
Da matuƙar sauri shima yaja baya yana mai sakin tsumman da layoyin da suke riƙe ahannun sa, sabo da yarce yaga gaba ɗaya hutar dake cikin kaskwayen sun mace, aƙoƙarin sa na ganin yayi abun da zai yi sanadin saduwar su da Gargabilu, abun da bai taɓa faruwa ba kenan tun wanzuwar su aduniya, wato mutuwar Hutar kasko, domin kuwa kullum cikin ƙara izata ake yi.
"Shin meke shirin faruwa da mune haka, mai ya sanya Hutar kasko zasu mutu ne Boka? Shin wane irin bala'ine yake shirin riskar mu, domin kuwa ko atarihi ban taɓa jin ance hutar kasko ta mutu ba, sai yanzu da abun ya faru agaba na."
Sarki Barbaru ya faɗa cikin tsantsar ruɗu da matuƙar tashin hankali, yana mai matsawa kusa da boka mai hutar kasko, da yake ta aikin zare idanuwa shima.
"Tabbas ba kai kaɗai ba, koni dana fika shekaru ban taɓa ganin hakan ya faru ba, sannan kuma ko atarihi ban taɓa jin ance akwai ranar da hutar kasko ta taɓa mutuwa ba sai yanzu, wanda hakan kuma shike nufi da cewar wannan abun yafi ƙarfin har abun bauta Gargabilu, domin kuwa ta wannan hanyar ce kawai muke da ikon saduwa da shi harya bamu mafuta, amma sai gashinan gaba ɗaya ta toshe hany...."
Sautin ihun da suka jiyo awaje da matuƙar ƙarfi ne ya sanya Boka mai hutar kasko tsayawa da maganar da yake, ba tare da yakai ƙarshen ta ba, tukun daga bisani suka fara ɗaga ƙafa suna masu dosar hanyar futa daga cikin ɗakin cikin sauri, dan suga abun da ke shirin faruwa.
*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN UNGUWAR ƊAN TANKI.*
_WASHEGARI_
Yadda Aishatu taga dare haka taga rana bata iya rumtsawa ba ko kaɗan, sosai mutuwar mahaifin nata ta girgiza ta, sannan kuma tayi matuƙar gigitata, tayi kuka iya kuka yadda kasan ranta zai futa, bata taɓa sanin haka zafin mutuwar iyaye yake da tsantsar raɗaɗi ba, sai ajiya da abun ya risketa.
Kwana sukai cir Ishaƙ na aikin rarrashin ta, aƙarshe ma da yaga takasa yin shiru sai ya sanya ta taje ta ɗauro alwala, tazo tai ta sallolin nafula tana mai roƙawarwa mahaifin ta rahama awurin Ubangiji.
Suna futowa daga masallacin asuba Ishaƙ yayo gida danniyar yazo ya shirya kayan sa, sannan suyi sallama da mutan gidan, domin kuwa jirgin dake tashi ƙarfe shida na Ƙasar Malin zasubi ayau ɗin, sai dai kuma me, yana shigowa cikin ɗakin yay tsaye awuri ɗaya yana mai bin Aishatu da idanuwa, sabo da yarce ya ganta zaune akan kujera sanye da hijab, ga kuma jakar kayan ta da nashi ajiye agefe, alamun shi kawai take jira ya ƙaraso su tafi, gashi shi kuma ko kaɗan bai tsara tafiyar da ita ba. To ta ina ma zai fara cewa zata bisa irin wannan doguwar tafiyar, wacce har sai an kwana kusan biyu ahanya, bayan ga halin da take ciki. Ya raya hakan acikin ransa daga bakin ƙofar da yake atsaye, tukun daga bisani ya fara takawa yana mai dosar wurin da take, idanuwan sa akan fuskar ta.
Yayin da ita kuma ta durƙusar da kanta ƙasa tana mai wasa da farcen hannun ta.
Agafen ta ya zauna yana mai miƙa hannuwan sa duka biyu ya riƙo nata da su, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amma dai kin san ba tare zamu tafi ba kina cikin wannan yanayin ko Aishatu, naga kin haɗo jakun kuna har guda biyu."
Dasauri ta ɗago kanta tana mai kallon sa, kafin daga bisani kuma hawayen da tasamu ta tsayar da su tun ɗazu suka sake ɓallewa daga cikin idanuwan ta da matuƙar gudu, kana ta buɗe baki cikin dashash-shiyar muryar ta tana mai faɗin. "Dan Allah kar kace bazan bika ba Abban Ahmad, domin kuwa muddin banje ba to bazan taɓa samun natsuwa anan ɗin ba. Ina son naje naga su Dada tare da sauran ahalina, ina son naje nayi ta'aziyyar mahaifina, sannan kuma na karɓi gaisuwar sa.
Na roƙeƙa da sunayen Allah kyawawa tsarkaka kar kace bazan bika ba Abban Ahmad." Ta ƙarasa maganar cikin kuka.
Yayin da shi kuma ya lumshe idanuwan sa yana mai murza tafin hannun ta da suke a cikin nasa, ba tare da yace komai ba, tukun daga bisani ya buɗe idon sa yana mai faɗin. "In banda ke Ummin Ahmad, ke yanzu ahaka yarce kike ai ko nida kaina nace ki shirya kije ya kamata ki tausayawa kanki kice bazaki ba, dan haka ina son kiyi haƙuri har zuwa lokacin da Allah zai saukeki lafiya, sai na ɗauke ku na kaiku dukan ku har yarama insha Allah, dan kuwa ke da kanki kin riga da kin sani wanda ya rasu ya riga da ya rasu, babu tayarce za'ayi ya dawo, sannan kuma koda bakije ba suma baza suji komai ba, sabo da sun san irin yanayin da kike ciki, sab...." "Assalamu alaikum." Muryar Kaka ta ratsa kunnuwan su daga bakin ƙofa, wacce ta sanya Ishaƙ dakatawa daga zancen da yake ba tare da ya ƙarasa ba, yana mai sakin hannuwan Aishatu.
"Wa'alaikumu salam." Ya amsa mata yana mai gyara zaman sa akan kujerar da yake.
Yayin da ita kuma kaka ta danno kanta zuwa cikin ɗakin bakin ta na faɗin. "Me kuma ya zaunar da kaine har yanzu, bayan kasan irin tafiyar da zakuyi bata wasa bace ba, tun ɗazu nake jiran naji futowar ka amma naji shiru, shi yasa ya nace bara nazo naga abun da ke faruwa." Kaka ta faɗa tana mai zama akan kujerar da take facing ɗin wacce suke akai.
"Wai Aishatu har yanzu kia nufin kice baki dena kukan nan ba?" Kaka ta sake faɗa tana mai kallon ta, fuskar ta cike da tausayin ta.
Nannauyan numfashi Ishaƙ ya sauke, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. "Dalilin da ya hanani futowa kenan Umma, wai kin ganta nan ta dage sai mun tafi tare, gashi ma har da haɗa kayan ta tayi." Ya faɗa cikin sanyi yana mai kallon mahaifiyar tasa.
Jim tayi itama ba tare da tace komai ba tana kallon Aishatu, tukun daga baya ta buɗe baki cikin sanyi tana mai faɗin. "Aishatu ina so..." "Dan Allah, dan rajara fiyayyen hallita, na roƙeƙi Umma kar kema kice bazan je ba, sabo da ayarce nake ji ayanzu muddin banje ba to bazan taɓa samun sauƙi ba acikin raina. Ina son nima naje akarɓi gaisuwar mahaifina tare dani, sanna kuma naga yarce ahalina suke ciki." Ta faɗa cikin kuka bayan ta sauko daga kan kujerar da take, ta durƙushe akan giuwoyin ta gaban Kaka.
Yayin da Kaka kuma tayi shiru ba tare da tace komai ba, sai tinani da ta tafi ma tana kallon Aishatu, tukun daga bisani ta girgiza kanta tana mai juyawa ta kalli Ishaƙ, sannan ta buɗe baki cikin sanyi tana mai faɗin. "Ka barta ku tafi tare Ishaƙ, nina sanya ka." Ta faɗa tana mai rumtse idanuwan ta.
"Amma Umma bakya ganin ha..." "Dan Allah karkace komai ishaƙ, domin kuwa komai da kake ganin ya faru agidan duniya muƙaddari ne daga Allah, sannan kuma babu wani abu da yake faruwa face dama can Allah ya rubuto zai faru, dan haka kuje wurin Baban ku kuyi masa bayani, muddin yace ku tafi tare to kuje Allah shine zai kare ku, kuma Insha Allah zaku isa lafiya kamar yacce zaku bar nan lafiya." Kaka ta faɗa cikin sanyi tana mai kallon sa.
Taune leɓen sa yayi na ƙasa tare da rumtse idanuwan sa, domin kuwa ko kaɗan shi dai bai so Aishatu zata bisa ba, sai dai kuma babu yarce zaiyi, tunda har mahaifiyar sa tace ya tafi da ita bai isa yaja da umarnin ta ba, sai dai kuma azuciyar sa yana fatan Allah yasa idan sunje wurin mahaifin nasa, shi yace bai aminta ba.
Miƙewa tsaye kaka tayi tana mai faɗin. "Ni na tafi, sai ku same ni aɗakin Baban ku, kuma kutabbatar kun gama duk shirin da zakuyi yanzu kun futo, sabo da bana son ku huce yau ba tare da kun shiga cikin Ƙasar Malin ba." Ta ƙarasa maganar tana mai fucewa daga cikin ɗakin.
Zaman ta keda wuya sai gasu nan suma sun shigo ɗakin bakunan su ɗauke da Sallama, kasancewar dama gaba ɗaya sun riga da sun gama shiryawa tas.
Ko da Ishaƙ ya faɗawa Baba yadda ake ciki, shima ɗin sai ya zamto ya faɗi magana irin wacce Kaka ta faɗa.
Hakan yasa ba dan ran Ishaƙ yaso ba ya haƙura ya ɗauki jakun-kunan nasu, bayan sunyi sallama da iyayen nasu suna masu yi musu fatan Alkhairi suka tafi.
Ƙarfe shida saura dai dai suka isa bakin ruwa.
Lokacin da sukaje sun tarar da har an fara shiryawa, domin kuwa duka -duka baifi minti goma ya rage jirgin ya tashi ba, hakan yasa Ishaƙ ya huce cikin sauri yana mai zuwa wurin da ake biyan kuɗi, tare da sauran abubuwa yayi musu komai su ukkun.
Tukun suka shige cikin tafkeken jirgin ruwan da yake ɗauke da komai na buƙata acikin sa.
Tafkeke ne jirgin ba kaɗan ba, gaba ɗayan sa rufe yake da tamfol saman sa, wato ba'a iya ganin mutanen da suke cikin sa daga waje.
Ƙarfe shida dai dai jirgin nasu ya tashi, yana mai ɗaukar hanyar da zaibi ta kaisa Ƙasar Malin a cikin ruwan nan.
ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.
Dan-dazon mutanen cikin masarautar ne suke ta ɓullowa ta ko ina, hankulan su abala'in tashe, banda ihu tare da sunan Gargabilu babu abun da bakunan su ke iya furtawa, sabo da yarce gaba ɗaya garin ya ƙara rikiɗewa yayi wani irin jajahur daga ɓangaren kudu, yayin da ɓangaren arewa kuma ya kasance baƙiƙƙirin, ga kuma ƙasa da take wani irin tashi sama, ƙura na buɗe ko ina da ina.
Cikin tsantsar ɗimuwa Sarki Barbaru ya buɗe baki yana mai faɗin. "Kayi wani abun mana Boka mai hutar kasko, kayi wani abun mana tun kafin komai ya ƙarasa lalace." Ya faɗa cikin hargowa yana mai kallon Boka mai hutar kasko.
Yayin da shima Boka ya sake ruɗewa fiye da da, sabo da yadda yaga garin nasu na sake juyewa.
Da matuƙar ssuri ya juya yana mai komawa cikin ɗakin sa.
Ko daƙiƙa biyu baiyi aciki ba sai gashi nan ya dawo hannuwan sa ɗauke da wasu irin layoyi, tukun ya buɗe baki tun daga inda yake yana mai faɗin. "Na tuna da hanya ɗaya da tarage wacce zanbi, domin na samu ganawa da abun bauta Gargabilu, dan haka yanzu maza maza ka biyo ni zuwa bakin daji gaban ruwan ruwa, domin kuwa anan ne kaɗai zanyi iya ai watar da wannan aikin." Ya faɗa yana mai juyawa ya doshi hanyar ba tare da ya jira Sarki Barbaru ba, yayin da shi kuma Sarki Barbaru ya juya cikin sauri yana mai komawa wurin da dokin sa yake.
Tun daga nesa ya buga tsalle yana mai hayewa saman dokin, tukun ya damƙi linzamin sa yana mai saita masa hanya.
Wata irin zabura dokin yayi yana mai bin hanyar da mahaukacin gudu, yarce kasan zai tashi sama.
Yayin da jama'ar nan kuma suke ta cigaba da ihun kiran Gargabilu, hankulan su na tsantsar sake tashi.
Acikin daƙiƙun da basu zarta biyar ba Boka da Sarki Barbaru suka isa bakin daji, wanda yake zagaye da wani irin tafkeken ruwa, da ko ƙarshen sa ba a iya hange ta kowane ɓangare nasa.
Gaban wani kogo da yake manne jikin wata danƙareriyar bishiya da take manne a gefen ruwa suka ƙarasa.
Hannu Boka mai Hutar kasko ya zira acikin kogon yana mai zaro wani baƙin kasko, yayin da cikin kaskon kuma ya kasance ɗauke da wasu irin karikitai kala-kaka acikin sa.
Cikin sauri yasa hannun sa yana mai furfuto da duka abubuwan dake cikin kaskon, sannan ya ɗebi wasu daga cikin su yana mai zubawa aciki, kana ya damƙi wata laya guda ɗaya da take riƙe ahannun sa da matuƙar ƙarfi yana mai rumtse idanuwan sa tare da faɗin. "Gargabiluuuu!"
Take awurin kaskon nan ya kama da wuta Bal, bal, bal, yana ci yarce kasan wanda aka zubawa fetir acikin sa, yayin da boka mai hutar kasko kuma ya cigaba da kiran sunan Gargabilu da ƙaraji, ta yarce har wurin ke amsawa yana mai haɗawa da wasu irin surutai, har kuma lokacin bai fasa matse layar dake cikin tafin hannun sa.
Ƙara tashi hutar nan tayi tana ci sosai, tukun daga bisani harshen ta ya rabu gida biyu daga tsakiyar su wani irin baƙin hayaƙi na tashi, kana kuma daga saman hayaƙin ya zamto kalar shuɗi.
Sosai Hutar ta kasu kala kaka har kimanin kusan kala biyar, yayin da Boka mai hutar kasko kuma yayi shiru daga furucin da yake yana mai durƙushewa awuri ɗaya ya nutsu sosai, sai dai kuma har lokacin bai buɗe idanuwan sa ba, kamar yadda bai buɗe layar dake cikin tafin hannun sa ba.
Yayin da ta fannin Sarki Barbaru kuma yaji wani rin daɗi, sabo da fahimtar da yay Boka mai hutar kasko ya samu damar ganawa da abun bautar su.
Sai da ya ɗauki kimanin daƙiƙa talatin rumtse da idanuwan nasa, tukun daga bisani ya sake miƙewa tsaye yana mai buɗe idanuwan sa, yayin da kalar Hutar nan kuma ta koma ja kamar yacce take tun farko.
"Shin meke faruwa ne Boka?" Sarki Barbaru ya jefowa Boka mai hutar kasko tambaya cikin sauri, yana mai matsawa kusa da shi.
"Haƙiƙa Al'amarin babba ne kamar yacce na faɗa maka tun farko, domin kuwa ayarce ubangiji Gargabilu ya sanar mun, sannan kuma nima na gani da idanuwa na, muddin bamuyi da gaske ba to komai na shirin rushewa, idan nace kuma komai ina nufin komai da komai." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana mai kallon Sarki Barbaru.
Yayin da shi kuma kwata kwata ya kasa fahimtar abun da yake nufi ko kaɗan, hakan ne yasa sa ya buɗe baki cikin sauri yana mai faɗin. "Kamar ya komai kenan Boka, domin kuwa har yanzu ban fahimci komai ba daga cikin abun da kalaman ka suke nufi."
"Tabbas bazaka fahimta ba ayanzu dama na sani, sai dai kuma ayanzu yanzu zan sanar maka tayarce zaka gane.
Da nace maka komai ina nufin komai namu zai lalace, duniyar mu zatazo ƙarshe, tarihin mu zai shafe tun daga na can baya har kawo na yanzu shafewa ta har abada, sunan Baƙar Masarauta zai ɓace acikin littafin tarihin duniya!"
"Shin me kake faɗe ne haka mai tsantsar raɗaɗi acikin kunnuwa Boka? Shin taya ya kake ganin hakan zata faru kuwa?"
"Ta hanyar barin Jinjirin adoron duniya, ko kuma kashe sa!"
"Har yanzu dai ban fahimce ka ba yakai shugaba Boka, na roƙeka da abun Bauta Gargabilu kayi mun yarce zan gane tun kafin ƙoƙon kaina yay bunduga awurin na." Sarki Barbaru ya sake faɗa amatuƙar rikice, da kuma tsantsar ƙaraji.
"Kanka bazai taɓa bunduga ayanzu ba, sai dai ko idan daga baya-bayan ka gama jin bayanin abun da ke faruwa, muddin ba asamu mafuta ba, domin kuwa ni ayanzu zan warware maka komai." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana mai juyawa yay taku ɗaya, biyu, zuwa ukku daga wurin da yake, tukun daga bisani ya sake juyowa ɓarin da Sarki Barbaru yake yana mai cewa. "Za'a samu shigowar wani baƙon Jaririn yaro namiji ne cikin ƙasar nan tamu, sannan kuma zai huce ta cikin jahar mu, shi kuma wannan jaririn bakowa bane face musiba da bala'i gare mu, domin kuwa ayarce ubangiji Gargabilu ya sanar mun kuma na gani da idanuwa na, shi yaron zai zamto mana musiba da bala'i acikin masarautar mu, domin kuwa zai wargaza ta, sannan kuma zai rusa gaba ɗaya tarihin mu, zai dawo ya yaƙe mu alokacin da bamuyi tsammani ba bayan ya girma, muddin muka barshi ya wuce ta cikin garin nan, domin kuwa gaba ɗaya wannan yanayin sauyawar garin da aka sama ansa mesa ne ta zuwan da zaiyi ya huce ta cikin kwanakin nan, sai dai kuma ni kaina ban san ko awace ranar zai huce ba, amma ayarce ubangiji Gargabilu ya faɗamun shine daga rana irin ta gobe har zuwa nan da makwanni huɗu masu zuwa zai iya hucewa." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana kallon sarki Barbaru.
"To amma Boka babu wata hanya wacce zamubi mu hana wannan mummunan abun faruwa?" Ya faɗa ahaukace, sabo da yarce duka magan-ganun Boka mai hutar kasko suka sake haukatar da shi.
"Akwai abun da za'ayi wanda zai sa agano sa, wannan abun kuma ba komai bane face binciko hanyar da zai bi ya huce ta ita, sannan akarɓe duk wani jariri da aka samu akan hanyar daga hannun uwarsa, bayan an karɓe sa kuma sai akai sa gaban kaskon huta a ajiye sa, daga nan kuma sai aɗaga kibiya ayi kamar za'a caka masa ita aciki, to muddin shine jinjirin zai sanya ƙafafuwan sa ya ture kaskon hutar nan, tayarce har sai ya rabe gida biyu, idan kuma har bashi bane ba, to bazai iya ture sa ba, dan haka sai kawai acaka masa mashin akashe sa duka, idan kuma shine bayan ya ture kaskon, sai aɗauke sa atafi da shi ya zamto Bawa acikin masarautar mu, hakan da za'ayi itace kawai mafuta garemu, domin shine zai zama aƙarƙashin ikon mu, muddin kuma akai kuskuren barin shi ya futa daga cikin masarautar nan, to wajibi ne zai dawo bayan shuɗewar wasu shekaru ya kuma yaƙe mu, sannan yaci galaba akan mu, haka kuma kashe sa ko ba ayanzu ba shima yana dai dai da tashin duniyar mu ne, domin kuwa bani bama, hatta da abun bauta Gargabilu faɗan yafi ƙarfin sa."
Boka mai hutar kasko ya faɗa idanuwan sa akan Sarki Barbaru.
"To ta wace hanyace shi jinjirin zaibi ya huce ne yakai Boka?" Cewar Sarki Barbaru cikin tashin hankali.
"Abun da nima ban sani ba kenan, sai dai kuma bawai zamu zauna bane, a yanzu tashi zamuyi mubi wata hanyar domin mu gano ta sashin da shi jinjirin zai huce, idan kuma har aka kai gobe bamu gano ba, to kawai zamu sanya dakaru su zagaye mana kowace ƙofa ta shigowa garin nan." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana mai yin gaba, tukun shima Sarki Barbaru ya bisa abaya, domin suje su cigaba da binciken hanyar da zasu gano ta inda Jaririn zai huce.
Kwana sukai cir suna abu ɗaya amma abanza, babu kalar tsafin da Boka mai hutar kasko baiyi ba dan ya gano ta hanyar da Jaririn zai wuce amma baiyi ba.
Har sun yanke hukuncin zasu hakura su subi waccan hanyar ta toshe ko wace ƙofar garin, sai kuma boka mai hutar kasko ya tuno da wata hanya da baibi ba acikin duka tsafin da yay.
Hakan yasa cikin sauri ya juya ɓarin da Sarki Barbaru yake yana mai faɗin. "Akwai wata hanyar bayan waƴan da mukabi da muka manta bamu yita ba, dan haka yanzu muyi sauri zuwa gaban ƙaramin rafi, domin kuwa anan ne kawai wurin da zanyi aikin."
Dasauri Sarki Barbaru ya bisa abaya hankali atsantsar tashe.
Gaban ɗan ƙaramin rafin da yake ɗauke da farin ruwa acikin sa Boka mai hutar kasko ya tsaya.
Wasu irin abubuwa ya watsa acikin ruwan, tukun ya fara wasu irin mahaukatan surutai yana mai zagaye rafin.
Lokaci ɗaya ruwan ya dinga wata irin hautsinawa da matuƙar sauri, tukun aƙarshe wani irin hoton tafkeken ruwa mai matuƙar girma ya bayyana acikin sa.
Dasauri Boka mai hutar kasko ya tsaya da surutan da yake yana mai faɗin. "Tabbas munyi nasara ayanzu, domin kuwa ga hoton hanyar nan tazo.
Jiniirin zai biyo ne ta tsakanin hanyar data ratso daga Ƙasar Hausa zuwa jahar ruman, dan haka sai muyi maza-maza yanzu mu koma cikin masarauta, domin ahaɗo kan dakaru da kayan aiki mutafi gaban ruwan, tunda babu wanda yasan lokacin hucewar sa." Ya faɗa suna masu juyawa cikin sauri suka tafi.
Acan ɓangaren Jirgin su Ishaƙ da Aishatu kuwa, adai-dai wannan lokacin ya.............✍
*BAƘAR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 14*
Ya huce ta ta cikin Baƙar Masatauta aguje, yana mai ɗaukar hanyar da zata kaisa Jahar Ruman kai tsaye.
Yayin da su Sarki Barbaru kuma tare da boka mai wutar kasko suka ƙarasa cikin Masarautar a matuƙar ruɗe.
Cikin daƙiƙun da basu zarta goma shabiyar ba duka aka haɗa kan dakarun.
Wasu irin jibga jibgan baƙaƙen mutane ne da suke sanye da ƴan gajerun baƙaƙen wandina babu ko roga ajikin su, yayin da idanuwan sa kuma suka kasance jajahur babu kyan gani, ɗauke suke da wasu irin makamai tun daga kan takubba, kibiyoyi da dai sauran dangunan su, kallon su kawai ya isa ya sanya mutum firgici, muddin bai saba ganin suba.
Gaba ɗayan su suka juya suna masu dosar bakin ruwan nan.
Zagaye sa sukayi ta kowane fanni, ya zamto duk ta inda mutum zai ɓullo sai yaci karo da su kafun ya huce, gaba ɗayan su riƙe suke da mugayen makamai.
Tsayuwar su keda wuya awurin wani ƙatoton jirgin ruwa ya tawo zai huce, cikin sauri suka hulla wata igiya mai tsantsar girma, wacce take maƙale da wasu iccina ajikin ta, tayarce jirgin bazai taɓa iya hucewa ba sai ya tsaya.
Ai kuwa kamar yacce sukai zato, jirgin yana hangar igiyar ya tsaya cak awurin da yake, yayin da mutanen cikin jirgin kuma hankulan su yayi bala'in tashi, sabo da abun da suka gani, ga kuma wasu irin mutane da basu da kyan gani da suke tun karo su gadan gadan acikin nasu jirgin ruwan.
Wasu daga cikin dakarun nan ne suka shige cikin jirgin ruwan Baƙar Masarauta, wanda yake zane da tambbarin ta tako ina ajikin sa, hannuwan su riƙe da makamai.
Suna ƙarasawa wurin da jirgin ruwan nan yake suka zare makaman su, suna masu nunawa matuƙan jirgin hanyar da zasu bi.
Cikin tsantsar ruɗu, tare da firgici, direbobin jirgin ruwan da suka kasance mutum ukku suka juya kan jirgin nasu, suna masu dosar bakin ruwan nan inda su sarki Barbaru suke atsaye.
Suna isa bakin ruwan Sarki Barbaru ya buɗe murya cikin ƙarfi yan mai faɗin. "Ina son kuyi maza maza ku shiga cikin jirgin nan, abincika mun ko ina na cikin sa lungu da saƙo, tare da jikin kowace mata da take cikin sa, muddin aka samu jinjirin yaro namiji, to akarɓo sa akawo mun shi nan, idan kuma har uwarsa tayi gardama wurin badashi, ku caka mata kibiya, sannan ku tawo mun da ɗan nata." Ya faɗa cikin wata irin muraya mai matuƙar amo da firgitarwa, yayin da su kuma mutanen cikin jirgin nan hankulan su ya sake bala'in tashi, tayarce har wasu daga cikIn su suka fara sakin ihu, yayin da wasu kuma suka sassaki fitsari awuraren da suke, musamman ma mata.
"Duk matar da taƙara gigin barin amon sautin ihun ta ya daki kunne na, to ta sani tabbas ƙarshen rayuwar tane yazo." Sarki Barbaru ya faɗa cikin tsawa, yana mai kai idanuwan sa kan mutanen da suke acikin jirgjn nan.
Take kuwa duka wurin ya ɗauki tsit, sai faman muzurai kawai da mata sukeyi.
Yayin da su kuna dakarun nan suka afka cikin jirgin suna masu miƙar da duk matar da suka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 76