Share this page
wani white roba jeans shima sabo fidigil, kana ta ciro wani ɗan ƙaramin mayafi da ya kasance fari shima. Sannan ta rufe wardrobe ɗin tana mai dawowa gaban gadon ta tsaya. Ɗaukar rigar tayi tana mai miƙar da ita tsaye tare da jingina ta a jikin ta, tukun ta girgiza kai tana mai sakin murmushi, sabo da sanin da tayi na dole ne ma rigar tayi mata kyau, kamar yadda ta kasance mai kyau itama. Kafin daga bisani kuma ta fara ƙoƙarin zira rigar a jikin ta, bayan ta sanya iner wear's a farko. Sannan ta zame towel ɗin jikin ta tana mai ɗauko wandon shima ta sanya sa. Sosai kayan suka yi matuƙar kama jikin ta-ta ko ina, kasancewar su gaba ɗayan su roba ne. Dauke rigar take da fararen botura masu matuƙar kyau a gaban ta da bayan ta, yayin da daga saitin ƙugun ta kuma take ɗauke da bell ajikin ta. Shi kuwa wandon gaba ɗaya yabi ya matse mata jiki tamkar dama da shi aka hallito ta. Tayi bala'in kyau cikin shigar iyakar kyau. Tafiya tayi zuwa wurin da take ajiye takalmanta da jakun kunan ta, tana mai sa hannu ta ɗauko wani baƙin hill shoe da yake ɗauke da igiyoyi ajikin sa, tare da ƴar ƙaramar baƙar jaka mai tsananin kyau da ta kasance mahaɗin sa. Tukun ta riƙe su a hannun ta tana mai dawowa wurin da mayafin ta yake a jiye shima ta ɗauke sa ta koma gaban dressing mirrow da su. Tsaye tayi a gaban madubin tana mai kama uban gashin dokin da yake kitse akan ta, kana ta sanya masa fararen riborm masu tsanin kyau, sannan ta sake sa ya zubo har kan gadon bayan ta, tukun ta durƙusa ƙasa tana mai cire igiyoyin takalmin nata mai tsanain tsini, ta sanya ƙafafuwan ta a cikin sa. Kana ta sake ɗagowa tana mai ɗaukar mayafin ta ɗora sa akan ta, sannan ta tattare sa daga gaban ƙirjin ta ya zamto a bayyane, tana mai watsa jelolin sa baya. Iyakar kyau tayi kyau, hakan yasa ta fara bin jikin nata da ruwan turarruka tana mai kallon kanta a cikin madubin, tare da sakin murmushi, domin kuwa ita kanta ta yaba da haɗuwar tata ba kaɗan na. Yayin da a zuciyar ta kuma take ta saƙa abubuwan da zata jewa Yarima Asad da su, wanda take tinanin Insha Allah bazai watsar da ita ba. Cikin takun ta na tsantsar ji da kai ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai nufar falon su. Ko da ta ƙarasa zuwa cikin falon bata samu Zee aciki ba, hakan ne yasa ta ɗan taɓe baki, tana mai fucewa gaba ɗaya daga cikin sa. Acan ɓangaren Yarima Asad kuwa, misalin ƙarfe huɗu da rabi ya gama shiryawa tsaf cikin shigar sa ta yau da kullum, wato dai black three quarter tare da wata ƴar yololuwa bluen t shirt da tayi matuƙar kama jikin sa, ta yadda har ake ganin gaba ɗaya surar jikin nasa a fili, sai dai kuma fa kwata-kwata baya yiwa kaya sawa biyu, wato da zarar yasa su yau shikenan kuma ya gama da babin su sai wasu sababbin, wanda hakan kuma yana ɗaya daga cikin abubuwan da Fulani bata so na dan gane da halayyar sa, sabo da ganin hakan da take amtsayin zallar almubazzaranci. Wasu tausasan bluen takalma na fata ya sanya fararen ƙafafuwan sa a cikin su, yayin da tsintsiyar hannun sa kuma ta kasance ɗaure da baƙin agogon fata mai tsananin kyau. Cumb ya ɗauka yana mai gyara lallausar sumar da take kwance akan sa mai tsananin yawa, da tasha wani irin shegen aski da yayi bala'in yiasa kyau. Kana daga bisani ya ajiye cumb ɗin akan mirrow'n da yake tsaye a gaban sa, sannan ya lumshe idanuwan sa yana mai shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren da yake futa ajikin sa, wanda baya taba gajiya da shi ako da yaushe. Tukun daga bisani ya buɗe idanuwan nasa yana mai fara ɗaga ƙafafuwan sa ya doshi hanyar waje. Tamkar ko da yaushe yau ɗin ma yana zama akan kujerar nan da take a gaban swimming pool ɗin, kyakkyawar baturiyar da take aikin a wurin ta tawo wurin da yake hannuwan ta riƙe da wani ɗan ƙaramim plate mai tsanain kyau, tare da cup da yake rife da murfi akan sa. "Weldon sir." Baturiyar ta faɗa tana mai dire plate ɗin akan table ɗin da yake a gaban sa. Inda take bai ɗago ya kalla ba ballan tana har tasa ran zai tanka mata. A hankali ta ɗauko mug ɗin da yake ɗauke da coppy a cikin sa tana mai sake matowa gaban sa. Tukun ta ɗan durƙusa tana mai miƙa masa shi. Still dai bai ɗago ya kalle ta ba ya miƙa hannun sa yana mai karɓar mug ɗin, sannan ita kuma ta juya tana mai komawa wurin da ta futo. Acan ɓangaren Billy kuwa tun misalin ƙarfe huɗu da rabi dai-dai ta ƙaraso wurin, sai dai kuma yau ɗin ma kamar ko da yaushe, wurin da take zuwa ta laɓe taje ta zauna. Hakan yasa tun tawowar sa wurin take kallon sa har zuwa yanzu da wannan baturiyar ta bar wurin sa. Cikin tsantsar fargabar rashin sanin yadda zai tarbe ta tasa hannu tana mai gyara kiston da ya ɗan sakko kan fuskar ta zuwa baya, sannan ta miƙe tsaye daga wurin da take tana mai ɗaukar jakar ta ta fara takawa. Yayin da take jin zuciyar ta na wani irin bugu aɗari-ɗari, sai dai kuma ta ƙudirtawa ranta cewar ko wane kalar tsoro zataji ayau ɗin sai ta ƙarasa wurin sa, domin gudun kar ta tsaya sanya wata tazo ta bangaje ta, wannan dalili ne ya sanya tayi shahada yanzu tana mai nufar wurin da yake gadan-gadan. Canza taku tayi a lokacin da taga ta kusa zuwa inda yake, tana mai komwa yin wata tafiya mai tsantsar jan hankali. Yayin da fuskar ta kuma take ɗauke da annuri, duk da ba ƙaramun tsoro ne ke danƙare a ƙasan zuciyar ta ba. Cikin wani irin taku na tsantsar jan hankali ta ƙarasa wurin da yake. A hankali kana kuma cikin wata iriyar murya mai matuƙar sanyi ta buɗe baki tana mai faɗin. "Excuse me." Yayin da idanuwan ta kuma suke kasance ƙur akan sa, ƙirjin ta kuwa wani irin bugu yake wanda ba zai misaltu ba. A fannin Yarima Asad kuwa tun lokacin da ta kusa ƙarasowa wurin da yake ya lura da ita, sai dai ko kaɗan batasan ya ganta ba, sabo da yadda taga ko motsi bai canza ba daga yadda yake ballan tana ya ɗago ya kalle ta, yayin da shi kuma yake kallon ta ta ƙasan ido yana mai jiran yaji abun da tazo da shi ita kuma, kafin ya yanke hukunci. Cikin wani irin salo Billy ta ɗan janyo ƴar kujerar robar da take kafe a gaban table ɗin da Yarima Asad yake, wato wacce take fuskantar mazaunin sa tana mai zama akan ta itama. Tukun ta ɗauki ƙafa ɗaya tana mai ɗora ta akan ɗaya, kana ta lumshe idanuwanta bayan ta ɗan ɗaga kanta sama. Tukun daga bisani ta sauke kanta ƙasa tana mai wara idanuwanta a hankali akan fuskar Yarima Asad, kafin daga bisani kuma ta ɗan juyar da kai gefe tana mai fesar da wata sassanyar iska daga cikin bakin ta, sannan ta sake dawo da kallon ta gare sa, tana mai ƙara buɗe baki cikin wata irin murya tace. "I'm Bilkisu Abubakar Sardauna by Name." Ta ƙarasa maganar tana mai lumshe idanuwanta, yayinda shi kuma Asad ya cigaba da sipping ɗin copy ɗin sa ba tare da ya nuna yasan da zamanta a wurin ba har lokacin. Yayinda azahiri kuma yake aikin kallonta ta ƙasan ido, yana mai mamakin ƙarfin halin yarinyar. Ɗan muskutawa Billy ta sakeyi akan kujerar da take bayan ta sake wara idanuwanta akan fuksar Asad. Kana ta sake buɗe baki cikin tattausan lafazi tana mai ɗorawa da cewar. "I was born in Ƙasar Hausa Wasai state. And then the daughter of Wasai Governor." Ta sake yin shiru tana mai ɗan sauke numfashi ƙasa-ƙasa, tare da jifan sa da wani irin shu'umin kallo ta ƙasan idanuwa. Yayinda shi kuma Asad ya janye mug ɗin dake riƙe a hannun sa daga kan bakin sa, kana ya dire sa akan table ɗin nan, sannan ya ɗago kai a hakanli yana mai kai idanuwansa kanta cikin wani irin kallo, azahirin gaskiya tini ya gaji da surutun ta, sa'ar ta ɗaya ma shine ƙasa-ƙasa take maganar itama, sannan kuma aɗan kallon da yayi mata na ƴan daƙiƙu ya fahimci ba bitch bace ita ɗin, domin kuwa yanayin nutsuwar ta wacce ta ara ta yafa kawai yasa ya kawo hakan aransa, amma banda haka da tini ya dakatar da ita ma. Kana daga bisani kuma ya ɗaga laɓɓan sa idanuwansa akan ta cikin yin ƙasa-ƙasa da murya yana mai faɗin. "Then what nex...." Maganar tasa ta yanke yana mai lumshe idanuwan sa, sabo da hango tawowar baturiyar budurwarsa ta jiya da yayi ta nufo wurin da suke cikin tsantsar fushi. Hakan ne ya sanya sa lumshe idanuwansa yana mai tafiya tinanin abun da zaiyi, wanda zai ƙona mata rai tayi nadamar zuwa wurin yanzu-yanzu. Yayinda ita kuma Billy ta ƙara gyara zaman ta akan sit ɗin da take tana mai fuskantar sa, tare da zumuɗin jin abun da zai futo daga bakin sa, domin kuwa tana tinanin tarkon ta ya kama sa. Acan wurin baturiyar na kuwa sosai taciyo uwar kwalliya cikin shigar wasu irin ƴan iskan kaya da suke kusan ɗaya da babu a jikin ta, danniyar ta na zuwa wurin dan ta bawa Asad haƙuri akan abun da tayi masa ko Allah zai sa ya haƙuran, duk da dai tasan hakan abu ne mai tsananin wuya, amma sai kuma tana doso wurin ta hango wata zaune a gaban sa. Lokaci ɗaya kuwa taji wani irin baƙin ciki tare da mugun kishi sun zo sun tokare mata aƙawon zuciya. Bata sake jin ranta ya ƙara matuƙar ɓaci ba sai da ta ƙara kusanto wurin da ta fahimci wacce take zaune agun, wato wannan yarinyar ta jiya da tazo kanta tayi mata tsaki tai gaba, hakan yasa ta fahimtar cewar sonsa take itama, shi yasa jiya har tayi mata tsaki ta huce. Hakan kuwa shi yayi matuƙar harzuƙata, har bata san lokacin da ta durƙusa ƙasa ba tana mai zame takalmin da yake sanye aƙafar ta wanda ya kasance mai matuƙar tsini da tsayi, tana mai riƙo sa a hannunta ta nufo wurin Billy gadan-gadan. Ita kuwa Billy ko kaɗan bata san da tawowar ta ba, domin kuwa hankalin ta gaba ɗaya yana kan Asad ne da take jiran taji yace wani abu. Da wani irin ƙarfi baturiyar nan ta ɗaga tsinin takalmin ta dai-dai lokacin da ta ƙaraso gaban Billy tana mai saita goshin ta da shi, tare da faɗin. "Who the h..." Maganar tace ta tsaya, sabo da yadda taga Yarima Asad yayi wani rin miƙewa tsaye a matuƙar zabure, yayinda Billy kuma ta juya da matuƙar sauri tana mai kai idanuwanta ɓangaren da tajiyo muryar nan, wanda hakan kuma yayi dai-dai da isowar tsinin takalmin gab da goshin ta. Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwanta jikin ta na matuƙar rawa, sabo da tabbatarwar da ta riga tayi na an riga da anji mata ciwo. Amma ba zato ba tsammani kawai sai ji tayi anyi wani irin funcikar ta, tana mai kifawa kan lallausan wani abun da bata fahimci ko menene shi ɗin ba. Hakan yasa ta fara buɗe idanuwanta a hankali, tana mai sauke ajiyar zuciya, har ta buɗe idanuwan nata duka akan faffaɗan ƙirjin sa mai matuƙar taushi, da yayi mata rumfa da hannuwansa duka biyu................✍ _MUN KUSA KAMMALA BOOK 1, KAFIN MU SHIGA BOOK 2 KUMA IDAN MUN DAWO DAGA HUTUN SATI ƊAYA._😅 *BY* UMAR FARUQ*D* *BAK'AR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 27* Wato dai ya rungume ta ƙam-ƙam a cikin ƙirjin sa. Wani irin farin ciki mara misaltuwa Billy ta tsinci kanta acikin sa, hakan ne yasa ta sake maƙal-ƙale sa gam-gam, tana mai sake kwantar da kanta akan ƙirjin sa, yayin da daddaɗan ƙamshin turaren sa ke dukan hancinta yana ratsa har tsakar ƙwaƙwalwar ta. Shi kuwa Yarima Asad tsaye yake a wuri ɗaya rungume da ita a ƙirjin sa, yana mai aikawa wannan baturiyar wani matsiyacin kallo mai kaɗa hanjin ciki. Ita kuwa wannan baturiyar cikin tsantsar baƙin ciki da takaicin yadda taga Asad ya rungume Billy a gaban ta fashe da wani irin kuka, kafin daga bisani kuma ta kaiwa mug ɗin tea ɗin da yake ajiye akan table damƙa, tana mai sake saita goshi Billy ta jefa mata shi. Amma sai Asad ya sake janye Billy daga wurin da matuƙar sauri, kana ya fara tinanin abun da zaiyi wanda zai ƙara ƙona mata rai fiye da yadda take yanzu, domin ta gane cewar shi ɗin muddin ya riga ya bar abu to fa ya barsa kenan har abadan abada, domin kuwa yana faɗa babu wata mace da ta isa ta ɓata masa rai a duniya, ballan tana kuma har ya rarrashe ta. A wani irin haukace baturiyar nan tayi kansu gadan-gadan, bayan ta saki wata irin ƙara. Hakan da Yarima Asad ya gani ne ya sanya sa yin sauri ya suri Billy gaba ɗayan ta a cikin hannunsa, yana mai yi mata ɗaukar jarirai, ba dan komai ba kuma yayi hakan, sai dan kawai ya ƙara harzuƙa zuciyar ta. Yayinda ita kuma Billy tayi wani irin maƙal-ƙale sa, tana mai sa hannuwan ta duka biyu ta saƙalo wuyan sa da su. Kana tana wani irin sakin kukan ƙaryar da take ƙwaƙulo sa, tana nuna cewar a tsorace take sosai. Yayin da azahirin gaskiya kuma wani irin farin ciki mara misaltuwa ya lulluɓe zuciya da ruhinta, domin kuwa tana ganin tamkar ta riga da ta gama mallakar Asad har abada, hakan ne yasa taji ina ma ace tare da Zee suka zo wurin nan, domin ta ganewa idanuwanta, dan tasan yanzu ko taje ta bata labarin abun da ya faru ba lallaine ta yadda ba. Tabbas yau ɗin ta ƙara tabbatar da cewa ita ɗin mai sa'a ce a duniya, kana kuma ta ƙara yadda da cewar babu wani abu da zai taɓa yi mata wuyar samu muddin taso samunsa a duniya. A ɓangaren Asad kuwa ganin da yayi wannan baturiyar ta sake yowa kansu ne, yasa sa wurga mata wani irin matsiyacin kallo daga wurin da yake. Ƙam ta cake a wuri ɗaya kuwa jikin ta na matuƙar karkarwa, domin kuwa ba ƙaramun firgita tayi ba da irin kallon da yake watso mata. Yayin da shi kuma ya juya yana mai fara ɗaga ƙafafuwan sa yayi gaba, hannuwan sa rumgume da billy tamkar jaririya. Wani irin kuka baturiyar nan ta ƙara fashewa da shi, tana mai ɗora hannuwan ta duka biyu aka tare da durƙushewa a ƙasa. Ita kuwa Billy cikin tsantsar farin cikin da ya lulluɓe ta lumshe idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su akan fuskar baturiyar nan, bayan ta zuro kanta ta saman kafaɗar Asad. Kana ta zaro harshen ta tana mai yiwa baturiyar nan da itama take kallon ta gwalo, sannan ta sake mayar da kanta cikin ƙirjin Asad, tana mai lumshe idanuwan ta-ta cigaba da shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren sa, da yake saukar mata da wata irin nustuwa da kasala a cikin jiki. Wani irin gigitaccen kuka baturiyar nan ta saki tana mai jin tsanar Billy na sake mamaye zuciya da ruhin ta, ta yadda har take jin zata iya kashe ta muddin zata same ta a hannu. Shi kuwa Yarima Asad direct ya doshi room ɗin sa rungume da Billy a ƙirjin sa. Haka nan shima yaji yarinyar ta ɗan kwanta masa arai, ta yadda har yake ganin zai iya dinga kulata, sai dai kuma ba wai yaji yana son ta bane a zuciya, asalima har yau shi baici karo da wadda takai yaso ta ba a cikin ƴammata. Hannun sa ɗaya ya sanya a cikin aljihun wandon sa yana mai zaro key'n ɗakin, sannan ya zura sa yana mai buɗe sa, kana ya murɗa handle ɗin ƙofar yana mai ƙara tura ta da ƙafar sa, sannan ya danna kansa zuwa cikin ɗakin. Da sauri Billy ta lushe idanuwan ta, sabo da daddaɗan ƙamshin turaren da ya daki hancin ta. Tabbas komai nashi na daban ne, tamkar yadda shi kansa ya kasance na daban, haka kuma komai nashi yayi, kamar yadda shima yayi ɗari bisa ɗari. Ta faɗa a cikin ranta tana mai bin kyakkyawan falon nasa da idanuwan ta daga saman hannun san da take. Shi kuwa Yarima Asad yana ƙarasawa cikin ɗakin ya dire Billy a ƙasa ba tare da yace mata komai ba, asalima ko kallon fuskar ta baiyi ba, sai hucewa da yayi zuwa gaban ɗan mini fridge ɗin da yake acikin ɗakin nasa yana mai buɗe sa, kana ya zaro robar ruwa ɗaya aciki mai matuƙar sanyi, yana mai dawowa ya zauna akan kujerar da take kusanci da shi. Sannan ya buɗe murfin jarkar yana mai kafa bakin ta akan ɗan ƙaramin bakin sa ya fara shan sa. Bashi ya ɗauke kai daga kan jarkar ba har sai da yasha kimanin rabin ta, tukun ya ajiye ta akan ɗan mini center table ɗin da yake agafen sa yana mai lumshe idanuwan sa a hankali, tare da sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya akai-akai. Ita kuwa Billy jin da tayi ya sauke ta anan ɗin ne, ba tare da kuma ya tanka mata bane ya sanya ta samun wuri akan kujerar da take akusa da ita, wacce ta kasance tana facing ɗin wacce Asad yake akai ta zauna. Kana ta durƙusar da kanta ƙasa tana mai yin wasa da ƴan yatsun hannun ta. Kafin daga bisani kuma ta buɗe baki a hankali tana mai faɗin. "I'm very sorry please." Sannan tayi shiru tana mai cigaba da wasa da ƴan yatsun hannun ta. Yayin da shi kuma Yarima Asad ya buɗe idanuwan sa a hankali yana mai ɗan ɗaga kai ya kalle ta, kana ya ɗan taɓe baki yana mai mayar da idanuwan sa kan wayar sa. Kafin daga bisani kuma a lokacin da Billy ta fara futar da tsammanin zaice wani abu taji sautin daddaɗar muryar sa yana mai faɗin. "Sorry for what?" Duk da har lokacin bai kalle ta ba. Jin hakan da Billy tayi ne ya sanya ta lumshe idanuwanta a hankali, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai ɗago kanta ta kalle sa, sannan ta furta cewar. "Da abun da naja wata tayi maka yanzu mana, tun da nasan da banzo wurin ba da ba zata yi hakan ba." Tayi maganar cikin wata irin murya, wacce take tattare da shagwaɓa a cikin ta. A hankali ya ɗan ɗago idanuwansa yana mai kaisu kan fuskar ta tare da ɗan taɓe bakin sa, tukun daga bisani kuma ya basar yana mai yin tamkar bai kalle tan ba, domin kuwa azahirin gaskiya ko ita bata san ya kalle tan ba. Kafin daga bisani kuma ya furta. "Uhm!" "Please! Please!!" Billy ta sake faɗa tana mai sake marairaicewa, tare da haɗe tafukan hannayen ta wuri ɗaya. "Is ok." Ya faɗa a gajarce, kana kuma a saman lips ɗin sa, yana mai miƙewa tsaye da niyyar shigewa cikin bedroom ɗin sa. Hakan da Billy ta gani ne ya sanya ta miƙewa tsaye da sauri itama, kana ta ƙara yin ƙasa-ƙasa da muryar ta tana mai cewa. "Please can i get your phone number?" Ta ƙarasa maganar a hankali, tana mai fatan Allah yasa kar yace a'a azuciyar ta. Yayinda shi kuma ya cigaba da tafiyar sa yana mai yin tamkar baiji abun da ta faɗa ba. Wani irin sanyi Billy taji jikin ta yayi. Gaba ɗaya murnar da take ta fara komawa ciki, sabo da ganin da tayi ya mata banza tamkar bai san da ita ba yana shirin shigewar sa cikin ɗaki. A fannin sa kuma yaji ta sarai amma yay tamkar baijitan ba, sai da har yaje bakin ƙofar da zata sadasa da cikin bedroom ɗin sa, tukun ya tsaya a wurin yana mai zira hannun sa cikin aljihun sa. Kana ya zaro katin sa wanda yake ɗauke da sunan sa da kuma number sa a cikin aljihun sa, yana mai cilla mata shi daga nan wurin da yake ba tare da ya juyo ba, sannan ya buɗe baki cikin maganar sa da sautin ta bai fiye futa ba, yana mai faɗin. "Zaki iya tafiyar ki yanzu ok." Ya ƙarasa maganar yana mai murɗa handle ɗin ƙofar tare da danna kansa ciki. Yayin da Billy kuma ta buɗe baki cikin tsantsar farin ciki tana mai faɗin. "Thank you Prince." Da ɗan ƙarfi yadda zai jiyo, tukun ta matsa wurin da katin sa yake tana mai durƙusawa ƙasa ta ɗauke sa. PRINCE ASAD Shine sunan da yake rubuce ɓaro-ɓaro da manyan baƙi ajikin katin nasa, yayin da special numbers ɗin wayar sa kuma da suka kasance har guda biyu suka biyu a ƙasan sunan. Cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa Billy ta ɗauki katin, kana ta suri jakarta tana mai juyawa ta kama hanyar waje fuskarta ɗauke da tsantsar annuri. Yayin da take jin zuciyar ta kuma tai haske fari ƙal, kana kuma ta ƙagu ta isa wurin Zee, domin ta ƙara tabbatar mata da cewar ita ɗin daban take da sauran fa, tamkar yadda ta faɗa mata bata yadda ba. Rufe masa ƙofar sa tayi bayan ta fuce daga cikin falon, kana tayi gaba abunta tana mai tafiya wurin da lipter take domin ta sauke ta ƙasa, sannan ta huce mazaunin su. *ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFU CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Sosai jikin Bir yayi matuƙar yin tsami sabo da dukan da yaci. Sai dai kuma ko kaɗan hakan bai sa yaji cewar zai iya haƙura da ganin Gimbiya Tasmir ya gudu idan sun haɗu ba, domin kuwa tun abun ya faru a jiya har kawo yau hoton kyakkyawar fuskar ta bai-bar cikin idanuwan sa ba. Asalima da zarar ya buɗe idanuwan ita yake gani durƙushe a gaban sa tana aiko masa da kallon ta, yayin da ko a cikin baccin sa na daren jiya shima ya kasance ɗauke da mafarkin ta gaba ɗayan sa. A takaice dai lokacin ɗaya yaji ta shiga ransa, sannan kuma zai iyayin komai domin ya samu ko kallon tane yayi. Yana jin wasu irin abubuwa dan gane da Gimbiyar irin waƴan da bai taɓa jin makamantan su ba akan wata tun da yazo duniya. Yanzu haka zaune yake a jikin bishiya, hannun sa riƙe da kwari da gwafar sa yayi shiru shi kaɗai. Lokaci bayan lokaci yake ɗan lumshe kyawawan idanuwansa yana mai sakin murmushi. Wani irin shauƙi yake ji tattare da shi, irin wanda bazai misaltu ba. "Haƙiƙa yanzu na fara shiga harkar ki Gimbiyar mu, koma nace yanzu zan fara shiga, saboda ada ban taɓa sanin haka kike da baiwar kyawu ba sai ajiya. Tabbas jiya kin zamto rana mai daraja a gareni, rana irin wadda ta shiga cikin kundin tarihina ta zauna, ranar da aka dakeni acikin BAƘAR MASARAUTA dukan yayi matuƙar sanyaya mun zuciya. Ranar da na fara ganin kyakkyawar fuska irin wacce ban taɓa yin tozali da makamanciyarta ba. Tabbas zan jure duk wata kalar huya da zaki bani, muddin idanuwa na zasu dinga arba da kyakkyawar fuskar ki, domin kuwa jikina na bani cewar ke ɗin zaki zamto hasken zuciya gare ni a wataran Gimbiyar mu." Ya ƙarasa maganar ƙasa-ƙasa fiye da yadda ya fara ta, yana mai sake lumshe dara-daran idanuwan sa. Yayinda yake jin tsigar jikin sa na wani irin mimmiƙewa, wani kalar yanayi na lulluɓe sa, sabo da hango ta da yayi acikin idanuwan nasa. Kafin daga bisani kuma ya wara su a hankali yana mai mikewa tsaye. Da ɗan ƙarfi ya taune leɓen sa na ƙasa, sabo da yadda yaji gaba ɗaya jikin sa a wani irin kakkame, tukun daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa cikin cizon leɓe, yana mai nufar hanyar da yake fatan ta sake sadasa da hasken zuciyar tasa. A ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa ba ita tabar cikin lambun nan ba jiya har sai da gari ya fara dubu. Shima kuma bawai dan taji zuciyar ta tayi sanyi da abun da ƙasƙantaccen bawan can yayi mata ne ba, sai dan kawai sanin da tayi na yanzu za'a fara neman ta muddin aka duba akaga bata nan. Wata irin tafar-fasa take jin zuciyar ta nayi mata aduk lokacin data tuno yadda bugun zuciyar ta ya sauya a gaban sa, ga kuma gizon da yake ta yi mata acikin idanuwan ta aduk lokacin data lumshe su, a lokacin da yake sakar mata kyakkayawan murmushin sa. Wanda hakan kuma shi yake matuƙar ƙara tinzira ta. Cikin tsantsar baƙin ciki ta doshi ɓangaren nasu, tana mai jin zuciyar ta na cigaba da ƙuna. "Haƙiƙa kana gab da shaƙar numfashin

Chapter 28 of 76