bakin ta tana mai faɗin. "I love you so much My Prince!"
Ƙala baice mata ba sai kallon cikin idanuwan ta kawai da yake yi shima. Ahankali ta cigaba da matsar da fuskar ta saitin tasa har ta samu damar haɗe tsinin hancin ta dana sa, tukun ta matsar da lips ɗin ta tana mai ɗora su akan nasa, kana ta zaro harshen ta tana shirin lasar nasa.
Da sauri ya janye fuskar sa daga jikin tata yana mai juyar da kai gefe.
Galala ta bisa da kallo baki asake, sannan kuma hankali atashe, sabo da baicika yi mata irin haka ba sai har idan yana son suyi faɗa da ita.
Cikin rawar murya ta buɗe baki tana mai faɗin. "What happened againe Baby?"
"I'm not in the mood!"
Ya faɗa yana mai jan wayar sa ya cigaba da shafawa ba tare da ya kalle ta ba.
"Please Baby i said I'm sorry!" Ta sake faɗe tana mai ƙara faɗawa jikin sa.
Uhm!
Ya faɗa ba tare da ya kalle tan ba dai.
"To please ka tsaya kaji." Ta faɗa tana mai sake kai lips ɗin ta kan nasa ta haɗe su wuri ɗaya.
Bai hana taba yanzu sai dai kuma bai taya ta ba, sai ita kaɗai kawai ya bari tana ta faman aikin ta.
Ganin da tai yaƙi ya ware kamar yacce take sone ya sanya ta ƙara dabai-baye sa sosai acikin jikin ta, tukun ta fara jansa da ƙarfi ba tare da ta sakar masa bakin sa ba daga cikin nata ba.
Binta ya fara yi ba tare da yay mata musu ba har tasamu nasarar matso da su bakin kujerar nan, tukun ta cigaba da kissing ɗin bakin sa cikin sauri, kana daga bisani ta shammace sa tana mai funcikar sa suka afka cikin swimming pool ɗin nan atare.
*BABBAN ZAURE LOCUS*
Unguwace wacce take agaban gidan slSarkin Wasai, Unguwace ta masu hannu da shuni dai dai gwargwado.
Duk gida jen da suke acikin unguwar sun kasan ce manyan ginin-nika ne na bene, sai dai kuma ahakan wani yafi wani girma.
Wani ɗan madaidl-daicin gida mai matsakaicin girma baƙar motar ƙirar coralla Lx ta danna kanta cikin get ɗin sa da yake abuɗe.
Farfajiyace mai girma dai dai misali acikin gidan, yayin da akabi aka ƙawata ta da wasu haɗaɗɗun kujerun silver daga can gefe.
Zagaye compound ɗin yake da furanni masu natuƙar kyau da ɗaukar hankali.
Direct matuƙin motar ya huce parkin space inda wasu motocin har guda biyu suke fake acikin sa da ita, tukun ya parka ta awurin ta, kana ya buɗe murfin motar ya futo hannun sa riƙe da jakar sa.
Farin ne dogo mai kimanin shekaru arba'in aduniya. Sanye yake da dack bluen shadda tare da baƙar wula akan sa, yayin da takalman kafar sa ma suka kasance baƙaƙe, sai tsintsiyar hannun sa kuma da take ɗaure da baƙin agogon fata mai tsananin kyau itama.
Ɗaga kai sama yayi yana mai kallon yarce giza-gizai keta haɗuwa, alamun ruwa na kusa kenan kasancewar yana yin damuna da ake ciki, tukun daga bisani ya sauke kan nasa ƙasa, yana mai kai tafin hannun sa kan fuskar sa ya shafi sajen da yake kwance lup-lup akan ta har zuwa dogon gemun dake manne ajikin haɓar sa da yasha gyara yana ta faman shignin, kana daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai dosar ƙofar da zata sada sa da cikin gidan nasu.
Da sallama ɗauke abakin sa ya danna kansa cikin ɗan madai -daicin falon da yake ɗauke da kujerun ƙasar turki acikin sa.
"Wa'alaikumu salam!" Datijjon mutumin da shekarun sa zasu kai sittin da biyar aduniya ya amsa masa, tare da wata tsohuwa da take zaune akan kujera dattijon mutumin na ɓare ayaba yana bata.
"Barka da hutawa Abba, ina yini." Matashin mutumin ya faɗa yana mai zama akan kujerar da take facing ɗin wacce suke akai.
"Lafiya ƙalau Malam Ahmad, fatan ka dawo lafiya kaima." Dattijon ya faɗa yana mai sakarwa ɗan nasa murmushi.
"Lafiya ƙalau wallahi Abba, sai dai kawai gajiya dana kwaso sosai." Shima mutumin da aka kira da Ahmad ɗin ya faɗa yana mai ɗan yamutsa fuska.
"To ai dama gajiya ta zama dole, tunda anyi aikin da za'a gajin ai." Mahaifin nasa ya faɗa yana kallon sa.
"Kai dallacan rufen baki kaima, gajiya ko ko zallar ragwanta irin tasa." Tsowuwar matar dake zaune akan kujera tana cin ayaba ta faɗa tana harar wanda aka kira da Ahmad. Tukun ta ɗora da cewar. "Yanzu Abdulkarimu kana gani ɗanka ya shigo har inda nake, amma bai gaishe niba sai kai kaɗai ya gaisar, shine ko kayi masa faɗa tsabar duniya ta lalace ko." Ta faɗa tana mai marai-raicewa kamar zata saki kuka.
"A'a Umma ta kiyi haƙuri, ai yanzu shima zai gaishe ki, kinga magana muke yine shiyasa baiyi ba tun farko." Ya faɗa yana kallon ta. Tukun ya juya ɓarin da ɗan nasa yake yana mai sakin murmushi yace. "Kai gaishe mun da uwata tun kafin ranka ya ɓaci yanzu yanzu."
"Ina ai abun bama zaije da haka ba Abbana." Ya faɗa yana sakin murmushi, tukun ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Kaka ta ina yini, barka da gida ya akaji da tsufa kuma?"
Ɗaure fuska tayi tamau ba tare data amsa masa ba, sai wata muguwar uwar harara data bugo masa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Amma ai da uwarka kake gaisarwa ba zakace mata ya tsufa ba."
Taɓe baki yay shima ba tare da ya tanka mata ba, yayin da shi kuma mahaifin nasa yake ta faman gumtse dariya, domin ko shida kansa yasan Umman tasa bata so jikokan ta suna ce mata ya tsufa.
"Ina Ummi take ne Abba?" Shekh Ahmad ya faɗa yana mai kallon mahaifin nasa.
"Tana sama tana ai'kin tinanin ta na sabo daka tafi kabar ta cikin sa mana." Mahaifin nasa ya faɗa yanayin sa na sauyawa lokaci guda.
Shima Sheikh Ahmad gaba ɗaya sauyawa yay, jikin sa duk yay mugun yin sanyi, yayin da ita kuma kakar tasu ta buɗe baki tana mai faɗin. "Aini na rasa gane wace irin mace ce Ai'shatu, ace shekaru ɗai-ɗai ɗai-ɗai har kimanin shekaru talatin da faruwar abu amma kullum jiya iyau abu yaƙi hucewa."
"To duk wace sila, da kinbi ta maganar Abba da yace baza taba ai'da duk hakan bata faru ba." Sheikh Ahmad ya faɗa yana mai miƙewa ya doshi hanyar stairs.
"To mara kunya fitsararre, daka tsaya baka tashi ba mana kaga yarce zansa yanzu yanzu ubanka ya mammake mun kai, sha-sha-shan yaro kawai, Sheikh ɗin ƙarya Malamin kwali kawai." Tsohuwar ta faɗa da ƙarfi tana mai bugawa bayan sa harara.
"Ke kika jiyo dai." Sheikh Ahmad ya faɗi haka ƙasa ƙasa yana mai ƙarasa hayewa sama.
"Gunguni kake min ko, ai'ko wallahi zaka futo ne kasame ni ina nan babu inda zan matsa daga ni har baban naka, ai dai nasan ba kwana zakai aciki ba dole ka futo ka tafi wurin bursun-sunar matar nan taka da ko ɗaurin zani bata iya ba."
Sheikh Ahmad ya jiyo sautin kakar tasa tana faɗin haka adai dai lokacin da yake shirin shiga ɗakin mahaifiyar tasa.
Taɓe baki yay yana mai danna kansa cikin ɗakin.
Zaune ya hange ta acan ƙarshen gado sanye da maroon ɗin hijab ta haɗa kai da guiwa.
Tsaye yay daga bakin ƙofar yana mai kallon ta ba tare da yace komai ba. Sosai yake jin ciwo acikin rai da zuciyar sa aduk lokacin da zai tadda mahaifiyar tasa cikin damuwa, ji yake ina ace yana da yarce zaiyi ya yaye mata damuwar ta, tabbas da ko kwana ɗaya baza'a sake ba sai ya samar mata da abun da take so, kafun ta koma ga mahallicin ta.
"Assalamu alaikum ya Ummi na." Ya faɗa da sauti cikin tattausar muryar sa daga inda yake.
Ahankali ta janye kanta daga tsakan-kanin cinyoyin ta, tukun ta ɗago fuskar ta ɗauke da murmushi wanda kallo ɗaya zaka mata kasan na yaƙe ne tana mai faɗin. "Wa'alaikumu salam yaro na!"
Ajiye jakar dake ɗauke ahannun sa yayi akan kujerar da take agefen sa, tukun ya fara ɗaga ƙafafuwan sa ahankali yana mai dosar gadon.
Hawa yayi kan gadon yana mai matsawa kusa da inda mahahifiyar tasa take ya zamto suna facing ɗin juna, tukun ya tanƙwashe ƙafafuwan sa agaban ta, kana ya miƙa hannuwan sa yana mai kamo tafukan hannayen ta ya haɗa dana sa ya rumtse su wuri ɗaya, tukun ya ɗaga idanuwan sa yana mai kallon ta, kamar yacce ita ɗin ma take kallon sa ƙwalla na tattaruwa acikin nata idanun, kana ya buɗe baki cikin sanyin murya da taushi yana mai faɗin. "Sh...............✍
#COMMENTS ND SHARE PLS
🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹
_*NA*_
UMAR FARUQ*D*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
*PAGE 04*
"Shin har sai zuwa wane lokacin ne zakicire damuwa aranki ummi na?" Ya faɗa yana mai kallon ta tare da murza tafin hannhn ta dake cikin nasa ahankali -ahankali.
"Har sai ranar da rabbi samawati wal'ard ya karɓi rai da ruhina." Ta faɗa tana mai kallon cikin idanuwan ɗan nata ƙwalla na tsinkewa daga cikin idanuwan ta.
"Subahanallah! Ummi na me yasa zakice haka? Ina al'ƙawarin da kika mun na cewar ba zaki ƙara kuka ba?" Ya faɗi haka muryar sa na rawa shima. Yayin da ita kuma ta buɗe baki tana mai faɗin. "Kayi haƙuri yaro na, domin ko na kasa cika sa, sannan kuma bana tinanin zan'iya cika sa!
Ba daga ni ɗin bace ba, ƙaddara tace tazo da hakan yaro na."
"Tabbas na sani ƙaddarar kice tazo da haka Ummi na, amma ya kamata ace kinyi abun da zaki cinye ta, ko dan kisamu tagomashi awurin ubangijin mu, domin ko duk musulmi na ƙwarai mumini ansan sa da yarda da ƙaddar mummuna da kyakkyawa ne Ummi na, shin me yasa kema ba zaki rungumi taki da hannu bibbiyu ba, zuwa yanzu kibarwa Allah komai." Sheikh Ahmad ya faɗa yana mai cigaba da murza tafin hannun ta, tukun daga bisani ya ɗora da cewar. "Dan Allah Ummi na ki taimaka ki rage sanya kanki acikin damuwa ko domin lafiyar ki, kinga gaba ɗaya yau satin ki biyu da baro asibiti duk ta sanadin damuwar da kike yawan yi, dan haka dan Allah ina son kimun al'ƙawarin bazaki ƙara yin kuka ba, ko kuma zama wuri ɗaya kina tinane-tinane Ummi na." Ya ƙarasa maganar cikin sanyi yana mai kallon ta.
Murmushin yaƙe ta saki tana mai kallon sa itama, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Na gaji da ɗaukar al'ƙawain dana san bazan iya cika sa ba, idan har nace na maka al'ƙawarin bazan ƙara tinani ba daga yau ba to kasani tabbas ƙaryace kawai na faɗa, domin ko koda nayi ƙoƙarin yin hakan ako da yaushe bana iyawa, ko kaɗan nima ba'ason raina nake haka ba, kuma bawai dan hakan na rage mun raɗaɗin abun da nake ji azuciya ta ba, sai dai babu yarce zanyi tinani agareni ya zama dole Yaro na.
Akullum ako da yaushe idan na tuna yarce aka rabani da jariri na ta ƙarfi, awurin dana haife sa ba tare dako ɗaukar sa nayi ba, ina mai jin zuciya ta na wata irin suya ne, ina mai jin raina na tsan-tsar tafasa da ƙuna, ina mai jin ƙwaƙwalwa ta na zafi, hankalina na sake tashi, komai na dawo mun sabo in dinga ganin kamar alokacin abun ke faruwa! Abu na biyu kuma da yake ƙara sanya ni cikin damuwa shine, canzawar mafarkin dana sabayi akan matashin da nake faɗa maka daga mai daɗi zuwa akasin sa, rabon da nace maka nayi bacci mai daɗi ni kaina har na manta Yaro na, domin ko da zarar na kwanta nake ganin sa acikin mugun yanayi yana mai miƙo mun hannun sa dan na taimake sa, amma sai dai da zarar na matsa wurin sai nima awurgar dani gefe, sannan aja sa ai gaba. To ko taya ya kake ganin zan iya dena tunani da shiga damuwa Ahmad?"
Mahaifiyar tasa ta faɗa ƙwalla na jiƙa mata fuska, har kuma lokacin bata fasa kallon saba kamar yacce shima bai fasa kallon ta ba.
Shi kanshi sheikh Ahmad wani irin raɗaɗi da suya yake jin zuciyar sa nayi masa.
Cikin sanyi ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Zaki iya denawa Ummi na, addu'a kawai zaki dingayi kamar yacce kika kasance kina yi abaya, sannan kuma aduk lokacin da zakiji abun na faɗo miki arai, to ki yawaita ambatar. *Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, lahaula walaƙuwwata illah billah! Allahumma ajirni fi musibati, wa'aklifni kairan minha! Hazbunallahu wani'imal wakil.* Da izinin Allah zaki samu sauƙin raɗaɗin da kike ji azuciyar ki tsawon shekara da shekaru, dan haka yanzu ki tashi mu tafi fallo wurin Abba da Kaka, sabo da idan kina zama cikin murtane shine bazaki dinga tinawa da abun ba akai-akai ba.
Ya ƙarshe maganar yana mai ɗaukar yatsun hannun sa ya fara ɗauke mata hawayen da suke kwance akan fuskar ta.
"Allah yayi maka albarka Yaro na, rabbi yasa kaima ƴaƴan ka suji ƙanka kamar yacce kake jin ƙanmu muma." Ta faɗa tana mai sakarwa Sheikh Ahmad murmushi, yayin da shi kuma ya miƙe tsaye yana mai sauka daga kan gadon fuskar sa ɗauke da murmushin shima, tukun ya sake miƙa mata tafin hannun sa ta riƙe sa, sannan itama ta sauko suka kama hanyar da zata sadasu da waje tare.
*JAHAR KAGUL, MASARAUTAR FULƊE.*
Sai da ta gama shawagin ta tare da abubuwan nishaɗin ta, tukun ta juya cikin takun ta wanda shi kaɗai abun kallo ne, tana mai kama hanyar da ta biyo.
Tayi nisa sosai tana shirin fucewa daga cikin wurin, sai ga wani mutumi nan mai kimanin shekaru arba'in ya dunfaro inda take da matuƙar sauri har yana ɗan haɗawa da gudu gudu.
"Ranki ya daɗe!" Mutumin dake sanye da kayan fulani rataye da sanda akafaɗar sa ya faɗa da ƙarfi, sabo da ganin da yayi tana shirin yin nisa, kasancewar shi ta ɓangaren kudu ya ɓullo wurin, saɓanin ita kuma da take yin gabas.
Juyawa tai baya dan taga ko wanene. Murmushi ta saki daga inda take sabo da fuskar da tai arba da ita, tukun ta koma jikin wata bishiya da take kusanci da ita tana mai jingina da ita tare da ɗaga kanta sama.
"Barka da warhaka kyakkyawar Gimbiyar Masarautar Fulɗe, Sarauniya kuma ga tsuntsayen Masarautar Fulɗe." Ya faɗa adai-dai lokacin da ya ƙaraso gaban ta yana mai durƙusar da kai ƙasa.
"Barkan ka dai amintacce na." Ta fada tana mai kallon sa itama, tukun ta ɗora da cewar. "Ya aka kwana ne, me ake ciki dan gane da binciken ka tun daga na jiya har kawo na yau?" Ta faɗa idanuwan ta ƙur akan sa.
Sake durƙusar da kansa ƙasa yay, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amsar dai duk itace take mai-maita kanta ya shugaba ta, ma'ana jiya da yau ɗin ma duk Duhu ne yake bayanna amai makon ganin wurin da yakasnce ashi, amma sai dai abu ɗaya dana sake ganowa shine, tabbas mutum ne shi ɗin ba Aljan ba." Ya ƙarashe maganar yana mai sake durƙusar da kai ƙasa. Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai juya baya ta fara taku daga inda take zuwa gaba, sai dai tayi yayi taku biyar, tukun ta tsaya cak awurin da take tana mai juyowa ta sake fuskantar mutumin nan da ta kira da Amintaccen ta. Sannan ta buɗe baki cikin kaushi tana mai faɗin. "Na riga na daɗe da sanin Giɗaɗo am mutum ne ba Aljan ba, dan haka daga yau bana buƙatar sake jin wannan daga gare ka, yanzu kai zaka iya tafiya, amma katabbatar ka ƙara azama wurin tayani binciken inda yake agaba, domin ko gaba ɗaya shine duniya ta ayanzu, sannan kuma ina jin muddin ban same saba to komai na iya faruwa dani." Ta faɗa tana mai rumtse idanuwan ta da ƙarfi.
"Insha Allahu zama asame sa nan kusa bada jimawa ba kyakkyawar Gimbiya."
Ya faɗa yana mai miƙewa tsaye daga durƙushen da yake, tukun ya juya yana mai sake bin hanyar da ya biyo yazo wurin.
Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal ta juya tana mai sake ɗaukar wata hanyar ba wacce take kan biba, fuksar nan ta ta aɗaure yarce kasan ba ita bace take aikin sheƙa dariya ɗazu ba.
Ba wata doguwar tafiya tayi ba ta ɓulla wani huri mai kama da daji-daji.
Gaban wani kogo dake jikn wata shirgegiyar bishiyar ɗorawa ta ƙarasa tana mai tsugunnawa, kana ta miƙa hannun ta tana mai janyo wani baƙin kasko aciki ta ajesa agefe, tukun ta sake zura hannu ciki, sai gashi ta ƙara janyo wata ƙatuwar gora wacce take cike da wani yellon ruwa itama ta ajeta kusa da kaskon, sake mai da hannun ta tayi ciki, wasu irin layoyi, tsummokarai da iccina ne masu matuƙar yawa ta sake zarowa aciki, kana suma ta ajesu agaban kaskon.
Buɗe gorar ruwan nan tayi tana mai tsiyaya yellon ruwan dake cikin ta acikin baƙin kaskon nan, sannan ta janyo wani tsumma mai matuƙar ƙura tana mai buɗe sa, wasu irin ciyayi -ciyayi tare da wata kalar ƙasa ne suka bayyana aciki, suma ɗibar su tayi ta zuba su acikin kaskon, kana ta ɗauki layun da suke awurin su kuma ta maƙalasu abakin kaskon.
Take ruwan nan ya fara juyawa da matuƙar gudu kalar sa na sauyawa daga yellow zuwa fari-fari.
Miƙewa tayi tsaye bayan ta ɗauki wata laya tare da wani icce ta rumtse su acikin tafin hannun ta, tukun ta rufe idanuwan ta da ƙarfi tana mai fara zaga wurin tare da buɗe baki cikin sauti tana faɗin. "Zaiba! Zaiba!! Zaiba!!!"
Wani irin hautsinawa ruwan dake cikin tukunyar nan ya farayi da matuƙar gudu, cigaba da furucin ta tayi cikin ƙarfi tana zaga kaskon, har lokacin kuma idanuwan ta arufe suke bata buɗe suba.
Wani irin hayaƙi ne baƙiƙƙirin ya fara futa daga cikin tukunyar yana mai tashi sama.
Dasauri ta buɗe idanuwan ta akan tukunyar tana mai zaro su waje tare da ja baya.
"Inaaa!!! Wallahi kai ɗin nawa ne ni kaɗai, babu wata mace da zata kasance mallakin ka aduka duniya bayan ni! Shin har sai zuwa wane lokaci ne zan gano inda kake ne Giɗaɗo am?" Ta faɗa da ƙaraji tana mai girgiza kanta, idanuwan ta akan wannan kaskon da yake futar da hayaƙi, tukun daga bisani ta ɗora da cewar. "Akan me zanga baƙin hayaƙi bayan farin ruwa nake buƙatar gani wanda zai hasko mun hanyar da zanbi zuwa gare ka? Akan me duk lokcin da naso gano inda kake abun baya yiwuwa? Shin me yasa kake bani wahala bayan babu wani abu da na taɓa so ya zamto mai wahala agare ni!" Ta ƙarasa faɗe da ƙarfi tana mai matsawa kusa da kasokon ruwan nan ta tuntsirar da shi aƙasa ya kife.
Sakin layar dake dunƙule acikin tafin hannun ta tayi hawaye na ɓallewa daga cikin idanuwan ta, tukun ta juya tana mai yin taku biyu daga inda take zuwa gaba, kana ta tsaya cak tana mai buɗe baki cikin kakkausar murya tace. "Ko ita ɗin wace ce, ko waye ubanta, koda ko tare kukazo gidan duniya da ita, muddin ya tabbata kuna soyayya dole ne kabarta kasoni ni kaɗai Giɗaɗo am!
Ni Gimbiya Haddiyal Ɗiyar Lamiɗon Masarautar Fulɗe nayi rantsuwa da mahallicin Shanu da Mutane sai ka zamto nawa, bazan taɓa gazawa ba wurin neman ka kamar yacce soyayyar ka baza ta taɓa yin gibi acikin zuciya ta ba, tabbas idan har tsafi gaskiya ne to ka sani zanyi amfani da wanda ya kasance acikin jiki na tun zuwa na gidan duniya domin na gano ka, haɗuwar bazata taɓa tsayawa cikin mafarki ba, tunda har na tabbatar da kai ɗin ba Aljan bane mutum ne kamar kowa." Ta ƙarasahe maganar muryar ta na rawa kamar ba itace ta fara ta ba akausashe, tukun daga bisani ta sake juyowa tana mai yowa wurin kaskon nan.
"Ina sonka Giɗaɗo am, kai ɗin ka zamto wani tsagi na daga tsagin zuciyar Haddiyal." Ta faɗa cikin sanyi hawaye na sauka daga cikin idanuwan ta, tukun ta durƙusa gaban kayan tsafin ta tafara haɗasu wuri ɗaya.
Sai da ta haɗe kansu tsaf, sannan ta mayar da su cikin kogon nan, kana ta tashi jiki atsan-tsar saɓule tana mai dosar hanyar da zata sadata da gidan sarautar nasu.
Duk inda ta gifta sai bayi sun zube suna kwasar gaisuwa, amma ko kallo basu isheta ba balle ta amsa, ahaka har ta ƙarasa cikin tamfatsetsen falon su kanta durƙushe aƙasa, ba tare da ta kalli kowa dake cikin falon ba ta doshi hanyar ɗakin ta kai tsaye.
"Haddiyal!"
Cak ta tsaya adai dai bakin ƙofar ɗakin nata da take shirin shiga sabo da muryar mahaifiyar ta data daki dodon kunnuwan ta, lokaci ɗaya taji wata irin faɗuwar gaba ta ziyar ceta, sabo da mahaifiyar tata bata fiye kiran ta da Haddiyal ba, sai idan zata faɗa mata wani abu mai muhimmanci ko kuma zata mata faɗa.
Cikin sanyi ta juyo tana mai kai duban ta inda tajiyo sautin muryar mahaifiyar tata.
Zaune take akan kujera yanzu hannun ta riƙe sa tufa tana ci, yayin da innahuro kuma take zaune agafen ta ta ɗora kanta akan kafaɗar mahaifiyar tasu tana cin inibi ita kuma.
"Gani Dadde na." Gimibiya Haddiyal ta faɗa adai dai lokacin da ta ƙaraso inda suke bayan ta samu wuri ta zauna itama.
"Me ya sameki ne naga idanuwan ki sunyi ja?" Mahaifiyar tata ta watso mata tambaya tana mai kafeta da idanu.
Uhm! "Dama.. Damm.. Fuffiken shale ne ya taɓan ido." Ta faɗa cikin in-ina tana mai sake sunnar da kai ƙasa.
Shiru mahaifiyar tata tayi ba tare da tace mata komai ba, sai idanu kawai da tacigaba da bin ta dasu.
Ta fannin haddiyal kuwa ta futar da tsamannin Dadden nata zata ƙara magana, sai daga bisani kuma ta tsunkayo sautin ta asama da yayi matauƙar hautsina zuciya da ƙwaƙwalwar ta tana mai faɗin. "Aɗazu bayan tafiyar ki Mahaifinki Lamiɗo ya shigo, yace in sanar miki atanadi madara da kayan itatuwa, gobe zakiyi baƙo ɗan Lamiɗon Masarautar Yamma zaizo batun auren ku, dan haka sai kitashi kije ki fara gyarawa!"
***
*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA*
Sai da suka tabbatar da tabar duka yankin, tukun suka dumfaro inda suka hangi Bir kwance cikin ƙasa da gudun su.
🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹
_*NA*_
UMAR FARUQ*D*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
*PAGE 05*
Durƙusawa sukayi ƙasa suna masu kamo sa, yayin da shi kuma yake ta faman juya kai har lokacin yana mai taune leɓen sa na ƙasa.
Ɗagosa sama sukayi ya zamto yana jingine ajikin su, tukun suka fara ɗaga ƙafafuwan su suna masu dosar kudu tare da jera masa sannu.
Sanye suke suma da fararen gajerun wandina na yadi kamar yacce shi ɗin ma ya kasance babu riga ajikin su, sai uban zanen tambarin masarautar tasu da ya kasance manne akan fatar su tako ina.
"Sannu ɗan uwa Bir, dama sabo da gudun shiga irin wannan matsalar ya sanya kullum nake ce maka kadena shigewa Gimbiya, amma sai dai kai ɗin ko kaɗan bakaji, to yanzu wa gari ya waya kenan, dubeka kaga yarce ka koma, gashi kuma kariga da kasan jibi -jibin nan ne ranar zagayowar bikin godiya ga Abun Bauta Gargabilu, kuma kasan muddin kana cikin BAƘAR MASARAUTA babu ruwan wani da larurar ka ko wace kalace ,sai ka ɗauki iccina har dai bikin godiya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 76